Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



🐾°•16•°🐾


A gefe guda matsalar Anti ta fara yawa. Gabadaya yanzu na tashi daga er riko na dawo er aiki. Ni ce gyaran gida, girki wanda zanyi amma kwayar abincin wannan ba zata shiga ciki na ba, nice rainon twins duk da cewa suna da nanny dinsu. Rayuwa ta dai a gidan ta dawo abin tausayi, irin ta yara marassa galihu, gashi na kasa sanarwa da kowa halin da nake ciki har shi uncle din kuwa, idan yazo mana weekend yayi ta tambayana meke damuna saboda yadda nake ramewa ina karewa a tsaye, sai dai kawai ince mishi babu komi ko kuma ince karatu ne.

Cikin watanni hudu kacal da tafiyar Uncle sai gani warwas a gadon asibiti. Ulcer tayi min mugun kamu, sai da aka kai ga rage min hanji saboda ya fara lalacewa. Aikuwa Anti ta ga tashin hankali a wajen uncle, rufe idonshi yayi ya zazzaga mata rashin mutunci, ya kuma tabbatar mata muddin tana son ganin zaman lafiyar ta dashi to lallai ta canza wannan sabon halin nata.

Ganin haka sai ta zubar da wadancan makaman yakin ta dauki wasu, duk ayyukan da take saka ni sai ta daina haka bata hana ni dora abinci da kaina, amma sai ta daina bani kudin break wanda uncle yake bar min a wajenta idan zai yi tafiya, ni kuma bana son fadan da suke yi ta dalili na. Don haka na binciko ATM card dina, daga gida duk karshen wata Yaya Faruq yana turo min kudi yace in dinga hidima dasu, da bana bi ta kansu saboda bani da matsalar komi, amma yanzu dasu nake en kananun hidindimu. Idan suka kare sai in kira wani a cikin yayyena ya turo min. Duk da cewa su basu nuna wani abu idan na tambayesu, amma ni kullum na musu wayar sai in dinga ji na wani banbarakwai, ko kadan bana jin dadin hakan saboda roko ba dabi'ata bace, amma kiri-kiri sai da anti tasa na koya.


Ranar litinin na tashi da sassafe na shirya a gaggauce saboda ina da jarabawar Visual art a ranar. Jiya ban samu na runtsa ba ko kadan ina ta karatu a sakamakon ban samu damar yin tests din course din ba saboda rashin lafiyar da nayi, so nake in samu inyi kokari a exams dinshi yadda idan aka hada da assignments dina in samu ko maki 60 ne cikin dari, in dai samu in wuce aji na gaba.

Na samu Anti a daki tana zaune na gaishe ta, ta amsa fuska a hade. Cikin dari-dari na mata maganar cikon kudin school fees dina ba a gama biya ba, kuma uncle yace min zai turo mata da kudin sai dai banji tayi maganar ba har yanzu gashi kuma makaranta sun bani deadline, muddin ban biya kudin yau ba to ba zan yi jarabawa ba.
Kai tsaye tace tuni Uncle ya turo min da kudin tun satin daya wuce, sai dai tuni tayi sha'anin gabanta dasu don haka inje in san yadda zanyi tun wuri. Wata irin kwalla mai tsananin yaji da radadi naji ta ciko idanuna tana son silalo min, na ciji bakina ina kokarin hana hawayen su zubo min. Ban furta uffan ba don nasan idan nayi magana kuka ne zai kwace min, na juya na koma daki na. Atm card dina na fara nema nasan kila kudin ciki su ishe ni, sai dai sama ko kasa na rasa katin nan, na hargitsa daki na yayi kaca-kaca amma babu alamun ATM. Sai kawai na zube a tsakiyar daki na rushe da kuka cike da bakin ciki, ban taba dana sanin zuwa gidan Uncle ba irin ranar. Ina da iyaye da en uwa masu sona amma gani nazo inda bani da dangin iya bare na baba ana treating dina kamar wata mara galihu. Nan na kudurce a raina idan na gama wannan shekarar zan koma Najeriya abina na cigaba da karatu na a gaban Ammie na da Ya Faruq masu so na.
Da dai naga bani da mafita, dole na mike tsaye. Na duba agogo na ga bakwai da rabi, kawai nace bari inje makarantar ko Allah zai sa su kyale ni. Abin haushi da takaici naje bus stop na tarar bus din da nake hawa har ta tafi. Na fara trekking zuwa babban titi don nasan acan zan samu tunda kudin hannu na ba zasu kai inyi shatar taxi ba.

