Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tun daga ranar Belloti Bai sake zancen Manal ba kusan kullum sai yaje gidan su Farida sabo da ya ganta su danyi Hira,Ana Haka har biki ya rage Saura kwana biyu,duk abinda ake na aure anyiwa Farida shi dai dai gwargwado Kuwa Akwati biyar Fuzail ya hadawa Tanko komai anyi a mutunce,Ana gobe daurin aure Dangin Malam da Dangin Hajiya da su Annatu Suka cika gida Ana Shan shagali Banda Amarya da Mamanta,Farida kwana take kuka,Hajiya ta rasa inda zata sa kanta ta rasa me zata Yi a fasa auren gashi tasan abinda tayi,a ranar Ana gobe aure cikin mutane lokacin Malam da Yan Uwansa maza sun shigo Yazed suna ta Hira da Annatu da Dangi Hajiya ta fito tana Kururuwa Haka Kawai,Farida dama tana daki kukan take Hajiya ta cakumi Malam wallahi baka Isa ba kayiwa yata auren dole ba,dama ai ba sonsa take ba yazo da abin arziki ne nayi Masa asiri,asiri na muku wallahi wajen Malam naje azo aje Wajensa kuji Ni Nace ayiwa Tanko asiri lokacin munyi zaton me kudi ne Ashe Dan karya ne,kaima Baki na rufe maka nace a saka lallai ka daura auren wallahi Duk nice na jawo Hajiya ta zube kasa tana kuka,Malam ya bita ya kwada Mata Mari yafi biyar,ya rufeta da duka Yana Allah ya Isa tsakanina dake,Yan Uwansa ne Suka rikeshi mutane dangi Suka fito kowa Yana tofa albarkacin bakinsa Ana tsinewa Hajiya,Malam tunani ya fada yace wallahi duk abinda kayi sai an maka Nima nayiwa wasu gashi Ashe Ana ta Yi min ban sani ba,an cutar Dani an cutar da yarana kamar yanda na cutar Dana wasu,Allah na tuba Bai kamata ma naji haushi ba Amma wannan malamin sai an tona Masa asiri.

Malam murmushin bacin Rai yayi bayan ya Gama zancen zucinsa yace muje ki kaini wajen malamin,Keyar Hajiya aka tasa da yayyen Malam su Uku aka tafi da Yan Sanda tare da Yan jarida,Malam Dan Haru aka Iske a dakinsa Yana kwance Yana Jan carbi Kamar mutumin kirki,Hajiya ta Shiga tare da cewa munafuki tashi duk Kaine ka jawo dubunka ta cika.
Malam Dan Haru mikewa yayi yace wlh sai dai dubunmu ta cika da ke,Yan Sanda Tsawa Suka daka Masa Nan take Malam Dan Haru yace zanyi bayani,Yan jarida suna dauka ya bada labarin duk irin asirin da Hajiya tayi da mutanen da tayiwa da tun lokacin da Malam shima Yana malaminsa,Malam sai kuka yasan duk abinda yayi ne ake masa,Jin yanda Manal ma ba a kyaleta ba Yazed Ashe duk su Suka hanashi Rawar Gaban hantsi,suka Kori Annatu sannan shima aka Yi Masa,Bai damu da wannan ba sabo da idan ya tuna shima ya cutar da wasu da yawan gaske,a ransa yace dole ya fara Neman Wanda ya sani su yafe Masa, Kallon Hajiya yayi yasan shi ya jama Kansa shi yasa aka jarabce shi,Kuma tun farko laifinsa ne shi ya dinga wulakanta su Hajiya shi yasa har ta koyi zuwa gidan Malam,Dan ya koya Mata darasi yace idan an wuce da Malam kurkuku kema kiyi gidanku na sakeki saki Daya.
Hajiya ta Fadi kasa tana Malam kayi min Rai Malam na tuba Hajiya tana kururuwa,Malam yace aure Kuma da Farida da Tanko ba fashi sai in Tanko ne ya fasa.

