Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nata kwayar idanun don ba zata iya jure kallon kwayar idanunsa ba yanzun. Yace to yanzu ya za ayi kenan? Gashi kuma ina so ki zama matar tawa! Ta dago ido da sauri ta kalli fuskarshi, kafin ta kawar da nata fuskar zuwa kallon wani sashen daban tace babu abinda za ayi, saboda ni bana so ka zama mijina... U're lacking so many things as a husband! Yace like what??... Tayi shiru bata amsa ba. Hannu ya saka ya juyo da fuskarta zuwa gare shi, cikin zafin nama ta buge hannun nashi tace "don't u dare touch me again Modibbo! Plss don't!!" ya kalleta da mamaki yace bana tunanin na aikata wani sabo don na taba fuskar matata! Cikin daga murya tace "sau nawa kake so na fada maka cewa yadda maka dauke ni a mata ba nima ban dauke ka a matsayin miji ba? Stop putting all dat shows and get lost!! Nasan you r just pretending, but baka sona kuma baka so ka aure ni ba!!" ya gyada kanshi, you r ryt! Bana sonki, sai dai abinda ya faru ya riga daya faru, aure dai an riga an daura bamu da yadda zamu yi haka ne? Don haka na yanke shawarar zama dake a matsayin mata duk da cewa bana sonki!" ta ja tsaki, "matsalar kace ka soni ko kada ka soni bai dameni ba ka gane? Abinda kawai na sani shine ni dai ba zan so ka ba! I've already given my heart to someone who deserves it!..."
Idanunshi cike da bacin rai yake kallonta, "me kike nufi kenan?" ta murguda baki, "abinda kaji shi nake nufi!!". Hannu yasa ya shafo tattausar sumar kanshi tun daga goshi har keya, bata ankare ba sai jin saukar lebensa tayi akan nata.....

Ta zaro ido cikin tsabar shock din da hakan ya haifar mata, jikinta yayi wani irin sanyi lakwas ta rasa duk kuzarin ta. Gare shi kam jin sa yayi kamar wanda yake ziyartar duniyar Neptune saboda wani irin feeling mai dadi da yaji yana ratsa shi har tsakiyar kansa, feeling wanda bai taba experiencing irinsa a duniyar sa ba. Tsananin taushin lebunanta da wani kamshi mai sanyi da suke fitarwa, ya taimaka kwarai wajen fitar da AbdulRasheed-Modibbo a hayyacinsa, wani irin hadamammen kiss ya dinga mata mai zurfi, gabadaya ta rasa kuzarin ture shi daga gareta. Shi da kansa yayi tunanin nan ba muhallinsa bane, a hankali ya fara janye bakinsa daga nata amma bai janye daga jikinta ba. Ya bude idanunsa dake lumshe ya sauke su a kanta, idanunta a bude suke rass cikin shock din da bata fita daga cikinsa ba. Sai lokacin wani karfi yazo mata, tasa duka hannuwanta biyu ta tura shi baya da karfinta. Yayi taga-taga kamar zai fadi don sam babu kuzari a tattare dashi, Allah ya takaita ya tsaya cak.
Ya nunata da yatsa yana magana a wahalce don har zuwa lokacin numfashinsa bai daidaita ba, yace "next time, try and mention anoda man in front of me again, ko kuma ki murguda min baki, I promise you that ba tsotsar bakin zanyi ba, cinye shi zanyi duka in ga karyar rashin kunya!!".
Ta daga baki kamar mai son tace wani abu amma maganar taki fita, sai ta hutar da kanta ta juya ta bar wajen cikin sassarfa. Ya bi bayanta da kallo idanunsa na lumshewa, ji yake kamar ya kara kamota ya cigaba da kissing lebunanta don bai gaji da tsotsar su ba. Ya jima sosai a wajen kafin ya shiga mota ya tafi masaukinsa.
Lokacin daya isa karfe dayan dare ta wuce, abokansa dake tare dashi har sun yi barci. Wanka ya fara yi yayi shirin barci ya kwanta, amma barci yace bai san idanunsa ba. Yayi-yayi abin ya gagara, juyi kawai yake a gadon, Ameenah kadai yake bukata a lokacin, ita kadai. Sai dai baya tunanin ko an kaita gidanshi zai iya yin wata mu'amalar aure da ita, zai jure ko wace wahala ce ya kauda kai daga gareta har sai ya tabbatar daya saka mata zazzafan son shi a zuciyarta.

