Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muka zauna zaman jiran sakamako.

A daren ranar muna falo mu duka cikin outfit na party, Uncle ya hada min er kwarya-kwaryar liyafa na taya ni murnar gama jarabawa lafiya. Aka kada door bell, na tashi da sauri na naje na bude. Wanda na gani ne a tsaye rike da bouquet yasa na zaro idanu na cike da mamaki. Ya kanne min ido daya, "Hii there.... Kina mamakin gani na ne? Ko ba ayi maraba dani ba in koma??" na sadda kaina kasa jikina a sanyaye, duk bidirin da muke ni da Marwan ko da wasa babu wanda yasan abinda ke tsakaninmu dashi. Muryar Uncle na jiyo yana kwala min kira, na kauce na bashi hanya ya shigo falon na maida kofar na rufe. Tare muka jera dashi muka koma falon ina ta sunke-sunken kai. Uncle ya taso da saurin shi ya ba Marwan hannu suka gaisa tare da nuna mishi wajen zama, na koma gefen Uncle na zauna kaina a kasa. Ina jin Marwan ya gabatar da kanshi wajen su Uncle, ni kam na kasa ko kwakkwaran motsi. Uncle ya sadda kanshi saitin kunnena yana min rada, "en matan Uncle yaushe aka yi saurayi Uncle bai sani ba??" na dukunkune fuskata a jikinshi, cikin shagwaba nace ni pa ba saurayi na bane! Yace da gaske?? To waye shi?? Na kasa magana sai turo baki, dariya yayi muka cigaba da gudanar da liyafar mu. Sai wajen karfe goma Marwan yayi haramar tafiya, Ni da Uncle muka raka shi har inda yayi parking motarshi, suka yi musabiha da Uncle ya juya ya tafi ya barni dashi a tsaye.

Ya maido da dubanshi gareni yana dan murmushi, "Ni pa da niyya biyu nazo gidan nan!" nace "niyya biyu? Ta me kenan??" ya daga kafadarshi, "well! Na farko in taya ki murna, na biyu kuma inyi confessing soyayya tah......!!".




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•20•°🐾


Na hangame baki idanuwa kamar zasu fado kasa har da kara karkade kunne wai ko banji daidai bane, "Ehhh?????!!" ya sake daga kafada, "it's not as if baki ji me nace ba.... Cewa nayi Ina Son Ki! Wat about u? Do u love me...???!" Wayyooo kasa tsage in shige mana! Na rufe fuskata da hannuwa ina wani irin murmushi, ina jin sautin murmushin daya saki. "I take that as yes! Je ki kwanta, sai da safe kinji??" ban iya motsi ba har ya shige motar shi yaja ya tafi. Na jima sosai a wajen nan a tsaye, da kyar na samu na iya komawa cikin gida. Anti da Uncle suna falo suna hirar su, suka bini da kallo har na shige daki. Naji dadi sosai da basu min magana ba don bani da kuzarin amsa musu. Ina shiga dakin nayi tsalle na dire kasa, "yesss!! I got him!!!" nayi tsalle na fada kan gado na dinga birgima ina shilla kafa sama, murna kamar inyi me? Na rungume filo kam-kam ina jin yadda zuciya ta ke racing. Ranar da kyar barci ya dauke ni.

Daga nan sai me?? Soyayyah mai karfi ta shiga tsakaninmu da Marwan, muka fara yin ta gadan-gadan. Gidanmu babu wanda bai san da zaman Marwan ba, haka idan yazo har cikin falo zai shiga su gaisa da Uncle da Anti. A dalilin haka zaman mu da Anti ya dawo normal, duk da haka ban gama sakin jiki da ita ba. Sai dai labarin soyayyar tamu bai shiga duniya ba saboda mutane.

