Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiyi wanka, it's past eleven already. Sai lokacin hankalinta ya dawo jikinta, tayi saurin kallon gefenta, wayam! Babu Al-Ameen, ta kalli Anti zata yi magana ta tare ta ta hanyar cewa "Uncle ya kaishi makaranta tun dazu" sai ta dan saki murmushi kawai ta tashi ta fada toilet. Yanzu ma haka ta tarar da bath tub cike da ruwa, an zuba wasu irin furanni a ciki yana ta tashin kamshi mai sanyi. Ta dan ja wani siririn tsaki don tasan aikin Anti ne, rariya ta bude ruwan yabi ta ciki ya fita ta sake hada wani ruwan ta matso kumfa ta shiga ciki. Kwanciya tayi a cikin ruwan ta lumshe idanunta, bata san iya adadin lokutan data bata ba sai da taji Anti ta kwankwasa mata kofa sannan ta bude rariya ruwan ya fita, ta dauraye jikinta ta fita. Ko mai bata tsaya shafawa ba ta saka jallabiya ta fito falo. Anti ce kawai a falon, ta karbi hutun karshen shekara ne a wajen aikinta. Kai tsaye dinning ta wuce ta hau daga kuloli, tsaki kawai take yi don kuwa gashin kifi ne da yasha magungunan data tsana, da wani irin kunun alkama da yasha hadin data rasa ko na menene, haka nan dai ta zauna ta dan tsakura ta tashi ta koma dakinta. Gyale ta yafa ta saka wani flat sandal na roba ta fita, unguwan ta shiga zagayawa da kafa saboda damuwa da kadaici da suka dameta. Anti Rukky ta kira ta suka sha hirarsu amma bata yi mata zancen daya danganci aurensu ba, itama sai bata tada maganar ba. Sai data je makarantar su Al-Ameen ta dauko shi sannan ta koma gidan. Da dare duk suna falo tana koyawa su Asleem assignment, Al-Ameen na gefe ta tura mishi puzzle piece na haruffan larabci yana ta bugawa. Uncle da Anti suka fito daga dakin Uncle din, Anti Jameelah ta wuce kicin zata hada mishi dinner shi kuma ya zauna akan kujera yana kallon Ameenah fuskarshi dauke da murmushin tsokana, yace "Amarya... Amaryah....!!" nan da nan annurin fuskarta ya bace bat kamar daukewar ruwan sama. Ta wani cune dan bakinta gaba kamar gidan tsutsa tana kunkuni, Uncle ya fashe da dariya. Anti ta fito daga kicin da tray a hannunta ta zauna a gefen Uncle ta fara serving dinshi, jefi-jefi suna hirar bikin Ameenah. Haushi ya cikata yazo mata wuya, sai kawai ta tashi ta sungumi danta ba tare data kara kallon su Uncle din ba ta nufi dakinta. Uncle ya kira sunanta, "Ameenah!" yana kokarin danne dariyar data kamo shi. ta dakata ba tare data juya na, yace "ki fara shiri nan da kwana uku zamu tafi Nigeria saboda kwanaki shida suka rage daurin aurenku" ta juya tana kallonsu kamar zata yi magana, sai kuma ta fasa kawai ta gyada kai ta tura kofar dakinta da sauri ta fada, suka bi bayanta da kallo cike da alhini. Bayan kofar tabi ta sulale a hankali, tasa duka tafukan hannayenta a fuskarta ta fashe da wani irin matsanancin kuka zuciyarta na mata zogi, sai da tayi ya ishe ta kafin ta lallashi zuciyarta ta tashi daga bayan kofar. Ta shimfide Al-Ameen akan gado, ta zauna a tsakiyar gadon ta kura mishi ido tana kallonshi cikin tunanika daban-daban, iri-iri, kala-kala.....!!.




