Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai aka dora musu alkyabba baka a jikinsu. Suna zaune akan wasu kujeru na alfarma sun fuskanci dubban jama'ar da halarci taron walimar auren su zazzaune akan fararen kujerun roba a karkashin canopies din. En jaridu da masu daukar hoto na gefe suna daukar hotuna, Wakili's Family babban family ne daya tara manyan en kasuwa, en siyasa, ta bangaren army ma ya tabo manya, family ne wanda ciki da wajen Gombe babu wanda bai san da zaman su ba, daidai gwargwado mutane suna girmama su. Muryar Malama Atika Abubukar ta karade wajen da sautin Wa'azinta ta hanyar lasifika, tayi magana akan hakkin miji akan matarsa da hakkin mata akan mijinta da kuma hakkokin da suka rataya akansu su duka, ta tabo mafi yawan matsaloli da ma'aurata suke fuskanta a wannan zamanin da kuma hanyoyin da take gani yakamata abi domin a magance su. Da yawan matan dake wajen jikinsu yayi sanyi sosai da wa'azin malamar, suma amaren jikinsu a matukar sanyaye yake saboda tunawar da suka yi cewa gobe war haka fa wani nauyi ne zai hau kansu wanda shi zai yi sanadin zuwansu Alanna idan sun sauke shi ta hanyar data dace, kuma dai wannan nauyi zai iya kaisu zuwa wuta idan har basu kiyaye dokokins sa ba. Ameenah kuka take yi sosai, tana rokon Allah akan yasa ta yiwa mijinta biyayya irin wadda Malama Atika tace mace na yiwa mijinta, tana tsoro! Tana tsoron zuciyarta, tana tsoron zuciya ta hana ta bin mijinta Allah ya jefata cikin azabarsa.
Daga karshe Malamar ta rufe taron da addu'a da fatan alkhairi ga Amaren, aka watse daga taron bayan an bi duk wanda yazo wajen da jaka irin ta biki mai dauke da sunayen duka amaren da angunansu, akwai kula a cikin jakar itama da sunayen couples din, kowa ya tafi yana musu fatan zaman lafiya mai dorewa.
Aka bar Ameenah a zaune har zuwa lokacin tana kwararar da hawaye cike da alhinin irin sabuwar rayuwar da zata shiga gobe. Sauran amaren kuwa tuni sun shige cikin kawayensu suna gaisawa dasu don haka babu wanda ya kula da halin data shiga. Ta mike a hankali take tafiya, kanta na masifar sara mata sam bata da karsashi. Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige ta kulle kofa ta kwanta ba don tana jin barci ba, Al-Ameen yana wajen Ya Faruq don haka bata damu data nemi inda yake ba. Har zuwa lokacin da nata angon ya iso tare da zugar abokanshi cike da dokin sake dora ido akan kyakkyawar fuskar ta, yau kawai da bai ganta ba zuciyarshi a matukar galabaice take. Amma neman duniya aka rasa Ameenah a cikin gidannan, an kuma kira wayarta aka ji a kashe. Sai jikin shi yayi wani irin sanyi, duk yadda yaso ya boye damuwar ranshi game da ita abin yaci tura, bai san me yasa ba yarinyar na da wani irin tasiri a ranshi wanda yasa sam bashi da wani katabus muddin akanta ne. Abokanshi sun lura da halin daya shiga a take, very disappointed, missing his bride very badly. Sai suka shiga mishi tsiya, wai ya daure mana, yau ne kawai ya rage, gobe war haka suna tare ta zama tashi. Hakora kawai ya dinga watsa musu cikin yake, don kuwa can kasan zuciyar shi is aching him, ita kawai yake son gani. Kawai sai suka shiga cikin sauran angwayen ana ta hirarraki da en matan amare, Sai bayan magariba suka bar gidan.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕


