Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bar 9ja, zuwa lokacin zazzabine sosai ya rufe Ameenah ruf da kyar ta samu ta raka su kasa, ta dawo ta libge akan gado kamar kayan wanki, da kyar ta sallaci magriba a daddafe ta kara komawa ta nade a cikin bargo.
Maodibbo bai shigo gidan ba sai da karfe tara ta gota, yana can tare dasu Muhseen suna ta hira bai kula da lokaci ya kure ba sai da daya daga cikin abokan nasu ya nuna mishi agogo yana tambayar wai ko dai ya manta da amaryah ne?? Ya wawuri makulli ya fita a sukwane babu ko waiwaye balle ya tankawa shakiyancin da suke mishi. Sai daya tsaya a wani suya joint ya sayi suyar kaji da tarkacen yogurts da fresh milk don yace wa Ummie a daina kai musu abinci ya hutar dasu. Sai daya canza shiga zuwa ta kayan barci sannan ya tafi dakin Ameenah.....




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•58•°🐾


Tana can tsakiyar gadon ta nade cikin bargonta mai damisa irin mai rubi biyu dinnan, amma still rawar sanyi take yi. Ya ajiye ledar hannunshi da sauri ya nufe ta a rikice, Ameenah lafiya?? Abinda yake nanatawa kenan har ya hau kan gadon ya janye bargon data rufa dashi, rawar sanyin data ke yi ta karu har hakoranta na hadewa da juna, ta kasa ko bude ido, hucin zafin jikinta ya bugo shi kamar wuta, ya dafe kai Ohhh God! Ya maida mata bargon da sauri ya fita, dakinshi yaje ya dauko first aid box yazo ya fara bincikar ta. Allura ya hada ya zurkuda mata, duk da halin da take ciki sai data yi dan kara, ya shiga lailaya mata wajen yana ambaton sorry!! Cikin ledar yaje ya dauko mata yoghurt, ya tsiyaya a cup ya mika mata, tayi saurin girgiza kai don ko karnin shi bata son ji, ya narkar da murya yace daure ki sha Ameenah magani zan baki, kinji? Karbi don Allah..... Ya shiga bata da kanshi, ko rabi bata sha ba ta amayo mishi yoghurt dinnan tas a jikinshi da dan sauran abinda taci da rana. Yana rungume da ita kamar zai rushe da kuka dan tausayi har ta gama, ya dauketa ya dora akan couch shi kuma yaje ya gyara wajen, ya kawo air freshener ya fesa a gun, shima ya koma daki ya canza kayan jikinshi ya dawo dakin cikin shiga fiye data dazu yana ta kwarara kamshi mai dadi. Ya kara ciccibarta ya maida kan gadon, da lallashi ya samu ta dan kurbi yoghurt din ya bata magunguna. Yaje ya tattara sauran kayan ya kai kicin, ya dawo ya taimaka mata ta kwanta. Ya dan rufa mata bargo duk da zazzabin ya sauka, shi kuma ya koma kan couch ya kwanta bayan ya kashe musu wuta.

