Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…

*Email*:[email protected]
*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R
27_28

Misalin karfe 5:00pm motar su fatuha ta tsaya a tasha lokacin har bacci ya dauke ta tana kafadar baba jinmai rungume da jakarta gari yayi zafi.ahankali baba jinmai ta shiga tashin ta.. Aiko nan tatashi tanayin wani wiqi wiqi da ido da qarewa tashar kallo. mutanene birjik..haka suka zuro kafafun suka fito daga motar. Baba jinmai ce ta zaro wayar ta cikin zani. y'ar baby nokia ce. bugu daya biyu' mom ta dauka. washe da baki baba jinmai da cewa.. "hajiya gani na iso ina tasha...daga bangaran mom murmushi tayi ta ce.. "masha Allah yanzu zan aiko driver ya dauke ko'... "Toh hajiya. Sannan ta katse wayar tana Murmushi ta kalli fatuha.. Yanzu za'a zo daukar mu kin ji yan'nan. kada kai fatuha tayi dan ita a wannan lokacin haushin kowa take ji ...


Ba'a fi 30 minutes ba driver ya qaraso tare da kwashi kayan su ya zuba cikin mota inda yayi yayi da fatuha ta bashi Jakarta ta qi ba yanda ya iya haka ko suka tafi


Kai tsaye sultan road suka wuce nan fa fatuha ta fara zare ido tana qarewa unguwar kallo kamar wanda ta zo aljana haka take gani... Washe baki tayi ta juyo tace... "Baba jinmai dama ashe aljanna kike zuwa... Baba jinmai dariya tayi ita da driven tace.. "aa fatuha nan ba aljanna bane birni kenan... "kai amma kwarankwatsi kinyi da kika zo dani dafa tare da fatsima kikaso zuwa ko... "ke da kikaita kuka baki san zuwa' "Qur'an yanzu ina san birnin.. ๐Ÿ˜ƒ ta'ida zancan lokacin yayi dai dai da isowarsu katafarin gate din gidan Alhaji Ibrahim. Zanso kuga yanda fatuha ke zarar ido ๐Ÿ˜‚


Dai dai parking space su kayi parking baba jinmai ta kwaso masu kayan su fatuha dai na maqale da ledar ta, ta gari yayi zafi


Katafaran parlourn gidan suka shiga. Qauyanci wajan fatuha ba'a magana dan ko zama taqiyi saboda tayals sai da baba jinmai tayi da gaske sannan ta zauna saman carpet tana ta zara ido


Mom ce ke saukowa daga upstairs cikin murmushi tace... "ah sannu da zuwa baba jinmai tare da qarasowa parlour da zama saman two star tana facing din su baba jinmai d'in, "ya hanya. Tace da ita tana murmushi.
Alhamdulillah, baba jimmai tace.. "oh tare da yarinyar kuka zo kenan gaskiya naji dadi.
"fatuha dake rabe jikin baba jinmai ta gaida mom cikin girmamawa " baba jinmai ce ta washe baki tace... "Ai diyar qanina ce jauro,
"a'a ki ce min yar tashi ta yi girman haka ' "aiko dai hajiya.. Sunyi hira sama sama inda fatuha ke rabe jikin baba jinmai tana qarewa gidan kallo tare da santinsa



Lafiyayan abinci mom ta basu shinkafa da miyar kaji wadda taji kosulo.. kauyanci ko wajan fatuha ba'a cewa komai saboda bata tab'a cin irin abinci ba dan haka ta saki tinbi ta ci har da side kwano da qari... Baba jinmai dadi taji dan taga fatuha ta saki jikinta


