Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bana manta wata ranar talata na dawo daga makaranta da yammaci likis a matukar gajiye don ranar sai karfe biyar na gama lectures kuma kafin in dawo yamma ta riga tayi gashi ni nake da girki ranar. A gurguje na shiga kicin na dora sassaukan girki, Allah ya taimake ni yau Hindu bata 6ata gidan ba. Farar taliya na dafa don ina da miya, nayi warming din wayar na saka kifin gwangwani a ciki, tana dahuwa na hada komi na kai kan dinning na ajiye. Na koma kicin na dauko lemuka da ruwa, a bakin kofa muka ci karo da ita, tana kokarin fitowa ni kuma zan fita, muka hada goshi da goshi ni da ita ji kake garammm! Muka ja baya a guje muna sosa wajen out of pain, ban gama warwarewa daga wannan ciwon ba naga wasu taurari masu haske suna gilmawa ta idona kafin duhu ya mamaye su sakamakon wani bahagon mari data kifa min a kunci na. Na dago a gigice na kalleta, ta nuno ni da yatsa cikin balbalin masifa, "ke dabbar ina ce da zaki kawo min karo kamar wata tunkiya? Banza, munafuka mai shiga tsakanin mata da miji.... Wallahi idan baki fita a harkata data mijina ba ina gab da nakasta ki anan gidan...! Ke wallahi zan iya na kashe ki har lahira ko na samu na huta daga bakin cikin da kike kunsa min...!!!".
Abin yayi yawa! Bayan rashin mutunci yau kuma har da mari?? I can't take it anymore! Banyi wata-wata ba na mayar mata da nartanin marin ta, nace "mind ur tongue Hindu ki kuma san wadda kike kira banza don kema baki da banbanci da banzayen...!!" tunkuda ni gefe tayi ta fita daga kicin din, nayi taga-taga sulbin tiles ya kwashe ni ya maka da kasa na fadi akan hannuna na dama. Na saki wata karar wahala sakamakon wata azaba data ratsa ni har tsakiyar kwalwa na, na kasa koda motsa yatsar hannu na ne. Hindu bata juyo ta kalleni ba ta wuce daki abinda. Nayi-nayi in tashi amma na kasa, hannun ma jin shi nake kamar ba a jikina yake ba. Wasu hawayen radadi da azaba suka shiga zarya akan kumatu na. Na kwashi tsawon mintuna biyar a haka, sai ga Marwan ya fado falon kamar wanda aka jefo. Nayi ajiyar zuciya ta ganin mala'ikan taimako. Cikin dakusasshiyar murya data data rine da kukan azaba na kwala mishi kira daga cikin kicin, "Marwannn...!!" ya shigo da saurinsa yana kiran sunana, gani na da yayi a kwance ya karaso wajena da sauri ya fara kokarin tada ni zaune, nan yaga yadda hannuna ya kumbura sosai, a rikice ya kwantar dani a jikinsa ya shafo saman wajen, "Meenah! Wat's wrong with you? Hu did diz to u??" na kara narkewa a jikinshi ina wani irin kuka na asalin shagwababbun yara, nan kuwa na kara gigitashi.
Ciccibana yayi cimak ya kaini cikin mota yaja muka tafi asibiti. Ashe tsagewar kashi ce, nan suka min allurar kashe zafi suka gyara min wajen amma duk da haka sai da naji zafi ba kadan ba. Yana gefena ana gyaran na nutsa kaina a jikinsa ina kuka, har muka dawo gida kuka nake shi kuma yana ta aikin lallashi na. A hanya muka tsaya ya jidar min kayan makulashe da gasasshen nama kafin muka karisa gida.