Tuni Yan Sanda sukayi gaba da Malam Dan Haru tare da cewa Hajiya kema ki Zama cikin shiri zamu nemeki,Yan Jarida zasu magana da Hajiya ta fisge abar daukar tayi jifa da ita ta tashi ta tafi gidan yayanta tana kurma Ihu.
Gaba daya Gidan biki ba Dadi,Farida tana Jin labarin komai wani kukan ya karu a Kan na Baya,gashi ance aure ba fashi, Ranar daurin aure da safe aka kawo Manal a wasu Shegun motoci Ana Mata kirari ga mace Daya me take Mata Baya da ita Suka shiga gidan,wani irin Material Manal ta zuba na Gaban kwatance sai kallonta akeyi Jakarta ma rike Mata aka Yi tafi karfin ta rike,Jikin Annatu ta fada su Hajiya Sharifa duk Suka saki Baki,Tace nahigai yanzu Kece Haka Manal kin Kara girma kinyi kiba kinyi kyau Haka kalli Fatarki Manal Kamar jini zai fito gaskiya angonki ya iya kiwo,larai tace yo ba Dole ba irin wannan koriyar Hinkafa da suke ci da yaluwa harda da ja,ga nama iri iri,Manal tana Dariya tace tare muke da shi fa,Sharifa da sauri Tace Allah? Iyye Wato bazai Zo ma ya Gaida surukansa ba ai Hike Nan ya kyauta ah nace kice Masa ya kyauta,suna Haka sai ga Fuzail kayansa ruwan kwai irin na Manal Amma nasa shadda,Nan take Sharifa tace anko sukayi ahe lobayya,Fuzail yaji Sanda tayi Gulmar ya fuske,gaba Daya kamshi ya turare su,Durkusawa yayi tare da gaisar da su suka amsa da Fara'a sai kunyarsa suke ji Wai suruki,Hajiya Sharifa tace ah Yasin abinku Ras duk Kun samu nutsuwa kaima kibar ahe kayita,Dariya Fuzail yayi kawai Annatu ta wani boye fuskarta Wai kunya,Masu take Masa baya suna daga kofa suna jiransa,Yana Gaida su ya Mike tare da riko Hannun Manal a gabansu,kunya ta Kama su Annatu ji suke Kamar su nutse suna ji yace sai karfe nawa zanzo daukanki? ,kwace Hannunta tayi Tace ba kwana zanyi ba na ebo kaya fa,Haka Mukayi Dake? Shike Nan Ni bazan ga Uwata ba,Baki Annatu ta bige Mata Tace biyar na yamma na yi azo a tafi da ita me zata Yi a Nan biki yau za ayi a Gama kwanan me Zaki Yi ga Baki ga Hanci,yaushe zaku koma? Sharifa tace jibi Inshaallah da Sassafe,yace to ba damuwa Allah ya kaimu.

Yana fita Ya wuce wajen daurin aure,Yayin da Yan Sanda tun jiya da daddare suka sa Malam Dan Haru ya karya asiri Nan take,tun a daren Tanko yake Jin haushin Kansa me yasa ma zai auri wacce Bata kaunarsa,kwanan bakin ciki Tanko yayi Yana tuna irin wulakancin da Farida ta Masa,Ranar daurin auren ma da kyar ya shirya ya fito jikinsa ba kwari Haka suka Zo da su Sani,Kowa ya hallara tare da wakilan ango Dana Amarya da Kuma wakilin Maimartaba Sarki Abban Ameer,Haka Kawai Tanko a wajen Ana Shirin Fara khuduba yace a tsaya na fasa Kar a daura na fasa wallahi tunda Bata kaunata bana sonta nima,me zakayi da Wanda baya sonka,duk Wanda ya nuna Bai kaunarka Bai kamata Kai kaci gaba da sonsa ba ko ta karfi ka rabu da shi,ko anyi auren Nan ba inda zai je a Bata Wanda take so ni Tanko na janye Allah ya kawo Mata Dangote ta Aura.