Bayan sun gama cin abinci mom ta kai fatuha dakin jidda ta gwada mata toilet da duk yadda zatayi anfani da komai na toilet din tare da Ciro mata uniform din yan'aiki farar Riga da skirt dai dai gwiwa
ba laifi fatuha duk abinda mom ta gwada mata haka tayi..
wanka sosai tayi da dirje jikinta tare da wanke kanta da shafo .masha Allah gashin fatuha har gadan baya sai dai rashin kulla da shine yasa duk ya cure gu daya amma hakan bazai hanaka ganin kyan gashin ba. daure da towel ta fito.. Mom na zaune saman sofa tana jiran fitowar ta. Koda ta d'ago kanta mom d'in. tayaba kyau irin na fatuha. Hakan yasata yin murmushi..
ita ko saitahau sunne kai.
"Ah har kin fito..
D'aga mata kai tayi alamar Eh , uniform din mom ta dauka ta bata' ga wannan kayan kullun su zaki rinqa sawa akwai su da yawa cikin wardrobe ranar Friday ne kadai zaki sa kayan gida suma akwai su cikin wardrobe. na ki kuma anfidda su waje sannan in kayan sunyi dati ki aje su akwai mai wanki zai wanke maki su ya goge.. Washe da baki fatuha ta ce, "toh


Mom har takai bakin kofa ta dawo tare da cewa, "gobe ki shirya za'a kaiki wankin kai.. "to tace tare da yima mata godiya.. mom na fita ta shafe jikin ta da mai tare janyo kayan da mom d'in ta aje mata a saman gado farar rigar ta fara janyowa ta saka amma sai da tasha wuya sannan ta iya balle mab'allin rigar.. Saidai dai dai gwiwa rigar ta tsaya mata. "Kwarankwatsi gidan ga gidan yan'iska ne yo jifa yadda rigar ta min, skirt din ta janyo ta sa tana sawa taga ya tsaya a gwiwa shima..kut amma Qur'an mutanan sun rainani yo in ban da iskanci haka zanbi gari qafafu bude tap bilahilazi ban fita haka guri ta samu tayi zamanta tana ta kunfar baki tare da jero Allah ya isa


Mom dake zaune parlour jin fatuha shuru bata fitu ba yasa ta leqo dakin zaune ta same ta har bacci ya fara neman dauketa saboda gajiyar tafiya. tab'ata tayi tare da cewa "Fatuha... Nanta ware manyan idanunta.. mom tasakar mata murmushi, "hala kin kasa sa kayan tashi kiga yadda ake sawa.. nan mom ta shiga gwada mata masha Allah kayan sun mata kyau duk da fatuha tsine wa kayan take a zuciyar tare da jin haushi kayan


Bayan mom ta gama gwada mata ta bata dankwali ta refe kanta ruf kamar wadda tayi acuci yadda kan ya gwada sannan ta taja ta suka je parlour suka zaune saboda Sadiq sun fita da jidda shan ice cream



Bayan sun gama shan ice cream suka biya shop rite ya siya wa jidda new Teddy's masu kyau da kayan wasa jidda ko sai murna take a gajiye suka dawo gida . Sadiq na dauke da jidda a hannu shi yana mata cakulkuli tana dariya *ola* na bayan su riqe da kaya cikin sallama suka shigo.. mom na zaune tana kallo fatuha na gefan ta a takure,a ahankali Sadiq ya qaraso jidda na maqale a jikin shi ya kai room pack, mom ce ta murmusa tace, "baby har kun dawo... "yes sweet voice din Sadiq ne ya doki dudan kunnan fatuha ta waigo baki bude tana qare mashi kallo shi da jidda sakin baki tayi a zuciyarta tace dama ashe ina da raban ganin yan'. makka kai baba jinmai kwarankwatsi kin dubamin , duk wannan zancan da take idanun ta na kan su jidda , dagowar da Sadiq zeyi su kayi 4 eye's harara ya wurga mata tare da kauda kanshi, "mom wannan wacece.. murmushi mom tayi tace "wadda zata rinqa kulla da jidda diyar qanin baba jinmai ce. kallan fatuhan yayi wadda ke kallan su bata dauke ido ba harara ya qara banka mata sannan fatuha ta Ankara ashe harara yake aika mata aiko itama ta fakaici idan mom ta banka mai harara har da murguda mai baki, nanko ya saki baki yana mamakin wannan wacce Mara kunyar mai aiki ce mom ta samu wadda bata da kunya a fusace ya tashi ya ce, "keeeee!! Ni sa'an kine.. mom da ke zaune ta ce "Sadiq lafiya yarinya na zaman zamanta ka fara yi mata bala'i ka bari mana ta kwana biyu sannan ka nuna mata bakin halin naka wai me yasa kake haka ne baby. mom fada ta mai sosai cikin zafi rai ya bar parlour sannan ta shiga ba fatuha hakuri fatuha washe da baki ta ce "ba komai, mom ta gwada mata jidda ba qaramin dadi fatuha taji ba zata kulla da balarabiya bayan mom ta gama yi mata bayani sannan taqara mata da batun zata riqa gyara part din baban jidda sosai.. fatuha taji dadin hakan.
a cikin zuciyar ta kuwa cewa ta ke Qur'an daba balarabiya ba ce da wallahi bani kula da Ita.. Shi kuma wancan balaraban ni zaiwa iskaci wai dan yana da kyau. Qur'an gyara mai zama zanyi bilahilazi duk wannan maganar tana yin tane a cikin zuciyar ta