Washegari data tashi babu zazzabin a jikinta sai dai rashin kwarin jiki, ya taimaka mata ta dauro alwala suka dawo ya shimfida mata abin sallah, shi ya tafi masallaci ita kuma ta sallaci tata a daki. Da gari ya danyi haske ya dawo ko sama bai hau ba ya fada kicin ya shirya mata sassaukan abinci da yake Abdul-Rasheed ba daga nan ba in dai akan girki ne, ya kware sosai kamar wani chef. Kafin takwas tayi ya gama komi, ya cicciba ya kai mata ta dan ci ya bata magunguna ta koma ta kwanta, sai daya ga barci ya dauketa sannan ya tafi dakinshi ya kwanta. Ranar bai fita ba sai can da yamma bayan ya tabbatar da ta wartsake sosai, sai bayan isha'i ya dawo. Kofar dakinta ya tura amma sai yaji kofar a rufe, mamaki ya kama shi, ya bubbuga yaji shiru. Sai ya leka ta kofar makulli ya hangota a zaune tana ta faman latsa remote da plate din yankakkun fruits a gabanta, yayi ajiyar numfashi, da alamun ta warke kenan tunda har ta iya sauka kasa. Sai ya koma kasa ya adana kajin da fresh milk din daya shigo dasu. Can wajen karfe goma yana kwance yaji karan bude kofar dakinta, cikin sauri yazo bakin kofar shi yana hangota, ita din ce ta zura dogon hijabi har kasa, yaji wata faduwar gaba ta ziyarce shi. Ina zata je da wannan daren? Ko dai guduwa zata yi?? Yayi kokarin bin bayanta sai ya tuna makullin gidan ai yana hannunshi, sai dai in doguwar katangar gidan zata kama ta dira. Yana nan yana saka da warwara yaga ta dawo hannunta dauke da kwalin fresh milk mai sanyi wadda ya shigo da ita ta shige daki ta kulle, ya jingina kanshi da kofar dakin yana karewa ceiling din dakin kallo.
Wasa gaske Ameenah ta daina yarda su hadu da Modibbo, kullum tana daki bata yarda ta fito sai idan ya bar gidan ta fito tayi en gyare-gyare da abinda zata yi kafin ya dawo ta koma.
Bai damu da hakan ba ko kadan, a ganin shi indai tana lafiya to Falillahilhamdu, sai dai a yawancin lokuta ya kan yi kewarta sosai, yana so ya sake kadaicewa da ita sosai, zumar daya dandana daga gareta zuma ce da ba dai a dandanata a barta ba, sai dai asha ta kuma ayi ta son nata har abada, sai dai ya kan lallami zuciyarsa ya nuna mata lokacin hakan bai yi ba, ya sha alwashin wani abu ba zai kara shiga tsakaninsu da ita ba har sai ya koya mata son sa, ba zai so haifar 'ya'ya da macen da bata son shi ba gudun kada kiyayyarshi ta shafi yaran. Cikin haka ya koma bakin aikinshi, idan ya fita tun kafin takwas sai karfe hudu ko biyar yake dawowa. Ya fahimci tana son shan fresh milk don haka yake kwaso mata ita yayi ta jibge mata su a fridge. A haka suka shanye wata guda cur, haduwarsu da Modibbo sai dai by mistake, kila ta fito daga daki shima ya fito su danyi starring din juna su kauda kai, watarana ya tambayeta tana da matsala? Sai dai kawai ta girgiza kai ta koma dakinta. Wannan rayuwar kadaicin data kirkirarwa kanta bata yi mishi dadi ko kadan, to amma ya zai yi???

Ta takura su Ammie sosai akan a kawo mata Al-Ameen dinta, Ammie tace ta fara tambayar izinin mijinta. Ta turo baki kamar tana gaban Ammien tace to ai tun farko sai da muka yi yarjejeniya dashi, ya yarda da zaman Al-Ameen a tare dani, menene kuma na sake fada mishi?? Ammie tace ke dai tunda nace ki tambaya to ki tambaye shi din.... Ta katse wayar. Tsaki ta ja tayi jifa da wayar.
Ya dawo daga aiki ya ganta coge a jikin kofar dakinta ta harde hannu a kirji kanta a kasa, kasa-kasa yake kallonta yana so yayi magana amma yana tsoron ta shige dakinta, sai kawai ya hau kokarin bude dakinta. Muryarta ya tsinkaya daga bayanshi, "Ammie tace a tambaye ka za a kawo Al-Ameen..." ya dan juyo yana kallonta, fatar jikinta tayi wani fess da gani babu tambaya kasan tana shan hutu, to bata zuwa koina, kullum sai dai taci ta kwanta ko hasken rana sai dai ta hango shi ta window. Yayi saurin janye idonshi daga kanta saboda wani abu da yaji yana taso mai game da ita, yayi kokarin saisaita muryar shi data fara tangadi, yace Allah ya kawo shi lafiya.... Kafin ya gama rufe baki ta fada dakinta ta rufo, yabi kofar dakin da kallo yana gyada kai cikin kunan rai.