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•47•°🐾

Ana washegarin zasu tafi Nigeria, komi na tafiyarsu ya kammala. Duk wasu kaya na sakawa a gida tun daga kan furnitures, kitchen wares, kai hatta da cokali daga India aka saye shi, tuni Uncle ya auna su zuwa Kano. Anti kuma ta dage da kimtsa ta abinda ya danganci gyaran jiki ciki da waje, jiya ma a Dulhania Saloon suka yini, wata shahararriyar mai gyaran jiki Xehrah Mahendi ta yaryarawa Ameenah kunshi sannan ta mata gyaran jiki dana gashi. Ta fito sak a amarya kuwa. Yanzu ma tana zaune ne kawai tana karewa lallen hannunta kallo, ya zanu ya matukar yin kyau. Anti ta shigo dakin hannunta rike da silver bowl karama data dama tukudi a ciki yasha kwakwa da dabino, zuma har dasu cikwi. Ta mikawa Ameenah, maimakon ta amsa sai ta cuno baki, tace kina yiwa Allah Anti ki daina dura min kayan nan haka, baki san irin wahalar da nake sha ta dalilinsu bane. Anti tayi dariya tace ashe dai suna aiki, daidai kenan. Ke kin fi so ne kije masa salam ba taste kamar ruwa? Ina so ne in sa surikin nawa ya gigice, ya kasa tantance wai Budurwa ce ne ko kuwa Bazawara??!
Ameenah ta kara turo baki tana wani hura hanci, tunda taji cewa Abdul-Rasheed Modibbo ne angon ta sanya ranta a inuwa akan abinda take kulafucin kada wani ya dandana bayan Marwan. Tace Anti kina yin abu kamar baki san halin Modibbo ba? Anti tace sanin halin nasa ne yasa nake so na rikita shi da fatar jikin ki ma kawai kafin akai can ciki.... Ai ke dai Allah ya nuna mana ranar auren nan lafiya mu sha bidiri. Maza ki shanye tun kafin ya sha iska. Ta amsa tana yamutsa fuska kamar wadda ta amshi kashi, Anti tace eyh, koma me zaki yi dai sai kin shanye shi tass kin bani kwanon nan Ina tsaye a kanki!! Ita karfin halin Antin ma sai ya dawo bata dariya, dole ta murmusa ba don ta shiryawa hakan ba, Anti tace to ko ke fa, Amaryar mu??!.


*GOMBE....*
kwance yake akan irin wooden couches dinnan na hutu da aka tanada a gefen swimming pool din dake cikin Vomella Hotel dake cikin Gombe, Modibbo ne yake sana'ar tashi (tada hayaki). Da yammar nan ya iso Gombe bisa aikowar mahaifanshi, sun ce yazo su kara fahimtar juna shi da amaryar tashi su kuma tsara yadda bikin nasu zai kasance. Wannan wata babbar dama ce a gare shi ta wargaza zancen bikin cikin ruwan sanyi ba tare da sunan shi ya fita ba, don haka koda ya karaso Gombe bai tunkari gidan su amaryar ba ya nemi babban hotel ya kama. Ya bari sai gobe ido na ganin ido zai je ayi ta ta kare, ya huta da wannan makalallen auren, in yaso daga baya sai ya nemo mace wadda yake ganin ta dace dashi, karfaffa ba irin wannan er shalau din ba kamar igiya, wadda yake ganin duk ranar da tsautsayi yasa ya rutsa da ita ya dora mata nauyin kirjinshi, sai dai wata amma ba ita ba, don kuwa raga-raga zai yi da ita. Don haka Allah-Allah yake gari ya waye yaje su hadu, shi kadai yasan kudirin dake ranshi.

*****

Ta 6angarenta ma jiran zuwan shi kawai take yi, tana tunanin cewa tana da wata dama ta karshe da zata kashe zancen auren nan ya mutu murus, tana jin cewa zata iya zaman aure da kowa amma banda mai baudadden hali irin Modibbo!
Koda sakon zuwanshi yaje mata a washegarin ranar, bata ji ko dar ba ta zari gyalenta ta tafi har wani harbin iska take yi, zuciyarta na gaya mata wannan shine 'The End' na zancen aurenta. Tasan cewa Modibbo baya daukan raini ko kadan, kuma baya son wulakanci, to abinda tayi niyar yi mishi kenan, tasan cewa idan tayi haka to babu yadda zai ci gaba da auren nan tunda tasan cewa shima ba son auren yake yi ba. Anti ta bita da kallo cike da faduwar gaba, Ameenah must be up to something, tasan ruwa baya tsami banza. Farin cikin dake shimfide akan fuskarta abin tambaya ne, sai ta shiga addu'ar Allah yasa ba ruwa zata ballo musu ba don tasan halin su biyun kamar yunwar cikinta.

