Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kar ya Zo Mana Kai baka San Hanya ba ko a taxi baza kazo ba? Fuzail yace ba ruwana da Fitowa a taxi Haka Kawai Na sake Haduwa da Dogarai Nasha Bulalai,Dariya sukayi,Ameer Yana jinsu yace wallahi ka fadawa Manal na ji ta Kuma Zan rama tunda Bata gode min ba,Kuma wallahi ka fito mu tafi wannan ai Iskanci ne ka ajiyeni a waje aikin banza Allah ka sake na tafi Ni kadai sai na fadawa Ummi kana Nan gidan.

Au Haka ka koma? Cewar Manal,Ameer yace sosai ma Dan Iskanci sai ya ajiye Ni a mota,Manal harda marairaicewa kayi Hakuri zai fito ne kaji Dan Ameeru gashi Nan zuwa abinci yake ci Indomie nake dafa Masa yanzu ma daga kitchen na fito ka ganni,Ameer Dariya ya shiga shekawa yace Ni zaku rainawa hankali Harda ke Manal Ina ganinki kamila to na bashi 2mnt Idan Bai fito ba Kawai na tafi,Ina laifin minti biyar ma Haba Yaya Ameer cewar Manal,Kina cinye lokacinku ne a Wayar nan ya kashe wayarsa.

Fuzail yace Dan iskan yaro ne Ameer sai fa ya tafi ya rainani,Manal ta jawo rigarta zata maida ya fisge rigar tare da Hugging nata a jikinsa tsam suka dauki kusan 10mnt a haka,Manal a hankali tace dama nayi bacci a Haka tana lumshe Ido,Fuskarsa ya goga a wuyanta me laushi sannan ya goga gefen Fuskarsa a tata tare da sake kankameta,Ji yayi Yana Neman yin bacci me Dadi,bakinta ya laluba Yana kissing Manal ta Shiga tayashi Bata sani ba,Yaji wani dadi yace har kin koyi darasin? a kunyace tana murmushi tace ai Brain ce Dani akwai kai ta bature yace Gifted,to ni Gifted ce,kin fiye kunya da shegen Pretending amma Zan canjaki zanyi gyara a kanki da yawa,Dariya sukayi da Kansa ya saka mata Yar rigarta ya wani rufe Ido,Mene na rufe idon Kuma? ta tambaye shi,yace idan na kalli manyan Breast din Nan nawa to bazan iya tafiya ba shi yasa na rufe Ido na, na tabbata yau bazan iya bacci ba Sunshine.

Manal tace Sunana Sunshine yanzu? Fuzail yace Yeah Yana Daukanta Suka Mike tare Tace Tab Ni Kuwa ba yanzu Zan sa ma suna ba sai Naga kamun ludayinka sabo da Namiji ba Dan goyo bane bazai yuwu ba sai na Haihu Naga idan baka canja ba,Fuzail Bai Gane Hausar ba yace Namiji ma Ana goyashi Mana ai ba mace kadai Ana Goya ba,Manal sai da ta ganar dashi me ake nufi, Ido Fuzail ya zaro yace har sai kin Haihu duk soyayyar da zamu Fara kwasa baza a min suna ba sai an Haihu? Manal tace ae sai nagani idan wajen Zamana ne to Haka Kawai a sa muku suna ku juyawa mutum baya inzo Ina Jin haushi Ina mayar maka sunanka daga Sweety ka koma Malam kaima,Dariya Fuzail ya dinga Yi da Yar guntuwar hausarsa yace babu Wanda Yana Isa ya ce zai kirani da Malam,Manal Tace dama ku Yan sarauta Kun gaji aure aure sai kace ayu Haka kuke dama naji Yan school dinmu jiya suna cewa mijinki dan sarki ne?kin Shiga uku da kishiyoyi gasu Sex machine ne su.