*A LOVE STORY SEALED WITH CHALLENGES.....*

🐾°•50•°🐾


Ameenah bata fito daga dakin ba sai da tara na dare ta gota, tun lokacin tana kwance babu abinda take yi sai kuka da tunanika, idan an kira sallah zata tashi tayi tunda akwai toilet a cikin dakin. Dama dai ba a zancen abinci, rabon data saka wani abu a bakinta tun wani tukudi da Anti Nadiya ta takura mata tasha da safiyar ranar, bayan shi bata ci komi ba, kuma bata sha'awar cin komi.
Su Anti Jamila na falon suna hira lokacin data fito daga dakin, idanunnan nata sun kada sosai. Cike da mamaki suke bin ta da kallo, sam basu yi tunanin tana dakin ba, ko kadan ma hankalinsu bai kawo zata je wajen ba tunda ba a cika ta'ammali da dakin ba. Anti Jamila ta kalleta tace baki da lafiya ne Ameenah? Ta girgiza kanta a sanyaye amma bata ce komi ba, Anti Nadiya tace tun dazu Ammie da Faruq ke neman ki, Al-Ameen yayi ta kuka da bai ganki ba. Sai lokacin tayi magana cikin shakakkiyar murya kamar wadda mura ta kama, tace can zan je yanzu. Ta juya a sanyaye zata fita, Anti Jamila tace kin kuwa ci abinci Ameenah? Ta juyo tana kallonta fuskarta dauke da dan murmushi duk don ta kore damuwar data hango zane baro-baro akan fuskokinsu, tace manta da abimcin nan Anti, a koshe nake. Sai da safen ku.... Ta karasa fita da saurinta.

tun daga nesa ya hango ta tana tafe a hankali kamar wadda kwai ya fashewa a jiki, ya saki wata irin doguwar ajiyar zuciya wacce bai ma san yayi ta ba. Tun komawarsu hotel din da yayi masauki shi da abokansa, gabadaya zuciyarshi ta rasa sukuni. Iya dauriya yayi amma abin ina, kasa daurewa yayi wai har sai gobe ne zai ganta, gani yake yi idan ya wayi garin gobe ba tare daya saka Ameenah a kwayar idanunsa ba, babu mamaki a tarar da gawarsa a daki. Ya rasa irin mayataccen son da yake yi mata, da dai abin bai kai haka ba amma tunda ya sake ganinta for the third time, ya sake rasa sukunin shi, daidai da sakan daya tunanin Ameenah yaki ya kyale shi, komi yake yi tare da tunaninta yake yin sa. Ba shiri ya dauki makullin mota ya taho gidan don Anti ta tabbatar masa cewa lallai Ameenah na cikin gidan.

