Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawwa muje a siyo Kawai ku tafi da abinku school sabo da karku makara,Falaqi da gudu ya kwaso kulolinsu na Yan makaranta suka fita gaba Daya,Gidan Maman Aisha babu abinda Bata dafawa na abincin siyarwa ko me kake so komai dare komai safiya zaka samu,Manal tace kowa ya zabi abinda zai ci,Suka zaba aka cikawa kowa Cooler dinsa sannan ta Basu Naira talatin kowa kudin Break Suka tafi school da murna.

Doya da kwai ta siyo da lemonta,Ta gaji da Halin su Hajiya Bata siyo da su ba ta kyalesu ta dawo gida da nata,tana zuwa ta zauna a tsakar gida ta baje abinci da maltina,Farida yunwa ta fito da ita ko za a tausaya Mata,Itama Hajiya ta dinga zaga tsakar Gidan ko za ace gashi Amma Shuru sai taje daki ta fito ta shiga kitchen ta fito,ta wuce ta Gaban Manal ta zabga Mata Harara ta wuce,ta sake dawowa Tace Allah sawwake abinda za a ce wani ne zai baka,me zaka Yi da kayan wani,Nima maganina kenan Dana ke karba,Farida tayi Mukus ita dai tana so a San Mata,Hajiya ta kalli Farida Tace Yar Iska marar zuciya sai kwalalo Ido kikeyi ke da kike shiga har gidan Sarki ki zaga inda kike so ko a gidan Sarki baza kici ki koshi ba muma ki taho Mana da shi banza lusara,doya da Kwan ce Baki sani ba kinyi asara wlh.

Farida tayi Shuru Kar ta fusata Manal ta hanata,Manal Bata kulasu ba sai ma kafa data harde kafa Daya Kan Daya ta daga gongonin Maltina ta tiltilawa bakinta tayi gyatsa me karfi Wai Dan suji tafa koshi,Wakar barmani coge ta fara Yi... sai dai tatashi nokai nokai sakarai Bata da wayo....muryarta ta Karo da karfi tana wakar sai dai ta tashi Nokai Nokai....Farida taja kwafa a ranta Tace Zaki sani Duk Randa na Zama Gimbiya Farida wallahi sai na tozartaki a duniya,Wayar Manal ce tayi Kara,Farida ta zaro Ido ita da Hajiya sai yanzu Suka kula da Wayar Manal,Farida ta taba ganin Wayar a Hannun Farooq ba shakka shine ya bawa Manal ita,wani bakin ciki ya Kama Farida Taya Manal zata rike Pop 3 ita tana fama da Vivo karama.

Manal Wayar ta daga tana kwankadar Maltina,Farida ta bayan Manal ta koma Dan taga waye ya Kira sai taga an sa (Maganin kuka na)Dariya ta Kama Farida Manal tana cewa Hello Farooq ita Kuma Farida da karfi Wai Dan Farooq din yaji ta sunkuyo da kanta saitin Wayar tare da cewa Yar Kauye Kawai Haka ake sawa Masoyi suna Wai wani maganin Kuka na banza doluwa Ana My love,Honey, Sweetheart ke Kuma kina wani maganin Kuka na kinji kunya kinyi asara wallahi,Fuzail Yana ji radau a wayarsa yaji duk Maganar Farida,wani Sanyi da murna ta kamashi shine ma maganin kukan Manal wayyo shi Kam ya haye Ashe tana sonsa haka,ya dinga Murna da nishadi Farida tana ji Yana ta dariya ta waya Yana tambaya da gaske Haka kika sa? Manal tana tsoron zai kalleta Yar Kauye ta daure a kunyace Tace ae,Wow ya Furta I'm such a lucky Man,Baki Farida ta tabe tare da furta Jaki ta Kara gaba,shi baiji me Tace ba yanzu ma bare.

Me kike ci ne Haka? Manal tana Dariya tace ai yau Allah ne ya jefo min kudi daga sama Ina gyaran dakina in fada maka na tsinci dubu uku a kasan pillow,Yan dubu dubu sababbi baka gansu ba Kamar Kar na kashe su,sabon kudi da kyau suke a Ido Amma Haka na fara kashe su,Jiyama nayi sabuwar kawa anjima Zan baka labarinta sunanta Shukrah jiya tazo,Fuzail yasan sakonsa ya fara zuwa yaji Dadi Shukrah ta fara Aiki,Yace to dubun ukun ya kika Yi da ita?