Malam shima Bai matsa ba Ana ta mamaki dama Amaryar Bata so,Fuzail yace Tanko kalau kake Kuwa? Tanko yace kalau nake Ranka ya Dade ayi min afwa wallahi na fasa har abada bana sonta Kamar yanda Bata kaunata,Abban Ameer me saukin Kai yace to yanzu ya za ayi Belloti Yana kusa yace Ni Ina sonta dama muna gaisawa idan tana so na a daura Dani,Tanko Yace ni Kuma duk abinda na kashe na bar maka a matsayin kaine kayi Sadaki Kawai zaka biya,har lefen na bar maka,Amma ba ita na barwa ba Kai na Bawa bawan Allah sabo Ni idan mutum Bai kaunata kwandalata bazai ci ba,Belloti yace Nima Haka nake bawan Allah zuciya ce Dani,sai da akayi Dariya a wajen, Malam da Kansa ya Nemo Farida har dakinta yace ki daina kuka ki godewa Allah Tanko yace ya fasa da kansa,Ihu Farida ta saki na murna,Malam yace ga Belloti Dan garin su Manal Kinga wannan mun San asalinsa sosai duk da cewa yanzu halin mutum ake so a duba ba gidansu ba ya kika gani? Farida ta rufe Ido tace gwara koma waye Malam,Ki daina cewa gwara Koma waye Haka zakice Allah yasa Haka shine mafi alkhairi,Alkhairi Allah ake Nema Farida,Farida Tace to tana murna a ranta tana zagin Tanko.
Komawa Malam Yayi akace Belloti ya kawo Sadaki,Tanko yace Nawa aka yanke Zan biya Masa,Fuzail ya kalli Tanko Yana mamaki,Dan kudin Tanko da ya Tara ragowar su kenan dubu Hamsim Kuma dubu Hamsim aka yanke Nan take Tanko ya zaro ya biyawa Belloti,Belloti ya dinga Mamaki abinda Tanko yayi ya girgiza kowa sannan ya birge mutane wannan yasa kowa yaji kaunar Tanko a ransa,Tanko Farin jini yayi aka dinga Kallonsa Ana yaba masa,Baki dubu sai Allah San Barka ake Masa,Belloti ba walliyyai yace Kar a damu zai zaba a Nan Baida matsala a gidansu,Malam duk da Haka sai da Yaja Belloti gefe yaji sana'arsa da inda gidansa yake, sannan yace bazai yuwu ba sai Dangin Belloti sun sani ko a waya ne.

Belloti sai ranar ya lalubi Babarsa yasan itace zata Goya Masa baya,tunda taji Danta yana nan da Rai murna tasa Tace yaushe zaka dawo yace Gwaggo sai Kun Amince an daura min aure Haka ya Dan Bata labari a takaice,murna yasa Gwaggo ta Kira Baban Belloti shima sabo da Murna yace Matukar Belloti zai dawo Kuma yaji Baban Manal ne ya bashi 'ya ai sai godiya yace a daura a wakilce su.
Malam hankalinsa ya kwanta
Nan Kuma aka nadawa Belloti wakilansa tare da Daura Auren Farida da Muhammad Bello Wato Belloti,Belloti ya tsinci dami a kala a banza yazo daga sama duk wannan jarabar fafutukar da Farida keyi Ashe Belloti ne,Belloti burinsa ya cika ya samu Yar birni wayayya me iya love hirarsu da sukeyi kullum a Majalisa da su Lawi kenan.

Belloti ya Kira su Lawi a waya yace to fa Ni nayi gaba Allah ya amsa ba Manal din ma Allah ya bani ba Yayarta na samu,shi yasa Idan zaka roki Allah ka rokeshi da Babban masaki sai ya bani Yayar Manal ma wacce tafi Manal wayewa sai dai Ita ba wata kyakyawa bace gata Nan dai ba laifi sai iya gayu,Lawi yace Yar Mai ce? Belloti yace tabbas akwai shiga kanti,ka shiga Uku Belloti siyen manta kadai sai ya karya ma jari,Belloti yace ba komai akan ta zauna min a baka gwara ko na kanti ne farin ta siya ba matsala Ni tayi min,Malam Dan Haru kuwa tuni an shigar da shi Kotu zata yanke Masa hukunci,Yan biki maza da Mata labari ya watsu Ana ta mamaki Ana yabawa Tanko,Manal ta dinga mamaki Wai Belloti Bata San Bellotinta ya goge ba,bayan mutane sun watse Fuzail ya kirata a waya yace tazo waje zai tafi,Manal tana fita taga Ango Belloti Dake Bai San za a daura Masa aure ba da kananan Kaya yazo wajen yasha shegen black jean dinsa me Dan kyau,da kyar ta Gane shi,Yana ganin Manal sai da zuciyarsa ta kusa bugawa sabo da tsananin kyan da tayi,da ganin Yanda ta wani goge ta waye ta zuba kyau ga Kaya na nunawa sarki,tun a Nan yasan Manal tafi karfinsa,Fuzail ya kalla ya sake kallo da motoci da masu take Masa baya ga Dogarai,Nan Belloti ya dinga kallon Naira da Mulki.

