Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

India. Yayi dariya yayin da gefen kumatunshi suka lotsa sosai irin double dimples dinnan, ya saki wasu fararen tantabaru guda biyu daga hannunsa sannan kuma ya bisu da kallo, wasu kyawawan butterflies suna shawagi a saman kansa. Wato zanen ya zanu sosai, kai daga gani kasan kwararre ne sosai yayi zanen. Daga shi har tantabarun jiki sun fito sosai a cikin zanen yadda kasan ka kirasu su amsa... Wani irin murmushi ne ya subuce a bakinta, very cute and soft, yle feeling very bitter deeply inside ha heart.
A hankali rayuwarta ta baya ta fara yi mata yawo a idanu kamar a lokacin take faruwa.....


*......AMEENAH SANI WAKILI.....!*




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•13•°🐾


*....AMEENAH SANI WAKILI....!*


Mahaifina Alhaji Sani Muhammad Wakili da mahaifiyata Hajiya Zakiyyah, en asali garin Gombe ne kuma dukkaninsu a cikin Gomben suke Da zama. Auren hadi ne aka daura musu ba tare da kowannensu ya sani ba, sai dai dukansu sunyi biyayya ga zabin iyayensu kuma sun ga falalar biyayya ga iyaye, da kuma samun budi cikin al'amuransu.

Allah ya albarkace su da haihuwar 'ya'ya takwas., Yaya Al-Mustapha shine da na farko a wajensu yanzu haka shi babban matukin jirgin sama ne, sai Yaya Fati tana aure a Ghana, Yaya Hadiza tana auren wani kusa a Gwamnati suna zaune a Abuja ita da iyalanta, Yaya Bashir kuma lecturer ne a FUG, Yaya Abdul-Hadi likitan ido ne dake aiki da asivitin Saudi-Nigeria, Yaya Faruq kuma yana aiki da matatar man fetur ta Najeriya dake rassan Gombe, Anti Rukky wannan shekarar ne ta gama karantunta na medical doctor a jami'ar KL, sai ni Auta Ameenah. Gabadayanmu mun taso karkashin kulawar jajurtattun iyaye, sun tsaya mana tsayin daka wajen ganin mun hada kawunan mu mun zama tsintsiya madaurinki daya, kuma Alhamdulillah mun taso ne cike da kaunar juna, sam bama son bacin ran junanmu.
Mahaifinmu ya rike kujerar Gwamnan Gombe a lokacin ko haihuwa na ma ba ayi ba, bayan ya sauka mutane sun so ya sake fitowa sai dai ya ki. Sai ya fara kasuwanci wanda cikin dan kankanin lokaci sunansa da kasuwancinsa yayi tambari a ciki da wajen Gombe, Allah yayi mishi nasibi a cikin al'amuransa. Mahaifina mutum ne mai son taimakon mutane, son zumunci, kaunar en uwanshi, wanda kuma abin hannunshi bai rufe mishi ido ba ko kadan. Yasan manyan mutane da manyan Gwamnati iri-iri, da wannan damar ya dinga amfani yana samawa matasa da diyan 'yan uwa da abokai yana sama musu aiki da gurbin karatu a wajaje da dama, haka ne tasa mutane ke girmama shi kwarai.
A kokarinsa na son hada kawunan en uwanshi waje guda saboda iyayensu sun jima da rasuwa, su hudu kawai suka bari duka maza, Kawu Tijjani shine babba, sai babanmu, Kawu Hamza sannan Kawu Shazali. Mahaifinmu ya sayi wani makeken katon fili ya fara gininshi da gidaje arba'in, clinic da katon store. Yayi niyar zai tattaro en uwanshi da iyalansu domin su zauna under one roof, an dai kammala ginin lafiya lau sai dai Allah bai nufa za a tare dashi ba, Allah ya amshi ransa a wani daren juma'ah a lokacin ina da shekaru takwas a duniya. Hakika munyi kukan rashi sosai, kukan rashin wani majingini muhimmi a cikin rayuwar mu.