Gashi Ina cin dadina da ita Bata fada Masa har kannenta da su Suka ci abinci ba sabo da Kar ya rainata da yawa ko taje tayi Abu Dan Allah ta zobe ladanta sai Tace ita kadai taci abin Dadi bayan ta karya,Yace Uhm Good kinji dadinki,Manal ta Mike ta bar ragowar abincinta ta saka Hijab suna waya tayi waje,Farida ba jira ta dauke ragowar ta lashe aka bar Hajiya sai hanji a ciki.

Manal tana fita katin MTN ta siya na dari biyar a cikin kudin Tace da Fuzail Ina zuwa Kawai ta copying Numbers din katin a kasa ta rubuta Ina sonka ta tura Masa ta text,Sai ganin Kati yayi ya shigo, ya dinga dariya Allah sarki tausayinsa take ji talaka ne shima bashi da kudi.

Sending back ya Mata abinta ya kirata Yana Mata fada shi baya so zai Fara sana'a Kuma Dan uwansu Yana Basu kudi,Manal Tace to Ni me zanyi da Kati tunda kana kirana,Nifa bana so na gode ban tura miki ba sai kece kina mace Zaki bani kudi karki sake turo min,Manal Tace to Dan Allah naji bazan sake ba Amma ka saka wannan Dana turo,Fuzail yaki yarda Ameer Yana jinsu yace Ni dalla bani na saka Nima naci irin kudin Prince,Fuzail ya kyafta Masa Ido Wai Kar ta ji,Ai Kuwa Manal Tace to bawa Ameer ya saka shi tunda na maka kyauta baka so ka watsa min kasa a Ido ai ya maka kyau Kuma Kar ka sake kirana munyi fada, idanba munyi fada ba ta kashe wayar tana cewa a bar katin ya gaji ya bushe a waya wallahi bazan saka ba.
Dole sai Ameer ne yasa katin Yana dariya Yana tsokanar Fuzail kaga na me tausayi inyee Dan gata har Kati ake sa maka,Fuzail ya share shi kawai.

Zuwa dare 10pm Manal tana dakinta suna waya da Fuzail da gwarancin hausarta tace Wai hadin gwiwa akayi da larabawa aka haife ka? Fuzail shima yace a'a mutum da mace Daya ne Suka haife Ni Zaki ce Wani Hadin gwiwa sai kace wani Business,Dariya Suka Yi gaba Daya tace kayi Hakuri ba nufina mutum da mutum ba Ina nufin Kai ruwa biyu ne Mamanka ko babanka ciki akwai Balarabe? Fuzail yayi Dariya yace ko Daya Haka Kawai Allah ya halicceni,Labarin Shukrah ta dinga bashi,yace kinyi Friend amma Banda fadar sirrinki ki kiyaye wasu matan Basu da hankali karki saurin yarda da mutum,to ai dama bazan saki jiki ba babu ruwana cewar Manal,Yace Good suna ta Hira a Haka suka Yi bacci ba tare da sun shirya ba.

