Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida zai tayata suyi ko Watarana ya hanata yi,Ana Haka masara da dawa Suka Kare aka kawo Wai sai dai su daka da kansu a turmi,Farida sissika ta samu,Da Sassafe Bayan ta Gama duk wani aikin gidan tana Dan hutawa,Belloti Yana dakin suna hira,Goggo ta shigo tace to ishashiya ke ga Yar birni ko kula Miji Kika iya sai ki fito ayi sissika da ke,Belloti yace Haba Goggo Wai duk abinda take muku bakwa gani duk Kun jawo tayi duhu ta rame Bata da hutu,har wanki da guga take muku fa,Baffa ne Kawai ke kaunarta a gidan Nan Dan tazo ta gaisar da ku Bai kamata ba , Goggo da bala'i Tace rufe min baki idan Kai ta shanyeka mu Bata shanye mu ba,gaba Daya ka tare gindinta sannan in zauna in girka tana zaune gansansan Mene amfanin Suruka,mu a Nan Suruka hutawa take Kai ka sani Indai danmu yayi aure Dole Babar Miji da Yan Uwansa su huta.

Farida ta gaji sosai kullum Aiki kamar jaka Bata da hutu gashi Bata Saba ba abin duk sai ya dameta ga masifa da hantara kullum,kannen Belloti suyi Mata rashin kunya su zageta amma duk masifa da Rashin kunyar Farida sabo da tana son Belloti Bata so ransa ya baci sai ta hakura duk wani cin Kashi Haka ake Mata shi a gidan Bata iya magana bare ta rama sabo da duk Wanda ya shafi Belloti kaunarsa takeyi a duniya.

Belloti Kamar yayi kuka Yana kallo Farida ta fita aka zuba Mata surfen Gero a turmi akace ke surfa wannan kunu za ayi mu Kuma ma daka dawa,Farida ta dauki jibgegiyar tabarya ta fara surfe da kyau,Goggo da bala'i Tace idan Zaki saki jiki ma kiyi aiki kiyi Nan Kauye ce da lafiyar mu muke ci,Farida ta fara surfe ta barke da kuka Hannunta ya fara kanta.

Kannen Belloti suna tabe Baki suna Dariya,Hakan yasa Belloti yaje ya kaiwa Baffansa Kara, ai Kuwa su Goggo sun Sha fada Amma Basu yarda ba ko a jikinsu suka ci gaba da kuntatawa Farida,hakan yasa Belloti ya matsa shi shanunsa zai siyar da gonarsa zaije ya Kara jali a birni sabo da su Basu San Belloti baida ko sisi a kasa ba,tunaninsu kudi ne da shi Farida ke karbewa,Baffa yace Sam Belloti Bai Isa ya siyar da Ko tsinke ba,Wasa Wasa har Farida ta kwashe sati Uku a Kauye duk da tana shafa Mai me kyau Bata wani dauki haske ba sabo da wahala da cima marar kyau, ko shayi idan zata Sha sai dai Belloti ya siyo Mata a boye sabo da kayan shayin Daya siyo Mata a birni Yan gidan sun daka musu wawa ba komai.

Wahala tayiwa Farida yawa idan tana so ta rage damuwa sai ta tafi wajen Annatu acan take cin me dadi,ganin Haka yasa Goggo ta fara bala'i ta hanata fita ko Ina a garin,tunanin duniya yayiwa Farida yawa,ta zauna tayi kuka taci kuka bazai irgu ba,Dana sani da nadama ta lullubeta kullum sai ta tuna samarinta na birni da tayi ta wulakantasu da Kuma halinta na banza da ta dinga Yi,da iyayenta da Bata yiwa biyayya ba gashi yanzu tana yiwa wasu biyayyar dole wacce ba Sannu babu na gode,Nadama ta Zowa Farida musamman da taji Rumaisa Fahad zata aura su chale Uk,Ga Shukrah ma Ashe wannan data wulakanta custome ne Bata sani ba, gata a Nan a Kauye soyayyar wani tana wahalar da ita,duk soyayyace ta jawo Mata ta hakura da halin da take ciki.