Ta bangaren Ameenah ma bata samu barci ba, da taga tunanika sun addabeta sai ta daura alwala ta kalli alkiblah. Tana kan sallaya tana karatun Al-Qur'ani mai girma aka kira sallah, ta mike tayi raka'atanil fijr ta sallaci asubahi. Sai lokacin taji wani irin mayen barci ya mamaye mata idanu, tana gama sallar ko abin sallar bata dauke ba ta koma kan gado ta kwanta, ta janyo Al-Ameen ta rungume tsam a jikinta kamar wadda take tsoron a kwace mata shi, a haka barci ya dauketa.



©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•53•°🐾


Karfe goma daidai na safiyar ranar Ameenah na gaban motar da zasu tafi Kano, cikin rakiyar duka yayyenta da wasu da yawa daga cikin jama'ar gidan, tuni en rakiyarta zuwa Kano sun nabba'a a cikin mota har da Anti Fati wadda a daren ranar zata bi jirgi ta koma Ghana. Sauran yayyenta mata duk a ranar zasu koma gidajensu. Ameenah kuka take yi sosai kamar wadda za a kaita kabari ba gidan aure ba, Ammie na kara yi mata nasiha akan wadda Kawun nan ta suka yi mata. Ya Faruq da kanshi ya bude murfin motar ya saka ta ciki, ya leka kanshi ta cikin murfin motar yace a sanyaye Auta menene abun kuka kuma? Kar ki jawo wa kanki ciwon kai fa... Ta daga baki cikin kuka tace Yaya, Al-Ameen.... Yace kada ki damu, zamu kula dashi in shaa Allah, kina yin wata guda acan zan kawo miki shi da kaina I promise you. Oyaa maza ki goge hawayenki, it's hurting me. Tayi murmushi tana goge hawayen, amma tana share su wasu suna kara gangarowa. Daidai lokacin angon nata ya bude bayan motar ya shigo, Safeenah ta leko ta tagar motar tana musu fatan a sauka lafiya. Muhseen abokin shi ya shigo ya tashi motar, daukacin jama'ar wajen suka daga musu hannuwa suna musu fatan a sauka lafiya. Ameenah ta kara bin farfajiyar gidan su da kallo idanuwnta cike da kwalla, karo na biyu kenan data bar gidansu zuwa gidan aurenta, wancan karon tana so kuma tana muradi da dokin kasancewa da wancan mijin, yayin da wannan karon kwatakwata bata son kasancewa da wannan mijin, bata kuma kaunarsa. Zuciyarta kuma na cike da tsoron kalar zaman da zasu yi da Modibbo, a yadda take ganin take-taken sa namijin duniya ne na gaske, tasan ba zai bata damar suyi zaman doya da manja irin yadda take so suyi ba. Tafi-tafiya ta daina kukan da take yi sai dai lokaci zuwa lokaci tana share hawaye dake zarya a kumatun ta. Modibbo kanshi na ga wayar hannunsa yana latsawa amma hankalinsa kacokam yana gareta, wani irin kuna zuciyarsa keyi saboda kukan da take yi babu sassauci, zuciyarsa na gaya mishi saboda bata son shi ne take yin wannan uban kukan. Anya a duniya akwai abinda yafi son maso wani kuna da kuma ciwo kuwa? Sai yaji kamar shima ya fashe da kukan, ya daure zuciyarshi ya cigaba da latsa wayar shi cikin kunan rai, idanunshi suka kada jawur. Muhseen ya lura kamar couple din basu cikin annashuwa irin ta sabbin ma'aurata, he was curious. Sai dai kasancewar sa wayayyen mutum wanda bai cika son shiga cikin harkar da babu ruwansa ba, sai ya juya ga Amaryar ya fara tsokanarta, wae ko bata son zuwa Kanon ne su juya ya maida ta Gombe yanzun nan? Tun dai tana mishi dan yake har ta ware tana tikar dariyar tsokanar Muhseen, yana da barkwanci sosai. Zuciyar Modibbo ta fara rage zugin da take ganin yadda Ameenah ta saki jiki sosai suna hirar kasar India ita da Muhseen da yake dukansu a can suka yi karatu shi da Modibbo. Bai saka musu baki cikin hirar tasu ba, ya kan dan murmusa dai kawai idan Muhseen ya tabo shi. A hankali ta fara jero hamma, barci sosai ya cika mata idanu ta dan kwantar da kanta akan Kujera barci yana fizgarta kadan-kadan, cikin dan kankanin lokaci ya kwasheta.
Ya dan saci kallon inda take, ta dan takure alamun iskar dake shigowa ta cikin tagar motar yayi mata waya, yanayin yadda kwanciyar da tayi ma kanta ba comfortable bace ba mamaki ta tashi da ciwon wuya. Sai ya mika hannu cikin tsanaki ya jawo ta ya saka cikin jikinsa, ya maida gilasan motar ya rufe, ganin haka sai Muhseen ya kunna musu AC yana dan murmushi.
Tsabar farincikin da Modibbo ya shiga a wannan lokacin baya misaltuwa, yau Ameenahr shi ce kwance a cikin jikinsa me ya kai wannan farin ciki da alfahari a garesa? Lallen hannunta yake kallo, ya fito sosai a farar fatar hannunta kamar a lokacin aka zana shi babu alamun disashewa, ya kamo duka hannuwan nata ya kai bakinsa ya sumbata cike da wani irin shauki. Muhseen yayi gyaran murya, harara ya jefa mishi, "Malam bi a hankali kada ka tasar min mata daga barci da wannan katuwar muryar taka" yayi er dariyar tsokana yace ahh, ni kawai ina tuna maka cewa ba ku kadai ne a motar ba don naga kana kokarin wuce gona da iri. Ya maida kallonshi gareta data dan motsa, yace ai ni ba dan iska bane irinka!! Muhseen ya kyalkyale da dariya yana dukan sitiyari yace banza je ka dai, na kyale ka ne kawai saboda kai farin shiga ne a harkar, so zan yi maka uzuri..." Modibbo ya gyada kai kawai yana dan murmushi ba tare daya tanka shi ba, tun asali shi mutum ne mara son magana sosai, shima Muhseen din yana cin darajar shakuwar su ne, abokansa ne tun yarinta. Ga Muhseen da dan banzan surutu da son tsokana, amma a haka ake abotar. Sanin hali sai shima Muhseen din yayi shiru ya maida hankalinsa ga tuki yana bin sautin wakar dake tashi a hankali daga cikin radion motar.


