Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taja kujera ta zauna .ruwan tea kawai ta iya hadawa tana sha kamar tana shan magani kamshin turaran da taji ne yasata dagowa sadiq ne cikin uniform din shi yana riqe da briefcase din shi yasha kyau har ya gaji sai dai fuskar shi ba walwala angel ce ta gaishe shi ya amsa tare da yi mata pack, kallan shi fatuha take har ta kasa kauda idanuwan ta haka shima sadiq ita yake kalla tuni idanuwan ta sun cika da kwalla girgiza mata kai sadiq yayi alamar kar tayi kuka lumshe ido tayi tare da qoqarin hadiye kukan da ke niyar kuboce mata, sallamar majeed ce ta doki dodon kunan ta. ware ido tayi tana kallan kofar sanye yake da uniform din shi sai sheqi yake qarasowa yayi tare da gaishe da su mom amsawa tayi cikin fara'a, tare da cewa yasu umma? umma lafiya lau mom , sadiq d'ake tsaye take fara'a shi ta dauke daurewa yayi ya tataro natsuwar shi tare da sakin murmushin karfin hali, my man yau kai ne da safenan Sosa keya majeed yayi tare da kallan fatuha kauda kai tayi ta cigaba da juya tea din dan ba sha take ba.


Haka sadiq ya rinqa danne zuciyar shi, fatuha kuma haka ta gama juya tea din ta tashi tare da daukar school bag din ta ta ja hannu jidda suka fice tare da yima mom sai sun dawo .tana fita majeed yabi bayan ta haka shima sadiq kasancewar office zasu ,

Zata shiga mota majeed yace baki ji, daure fuska fatuha tayi dan wata tsanar majeed take ji juyowa tayi a fusace dan ta gayamai mara dadi hango sadiq tayi bakin mota da alama su yake kallo , kauda kai sadiq yayi yana wani jin suya a zuciyar shi da radadi bale murfin mota yayi ya shige, murmushi fatuha ta saki wanda iyakar shi laban ta tace uncle majeed inakwana, cikin zaquwa yace lafiya lau my love, cikin sunyi murya yace "Fatuha!" na'am tace a taqaice dan da kyar take mai magana saboda tsanar shi da ke bin zuciyar ta, nasan na maki laifi my love naje nayi abu bada sanin ki ba amma please kiyi hakuri wasu Sabin hawaye fatuha ta h'ade tace "Ba komai tana qoqarin bale murfin motar, idan dai kin hakura please ki bini nayi dropping din ki? daure fuska fatuha tayi dan bata jin zata iya bin majeed a yanzu, lagwabe kai majeed yayi yace please ki bani dama duk da nasan bani da mazauni a zuciyar ki,Am ma Dan Allah Kiyi hakuri kisoni koda kadane,tunda nataso bantaba samun yarinyar DA ta kwanta min a rai kamarki, fatuha please ki bani dama na gwada maki soyayyar da nake maki haka majeed ya rinqa magiya da kyar ya samu fatuha ta shiga motar shima sai da jidda suka shige ya ja motar.

Sadiq dake zaune cikin mota yana k'allan duk yadda suke ,da kyar ya iya saita numfashin shi, tabas yasan ranar da fatuha zata zama malakin majeed ba abin da zai hana shi zama gawa .da kyar ya iya bude baki ya ce ma driver ya jasu,ba musu yabi umarnin ogansa suka bar haraban gidan.suna zuwa wajen aikinsu SadiQ ya bude motar yafito tare DA daukar jakarsa ,ahankali yake tafiya kamar kazar DA kwai ya fahema aciki. Duk inda ya wuce ma'aikata Nata gaisheshi hannu kawai yake daga masu, domin jiyake bakinsa yayi masa nauyi. Yana zuwa office dinsa yabude yashiga ,yayi jifa DA breekfest dinsa ya zauna bisa kujira wani kuka ne ya subuce masa Mai radadi DA ciwo, jiyake duniyar nayi masa zafi,bai tab a sanin yana kaunar fautuha ba sai yanzu DA yake shirin rasata. Way majeed ! Me yasa zakamin haka? Me yasa kake Neman ruashemin farinciki na? Me yasa zakace kanason Fatuha alhalin nafika bukatarka a yan " DA karfin tsiya ya d'aki teburin d'ake gabanshi yace nooooo Fatuha tawace insha Allah wani murmushin karfin hal'i yayi (DA Ni Salma nakasa gane ma'anar hakan).