Bayan Kwana biyu Shukrah Bata Zo ba sai a kwana na Uku taci kwalliya ta sake zuwa da Yamma,Manal sanye take da wani tsohon lace dinta pink,ta ja Shukrah Suka shige dakinta,Shukrah ta dinga Jan Manal da Hira har ta Dan saki jiki sannan Tace Manal a rugar da kika Bari kinyi makaranta? Manal Tace a'a Amma na fara iya karatun hausa da Dan wani turancin ma,Shukrah tace to ba damuwa ki tanaji littafi da biro daga yanzu kullum na samu time Zan dinga shigowa Ina Dan koya Miki wasu abubuwan,Manal tace Kai Amma na gode Allah ya bada Lada,Tace Ameen,Shukrah tace akwai wasu Kaya Kala hudu Dana dinka,Amma telan ya min shirme yayi min Dinki karami gaba Daya baifi size dinki ba,telan Nan ya cuceni Zan kawo Miki su ki dinga sawa naga kina da karancin sutura gaki Budurwa ya kamata kema ki canja,Manal ta dinga Murna tana godiya harda Rungume Shukrah sabo da ta tuno Farooq zai zo zance zata Masa kwalliya sosai shi yasa take ta faman murna,Shukrah Tace harda takalmi da mayafi Zan hado Miki,Manal tace wayyo muje ki nuna min gidanku kawancen Nan naki Naga da gaske kikeyi,Shukrah ta dinga dariyar Manal duk ta haukace akan kayan sawa,Shukrah tace gashi an Mana Albashi harda kayan kwalliya Zan siyo Miki,Manal ta Bude Baki harda Hawaye Tace Dole muzo gidanku da Farooq Dina ya Miki godiya ta musamman,Shukrah tace au har saurayi ne dake? Laaaa ai na kusa aure jira nake Yaya da Babanmu su dawo za a kawo kudi,Shukrah Tace mashaallah na tayaki murna Yar uwata yanzu dai kawo min ruwa na sha,Manal ta Mike da sauri ta fice lokacin Shukrah ta sake Bude kayan sawar Manal Wanda ta wanke ta linke,cikin ninkin zanin atamfa ta sawa Manal dubu biyu.

Bayan Shukrah ta tafi Manal tana gyara kayanta kudin suka Fado Amma wannan karon tsofaffin kudi ne tukuf,Manal tsoro ya kamata Nan take ta Kira Fuzail a waya tana kuka,tsoro ne ya kamashi duk ya rude Yana tambayarta lafiya? Tace kaga wani kudin na sake tsinta a cikin kayana dubu biyu,Fuzail ya sauke Ajiyar zuciya tare da furta kin bani tsoro wlh nayi zaton ko Baki da lafiya ne,Allah ne ya Baki karki ji komai ki kashe abinki,Zuciyarki ce me kyau Allah yake dafa Miki,Manal tana shesheka Tace nidai Kar nazo ko Aljani ne yake biyan Sadaki na,sai na ci kudinsa da yawa yace ya aure ni,Dariya ta Kama Fuzail da kyar ya Mata wayo hankalinta ya kwanta.

Hajiya ta kwana da yunwa ta yini Nan fa Ulcer ta shigeta me karfi ta fara ciwon ciki da ciwon baya tare da zafin kirji,kwana tayi tana murkususu,Farida Suma ta cikinsu sukeyi da kyar Tace ki tashi muje wajen Kawu Sani a kaiki asibiti,Hajiya tana rike ciki da kirji tace Manal ce tayi min asiri na sani a samu a kaini wajen Malam Dan Haru shi zai min magani wayyo gadon bayana,Farida Tace Ni wallahi wajen Ruma zanje ta bani dari biyar nazo naci abinci sai dai ki jira tukun tayi ficewarta ta bar Hajiya su Falaqi suna jinya, sai da Rana sosai Farida ta dawo cikinta a cike ko wajen Hajiya Bata kalla ba Ganin Manal ta tafi raka Shukrah sai ta shiga dakin taga irin kayan da Shukrah ta kawowa Manal sababbi na sawa Takaici ya Kama Farida,Wayar Manal ta hango saman katifa,da sauri ta dauki Wayar ta dauki ragowar pure water ta samu ta dura ruwa a ko Ina na kafafen Wayar sai da ta tabbatar ruwa ya ratsa Wayar sannan ta goge jikin Wayar yanda baza a Gane ba ta fice.

Ita Kuma Manal Bayan ta raka Shukrah Chemist taje ta kwatantawa me Chemist irin ciwon da Hajiya ke fama da shi,Ya hado Mata maganin Ulcer,ta tsaya ta siya Mata Maltina da Madara da abincin ci sannan ta siyowa su Falaqi ta dawo gidan har dakin Hajiya ta Kai mata,Wahala da yunwa ta ishi Hajiya ba shiri ta fara Shan kowanne maagani,Cikin Yan mintuna sai ga Hajiya ta warke,ta dauki abinci taci ta sha,Su Falaqi ma Suka koshi,Amma Farida tana zuwa Hajiya ta kalleta tace shegiyar ta karya tsafinta,Maganin Ruwa Gestid ta daga tace wala'allah a Nan ta Sako maganin taga mun ganeta shegiya har da siyo min abinci sabo da Kar na mutu na rataya a wuyanta,Falaqi yace Wai Me Manal tayi muku ne mu muna sonta tana kula da mu,Farida ta zuba Masa rankwashi,Sa'iha tace daga ya Fadi gaskiya,Masatura Tace Ni wallahi ma Nan gaba dakin Manal Zan koma da kwana,Alhaqatu itama Tace Nima Haka mu dinga koya Mata karatu.