Ba zato taji an ja hannunta anyi gefe da ita, baki ta kware da niyar kwala ihu taji ansa hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka ce "shhhh!!!" manyan idanunta da suka canza kala ta daga a hankali ta kalleshi, inda suke babu wadataccen haske. Duk da cewa bata ga fuskarshi ba, amma ta dauki muryar shi. Cikin sauri ta ture hannunshi daga bakinta ta fita fili wajen haske, ya biyo bayanta ya tsaya a gabanta suka fuskanci juna. Ya matsa daf da ita kamar wanda ke son shigewa jikinta, yace ina kika shiga tun dazu muke ta nemanki? Ta dan matsa baya kadan, cikin tamkewar fuska tace bana tunanin abu ne wanda ya shafe ka sanin inda naje din!. Ya daure fuska, "ban gane ba? Kin kuwa san irin kunyar da kika bani dazu? Nazo da tarin abokaina suna son ku gaisa amma aka neme ki aka rasa, kin san irin muzancin dana shiga lokacin?" tace Wannan ba damuwa ta bace Modibbo! Plss idan baka da wani abin cewa excuse mee... Kaina yana sara min. Ya bude manyan idanunshi akanta, hakan ya janyo mata jin wani irin kasala a jikinta. Yace me yasa ne baki da kunya ko kadan Ameenah? Me yasa sam baki san inda ya dace da wajen da bai dace kiyi rashin kunya ba??" baki ta murguda tace ina ga ai kai ka tari rashin kunyar, Kai ka shiga harkata da rayuwata don haka indai rashin kunya ne to yanzu kuwa ka fara gani!. Ya dage gira sama, "Allah da gaske? To Dan Allah sake yi mun rashin kunyar yanzu mana ki gani, zanyi maganinki anan take wallahi, don't try me Ameenah I don't tolerate sh**t da kike gani na nan!!". Kashedin ya shige ta sosai ya kuma fadar mata da gaba, amma hakan bai hanata bude baki cike da jarumtaka ba tace anyi maka rashin kunya din, kayi duk abinda zaka yi....!!" babban yatsan hannunshi na hagu ya hada da yatsan tsakiya ya sakar mata su a baki, ba shiri ta sanyawa bakinta kwado, tasa hannu ta dafe wajen Saboda tsananin zugin da yake mata. Kan kace meye wannan? Hawaye sun fara zarya akan kumatunta kamar an bude famfo, dariya ce ta kusa kamoshi, lallai yarinyar nan a shagwabe take. Murya irin ta wanda ke son fashewa da kuka tace "Allah ya isa na mugu! Kuma ma auren an fasa tunda kai mugu ne!!".
Ya saki murmushi sosai yace "very good! Da kin kyauta min sosai kuwa, kuma Ke zaki yiwa kanki babun badinahu. Kin dai san ko yanzu kika fasa aure na to a goben ko mata hudu nace zan aura ba zan rasa ba, saboda ni saurayi ne sabon jini, fresh guy babe! Sabanin second hand. Ke kanki kinsan bacin kaddara babu abinda zai yi hadin saurayi da Bazawara!!". Sai ta damke bakinta da hannu ta falfala cikin gida da gudu don kuwa ta tabbata idan ta bude bakin to kuka zata fashe dashi, abinda kuma bata so kenan; ya gano weak point dinta.
Shi kam binta yayi da kallo har ta shige cikin gidan, ya shafa sumar kanshi yana murmushi cike da nishadi marar misaltuwa, yace "yarinya ki gama duk kewaye-kewayen ki da rashin kunyar ki, gobe war haka nasan tuni na kashe bakin tsanyar" ya fada motarshi ya fita daga gidan a nishadance.

Sai data tsaya a bakin kofar falonsu ta share fuskarta sannan ta shiga ciki, ba kowa a falon don haka ta shiga dakin Ammie. Tare ta same ta da wasu daga cikin en uwansu da suka zo bikin, ta gaishe su suna ta tsokanarta. Alfarmar ta musu yaken murmushin data saba ma yau basu samu Ba. Ammie ta dinga bin ta da kallo har ta iso wajenta, tace Auta nah kin kuwa ci abinci? Karya ta mata tace Ehh. Ta gyada kai tace to Maza kije ji kwanta dare yayi, da ganin ki kuma kina bukatar hutu. Sai da safe ta musu ta juya ta tafi dakinta, akan gado ta samu Al-Ameen a kwance yana barci, tayi murmushi ta shafa sumar kanshi tare da sumbatar goshin sa. A hankali ta haura kan gadon ta kwanta tare da rungumoshi zuwa jikinta, fatan ta daya Allah yasa kada Ammie ta hanata tafiya da Al-Ameen idan zasu tafi Kano gobe, ta lumshe idanunta har barci ya dauketa.


*_Washegari...._*

Qarfe goma sha daya na safe aka daura auren Amaren hudu, da yake gabadaya aka hada auren aka daura har na Safeenah saboda Alhaji Abbas yace kada a wahalar da mutane kawai a daura anan, Ana daura auren maza suka zarce da reception a Vomella Hotel, yayin da aka dauko Amarya Safeenah daga Kano aka taho Gombe da ita saboda ta samu ta halarci dina da za ayi da dare.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:06 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•51•°🐾