Majeed nayin parking a harabar makarantar Fatuha ta Kama murfin motar zata bude ,DA sauri ya Dana wani remot ya rufe koffofin motar ,cike DA tsiwa ta dubeshi suna hada ido dashi ta sunkuyar DA kasa, batasan meyasa majeed yake Mata korjini duk yanda taso yimasa rashin kunya suna h'ada ido zata nemi natsuwar ta tarasa. Murmushi majeed yayi yace, "Haba My love ,ya za'ayi kifita kibar mijinki DA tsananin tunanin ki? Ya kamata kifada min wata kalma DA zaisani tunanin ki koda Ina office plsss matata kada kice min aa". Takaicine ya lulube Fatuha ,banda iskanci gidan uban wa aka d'aura mana aure d'ashi DA har zai kirani matarsa taja tsaki a ranta mtsss ,a fili kuma tace " Plsss oncl kabarni natafi Dan Allah ta karasa maganar kamar zata Mai kuka" Sorry my lovely Zaki tafi amma Dan Allah Kiyi min murmushi KO Zan samu tsuwar zuciyata?" Fatuha tace a ranta "Dan iska shege mugu kawai Allah yasa zuciyar ka ya dawama DA bakinciki k'amar yand'a kak'e ko'kari'n sani". A fili kuma tayi murmushi DA iyakarshi lebenta, majeed ya b'ude masu kofa'r DA sauri ta fita tayi gaba, jeedah nako'kari'n binta majeed yaciro kudi masu yawa yaba jeedah shi kansa baisan KO nawane. tayi Mai godiya tare DA Mai piek a kumatu ta tafi DA gudu domin har Fatuha tayi Mata nitsa, shima majeed cike DA farinciki ya bar harabar makarantar....

*_Kuyi h'akuri da wannan page din, b'ana samun time sabod'a yanzu na k'oma skul._*


*Taku h'ar kullun salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM



79_80


Ko da fatuha ta shiga class ba wani walwala, haka su nana suka rinqa tanbayar ta "Ta fada masu meke damun ta?" amma firtaqi gaya masu damuwar ta, Nana ce tace, "Haba fatuha kenan baki daukemu a matsayin qawayan ki ba? da har zaki boye mana abun dake damun ki" Zara ce ta budi baki tace, "Kyale ta Nana ai dai mun san matsayin mu yanzu "Zara na qoqarin jan nana subar seat din , fatuha ta riqe Zara please kuyi hakuri, zan fada maku damuwa ta ida zancan hawaye na sulalo mata. duk abin ya faru haka fatuha ta kwashe ta fada masu, Zara taji haushi ba kadan ba haka suka rinqa bama fatuha hakuri tana raira kuka da kyar suka shawo kanta.


Bangaran majeed inbanda dad'i ba abinda yake ji ,zuciyar shi fes take d'aya lumshe ido kyakyawar fuskar fatuha yake hagowa sai ya qara sakin smile,


Jingine yak'e saman kujera office ya rasa sukunin shi, idanuwan shi na lumshe saboda nauyin da suka mai har wata masasara ke rufe shi ga qirjin shi dak'e mai zafi. a hankali ya ware sexy eye's ball's din shi da suka rine sukayi jaa wayar shi dak'e ruri cikin aljinhun shi ya curo sabuwar number ce baro baro a screen din, da kamar ba zai dauka ba sai ya daure ya dauka tare da karawa a kunne. Cikin zazakar muryata cikin yauki basma ta mai sallama, amsawa yayi a taqaice tare da tanbayar wake magana? gyara kwanciyar tayi d'aga inda take tare da kankame wayar dan wani irin sanyi ke ratsata, dan gyaran murya tayi cike da shagwaba tace, "Yaya sadiq ni ce fa basma? ko number ta ashe baka da ita? ta ida zancan cikin shagwaba" Sadiq d'ake kishingide saman kujera, ranshine ya qara suya dan shi duduniya ba macan dak'e birge shi ko bashi sha'awa kamar fatuha, ko wannan magana ma da take yi jiyake kamar tana watsa mai ruwan zafi, tsuke fuska sadiq yayi kamar tana ganin shi yace, "Yanzu ina wani aiki ne letter mayi magana in na dawo" be jira ce wata ba ya katse wayar tare da yin wurgi da ita ta dak'i bango ta dawo watse ko ta kanta be bi ba ya sa kai ya fice d'aga office din.domin idan ya cigaba da zama tabas kwakwalwar shi da zuciyar sa suna iya bugawa. bin wayar tayi da kallo tare da dan bata fuska , ta aje wayar ta kwanta.