Daki Farida ta koma ta fashe da kuka a Haka Belloti yazo ya isketa,Tausayinta ya Kama shi Yace Mene ya faru? Farida tana shesheka Tace Dan Allah ka maida Ni gidan mu please,ko mu fadawa Manal halin da muke ciki su kawo Mana agaji mu bar kauyen Nan wallahi na tabbata har gidan Zama zasu bamu,ko mu fadawa Malam ko Yaya Yazed,Dan Allah ka dauke ni daga garin nan,Farida tana ta sharbar kuka gaba Daya nishinta da walwalarta ta gudu a kauyen shi kanshi Belloti Bai Jin dadin hakan gaba daya,gashi har sun kwashe wata guda.

Hawayenta ya goge Mata yace Inshaallah baza mu sake sati ba a garin Nan ba ko da kudi ko babu,Haka Belloti ya nemi Lawi Suka Yi shawara Kawai a siyar da gonar a boye a bar shanun,ai Kuwa Baffa Bai Sani ba suka siyar Belloti ya hada dubu dari biyu da Hamsim cas a account dinsa.
Sai bayan ya siyar sannan ya sanarwa Baffansa,Baffa ya dinga Fada yace tunda ka siyar mene sai ku tafi ka Kara jarin Allah Sanya Albarka,Su Goggo suka dinga bakin ciki Belloti Wai bazai tafi ba sai dai ya zauna gaba Daya a garin,Belloti kuwa Suka hada nasu ya nasu,ranar Farida Allah sarki sabo da Murna ko bacci bata iya Yi ba,Da Asuba tana yin Sallah tayi wanka ta shirya sannan ta tashi Mijin Bata Dake kwasar bacci,shima Haka yayi Sallah ya shirya,Lawi da wuri ya Kira musu me Golf din da Suka saita da shi zai kaisu,suka tattara kayansu kaf Suka musu Sallama Goggo sai cika take tana batsewa,Lawi a sirri yace ga number din me gidan da zai Baku hayar Yana jiranku yace ba a state din Nan yake ba sabo da ku yazo.

Bello ya karba sai Kano ta dabo suka dawo Yana Kiran me gidan ya Basu address din gidan da Suka Kama Hayar Wanda Lawi ne ya musu hanyarsa,Suna zuwa Alhajin Yana rantsatsiyar motarsa Yana jiransu bazai iya bada gidansa ba sai yasan waye me zaman Kar a Bawa samari su dinga kawo Masa Mata karuwai gida,Su Farida Suka fito suna kallon gida sabo Dan madaidaici harda gate yasha tiles ko Ina,Alhajin ne ya fito karaf Farida taga Alhaji Kasim saurayinta Wanda ta mareshi a Kofar gidansu har tana Kiran motarsa da Gongoni,Yayi mamaki ganin Farida yace Allah me iko.......







Ayi Hakuri fans kwana biyu bana Nan ne nayi tafiya shi yasa ban samu time ba.
Ina bada hakuri.

Masu magana a groups da masu kirana a waya da masu min magana ta PC aji ko lafiya Ina godiya sosai,Allah ya bar kauna.












AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭





DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP







91-95






Official







By
AsmaBaffa







Page naku ne

Maman Nusy
Maman Al'amin
Maman Humairah&Ikhram
Feenat
Oum Abdallah
Oum Naeem
Mmn Waheeda
Leemat
Umma Musa
Ummu Ilham
Yar Gata
Yar Abba Ta Annabi
Maryam T Baliya







Alhaji Kasim yace Farida kece Wai? Farida kunya ta kamata sai ta koma Bayan Belloti ta buya,Belloti yace lafiya ana Miki magana kina wani buya? Farida gefen gyalenta ta Kama tana ci a kunyace tace Ina yini? Alhaji Kasim yace rayuwa kenan,duk duniya ba Wanda ya taba kunyata Ni ya min wulakanci a idon duniya irinki Farida naji kunyar da ban taba ji ba,amma ba komai Ni bazan Miki Haka ba,Hannu ya bawa Belloti suka gaisa yace wanne Aiki kake Yi ne? Belloti yace da dai Ina Zama a shagon wani Uche Christain ne na daina sabo da har giya yake siyarwa Ni Kuma na hakura sabo da bana son Iyalina su taso a cin Haram,Ina ciyar da su da Haram ba tsari, Alhaji Kasim ya furta ka birgeni hakan yayi Haka ake son musulmi,yanzu kayi makaranta? Belloti yace a'a Uche dai ya dinga koya min karatu da Rubutu Sanda na fara sanin me nake Yi ya biya min Waec na zana ko duba Exam din banyi ba sabo da nasan Banda kudin daukan nauyin kaina karatu a kasar Nan ya Zama abinda ya Zama sai kana da kudi.