Ina rungume a barinsa na dama ya riko kayan da muka siya da daya hannunsa muka shiga falon, tana zaune a falon tana kallo, kallo daya ta mana ta dauke kai taja wani mummunan tsaki, muna wucewa ta gefenta naji tace wahalallen banza kawai, mijin tace!! Wuce ta muka yi ba tare da mun tanka ta ba, idan da sabo ai ya ci ace mun saba da irin wadannan kananun maganganun.
Komi dana saba yi a ranar shi ya min, ya min wanka ya shirya ni tsaf, ya kuma ciyar dani kazar da muka siyo da fresh milk wadda nima yanzu ta zamo daya daga cikin al'adun rayuwata. Ya kalmashe ni cikin jikinsa muka sha barcinmu mai cike da natsuwa. Washegari ko daya tambayeni ce masa nayi zanewa kawai nayi shine na fadi, kallona yayi kawai yayi murmushi kafin yace to Allah ya sauwake, ba wai don ya yarda da abinda nace ba, saboda yana smelling something fishy, ranshi yana gaya mishi kamar Hindu tana da alhaki game da ciwo na don yasan halinta sarai.

Tsawon sati biyu yana jinyata har na warke garas, ko su Anti da suka zo duba ni ban fada musu gaskiyar abinda ya faru dani ba, bayan duk zaman jinyar nan dana yi Hindu koda wasa bata taba yi mun sannu ba.
Ana cikin haka kwatsam bayan kamar kwana biyar yace mata ta hada kayanta yau zata yi parking zuwa gidan daya samar mata, gaskiya nayi farinciki sosai don a hakikanin gaskiya na tsorata da lamarin Hindu kwarai da gaske. Gareta kam kamar bata ji dadin hakan ba, saboda har ta gama kintsawa muka tafi raka ta tana ta kumbure-kumbure. Gidanta hawa daya ne wanda aka yi shi da zallar duwatsun siminti. Ire-iren gininnikan da nake ganin kamfanin Duala-Herab na tsarawa da ginawa ne. Maganar gaskiya gidan nata ya burge ni sosai. Na kama mata muka yi en gyare-gyare duk da gidan ba wata kura yayi ba, sai wajen karfe goman dare na musu sallama na taho, Marwan ya dawo dani gida ya koma can da yake ranar girkinta ne. Ranar kam hadadden barci nayi mai suna barci, na rabu da masifar Hindu!!




©Jeedderh🐾
[5/2, 10:58 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•29•°🐾


Bayan watanni biyu muka samu hutu sati biyu na karshen zangon karatu na farko, a cikin dan tsukin kuma kamfanin Marwan ya mike har sun zuba ma'aikata an fara kera jewelries da takalma har da jakunkuna, kaninsa Muhammad Kabeer da yake shekararsa na karshe a jami'ar Cambridge shi zai dinga kula musu da kamfanin idan ya dawo amma ya samu wanda zai kula da kamfanin for the time being kafin Kabeer din ya dawo saboda shi ayyukanshi ba zasu bari ba.
Ranar wata assabar ina kicin ina girkin rana ya shigo gidan a gaggauce ya same ni, yace in hada mishi kayanshi yanzu karfe hudu zai bi jirgi zai je New Delhi amma ranar litinin zai dawo. Nace me zaka yi acan? Yace gobe ne Holi Festival, akwai film da nake kan yi kuma festival din is part of d film. Nace menene kuma Holi Festival? Yana balle maballan rigarsa yace Holi festival bikine da mutanen kasar India, Asia da makotansu ke gudanarwa a duk ranar karshen watan Phalgun (February) ko ranar farkon watan Purnima (March). It's a Spring Festival also known as the festival of love or colors. A bikin zaki ga ana wasa da kaloli iri daban-daban ana raye-raye da kide-kide, wannan shine Holi Festival. Nace Woahh! Wallahi ina matukar son in ga hakan a zahiri, don Allah in biyo ka? Yace naaa.., ai na fada miki ba jimawa zan yi ba, kiyi zamanki a gida kinji?? Daga haka ya fada toilet. Yana fitowa na tare shi da magiya kamar zanyi kuka har dai ya amince, nayi tsallen murna na dale jikinshi ina murna. Na janyo akwati na shirya mana duk abinda nasan zamu bukata acan. Karfe shida da rabi jirginmu ya sauka a New Delhi, tuni ya mana booking din daki a Nas-Vegas hotel don haka muna isa mota tazo daga hotel din ta kwashe mu zuwa cikin hotel din. Wanka muka yi yaja mu jam'in sallar magriba da isha'i, muka ci abinci daga nan ya fita wajen director din film dinsa zasu kara tattaunawa game da shirin. Sai da nayi barci ya dawo dakin, kayan barci kawai ya saka ya hau gadon ya rungumo ni tsam har barci ya dauke shi shima.

