Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wacece Hindu anan? Dama na kula tun daya shigo ta tsure da ganin shi, a razane ta mike hannunta a kirji tace gani, lafiya? Ya kare mata kallo kafin yace haka nake fata, amma muna da case dake don haka akwai yiwuwar zaki biyo mu zuwa can police station don amsa wasu tambayoyi! Ta zaro ido muryar ta na rawa tace "memm.... me nayi...???" Ya girgiza kai, "idan mun je can zaki ji".

Mahaifiyar Hindu ta mike a dan zafafe, "Malam ban gane ba! ta yaya zaka zo ka dinga neman rainawa mutane wayo? Me tayi da zaku tafi station da ita??" a sanyaye Marwan ya dubi dan sandan yace Malam, idan da akwai matsala ne ka mana bayani kawai, ba wai ka zauna kana kwana-kwana ba. Kasan ba zai yiwa ina zaune ka tafi min da mata zuwa station ba tare da ka bani kwakkwarar hujja ba" dan sanda ya gyada kai yace "ban so zan fada ba, amma tunda Kun matsa shikenan.... Dama wanda muke tsaro ne cikin wadanda suka suka dira gidan Marwan ya farfado daga dogon suman da yayi, ya mana bayanin wanda ya tura su gidan bayan yasha dan karen duka, yace Hindu ce ta tura su su kashe Marwan!!"
"What???!" kusan duka dakin muka fada a razane tare da mikewa tsaye, ita kuwa Hindu zubewa tayi akan gwiwoyinta tana kuka hade da fyace majina.......




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:02 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•36•°🐾


"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!" muka dinga maimaitawa, kafin mu ankara sai ganin Maah muka yi rike da wuyan rigar Hindu tana jijjigata cikin karaji da rishin kuka, tace "me muka miki Hindu? Me dana ya miki daya cancanci wannan muguwar sakayyar Hindu? Ashe duk soyayyar da kike ikirarin kina mishi ta karya ce? Na tauye farin cikin dana na aura masa ke duk da cewa baya so, amma haka ya zauna dake, Hindu duk baki ga wannan ba kike so ki kashe min shi???" kuka take yi sosai tana magana, itama Hindun kukan take yi kamar zata hadiye zuciyar ta. Mohammad Kabeer ya tashi jiki a sanyaye ya janye Maah daga jikin Hindu yana fadin relax Maah! Just relax.... Ta hayayyako masa sosai kamar zata duke shi, ba zanyi relaxing ba Kabeer, dana pa take nema ta kashe min? Wallahi ba zan yarda ba sam!! Da kyar ya samu tayi shiru ta zauna, amma fa sai kwafa take yi tana girgiza kafa. Marwan dai bin kowa yake yi da kallo ba tare da yayi ko tari ba, Allah kadai yasan halin da yake ciki a wannan lokacin.
Kabeer ya kalli Hindu tana ta faman kuka, fuskarta tayi jawur abinka da farin mutum. A nutse kuma a tausashe yace "Hindu, ki mana bayanin abinda ya faru tsakaninki da Allah, na miki alqawarin komi munin abinda kika aikata zan tsaya a bayanki!" Maah tana neman yin magana yayi saurin katseta, "plsss Maah....!" yana mai daga mata hannu alamun tayi shiru.

"wallahi ni ban tura a kashe Marwan ba na rantse da Allah!!" abinda ta fara fadi kenan cikin shesshekar kuka, yace naji, to wa kika tura a kashe? Ta girgiza kai, ban ce a kashe kowa na, kawai..... Sai kuma tayi shiru tana goge hawayenta. Ganin tayi shiru bata sake magana ba yasa yace a dan tunzure da yanayinta na kamar tana son rainawa mutane wayo, "muna sauraronki.... Idan kuma ba zaki iya bayani anan ba zan hada ki da dan sandan nan idan kunje station sai kiyi bayanin acan ko?" ta girgiza kai a hankali, ta bude baki da kyar ta fara...