Alhaji Kasim yace Alhmdllh tunda ka Dan Iya karatu da rubutun Zan baka Manager a gidan Mai na,idan Naga kwazonka ma Zan Kara maka gidan Mai biyu ko Uku ka dinga kular min da su,Belloti ya dinga Murna da godiya,Farida ma Sai godiya takeyi harda hawayen nadamarta tace ka yafe min Dan Allah,Alhaji Kasim yayi Dariya yace ai ya wuce Farida ba komai,ga gidan Nan ku zauna kyauta har zuwa lokacin da Allah zai hore muku ku mallaki naku,Belloti yace wannan taimakon yayi yawa,ba komai Dan Allah nayi ai,Haka suka Yi Sallama da Alhaji Kasim,Belloti bayan sun shiga gidan yace Wai me kika Masa? Farida ta bawa Belloti Labari,Belloti yace kinyi shirme ita rayuwa ba a haka gashi yanzu shine zai Zama silar cin abincinki kwana Nan Zamu samu Shinkafa Available,Dariya Farida tayi Tace wallahi Kuwa Harda shinkafa da Miya da Naman kaza,Ga dafaduka me yaji cewar Belloti,Da shayi me kauri ko? Belloti yace ai harda doya da kwai,ga dankalin turawa cewar Farida,Kwanan nan Zaki koma shafa lotion Dan dubu bakwai,Dariyar farin ciki Farida tayi Tace da takalmi coge me kyau,harda jakarsa za a siya Miki me Injin Daf,Ga su lemo Fanta da Juice,Belloti yace ai rabarbashewa zamu Fara har da Madara me gardi kiyi Addua ya tabbata,Farida tace daga yau na Fara Nafeelar dare kenan a samu aikin nan.

Gidan ba ko tsinke a ciki abinci ma a Resturant Suka ci,ranar a saman Bedsheet Suka kwanta Kawai,washe Gari Kuwa kudin Belloti dubu dari biyun ya cire ya sa musu katuwar Katifa da tarkacen kayan girki sai abinda ba a rasa ba,kayan abinci Suka siyo daidai gwargwado sai kudin cefane da Suka rage,Haka a ciki sai da aka sake turawa Hajiya kudin abinci 5k.
gidan nasu me 3bed rooms an Palo,sai kowanne room da toilet dinsa ga store da kitchen da compound,gidan ya hadu harda flowers ga wajen parking Wanda zaici motoci Uku,ko Ina yasha interlock,ga tiles har jikin bango,gidane bana Wasa ba,Belloti yace da Zan samu kudi gidan Zan siye Kawai ya koma namu,Farida tace gaskiya yayi wlh bamu da kunyar kowa yanzu da ace akwai furniture yaushe Zan Hana kowa zuwa ko nace wa Malam munyi wani sabon gidan ayi min furniture Dina na aure? Allah ya kiyaye Ni Zan Miki da kudi na,Suna Haka Manal ta Kira Farida,Dagawa tayi tace Aunty me duniya kin bar kauyen ne? Farida Tace ae mun koma gida,Manal Tace mu fa har yau Muna Bauchi,me kukeyi? Muna Hotel Honey moon muke Yi,Kun Shiga Uku wlh,Dariya Manal tayi Tace to ki bani account Yarima zai Miki kyauta,Farida farin ciki ya kamata tace kice Ina godiya Kar ayi min karamar harka,Manal tayi Dariya tace Yana jinki ai kina Nan Farida da son kudinki? Farida tace yo me Za'a fasa wa yaki Dadi da Hutu,duk Wanda yace ka fiye son kudi wallahi ya Raina maka hankali ma,uban waye baya son kudi.