Manal Kuwa tunda ta duba Wayarta taga ta dauke duf,gaba Daya komai yaki Yi,batayi Hankalin budewa ta goge ba Kawai ta barta ta kwanta Haka gashi gobe Farooq zaizo zance ta Gama shirinta,shima Fuzail Yana ta Kiran Wayarta ya fada Mata zaizo fa Amma da dare Shuru Wayar Bata shiga ya rasa dalili Haka ya hakura zuwa da safe.

Da safe ma Shuru Wayar Manal,Manal Allah yasa ta haddace number Farooq Kawai Wajen me shagon Kofar gidansu taje tare da karbar Aron waya ta Kira Fuzail,Shuru ba a daga ba,shi Fuzail ba sosai yake daga number da Bai Sani ba,Yana Gaban sarki yaji an dameshi da Kira Tsaki Yaja sannan ya daga,sai yaji Muryar Manal zumbur ya Mike tare da barin wajen memartaba sarki.

Wace Manal?







Masu Sharhi kunfi kowa birgeni,Ina sane da ku akwai special pages kowacce Bata Guda.








AsmaBaffa








AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭









IS DEDICATED TO

DUNIYATA AAMNA FANS GP.











31-35












Official








By
AsmaBaffa











Page naku ne

UMMIE ~ZARIA
MRS OM@R
ASMAU SANI
ABDULMOUMUNIBARIRA
BILYN NAS
UMMU JAFAR
SADIYA GARBA SHESHE
MAMAN AFRAH
MUM KHADY



















Malam Rabiu Isa Wanda kowa ya sani da Malam shine cikakken sunan Baban Manal,Asalinsa yankin Nasarawa state ne can cikin wani kauyen Shagari,Su biyar Iyayensu Suka Haifa duka maza a kauyen,Malam Salahu Shine na farko sai Murtala,Malam Nasiru sai Malam Umaru Wanda Allah ya Masa Rasuwa,sai Mas'ud shima Allah ya Masa rasuwa,Saura su Uku Suka rage,kafin Iyayensu su Rasu ba abinda Suka gada sai Harkar malinta,gidansu kaf limaman kauye ne,kowannensu Yana da Almajirai Kamar yanda Suma daga almajiranta Suka Zama Malamai,Suna da Ilimi na Masu karatun Allo hakan yasa tun suna matasa Suka fada Harkar tsubbu,Suka shiga rigar Malamai Suka koma Harkar bokanci tare da kulla alaka da Aljanu Wanda zasu dinga Yi musu hidima Suma suna biya musu bukatunsu,kaf kauyen tsoron gidan lilaman akeyi sabo da an San Basu da Imani ko digo.

Cikin ikon Allah Rabiu ya tashi da almajiransa ya bar Kauye ya koma cikin birni tare da Kama hayar gida shi da yaransa Almajirai daga Nan kasuwar bokanci ta bude a birni har ya mallaki gidan da su Manal ke ciki yanzu,Ana Haka Ya hadu da Hajiya Babar su Farida Zulai wacce asalinta Yar Katsina state ce itama gaba Daya tashi tayi ta tsincesu da danginta da yawa a Nasarawa,Tana da Yayye maza biyu sai sauran Yan Uwa,Iyayenta Kuwa dama basa raye a Hannun Dan uwanta ta girma Kawu Sani.