Wata daya da rasuwarsa Kawu Hamza ya tattara mu muka koma estate din da zama. Babban Yayanmu Al-Mustapha shi ya amsa kason mu bayan an raba mana gado ni da Anti Rukky, Ya Faruq dana Ammie ya hada da nashi ya cigaba da juya mana.

Kawu Hamza ya cigaba da tallafarmu ya kuma rike gidan kasancewarsa mutum ne mai zafin nema da kuma fada yasa kowa ke shakkarsa a gidan. Da yawan wadanda Abbanmu ya samarwa aiki sun ci gaba da waiwayar rayuwarmu duk da cewa ba ma cikin rashin komi, ciki har da Uncle Mukhtar wanda Abbanmu ya sama mishi aiki a Jordan bayan ya gama degree dinshi akan engineering, ita kuma matar shi Jameelah ya samar mata gurbin karatu. Allah ya hada jini na da couple dinnan tun asali, shekarunsu uku da aure amma har lokacin Allah bai basu haihuwa ba. Lokaci zuwa lokaci idan mun samu hutu a school uncle Mukhtar ya kanzo da kanshi ya daukeni inje in musu hutu a Jordan, haka idan suka tashi zuwa Najeriya to akwatun tsarabata daban ne, na saba dasu sosai fiye ma da wasu en uwana da muke zaune dasu a cikin estate din saboda yadda suke tattalina.

Duka-duka watanni shida ne da rasuwar Abbanmu lokacin da Uncle Mukhtar ya diro Najeriya da burinsa na son a basu rikona. Ganin yadda muka shaku dasu sosai yasa bai samu matsala daga wajen su Ammie ba sai wajen Yaya Faruq daya kasance duk cikin yayyena ba wanda muka yi sabo dashi kuma yake ji dani kamar shi. Yayi tsalle ya dire kan cewa bai yarda in tafi in barsu ba, aka yi lallashin duniya amma ya ki yarda sai da Kawu Hamza ya mishi jan ido kafin ya amince ba don ranshi yaso ba. Cikin kwanaki uku kacal abubuwa suka kammala, muka daga kasar Jordan.

A Jordan na tarar da wata irin sabuwar rayuwa mai tsananin ni'ima da gardi, gata, tattali, da kulawa. Kasancewar ni kadai ce a gabansu yasa babu irin so da ban ga kalarsa ba a wajen wadannan bayin Allahn. Bana kewar gida ko kadan saboda kullum muna cikin waya dasu, kuma sukan ziyarce ni lokaci zuwa lokaci musamman Yaya Al-Mustapha idan harkokinsa suka kawo shi Jordan, haka kuma nima Uncle yana kaini hutu wajensu, a haka rayuwata take tafiya. Lokacin da na cika shekaru goma na kammala elementary school. Lokacin Uncle ya samu karin matsayi a wajen aikinsa an kuma canza masa wajen aikin zuwa Mumbai sai dai lokacin saura shekara daya kacal ta gama karantunta saboda haka shi ya tafi ya barmu a Jordan. Na jira Anti Jameelah ta gama karantunta yayin da nake zuwa makarantar hadda cikin dan lokacin, kafin kuwa shekara guda din ta zagayo tuni na sauke Al-Qur'ani mai girma har ma na fara nisa a haddar shi har Anti Jameelah ta kammala karantunta muka koma Mumbai da zama.

Tun tasowa na, kai tun ma ina yarinya Allah ya hore min baiwar iya zane, ko a makaranta a inda nafi maida hankali kenan, don haka Uncle ya sama min makaranta wanda su base teaching dinsu akan arts & painting ne, a can na kara samun experience sosai.

Wannan kenan....!!!