*Tah ku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…


https//,mobile.facebook. com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&_yn_=H-R


*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



29_30

Mom ce ta haura upstairs ta bar jidda da fatuha zaune a parlour ,a hankali fatuha ta matso kusa da jidda washe da baki tace "Ya sunnan ki?" smile jidda tayi tare da fada mata sunan ta, sun dade a parlour zaune sannan jidda ta ja fatuha suka koma bedroom din jidda, jidda ta fara kwaso wa fatuha kayan wasa, washe da baki fatuha ta amshi teddy, kai Al Qur'an birni dadi garai yanzu sabida Allah ji wanga halita duk wasa ake da ita kai jama'a, jidda ce ta katse mata zance da cewa" Anuty garin Ku ba wannan teddy ne? nima daddy ke siyo min" dariya fatuha ta fashe da ita ke kekika san wani Daddy mtsss, kuma me Anuty da tedil (teddy) , jidda dariya tayi tace Aunty ba sunan shi tedil ba sunan shi teddy ,Anuty kuma in mutun ya girme kane sai ka rinqa ce mai Anuty, aiyo ai mu a kauyen mu yaya ake cewa ko gwago, Ah wanga suna Qur'an dadi garai haka birni ya ke, jidda dai washe baki take tayi ta samu yar'uwa kamar ta me shegen surutu.


Haka suka rinqa zuba hira tare da wasa ita dai fatuha, zuciyar ta fes dan a ganin ta ta samu gurin zama kiran sallah magrib ne yasa suka tashi fatuha tayi alwala tare da jidda sannan suka fito Dan gabatar da sallah.


Bayan sun gama sallah suka dawo parlour, parlour ba kowa sai baba jinmai da ke ta jera abinci ita da rabi'a washe da baki fatuha ta gaida baba jinmai da rabi'a, baba jinmai ce tace, "Ah fatuha anware kenan?" dariya kawai tayi , um ga abinci nan in kuna jin yunwa Ku zo Ku ci ki tabatar kin ba jidda ta ci ta koshi inji baba jinmai, toh kawai fatuha ta ce mata sannan baba jinmai da rabi'a suka shiga kitchen.

Kamar jira take su shige tayi tsale ta haye kujera dining area da kyar ta iya bude kulolin farfesun yan'ciki ne sai dafaifan doya da miyar kifi, tunkan ta fara ci miyan tbakinta ya tsinke, zubawa ta fara yi sai da kwanan ya kai har baki sannan ta tsayar da zubawa, jidda ko sai zaro ido take tana mamaki irin ci na sabuwar Anty ta,
lol.


Washe baki tayi tace, "Yauwa jidda sauko muci dan Qur'an ban iya ci a saman wannan abin , haka ko akayi suka sauko qasa suka fara ci, fatuha na ci tana zaro ido saboda dadi kuma ba wai qaramar loma take ba haka zata dauko doya biyo ta turawa kanta ta kuma turawa jidda.




Zaune yake saman sofa da alama daga wanka ya fito, shafe jikin shi yayi da lotion mai kamshi, yana gamawa ya feshe jikin shi da turare mai sanyi dadi wardrobe ya bude ya ciru 3quarte black sai fara t-shirt hannu rigar dai dai tamatsa ba qaramin kyau yayi ba gashin nan nashi ya kwanta abin sha'awa, ahankali ya kama handle din kofar part nashi ya fito.