Makarantar mu suka samu matsala wajen fitar da sakamako, don haka ne suka bada sanarwar mu yi hakuri sakamakon jarabawar mu ba zai fita yanzu ba sai nan da watanni takwas. Dalibai suka shiga zanga-zanga suna cewa basu yarda ba, sai dai babu wani cigaba dole dai suka hakura. Ganin zamana a gida baya min dadi, Uncle ya nemi shawarata akan zai samar min Diploma school ko ta koyon girki ko computer ko kuma koyon sana'o'in hannu, tunda su diplomar su wata bakwai ne, nace ya cike duk wadda yaga tayi mishi.
Bayan kwana biyu da yin haka Marwan yazo gidan mu, mun jima dashi a farfajiyar gidan inda muka saba hira dashi har dare yayi ya tashi zai tafi, anan ne ya miko min wata takarda, na amsa na duba. Police training centre naga an saka a sama har ya cike min, naji mamaki, me zai yi hadi na da police ni kam? Yace it's just 9 months pa! Nasan zuwa lokacin sakamakon jarabawar ku ya fito. Wallahi ina sha'awar ganin mace na aikin en sanda, I know it'll suit you. Ban ce kiyi aikin dan sanda ba fa! Kawai kiyi training din ko yaya ne, kuma ma kinga zaki koyi yadda zaki dinga kare kanki idan bukatar hakan ta taso". Nace to zan nunawa Uncle, yadda yace zan fada maka. Daga nan muka yi sallama dashi ya tafi.
Uncle kam cewa yayi hakan ma yana da kyau, inje kawai. Nan na fara zuwa training din, amma fa ba karamar wahala muke sha ba a wajen amma haka na jajirce ko don in farantawa Marwan rai. Muna cikin wata na takwas jarabawar mu ta fito, sakamakon mu kuma yayi kyau sosai. Uncle da Marwan suka fara fafutukar nema min gurbin karatu a jami'a. Lokacin training dinmu ya dauki zafi sosai saura wata daya mu gama.
Muka gama training dinmu na fito da 3rd class position saboda na nuna kwazo sosai.
Ranar da za a yaye mu har Yaya Faruq sai da yazo wajen taron, ni ce kira ta uku cikin jerin sunayen mutanen da za a ba Kyauta. Na tafi cikin fareti da kayan junior police a jikina har na isa gaban shugaban makarantar, Marwan ya bini da flashes har kan step. Ban suka rataya min sarkar ban girma ta uku mai dauke da sisin gwal. Haka aka cigaba da gudanar da taron yaye mu cikin tsari inda daga karshe muka rufe taron da fareti kowa ya watse. Ranar kam bakin Marwan yaki rufuwa sai fara'ah yake tayi, a cewar shi bai taba ganin wanda kakin dan sanda yayi wa kyau ba kamar ni. Nima farin cikin ne ya lullube ni, domin buri na kenan, fatana ne hakan in dinga ganin shi cikin farin ciki.




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:52 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•21•°🐾


Ba ayi sati biyu ba admission dina ya fita a babbar university ta Kelvin University of Arts, sun bani painting and drawing kamar yadda nayi applying. Na fara shirye-shiryen fara zuwa karatu, Hanan sun koma New Delhi ita da iyayenta acan zata cigaba da karatunta.
Kwatsam sai ga Kawu Hamza ya diro Mumbai, muka tarye shi cikin murna sosai musamman ni dana jima ban ganshi ba. Bayan ya huta mun gyara mishi mazaunin da zai kwanta, aka kai mishi abinci yaci. Ya tara mu mu duka a falo ya sanar damu dalilin zuwanshi takanas babu sanarwa. Yace bai yarda in tafi jami'a ba har sai ya aurar dani, domin haka mahaifinmu yake yi tun kafin rasuwar shi. Duka yayyena mata suna gama sakandare yake aurar dasu, wadda mijinta ya yarda ta cigaba da karatun a gidanta sai taci gaba, wadda kuma bai yarda ba shikenan. Anti Rukky har an saka nata ranar auren, watannin baya mijinta yayi hadari ya rasu, shi yasa Kawu ya kyaleta ta tafi KL kafin Allah ya kawo mata miji.