©Jeedderh🐾
[5/2, 10:41 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•14•°🐾


Ana cikin haka ne Anti ta samu ciki, farin cikin da muka yi ni da Uncle abin bai faduwa. Dadi na daya za a haifa min en kanne ina wasa dasu, in goya su, muje park tare. Idan ina gayawa Anti ko Uncle haka sai dai su yi ta dariya. Hidimar gida sai ta dawo hannu na, muddin ina gida to bana barin ta daukar ko tsinke, fannin girki ne kawai take dan kama min don zuwa lokacin ba iya shi nayi ba tunda dama can ni bana shiga kicin. A haka cikin ta yayi ta girma har ya shiga watan haihuwarshi, Anti ta haife twins dinta mace da namiji Uncle ya musu huduba da Salmah da Asleem. Duk da cewa muna nesa da gida amma dangi sun halarci taron suna sosai. Yayar Uncle Hajiya Karima taje tayi kwana daya ta koma, sai dai cikin Ikon Allah har ta tafi bamu hadu da ita ba, dalilin da yasa sam ban gane ta ba lokacin da naje Kano.

Wata kanwar mahaifin Anti Jameelah ce aka bari zata yiwa Antin wankan jego, zaman Iya Hari a rayuwarmu shi ya kawo tabarbarewar zaman lafiya da kwanciyar hankalin dake gidanmu. Tunda matar ta zo na kula cewa bata yi maraba dani ba sam, idan na gaishe ta bata amsawa sai dai harara ta biyo baya, don haka na fara yin baya-baya da ita.
Watarana da safe na shiga dakin Anti daure da tawul iyaka gwiwa ta, maclean din toilet dina ne ya kare don haka naje zanyi amfani da nata. A bakin kofar dakin muka ci karo da Inna Hari, na dan durkusa na gaishe ta, bata amsa ba sai bina da tayi da kallo har na kule uwar dakin Anti ta sameta a zaune bakin gado tana shayar da Asleem. Muka gaisa sama-sama na sanar da ita bani da maclean ne, nan ta kawo guda daya ta bani. Ina juyowa muka kara cin karo da Inna Hari ta shigo dakin, ta sake bina da wani irin kallo wanda ya fadar min da gaba sosai, har na baro dakin ina jin idanuwanta a jikina. Jiki a sanyaye na gama shirin makaranta na fito, dakin Anti na koma zan amshi kudin makaranta na da yake a wajen ta Uncle yake bari. A bakin kofar na jiyo muryar Inna Hari kamar cikin fada tana magana, ".....kada ki yarda Jameelah! Wannan yarinya da danyen jiki irin wannan kike bari tana yawo a tsakar gidanki har ki barta da mijinki a waje guda?! To wallahi ki kiyayi zamani da yaran zamani, idan baki tashi tsaye ba wallahi sai dai kiji gari ya waye ana buda ta zama kishiyar ki...!!".
Gabana ne yayi wani mummunan bugawa, kafafuna suka shiga rawa sosai, da kyar na samu na iya saisaita kaina nayi sallama na danna kaina dakin. Gani na a shirye tsaf cikin kayan makaranta, Anti ta bude jaka ta miko min kudi na amsa cikin rawar hannu. Ban iya furta ko uffan ba na juya na fita, Inna Hari ta sake bi na da wani kallon, zan iya cewa a tarihin rayuwata ban taba cin karo da irin wannan kallon ba sai yau. Sai dai dadin da naji shine ko da na dawo daga makaranta ban ga wani canji daga Anti ba, hakan sai ya sanyayar min da rai.

Kwanaki suka cigaba da tafiya, ni dai ban san ya aka yi ba, amma as time goes on sai naga sakin fuskar da Anti take yi mun ya ragu, haka ta daina yawan ja na a jiki da take yi. Bata cika son ina rabar jikin Uncle ba hakan ni kuma hakan ya riga ya zame min sabo... Kai ko waya taga ina yi dashi sai ta hau ni da fadan me yasa zan kira shi? Kai kafin dai Inna Hari ta koma Najeriya sai da ta wargaza mana zaman lafiyar gidan mu tas.