Ina tafe akan titi ina rangajin gajiya, ga yunwa, barci, gefen kaina sai sara min yake yi da karfi (migraine) ga ciki na dake cakudawa yana min ruri, haka na hau titin nan kwalam ina tafe ina sharar kwalla. Ban san cewa na hau tsakiyar titi ba sai da naji wani irin kuuuuu!! karar take burkin mota a baya na. Razanar da nayi ne yasa na tafi luuu na zube a gaban motar kafin daga bisani na silale kasa, na zube warwas bisa kwalta. Nayi nayi in tashi amma na kasa, wani irin zogi nake ji a hannuna mai gigita kwalwa. Ji nayi an bude murfin motar an fito, sautin Innalillahi....! Naji yana tashi cikin wata tattausar murya mai laushi cike da ginshira. Duf! Kamar daukewar ruwan sama haka naji na nemi ciwon nan na rasa, cike da tsananin mamaki na waro ido ina kara kallonshi cikin tantama, shine ko ba shine ba......?????????!




*Happy Birthday To U my dearest ANTI ZEE....*




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•17•°🐾


I couldn't really believe what I saw! Marwanuddeen ne tsaye a gabana, ya hade cikin jeans da T-shirt din formies, takalminshi baki sau ciki shima dai na formies din ne, sai jar hula pick up ruwan shirt dinshi wadda nake zaton saboda badda kama ya saka ta saboda shi kadai ne yake jan motar ba tare da security ba. Bai yi wata-wata ba ya kamani na tashi zaune, ya saka ni cikin motar yana jero min sannu har ya zagaya daya gefen yaja motar. Tuki yake a hankali kuma a nutse cikin kwarewa ba tare daya nuna tsarguwa ko damuwa da kallon kurilla da nake jifanshi dashi. Tafiya mai dan nisa muka yi yaja tunga a bakin wani karamin clinic. Ya fito daga motar bayan ya maka bakin gilashi a fuskarsa, zuwa lokacin kafata ta saki don haka da kafafuna na taka har cikin clinic din, aka min dressing a hannu don anan kawai naji ciwon. Likitan yaso in zauna in samu hutu ko da na awa daya ne amma fir naki amincewa nace mishi ina da jarawabawa yau n I can't lose it, sai ya bani magunguna. Muka tafi yana jaddada min lallai in samu wani abu inci saboda ulcer ta tana gab da tashi.
Cikin motar muka koma ya tashe ta muka bar asibitin, a motar nayi luf akan kujera cike da tunanika barkatai a raina har zuwa lokacin bayan sannu babu maganar data kara hada mu dashi. A bakin wani shago da aka rubuta Ice Land yayi parking ya fita ya shiga wajen, bai jima ba ya dawo hannunshi rike da leda mai dauke da tambarin wajen, ya shigo motar ya miko min ledar. Ba musu na amsa ina godiya, biscuit ne da meat pie da fresh milk. Yawuna ya tsinke sosai, tsohuwar yunwa ta ta taso, na mike kafa na fara turawa cikina meat pie da biscuit ba kakkautawa ina yi ina korawa da fresh milk din nan, sai dana musu tass, nayi gyatsa na godewa Allah. Sai lokacin da hankali na ya dawo jikina na lura da irin kallon da yake jifa na cike da mamakin yadda na cinye abubuwan, murmushi na danyi cikin jin kunyar shi na kauda kaina gefe.
Sai da muka hau kan babban titi ya dan kalle ni, cikin turanci ya tambaye ni a wace makaranta nake? Nima cikin turancin na mayar mishi da 'Empirical College of Arts'. Ya kada kan motar shi zuwa titin makarantar, har kofar gate din makarantar mu ya ajiye ni, na mishi godiya sosai na fita daga cikin motar.