Tallan goro takeyi a kasuwa Malam ya hadu da ita Suka Fara Soyayya har sukayi aure tare da Yan Uwansa Suma,Malam Baida Imani a lokacin,baya tausayin mace ga wulakanci gashi da son Mata,ko magani Mace tazo Nema Wajensa sai yayi Zina da ita zai Mata magani,sabo da Aljanun da yake Muamula da su sune suke sa shi hakan sannan bukatarsa zata biya.
Ana Haka ya tafi Bauci Karin Ilimin bokancinsa a can ya hadu da Annatu Wato Hadiza Me tallan Fura,fara kyakyawa,tun daga siyen fura yaji shaawarta lokacin Kuma Zulai Wato Hajiya Shuru Taki Haihuwa alamar Bata Haihuwa.

Yana auren Annatu
Shekararta Daya ta Haifi Yazed sankacece fari tas Dake Annatu Fara ce kwal Haka Malam ma Yana da haske daga Nan Kuma Malam soyayya ta kare, sai ya tsani Annatu da jaririnta,ba Wanda ya tsana irin Yazed.

Komai zaiyi sai yayi shawara da aljanunsa sunan Jariri ma su Suka ce a sa Falaqi, ranar suna ya sa Masa Falaqi,Annatu Tace wallahi sai ta canja suna Dan baida ma'ana suka dinga Fada Hajiya tana ji tana murna sabo da ita Bata Haihu ba,ba a Dade ba Annatu ta yanka tinkiyarta tare da cajawa Yazed suna ta sa Masa Yazed,Haka Yazed ya taso cikin duka,zagi da tsangwama wajen Malam sabo da Aljanu sun bada suna Anna ta canja masa.

Bayan Shekaru Bakwai Hajiya ma ta samu ciki,murna Kamar tayi hauka itama tana samun ciki Malam ya tsaneta,bayan ta Haihu Nan ma Aljanu Suka ce a sa Mata Masatura,Itama Hajiya ganin an canjawa Yazed shine ta canja zuwa Farida,Malam ya dinga Bala'i yace sai ya koresu da kyar aka bashi Hakuri,Bayan wasu Shekaru Anna ta sake Haifo Manal,ranar Suna rikici ya hauke tsakanin Malam da Anna, aka sawa Manal Waqia da Umarnin Aljanu,Yazed da Kansa ya canja Mata suna Manal,Lokacin sai da Malam ya Kori Yazed daga gidansa ya koma kwana a masallaci,sai da ya kwashe watanni kafin Malam ya dawo da shi,duk wani aikin walaha Malam to Yazed yake sakawa har Yazed ya taso sosai tsakaninsa da Malam sai Harara,Kudin Makaranta ma Anna ke siyar da dabbobinta tana biya masa.

Lokacin Aljanu Suka hanashi Saduwa da matansa na sunna sai dai matan banza kullum baida Aiki sai Zina da Mata iri iri,gashi duk irin asirin da aka ce yayi ba ruwansa aikatawa zaiyi,ya raba aure ba adadi,ya haukatar da mutane,yayi Abu munana iri iri Wanda kisa ne Kawai Bai taba kashewa ba,Hajiya gajiya tayi ta fara masifa akan baya Bata hakkinta har an kwashe shekara Biyu,ganin Haka sai ya koma amfani da Yatsansa Wai Haka zai biya musu bukata,Kowacce ranar kwananta to da yatsa zaiyi amfani,Annatu ta rasa Gane inda yasa gaba Ganin irin wulakancin da yake wa matansa

Ganin Haka Hajiya ta tashi tsaye tace ai shima mutum ne Dole tsafi zai ci shi direct ta tafi gidan Malam Dan Haru Wanda taji Mata suna labarin iya aikinsa,tana zuwa Tace so take a juyo da Hankalin Malam gareta ya dinga Mata abinda take so,Ai Kuwa Aiki yayi Malam sai yanda Hajiya tayi da shi,ita Yana biya mata bukata Amma Banda Annatu da ta Zama aikinta gyaran gida da girki ta koma Yar aiki a gidan sun hade Mata Kai da Hajiya,Ana Haka Hajiya ita taci gaba da Haihuwa ita Kuwa Annatu shuru Sabo da baya ma Saduwa da ita,Katsam Watarana aka Kama Malam da yarinya karama Yar Shekara goma zai Mata fyade Allah yasa wasu maza a cikin Almajiransa suka Tona masa asiri sai da ya zauna a gidan yari na wata takwas,Bayan ya fito ya Dora daga inda ya tsaya ba abinda ya fasa,tunda Manal ta taso gwanin sha'awa kyakyawa da ita Fara kwal Hajiya ta tsaneta,Watarana Annatu ta shiga makwafta kafin ta dawo Hajiya ta durawa Manal Fiya fiya a kunne,Anna ta Iske Yarta ta sankame da gudu ta kaita asibiti yarinya tana Suma,Malam Kuma yace kwandala bazai biya ba,tunda Anna ta samu Manal ta warke ta hada tarkacenta da Manal ta gudu kauyensu,Malam sai takardarta ta saki ya aika Mata,Yazed yayi kuka ya gode Allah.