Ko da aka tashi su fatuha majeed ne ya zo daukar su ,ganin shine yasa ta had'a gira sama data kasa dan ba abinda ta tsana kamar ganin shi. ba yadda ta so haka ta bale murfin motar ta shiga tare da gaishe shi, kallan ta yake me cike da so da kauna , sannan yace "My love d'aga gani yau kin sha wuya da yawa? ina fata dai kina kulla min da kanki?" dan guntun tsaki fatuha ta ja ciki ciki sannan tace a cikin zuciyar ta "Har wani Kira kake na kulla ma da kaina mtww dan iska kawai" muryar majeed ce ta doki dodan kunnan ta a karo na biyu yace "My love! ko duk gajiyar ce tasa ko magana ba'a San yimin?" dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi laban ta tace "A'a" murmushi majeed yayi tare da cigaba da driven din shin, haka ya rinqa janta da surutu tana amsa mai sama sama sannan ya wuce da su bakery yayi masu siyaya ice cream da cake. jidda ko sai dadi take ji dan har yanzu bata san inda aka dosaba.



Suna kunna hancin motar su. suka ci karo da sadiq wanda shima dawowar shi kenan wani irin dogwan numfashi sadiq yaja a duk lokacin da yaga majeed da fatuha, numfashin shi sai ya nemi ya dauke ko qirjin shi ya rinqa mai zafi. da kyar ya iya d'aga kafar sa dan baya so ko fuskar su ya gani sun fito a tare, amma sai dai kash majeed ya riga ya kira sunan shi. lumshe ido yayi ya tsaya chak! sai da ya kwashe yan mintina sannan ya waigo tare da sakin smile din karfin hali, ta gaban shi fatuha ta raba ta wuce jidda nata zuba mai surutu sannan itama ta shige, miqa mashi hannu majeed yayi suka gaisa, big man duk yau ban ganka a office ba oh ina cikin office ina wani aiki ne gobe ma nake so na wuce Lego's , Lego's kuma ?me zaka je yi loges? inji majeed zan je nayi 2week ne cikin ruwa na dawo , Eyya to Allah ya taimaka ameen yana qoqarin shigewa majeed yace, "Baby!" yes yace a taqaice dama ina so muyi wata magana ok mu shiga ciki ok majeed yace tare da bin bayan sadiq suka shiga part din sadiq briefcase din shi sadiq ya aje tare da rage kayan jikin shi ya shiga toilet, ya dade a toilet din beyi wankan ba yana kukan bakin ciki sannan ya tashi yayi wanka sanye da bathrobe ya fito qaramin towel a hannu shi yana goge jikin shi. majeed na zaune saman sofa shima tashi yayi ya shige toilet ya sheqa wanka ya fito ko da ya fito lokacin sadiq ya shirya cikin black 3 quarter din shi da white shirt mai gajeran hannu, yana zaune saman sofa idanuwan shi lumshe, shiryawa majeed yayi a tsanake sannan ya bude wardrobe din sadiq ya ciro riga da wando riga blue sai dark blue jeans sannan ya bude fridge ya curo fresh milk ya tsiyaya a cups ya miqama sadiq ya amsa, zama yayi kusa da sadiq yace, "Please ina so kamin taimako guda please?" ok inajin ka indai baifi karfina. murmushi majeed ya saki yace "Befi karfin ka ba" gyara zama sadiq yayi yana sauraran majeed riqe hannu shi majeed yayi cikin lagwabe kai please baby kamin hanya fatuha ta so ni .tsura mashi ido sadiq yayi da idanuwashin da suka cika da kwalla hadiye su yayi yana saurara majeed, baby wallahi ina san fatuha ban taba jin San wata ba kamarta ba baby karkayi tunanin irin sanda nake ma sauran yan'mata nea nake mata a'a santa nake da gaske wallahi inna rasata zan iya rasa rai na majeed ya fada. sadiq dai binshi yake da ido kamar sakarai gabaki daya jikin shi ya mutu sai zuciyar shi dake ta har bawa da sauri kamar zata fito waje ,dan matse hannu shi da majeed yayine ya sasa dawowa d'aga duniyar tunanin .smile ya saki, haba my man karka damu kaji dan jama aji take amma nasan zata so ka kaji Kasan yadda mata suke amma nasan zata so ka har ku dai-daita .murmushi majeed ya saki tare da kaima sadiq hug hawaye suka cigaba da yima sadiq anbaliya dan ko yasan ya rasa fatuha Dan baya fatan abinda zai samu majeed dan uwan shi abokin shi bashi da aboki dan uwa saman da majeed. lokaci yayi da ya kamata ya ba zuciyar shi hakuri jin majeed zai zame jikin shi yasa sadiq saurin share hawayan shin tare da sai ta kanshi murmushi suka sakar ma junan su, fira suka fara sama sama kiran sallah magrib ne ya tashe su,