Cikin faduwar gaba na dumfari gate bakina dauke da addu'ar Allah yasa Computer dake dauke da sunayen wadanda basu biya school fees ba a kashe take. Sai dai cikin rashin sa'a ina gama shigar da sunana cikin computer matsayin attendance taki shigar da sunan nawa, securities suka hana ni shiga. Har kasa na durkusa ina rokon su taimake ni su Barbi in shiga in zana jarabawa, jibi kawuna zai dawo daga tafiyar da yayi yazo ya biya min amma fir suka ki sai ma kora ta da suka shiga yi. Idanuna suka yi luhu-luhu cike da tashin hankali, idan na rasa jarabawar nan nasan nayi asarar wannan shekarar kenan dole sai na maimaita wata.

Ji nayi wasu tausasan hannuwa sun dafa ni, nayi hanzarin dagowa na kalli wanda ya dafa ni. Mamaki ya kama ni ganin ashe har yanzu bai tafi ba, ya tashe ni tsaye ya tambaye ni meke faruwa? Cikin harshen turanci. Na sadda kaina kasa ina cizon lebba na na kasa na kasa magana, ina jin nauyin fada masa, sai kuma naga cewa shine last hope dina a yanzu dai, idan na bari ta tafi zan cuci kaina ne kawai, zan rasa jarabawa na har abada! Ban san lokacin dana bude baki na fada mishi cikon kudin makarantana na wannan term din ne ban gama biya ba, gashi Uncle dina da zai biya min kudin baya nan yana Australia kuma na rasa contact dinshi ban san ya zanyi ba.... Na gama fada ina matse kwallar ido na. Ya matsa ga securities ya tambaye su nawa ne kudin? Suka latsa computer take ta nuno musu adadin kudin da ake bina, rupee dari biyu da hamsin kimanin Naira Dubu Saba'in da biyar. Ya zaro master card daga cikin wallet dinsa ya mika musu, suka zira shi cikin wata na'ura suka yi en danne-danne a jiki nan ya zari abinda zai zara ya fito da wata takarda tare da card din, suka mika mishi ya rike card din ya miko min takardar.
Na rasa irin godiyar da zanyi wa bawan Allahn nan, sai kawai na zube a kasa bisa gwiwoyina ina hawaye, shima ya fahimci na kasa yi mishi godiya ne. Sai yayi murmushi wanda yasa kuncinsa na dama ya lotsa sosai, naji wata irin faduwar gaba ta ziyarce ni saboda wani irin kyawu da naga ya kara yi a idanu na, ya dafa kaina yace kar ki damu, je ki kiyi jarabawar ki Allah ya baku sa'ah! Ya wuce ya shige motar shi yaja yayi gaba, sai dana hangen motar sannan na tashi na karkade jikina na shiga makaranta.
Kai tsaye library na wuce, a can na samu Hanan tana karatu. Nima na samu waje na zauna na fara kararun kafin lokacin shiga jarabawar yayi.
Gidansu Hanan muka wuce daga makaranta, nayi wanka nayi sallah naci abinci ta bani kayanta na saka. Muna falonsu ni ina kwance akan kujera take tambayana abinda ya same ni a hannu na, na bata labarin duk abinda ya faru sai dai ban fada mata Marwan ne ya biya kudin ba, ta tausaya min sosai. Tace waye wanda ya taimaka miki? Ban san lokacin da wani murmushi ya subuce min ba, na lumshe idanuna, a hankali kamanninsa da duk wasu wasu moves nashi ayau suka shiga dawo min a cikin idanuna, na bude idanuna fess cikin na Hanan na sakar mata wani kayataccen murmushin, cikin wata irin soft murya mai cike da wasu irin feelings nace mata "Wani neh.....!!!!"