*KANO TA DABO.....*

Karfe daya na rana a cikin kwaryar garin Kano ta musu, Ameenah na dukunkune a jikin Modibbo tana barcinta cike da natsuwa har zuwa lokacin. Kai tsaye Lamido Crescent gidan amaryar suka wuce, hadadden gida ne hawa daya mallakin Modibbo. A wani zamani da aka tura shi Pondicherry yin wani course, ya ci karo da irin gidan a can, gidan yayi matukar birgeshi. Ya ga dacewar ya gina shi a matsayin gidan da zai rayu da masoyiyar shi a ciki, don haka ya dauko zanen gidan gabadayansa ya kawo aka fara gina mishi, lokacin da aka gama ginin ya ma cire rai da samun ta a rayuwarshi kwatakwata, don haka ya rufe gidan da kudirin ko da ace zai yi wani auren sai dai ya nemi wani gidan su zauna da matar amma ba dai wannan ba. To da yake shi mutum baya taba rasa abinda yake rabon sa ne sai gashi wadda aka gina gidan domin ta da kuma sunan ta ne zata shiga gidan, Allah Kenan!!
Tsayuwar da motar tayi a cikin gidan ne ya farkar da Ameenah daga barcinta. Tayi shiru tana so ta tantance a inda take kwance, ta dago a hankali ta kalleshi ba tare data janye daga jikinshi ba. Idanunshi fes a kanta ya ja fuska kamar bashi ba, kunya da takaici suka dirar mata sosai, kenan tunda ta fara barci a jikinsa take duk wannan tsawon lokacin? A hankali ta janye jikinta daga nashi ta gyara zaman gyalenta ta bude murfin motar ta fita, ya bita da kallo amma bai yi yunkurin fita ba. Muhseen dake kokarin fita ya dubeshi yace malam a cikin motar zan barka koh? Ya doka mishi harara yace idan kai kafiri ne toh ni musulmi ne, masallaci zan wuce. Ya dan dafe bakinshi yace awwwh! Na manta ashe anyi azuhur. Cikin motar ya koma ya tasheta yabi ayarin sauran abokansu da suke fita daga gidan bayan sun sauke en rakiya.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•54•°🐾