Tunda taji an daura aure jikinta yayi wani irin sanyi marar misaltuwa, gado ta haye saboda zafi da jikinta ya dauka ta dukunkune a cikin bargo tana rawar sanyi. Anti Jameela ta shigo dakin ta same ta a halin da take ciki, tayi salati tana tafa hannu ta nufeta da sauri, ta tsorata da halin data ganta. Tace Ameenah kan ki kike so ki kashe ne?? Ta fita da sauri sai gata ta dawo da kwano da magani, ta taimakawa Ameenah ta tashi zaune, da kanta ta dinga bata abincin tana lallashinta cikin tausasa murya. Ya Faruq ya shigo dakin sanye da bugaggiyar bakar shadda, ta daga ido a hankali tana kallon Yayan. Wani irin haske da annuri ne kawai ke fita a fuskarshi, lallai shekin angonci daban yake. Ya zauna a gefen gadon ya dan dafa goshin Ameenah yana tambayar Anti ya jikin nata? Tace mishi zazzabin ya dan sauka yanzu. Ya amshi magani a hannun Anti ya durawa Ameenah a baki Anti tabi da ruwa, suka shiga bata kalamai masu taushi sai gata tana murmushi. Shi da Anti suka yi dariya a lokaci guda, Faruq yace toh ko ke pha Auta?? Maza tashi ki wa baby wanka a shirya min shi, mu je mu taro amarya ta dashi tana kan hanya. Ameenah tayi dariya ta sungumi Al-Ameen dake barci a gefenta ta shige toilet, su Anti suka fita suka ja mata kofar dakin.
Ta wanke Al-Ameen tas wanda sanyin ruwa ya farkar dashi ya bude ido tangararas yana kallonta yana mata wasanni wadanda suka saba idan tana mishi wanka. Ta biye mishi itama, baka jin komi a lokacin sai sautin dariyar su. Ta nade shi cikin towel suka fito, daidai lokacin Anti Hadiza yayarta ta fado dakin, tace yauwa Anti ga dana ki shirya min shi, bari inyi wanka" ta koma bandakin Anti kuma ta dauki Al-Ameen ta fara shirya shi.
Lokacin data fito har Anti ta gama shirya shi cikin tattausar farar shadda irin ta jikin Faruq, sai tashin kamshi yake. Ameenah ta rungume yaron tana jin kaunar shi sosai a jikinta. Ta dago shi daga jikinta tace kayi kyau yaro na! Yayi dariyar shi mai kyau dimples dinshi suka lotsa sosai, yace Ke ma mommy. Dariya tayi ta nutsa yatsar ta a kumatun shi inda ya lotsa tace Love yah baby. Gaban mirror ta koma ta shafa mai, ta zira rigar sallah a jikinta ta sallaci azuhur. Sannan ta dawo gaban mirror ta zauna ta fara shafe-shafen hoda, duk da ba wata kwalliyar azo a gani tayi ba amma kyawunta ya fito sosai. Tana cikin zira gown din atamfa da Anti Hadiza ta fitar mata na ankon su, Antin ta sake shigowa da plate a hannunta, tace baby Al-Ameen Faruq yana jiranka a falo. Ya fita da gudunsa yana wa Ameenah bye.
Ta mikawa Ameenah plate din tace "amshi ki cinye yazo Auta" ta kalli plate din farfesun kaza ne yana ta kamshin daddawa da tafarnuwa mai dadi, ta cuno baki kamar zata yi kuka tace "wai farfesun ne again?? Ni pha na gaji da cin abubuwan nan!" Anti Hadiza tace ba zaki gane irin gatan da muke kokarin yi miki bane yanzun har sai kinje gidanki Auta, wannan shine martabar ko wace 'ya mace. In dai kina son kiyi gashi a idon wannan mijin naki to ina tabbatar miki wadannan sune manyan makamai daya kamata ki yake shi dasu musamman da ba a budurwa zai aure ki ba" tace to wai ni dama nace miki ina son yaso ni ne? Anti tayi murmushi tace baki ce ba, yi hakuri kici wannan ne na karshe kinji? Tana kumbure-kumbure da gunaguni haka ta amsa ta cinye kazar ta shanye romon. Anti ta dauki kayan kwalliya ta kara gyara mata kwalliyar ta, ta dauki dankwalin atamfar ta mata wani irin nadi a kai sai ta fito kamar wata African queen. Anti Hadiza tayi murmushi tace Masha Allah!! Kin yi kyau sosai kanwata. Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, Ameenah mutum ce mai tsananin son compliment. Anti tace yauwa, just continue smiling like this for the whole day, promise?? Ameenah ta gyada kanta da sauran murmushi a fuskarta. Anti tace good! Muje ku gaisa da baki. Ba musu ta bi bayan Antin. Falon nasu a cike yake da mutane, tana fitowa sai kowa yayi caaa a kanta, masu guda nayi, masu tsokana nayi, da kyar ta samu ta fita daga sashen ta tafi na Ya Almu inda a can sauran amaren da kawayensu suke. Tana shiga hasken flashes na camera ya dallare mata ido, tayi saurin saka hannu tana karewa. Muhibba daya daga cikin cousins dinsu ta riko hannunta suka shiga daukar hotuna kamar ba gobe, suna yi suna shakiyancin su kamar dai yadda kawayen amarya suka saba yi, Ameenah sai dai tayi murmushi kawai idan suka tabo ta.
Sai karfe hudu na yamma amaryah Safeenah da tawagarta suka iso, Ya Faruq ya kamo hannun matarshi dake lullube cikin lafaya ya jata har sashen ta inda zata zauna, bai kuma saki hannun ba sai daya kaita har kan gadonta ya zaunar da ita, mutane suka bi bayansu masu shewa nayi masu daukar hoto nayi. Abokan wasa suka mishi caaa akai dole ya bar gidan. Nan sashen amaren suka koma aka cigaba da gashi.