©Jeedderh🐾


[5/2, 10:50 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•18•°🐾


Ban koma gida ba sai da Magriba, nannyn su Asleem kawai na tarar a gidan, Chandni sunanta tana zuwa da safe tayi rainon su Asleem da hidimomin su zuwa dare sai ta tafi. Na dauki yaran na dan musu wasa sannan na wuce daki na.

Sai dana kammala komi nayi shirin kwanciya barci sannan na haye gado na. Na janyo waya ta na bude e-mail dina na turawa Marwan sakon jinjina da godiyar irin taimakon da yayi min yau. Ba a dauki wani dogon lokaci ba sai ga amsar shi yana tambaya na cike da mamaki, wai ashe nice yarinyar dazu? Yace no wonder! Ashe dalilin da yasa ya dinga ji a jikinsa kamar ya sanni kenan? Haka kawai yaji ina bashi dariya musamman idan ya tuno da yadda na dinga cin abinci hannu baka hannu kwarya dazun. Na dinga dariya kuwa ni kadai a daki. A wannan ranar na kara mishi wani matsayi a zuciyata. Muna hira dashi barci ya dauke ni cike da wani irin nishadi da rabon inji kamarsa har na manta.
Washegari ina tashi da safe na fada toilet nayi wanka, ina cikin shafa na janyo wayata na bude. Kai tsaye sashen sada zumuntar Marwan na face book na shiga, wani post daya yi a jiya da dare misalin karfe sha daya na daren ne ya dauki hankali na., cikin yaren Hindi yayi posting din 'Today for the very first time in my life, I met an amazing woman. Usually I don't like seeing females eating roughly in front of me, but wen I saw ha eating like that, I wanted to just........! 😘😎' bai karasa ba ya dora alamun emoticons. Aikuwa comments sun fi dubu ashirin kowa na tambayar shi wace ce yarinyar nan?? Naji ni wani sakayau, feeling very empty kamar bani ba, kar dai dani yake?? Naso in tambaye shi nima inji ko dani din yake, sai dai tsoron kada yace ba dani yake ba yasa na basar da zancen duk da cewa abin yana cikin raina.


✿✿ *♡LOVE♡*✿✿
Mun samu hutu na tsayin sati biyar, duk da cewa wannan karon position dina na 8 ne sabanin na hudu ko na uku, amma nayi murna da na wuce zuwa aji na gaba. Da kyar na samu na shawo kan Uncle ya yarda ya barni inje Najeriya inyi musu hutun sati biyu, nan na hau shirin komawata gida Najeriya ba tare da na sanarwa da kowa kudiri na ba saboda gudun kada a sagar min da gwiwa.

Ranar asabar lokacin saura kwana biyar in tafi gida, uncle yazo mana weekend. Ya kwashe mu duka gidan muka je wani babban amusement park har da Hanan. Mun zagaya wajen sosai mun sha wasanninmu da daukar hotuna, muka yi sayen kayan makulashe masu yawa. Mun jima sosai a wajen kafin muka yi haramar komawa gida. A bakin gate aka tsayar damu ana checking bayan booth din masu shiga da fita don tabbatar da tsaro, ana cikin duba na gabanmu kafin azo kanmu, na juya ina kallon motocin dake kokarin shigowa. Daidai ana sauke bakaken gilasan bayan wata hadaddiyar bakar matrix, nayi ido hudu da kyakkyawan matashi Marwan. Wani tattausan murmushi ne shimfide akan kyawawan kumatunsa, bakin shi ya motsa da kalmar, "aap kaise hain??" (how are u doing?), nima murmushin na saki sosai cike da farin cikin ganinsa, ban san me ya kawo sa wajen ba amma nafi kyautata zaton ko harkar fina-finan shi ce ta kawo shi. Na motsa lebbana nima a hankali na mayar masa da amsa, "mein theek ho! Aur aap??" (am fine.... And you??) ya sake murmusawa yace mein too! (me too!). Ya min alamun bye, direban dake tuka shi yaja mota suka tafi har lokacin da murmushi a saman fuskar shi.
Na bi motar da kallo nima ina murmushi cikin wani yanayi har suka bace min. Uncle ya ja mota muka fita muma. A hankali na saukar da ajiyar zuciya tare da kwantar da kaina akan kujera ina tunano Marwan, ban san me yasa ba, a barci nake ne ko a farke, aiki nake ko karatu, a kwance nake ko a zaune, tunanin mutumin nan shi kadai ransa yana like dani kamar wani magnet. Ya mamaye kaso mai girma a duniyar tunanina, ko ina na juya shi kadai ke min yawo a fuska na wanda ni a karan kaina bansan dalilin da yasa hakan ke faruwa dani ba!.