Yanzu idan baka da shi babu me harka da kai,idan kana da kudi ko baza ka bada sisi ba Haka zaka ga Ana kaunarka Ana ji da Kai,Manal tana Dariya tace ai nayi zaton Cucumber ta isheki rayuwa yanzu,Kin rainani Manal wallahi Zan fadawa Yaya Yazed a Gaban Fuzail kike min Haka ko? Ina Mijin naki?Manal ta tambaya, Fuzail daga ji an tambayi Belloti yace ta Baki accnt Ni bana son gulma,Manal Dan ta tsokani Fuzail Tace Bawa Yaya Belloti mu gaisa Dan Yayanmu Allah sarki Manal ta furta, Fuzail Yana saman kujera tana kasa a zaune yasa kafa a wuyanta tare da Danna kanta kasa Manal ta saki Kara amma bata fasa tambayar Belloti ba,Tace Aunty kinyi Dace wlh Ni ai ban San Belloti ya Kai Haka ba sai Rannan wani santaltali Haka,Aunty ana holewa Sannu...Farida tace ke fa munafuka ce Manal shi yasa bana daga Miki kafa,Manal tana Jin Belloti Yana cewa Me Injin trailer Zo ki gani,ta Muhammadu Belloti me komai Dozen,Me Injin Daf,Manal ta dinga dariya Tace Ina jiran accnt ta kashe wayar tana ta faman dariya,Fuzail ya kalleta Kawai yace sai kin haifar min Jariri ya Fado Yana sheka dariya ko? Ki ta dariya ke daya,Manal tace Wai kaji sunan Farida Me Injin Daf,Me Injin Trailer ta Belloti me komai Dozen,Dariya Fuzail yayi yace to yaro yaji Dadi sai ku takura Masa Haka kawai.

Fuzail Nan take ya turawa Farida Dubu dari Biyar,Farida sai murna ta sake Kiran Manal Tace ki bashi na Masa godiya, Fuzail yace kice Kawai na amsa Nima na gode tukwicin kwada min botiki da watsa min ruwa da tayi,Farida tace Ina jinsa to kice yayi Hakuri tana Dariya,Manal tace an Gama me Injin Daf,lokacin Fuzail ya gaji da Halin Manal tana ta bashi dariya ya koma Bedroom ya kwanta Yana so yayi bacci ta shigo,yace Dan Allah karki Zo ki hanani bacci ke hannunki baya Zama lafiya,Dariya tayi tace sai nazo Kuwa Indai ba Wani Abu Zaki bani ba Karki Zo nan ki taso min da masifa kice cikinki ciwo kwana biyu Haka kike min ace har kwana biyu kin hanani Abu shi yasa fa yau na tashi da azumi na,Manal tace au azumi kakeyi shi yasa kake avoiding Dina?

Ai Kuwa yau sai na balla shi,Dariya Fuzail yayi yace Dan Allah kiyi Hakuri kina gani kusan 5pm na kusa samun ladana,Me yasa baka fada min ba nace kayi Nafeelar azumi ne? to yau sai an bani Cassava yanzu,Manal ta hau cire kayan jikinta Fuzail yasa Pillow tare da rufe Fuskarsa,Bed din ta haura daga ita sai pant da wata Yar mayyar Vest farare,Baya ya juya da sauri tare da kankame Fuskarsa a cikin pillow,Manal ta rungumeshi ta baya suna dariya yace Zan Miki rashin mutunci, tashi yayi daga saman bed din zai gudu Manal ta cafko rigarsa tare da cikwikwiye shi duk yaso ya Bata Rai ya Mata Barazana ya kasa sai Dariya take bashi dole sai ta balla Masa azumi wai,Janyeta yayi daga jikinsa suna Dariya yace ki Bari please, Manal da gudu ta Sha gabansa tare da rungumeshi ta gaba tare da Furta Ahhhh... Dadi....fresh Cucumber tazo ga Gwagwalada....,Ba shiri Fuzail ya fara Dariya zai fece Manal ta rike shi Kam tana dage kafafu sama Wai sai ta Masa kiss, janyeta yayi ya gudu Palo ta biyoshi tace Jajjage Ambaby....ga abincin Baby Kar yazo duniya baka koshi ba gwara ka Sha abinka ya isheka tun yanzu,Ji Yayi zai canja yanayinsa hakan zai sa ta karya Masa azumi yace Dan Allah ki Bari na kusa kaiwa bakya so na samu Lada? Manal tace bakin ciki nake maka Ni ban samu ba Kai ka samu Hassadata ta motsa sai na balla shi wa yace karka fada min tun farko,Kwancinya tayi a jikinsa tare da turo Masa Kirjinta gaba,Fuzail ya tashi da sauri ya shige Toilet ya kulle sai da tace ta fasa balla masa azumin sannan ya fito ya wuce masallaci sai da ya Sha ruwa ya dawo.