Daga Nan Kuma Hajiya ta koma Kan Yazed,Yana Namiji amma har girki shi yakeyi a gidan,ga shara da sauran ayyuka,Idan yayi ma Bai huta ba Haka Malam zai bishi da zagi da duka,Itama Hajiya tana yi masa mugunta kala kala a Haka Yazed ya taso har ya girma,duk da Haka Kuma Yana Dan fita ayyuka iri iri idan ya samu kudi ya biya kudin makaranta ko Annatu ta siyar da dabbobinta tana turo Masa kudin a Haka har ya Kai matakin Degree Lokacin Hajiya tana da Yara biyar hakan Kuma Malam Aljanu Suka hanashi Haihuwa tunda ya bawa Hajiya wani ruwan Rubutu ta Tasha Bata sake samun ciki ba har yau,duk Halayen Malam Dana Yan Uwansa babu Wanda Bai Sani ba,ba a yabonsu ko kadan.

Katsam Allah yajarabce shi da wata cuta wacce an rasa kanta,Kafafunsa basa Aiki,Haka wuyansa ya karkace gefe ga hannu ma ba sosai yake Aiki ba komai sai an Masa,magani ba Wanda basuyi ba,test anyi iri iri ance lafiya komai nasa,gaba Daya cutar Saida ta cinye arzikin da Malam ya Tara kaf Haka ta cinye na yan Uwansa,ga Harkar malitar tasu ta tsaya an daina yayinsu maganinsu ya daina Aiki kaf,gaba Daya sai Suka daina ta Dole,ga Talauci Yana Kara riskarsu Yan gonakin ma da suka rage Gomnati ta kwace,Ganin Bala'in yayi yawa Malam da Yan Uwansa Suka Fara Dana sani,kullum cikin nadama suke,Yazed Kuma ya gaji sabo da lalura akwai tausayi,Malam Salahu yace yazo da Malam Kaninsa a gwada Yi Masa karatun Qur'ani na sati biyu ko za a dace Suka tafi da Malam Kauye za masa maganin.

Ci Gaban labari

Fuzail da fara'a ya furta Ina kika Shiga Haka? me ya samu wayar? Manal tana wani murmushi Jin muryar Sahibinta harda lankwashe Murya Wanda Bata San ma tayi hakan ba ta furta Wayar ce jiya ta dauke duf nayi nayi taki kunnuwa na rasa dalili,yanzu wannan layin na waye? Fuzail ya tambaya ta furta Na me Shago ne,Kishi ne ya Kama Fuzail me ya hada ki da me Shago har da wani karbar wayarsa? to ba Kai Zan Kira ba shine hadina da shi kawai,Ana yin Sallar Magriba Zaki ganni a Kofar gidanku,Manal ta matsa gefe tana kasa da Murya cike da Jin Dadi tace kayi min kwalliya Shadda zaka saka min,Fuzail yasan an bashi Aiki sabo da saka shaddarsa baifi sau hudu ba a duniya,to Kawai yace,Tace Anjima Yaya Yazed zasu da dawo da Malam idan kazo sai ku gaisa,Fuzail yace Allah ya kaimu,me Zan siyo Miki? Ba komai gwara ka dinga Tara kudin Nan sai munyi aure ka siya Mana kayan abinci shinkafa buhu Guda nasan ma Sai mun shekara Bamu cinye ba,Dariya ta bawa Fuzail ita Bata da Aiki sai zancen abinci.