Yana cikin motar da yazo a cikinta Discussion Continues sanye da suits na wani cotton mai tsananin taushi maroon color, yasa bakin tie da bakin cover shoe, rigar ta sama ya ajiye akan kujerar mai zaman banza ya bar er ciki fara kawai, fuskar nan tasha wani makeken sun glass na Prada wanda ya mamaye rabin fuskar. Kafarsa daya na cikin motar daya na waje, idanunshi nakan kofar sashen su yana jiran fitowarta.
Can sai gata ta bullo tana takun nan nata mai daukar hankali, cike da natsuwa.....

Bai gasgata abinda idanuwansa ke hango masa ba har sai daya kai ga zare gilashin idonsa ya runtse ido na dan lokaci, ya sake budewa, but still, ita din dai yake gani tana tunkaro shi. Yarinyar nan fara... mai zubi da kira mai kyau... Aljanar shi... Wacce gani biyu ya taba mata a rayuwar shi amma ta cigaba da zuwar mishi cikin mafarkinshi!! Kar dai??... Ko dai....???! Ya shiga girgiza kansa cikin wani irin yanayi, sam ya gaza tantance halin da zuciyar sa ke ciki, farin ciki ko akasinsa??
Gare ta kam, tunda ta tunkaro shi taji gabanta na bugawa sosai, wani irin kwarjini ya mata marar misali. Sai dai ta kasa tantance ma'anar kallon da yake jifanta dashi wanda tafi kyautata zaton shine ya haifar mata da faduwar gaban. Har ta matso kusa dashi idanunshi na kanta cikin wani mayataccen kallo kamar wanda ke son gano wani abu a fuskarta, ba zato ba tsammani taga yaja murfin motar ya rufe garammm! Kamar tashin duniya, ya kuma warci motar a dari da tamanin ya bar gidan. Sai tayi turus tabi motar da kallo bakinta a bude, da salon rashin mutuncin da yazo dashi kenan? Ai kuwa daidai kai ka samu. Tana daga idonta ta hango Kawu Hamza a tsaye daga can kofar sashen shi, babu mamaki ya ga duk abinda ya faru a tsakanin su, bata nuna alamun ta ganshi ba ta hau matse hawayen karya zuciyarta fal farin ciki, tasan Kawu Hamza will not stand it.
Kawu Hamza kam iya shaka ya shaka sosai, wannan wane irin wulakanci ne surikin nasu yazo dashi? A fusace ya koma cikin gida ya lalubi waya ya dannawa Mukhtar kira, yace lallai-lallai ya nemo Modibbo duk inda yake a garin Gombe yana nemanshi, bai kara ko a ba ya kashe wayar ya bar Mukhtar cikin faduwar gaba da tambayar kanshi lafiya???




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•48•°🐾


Modibbo kuwa Allah ne kadai ya kaishi masaukin sa lafiya, ya shige dakinsa ya kulle da makulli ya hau kan gado ya kwanta ruf da ciki idanunsa a runtse gam. He still couldn't believe what he'd seen, did he really saw ha? Was it not illusion?? Kai ko dai mafarki yake yi ne? Nan ya tashi zaune ya fara mintsinin tattausar fatar hannunshi, da alamun dai da gaske ne hakan ya faru.
Yana cikin wannan halin kiran Uncle Mukhtar ya shiga wayarshi, a kasalance ya daga, ya tambaye shi yana ina? Sai ya rasa abinda zai ce, babu mamaki yayi witnessing rashin mutuncin daya zabgawa Ameenah ne yanzu, da kyar ya lalubo abin fada, yace "ina nan asibitin fata na Gombe, dama akwai wasu ayyuka da zanyi acan din to kuma yanzu har na shigo gida zan ga Ameenah sai aka min emergency kira, shine na tafi tun gabanin mu gaisa., yanzu haka ina shirin shiga tiyata ne ka kira ni!" Uncle yace to Allah ya kyauta, dama Kawu Hamza ne yace a kira ka yana nemanka, bari in sanar dashi. Suka kashe wayar a lokaci daya. Modibbo ya sake wata kakkarfar ajiyar zuciya fuskarshi dauke da murmushi, so it's her! Yarinyar data hargitsa mishi tunani ta mayar dashi wani gaula! Ashe bakar yarinyar nan ce, ita ce Ameenah. Farin ciki ya cika shi ya rasa me ma zaiyi? Ba zato ya kwala wani kakkarfan ihu, ya fara birgima akan gadon yana ihu kamar wani sintacce, daga karshe ya diro daga gadon dalilin kiran sallah da aka yi, ya shiga toilet ya dauro alwala ya fita zuwa Masjeed. A can ma bayan an gama sallah mikewa yayi ya fara jero nafilfili yana mai godewa Allah bisa wannan kyauta daya mishi, da ace ya 6ata auren nan tuntuni da hakika ya kasance cikin dana sani mara amfani for the rest of his life, and he wouldn't be able to forgive himself idan yayi hakan!!