Da misalin karfe takwas na daren ranar, amaren na zazzaune a gaban mirror sanye da dinner gown, masu kwalliya na tsaye a kansu kowacce na gwada basirar da Allah yayi mata ta wannan fannin. Kada ku so ku ga amaren a wannan lokacin, yadda kasan a sace su a gudu saboda tsananin kyawun da suka yi kamar wasu masu modeling. Doguwar riga ce har kasa a jikinsu ta wani silk yadi, sai dai kowannensu kalar shi ta banbanta, wani net aka yi amfani dashi aka yi tattara a bayan rigar inda sauran ya zuba har yana jan kasa. Da yake dukansu suna da gashi Masha Allah, sai suka kitsa gashin jela daya bayan sun bar wani style a gaban goshin su, suka nade jelar gashin ya bada wani style na daban kamar nadin fure, suka yi amfani da pin suka nade karshen, sai suka dauki siririn gyalen kayan suka dan zizaro shi daga sama sauran gyalen ya sauka a gadon bayansu. Kamshi suke fitarwa mai sansanyan kamshi. Kafin a gama shirya su tuni Abokan anguna sun kwashe kawayen amarya, saura angunan kawai da amaren.
Kowacce wadda ta shiryata ta kama hannunta suka fita, motoci ne bakake har guda hudu anyi parking dinsu a kofar falon, angunan na tsaye cikin shiga ta yadi mai taushi wadda ta hau da kayan dake jikin amaren. Kowane Ango ya tafi ya taro amaryar shi cike da tattali ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, amma shi Modibbo tsayawa yayi cak kawai ya kurawa amaryar tashi ido cike da maita. Ji yake kamar ya hadiyeta ko ya samu ya huta da wannan azababben son da yake mata, kanta a kasa haka suke tafiya amma tana jin idanuwansa akanta, don haka koda wasa bata yi kuskuren daga idanuwanta ba, sai da suka isa daf dashi kafin ya samu kuzarin dauke idonshi daga kallonta, yayi azamar sa hannu ya bude murfin motar na baya, matar ta taimaka mata ta shiga, ya maida murfin ya rufe. Daya gefen ya zagaya ya shiga ya zauna a gefenta, direba yaja motar a hankali suka bar farfajiyar gidan.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:06 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•52•°🐾