Washegari wajen karfe goma na safe muka fita zuwa wajen Shooting din, na shirya cikin riga da wando en Pakistan wandon ruwan gwaiduwar kwai rigar kuma peach sai gyalen su multiple color na peach da yellow, yayinda na rataya peach din jaka nasa yellow din takalmi. A kasar hotel din muka tsaya na sayi er karamar camera sannan muka tafi.

A wata babbar majami'a suka yi shooting din, ina zaune daga gefe rike da camera ta ina ta daukar motsin Marwan. Suna gamawa yaja ni muka shiga wurare iri-iri har da kananun kauyuka da suke near Delhi, duk mun shiga mun ga yanayin yadda suke gudanar da nasu bikin. Bamu koma masaukinmu ba sai yamma likis, acan bakin hotel dinma mutane muka samu babu masaka tsinke ana ta kide-kide ana watsi da kaloli, kafin ma mu karasa bakin hotel din jikinmu ya baci da colors. Na tsaya ina daukar hotuna, ban ankara ba naji nayi karo da mutum, kafin in dago in bashi hakuri Marwan ya matso ya janyo hannuna muka kutsa ta cikin mutane muka shige hotel din ba tare dana kula da camera ta data fadi ba. Sai da muka isa daki har mun gama shirin kwanciya na tuna da camera ta, na Benet neman duniya amma tace daukeni inda kika ajiyeni. Ai kuwa ranar Marwan ya ga daru, tasa shi nayi a gaba ina kuka kamar karamar yarinya. A cewata shine yasa na rasa ta. Ranar banyi barcin kirki ba ina ta mita, shima kuwa haka na hana shi yayi barcin, motsi kadan sai ince mishi sai ya biya ni hotunan camera ta. Tun dai yana lallashi na har dai ya gaji ya koma gefe yana dariyar mita ta, daga baya ya janyo ni jikinsa ya rungume kam-kam yana shafa bayana a hankali, a haka ya samo kaina nayi shiru har barci ya daukeni.
Washegari da kyar ya lallasheni na yarda na shirya muka fita zagaya gari, amma sai da muka tsaya a shagon dana sayi camera muka kara siyan wata sannan muka tafi. Mun zagaya New Delhi sosai, mune malls, parks, gidajen tarihi, mun dai sha yawo don a gajiye tulis muka koma masaukinmu. Washegari litinin da safe muka juya Mumbai gida.


*♡BAYAN SHEKARU BIYU...!!!♡*





©Jeedderh🐾
[5/2, 10:59 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•30•°🐾


*♡BAYAN SHEKARU BIYU...!!♡*


Zaune akan three-seater dake girke a tsakiyar falon, ni kuma ina kwance akan akan kujerar nayi matashin kai da cinyarsa yana shafar gashin kaina a hankali. Sanye muke da couples attire wando 3-quarter da er shirt iri daya banbanci kawai nashi na maza ne nawa kuma na mata. Lallashina yake akan in daure in dan ci ko da tuffa ne daga cikin jerin fruits din daya zube min cikin wani dan kwando, ya bani magani in sha ni kuma naki. Muna cikin haka muka jiyo knocking din kofa, ba tare daya motsa daga zaunen da yake ba ya bada izinin shigowa. Hindu tare da wata mata da zata yi sa'arta suka danno kai cikin falon babu ko sallama, ta danyi turus da ganin yanayinmu kafin ta dake ta karaso tsakiyar falon suka nemi kujera suka zauna. Na yunkura zan tashi zaune jiri ya kwashe ni ya mayar kan cinyar Marwan, dole na kara kwantar da kaina a jikinshi. Na dube su na gaishe su cikin er fara'ata cikin fargabar abinda ya kawo ta gidana, zamanmu da ita har yau babu abinda ya ragu sai ma karuwa da yayi, suka amsa a yatsine suna kara kare min kallo, kamar wadda aka tursasa haka ta bude baki da kyar tace ya jiki? Na amsa mata da jiki Alhamdulillah! Daga haka tayi shiru tana kallonmu kasa-kasa tana turo cikinta dan kimanin watanni shida da en kwanaki. Marwan ya mata murmushi yace Maman baby, ya darling dina? Da fatan dai bata takura miki koh? Ta tabe baki tana girgiza kai a yatsine ba tare da tayi magana ba. Wani irin kallon tuhuma take min tunda suka shigo falon, ina ga ta kasa hadiyewa ne har sai data amayar da abinda ke cikin ranta, "naga kin dashe da yawa, ko dai cikine dake??" na sunkuyar da kaina kasa ina dan murmushi, shi kuma ya kalloni yana dan murmushi shima amma ba wanda ya bata amsa. Ganin haka yasa ta fahimci cewa hasashenta ya zama gaskiya kenan. Wani irin mahaukacin kishi ya turnuke mata zuciya, babu shiri ta mike tsaye kawarta ta rufa mata baya suka mana sallama, na samu na mike zaune da kyar na jingina da kujera saboda jiri, nace tun yanzu? Ko ruwa pa baku sha ba! Ban samu albarkacin ko kallo daga garesu ba suka sa kai suka wuce Marwan ya musu rakiya har inda suka ajiye motarsu, sai daya ga fitarsu daga gidan sannan ya dawo ciki.