"Tun wata dubiya da muka je wajen Ameenah, na ga kamar tana da ciki. Tun daga wannan lokacin naji Hankalina ya tashi, a wautata bai kamata ace mun jera haihuwa da ita ba a matsayina na babba. Kawata kuma makociyata matar Raj Mooby...." ta dago tana dubanmu daya bayan daya tace nasan ai kun san ko waye Raj?? Na daga Kai a hankali ina tunanin kwanakin baya da dadewa sun taba yin takun saka da Marwan akan wani film da aka saka Raj yace ba zai yi ba shine aka maida Marwan har aka kara mishi kudi kan wanda aka ba Raj, hakan ya jawo sanadiyar batawar su. Ba a jima ba da aka sake maimaita haka, aka cire Raj a film saboda halayen daya dinga nunawa aka maye da Marwan tare da ninkawa Marwan din crores da aka taya Raj dasu ya raina, shine yaji haushin abin har yaci kwalar rigar Marwan a lokacin yana ikirarin zai yi maganin shi a cikin industry. Bayan an raba fadan da kyar, daga baya kuma suka shirya har suka yi wani film su biyun.... Hindu ta cigaba da magana.... "...itace ta dinga zuga ni da mugayen shawarwari akan lallai in san yadda zanyi kada Ameenah ta haifi wannan cikin. Ni kuma na hau na zauna, a washegarin ranar ta raka ni gidan Ameenar ita da wata kawarta da niyar mu mata dukan da zai sa cikin ya zube sai kuma muka yi rashin saa bamu same ta ba. Nace mu Kyaleta kawai tunda koda ace zata haihu dai ni zan riga ya, itama ta nuna hakan yayi. Bata kara tayar min da zancen ba sai a satika biyu da suka wuce, ta dinga zuga ni da maganganu iri-iri, shaidan da kishi suka tunzura ni muka yanke shawarar cewa zamu yo hayar yan banga su je su yiwa Aneenah duka na fitar hankali sai su hada da satar mata golds dinta yanda babu wanda zai zargi wani abu sai dai kawai ace yan fashi ne.... Ashe ni ban sani ba amfani suke yi dani ita da mijinta.. Bayan na samu labarin abinda ya faru na tafi gidanta da kukana zan gaya mata, kawai na tadda ta ita da mijinta da sauran en bangar nan suna hira da dariya, suna fada musu cewa irin bugun da suka wa Marwan da kyar ya tashi su kuma suna ta kwasar dariya..... Don Allah ku yafe min, nasan cewa na aikata babban kuskure....!!"
Ta kifa kai cikin tafukan hannuwanta tana rusar kuka sosai. Maah ta mike tana kuka kashirban lullubin saree dinta yana warwarewa, fadi take tana karawa wallahi idan danta ya mutu ta rantse da Allah ba Raj da matarshi ba, ita kanta Hindu din a gidan yari zata kare rayuwarta. Muka mike muna lallashinta ko ta daina ihun da take yi, kawai sai ganin Marwan muka yi ya zube warwass akan gadon......




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:02 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•37•°🐾


Na kwalla kara na nufe shi da gudu ina kuka ina jijjiga shi, likitoci suka shigo a sukwane suka kora mu waje, ba da son ranmu ba muka fita muna kuka kamar ance mana ya mutu. Ina fita naci karo da Ya Faruq da Uncle Mukhtar, na fada jikin Ya Faruq ina kuka ina ce mishi Marwan zai mutu... Wallahi idan ya mutu qila nima mutuwar zanyi....!! Hawaye suka ciko idanunshi yayi ta maza ya hana su zuba, a hankali yake dan bubbuga bayana gami da shafa kaina a hankali, "ba zai mutu ba Auta, In shaa Allah tare zaku rayu dashi har abada!".
Fiye da mintuna talatin muna tsaye a wajen cike da taraddadi, kofar dakin da muke tsaye ta bude, gabadayanmu muka juya muna kallon likitan daya leko fuskarshi babu walwala, yace "majinyacin yana son ganin ku" muka fada dakin gabadayanmu cikin rawar jiki....