Uncle yayi iyakar kokarinshi yayi wa Kawu bayani yadda zai fahimta, cewa nayi kankanta da aure yanzu, ya daure ya bari koda nan da shekaru biyu ne sai ayi amma Kawu ya kekashe kasa yace ba dashi za ayi wannan abun ba, ga yadda al'adar gidanmu take shi kam ba zai ruguza ta ba saboda wani dalilin Uncle maras kai da kafafu. Cewa ma yayi idan bani da mijin aure a hannu yanzu to ya riga da ya min a Najeriya, zai turo shi mu gana. Ganin cewa Kawu ya dage ne da gaske yasa Uncle ya kira Marwan a waya ya mishi bayanin halin da ake ciki, duk da cewa baya gari amma haka ya ture duk abubuwan dake gabanshi ya dira a Mumbai washegari. Suka tattauna da Kawu sosai ya mishi bayanin komi da dalilinsa na yin hakan, yace to a bashi zuwa nan da jibi zai je yaji ta bakin mahaifiyar shi. Kawu yace babu damuwa, zai zauna zuwa jibin, idan ya dawo sai ya koma. Ko hirar kirki bamu yi ba dashi ya kada kai ya tafi Shimla inda anan ne mahaifiyarsa take zaune.

Bamu hadu a waya ba sai da dare, ya kira ni lokacin ma har na kwanta. Na daga kiran da sansanyar murnata, ya amsa a kasalance, muryar shi na bayyana halin damuwar da yake ciki. Gabana ya fadi, abu na farko daya fado min a rai shine cewa mahaifiyar shi baya yi na'am da zancen auren mu ba kila. Cikin sauri da sarkewar murya na tambaye shi lafiya? Yace babu komi Meenah, mura ce ke damu na. Ban yarda da hakan ba, amma sai na kyale shi kawai. Muka fara hira yana tambaya na game da makaranta da yake last week na fara attending classes, ni kuma Ina bashi labaran ban dariya. Nan da nan ya wartsake yana ta kyakyatawa, naji sanyi sosai a raina. Dare ya tsala sosai lokacin da ya min sallama yace zai kwanta, nayi kan-kan da muryata tayi kasa sosai na kira shi da sunan da yake tsananin faranta mishi rai idan yaji na fade shi.., nace "Mera Dil Khushi.... (Farin cikin zuciyata!)" ya dan ajiye numfashi tare da yin murmushin jin dadin da sunan ya mishi yace menene Meenah darling?? Na kara sanyaya muryata yadda zai jita har cikin ransa nace "meke damun ka ne? Ka taimake ni ka fada min damuwar ka ko na samu nayi barci mai dadi, kasan cewa raina ba zai taba mun dadi ba matukar kana cikin damuwa..." yayi shiru na dan lokaci kafin yayi faking wata dariya wadda kana jinta ma kasan cewa kakalo ta yayi don dole kawai don ya kwantar min da hankali, yace m fine fa darling, me kika gani ne har ya saka ki zargi cewa ina cikin damuwa? Na girgiza kaina, haba dai! Kaima kasan cewa ba haka na saba jin muryar ka ba, duk da cewa bana ganinka amma nasan cewa kana cikin damuwa. Plssss ka fada min mana ko na samu sanyi a cikin raina, kaji?? Yayi shiru na dan lokaci har sai dana sake cewa huhhh??? Dan Allah!!
Ya ja ajiyar zuciya mai nauyi kafin yace "Meenah ina tsoron hukuncin da Mahaifiyata zata yanke min akan aurenmu dake ne, wallahi jikina ya bani ba zata amince min nayi auren nan ba!!" a sanyaye kuma cikin matsanancin faduwar gaba nace Me yasa kace haka?? Ya sake jan wata ajiyar zuciyar, yace "saboda..... Ermmm.... Saboda ex wife dina!!!" na zabura na tashi zaune dangargar daga kwanciyar da nayi a sukwane, nace "what!??? Ur ex-wife????!!"