Bayan kwana biyu Ya Faruq ya kawo mata shi da kansa kamar yanda yayi alkawari, tare suka zo da Safeenah. Ta kara habakewa ta zama lukuta ta gaske, sunyi kyau sosai daga ita har Faruq din. Al-Ameen ma ya kara girma sosai, ya kwaso da gudu yana Mommy.....!! Ta daga shi sama ta cilla shi ta cafe tana dariya, tana jin kamar ta maida shi ciki. Ta dinga ina taka saka ina taka tsare da bakinta, babynta na jikinta. Suna nan Modibbo ya dawo daga wajen aiki. Bayan anyi isha'i gabadaya suka rankaya gidan su Ummie, wannan shine karo na farko da Ameenah taje gidan tun da aka kawo ta, Ummie dai tazo kuma ana kawo mata su Hauwa akai-akai suna mata yini. Ummie tayi murna da zuwansu sosai, suna nan suna hira har sai da sha daya ta wuce sannan suka musu sallama suka tafi, Faruq masauki ya kama, anyi-anyi dashi yaki kwana a gidan su Ummie. Washegari ya koma, Safeenah ta kara kwana biyu itama ta bi bayan shi.

Dawowar shi daga wajen aiki kenan, yana kokarin bude dakinshi ya jiyo muryar Ameenah sama-sama, "ya za ayi baby? Ba a sako maka underwears da kayan shan iska ba..." ya danyi murmushi ya shige dakinshi, wanka ya fara yi ya canza shiga ya dauki makullin mota ya fita. Sai gashi niki-niki da ledoji a hannu, ya tsaya bakin kofarta ya bubbuga. Ta taso ta bude cikin mamaki don bai taba mata haka ba, a kofar ya coge yana mata wani kwantaccen murmushi tace lafiya?? Ledar hannunshi ya mika mata, ta amsa. Tana shirin maida kofa ta rufe Al-Ameen ya leko kai ta kofar, yace mommy! Modibbo ya sakar mishi murmushi ya durkusa a gabanshi yace "hello baby, ya kake?" ya kalli mommyn ya sake kallonshi, ya turo baki yana kallon Ameenah. Bata bari yace wani abu ba ta janye Al-Ameen ta maida kofar ta rufe shima ya juya abinshi. Al-Ameen ya dame ta da tambayar wai wanene wancan?? Tace sunan shi Uncle, yace Uncle Wa? Tace kace mishi Uncle kawai. Zai sake watso mata wata tambayar tace mishi shhhh! Ya kuwa yi tsit.
Ga mamakinta koda ta bude ledar kayan shan iska ne da underwears na yara daidai Al-Ameen, har da su turaruka da takalma, sayayya dai rankataf! Ta dan yi murmushi kadan, "well thanks for this, yau dai ya dan birge!" ta fada a ranta.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•59•°🐾