Wannan School naku baiyi ba Yan ajinku munafukai bazan sake musu kyauta ba tunda lalata min tunanin Mata sukeyi na daina mutunci da su...Ameer ne ya sake Kira yace na rantse da Allah ka sake minti biyu baka fito ba na tafi kawai,Hijab Manal ta saka ta rakashi har Kofar gida Hannunsa cikin nata Tace Bye gobe kazo mu tafi makaranta Indai baka zo ba bazanje ba na fada maka,zanzo Mana cewar Fuzail...Ameer ne ya sake Danna Horn da karfin gaske sannan Fuzail yaje ya shiga mota ,Ameer ya Fisgi mota Yana bala'i yanzu da gaske cikin kaje Yi? Dariya Fuzail yayi yace Ina ruwanka Sarkin gulma idan cikin ya fito kwa ganshi,Ameer yace zaka aikata baka da kunya ai,kayan jikin Fuzail ya kalla duk jambakin Manal ne a jikin farin kayan,Ameer yace zaka ci Ubanka yau idan ka sake Ummi ta ganka wallahi zaka Rusa kawo Amarya jibi,Kalli rigarka,sai lokacin ma ya lura,wata t-shirt dinsa ya dakko a bayan motar ya zare rigar yard din ya saka t-shirt ya bar wandon Yard din,Nan ma Ameer ya kalla ya dinga dariya yace wlh gwara ka maida rigarka t-shirt karama to kalli gabanka Malam,Shi Fuzail ma ya manta da garin Romancing yayi Release,Sake canja rigarsa yayi ya maida ta yardinsa kawai.

Sai da Ameer ya sauke shi a part dinsa ya wuce,Yana shiga sashensa sai Kuwa yaga Ummi tana jiransa ranta a bace so take taji inda ya tafi tun dazu har dare,Dan Kar ya tsaya Ummi ta Gane shi kawai ya nuna Bai ma ganta ba ya wuce da sauri ya haura sama harda hadawa da gudu,toilet dinsa ya shige Kawai.

Belloti Allah ya taimakeshi Bai ko kwana a Hannun Yan Sanda ba Rahila tayi ruwa tayi Tsaki sai da ta gamsar da Yan Sanda aka sake shi bayan ta biya cin hancin dubu biyar,Belloti ba irin godiyar da baiwa Rahila ba,Rahila ta rubuta Masa Address din gidansu sannan ta bashi kudin mota zuwa garinsu,Belloti ya karba sabo da kudinsa Wanda Suka Fara dukansa wani barawon ya sace a aljihunsa,yace da Rahila kauyensu zai koma Suka rabu,Rahila na Tafiya Belloti yace ai bazai yuwu ba kudi Zan shiga Nema duniya kawai ya fasa komawa garinsu ya nausa cikin Birnin Kano Yana bulayi,kasuwanni ya zaga Yana Neman wata sana'ar inda zai samu ya Raba Amma duk wasu musulmanmu sunki saurararsa Tsoronsa ma akeji sabo da Duniya ta lalace gashi Dan Fulani.
Dan kudinsa duk sun Kare ya cinye su a cikinsa ga yunwa ta dameshi ga kowa Yana kyamatarsa hakan yasa ya canja ya tafi inda Christain Suke da yawa kasuwar Sabon gari, tunda yaje abincin da zaici ma Sai yayi bara,Haka idan an rufe kasuwa cikin Almajirai masu kwana a bakin shagon kasuwa a Nan yake kwana abinsa,Almajiran Basu da Aiki sai shiga bara gidan giya da Club,anan suke zuwa idan an rage Abinci da giya Arne yana Shan abarsa ya rage sai ya Basu Suma su Sha,yawanci a Haka Almajirai Yaran al'umma suke ta fadawa halaka,wasu sun koma Yan daba,zuciyarsu ta bushe,wasu barayi suke komawa.

Belloti ganin Almajiran Basu da kunya ya bar bangarensu ya koma kwana a bakin Resturant din wani Igbo Wanda abinci ake ci Ana Shan giya iri iri a wajen,Igbo kullum ya fito sai yaga Belloti a kwance da safe Watarana yaga ya zuba tagumi,Tausayin Belloti yaji yau ma Yana zuwa ya ganshi a zaune ya Zama Kamar maraya,Igbo da Hausarsa kadan yace Yarinya kullum kana kwana anan kina kwana Baki da Iyaye? Belloti Kawai yace Yana da Iyaye kudi ya fito Nema,Igbo yace is Good very nice,Yaro You get Heart woooo....Ana so ana sana'a a daina Zama Almajiri,Ni Sunana Uche Zan baka Aiki a Resturant Dina Zan na biyanka Albashi duk wata ya kace? Farin ciki ya Kama Belloti yace zanyi na gode,Igbo yace ya suna naka? Bello harda gyara sunan bazai ce Sunansa Belloti ba,Belo da Chau kana son Aiki da Chau sose cewar Uche.
Tun daga ranar Belloti ya fara aikin siyar da Abinci da giya,idan Hausawa ne Suka zo Shan giya duk lokacin da Belloti ya kawo musu ita sai ya dinga cewa Alhaji a Sha Lafiya,tun Belloti Bai koyi Shan giya ba har ya iya shan giya sosai,Lokaci kadan Belloti ya fara wayewa,sabo da Zama da yare ya fara tsintar turanci,Duk Kuma abinda yake baya Wasa da Sallah,Ana haka Belloti yasan cikin birni sosai Idonsa ya bude gashi yayi abokai da yawa mashaya giya gashi Uche daki Guda ya bawa Belloti a gidansa.