Knocking ya Mata tace waye? Ki bude,Jin Muryarsa ce ta Bude tana cewa Oyoyo Ambaby,kallo ya bita da shi yanda tayi wani kyau na musamman sanye take da wata English gown iyakarta cinya me sililin Hannu marar nauyi,kunya taji yanda yake Binta da mayen kallo yace Zo ki balla min azumin yanzu ya jawota jikinsa,Manal tace sai da ka Gama Shan ruwan karka shigo Dan Allah ka koma ka siyo min kifi shi nake so naci anjima,tunda sai anjima sai muje muci a can ko? Alright ta furta tana Jin kunya yanda yake binta da kallo tace Mene ne kake kallona Haka? Kinyi kyau ne da yawa kayan sun Miki kyau sosai juya na gani,Juyawa tayi tana murmushi yaga Hips sosai da sosai Wow.....ya furta,Manal harda cewa Wayyo Rika min shi Kar ya fado....Fuzail ya fara Dariya tare da cewa kin lalace da yawa Sunshine,ai Kaine ka lalatani kasan mu irinmu Yan Kauye idan Muka tashi Bamu iya lalacewa ba,tunda a gabana kika lalace ai shike nan Haka ake so,dama abinda nake so kenan cewar Fuzail,Daukanta yayi tace me kaci? Fresh Milk Kawai sai mun fita zanci abinci,wanka ya shiga yayi ya fito yaje Sallar Isha ya dawo Yana dawowa Manal ta cakare cikin Wata doguwar rigar atamfa me aljihu da kwala,tayi kyau Yar dagwas fuskarta ta fito a babbar yarinya,Fuzail Kuwa wani danyen yardi ya saka ruwan kasa sun zuba kyau,Hannunta ya rike suka fito,wata dalleliyar motarsa Dake ajiye a Hotel din Baka Suka Shiga shike driving da Kansa Suka je yawon shakatawarsu Suka dawo,Suna shigowa bedroom kafin ya karasa sa key a Kofar sun Fara kissing din juna,Fuzail kwana biyu baiyi komai ba Manal Bata da lafiya shi yasa ya Dan barta,jikinsu rawa yake Kamar me,Kissing juna suke Kamar zasu cinye junansu,Ledojin Dake hannun Manal ta saki a kasa tare da sakalo hannayenta ta wuyan Angonta suna tsotsar juna,makalkaleshi tayi tana manne shi Kamar sun zauce,tun a palon Suka Fara raba kansu da kayan jikinsu har zuwa Bedroom,light ya kashe Kawai Manal muryarta tana rawa tace ka Sha min tana daura hannayensa a kirjinsa,tana nishin Dadi tace yau Style goma zamuyi Kuma bana son Wasa Kawai karka tsaya kana min surutu....duk da baya hayyacinsa sai da yayi dariya.