©Jeedderh🐾

[5/2, 10:52 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•22•°🐾


A sanyaye yace "kiyi hakuri, ban sanar dake akan lokaci ba. Sunanta Hindu, diyar kawar Mamanmu ce ta kut da kut, Maah ta hada mu auren zumunci da ita bayan na kammala degree na wai da niyar kara dankon zumunci a tsakaninsu. A New Delhi muka zauna da ita lokacin ina karamin star ne a harkar fina-finai na ban yi waya shaharar azo a gani ba. A iya tsawon zaman da muka yi da ita na shekaru biyu na fahimce ta a wata irin mace mara tarbiya, wadda bata san darajar mijinta da auren da yake kanta ba. Wallahi tunda na aure ta jin dadi da natsuwa suka yi kaura daga cikin rayuwa ta, na nemi walwala da kuzari na na rasa. Magana ta gaskiya na auri Hindu ne don yiwa mahaifiyata biyayya ba wai don ina sonta ba, ta fannin Hindu ne dai nasan cewa I was her crush since college, ban san zuwa lokacin ko tana sona ba still. Hindu macece mara son zama lafiya da dan banzan korafi, dan kankanin laifi zan mata sai ta kai kara ta wajen mahaifiyata, sai tafi sati tana nanata magana guda babu gajiyawa. Akwai wani kamfanin mahaifinmu da muka ci gadonsa ni da kani na Kabeer yana nan Mumbai, da na fara shirye-shiryen dawo dashi New Delhi ne, amma saboda Hindu yasa na canza shawara kan zan barshi a Mumbai kawai. Hankalina sai ya koma kan tado da kamfanin da da a rufe yake, sai harkokin film dina da zamana a gida duk suka ja baya. Ina so ne in yi saurin tayar da kamfanin yadda idan Kabeer ya dawo daga makaranta yana karantar business administration zai cigaba da kula da kamfanin, ni kuma in cigaba da gudanar da harkokin film dina a nutse.
Sau biyu ina kama Hindu tana zubar min da ciki, raina ya baci sosai da abinda take yi, na mata kashedi na karshe akan cewa kada ta kara zubar min da gudan jini na. Sai dai bata dauki gargadina a wani abu ba, ba a kwashe watanni biyar cikakku ba sai gata a gadon asibiti ta zubar da wani cikin. Raina yayi mummunan baci har na rasa abinda zan ce mata, da naje asibitin da aka kwantar da ita tana kwance ta wartsake daga azabar da tasha, idanunta fess babu alamun komi ta kalloni wai tana tambaya ta ya aka yi nasan cewa tana nan? Kawai ce mata nayi daga nan ta wuce gidan su, zan neme ta idan na yanke shawarar yadda zanyi da ita.
A ranar ban kwana a New Delhi ba na wuce Goa zanyi shooting film dina da zai fita, washegari tun da safe kiran mahaifiyata ya riske ni, tace lallai tana son gani na in ajiye komi nake inje. Haka na tafi Shimla bayan na dauki duk wasu takardu shaidar zubar min da ciki da Hindu tayi. A can na sameta a gidan mahaifiyata fuskarta tayi jawur da shacin hannu wai ni na mare ta. Maah tayi ta fada kamar zata dukeni, sai dana bari ta gama fadace-fadacen ta sannan na zube mata takardun na kuma yi mata bayanin halin da muke ciki ni da Hindu, duk da cewa ban fadi wasu abubuwan bama amma ran Maah sai daya baci sosai. Nan ta shiga yi mata fada kan cewa abubuwan da take yi bata kyautawa, menene abun zubar da ciki kuma?? Wallahi budar bakin yarinyar nan sai cewa tayi, ita bata shirya haihuwa dani yanzu ba, idan ita Maah din ta damu da in samu dan cikina mai zai hana ita ta haihu dani?? (Wa'iyazubillah!!). Ai a take na tashi na watsa mata yatsu na biyar a kuncinta har sau hudu, na kuma furta mata kalmar saki biyu. Nan ta fita tana masifa ta bar Maah na kuka da sallallami. Da kyar na samu na shawo kanta ta daina damuwa, sai dana ga ta dawo cikin natsuwarta sannan na mata sallama na koma wajen aikina.
Yanzu shekarunmu biyu da rabuwa da Hindu, ban san ya aka yi suka shawo kan Maah ba ita da mahaifiyarta, ni dai naga sun shirya har ta fara matsa min da maganar in dawo da Hindu. Yanzu dai a inda muke da ita kenan, to kuma bansan ya zamu kare da ita akan zancen aurenmu dake ba."