*1week letter*

Shirye shirye aketayi a family house, kasancewa yau za'a sa rana biki duk wanda ka kalla cikin farin ciki yake musanman basma da majeed, zaune suke cikin daki'n yan'mata ana zuba hira muryar basma k'adai ke tashi fatuha na gefe tana matsar kwalla dan har yanzu gani take kamar wasa ,kamar mafarki tashi tayi ta fita dag'a dakin ganin kayan da ake ta wucewa da sune yasa jiki fatuha ya qara sanyi. fitowa tayi d'aga parlour hango qanan baban ta tayi su baba barau wasu hawaye masu zafi suka sulalo mata yanzu ta tabatar za'a Samata rana da wanda bata so a matsayin miji kuka ne ya ci karfin ta. fita tayi d'aga gidan gabaki daya dan ko sanin inda zata ba dan inda zata ba. can baba jinmai ta fado mata a rai kekenapap ta tara ta shige tace "A kaita gadan qaya" kasan cewar gidan baba jinmai kan titi yake bata wani sha wahala ba ganin gidan. kukan da take yasa mai kekenapap din bar mata kudin saboda ya tausaya mata ko sallama bata cika ba ta shige gidan, baba jinmai dake qoqari fita, fatuha ce ta fada jikin ta tare da sakin kuka kamar ranta zai fita. rudewa baba jinmai tayi tana kallan ta baki sakรฉ, zaunar da ita tayi saman kujera tana tanbayar ta lafiya? kuka take sosai, cikin shasheqar kuka tace "Wallahi baba bana san majeed bana jin zan iya zaman aure da shi ta ida zancan tana rushewa da kuka" sallati baba jinmai ta hauyi tare da tafi na Shiga uku ni jinmai , me nake ji haka fatuha sokike ki ja mana abin fade ?toh in ba majeed din ba wakike so? kuka ta kuma saki cikin shasheqar kuka bakin ta na rawa tace "Baba sadiq nake so! wallahi ina rasa sadiq mutuwa zanyi" ta ida zancan tana kuka mai tsuma zuciya, zaro ido waje baba jinmai tayi na Shiga uku ni jinmai. rungume fatuha tayi tana lalashi dan ita kanta ta tausayama fatuha ita kanta taso ace da sadiq din za'ayi ,amma ya zasuyi tunda shi be ce yana so ba? d'ago da fatuha tayi tana share mata hawayan ta kiyi hakuri fatuha kinji ki cigaba da addu'a Allah yana tare dak'e Allah zai dubi zuciyar ki ya baki mafi alheri fatuha kisama zuciyar ki sallama kinji .ajiyar zuciya kawai take saki tayi lamo a jikin baba jinmai.