Su Falaqi sai Murna sukeyi Malam ya yarda an canja musu sunaye Falaqi ya koma Suhail,Masatura ta koma Arfat,Sa'iha ta koma Suhailat,Alhaqatu ta koma Raudah,Har a school an canja musu suna yanzu duk Wanda ya kirasu da sunansu na Baya basa yarda su amsa ma bare dole ka kirasu da sabon suna.
Hajiya Kuwa haukacewa tayi Jin Malam ya manta da ita har Yana neman auren wata bazawara,Hajiya harda kuka tana nadamar halayenta,Hakan yasa ta shiga Kiran Malam a waya Amma yaki dagawa kunyarta ta danne tazo har gida tana kuka tana Bawa Malam Hakuri,duk ta rame ta lalace,Su Arfat (Masatura) sai Malam suke bawa Hakuri Amma Malam yaki yarda,Har Farida sai data Kira waya tana rokonsa Dan Allah Malam ka yafe Mana abinda Muka maka,Malam Yayi mamakin canjawar Farida,ba karamin farin ciki ya shiga ba lallai aure Rahma ne Wai Farida ke bada Hakuri,Bai Gama mamaki ba sai da yaji tace ya Nema Mata Yafiya wajen Yaya Yazed,Malam sabo da Haka yace ya yafe musu Kuma zai dawo da Hajiya Amma sai ta tabbatar ta daina kazanta sannan Kuma dole sai ya Kara aurensa,Farida a hakan ma godiya Suka Yi.

Kudin da Fuzail ya bawa Farida da shi Suka zuba Furniture a gidan masu kyau Yan kasar Mu Nigeria amma Kalar na yan gayu,sannan Belloti ya fara aikinsa a gidan Mai,Yana ta kwazo ga rikon Amana ba zalunci, Yana samun kudi sai abinda Farida take so, Sai lokacin Farida ta fara Kiran Kawayenta su Walida tana damunsu da yaushe zasu Zo ne? Sunce zasu samu time suzo,an turo Mata ankon Rumaisa da Shukrah,tuni Belloti ya siyo Mata aka Kai dinki wajen Hadadden tela,Belloti kuwa tunda ya fara samun kudi kusan kullum sabon Kaya yake sakawa Yan daidai karfinsa yake siya kananan Kaya da manyan kaya,Haka Farida komai ya gani idan ya Masa sai ya siyo mata.
Belloti Yana Office a gidan Mai wata Igbo Tasha kananan Kaya sun Mata kyau wata Yar gayu da ita ta Parker rantsatsiyar motarta zata Sha Mai Belloti ya hangota yaga kayan sun Masa kyau,Fitowa Belloti yayi har wajenta da Dan turancinsa ya tambayeta Dan Allah Ina kika siyi kayan Nan? Murmushi tayi tace ai a sabon Gari ta siya Botique din kanwarta ta bashi address din wajen,Belloti sai yaje can ya siyowa Faridansa harda wasu kalolin Yana komawa gida da su ya shiga 8pm,ya Iske Farcy Tasha gayu cikin wani Bumshort da wata Riga me sililin Hannu red and black,gashiin Nan yasha gyara,tayi wani fresh,kowa ya kalli Farida yasan tana Jin Dadi Yanzu tayi wani kyau,Belloti a gabanta ya tsaya tare da rike Haba ya Kura Mata idanuwa ya tsaya kamar gunki,Dariya ya Bawa Farida tace Baby Mene Haka Kamar gunki,Bai kulata ba yaci gaba da Kallonsa Kuma Bai motsa ba,gida yasha gyara sai kamshi yake ta ko Ina,Farida Ana kallo a wata plasma tv Yar katuwa Haka,mikewa tayi tace Bari na kawo maka ruwa,Belloti ya washe Baki yabi Farida da kallo.

Farida tana farin ciki cikin Jin Dadi ta birge mijinta ta fara tafiya ta Jan hankali tana wani girgiza jiki,Belloti har ta kawo Masa lafiyayyen zobo me sanyi Bai Sani ba sai data ce Baby....kinyi kyau Me Injin Roka,ya karba tare da furta thanks Yana Sha a wani glass cup,sai da ya sanyaya makoshinsa sannan Farida ta jashi daki tace muje ayi wanka,Belloti ya rungumeta yace sauri zanyi yunwa nake ji,Farida tace ga girki can me shegen Dadi na maka abinda kafi so shi na maka,tayashi tayi ya cire kayansa sannan ya Shiga wanka Tace nazo na tayaka? No karki Bata min kwalliyar Mana yanzu Zan fito.
Ko da Belloti ya fara wanka gaba Daya hankalinsa Yana Kan Faridansa.
Tunda Belloti ya fara samun kudi yake turawa Iyayensa kudi Wanda zasu siyi kayan abinci,sai haushin Farida suke ji sun San tana can tana karbewa Belloti kudi,ya auri Yar bariki,Goggo tace Bari na samu lokaci da kaina zanje Birnin na gani da Ido na,ya auro karuwa gaba Daya ya haukace a kanta wallahi bazan yarda ba.