Likitoci biyu ne a kanshi da nurse, muka zagaye gadon da yake kwance muna kuka sosai. Ya kai dubanshi ga Maah dake tsaye a saitin kanshi, cikin shakakkiyar murya yace "Maah ki yafe min idan na taba saba miki...." kuka ya kufce mata, tace chufff Marwan, baka taba saba min ba, ba zaka mutu ka barni ba, ina zan sa raina??? Shima hawaye ne ke ta kwaranya daga cikin idanunshi, ya kalli Hindu yace "na yafe miki Hindu, Allah ya yafe miki kurakuranki na yanzu dana baya...." Ya danyi tari, "ku zama shaidata ko a wajen Allah, ko a bayan raina na ba Ameenah kyautar Al-Ameen har mutuwarshi...." ya kalleni, "na baki amanar dana Ameenah, ki rike amana.., ki bashi tarbiya mai kyau da nagarta wadda kika taso da ita...." wani tari mai karfi ya sake sarke shi. Cikin azama da dukan zuciya mai karfi na riko hannunshi na rike tamau, nace "kada ka min haka Marwan... Alkawari kamin cewa tare zamu mutu. Ka taimake ni ka tashi mu tafi gida mu cigaba da rayuwar mu da muka fara shimfidawa... Idan ka tafi ka barni nima mutuwa zanyi, ba zan iya jure rashin ka ba....!" na kifa kaina akan kirjinsa ina kukan daya karyar da zuciyar mutanen dake dakin suka fara sharbe. Iklimah ta matsa gaban gadon tace Yaya.... Ya juya ya dubeta da idanunshi da suka fito kuru-kuru suka yi jawur, ta fashe da kuka tace kai ka zame mana uba bayan rasuwar namu mahaifin, idan ka tafi ka barmu mun tabbata cikakkun marayu kenan, don Allah ka tashi!!.
Ya daga baki da niyar yin magana amma tarin daya sarke shi ya hana shi. Wani irin tari ya dinga yi babu kakkautawa, daga baya kuma ya fara kakari. Jikina ya fara rawa, zuciyata ta dinga bugawa da sauri, jikina ya bani lokacin rabuwa na da Marwan yayi. Ban san daga ina karfin zuciya yazo min ba, kawai ji nayi ina lakanta mishi kalmar shahada. Sai dana maimaita sau hudu kafin naji ya amsa, ya kara damke hannuna sosai.

Daga nan jikinsa ya saki, hannunshi dake rike da hannuna ya saki ya koma ragwaf ya zube akan gadon, kyawawan fararen idanunsa da suka washe suna kaina, har yau sun ki gogewa a memory na, haka kyakkyawar fuskarshi ma'abociyar haiba da kamala ta kunshe da wani irin murmushi.....

Ga alamu nan a baiyane cewa Marwan dina ya koma ga mahaliccinsa amma da gangan zuciyata taki aminta da hakan, duk da cewa na ga mahaifiyarshi da sauran mutanen dakin suna kuka da salati amma ban yarda cewa ya mutu ba....

A gigice na dinga jijjiga shi ina kiran sunanshi da karfi kamar wata zararriya, ji nayi an janye ni daga jikin nashi, a haukace na juyo nayi tozali da Ya Faruq, sai kawai na dinga nuna mishi Marwan da yatsa na amma bakina ya gaza furta komi. Muhammad Kabeer yayi karfin halin yaja bargo ya rufe gabadayan jikin Marwan tare da rufe idanunshi kwallar fuskar shi na diga a kasa....

Nayi sak, yayin dana dinga jin kaina kamar ba a jikina yake ba, kai gabadaya ma ji na nayi kamar bani ba ce ba.......



********




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•38•°🐾


*********

Har aka gama shirya gawar Marwan aka fita da ita daga cikin gidana ban san ina kaina yake ba, gani nan ni dai idanu na biyu ras a bude amma na kasa tabuka komi... Na bi makarar da aka saka shi a ciki da kallo, tun ina mata kallon sosai har ya zamo na fara ganinta dusu-dusu, mutane suka fara dawo min biyu-biyu, zuwa uku, daga nan kuma sai naji komi na duniyar ya bace min, ban kara sanin inda kaina yake ba.....