[Mamielow., na ga sakon ki akan littafin Bayan Rai. Nima nagode sosai da irin yabon ki da kuma shawarwarinki,nima kuma Ina kaunar ki dama Masoyan littafin Bayan Rai baki daya......!]




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:51 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•19•°🐾


Ranar Alhamis jirgi ya daga dani, mun jima da Uncle akan waya a filin jirgin kafin mu tashi kamar ba zamu rabu ba, yace min shima next week zai dawo gida gabadaya, ni kam ina tunanin hirar karshe ce muke yi dashi a garin India don na gamawa kudurcewa a raina cewa na bar gidan Uncle har abada.
A Najeriya na tadda cincirindon en uwana sun zo tarba na a filin jirgi, na rasa ina zan sa kaina? Yau gani a gaban Ammie na da Ya Faruq da en uwana masu so na. Nan dai muka rankaya gida, a can ma wata tarbar na tarar ta abinci iri-iri. Musamman Ammie ta shiga kicin da kanta ta shirya min kaloli na nau'in abincin da nake so. Daren ranar bamu runtsa ba, muna dakin Ammie muna shan hira har dare ya tsala, sauran yayyena suka tafi suka barmu da Ya Faruq da Ammien. Muna jan ta da hira muna ta kwasar dariya, akwai fahimtar juna tsakanin mu da mahaifiyarmu, tana jan mu a jikinta sosai shi yasa bama jin nauyin bayyana mata duk damuwar mu. Sometimes idan ka ga yadda muke hira da ita muna tsokanarta sai kayi tsammanin cewa kakarmu ce. Shima Ya Faruq daya gaji da hirar nan ya barni ya mana sallama ya tafi dakinshi. Ni kam ranar a gefen Ammie na na kwana.

Sati na biyu cif a Gombe, nayi kiba abi na nayi fresh dani saboda bana tare da wata damuwa. Uncle ya bugo waya in koma, na kuwa ce babu inda zan koma ni na dawo gida, aka kuma yi yin duniya naki fadar abinda su Uncle din suka min, kawai dai nace ni yanzu nafi son zama cikin en uwana ne. Ammie tace bani da hujja kenan, Ina kuka riris haka suka raka ni filin jirgi muka rabu cike da kewar juna.

Kai tsaye Abuja jirgin ya wuce damu, ya ajiye fasinjoji ya dauki wasu, ni dai ina zaune cikin tafasar zuciya cike da takaicin komawa ta gidan Uncle, na baro inda ake so na ana nan-nan dani zan komawa lonely and scattered life dana fara mantawa da ita. Na dauki jaridar Vanguard ina dubawa kafin jirgi ya gama lodi a tashi, ni kam ji nake dama ace jirgin ba zai tashi na, da nafi kowa murna da farinciki.