Kamar dai watarana bayan tafiyar Inna Hari, Uncle yayi wata tafiya ta sati biyu ya dawo. Dama na matsu da dawowar tashi saboda a matukar takure nake da sabon yanayin da Anti ta tsiro dashi. Ina jiyo sallamarshi na mike da hanzari na tare da jefa laptop din da nake game dashi akan kujera na saki ihu, na tafi da murnata na dale jikinshi ina mishi oyoyo. Nan ya daga ni sama yayi juyi dani a falon yana dariya kamar yadda ya saba, sam baya jin nauyin jikina haka zai daga ni sama yayi ta juyi dani kamar wata baby, ya dire ni kasa ya durkuso da kanshi saitin kumatu na da niyar bani peck a kunci ko goshi....
Wata irin gigitacciyar tsawa da aka ba shiri nayi baya a razane., Anti ce tsaye a kanmu tana huci kamar wata macijiya, banyi mamaki ba don kwanan nan irin wannan side din nata ne nake gani. Uncle kam baki ya saki cikin mamaki yana kallonta. Ta iso fusace ta janye ni daga wajen tayi wurgi dani gefe, Allah ya taimake ni na fada kan kujera. Uncle ya cika da mamakinta sosai, yace Jameelah meye kike yi ne haka? Aikuwa ta zabura ta hau masifa da jidali, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wai akan me zai kama ni ya rungume ya hada da jikinsa har da kokarin yi mun kiss, akan me? Ita dai ya kiyaye ta don ba zata laminta ba..... Ta wuce dakinta fuuuu a fusace kamar kububuwa tana maganganu da sam ban fahimci ko kalma daya daga cikin su ba. Ya bita da ido yana kallo cike da tsananin mamaki, can kuma ya dawo kaina ya fara lallashi na don kuwa kuka nake sosai saboda tsoron da Anti ta bani, sai da yaga na ware sosai sannan ya tashi ya bi bayan matarshi. Bai jima ba ya fito fuskarshi dauke da alamun damuwa, gani na zaune a falo yasa ya dan saki fuskar tashi. Yazo ya kama hannuna muka tafi dakina, a can ya tambaye ni ko naci abincin rana? Na girgiza kaina a sanyaye don ko karyawa ma banyi ba, wani guntun sauran cookies dana siya a makaranta ne na samu naci yau da safe. Ya girgiza kai cikin tausayi kafin ya tashi ya fita, can ya dawo da leda mai dauke da tambarin wani suya spot. Ya zauna a gefena ya bude ledar ya fiddo gashin kaza yayi jazur yana ta kamshi, da kanshi ya yanko min kazar ya miko min, hannu na rawa na amsa na fara ci hannu baka hannu kwarya, rabon da inci nama har na manta, kai ba nama kadai ba, sauran abubuwan makulashe ma, da har sai naci na ture amma yanzu babu su. Uncle kam bina yake da kallo cikin tausayi, sai dana kusa gama cinye kazar nan kuwa, Uncle yace kin koshi ne? Na gyada mishi kaina. Ya bude robar yoghurt ya tsiyaya ya mika min, na amsa. Sai daya tabbatar da na koshi sannan ya Kyale ni ya tafi dakinshi. Ganin yanayin gidan yau babu dadi yasa da yamma na shirya na tafi gidansu wata kawata da muke aji daya a makaranta a can bayan gidanmu, Hanan. A can na jima sosai muna hirarrakin duniya, sai bayan magriba ta raka ni na koma gida.

A hankali na fara fahimtar inda Anti ta dosa, sam bata kaunar ta ga na rabu da jikin Uncle har shi kanshi din ko kadan. Da na gane hakan sai nima na kame kaina na daina kusantar shi, mu'amalar mu dashi sai ta fara yin baya, idan ka ga hirarmu dashi sai dai a waya idan baya gari, shima sai dai in kule a uwar daki na.


Tafi-tafiya na fara wata irin rayuwa ta cikakken 'yanci, babu kwaba idan nayi ba dai-dai ba, babu tambayar ina zaki je idan zan fita, haka idan zan fita in kwana a waje Anti ba zata tambaye ni ina naje na kwana ba, babu tashi kiyi sallah ko wani abu makamancin haka, tsakani na da Anti sai dai kyara da tsangwama. Aikuwa sai na fara rama nan da nan saboda damuwar da nake sa wa raina, ban taba kwana in tashi da yunwa ba sai a wannan tsakanin, saboda na saba a kodayaushe sai dai in ga abinci a shirye kan table, wani lokacin ma sai an hada da lallashi kafin in ci abincin. Yanzun kuwa sai aka daina shirya abincin kan table sai dai a barshi a kicin, ni kuma lokacin ji na nake kamar wata bakuwa a gidan. Sai idan naga yunwa tana nema ta kashe ni ne zan tafi kicin in dauki abinci, to watarana ma sai dai in tarar ba a ajiye mun ba sai dai in dora tukunya in dafa.