Kannen Fuzail ne Suka shigo part dinsa su Hudu,Yan Mata biyu Na'ima da Fatima sai Maza biyu Yan matasa Hassan da Hussain,Duk sun Sha gayu suna zuba kamshi sanye da wasu arnayen yadika masu tsada,matan Kuwa wasu lace ne a jikinsu masu tsada,Fuzail Yana waya da Manal suna Kallonsa sai Dariya yake Yi,suka dinga mamaki su Basu San ma ya iya Dariya ba, Kallonsa suke Yi Kawai kamar sun samu Tv,Har ya Gama sannan Na'ima Tace Yayan Brazil wannan tayi sa'a ko wace Wai a Ina kuka hadu ne ko a London kuka hadu? Fuzail yace no a Nan take,Wow Yar waye Haka nasan ma Yar gidan wani kusan ce a kasar Nan ya sunanta? Fuzail ya fadada murmushinsa duk akan zai ambaci sunan Budurwarsa ya Furta Manall harda wani Jan L din,Fatima ta koma kusa da shi Tace Nice name yaushe zaka hada mu da ita ta Zama kawar mu? Fuzail yace me tsada ce sai an kusa biki Zan hada ku,wannan Kalar ba irin Taku ce ba ta manyan Yara ce,Huuuu Na'ima ta Furta Allah na matsu Naga irin Haduwar ta nasan ma muguwar Yar gayu ce,Fatima Tace me Ilmi ma Kuwa Allah yasa muma a London Muka Yi karatu mun Iya irin turanci nasu, Fuzail shi yasan me ya sani Kawai Hmmm yace,Hassan Yace Watarana zamu rakaka zance tun yanzu ya kamata na Zama Dan Gaban goshinta,Hussain yace nine me rike Mata jaka Yayan Brazil,Fuzail ya wani harde yana karkada kafafu Yana hango Kansa Manal ta Zama matarsa ma yace Wanne Dan Gaban goshinta zaka Zama Ni Kuma ta kaini Ina? A keya za a ajiyeni Ni ko a gadon Baya? Fuzail yace ji min yara so kuke ku kwace ta ku kuna a gabanta Ni ta maida ni Bayanta kenan, Su Na'ima Suka dinga dariya su dama suna son Hira da Fuzail zasu ci Dariya.

Yau Farida da Rana ta shirya zuwa gidan su Ruma zata karbo kwancen kayan sawa,ta sauka a Napep kenan zata Dan shiga ta layin su Ruma a kafa sai ga Arnayen Motocin Fuzail sun Kai hudu ko wacce tana sheki da walwali masu tsadar gaske,sai binsu ake da kallo,Katsam Farida taga Number Fuzail ai sai ta hau dagawa Motocin Hannu suna wucewa tana daga musu Hannu tana washe baki tana Mijina...Mijina,Fuzail Kansa na kasa a mota gashi ta Sha tint Bai ma ga wata Farida na daga Hannu ba,Yau Kuma a cikin motar Fadawa masu kula da prince Tanko Yana ciki shine ya kula da Farida a gefen Titi tana daga musu Hannu,Dake Motocin a hankali suke Tafiya da sauri ya sauke Glass kasa tare da leko da Kansa ta window yace da karfi Faridaaaaaaaa.......na gani na gode daga Hannun ya Isa Haka Kar damatsanki su kumbura,Ganin Tanko ne da sauri ta sauke Hannunta tare da Jan Tsaki kafin ta tafi ma tuni Motocin sunyi nisa Amma duk da Haka Farida da Murna a ranta ta Shiga gidan su Ruma Baki Kamar gonar auduka.

Manal shirin tarbar Masoyi akeyi da wuri ta wuce gidan su Shukrah Kamar yanda Suka tsara ,Shukrah tace tazo su yiwa Saurayin nata Samosa da Springrolls, Shukrah sabo da kirkin Manal da kudinta ta siyo kayan hadin komai,Itama Iyayen Shukrah da danginta zuwan Manal biyu kacal amma ta Shiga ransu,Maman Shukrah harda ita ta tayasu aka Yi da yawa yaji Hadi,Maman Shukrah tace idan Bai ci ba ki zuba Masa a Leda ya tafi da shi,Manal wacce ta

Please Login or Register in order to submit comment