Manal ce ta Masa Magana Belloti Ango Kaine tayi Wajensa sai suka koma Fulatanci suna ta yaren,Kishi ya Kama Fuzail yaji labari ance tsohon Saurayin Manal ne,sai ya Shiga mota Kawai yayi tafiyarsa Yana ta Fushi zuciyarsa tana Jin zafi yanzu shike Nan tana can tana yiwa Belloti murmushinta me kyau Wanda shi ya kamata ya kalla,Manal sai juyowa tayi taga ya tafi tuni,sai da suka Sha Hira da Belloti sannan ta shiga gida ta Iske Farida cikin kayan lefenta ta Sha lace brown and milk,tayi kyau Tace Manal Dj za a kawo fa Yanzu su Walida Kawayena zasu Zo ku shirya tikar rawa,Murmushi Manal tayi Tace Farida ki rage murnar Nan kiyi Addua sannan tam,da Masifa Farida ta yo Kan Manal da abani Tanko gwara na auri ko waye wallahi,Wannan Bellotin yafi birgeni sau dubu akan Tanko,dama ai tsohon saurayinki ne nasan kishi kike,Waiyazubillah da Auren Nawa? Me zanyi da Belloti Ni Kam da Ina sonsa da tun a Kauye ban aure shi ba,Belloti shine Silar gudowa ta Birni amma Allah ya Baki Hakuri.
Farida tana shafa jambaki Tace Ameen yanzu zai kaini wajen Hajiya naji halin da take ciki,su Walida zasu Zo ki kula da su Dan Uwarki Saura ki tsaya mulki ke ga matar Yarima to su Walida ne kin San halin Kawayena gogeki zasu Yi,Manal Tace kutmar wa suka Isa su goge wallahi da sun jama kansu,Mrs Fuzail Guda ai kallo na ma sukayi Basu Isa ko kallon banza su min ba,Ance Miki Manal din da ce me Awara? Ko yanzu na Zo daga Kauye? Farida ta girgiza Kai Naga yanzu kin sake fetsarewa wallahi Zaki San Ni ba Sa'arki bace,Manal Tace ke kin Sanni tun a baya duka nake Miki yanzu ma badan Allah yasa Ina tsoro ko Ina da ciki ba Hmmm...

Dariya Farida tayi Tace to Manal munji kina da cikin Fuzail sai me? Anji kin auri me kudi so what? Farida tana fita motar Belloti ta shiga wacce Bata San ta Uche ba ce ya figeta sai wajen Hajiya wacce ta rame lokaci Guda sai Ido zuru zuru kamar tayi zawon wata Guda,Taga Faridanta ta Sha wanka a sanyaye Tace An daura da Tanko ko? Farida tace a'a da wannan Bellon aka Daura Dan gayu Wanda yazo gidanmu Wanda jiya Muka zo da shi ya kawo Ni da dare? Hajiya Tace Alhmdllh gwara shi,Ina su Falaqi su Sa'iha? Farida Tace sun tafi Wai gidan kwalliya Falaqi Yana wajen Yaya Yazed.