Cikin natsuwa yake sakowa daga upstairs, sanye yake da bakin Sweet yayi matsifar yi masa kyau, fatuha da jidda na zaune a kasa ga plate ร  gabansu sai loma fatuha ke tura wa jidda, dan ita har ta koshi kuma da hannu take bata abincin, a fusace sadiq ya qaraso tare da dakawa fatuha tsawa "Keeee! Are you mad, your very stupid" futaha ko ware ido tayi washe da baki ta kalle shi tace, "Tap kai ka san wannan gwalangwatsin Qur'an" sannan ta cigaba ta dirkawa jidda doya jidda ko sai amsa take hankali kwance, lumshe ido sadiq yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi daka mata wata tsawar yayi ya ce, "Dan ubanki baki jin nane? uban waye yace kiyi feeding din angel ba spoon eeeh?" Turo baki gaba fatuha tayi tace, yo ni ban san inda fida (feeding) take ba ashe ba'a yaye taba Qur'an ban sani ba, sannan fatuha tace da jidda shine kika saki tinbi ina ta dirka maki abinci ,to ta yaye kanta sai ka zubar da fida(feeding)lol.


Wani irin baqin cikine ya turniqe sadiq ya qara wurga mata harara , aiko itama ta rama, yo ankan me mutun tunda na zo gidan su sai aika min hararata yake, ba Dan nayima Hajiya Alkawari zan zamna da ita iya wuya ,da sai nace banyin aikin ko ana dole ne ,kama gode wa Allah saboda Kuna kama da larabawane shiyasa na tsaya da bilahilazi da tuni nayi tafiya ta aha, tare da gyara tsayuwar ta, sadiq ko baki ya saki yana mamaki irin wannan iskancin ta, tsawa ya kuma daka ma fatuha wadda tasa yan'hancita katsawa dan ubanki ni sa'an kine eeeeeh ido fatuha ta qara zarowa, sannan ya nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi duk sanda na qara magana wannan dan banzan bakin naki ya maida min sai na fasa shi, ya qara wurga mata harara sannan ya sa hannu ze dauki jidda, ihu fatuha ta saka hakan yasa sadiq juyowa yana mata kallan wulaqance, Qur'an ba inda zaka da balarabiyannan kwarankwatsi, ko na fada ma hajiya tunda ita ta bani ita, dariya abin ya kusa ba ma sadiq amma sai ya daure ya wurga mata harara.


Mom dake bedroom taji ihu fatuha hakan yasa ta fito da sauri, ganin sadiq dauke da jidda fatuna na gefe tana ihu yasa mom qarasowa, harara ta aikawa sadiq tare da cewa, "Lafiya fatuha? me kuma ya miki?" turo baki tayi ta ce, "Yanzu saboda Allah hajiya ba ke kika bani wannan balarabiyar ba, na kulla da ita , to shine wai daga yaga ina bata abinci ya hau zagina har da ce min wai feda take sha" hajiya ko dariya abin ya bata saboda ta gano abinda fatuha take nufi, sannan fatuha tace, "To shine hajiya yasa hannu ze dauke min ita Qur'an ban yadda ya maido min abuta" hajiya ta washe baki tace "Yi hakuri fatuha ai baban tane shiyasa" aiyo toh shine hajiya be iya fada min dan girman Allah, ki ce ya ban yarinyar dan Qur'an Santa nake tare da matse kwalla, mom ko dariya abin ke bata sadiq ko mamaki abin ke ba shi yau shida diyar shi za'a mai qarfin hali.


Toh shikenan sadiq bani jidda in ta mata wanka sai ta kawo ma ita ai shikenan anraba rigama ko fatuha, sadiq bata fuska yayi ji yake kamar ya shaqe fatuha dan haushi.


Haka sadiq ya miqa wa mom jidda tare da haurawa sama, sannan ya dau alwashin sai ya gyarawa wannan yarinyar zama dan yaga alamar da rashin kunya tazo.