Watan Maulidi ne yazo wani ya hada gagarumin Maulidi Belloti yaji Ana ta gayyatar Maulidi yace ah yau fa akwai chasu,shi da Abokansa Suka tafi wajen Maulidi da kwalaben giya,Ana Maulidi su Belloti giya suke bulbula,Wani Sheikh ya gansu da Idonsa yasa Yan Sanda suka kamasu Ashe Belloti akwai giya a aljihunsa ya tafi da ita,Sheikh yace wlh kotu Za'a kaisu Direct,aka tafi Dasu kotu Kuwa,Alkali Yana sauraren Kara Belloti ya zaro giya kwalaba Guda a Gaban Alkali ya daga abarsa tiltiltiltil Yana tiltilawa cikinsa,Alkali ransa ya baci Nan take ya yanke musu hukuncin Bulala tamanin tamanin,Haka aka Zane su Belloti tsaf sannan aka sake su.

Manal Kuwa Bayan ta raka Fuzail da wani irin farin ciki ta dawo cikin gida tana shigowa tana rawa ta shigo ta kalli su Farida tace Me Laya ki yayi me zamani,Idan da Laya kuke takama Ni da zamani nake takama,nice nake zamani,Kai Allah na gode maka Ina zamani Ina lokaci wallahi,Ni ake yayi yanzu , Manal tana lokaci,Waka ta Mai da abin tana irin Rawar Kauye a jefa Kafa gaba ana dawo da ita baya tana waka Manal tana lokaci ganjiganjigaganjiganjiga tana girgiza da juyi har Gaban Hajiya ta girgiza Mata kafada tare da cewa ehhhh sawa,Kudin da Fuzail ya Bata Yan dubu dubu sababbi Kar da yawa ta zaro tare irgo Guda biyar ta mikawa Farida karbi Yar kurkura mu gobe ma wasu za a kawo min,ko nayi waya yanzu kiga an aiko Tanko Yana gudu Yana faduwa ya kawo min wasu yanzu,Haushi yasa Farida duk son kudinsu suka ki karba,Manal Tace ba komai gobe zaku ci shinkafa da kudin,shinkafa Zan siyo duk bala'inku sai na taimakeku wlh ya zakuyi da me lokaci yarinya daga ruga ta zama 'yar yayi Manal me zamani,kudin gaba Daya ta mikawa Farida tace ki karba ma duka ko albarkacin Mafarkin da kika dinga Yi min kullum ai a Baki Lada wallahi wannan irin mafarki Haka Sannu Aunty Ni wallahi bazan ajiyeki a Cameron ba Original kasar waje Zaki je ki kalli turawa-turawa ma su kalleki,Kuma ko ba komai Zaki dinga zuwa gidana Abuja Inshaallah kusa da Villa,idan Kuma Lagos dince a cikin mafarkinki Makwafta nake da Davido da Wizkid ko pics prince Charming ya hadaku ki dauka ki samu na status,kizo gidana insa kuyanga ta goge Miki kaushin kafarki fes.

Farida sai Hawaye ita yanzu da gaske ma ba kudin Fuzail take so ba Fuzail din take so Bilhakki da gaskiya batun wani kudinsa ya Kare a wajen Farida,Farida kuka ya kwace Mata me karfi Wanda ya jawo Manal tayi Shuru tana kallon ikon Allah,Farida durkusawa tayi har kasa a Gaban Manal ta fara rokonta tana kuka Dan Allah Manal Dan girman Allah Kinga ke Yar uwata ce kanwata uba Daya ba Wasa ba,Dan Allah Ina neman Alfarmarki, wallahi na Shaku da Fuzail a mafarki,mun Shaku da juna da shi a mafarki,wallahi Ni yanzu tunda na ganshi ranar da aka Daura muku Aure ranar na fada sonsa na gaskiya,duk son da nake Masa na mafarki son kudi ne,amma yanzu Dana ganshi wallahi ji nake Kamar Zan mutu sabo da sonsa da nake ji,Dan Allah Yar uwata ki bar min Fuzail kice ya sake ki ya aureni Dan Allah.