Ana cikin haka aka tura Uncle kasar New Zealand zai yi wani course na watanni goma, saboda karatuna Uncle yace ba sai mun bishi ba, mu zauna a gida zai dinga zuwa mana weekend duk bayan sati biyu. Anti taji haushin haka sosai don har sai data kasa boyewa tayi magana wai saboda nine zai tafi ya barsu anan? Ya dai samu ya lallashe ta ya tafi yana mai kara jaddada amanata a hannunta don ya kula da rikon sakainar kashin da take yi mun. Ashe hakan ba karamin kara bata mata rai yayi ba, bayan tafiyar Uncle babu irin tsirfa da rashin mutuncin da ban gani ba daga gareta ba, dan abincin da nake dafawa ma kiri-kiri ta hana ni kunna gas wai kada in tada mata gobara a gida, dole dai na hakura na koma siyen abinci da kudina, watarana kuma in dauki abincin a haka inje gidan su Hanan in dafa.

Duk wannan bidirin da ake yi babu wanda yasan halin da nake ciki a gida, Allah ya halicce ni wata irin mutum mai dan banzan zurfin ciki, kafin kaji damuwata aiki ne babba. Ko da can da ina gida Ya Faruq ne kawai mai jin cikina, yanzun kuwa da bana kusa dashi idan mun yi waya ko ya tambaye ni akwai damuwa? Sai dai in girgiza kaina ince babu..... Babu wanda na sanarwa irin sabuwar rayuwar da na shiga.





©Jeedderh🐾
[5/2, 10:42 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•15•°🐾


Ana cikin haka aka tura Uncle kasar New Zealand zai yi wani course na watanni goma, saboda karatuna Uncle yace ba sai mun bishi ba, mu zauna a gida zai dinga zuwa mana weekend duk bayan sati biyu. Anti taji haushin haka sosai don har sai data kasa boyewa tayi magana wai saboda nine zai tafi ya barsu anan? Ya dai samu ya lallashe ta ya tafi yana mai kara jaddada amanata a hannunta don ya kula da rikon sakainar kashin da take yi mun. Ashe hakan ba karamin kara bata mata rai yayi ba, bayan tafiyar Uncle babu irin tsirfa da rashin mutuncin da ban gani ba daga gareta ba, dan abincin da nake dafawa ma kiri-kiri ta hana ni kunna gas wai kada in tada mata gobara a gida, dole dai na hakura na koma siyen abinci da kudina, watarana kuma in dauki abincin a haka inje gidan su Hanan in dafa.

Duk wannan bidirin da ake yi babu wanda yasan halin da nake ciki a gida, Allah ya halicce ni wata irin mutum mai dan banzan zurfin ciki, kafin kaji damuwata aiki ne babba. Ko da can da ina gida Ya Faruq ne kawai mai jin cikina, yanzun kuwa da bana kusa dashi idan mun yi waya ko ya tambaye ni akwai damuwa? Sai dai in girgiza kaina ince babu..... Babu wanda na sanarwa irin sabuwar rayuwar da na shiga.

Ranar wata Alhamis ina dakina da safe, kadaici duk ya dame ni. Zane nake yi a cikin art pad dina lokacin da kiran Hanan ya shigo waya ta. Hanan kawa tace sosai, makarantar mu daya da ita kuma ajin mu daya, kaf fadin makarantar mu ita kadai ce kawata. Haifaffiyar garin Rajashtan ce, aiki ne ya kawo babanta Hashim Mumbai.
Da zumudi na na daga wayar muka gaisa da ita, tace in shirya anjima da misalin karfe goma zata biyo ni muje babban Stadium, yau babban dan wasan kwaikwayo na kasar India superstar Marwanuddeen Muhammad Khan zai yi shooting part din wani film dinshi da zai fita wata mai zuwa. Nayi tsallen murna na dire cike da farin ciki, Marwan is my hero. Ina matukar kaunar acting din mutumin sosai don bana jin dadin shirin ko wane dan wasa irin yadda nake jin dadin fina-finan sa. Na tambayeta zancen ticket tace tuni ta siya mana, don haka muka yi sallama da ita akan zamu hadu a gidansu.