Yar Hira sukayi sannan Farida ta dawo Belloti ya fisgota a mota kamar zai tashi gari faaaaaa duk Wanda ya ganshi da gudu yake kaucewa wuta Kawai yake shararawa shi ga me Amarya, ya kalli Farida yace akwai chasu a Kano idan Muka koma,Farida ta saki murmushi tana kallon Uwar Sumar Belloti daya Tara ta Yan Fulani me kyau baka me santsi,Kida Belloti ya ware a motarsa duk inda Suka wuce Ana Jin kidan sosai wakar Amarya da ango tana tashi,Belloti har sitiyari yake saki ya Dan Yi rawa da kirji yaci gaba da tuki, Belloti an waye yace muje Asibiti ayi Mana test sabo da tsaro,Haka ya kaisu wani lab aka musu gwajin aure Allah yasa komai lafiya kowa lafiya yake,Belloti yace yawwa dai dai kenan.
Gobe zamu ware da ke tunda ba a shirya bikin ba daga Ni sai ke sai uban gidana zamu wuce Kano,Farida Tace kano ta dabo tumbin giwa tana rausaya Kai.











AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭



DEDICATED TO DUNIYATA AAMNA FANS GP






76-80






Official



By
AsmaBaffa






Page naki ne ta wajena

HABEEBATULKHAEER


Jinjina ga
GIDAN HAUSA NOVELS







Belloti Yana sauke ta ya bada kudin Dj yace matsalar Ni bana saka manyan Kaya yanzu duk da kana Nan Kaya na shigo garin Nan,a Kira me Dj na cashe Iya rabona zanje na dawo da Yamma,Farida tana Murmushi tace a dawo lafiya ta Balle murfin mota ta fice shima ya Fisgi mota ya Kara gaba,Tana shiga ciki ta Iske Kawayenta da yawa su Rumaisa,Walida gasu Nan da yawa sunfi su Goma Sha biyar wasu ma suna Kan Hanya,ita dai Manal Shukrah Kawai ta gayyato sauran Yan makarantar tasu Bata gayyaci kowa ba,su Walida ne Suka ja Amarya saloon aka gyara Mata gashinta sosai, Yan Magungunan Mata Suka siyo Mata da wasu abubuwan na gyaran jiki Wanda zata tafi da su Yan kadan kasancewar Basu shirya komai ba sakamakon Tanko ne Angon,Amma yanzu tunda Belloti ne yafi Dama dama zasu shirya ko Yaya ne.

Zuwa 2pm Suka dawo tare da sake sabon wanka Ana Jiran Masu Dj zasu Fara,suna ta daukan wanka wasu suna shigowa kuma sun Sha gayu,Su Annatu ne Suka Yi shinkafa da Miya sai Abincin da Yazed ya bada a wani Restaurant Ayo,aka kawo Fried rice lafiyayya da Pepper chicken ga lemuka Nan da ruwa sai ka gaji,Manal wanka ta sake Yi tare da Shafa lotion dinta me kamshi,Walida ta daga lotion din Jin matsiyacin kamshinsa Tace Nawa kika siyi wannan? Manal Wai Prince Charming ne ya siya ba Ni ba,Baki su Walida Suka tabe sabo da dama Mata Haka suke sun tsani a fisu,duk wacce kaji Mata suna Zaginta ko Ana tabe Mata Baki to tafisu ba yanda zasu Yi sai a dinga Mata gani gani,Rumaisa ce Tace naganshi ana talla dubu ashirin da biyar, Farida yatsina Fuska tayi tana taje gashinta Walida tace Farida ya Naga gashin naki Yana ta Kara tsayi ne? Tace sai ma yaji sinadarin jikin Muhammad,Wai harda canja Masa suna baza ace Bello ba.

Dariya Manal tayi da sigar wasa Tace Zaki fada musu ne sai Daren farko Allah ya kaimu,Farida da masifa tace Wai Ina ruwana da harkarki? Ina magana da Kawayena kina tsoma min Baki ni kina nufin Ni yarinya ce Kenan fuuuu Farida tayi waje tare da Kiran Yazed Tace ka rabani da Manal wallahi a Gaban Kawayena zata dinga ce min Yarinya tana fada min Maganar data ga dama Ni sa'arta ce, Manal Bata Saka kayanta ba Tana kwance tana tunanin mijinta me yasa ya tafiyarsa dazu oho Bata sani ba,ta Kira wayarsa yaki dagawa,Muryar Yazed taji ya kwala Mata kira,Kasancewar ba Kaya a jikinta Hijab ta saka ta fita kawayen Farida suna wani tabe Baki Walida tace wlh Yarinyar Nan iyayinta ya baci Yar Dakikiya Wai Dan tana auren Prince Wai Charming Prince ko Prince Charming jaka,Rumaisa tace Banga laifinta ba ai abin Alfahari ne wlh ko nice abinda yafi Haka ma zanyi waye Bai son Harkar Hutu,Zugar Yan Rawar Solo ne Suka zo Mata suna da yawa Shegu ne wajen taka rawa,a Haka Kamar na kirki,Dj dinma nasu ne da abinsu Suka zo.