Ranar assabar da safe ya ci kwalliyar shi cikin kananan kaya sai kamshi yake yi, yayi knocking a kofarta. Ta taso ta bude kofar ta coge a bakin kofar tana kallonshi, cikin murmushinsa da baya bacewa a fuskarsa in dai yana tare da ita yace morning! Ta dan ji kunyar kin gaishe shi da bata yi ba, ta kauda kai gefe ita bata amsa gaisuwar shi ba ita kuma bata gaida shi ba. Yace a bani aron Al-Ameen zai raka ni unguwa... Ta dan tsaya tana kallonshi, sai kuma ta juya ta kwalawa Al-Ameen kira, yazo gun a guje yace mommy gani. Ta dan kalli Modibbo tace kazo ka raka Uncle unguwa. Ya kuwa koma dakin da gudunshi ya kwaso takalman shi ya dawo, ta duka ta sanya mishi takalman, Modibbo ya kama hannuwanshi suka tafi yana mata bye.
Bayan fitarsu wankin kananan kayansu ta musu da yake akwai wanda yake musu wanki da guga, mai aikin da yake zuwa kullum yana share farfajiyar gidan da ban ruwan fulawowi shi yake musu wanki da guga. Ta gama tayi wanka tayi lunch, ta zauna jiran dawowarsu duk kadaici ya cika ta amma har aka kira yi sallar la'asar shiru sai da yamma likis tana falon kasa a cikin kicin taji Al-Ameen ya shigo da gudu yana kiran sunanta, ta tare shi tana mishi oyoyo. Bakinshi kamar zai tsage yake bata labarin Daddy ya saka shi a makaranta, tace wane daddy?? Yace daddy na nan gidan mana, yace sunan shi daddy ba Uncle ba. Ta kama haba, "kaji wani karfin hali., ko yaushe ya zama danshi??" ta shafa kanshi tace kace makaranta ya kaika? Ya gyada kai da sauri, "Ehh mommy. Ranar litinin zan fara zuwa" tayi mamaki, kuma tayi farin ciki sosai don dama abinda take tunani kenan, sai dai bata san ta inda zata fara bane. Ya coge a bakin kofar kicin din yana kallonsu ita da dan nata suna ta bashi sha'awa. A jikinta taji ana kallonta, don haka ta waiga a nutse ta kalli bakin kofar, ya soke hannuwa a aljihun jeans dinsa, idanunnan nashi farare tass suna kanta, ko data waigo ma har idanu suka hada amma sai ita ce ta janye nata, yace "makaranta na kai shi, ranar litinin zai fara zuwa. Ai kinsan Nurul-Huda to can ne, nasan kin san tsarin su tunda su Adamu ma a can suke" ta gyada kai kanta a kasa tana kokarin kaucewa hada idanu dashi don suna jefa ta ne a cikin wani yanayi da kasala mai yawa, tace an gode, amma da ka bari nima da ina shirin zan kai shi. Yace tunda na riga ki kaishi ai an wuce wajen koh? Ta sake gyada kai, "an gode!" ya dan saki murmushi mai sauti, "naaa don't mind! Al-Ameen kamar da ne a gareni.... Uniform din sa na dakin ki" ya juya ya tafi, ta bishi da ido zuciyarta na kwarzanta mata kirki irin na Modibbo, amma tana hana bakinta fada, musamman kalmarsa ta kusan karshe a gareta, ".... 'da ne gareni.....!" zuciyarta ta jima tana nanata maganar a cikin ranta, daga karshe ta watsar da komi ta cigaba da girkinta dan ta na mata surutun wajajen da suka je. Tana gama girkin ta warewa Modibbo nashi, ta kwashi sauran suka kule a daki ita da babynta.

Ranar litinin tunda asubahi bata koma barci ba, ta je ta hada breakfast ta kuma hadawa Al-Ameen lunch box wanda zai rike mai ciki sosai tasan idan ya tafi sai biyar zai dawo na yamma. Ta koma daki ta tashe shi yayi wanka, ta shirya shi tsaf cikin uniform din makaranta. Dogon wando ne trouser blue mai cizawa sosai, sai shirt grey, neck tie kalar wandon, bakin belt da takalmi sau ciki shima baki. Ta taje mishi tattausar sumar kanshi wadda ta kwanta lambam a wuyanshi, yayi kyau Masha Allah kamar ka sace shi ka gudu. Ta dube shi tun daga sama har kasa, komi ya hau perfectly, ta kara gyara mishi zaman name tag din shi a aljihun shirt dinshi, an rubuta Al-Ameen Muhammad Marwan.... Tayi murmushi tace u look muah baby! Dariya kawai ya mata. Ta zaunar dashi akan cinyarta tana bashi abinci a baki.

Karfe bakwai da rabi Modibbo ya bayyana a bakin kofar da yake yau bata rufe kofarta ba, hannunsa rike da brief case alamun yayi shirin tafiya ofis, yace "baby zo in sauke ka a school kafin a samo maka direban da zai dinga hidimar makarantar ka" ya warci school bag dinsa ya tafi yana cewa mommy sai na dawo! Ta mike tana dariyar dokin da yake tace gandoki kenan! Muje in maka rakiya toh!! Ta kamo hannunshi suka bi bayan Modibbo suna er hirarsu. Modibbo jin sa ya dinga yi kamar ya dora hannu aka yayi ta kwarara ihu saboda tsabar farin cikin daya cika mishi ciki, yau shine zai je wajen aiki cikin rakiyar Ameenah? Duk da cewa dai rakiyar was not meant for him, amma shi wannan abin alfahari ne a gare shi ba karami ba kuwa, don haka har ya shige mota ya tasheta annurin dake shimfide a fuskarsa ya gaza boyuwa sam. Ta bude gidan gaba Al-Ameen ya shiga, ta dora mishi jakarshi da lunch box akan cinya ta duka ta sumbaci goshinsa tace Allah ya tsare baby nah!, ayi karatu sosai fa, kuma ka ci abinci kaji good boy? Ya gyada mata kai yana mata murmushi, da hannuwanta biyu ta dinga musu bye-bye har suka tafi.