Na saki ajiyar zuciya yayin da wata zufa ta lullube ni. Nayi shiru da tunanika barkatai a raina har na rasa da wanne zanyi dealing. Ranar dai haka muka yi sallama dashi ran kowa a jagule, jiki a sanyaye babu kwari balle mu samu tausar junanmu.




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:52 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•23•°🐾



Washegari tun safe har dare babu labarin Marwan, nayi duk iya kokari na to reached him even at phone amma ban samu damar yin hakan ba. Jikina yayi sanyi sosai, na kasa hadiya ko ruwa a cikina, jikina ya gama bani cewa mahaifiyar Marwan bata yarda da auren mu ba, idan hakan ne kenan Marwan zai kyale ni? Idan ya kyale ni ya zanyi da rayuwata?? Kawai ji na nayi na kece da kuka mai karfi, na dukunkune akan gado nayi tayi ba kakkautawa. Anti ce ta shigo ta same ni a wannan halin, cikin sauri tazo ta tashe ni daga kwanciyar da nayi hankali a tashe tana tambayata me ya faru?? Duk yadda naso in boye mata maganar kasawa nayi, at least yakamata ace wani yaji ko don a bani shawara. Na bayyana mata komi babu abinda na boye mata, na kula itama nata jikin yayi sanyi sai dai ta boye min. Ta rungume ni tana dan dukan bayana cikin alamun rarrashi tace min kada in damu, in Allah ya nufa Marwan mijina ne to babu makawa dole sai na zama matarshi no matter what. Zuciyata ta danyi sanyi, sai dai duk yadda taso akan in samu in dan ci wani abu kasawa nayi, da kyar ta samu ta dura min robar yoghurt. Ranar dai haka raina ya kwana a jagule.

Washegari wajen karfe tara na safe sai ga Marwan a gidanmu, wayyoo dadi! Kasa jira a fada min abinda ke faruwa nayi, na tafi bakin kofar dakin Kawu ina labe. Marwan ya ba kawu hakuri akan rashin dawowa jiya da bai yi ba yace bai iso garin da wuri bane sai wajen karfe sha biyun dare, ya kuma kara da cewa mahaifiyar shi ta amince da zancen aurenmu, Yayan mahaifinsa dake Kano zasu je neman aure na a wajensu Kawu idan ya koma gida. Kawu Hamza yayi hamdala ga Allah kafin ya saka mana albarka, a ranar ya juya gida. Murna a waje na kamar inyi me! Na ruga daki na da gudu nayi sujjada ta godiya ga Allah. Anti ta shigo da fara'ar ta zata bani labari, ganin halin da nake ciki yasa ta gane cewa labari yazo min tuni don haka ta juya. Wayata na janyo na kira Marwan ina bayyana masa farincikin da nake ciki, "akwai pa matsala Meenah!!" cewar shi a sanyaye. Gabana ya dan fadi, murnar da nake ciki tayi kasa, nace matsalar me kuma? Ya nisa, yace Maah ta amince da aurenmu ne akan sharadin zan maida Hindu dakinta, ni kuma na amsa mata da zan maida ta ba tare da na nemi shawarar ki ba. Duk da dukan da zuciyata tayi bai sa na kasa kakalo murmushin dole ba, "to sai me don zaka mayar da tsohuwar matarka? Ni in dai akan wannan ne kake damuwa to ka daina, na amince dari bisa dari akan ka maida ta" yace da gaske kike? Sai na saki murmushi very soft, nace "anything for ur happiness dear...!!" sai yayi dariya, yace nagode my angel, Allah ya kawo ranar aurenmu. Nace Ameen.