In banda tari ba abinda yake har wani jiri yake gani ,majeed d'ake gefan shi sai sannu yake mai. toilet ya shige da sauri yana cigaba da tarin gaban zing kallan mirror d'ake manne jikin zing din yayi jini da ya ganine gefan bakin shi ya sashi zaro ido! hannu ya kai ya taba ganin kamar jinine yasa gaban shi ya qara faduwa hawayan dake maqale a idanuwashi suka sulalo.zamewa yayi a qasan toilet din yayi yana mai da numfashi sama sama miqewa yayi da sauri ya fito duk da yana jin jiri .majeed dak'e zaman jiranshi ne ya ta shi yana mai sannu ko amsa mai sadiq ya kasa, wardrobe din shi ya bude ya janyo trolley ya fara zuba kayan shi yana zubawa jiri na dibar shi ga tarin sai zuwa yake tare da jini amma duk wannan abun yaki yadda majeed ya gane sai da ya gama had'a kayan shi tsaf majid na gefe tsaye riqe shi yayi yace "Baby wai me ke faruwa ne? naga muna lafiya lau lokaci daya ka rude" murmushi yayi yace "Karka damu tunawa nayi da flight dina na zuwa Lego's yau zai tashi kuma gashi saura 10 minutes ya tashi" ok muje nayi dropping naka ka barshi kawai nayi ma driver magana kaji? ok ya ce mai tare da yi mai pack sannan ya sa kai ya fita da kyar ya iya jan trolley ya fita waje yana tafiya yana tari tunkan ya qara so ashuru driver ya bude mai murfin mota amsar trolley din yayi yasa a boot sadiq yana Shiga mota ya fara b'ale bottle din rigar shi saboda zafi ga numfashin shi d'ake daukewa yana dawowa. ko da ashuru driver ya shigo mota ja yayi suka bar harabar gidan ta cikin mirror ya fara ganin halin da sadiq yake ciki. yallabai! yace a tsorace cikin murya da kyar da kyar sadiq ya iya furta kaini wajan Dr yakub aiko da gudu ashuru ya fisgi mota sai asibitin Dr yakub suna Isa asibiti sadiq ya bude murfin motar duk da yana ganin jiri ga numfashin shi dake mai sama sama office din Dr yakub ya nufa yana bude kofar ya fadi sumame a wajan...๐Ÿ™†โ€โ™€๐Ÿ˜ฐ

Muje zuwa fan's

*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
[6/29, 7:58 PM] โ€ช+234 803 478 2721โ€ฌ: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


81_82

Mikewa Dr yakub yayi dan kawowa sadiq taimakwan gagawa. gabaki d'aya shima ya rude kwalawa norses kira ya shiga yi da sauran ma aikatan asibitin kafi kace me har an daura sadiq a gadan asibiti ,ashuru driver da shigowar shi yanzu ya gani bin gadan yayi yana matsar kwalla, ba'a zame da sadiq ko ina ba sai emergency, ashura na ganin hak'a ya ci birki bakin kofar yana zarya yar wayar da ke aljihu shi ya zaro dan ya kira gida amma sai dai wayar ba chaji kuma bai iya tafiya ya bar sadiq a yanzu dan ana iya buqatar wani abu. h'aka ya rinqa zarya baki'n kofar ga baki d'aya ya rude.


Hak'a baba jinmai ta rinqa lalashin fatuha sannan tayi shuru, fatuha tashi kiga mu koma tunda dai kin san aiki na can na jira na ? matsar kwalla ta fara cikin sanyin murya tace "Dan Allah baba ki barni a nan wallahi bana san zuwa, bana san jin hayaniyar kowa! mudin na cigaba da ganin abinda ake a gida ina iya shiga wani hali" duk yadda baba jinmai taso ta tafi da fatuha firtaqi ba yanda ta iya shiya ta barta ta tafi ko da baba jinmai ta fita kuka fatuha ta dasa.