A cikin motar babu wanda yace da dan uwansa ci kanka, ita gefe guda ta juyar da kanta tana kallon hanya tana tunano wani lokaci da aka mata kwalliya cikin saree zata je dinar auren su ita da Marwan, irin tattalin daya dinga mata da kulawarshi a gareta, farincikin daya shiga a wancan lokacin...., sai zuciyarta tayi saurin ce mata kul! Yanzun ke matar aure ce, matar wani... Tayi saurin lumshe idanunta tana jan a'uziyyah tana istigfar. Yayin da Modibbo ya jingina bayanshi da seats din motar ya dafe kanshi, a zahiri idan ka ganshi zaka yi tunanin stress da gajiya ne suka tarar mai, though yes akwai gajiya wadda kusancinshi da Ameenah ya saukar mishi yanzun nan. A kaikaice kuma hanci ya ware yana shakar daddada kuma tattausan kamshin da Ameenahr keyi wanda yake jin kamar duk shaka daya da zai yi yana kara mishi tsabar son ta da sha'awar kasancewa da ita, hakan ya saukar mishi da wata irin kasala marar misali. Jikinshi lakwas haka suka isa Vomella Hotel inda za ayi dinar. Wajen ya kawatu sosai, haske tarr yadda kasan rana ce ba dare ba, mutane dankam suka tarar a bakin shiga wajen suna jiran isowarsu. Da isar su kuwa en jaridu da masu hotuna suka taro su da ruwan flashes har kan mazauninsu sannan kowa ya nemi waje ya zauna, babu bata lokaci aka fara gudanar da events na dinar. Muhseen babban abokin ango Modibbo shi ya bada tarihin ango na karshe (Modibbo), bayan ya gama bada tarihin ya kara da cewa shi bai taba ganin taro ko biki wanda ya kayatar dashi irin wannan ba, ya kuma ce bai taba ganin ango da amarya da suka dace da junansu irin wadannan ba. Ya kara da cewa akwai yiwuwar shima zai zagayo ya lallabo cikin Wakili's Family ya nemi wadda zai yi plan B da ita don ya kula duk kyawawan 'yanmata ne masu cike da zati a cikin familyn. Duk sai aka kwashe da dariya a wajen sosai, yayin da enmatan wajen suka ji kansu ya fashe sosai. Sai wajen karfe goma sha biyu aka tashi, daga nan aka wuce da amare Rukky da Maimunah gidajensu don dama tuni sun yi sallama da iyayen su, suka rungume Ameenah su ukun suna kukan rabuwa da kyar aka samu aka janye su.
Wannan karon ma Modibbo ne ya bude mata motar ta shiga, direba yaja motar suka tafi. Har suka bar wajen idanunta basu daina zubar da hawaye ba, akai-akai ta kam sa yatsa ta dauke hawayen. Ido ya zuba mata jikinshi a sanyaye, zuciyarshi na tsikarin shi wai ya rungumota ya lallashe ta, amma sam yaki ba kanshi damar yin hakan. Baya so yarinyar ta samu damar raina shi tun yanzu, yanzun ma har suka isa gida bata kalli inda yake ba, direba yana gama gyara fakin ya musu sallama ya fita daga cikin motar.
Cike da wata irin takama ya bude motar ya zagaya ya bude gefen da take, ta zuro kafarta ta fito a hankali, ya maida murfin ya rufe. Yaki matsawa ya bata hanya ta wuce, taku biyu ya kara ya isa dab da ita har suna jin numfashin juna don itama Ameenah ba baya bace wajen tsawo, ta dan ja baya a hankali, ya kara matsawa shima, haka suka yi tayi har sai daya dangana ta jikin motar. Ya kai bakinshi saitin kunnenta kamar mai rada yace "so, ina kike shirin tafiya ba ko sai da safe? Me yasa ba kya respecting dina ne Ameenah?? Dazu fa ko gaishe ni baki yi ba.... Kin kyauta kenan??" dan karamin bakinta ta tabe tace zancen kyautawa da rashin kyautawa bana zaton akwai shi a tsakaninmu... Gaisuwa kuma ban ga dalilin da zai sa na gaishe da kai bane. Yayi kasa da muryarshi yace ko albarkacin ina mijinki ba zan ci ba kenan?
Ta daga idanunta tana kallon tsakiyar idanunshi tana murmushin da yafi dangana shi dana takaici, tace da ka ambaci kalmar miji sai naji ka bani dariya, ko ka manta cewa kai da bakinka Ka fada min cewa aurena kawai zaka yi don ya zamar maka dole ba don kana sona ko kuma kana maraba da auren ba? Ina ganin kamar idan ka kira ni matar ka baka yiwa kanka adalci ba don ban cancanci na zama matar ka ba.... Shima murmushin ya saki sosai cikin kara kaurara idanunsa cikin nata, kallo mai ma'anoni da dama, sai ta rusunar da

Please Login or Register in order to submit comment