Lokaci Yana ja Yayinda auren Tanko yazo gaf Saura sati Daya sai lokacin Ummi ta damu Fuzail ya dawo zata tafi ita amma tana so taga surukarta sai lokacin Fuzail Suka dawo gidan Sarki,sunyi wani kyau da haske suna ta hutawa,Ummi sai wani ji takeyi da Manal,ba dama taga Manal a kitchen sai ta dinga fada Wai cikinta Kar a samu matsala,Haka Yan gidan kowa kaunar Manal yakeyi sai Wanda ba a rasa ba sabo da duk yanda ka Kai sai ka samu makiya ba yanda za ayi ace kowa sai ya soka,Sabo da Haka akwai Wanda Basu damu damu da wata Manal ba a gidan,Sama sama ake Yi da su ba yabo ba fallasa musamman Yan bangaren Amarya.
Yau 9pm Manal tana sashenta Ummi ta shigo ta samu Manal tana Gyara kitchen ta Gama girki, Ummi tace bakya Jin magana Manal, me Yaron ciki Lallabawa akeyi kina ganin kamar ba Wani Abu bane wallahi sai ki samu matsala,Dan Allah ki kyale jikana yazo duniya lafiya ku Yara dama Sai Hakuri Sam Baku San ciwon jikinku ba,Dariya Manal tayi tana mamakin Ummi yanda ta damu da ita da Yaron cikinta ta hanata sakewa baza tayi komai ba, Inshaallah na daina Ummi Zan kiyaye,Haka kike cewa kullum Kuma ki dinga rage karfin ac Kar sanyi ya Kama shi yazo ba lafiya,Manal tana Dariya a ranta tace to,Ummi yanzu ta Gama takura musu ta dawo Kan cikin Manal da Jariri.

Ummi ta sake cewa girkin me kike Yi Kuma? Prince ne yace na Masa girki yanzu zai dawo,Ke sai ki biye masa duk ga Yan Aiki nan ko Ina Iyayin mazan zamani Zaki biyewa,Manal tace Ummi fada zaiyi fa ai ban Isa naki yin girkin Nan ba da na shiga Uku Yau,Ummi tace ku maza suke zarewa Ido Iyayin Yaron Nan yayi yawa Bari ya dawo mutum Yana da juna biyu baza a barshi ya sake ba,Fuzail ne ya shigo Yana Jin maganganun su Ummi me suke cewa Yace Ummi zuga min Mata Kuma zakiyi ta rainani? Fuzail na fuskanci ka rainani yanzu ban hanaka sa Yarinyar Nan Aiki ba? Kai Ummi wani Aiki tayi wannan so nake ma taje ta gyara min samana,Ummi ta kalleshi tare da cewa a'a ka barta ta huta ni sai na gyara maka saman naka tunda baka son Yan Aiki,Manal tana Jin Dadi a ranta,Fuzail Dan ya Kori Ummi ya fara kashewa Manal Ido Daya Yana Mata wani Signa da gira da Ido,ba shiri Ummi tayi tafiyarta tasan Dan nata ba kunya ce da shi ba.

Bikin Ameer Rana Daya ne Dana Tanko sai shiri suke Yi ba Zama,Wannan karon Islaha taga lefe na gaske akwati Takwas aka Mata Kaya masu tsada,Itama na Matar Ameer Akwati goma Sha hudu,duk abinda za ayi anyi komai na auren Fuzail ne yayi musu Tanko da Ameer duk mutanensa ne,Sabo da abin Alkhairi da Tanko ya yiwa Belloti shi yasa Maimartaba ya bashi

Please Login or Register in order to submit comment