Da misalin karfe biyar na yammacin ranar, tsaye yake a gaban dressing mirror. Wata shadda ce getzner ruwan makuba da aka mata dinkin Abacha a jikinshi, ta mishi kyau sosai yadda kasan bashi ba, ya dora karin hula ta zauna mishi das, turarukan daya fesawa jikinshi kuwa basu da adadi. Kanshi yake karewa kallo yana son ganin ta ina zai ga wata makusa? Amma bai gano komi ba, ya saki kayataccen murmushi tare da daukar makullin motar shi ya fita. A nutse yake tukin zuciyar shi na azalzalarshi da son sake ganin Ameenah. Tunanin ta sigar da zai je mata yake yi, matsayin masoyi? Ko kuwa wanda zai aureta kawai? Da wadannan tunanikan ya tura kai falon Kawu Hamza bakin shi dauke da sallama, Uncle Mukhtar ya biyo shi a baya.

Tana sashen Yaya Abdul-Hadi ana ta shirye-shiryen walimah da za ayi gobe da safe anan farfajiyar gidan. Tana zaune ne kawai, amma sam tunaninta baya tare dasu, ta cilla wata duniya ta daban. Imran dan gidan Ya Abdul-Hadi ya shigo inda suke da gudu yana kwala mata kira, ta dube shi tana dan murmushi tace ya aka yi ne Imu na?? Yace Kawu Hamza yana kiran ki. Gabanta kam ya fadi sosai, ta tambayi kanta me ya faru? Haka nan dai ta mike ta tafi cike da taraddadi.