Fatuha ko washe da baki ta amshi jidda, jidda ko sai raba ido take gashi cikin ta ya cika dam kamar yayi magana.....




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…

https//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial&_yn_=H-R


*Email*:[email protected]


*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITRESFORUM.com



*rip rip this page is for you my lovely one so enjoy the page this na for u no be so*๐Ÿ˜‰


31_32

Washe da baki fatuha ta amshi jidda ta wuce da ita bedroom ta cire mata kaya direct toilet ta shige da ita sai da ta wanke jidda tas sannan suka fito.


Ah bilahilazi birni tayi yanzu dubi sau biyu ina sab'e ki , jidda ce ta washe baki ta ce "Anuty daddy ban san dati shiyasa" always yake min wanka yayi ma kanshi um tabe baki tayi tace yo ke ki kasan wannan, washe baki jidda ta kuma yi tace baba na fa nake nufi Anuty aiyo wai wannan baban naki ai dole yake wanka daga ganin shi ya cika tsirfa daddy nawa, um ke ni wani mai ake shafa maki in anmaki wanka smile jidda tayi ta dauko mata lotion din ta mai kamshi fatuha ta amsa, ah'ah wanga farin mai haka fa yo ai wannan kamar turare ne jidda ce ta fashe da dariya tace Anuty ba turare bane maine ga turare na chan saman dirss mirror Wanda daddy ya siyo min a uk, tir qashi me kuma uk, washe da baki jidda tace wata qasa ce haka a'a shi baban naki har shawagi yake qasa qasa tap kinga matso na shafe ki da mannan kar yaji shiru ya zo ya min tijara dan na lura dan ta kife ne baban naki ,haka ko ta shafe jikin jidda da lotion tare da anyana man a ranta ita ma ta gama shafa basilin dan ita yanzu ta zama yar birni.


Sai da ta gama shafe jidda da mai tsaf sannan jidda ta gwada mata inda night dress din ta suke kar ku ga abu komai fatuha ta gani sai ta mai sharhi bayan ta gama shirya ta tsaf, sannan ta dauke ta dan kai ta dakin baban nata Wanda tayi ma laqabi da sangami.


Direct part din Sadiq suka wuce a hankali ta murda handle din kofar ta shiga , jidda tana ta zuba mata surutu, tana shiga parlour ta saki baki da hanci bata san sanda ta dire jidda ba a qasa wani irin sanyi dadi ne da kamshi ya doki hanci ta kasan cewa sadiq mutun ne mai san sanyi da kamshi shiyasa part din shi yafi na kowa sanyi a gidan, washe baki tayi tana qarewa parlour kallo saboda iya kar haduwa parlour ya hadu.


Jidda ko bedroom ta shige da gudu lokaci sadiq ya fito daga wanka, sanye yake da bathrobe hannu shi riqe da towel yana goge gashin kan shi jidda ta ruga ta rungume shi daddy wani irin murmushi ya saki tare da shagwabe fuska, um ni fushi nake da angel tare da daukar ta ya zaunar da ita saman bed shine saboda kinyi new Anuty kika manta daddy ko angel, shagwabe fuska ita ma tayi tare da daura hannu ta saman cheek din sadiq sorry daddy ta marairai ce kamar za tayi kuka ,dariya yayi tare da fara yi mata cakulkuli, dariyar su jidda ta ankarar da fatuha washe da baki ta nufi kofar bedroom ta bude a hankali ta shige, zaro ido tayi waje tana kallan dakin baki bude kai Amma wanga gida ya hadu kwarankwatsi yanzu gobe ni zan gyara wanga gurin , baki ta qara washe wa duk wannan maganar tana yin tane cikin zuciyarta, sadiq dake ma jidda cakulkuli tana dariya jin kamar an bude daki an shigo yasasa da gowa a hankali , ya sauke sexy eye's ball's din shi kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata ita dinma shi take kallo tana aiyana irin kyau na sadiq tap amma dai sangami ba qaramin kyakyawa bane Qur'an, washe baki ta kuma yi tace "Amma fa sai bakin rai kamar fir'auna tir da wannan hali wallahi ga kyau ga bakar zuciya, ko da yake na kusa maganin shi ai, daka mata tsawar da sadiq yayi ne yasa ta dawo daga dogon tunanin da take tayi wiqi wiqi da ido, ur are very stupid ina maki magana kin yi shiru ehhh ?are u deaf or what tsawar da sadiq ya daka wa fatuha har wani fitsari taji ya taho mata gadan gadan ganin yana nufo ta yasa ta bude kofar tafita dakin da gudu sai da taje dai dai kofar parlour ta bude baki yadda zai jita tace Allah ya isa mugu kawai sannan ta bude kofar ta ida fita a guje sadiq dake bakin kofar bedroom yana jin ta lumshe ido yayi yana jin wani irin tsanar fatuha na ratsashi da mamakin rashin kunyar ta ,a hankali ya ja jikinsa ya koma saman bed lokacin jidda har tayi bacci shima kwantawa yayi tare da kara masu gudun AC ya ja masu blanket.