Yazed Kuwa Hararar Manal yayi yace kin San Allah yanzu sai na sa a maida ki gida so kike Ana zaune lafiya ki jawo rigima bana son Iskanci fa,Sa'arki ce a mutane Zaki dinga kunyatata,Manal tace Ni wallahi ba abinda nace Wasa nayi Mata ma Allah Yaya,Wasan dole ne? Tunda Bata so ta fada Miki ki hakura Mana,Ko Wasa kayi da mutum kaga baya so ai sai ka hakura,ki shiga hankalinki ai ba Sa'arki bace,Farida ta Mata gwalo tace Wai Dan ta rigani Aure shine take ganin Kamar kanmu Daya Ni zata gayawa duniya matar da yaushe ma ta waye yaushe ma ta shigo birni Kawai Dan ta auri Prince sai ta rainani,Yazed yace kiyi Hakuri to ke Kuma kika sake Mata abinda Bata so wlh kin Gama bikin nan,Manal tace shike Nan ya wuce Indai nice baza a sake ba,Farida Tace sai kije ki zubawa Kawayena abinci Kuma Banda waccen girkin na mutan Kauye Wanda Yaya ya kawo shi za a basu,Manal Tace Ni fa wallahi ba dadin jikina nake ji ba,Kuma ma Ni akwai abinda ke damuna kina kallo Fuzail yayi Fushi yayi tafiyarsa na rasa dalili,Farida tace Wai ke Baki da Aiki sai zancen Fuzail...Fuzail...Yarima...prince haba uban waye yace ki tsaya da Mijin wata ba naki ba,Dariya Manal tayi Tace Kai Aunty Farida Ko Kara babu,Ke wallahi ki kiyayi tsayawa da Bello yawwa karki jawo min,kije ki Basu abinci ni ba ruwana da wani mijinki Yana Fushi,ya shekara Yana Yi,Manal tace karki jawo naki zubawa,da Kuwa Na Kai karar ki wajen Yaya Yazed wlh yaci Ubanki.

Manal Cooler Kawai tasa aka ajiye musu da komai har ruwa da lemuka Suka ce sai an fara cashewa zasu ci a barshi,ita Manal Pepper chicken din ta zuba a plate Kawai tana ci da lemonta,Farida Tace kiyi sauri rawa za ayi fa,Manal Tace Rufa min asiri ni yanzu Fuzail ya kamani Ina rawa Gaban karti ai Naga ta kaina....ke dalla Yar Kauye ki zauna ki tsufa akan kinyi aure,Shukrah da shigowarta kenan itama taci gayu tace Manal dole fa muyi rawa,Gane min Hanya Yar gari.
Manal Dakin su Annatu ta koma zata shirya ta sake kwanciya kusa da Annatu,Hajiya Sharifa tace ke Yar Nan ko ciki ne da ita ne Alqur'an,Naga tunda tazo sai kwanciya ta kwanta can Hyaraf ta tahi can Ni ko gidan Hutu ne ya lalata ki an Saba da Hawa gado kullum? Dole ta koyi bacci ai wannan ac Haka ko Ina sai sanyin Dadi ga gado
Sabin by Sabin (Seven)
Annatu tana jinsu suna ta tsokanar Manal ta musu shuru.