*******

Sati uku kacal aka saka a matsayin ranar biki, ni kam kafin lokacin na cigaba da zuwa makaranta abi na. Saura sati biyu a fara bikin muka tafi Nigeria don mu uku za ayi wa bikin, akwai Jamila diyar Kawu Jazuli sai Lawisa diyar Kawu Hamza, don haka shirye-shirye ake yi bana wasa ba. Duk da hakan na fita ta daban a cikin amaren, domin tun a India Anti take ta faman gyaran jikina, gashi mun dawo nan Ammie ma ta dora da nata. Nayi wani irin fresh na ban mamaki yadda kasan cewa an canza min kamanni ne, ga wani popularity da nayi cikin dangina da abokaina, ko ina nayi sai dai kaga ana nuna ni, ala dole zan auri celebrity. Ana saura sati daya daurin aure yayyena mata suka fara dira, su kam irin nasu shirin ba a yin magana. A cewarsu bikin Auta Ameenah ne da Marwan, dole ne duniya tasan cewa ni pa er gata ce.

Ban san ta yaya zan bayyana tsaruwar bikin mu ba, illa iyaka ince ban taba ganin bikin daya burge ni irin bikin mu ba. Garin Gombe ya kwashi baki kala-kala da celebrities dangin mawaka ne da en wasan kwaikwayo iri-iri musamman daga India, bikin da mutane da dama suka ce basu taba ganin taron da yayi jama'a irin bikin mu ba. A daren ranar aka mika ko wace amarya gidanta, nima a daren ranar jirginmu ya daga zuwa India. Fadin irin kukan da nayi a lokacin ma bata baki ne, duk da cewa ba yau na saba barin su Ammie na ba, amma sai naji kamar idan na tafi shikenan, a haka dai muka rabu da en uwana ina kuka suna taya ni.

(Sauka lafiya Amaryah Meenah-Auta!)




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:53 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•24•°🐾


Garin Shimla muka sauka, gida guda aka ware mana ni da en rakiya ta. Mun samu tarba ta mutunci da karramawa daga hannun en uwan Marwan, muka yi wanka muka biya bashin sallah data same mu cikin jirgi muka ci abinci, daga nan muka kwanta sai barci. Wayan da Marwan ya bugo min ce ta tashe ni daga barcin da nake, na daga wayar cikin magagin barci muka gaisa ya min barka da zuwa don ba dashi aka je taro mu ba. Muna ta hirarmu yace da dare zai turo azo a tafi dani wajen dinner da abokanshi suka shirya ta taya mu murnar aure, na amsa da Allah ya kaimu daren lafiya. Daga nan muka yi sallama. Da dare sai ga wasu mata su biyu sun zo wai zasu shirya ni don zuwa dinner, nace toh. Nan suka hada wani irin ruwa da wasu furanni suka min wanka sosai da wasu irin sabulai masu kamshi, suka wanke min gashi tass, daga nan suka min gashin jiki da gashi da wani irin turare mai kamshi. Awanni biyu curr suka dauka suna shirya ni, sai gani na fito tsab cikin saree mai tsada na en asali kasar India, suka saka min sarkar gwal a hannu, kunne, kafa, yatsun hannu har a hanci na. Gashina suka shirya shi ya kwanto har gadon baya na, suka bi suka manna wasu stones a jikin gashin sai sheki

Please Login or Register in order to submit comment