Tana isa daki ta kulle da makuli gudun kar sangami ya shigo wato sadiq toilet ta shige da gudu tayi fitsarin data matseta saboda tsabar tsawar da sadiq ya daka mata shi ya haifar mata da fitsari dole, tsoki ta ja tare da cire kayan jikin ta tayi wanka sai da ta wanke jikin ta tas sannan ta dauki karami'n towel ta daure ta fito, rigar baccin da mom ta gwada mata ta Ciro ta sa duguwar riga ce pink mai manyan follows milk rigar ta wuce gwiwa ba qaramin kyau tayi ma fatuha ba, ita kanta sai da ta yaba kyan rigar sannan ta kwanta saman bed tare da janyo blanket ta lulube ko 2 minutes ba tayi ba bacci ya sureta.


Asuba ta gari, tsaye yake gaban dress mirror yana shiri cikin uniform nashi kasan cewa yau Monday ba qaramin kyau yayi ba kofar bedroom ya kalla tare da jan tsaki sannan ya kalli bed jidda na bacci.


Fatuha ko yau bacci har da munshari ba ita ta tashi ba sai 6:00am, cikin sauri ta tashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka ko mai bata tsaya shafawa ba tayi sauri ta zura uniform din ta kasan cewa mom ta fada mata jidda na zuwa school yasa take shirin cikin sauri cikin sauri ta nufi part din sadiq dai dai bakin kofa ta tsaye gaban ta na dukan uku uku saboda ta tuna artabun da suka sha da sangami jiya kawai shahada tayi tare da qundun bala ta bude kofar ta shiga tarรฉ da yin sallama, ba kowa parlour hakan yasa ta murda handle din kofar bedroom sadiq ta hangoshi tsaye gaban dress mirror a hankali ya dago sexy eye's ball's din shi wani irin kallo ya wurga mata tare da jan tsoki, cikin tsawa ya ce "Yanzu ne time din da ya kamata ki shigo eeh? baki san tana zuwa school bane, koko rashin sanin muhinmanci ilimi yasa kika zauna baki zo ba eeh? nuna ta yayi da yatsa yace as from to day karki qara kai wannan time din baki zo ba stupid girl kawai" duk da bata san Kalmar da ya fadi aqarshe ba amma jikin ta ya bata zagin ta yayi sai da ta fakaici idan shi sannan ta bala mai harara tare da daukar jidda daga saman bed zata fita da ita har ta kai bakin qofa, ya kara daka mata tsawa yace "Kin makarar da ita? yanzu Kuma ina zaki kaita? oya wuce ki mata wanka a bathroom dina, wiqi wiqi da ido fatuha tayi dan ita bata san me ye bathroom ba, wata uwar tsawa ya kuma daka mata oh waike wata irin yarin ya ce ehh ki kai ta ban daki na kiyi mata wankan yar qauye kawai mtss, saura kuma inkin je kinmin kauyan ci jiki ba kwari fatuha ta shiga toilet din ba laifi dan kauyanci da tayi kadan

Please Login or Register in order to submit comment