Shewace ke tashi yadda kasan yaune daurin auran. zuhura ce ta shigo da sauri ta fada jikin basma tare da cewa "Ansa biki wata d'aya" washe baki basma tayi tare da curo wayar ta fara kiran sadiq duk wannan kira da take ba'a dauka ba tabe baki tayi tare da cewa duk kayi ka gama aure sai munyi duk wulaqanci da kake zubamin bashi zai sa na daina san ka bรข,ta ida maganar tare da jan dan guntun tsaki, hanan ce tashigo jiki a sanyaye basma ce tace "Ke kuma lafiyar ki kuwa?" wallahi tun dazu nake neman fatuha a gidan nan narasa inda ta shiga? na kira wayarta yafi aqirga" toh fa! dazu dai tanan cikinmu har tace min "Kanta na ciwo na bata magani, namayi tunanin bacci tayi?" ok qila ta koma gida. amma bari inmun gama abinda muke sai muje ko? eh gaskiya sannan hanan tasa kai ta fita.

Bangaran iyaye angama komai inda mom ta yanke shawarar basma ta koma can gidan yadda za'a ji dadin kula da amaran. waje daya kuma kowa ya amince da shawara.


Haka doctors sukayi cha a kan sadiq dan ceto rayuwar shi inda suka ci sa'a ciwo zuciyar bai dade da kamashi ba, daya sha magunguna yadda ya kamata zai warke sai da yama likis aka fito da shi. ashiru yabi bayan su aka ba sadiq daki, har lokacin sadiq na kwance yana bacci sai qarin jini dak'e mai wanda doctor yakub ya bada nashi, ashiru zama yayi d'aya dag'a cikin kujerin dakin sai da ya dan jima sannan ya wuce office din Dr .ko da ya shiga lokaci yakub ya fita ganin wasu marasa lafiyar haka ya wuce gida dan sanar masu halin da sadiq yake ciki.

A hankali yake ware sexy eye's ball's din shi da yamai nauyi, bude kofar akayi a ka shigo ba kowa bane sai Dr yakub qarasowa yayi gadan tare da zama gefe a hankali ya kai hannu goshin sadiq har yanzu da zafi rau cikin sanyi murya Dr ya fara magana "Captain me yasa kake wahalar da zuciyar ka da tunani tuntuni? nayi tunanin ka daina tunani amma yanzu ka dawo da shi ?sadiq har kaja ma kanka ciwo zuciya" lumshe ido sadiq yayi kawai yana sauraran Dr. na rasa wanne irin tunani kake wannan sadiq? ciwo nan da kake gani yana iya jama ka rasa aikin ka sadiq, da ace asibitin mu ka je ai da yanzu an farama shirin sallama. rike hannu sadiq yakub yayi tare da sake cewa p"Please ka fada min damuwar ka please sadiq?" hawaye ne masu zafi daya ke bin daya a fuskar sadiq shi kan shi yakub ya firgita da yanayi da sadiq ya koma yanzu, cikin sanyin murya Dr yace "Tunda baka iya fada min ya kamata a gida a san damuwar ka ya fadi hakan yana qoqarin fita" riqe hannun sa sadiq yayi tare da ware idanuwashi da suka zama ja y'a ce "Please karkamin haka Dr bana fata kowa yasan abinda ke damuna a yanzu please kamin alqawarin baza ka fada ma kowa ba?"zame hannun shi Dr yayi dan baya jin wannan karan zaiyi shuru .har ya kai bakin kofa sadiq yace " Dan Allah karka fadi please ya ida zancan yana kuka mai cinrai" chak Dr yakub ya tsaya dan gabaki daya tausayin sadiq ya lulube shi dawowa yayi da sauri saboda tarin da yake taimako gagawa ya bama sadiq tare da yimai allura samun hutu. ya fita ko da ya shiga office ya kasa zaune ya kasa tsaye yana tunanin inda matsala sadiq take dan yanzu ya lura ko yasha maganin indai zai cigaba da tunanin da yake zai zama anyi ba ayi ba.


Ko da ashiru driver ya koma gida har yanzu basu dawo ba, suna family house juya wa zaiyi da motar ya wuce family house kenan, sai ga fatuha mai kekenapap ya ajeta ta fito sukuku ba alamar walwala dan itama a tunanin ta sun dawo. ashuru ne yayi parking tare da qarasowa ida take gaishe shi tayi a taqaice tana qoqarin shigewa gida, fatuha "Na'am" tace tare da waigowa dama dama gaban tane

Please Login or Register in order to submit comment