Suna hawa kan titi Hindu ta gangara gefen titi tayi parking tana numfashi cikin bacin rai da fusata kafin ta fashe da kuka bakin ciki, abokiyar ta wadda take makociyarta ce matar wani dan wasan kwaikwayon India shima ta shiga bata baki tana kara kitsa mata mugun abu.... "Ki daina kuka Hindu nasan abinda kike gudu, kuma na goyi bayanki dari bisa dari. Ba zai yiyu ki jera haihuwar 'ya'ya da ita ba wallahi, har abada hakan ba zai faru matukar ina raye! Ki kwantar da hankalinki kawata ni nasan abinda zamu yi, wallahi wannan cikin karya yake yazo duniya... Da wanne zaki ji? Da shariyar miji baya sonki ko kuwa da tulin 'ya'yan kishiya??" Hindu ta tsagaita da kukan da take yi tace me zamu yi yanzu er uwa? Ki taimakeni don Allah! Tayi dariya tace kada ki damu, nice pa! Ki bari muje gida zan fada miki. Hindu tayi murmushi tace I believe you kawata, nasan matsalata zata warware yanzu, suka yi dariya ta ja motar suka wuce.

Cikin kwanaki biyu na warware daga zazzabin daya min mummunar damka fiye da sati biyu ina jinya a gida, amma kwana biyun nan na samu sauki har na komawa lectures dina. Ranar laraba wajen karfe goma na safe ina cikin bayi ina wanka zanje makaranta na dinga jiyo karan intercom. Mamaki ya kama ni, wanene a wannan lokacin? Marwan dai baya gari yau da asubahi suka tafi Pretoria harkokin film dinsa sai yayi sati biyu ma sannan zai dawo. Na dauraye jikina na daura babban towel na fito, hijabi babba na saka a jikina wadda ta rufe har duduniyar kafata sannan na fita wajen kofa. Zuwa lokacin an daina buga kofar amma kuma da alamun akwai mutane a bakin kofar, na kama handle din kofa kenan zan bude naji kamar muryar Hindu tana magana, na dakata da bude kofar na kasa kunne a jikin kofar, tabbas kuwa ita dince., "mu tafi kawai tunda ba a bude ba nasan bata nan, kila makaranta taje" naji wata muryar daban tace "...muje kawai, amma banji dadin rashin samunta ba wallahi" wata murya kamar ta matar da suka zo da Hindu ranar nan tace "amma yarinyar nan ta auna arziki sosai. Da mun sameta Allah sai mun lakada mata na jaki, sai mun mata dukan da zai barar da wannan cikin Allah wallahi!" duk cikin yaren Hindu suke yin maganganun, Hindu tace kada ku damu, next time zamu gauraya da ita ne, ai ba karaya zamu yi ba, nice kadai wadda zata dinga haifewa Marwan yara a gidansa, babu wata 'ya mace da zata samu wannan ikon!!!