Mikewa Manal tayi ta zauna Tace Annatu Ina Saniya ta? Ke karki dameni da jarabar Saniya bakya mantawa da ita tana can ta Haifi Yan biyu,Manal ta dinga Murna Tace Tinkiyata fa? Tsohon ciki ne da ita,Kaza ta fa? Idan Yaran sun girma ki dinga kamawa kina yanka su kici kinji Anna,to naji tashi ki koma wajen Yan matan ku can,Shiryawa Manal tayi ta saka wani Sabon lace dark green and Golden tayi kyau sosai Ana ganinta an San akwai Naira,Hajiya Sharifa da Bata gani tayi Shuru tace Uhmm matan manya a saka wannan a fita a saka wancen wannan kyau Haka dole Angon naki ya zauce to anga Jar fata jiki Kamar jini ya fito ba dole ba,hi yasa duk Rawar jikin Nan da yake akanmu nasan ba banza ba,kafarki kafarsa kullum nanai nanai da ke Yana Rawar jiki Unguwar ma baza a barki ki sake ba,Dahara tace Banga laifinsa ba,Yaran zamanin Nan dama Yaya bare Kuma an samu dama,Allah Ni kunya ma yake bani cewar Wata Hindatu tace Yana gaihe mu amma Idonsa Yana kanta Kai wannan Surukin namu,Wani kallo da yake mata Ni ban taba ganin irinsa ba a duniya sai yau hyu'umin kuma ya iya cewar Hajiya Sharifa,Tace yo aike Hindatu Baki hya kallo ba sai ranar da aka Daura Masa aure da Manal Munga bidiri ni Hyarifatu nace cab.

Suna ta faman Yi Manal tana jinsu tace surukinku ne dai,Wlh Kuwa cewar Dahara,Kida ne ya fara tashi Yan Solo tuni sun Fara taka rawa ta fitsara Ana ta Shan kallo Mata da maza Yara da maza gasu Nan Yan solo sun ja Hankalin kartai,sai liki ake Ana zuba kudin ka rantse dama an shiryi abin,Amarya tana Shan liki,Yahaya tsohon abokinta shima suna wajen da abokansa suna ta cashewa da su ake iskancin Rawar,Yan matasa da su sunyi kicin kicin duk mutanen Farida ne,Hajiya ce ta dakko wanka cikin Shadda wata sea Blue dinkin manyan mata ,idan kunga Hajiya ba Wanda zai Gane ta,ta zuba Uban kyau ta Sha make up ta gaske harda Eyelashes aka sa Mata Kamar Budurwa Haka ta dawo dama Hajiya Yan Birni,Takalminta Kalar zaren dinkin dark pink da mayafinta har Jakarta me tsada dama sabo da bikin ta dinka,Malam can Yana Sallamar Baki yaga Hajiya ta zuba kyau Hajiya ba karya Yar birni ce ba a barinta a baya musamman a biki,Malam ya hadiyii yawu tare da sharewa Kamar Bai ganta ba,Su Walida Suka Yanyame Hajiya suna tafi suna ai sai Hajiya wallahi kinyi Kyau,Hajiya tana murmushi Tace Ina ta godiya ba adadi,Rumaisa tace Hajiya kinyi wlh, Hajiya Tace na gode ta wajena,dalilin Farida duk suna Dan Wasa da Hajiya kadan kadan,Hajiya Kamar kawarsu Haka suke Abu da ita,Walida ta rike Hannun Hajiya tace Hajiya shiga mu zuba liki,ciki aka shigar da Hajiya Ana ragargazar uban kida, Suka saka Hajiya a tsakiya Suka zagayeta suna zagawa suna cashewa ana liki Hajiya tana musu suna Mata itama,Hajiya tace ku fita na kwaso Shoki Nima yau sai na Rama wallahi,Manal Bata San ramuwa za ayi ba ta taho da sauri da kudinta Yan dari biyu biyu zata Yi liki,lokacin an tsaya da kida, Hajiya ita kadai a fili ta kalli Dj da karfi Tace Music......sai aka saki kida Hajiya nata Shokin ma har kasa ta tsuguna ta kwarfo shi itama dai dai Manal ta fara Mata liki tana Dariya Hajiya tana Ebowa ta juyewa Manal a tsakiyar kanta har da dangwara tafin Hannunta sosai a tsakiyar Kan Manal sai da Daurin dan kwalin Manal ya ware kadan Amma ba cire ba,Hajiya ta Kama bakin mayafinta ta sake kwaso Shokin da shi ta watsawa Manal,aka saki Ihu da dariya,Manal ta Gane Wato Hajiya ita a Mayafi ma zata kwaso

Please Login or Register in order to submit comment