Lokacin da muka isa stadium din ya cika makil da mutane duk da cewa ba a fara shirin ba, muka nemi waje muka zauna muna hira muna hadawa da cin pop corn har aka fara daukar shirin. Wasan shine ending part a sabon film dinshi 'Real Footballer' da zai fita wanda shi Marwan din ya fito male leading star actor, usually ban cika son kallon ball ba, amma yau da naga yadda jarumin yake mulmula kwallon da kafarsa kamar wani Ronaldo sai naji ta bani matukar sha'awa kuma jarumin ya kara burge ni. Bayan an gama daukan shirin jarumin ya shiga gaisawa da masoyanshi, sannan ya sanar damu ranar da film din nashi zai shiga kasuwa. Sai da nayi yadda nayi na kutsa ta cikin mutane na dauki hoton mutumin nan sannan muka tafi, a hanyar mu ta komawa baki na yaki rufuwa saboda tsabar murnar da nake ciki. Hanan ta bani e-mail address dinshi, tace wannan personal address dinshi ne wanda yake dashi mainly for shakikanshi da manyan fans dinshi, itama a wajen PA dinshi ta amsa da yake abokin yayanta ne, saboda yadda ta ga ina son actor dinne yasa ta amsar min. Na kuwa yi mata godiya sosai. Aikuwa ina komawa gida na janyo wayana na tura mishi sakon ban gajiya da yadda nake dokin film dinshi ya shiga kasuwa, har zanen da na mishi lokacin da yake buga kwallo sai dana tura mishi. Nayi mamakin tsintar hoton a shafin sa na twitter washegari, bayan kwana biyu kuma na tsinci sakon godiya daga gareshi, yana cewa zanen ya burge shi sosai, kwarai rashin girman kanshi ya burge ni.

*☆☆☆☆☆☆*

Marwanuddeen Muhammad Khan wanda aka fi yiwa lakabi da superstar Marwan, shahararren dan wasan kasar India ne na Bollywood wanda tauraruwar sa ke matukar haskawa a wannan zamanin, yana da masoya bila adadin a kowane sassa na wannan duniyar. Darajarsa a Bollywood industry zata kai kimanin crores ashirin da dori, wanda canjin sa a kudin Najeriya zai kai kimanin miliyan dari bakwai da arba'in kenan.

Fahimtar shi da nayi a wani irin mutum mara girman kai yasa jifa-jifa musamman idan na kalli films dinshi. Wajen daya burge ni ina tura mishi comment, inda ya bani dariya kuwa zama nake yi in zana wajen inyi comment din tsokana in tura mishi, wajen daya bani haushi kuma ko bai burge ni ba kai tsaye nake fada mishi wajen bai yi kyau ba babu wani kwane-kwane.

A hankali wani irin sabo ya fara shiga tsakaninmu dashi, duk da cewa bamu taba jin muryar juna ba ko haduwa face to face, ya kance bai taba haduwa da mutum iri na ba, mutum straight forward wanda baya damuwa da halin da wani zai shiga muddin zai fadi gaskiyar sa ne, gani kuma ina da ban dariya. Idan ya fadi haka ni kuwa sai inji kaina ya fasu don murna. To ni kaina halin Marwan yana burge ni ba kadan ba, mutum ne mara girman kai wanda bai dauki rayuwar shi da nisa ba kamar yadda wasu celebrities din suka dauki tasu rayuwar ba. A takaice dai sai ya zamana babu abinda ke debe min kewa irin fina-finan Marwan dashi karan kansa Marwan din, kasancewar sa mutum mai yawan barkwanci.





©Jeedderh🐾
[5/2, 10:49 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




Please Login or Register in order to submit comment