Ina jinsu suka juya suka tafi suna maganganu, na leka ta kofar makulli ina lekensu, su hudu ne biyun cikinsu ma kamar sun girmi Hindun. Sai dana tabbatar da cewa sun bar kofar gidan sannan na koma cikin falo, na lalubi kujera na zauna ina ajiye numfashi kai kace har sun min dukan ne. Da kyar na samu na kaurara jikina na tafi lectures ko wankan ban karasa ba haka na fita. Ranar kam ban fahimci komi na lectures din da muka yi ba saboda tunanika da suka cunkushe min a zuciyata. Daga makaranta gidan Uncle na wuce direct. Anti kadai na samu a gidan yara suna makaranta, Uncle yana wajen aiki, itama Antin dawowarta daga wajen aikin kenan da yake ta fara aiki. Sai da muka yi sallah muka ci abinci sannan na zayyanewa Anti duk abubuwan da suke faruwa tsakanina da Hindu, da abinda suka zo suka yi yau da safe. Anti ta kama baki cikin jimami tana jinjina lamarin, tace wannan Wace irin masifa ce mata baki sha mata ba baki ci mata ba amma ta dinga neman raba ki da cikin ki? Wannan ai hauka ne da rashin tunani!! Na rausayar da kaina gefe guda, nace to ai ko da ace sun min dukan, to dukan banza zamu min tunda ni dai bani da wani ciki da zasu zubar. Anti tace kika sani? Nayi murmushi kawai na kauda kaina gefe. Anti tace for now kiyi shiru da bakin ki kada ki fadawa kowa, amma idan suka sake dawowa to in fadawa Marwan yasan matakin da zai dauka saboda she can be a threat to my life, ta kuma ce in dage in dinga addu'a akan Allah ya kare ni daga sharrinsu. Na mata godiya da shawarwarin data bani. Ina nan a gidan har su Aslim suka dawo daga makaranta, suka zagayeni muna hirarraki da wasanni har na taya su yin assignment. Sai bayan magriba su Anti suka rakani gida har Uncle dasu Aslim, acan ma sai data kara yi mun nasiha ta bani shawarwari sannan suka koma gida. Bayan na gama duk abinda yakamata inyi a daren, na rufe duk kofofin gidan da windows, na kashe wuta, sai na janyo wayata na fada kan gado na kwanta na dannawa Marwan kira, nan muka raba dare dashi muna hira.



_Plsss ku dinga yi mun uzuri kwana biyun nan bana yin posting akan lokaci kuma bana yin mai yawa, akwai wasu abubuwa da nake ta fama dasu ne wallahi. Ina fata masoya littafin Bayan Rai zasu saka ni cikin addu'a tare dani da sauran en uwa musulmai akan Allah Mai Girma ya warware mana duk matsalolin mu... Ina kuma godiya ga mabiya littafin akan irin comment dinku da yadda kuke karfafa min gwiwa wajen correction, nagode sosai Allah ya bar kauna!_




©Jeedderh🐾
[5/2, 11:00 PM] ‪+234 816 492 9724‬: 💕🐾•°•° *BAYAN*•°•°🐾💕
💕🐾°•°• *RAI...*°•°•🐾💕