Wasu cousins din Modibbo su biyu suka fito daga can wata siririyar hanya suka tari amaryar da en rakiyarta, suka musu jagora har cikin gidan. Ameenah ta saka kafarta ta dama a falon bakinta na dauke da bismillah da addu'ar da Ammie tace ta dinga yi. Babban falo ne wanda ya sha saitin wasu genuine Italian leather seats manya, kofofi biyu ne kacal a falon kasa sai babban dinning table orange color da kujerunsa. Falon babu wani tarkace, daga katuwar plasma, sai wani katon flower vase baki da aka dora bisa dan karamin center table din dake tsakiyar falon. Gabadaya falon lullube yake da wasu mahaukatan marbles masu sheki sama da kasa, komi na falon a bisa tsari yake irin dai na cikakkun en boko da suka san ma'anar bokon. Fuskar amarya na lullube a cikin gyalenta babu abinda ta gani a falon ta dai ji suna ta zuzuta tsaruwar falon. Suka taka steps din bene suka hau sama, dan karamin falo ne a saman da dakuna guda shida reras. 'Yanmatan nan suka kai baki inda aka tanadar musu don su huta su kuma ci abinci, Anti Fati da amarya suka shiga dakin amaryar. Suna shiga ciki kafafunsu suka nutse cikin wani tattausan carpet bugun hannu, dakin babba ne sosai. Daga can gefen kudu na dakin katon gado ne wanda ke barazanar lashe mutane biyar ba tare da sun matsi juna ba, kafin ka kai ga gadon sai ka taka matakalar hudu, an lailaye gadon da wani lallausan bedsheet beig color, gadon rufe yake ruf da wani shara-sharan material mai kama da net shima beig. Sai toilet, dressing mirror, da wardrobe. Komi na dakin beig ne yana ta fitar da kamshi mai dadi.
Anti ta umarci Ameenah data shiga toilet ta dauro alwala, sai lokacin ta yaye rufar da tayi tana karewa dakin kallo a nutse. Zuciyarta ta karye sosai, wace irin kauna su Uncle suke yi mata a duniyar nan? Duk wata kauna da da yake bukatar samu daga wajen iyaye to ta samu fiye da irinta a wajensu. Da kyar ta iya daga kafa ta shiga toilet din, nan ma wani sabon babin kallo ne ta bude baki a hangame. Duk shige-shigen ta da yawace-yawacenta bata taba ganin toilet daya tsaru irin wannan ba, fadar abubuwan cikinsa ma bata baki ne kawai dai tasan ya hadu sosai. Alwala tayi ta fito, har Anti ta shimfida mata abin sallah. Ta tada kabbarar sallah ta fara da nafilah kafin ta sallaci azuhur. Kafin ta gama aka shigo musu da abinci mai rai da lafiya, Ameenah dai bata samu ta ci ba, gabadaya a koshe take jinta. Da kyar Anti ta samo kanta ta dan tsakuri abincin. Da suka gama suka fita har amarya din suka zagaya gidan, ashe basu ga komi ba dazu, yanzu ne suke ganin asalin gidan; kicin dinta kawai da kayan dake cikin kicin din sun isa su sa mutum ya sare da lamarin mutanen nan. Sai da suka zagaya ko ina na gidan har da su lambu a bayan gidan da wajen hutawa, gida dai yayi dari bisa dari sai fatan Allah ya ba maxauna gidan zaman lafiya mai dorewa, addu'ar da suka dinga yi musu kenan.
Anti Fati ta ja Ameenah suka kule a daki ta dinga mata nasiha tana kara nusar da ita game da falalar dake cikin aure da amfanin aurenta a garesu, tace "ki duba irin gatan da Mukhtar ya miki Ameenah, kina zaton akwai abinda zaki yi a duniya ki rama irin halaccin da yayi miki?" Ta girgiza kai, Antin tace "to wannan dama ce kika samu ta rama halaccinsa a gare ki, don Allah Ameenah kada ki rama alkhairi da sharri. Nasan duk wahala jinin Uncle Mukhtar yafi karfin kallon banza daga gareki, kada ki manta Abdul-Rasheed dan gidan yayar Mukhtar ne uwa daya uba daya, ko don darajar Uncle don Allah ki zauna lafiya dashi ko da ba kya son shi, kada ki saba umarnin shi, kada ki guje shi a shimfida don Allah da mala'ikun sa na fushi da masu aikata haka, ki daure ki ba mara da kunya kinji Auta?? Yadda na sanki a yarinya mai biyayya da jin maganar na gaba da ita don Allah kar ki sauya daga haka, Yanzu Abdul-Rasheed shi zai zama komi naki, sai kinyi masa biyayya ne zaki shiga aljannah kin fahimce ni?" ta girgiza mata kai tana hawaye. Anti ta fara janta da hira data taimaka wajen sanyaya mata rai har zuwa lokacin da direban da zai kaita airport ya iso, Ameenah ta rike Antin tana kuka riris har tana hadawa da ihu, da kyar ta saki Antin ta fita itama tana matse kwallar kewar Autar tasu.
Ana kiran magriba wata motar tazo ta kwashe en rakiyarta zuwa gidan Ummie, umarnin Ummien ne wai saboda kada su takurawa amarya da angon, gobe tun da safe zasu juya Gombe kenan ba lallai su sake haduwa da amaryar ba a goben, don haka suka mata bankwana suka tafi bakinsu dauke da addu'ar fatan sake saduwa da junansu cikin Alkhairin Allah, aka bar Amarya-Ameenah cikin tangamemen gidan AbdulRasheed-Modibbo ita kadai kwal kamar mayya. Har ta sallaci ishai da misalin karfe takwas na dare amma bata ji duriyar angon ba. Sai ta koma can karshen gado ta takure kanta a jikin bango, tana cike da kewar Ammie da Al-Ameen, amma tsoron kasancewarta ita kadai a cikin gidan ya danne kaso tamanin na kewar dake cin ranta, a tsorace take sosai.