Mutane suka gama shigowa jirgi ya fara haramar tashi, cikin siririyar murya naji anyi sallama a gefena an zauna a kujerar kusa dani, na amsa ina waiwayo wa. Kamar hadin baki shima ya waigo, sai kuwa muka hada ido. Cikin mamaki na zaro idanuna ina kara kallonshi, shima ya zare sun glass din idanunshi cike da mamaki. Mamakina daya me ya kawo Marwan Nigeria? Ko dai yana da alaka da nan ne? A lokaci guda muka furta "how comes??" ni dashi, muka saurara muna sauraron jin amsa daga bakin dayan mu, muka kara cewa "what brought you here??" a lokaci daya again. Kawai sai muka kyalkyale da dariya, muka yi tayi har dan tari ya sarke ni, ya fara dan bubbuga min bayana a hankali har na samu na nutsu. Ya dube ni a tausashe yace "go ahead and ask me..." na gyara zamana na kalle shi nace "me ya kawo ka Najeriya? Kana da alaka da nan ne ko kuma kazo yin wani abu ne?" yayi wata tattausar dariya da tasa gefen kumatunshi na dama da cleft dinshi suka lotsa, yace "mahaifina haifaffen garin Kano ne, iyaye, kakanni, yayye, da kannenshi duk suna nan Kano" na gyada kaina cikin mamaki, "ban taba sanin hakan ba, asali ma ni ban taba tsammanin hakan ba don ko kama baka yi mun da dan 9ja" ya sake wani murmushin, "ba lallai kowa ya tsammani hakan ba don a India na taso nayi karatu da komai nawa, sai dana girma ne sosai na fara zuwa wajen dangin mahaifina..... Amma ke dama kina da dangi ne a 9ja ko wani abu kika zo yi ??". Nace ni anan aka haife ni, kawai dai ina zaune ne wajen Uncle dina dake aiki a can Mumbai din. Ya gyada kai, "Kema ai ba kya kama da en Nigeria, wallahi kin fi mun kama da irin larabawan nan half cast na Libya da Moscow!" na kama baki ina jijjiga kai cikin dariya nace ni din?? Yace da gaske pa!! Na jingina da kujera ina kallonshi ina cigaba da dariya.....

Muka cigaba da hirarmu a nutse, musamman daya fara kwabo min hausarshi kamar ta en koyo wai shi a dole ya iya hausa, ni kam me zanyi ba dariya ba? Nan nayi ta kyakyatawa kamar bani da wata damuwa a raina. Har jirgi yayi landing a Mrs. Jick airport dake birnin Mumbai din, muka fito muna cigaba da hirarmu. Da Uncle na fara tozali, sai Anti dauke da Asleem Hanan kuma na rike da Tasleem. Tuni na manta da wanda ke gefe na wanda shima escort dinshi da dangi suka lullube shi amma hankalinshi na kaina. Da er sassarfa ta na karasa wajen su Anti, madadin in rungume Uncle kamar ko yaushe, sai na kai gwiwoyina har kasa na gaida shi ya dafa kaina yana murmushi ya amsa, na juya ga Anti na gaishe ta, ba laifi ta amsa da dan alamun afuwa a fuskarta. Nan na rungume Hanan, na amshi en biyu ina ta murnar ganinsu, daga nan muka fada mota Uncle yaja mu sai gida.

Ban tashi tunawa da Marwan ba sai da ina duba mails dina naga sakon shi, cikin hausar da bai kware ba wai "kun keuta! She ne kika tafi ba sai anjime ko?? 😠?" nan kuwa na kwashe da dariya sosai kafin na mayar mishi da amsar ban hakuri. A hankali a hankali rayuwa tana tafiya, wani matsananciyar shakuwa ta ginu tsakani na da Marwan, ta kai matakin da idan daya bai ji muryar daya ba a wuni to babu kwanciyar hankali. Yanayin zaman mu da Anti ya dan sauya, yanzun muna zama mu ci abinci tare, ina gaishe ta ta amsa faram-faram, ni dai nafi kyautata zaton ko don taga Uncle ya dawo gida ne yasa ta canza hali. A haka muka zana jarabawar fita daga makaranta

Please Login or Register in order to submit comment