•••••••••
A hankali na dinga bude idanu na da suka min nauyi, fanka na fara gani tana wulwulawa, ban iya tuna komi ba amma kokarin tunawa nake yi sanda naji an kira sunana a tausashe, "AMEENAH??!" na kalli inda sautin ya fito, Ammie, Anti Rukky, Uncle, Anty, Ya Faruq da Muhammad Kabeer suna tsaye a gefena na dama fuskokin su dauke da damuwa. A take komi ya fara dawo min cikin memory na, na lumshe idanuna cikin jin wani matsanancin zafi a zuciyata. Ya salam!! I wished idan na bude idanuna at that time zan ga cewa mafarki nake, mummunan mafarki wanda ba zan kara marmarin in rufe idanu na ba saboda kada in sake maimaita shi, sai dai ko da na sake bude idanuna ina kan gadon asibitin nan a kwance, mutanen nan na tsaye a gefe na, da gaske dai Marwan ya tafi ya barni. Na dafe saitin kirjina nace "Inna lillahi wa Inna Ilaihi raji'un... Allahumma ajirni fi musibatun wa akhlifniy khairan min ha...!!"
Wasu hawaye masu tsananin zafi da yaji suka fara xubowa kan kumatu na, Ammie ta kamo ni ta rungume sosai tana shafa kaina a hankali, sai lokacin na samu na fashe da kuka mai karyar da zuciya, duk jikinsu yayi sanyi su ma suka fara sharar kwalla.

Sai a washegarin ranar aka sallame ni daga asibiti, ashe kwana na biyu a kwance ban san inda nake ba. Gidana aka wuce dani don acan ake zaman makoki, ina ganin dumbin jama'a a cikin gidan zuciyata ta karye, da kyar muka samu muka shiga cikin gidan saboda en jaridu da suka baibaye me suna neman bayani. A cikin gida ina dora idanuna akan Al-Ameen wani sabon kuka ya tashi, muka hadu da Hindu da Maah muka yi tayi kamar ba zamu daina ba, da kyar muka samu muka lallashi kan mu. Tun daga ranar Al-Ameen ya dawo hannuna, abinda ke kaishi wajen Hindu to shan nono ne, yana gamawa zata miko min shi, in goye shi tsam a bayana ina jin shi kamar Marwan. Sati biyu mutane na nesa dana kusa sun koma gida, aka barni ni da Hindu da wata er uwar su Maah a gida muna takaba. Wannan zaman kam zama ne na girmama juna da ganin kimar juna muke yi, muna zaune lafiya lau kamar ba mu ba. Zamu hadu da Hindu mu sha hirar mu akan zaman mu na baya, wani lokacin muyi dariya wani lokaci kuma mu sha kuka.
To dama ita rayuwa ba wata aba bace ga wanda ya hankalta, Allah yasa mu dace!

Tuni en sanda suka cafke Raj Mooby da matarshi ana ta bincike, da yake abu ne na manyan mutane domin kuwa daraktocin Marwan sun yi ruwa sun yi tsaki akan lamarin don haka abin bai zo wa su Raj da sauki kamar yadda suka yi zato ba.


Mun gama takaba da sati biyu muka hallara a wata babban kotun shari'ar musulunci anan cikin Mumbai, kotu tayi rabon gado inda Al-Ameen ya tashi da shares din Marwan dake kamfanin su Marwan din shi da Kabeer da wasu filaye da gidaje da kuma kudade, ni da Hindu kuma kowa gidan da take zaune, Hindu aka bata wani indomie joint ni kuma gidan yin ice cream duk anan cikin Mumbai da kuma zunzurutun kudi. Mahaifiyar shi da sauran kannenshi duk sun samu nasu rabon, hakika Marwan ya tara dukiya kafin ya tafi, sai dai Alhamdulillah! Duk yawan dukiyar nan tashi bata dame shi, yana taimakawa gajiyayyu da ita, yana taimakawa addinin Allah da ita, yana kuma kashe dukiyar ta hanyar data dace. Don haka sai dai ince Alherin Allah ya kai masa har cikin kabarinsa.