A falon na Kawu durkushe take a gabanshi cikin dar-dar kamar ace mata at! ta fece da gudu, ta dan saci kallon Modibbo daya nutsu sosai a gaban Kawun kamar wani kamilin gaske, shima ita din yake kallo. Tayi saurin kau da kanta gefe bayan ta auna mishi harara. Kawu yayi gyaran murya ya dubesu yace "dalilin tara ku anan wajen ba wani dalili bane sai don na kara tambayarku game da ra'ayin juna musamman ke Ameenah, bana so daga baya wani abu yazo ya faru a kuma zo ana kuka gani. Don haka Ameenah menene ra'ayin ki game da wannan aure? Kina da matsala dashi ko kuwa??" ta ciza tattausan lebenta na kasa cike da wani irin murmushi, babu mamaki Allah ne ya dubi halin da zata shiga ya kawo mata wannan kyakkyawar damar. Babu jin ko dar game da hukuncin data yanke tace "zan amince Kawu, a bisa sharadi daya; idan har ya amince da zaman Al-Ameen tare dani, ba kuma zaman agolanci ba to babu damuwa daga bangare na, na amince!" Kawu ya maida kallonshi ga Modibbo da zufa ta yanko mishi, yace to kai kaji abinda Amaryar taka tace, shin ka amince??
Ya saci kallon inda take zaune, kanta na kasa amma yana hango wani kwantaccen murmushin mugunta a bisa fatar bakinta, nan ya kamo bakin zaren. Ya dage gira sama, wato abinda ta kulla kenan? Tana tunanin idan tayi hakan zai ki amincewa ne? Ai kuwa idan hakane u're wrong Ameenah! Ba wai da daya na, idan ma duka duniyar ne zaki tare da ita a gidana I will accept u, as a wife and they, my children.., ganinki kawai tare dani babban makami ne na kare kaina daga bacin rai.
Sai yayi murmushi ya kalli Kawu daya zuba mishi ido yana jiran amsar shi, yace Kawu na amince, na kuma yi alkawarin rike shi amana tamkar dan dana haifa a cikina!.
Fuskar Kawu ta washe da farinciki sosai, yace Masha Allah! To ke Ameenah kin dai ji abinda yace. Allah ya gani na fita hakkin ki, don haka aure babu fashi. Jibi war haka an daura In shaa Allah!! Ku tashi kuje na sallame ku, Allah ya muku albarka. Yadda kasan wadda aka bugewa kafafu haka Ameenah ta mike da kyar, jiki a sanyaye ta fita. Ya kara dukawa yawa Kawun sallama ya rufa mata baya da sauri. Kawai ganin mutum tayi ya tari gabanta, taja ta tsaya ta kama kugu tana kallon shi fuskar nan kamar wadda taga mala'ikan mutuwa. Tace malam lafiya? Ya daga kafada, ita ta kawo haka malama! Naga Kina shirin wucewa ne ba tare da kin tsaya mun tattauna yadda zamu tsara bikin mu ba. Ta kara tamke fuska tace "Malam ni babu wani biki da zanyi, idan kai kaga zaka iya sai kayi amma fa ba dani ba" yace "ahhhh! Sai Yanzu kika tuna min. Ashe fa matar tawa ZAWARA ce! Su kuma Zawarawa ba ayi musu biki irin na 'YAN MATA..... Well, ki godewa Allah ma zaki samu albarkacin 'yanmatan da za a hada ku tare dasu ayi shagalin biki mana, don haka dole zaki je duk bukukuwan da za a gudanar" tace dalili?? Zuciyarta cike da takaicin kalmar Zawara daya kira ta da ita. Yace "dalili? Saboda nima zan je, idan har zan je ya zamar miki tilas kema kije!" taja tsuka, "to ba zan je din ba, sai dai idan gawana za a cicciba akai wajen bikin". Ta bi ta gefenshi zata wuce, ya janyo hannunta da karfi ta dawo gabanshi suna fuskantar juna, ya maida fuskar shi ya dinke tsaf daga sassauta din da yayi. Yace watch your mouth Ameenah, don ina shirin zama mijinki ba wai yana nufin zan zauna ne ina fadar magana kina mayar min gatsar babu respect ba kin gane? Yasa hannu a aljihun shi ya ciro bundles na dubu ya kamo hannunta ya dora mata su, "ga wannan kiyi hidimar biki dasu ke da kawayen ki, ni yau zan koma Kano in shaa Allah gobe zan juyo tare da abokai na, Jibi a daura aure in dauki er Bazawarar Amarya ta mu tafi Kano....!" Haushi ya kawo ta wuya, anya yasan irin dafin dake tattare da kalmar nan tashi ta zawarci? Ba zata iya jura ba..., da gudu tabi ta gefenshi tayi part din Yaya Abdul-Hadi. Ya bita da kallo yana jin kamar ya bita ya kamota ya rungumeta ya lallashe ta don yasan ya bata mata rai sosai, sai dai idan yayi hakan ya bada kanshi da wuri, ya kula yarinyar sai an biyo da ita ta bayan gida kafin a daidaice da ita, ya kada kanshi ya fada mota ya mata key ya dauki hanyar Kano, to sauka lafiya!

Can kuryar dakin Anti Nadiya ta shige tana huci kamar wata tsohuwar zakanya. Anti Jameela ta biyo bayanta don ganin yadda ta shigo a gigice, ita kuma daidai lokacin tayi jifa da kudin, Anti ta cafe su ta waro ido a kansu tace "yauwa! Angon nan naki yasan yayi abu at d ryt time, kamar dama yasan tunanin inda zan lalubo kudin da za a sayo kulolin da zaa raba a wajen walimah nake don na hannunmu sun kare tun a cikin gida, kin ga sai a karo da wannan!" ta juya ta fita tana kwalawa Sadi kira. Ameenah ta bita da kallo cike da takaici, tana jin kamar taje ta kwace kudin ta yayyaga su gutsi-gutsi.