Sai wajen karfe tara taji alamun bude gate, mota ta shigo an rufe, bata motsa daga inda take zaune ba amma jikinta ya bata kila ko Modibbo ne da abokansa. Ba a dauki wasu lokuta masu tsawo ba taji an turo kofar dakinta an shigo. Har zuwa lokacin kayan dazu ne a jikinsa wato babbar riga da er ciki kalar teku, kowa dai yasan yadda kalar sea ocean ke fitar da kyawun baki, ga bakin nashi ya hadu da shekin angonci don haka yayi kyau sosai ba kadan ba. Fuskarsa dauke da wata irin fara'ah ya shiga dakin yana mai zabga mata kirari, "amaryah... Amaryah ta buda sha kallo.... Amarya ba kya laifi sai kin kashe dan masu gida!!!" tayi gaggawar kawar da kanta can gefe guda zuciyarta na tambayarta dalilin daya hana ta kulle kofarta tun dazu cike da da-na-sani.
Ya ajiye ledar daya shigo da ita bisa dan karamin teburi dake tsakiyar dakin, ya janyo resting chair kusa da teburin ya zauna akai tare da mike kafa daya akan daya ya kalleta, "taso ki ci kazar amarcin kafin ta huce, kin san da zafi tafi dadi" ba ta tashi ba, hasalima kwanciya tayi ta juya mishi baya. Hular kanshi ya cire ya ajiye akan kujerar ya tashi ya nufeta cikin wani irin taku na cikakkun maza!.... Kafin ya isa inda take ya zare babbar rigarsa ya saura er ciki kawai, ya dora rigar akan gadon. Hannu yasa ya juyo ta suna fuskantar juna, yace ba dai jan aji ne zaki yi ba? Ina jan aji bai kamace ki ba tunda wannan ba shine karon ki na farko ba, ni nine farin shiga, in kika ja min aji ba ki min adalci ba. Da kyar ta bude baki tace sanin cewa kai farin shiga ne ya sanya naki jerawa da kai don kwatanta adalci, Farin shiga ai sai farin shiga ba tsohon hannu ba. Ya fadada murmushin dake fuskarsa sosai yace yeah! U're ryt! Buh kada ki damu, farin shigar ma na nan zuwa, but for now zanyi maneji da tsohon hannun.... Ya juya zai tafi, "....ki taso ki ci abinci fa ina fada miki" komawa tayi ta sake kwanciya, sai daya kai tsakiyar dakin ya juyo ya ganta a kwance. Komawa ya sake yi ya tsaya a gefen gadon, "Ameenah ki tashi ki ci abinci ko in ciccibe ki Allah-Wallahi...." Kara lafewa ma tayi akan gadon, yayi kwafa yana balle links din hannun rigar shi ya nannade hannun, ba tare da zaton ta ko tsammani ba taji an daga ta sama cimak kamar wata er tsako......!