Bayan anyi rabon gado, aka fara shari'ar su Raj. Saboda kwararan hujjoji da aka samu a take kotu ta yanke musu hukuncin daurin gidan yari na shekaru biyar tare da biyan tara, Hindu zata yi waya takwas a gidan yari da aiki mai tsanani don hakan ya zama darasi ga yan baya. Ana gamawa kotu ta tashi, na kama hannun Hindu na rike kam da kyar en sanda suka janye ta muna kuka, Maah ta zo ta rungume ni tana kuka take rokon in yafe mata, ta min kaza, ta min kaza saboda Hindu, gashi dan nata da take yin hakan saboda dashi ya tafi ya barta, wadda tayi don ita kuma taci amanar ta... Kai maganganu barkatai kamar wadda kwalwarta ta juye. Ji nayi kafafuna sun kasa daukata, na tafi na zube a tsakiyar kotun jikina a sanyaye, na rasa abinda zan yi a lokacin. Na jima sosai a haka kafin na tashi da niyar tafiya, taku daya, biyu, ana uku sai na zube anan.....



*>To all BAYAN RAI readers, ina ta samun korafin ku na cewa bai kamata Marwan ya mutu ba, sai dai idan Marwan bai mutu ba abubuwa da dama ba zasu faru ba, sannan shi kan shi littafin ba zai amsa sunan Bayan Rai ba kenan..... Kowane rai yana da kaddarar sa, kuma ko wane rai zai dandana zafin mutuwa..... Ina fata makaranta sun fahimta. Ku cigaba da bibiyar labarin don jin yadda zata kasance! Love Yah!<*




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:03 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•39•°🐾


Sai bude idona nayi na tsinci kaina a gadon asibiti, sati na biyu cikin coma wadda shock ya haddasa min. Ammie na fara ganin kafin Kabeer da Ya Faruq, suna ganin farkawa ta suka shiga hamdala. Ya Faruq ya fita da kanshi ya kira Dacta, wata kyakkyawar farar mata ta shigo da fara'ar ta ta duba ni, komi ya nuna normal. Ta fara cire na'u'rorin da suka manna min a jiki tana tambaya na fatan babu inda yake min ciwo? Nace babu. Ammie ta kama ni muka je bayi ta taimaka min na wanke jikina tas da ruwan dumi, na fito na zura wando da riga marassa nauyi wanda asibitin ya tanada saboda patients. Na zauna a gefen gado bayan Ammie ta saka min filo a bayana. Ina shirin tambayar ina baby Al-Ameen su Uncle suka yi sallama shi da Anti Jameelah suka shigo, Tasleem da Asleem na biye dasu yayin da Al-Ameen yake a hannun Anti. Fuskokin su ya nuna jin dadi sosai da gani na a zaune, su Asleem suka baibayeni suna watsa min surutan makaranta. Na dan ji sanyi sosai a cikin raina, Uncle ya kalle ni ya min murmushi na dan sadda kaina kasa ina dan murmushi, Anti Jameelah ta miko min Al-Ameen na amshe shi. Yayi bul dashi alamun yana samun kula sosai, naji kwalla ta ciko idona. Na rungume shi a jikina ina dan jijjiga shi, na kalli Anti nace "Anti nagode for taking care of him" ta zauna a gefena ta shafo kumatu na, "stop embarrassing me girl, Al-Ameen da na ne nima. I prepared a very delicious and yummy potato porridge for you, Asleem miko min box din abincin can...." nayi saurin tare ta, "nooo Anti, ba yanzu ba, bana jin yunwa" Ya Faruq yayi saurin kallo na, me kika ci da ba kya jin yunwa? Na danyi murmushi, "cikina ne a cike Ya Faruq, zan ci anjima in shaa Allah..." ya gyada kai kawai muka cigaba da hira.
Da dare muna zaune daga ni sai Ammie a dakin, sauran duk sun tafi gida. Lallashina take yi in daure in ci abinci, tunda na tashi babu abinda ya shiga ciki na. Shiru kawai na mata na sadda kaina kasa, tunanin yadda zan saka wani abu a cikin baki na nake saboda ji na nake full bana bukatar komi a wannan duniyar da Marwan ya tafi ya barni in rayu ni kadai a cikinta, i was depressed and i lost any other hope. Fatana daya a lokacin nima in bi bayanshi, bani da wani buri ko sha'awar koyawa zuciyata rayuwa a duniyar da babu Marwan, Marwan becomes a part of my being wanda yake tattare da bugun zuciyata, ina mamakin ta yadda mutum zai rayu a duniya without heart beat...! Sai na fara sharar kwalla a hankali. Ammie ta fusata, ta dankwafar da bowl din hannunta ta tashi daga kusa dani, tace "sai kije kiyi tayi Ameenah, maza kiyi starving din kanki ki mutu ki bi bayan Marwan ko ba haka kike so ba? Wallahi da haka ake so da bamu yi shi ba, ba son Marwan kike yi ba tunda har kin kasa yarda da kaddarar da Allah ya dora miki. Kin rasa mahaifin ki ma balle miji? Kina nema ki bata musuluncin ki saboda wata banzar soyayya??!...." sosai ranta ya baci dani, ta dinga fada ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba. Kawai sai na ida rushe mata da kuka, da wanne take so inji ne? Yaya take so inyi da rayuwa ta? Son Marwan a jinina yake, ban san ta yanda zan yi in cire shi ba ko kuma in koya wa zuciya ta hakurin rashin sa ba, sai dai idan jinin jikina za a zuke a tittila min wani....