☆☆☆☆☆☆☆

Hausawa suka ce 'mai da wawa!' da wannan karin maganar Modibbo yayi amfani a matsayin makamin yakin yakar zuciyar Ameenah, tsawon sati biyu yana hidimar kai da dauko Al-Ameen daga makaranta har dai aka samar masa da direba, bai taba fita ya dawo hannunsa babu leda ko wani abu da zai ba Al-Ameen ba, haka a kowane dare su kan zauna a falo shi yake koyawa yaron duk wasu homeworks dinshi ya kuma wayar mishi da kai akan abinda bai gane ba. Idan kaji yanda yake maida kansa yaro yana biyewa Al-Ameen suna wasa abin sai ya matukar baka mamaki, cikin kankanin lokaci yaron yayi matukar sabawa da Modibbon kamar wanda suka shekara a tare. A hankali sai Ameenah ta fara cire shi daga layin mutane masu girman kai da baudadden hali data saka shi, ta maido shi layin mutanen kirki masu girman kai. A cewarta duk rashin fahimtar halin shi ne ya kawo haka, amma yanzu data fara fahimtar shi ta fara gane irin halayen shi.
Saboda shi Ameenah ta daina rufe kofa, don ko ta rufe sai Al-Ameen ya dameta akan ta bude shi dai hira zai je wajen daddyn shi, watarana ma idan ya tafi a can yake kwana. Tun dai tana mishi fada har ta gaji ta daina tunda ba ji yake yi ba, ta kawo na mujiya ta zuba musu.

*********

Yau ranar talata, yawancin ma'aikata da dalibai duk suna gida ne a dalilin public holiday da ake yi. Tun data shirya breakfast suka koma kan gado suka nade, bata farka ba sai wajen karfe goma na safe. Al-Ameen na zaune dangargar akan gadon da puzzle game a hannunsa yana kokarin hadawa. Ta ciccibe shi yana zillon ta sauke shi ya gama game din shi tayi kunnen uwar shegu dashi, wanka ta mishi ta nado shi a babban tawul ta dire shi akan gado sannan itama ta shiga wankan. Ba wani jimawa ta fito daure da tawul pink mai matsakaicin tsayi tunda bai sauka har gwiwarta ba, ta janyo jakar kwalliyar Al-Ameen ta nufo shi, hankalinsa na kan game dinshi, ta zauna a gefen gadon tana kokarin tsiyaya mai a tafin hannunta, tace come on baby, zo a shafa mai. Ya kallota cikin shagwabe fuska, "mommy don Allah ni dai ki bari in gama game dina, please kinji??" tace to ai ban hana ka game ba ko? Cewa nayi kawai kazo in shirya ka. Ta fada tana kokarin janyo shi, kafin ta ankare ya dira ta daya gefen rike da game din ya nufi kofa da gudu, ta dafe kai "da alamun shiririta ce akan Al-Ameen yau" ta fada a hankali. Tashi tayi tabi bayanshi da dan gudunta tana kwala mishi kira, dakin Modibbo ya fada, bata yi wata wata ba ta rufa mishi baya itama.
Yana tsaye a gaban mirror daure da towel, shima fitowarsa daga wanka kenan ya tsaya yana karewa kansa kallo ta cikin dogon yaro, ya dan fada kadan. Yana ta sake-saken yadda zai bullowa lamarinsa da Ameenah don a gaskiya hakurinsa ya kusa karewa, a matukar takure yake. A daren jiya kaf bai samu yayi barci mai kyau ba, yana ta kokarin nemawa kansa mafitar data dace dashi don zaman nan da suke yi da Ameenah baya jin zai iya jurewa su ci gaba da yin irin shi.
Yana cikin wannan halin yaji an banko kofar dakinshi an shigo da gudu ana kiran daddy!! Cikin sauri ya juya, Al-Ameen ne, ya labe a bayansa ya cukuikuye shi, sai gata itama ta shigo da dan gudunta, idanunta a rufe ta nufe shi tana magana, "ka zo in shirya ka Al-Ameen sai ka hau guje-guje? Ni nace zan hana ka yin game din ka ne...???"