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:07 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•55•°🐾

Duk zille-zillenta ko a jikin Modibbo, sai daya kaita har kan kujera ya zaunar shima ya zauna a gefenta. Ba tare daya nuna ya damu da irin kallon takaici mai cike da tsana da take jifansa dashi ba ya janyo ledar daya ajiye yana kokarin juye abinda ya shigo dashi a cikin plate, duk da cewa a can kasan zuciyar shi kallon yana mintsinin ranshi. Gashin peacock ya juye a cikin plate din tangaran, yaji albasa da tumatiri da dan attaruhu gashi ya danyi ruwa har tiriri yake yi alamun ba a jima da sauke shi daga kan wuta Ba. Yayi amfani da fork da wuka ya yanko naman ya nufi bakinta dashi, tayi saurin janyewa. Ya kura mata ido cike da tuhuma yace me nufinki kenan? Kai tsaye tace ba zan ci ba! Yace wasa kike yi koh? Me kika ci ne? Ya fada yana kokarin taba cikinta, ta ja baya da sauri tana watsa mishi harara. A fusace tace idan ma ban ci abincin ba ina ruwanka, cikin ka ko nawa? Yayi kasa da murya cikin sigar lallashi wanda bai ma san ya aka yi yayi hakan ba, abinda ya sani kawai shine yana so ta saka wani abu a cikinta don ya tabbata babu wani abin kirki data ci, hakan kuma ya dame shi zai yi komi kuma don ganin ta ci abincin ciki har da lallashinta. Yace da ruwana Ameenah, saboda kula da cin ki da shan ki duk yana karkashin iko na ne yanzu, ba zan so Allah ya tambayeni dalilin barin ki da yunwa ba.
Ta tashi tsaye daga kan kujerar, tsakaninta da Allah tace in dai wannan hakkin ne na yafe maka duniya da lahira, kai har dama duk wasu sauran hakkoki nawa dake kanka kaje na yafe... Hannu yasa ya dawo da ita ya zaunar inda ta tashi, ya kara dauko naman ya nufi bakinta dashi yace "naji nagode, amma ni ban yafe miki nawa hakkin dake kanki ba, umarni nake baki yanzun.... Karbi kici tun kafin na miki dura kin dai san zan iya!". Kwalla ta ciko idanunta kamar ta kece da kuka haka take ji, da wannan damar ta hakki zai yi amfani yana kwararta. Abinda ta dinga fada a cikin ranta kenan, ta bude bakin a hankali ya saka mata naman, shima ruwane ya tasattsafo a nashi idanun, yayi saurin maida su. Ya dinga bata naman zuciyarsa cike da alhini, ga dai Ameenah macen daya jima yana mafarkin kasancewarta matarsa a gabanshi yau, kuma a

Please Login or Register in order to submit comment