Likitar nan ta dazu ta turo kofa ta shigo, sanye take da doguwar rigar castrada anyi wa wuyan rigar da hannunta surfani mai kyau irin na mutanen yammaci Asia, tayi rolling da grey gyale na rigar, fuskarta saye da farin madaidaicin medicated glass. Ta tako a nutse ta nufo inda nake zaune fuskarta dauke da murmushi, haibarta da kamalarta suka cika min ido. Her charismatic feature is one in world, ban taba ganin mutum mai tarin baiwarwaki irinta ba. Kamshin turarenta kadai ya sanyayar min da zuciya, murmushinta kawai ya tsayar da kukana, irin wadannan mutane daidaiku ne a doron kasa. Ta zauna a gefe na a nutse har zuwa lokacin tana murmushi, ta dafa kafadana ta fara magana cikin turanci, tace "haba Ameenatu autar mata? Waye ya fada miki don ka rasa miji shine rayuwar ka ta kare? Ina tawakkalinki? Kin manta da cewa yarda da kaddara yana daya daga cikin ginshikan imani? Ko kuwa kin manta cewa duk wani mai rai mamaci ne? Kuma ita mutuwa tana kan kowa? Ko daina yiwa Marwan kuka don baya bukatar shi daga gare ki, addu'arki yake bukata, yana bukatar karfin zuciyar ki da kika karya, yana bukatar ki kula da dansa amma kin kwanta kin ki ki kaurara jikinki balle ki kula dashi din... Kina ina yara suke rasa iyayensu, iyaye su rasa yayansu, yayye su rasa kannensu, kuma su yi hakuri su yarda da kaddara and move on with their lives??..."
Na sadda kaina kasa, zuciyata ta fara rage suyar da take min, naji wata natsuwa da tsoron Allah na shiga ta, kalaman likitar nan suka dinga huda jikina suna ratsa ni. Abin kamar wani magic, naji wani karfi ya mamaye raunin da zuciyata tayi, wani kuzari ya dinga shiga ta yana kara min karfin jiki dana zuciya. Likitar ta kara cewa,


Please Login or Register in order to submit comment