☆**☆**☆**☆




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:05 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•49•°🐾


Karfe takwas da rabi na daren ranar a cikin farfajiyar gidansu ta mishi, ya kashe motar ya fito cikin wani nutsattsen taku fuskar shi na dauke da kayataccen murmushi, jinshi yake kamar wanda aka yiwa albishir da gidan Aljannah. Yayi sallama a kofar falon tare da tura kofa ya shiga a lokaci guda, Ummie da Safeenah ne kawai a falon da alamun suna sirrantawa ne, baki en biki wadanda suka zo suna sashen baki har sun kwanta. Ya zauna akan kujera kusa da Ummie yana wasa da makullin motarshi, farin ciki da dokin dake fuskar shi sun kasa boyuwa. Cike da mamaki suke binsa da kallo, kamar kuma suna doubting anya Modibbo ne kuwa? Yanayine da basu taba ganin irinsa a tattare dashi ba, hatta da mahaifiyarshi kuwa a iya tsawon rayuwar ta. Safeenah tace Yaya wat happened? U look so happy, jubilated...me ya faru ne hmm?? Ya kara sakin wani tattausan murmushi triumphantly, feeling so high. Sai Biebie ta kara sake baki tana kallonshi cike da mamaki marar misaltuwa, bata taba ganin Yayan ya murmusa haka ba. Mutumin da sam ganin murmushi a fuskarsa na en sakanni ne amma ji yadda yake ta murmushi tunda ya shigo, kana iya hango tsabar Farin ciki da murna shimfide a kwayar idanunsa, gashi nan kuma zane baro-baro a fuskarsa. Ta tabbata koma meye ya faru ba karamin al'amari bane. Yace babu komi Safeenah Amarya, kawai ina cikin muuudu mai kyau ne kawai. Ummie tace ya aka yi ka dawo yanzu? Yace gobe in shaa Allah zan koma tare da abokaina. Tace to Allah ya kaimu ya amsa da ameen Ummie, bari in je in kwanta, m extremely tired wallahi, very tired!! Ummie tace gashi Mukhtar yace a tambayeka a inda za a kai kayan Ameenah, gobe zasu iso daga India. Yace a kaisu gidana na Lamido crescent, acan zamu zauna. Ummie ta gyada kai, "amma da kake cewa ba zaka zauna acan ba?" dariya kawai yayi ya tashi ya musu sai da safe, Safeenah tace Yaya Ango!! Cike da tsokana, tasan cewa harara ce zata biyo baya don kuwa baya son sunan ko kadan. Amma ga mamakinta sai ya watso mata fararen hakorannan nashi tas-tas dasu har wani reflecting suke, yace haka yake amaryar mu Safeenah...! Ya fita daga falon yana en wake-wake cikin nishadi. Suka bishi da kallo suna tattaunawa game da canjin da suka gani tare da Modibbo kamar bashi ba.
Yana shiga daki ruwa ya fara watsawa, bayan ya fito daga wanka ya zura kayan barci ya dauki waya ya samu gefen gado ya kwanta ya shiga kiran abokanshi yana fada musu daurin auren shi Jibi ne, duk sun sha mamaki suka yi ta mishi korafin kin sanar musu da wuri da yayi, hakuri kawai yake basu yana cewa daurin auren ne yazo kai tsaye shi yasa. Wasu sun ce a goben zasu bishi, wasu kuma suka ce sai ranar daurin auren zasu je, wasu kuma suka ce idan amarya tazo zasu je su gaisa. Dariya yayi yace ko basu zo ba ya gode da fatan alkhairin da suka mishi.....

Farfajiyar gidan ta Wakili's estate cike take da manyan canopies marassa adadi, babban guri ne da aka tanada musamman saboda shagulgula irin wannan. Amaren guda uku sun sha adon riga da siket na wani tattausan yadin silk sky-blue, Anti Jameelah ce tayo musu shi daga can India,

Please Login or Register in order to submit comment