🐾°•31•°🐾


Cikin Ikon Allah har aka yi sati biyu Marwan ya dawo ban sake jin duriyarsu ba. Suna sauka a filin jirgi ya kira ni ya sanar dani dawowarsu yace in shirya masa lunch a gidana zai sauka duk da cewa ba nice da girki ba ranar. Na fada kicin na hada mishi kalolin abinci musamman na arewacin Najeriya don yana son irinsu sosai, nayi wanka na tsala kwalliya mai kyau amma ba mai daukar hankali ba don nasan ba girki na bane kada in shiga hakkin abokiyar zama na. Ina sallame sallar isha'i na jiyo knock din kofa, na tafi da sassarfa ta na bude kofar. Yana tsaye a bakin kofar muka hada ido dashi, nayi tsalle na dale jikinsa ya rungume ni tsamm a jikinsa yana dariya. Ina jikinshi muka shiga cikin falon ya maida kofar ya rufe, a tsakiyar falon ya daga ni cakk yayi juyi dani muka zube akan kujera muna shesshekar dariya. Na kura masa ido ina kallon yadda ya kara kyau da fari, ga wata tattausar gargasa da saje da suka yi luf a gefen kumatunsa. Ya kanne ido gami da dage gira yana murmushi, "me yasa kike kallona like this?? Na canza miki ne baby???" na dan yi ajiyar zuciya, nasa hannu na shafa gefen kumatunsa, "kayi mun kyau sosai Khushi, I missed you!!" yayi er dariya yaja kumatuna, "silly girl! Ai kin fini yin kyau ma, amma nayi kewarki fiye da yadda kika yi kewa na baby.... Oya taho ki bani abinci yunwa nake ji".
Na mike a nutse na doshi hanyar kicin cikin takun daukar hankali, ya bini da wani irin kallo lustfully yana kissima wasu abubuwa a cikin ransa, komawa yayi cikin kujerar ya kwanta restlessness ya lumshe idanunsa. Sai dana gama shirya dishes din a gabanshi sannan ya sauko daga kan kujerar, ya zauna a tsakiyar falon inda na shimfida mishi ledar cin abinci, ya tankwashe kafafu kamar yadda ya saba cin abinci. Ni kuma na zauna a gefenshi ina zuba mishi abincin a nutse, ya kuwa ci abincin sosai. Daya gama na kwashe kayan na kai kicin, na dawo na zauna muka dasa hirar yaushe gamo har karfe goman dare ya wuce bamu ankara ba, sai da Hindu ta kira shi a waya sannan ya min sallama, na tashi na raka shi har bakin mota. Anan ma kamar kada mu rabu, da kyar muka yi sallama ya tafi ya barni cike da kewarsa, naso ace yau din ranar girki na ce, in kwanta a faffadan kirjin mijina mai sanya ni natsuwa. Na lumshe idanuna a hankali cike da tunanin Marwan.


☆☆☆☆☆☆

*TWO WEEKS LATER*

Tsaye nake a jikin dogon yaro ina tufke gashin kaina bayan na gama kwalliya cikin wasu English wears riga baka da farin siket, rigar doguwa ce har gwiwa sai dai a gefen cinyoyin rigar anyi wasu tsaga tun daga kwankwaso har kasa, tana da dogayen hannuwa ta kuma kama ni tsam wanda hakan ya taimaka kwarai wajen fito da zahirin tsarin diri da kirar da Allah yayi a kirjina, siket din kuma single ne ya tafi gabadaya babu wani kwalliya ko style. Na kurawa kaina ido ta cikin madubin ina kallon halittar jikina, a yau da nake tsaye a hakan ina cikin shekaruna na ashirin da biyu ne cif da dorin watanni. Nayi aure ina da shekaru sha tara da dori, na samu tsawon shekaru biyu da watanni shida a gidan aurena, amma har yau da nake tsaye haka ni din budurwa ce, ban san dadin aure ba, ban san me ake ji a cikin gamayyar aure ba. Tun bana damuwa da hakan har na fara damuwa, lokaci tafiya yake yi, kuma ni mutum ce lafiyayyiya, ina bukatar abokin rayuwa a gefena to fulfill my desires, amma ban ga alamun daga Marwan ba, he's still seing me as an underage girl wadda bata kai ta fara daukar lalurar aure ba, a cewar shi har sai na shekara ashirin da biyar, lokacin......
Agogo ya buga karfe bakwai da rabi, hakan ya farfado dani daga duniyar tunani dana tafi ya kuma tuna min cewa Marwan yana falo yana jirana zamu yi sallar isha'i. A gaggauce na dauki hijabi na saka na fita falon, yana kan sallaya yana jan carbi, na zauna daga bayansa nima ina jan carbi har aka kira sallah, yaja mu muka yi isha'i muka hada da shafa'i da wutiri, sannan muka ci abinci muka zauna kallon labaran dare.

Da misalin karfe goma da rabi nayi sallama a dakinshi hannuna dauke da tray wanda na dora goran madara mai sanyi da kuma kofuna. Yana zaune a gaban computer yana latse-latse, na matsa gareshi na ajiye tray din na zauna a kusa

Please Login or Register in order to submit comment