Modibbo kam mutuwar tsaye yayi ya kura mata ido, rabin gashinta data jika ya zubar mata a kirji da gadon baya yana digar da ruwa, ga santala-santalan kafafunta masu tafiyar da hankali da suke lullube da wasu bakaken gassu suma har yanzu da sauran lema a jikinsu, ya sauke kallonsa akan jajayen tausasan lebbanta tana wa Al-Ameen magana, ya kai harshe ya laso siraran bakaken lebbansa yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi, "tsuntsu daga sama gasasshe!!" ya fadi hakan a can kasar zuciyarsa.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:08 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•60•°🐾


Dariyar Al-Ameen ce ta dawo dashi hayyacinsa, ya maida dubansa gare su. Yaron ya mayar da abin wasa, idan Ameenah ta biyo shi nan sai yayi can, daga karshe dai ya mata wayo ya sille ya bar dakin ta daga kafa zata bishi, Modibbo ya saka mata kafa, ta tafi lauu zata fadi.... Cikin saddakarwa ta runtse idanunta tana sakin er kara kadan, sai ji tayi caraf! Hannu ya ratsa ta tsakanin kirjinta an rike mata towel, ta tsaya cikk!! Ita bata kai kasa ba, kuma ba a tsaye take ba. Wani electric shock ya dinga ratsa ta a daidai shacin kirjinta inda yatsun shi uku suka ratsa, ya zuba mata mayatattun idanunshi masu cike da tarin sonta da sha'awarta matsananciya. Sakonnin dake fitowa daga karkashin zuciyar shi suna biyowa ta cikin idanunsa suna ratsawa ta nata idanun masu girma ne, nauyinsu yafi karfin er juriyar data rage a cikin zuciyarta, kafafunta ne suka shiga rawa cikin nuna gajiyawa da yanayin tsayuwar data yi, ta fara tafiya luuuu cikin sagewar kafafu, yayi azamar janyo ta da karfi ta fada cikin faffadan kirjinsa, yasa hannuwanshi duka biyun ya rungumeta tsantsam, ya nutsa kanshi cikin gashinta daya ratso ta gefen wuyanta yana shakar daddadan kamshin shampoo data yi amfani dashi ta wanke gashin. Zazzafan hucin nasa ya dinga ratsawa ta cikin gashinta yana riskar fatar wuyanta, yana huda duk wasu hudoji da kofofin jikinta yana aikawa gangar jikinta da kwakwalwarta wasu irin sakonni masu wuyar kwatantawa. Ta fara zame jikinta daga nashi a hankali idanunta a lumshe, hakan yasa ya dan sassauta rikon daya mata ta dago fuskarta yana kare mata kallo, tsawon wasu mintuna ya kira sunanta cikin wata murya data saka ta doubting Anya Abdul-Rasheed ne kuwa?? Ta bude idanunta a hankali ta sauke su a fuskar shi amma ba cikin idanunshi ba, yace "you are beautiful Ameenah! Komi naki mai kyau ne.., idanunki... Hancinki.... Girarki... Kuncin ki... Bakin ki...." yana yi yana sumbatar duk inda ya fada, ya kalli tsakiyar idanunta ya kara narkar da muryar shi yace "n I fancy your mouth most..." ya kai mata wani deep kiss a bakin wanda ya kusa shidar da ita, cikin yanayi na fita hayyaci ta kankame hannayenta da zuciyarta ke azalzalarsu dasu rungume Modibbon yadda zai ji dadin sumbatar ta da kyau. Ya fara manna fatar bakinsa a wuya, kafada, zuwa saman kirjinta idanunsa a lumshe. Yayin da aka fara maida bayanai tsakanin gangar jiki da zuciyoyin Ameenah, gangar jikin na matukar son abinda Modibbon yake mata, zuciyar tana so sai dai wata zuciyar ce dai take kushe hakan, take hana mata jin dadin abubuwan da yake mata, tana ce mata wai "wanin Marwan ne fa!" daya zuciyar tace "ko ma Uban Marwan ne, desire have no boundaries, idan ka samu dama kawai ka kawar da ita at the immediate moment...." sai suka saka Ameenah cikin

Please Login or Register in order to submit comment