Majina Farida ta ja tana kuka Tace Dan Allah Manal ki bar min Fuzail Ni Kuma na Miki Alkawarin wallahi ko Nawa ne idan ya aureni Zan baki,Manal tayi Shuru ta kalli Farida tace Farida kina da hankali Anya? Haukar Manal tunaninta me Chemist ma Likita ne,dama tana da number me Chemist na unguwarsu a daren ta Kira Salisu a waya tace da Allah kayi sauri kazo Salisu da kayan aikinka ka taho da komai na aikin gwaje gwajenka zaka auna min Wata,Farida tana ta rokon Manal har Salisu yazo da ledarsa Viva,yawwa Salisu dakko kayan aikin ka gwada min kwakwalwar Aunty wallahi wajen shekara biyar kenan da samun tabin hankalinta,tun abin nata tana Yi a mafarki har yanzu ya taazzara ya fito fili Ina me tabbatar maka gaf take da Fara tsincetsince a bola ko ta fara duka.

Salisu yace Eyya ai mu ba likitoci bane Kawai idan Likita ya rubuta magani mu ake kawowa a siyi maganin,sai shishiginmu da katsalandan na Yan Nigeria Me Chemist sai azo a fada Masa matsala Kuma ba gwaji ba komai shi ba Doctor ba ya dauki magani ya ba mutum Wanda sai an samu akasi Kuma a komawa asibiti da jangwangwama musamman a kauyuka wasu ma Basu Yi karatu ba Kawai koya sukayi da ka,Yanzu Nima a shishigi na Ina yiwa Mata awon ciki,da awon Hawan jini,malaria,da sauran kana Nan abubuwa Kuma duk wannan ba Aiki na bane,yanzu ai asibiti Zaki kaita a Mata gwaje gwajen Daya kamata su rubuta Mata magani idan an Rubuta sai kizo ki siya a wajena,Manal Tace Kai Allah wadaran Yan Birni da karya,Salisu jeka Harkar Taku duk karya ce.

Salisu Yana Tafiya Farida taci gaba da rokon Manal tana cewa Kinga dai irin abinda na yiwa Fuzail bazai surareni ba Ni kaina bazan iya tunkararsa ba bani da bakin magana tunda Yana Jin maganarki Dan Allah tunda nasan ba abinda ya shiga tsakaninku na aure ki bar min shi,Wata Shewa Manal tayi tana tafa Hannu tare da cewa duk wata dama Allah ya Baki ita akan Fuzail wulakancinki da Rashin tarbiyya ya ja Miki,Duk abinda Hakuri Bai baka ba rashinsa bazai baka ba,rashin kunya ba inda zasu kaiki,Kuma Nufinki da zai saurareki sai kije kice kina sonsa? Farida Tace da gudu ma kuwa Nifa idan Ina son Abu ba abinda bazan Yi ba.

Girgiza Kai Manal tayi tace Naga Alama ke wata Dusa ce a cushe kanki yake har abada baza ki samu abinda kike Nema ba,Hajiya Haushin Farida ya Gama kasheta Wai ta durkusa tana rokon Manal ta bar Mata Fuzail su da suke so su kwace shi ta karfi su nunawa Manal ita ba kowa bace Amma ta zauna tana rokonta,ai Nan take Hajiya Haushin Farida yasa ta Dinga durmawa Farida duka karshe ma ta rufeta da duka tana cewa Ashe Baki da zuciya Baki gaje Ni ba? Ni zuciya ce Dani wallahi wani Bai Isa Dan Ina son Abu na roke shi ba,Yar Iska mahaukaciya,Manal ta dinga dariya tace Kara Mata Hajiya Yi Mata Kutufo wallahi,Nan Manal ta barsu Farida tana ta kuka.

Hajiya ta ja ta daki Tace Yar Iska ke da nake so tunda Munga Fuzail din bazai samu ba kema ki canja salo ki samo wani Alhajin me kudin gaske ki aure abinki yanda zamufi karfin Allah sarki,idan kema kika auri me kudi waye zai daga Miki Kai,gidan sarauta ne Kawai masu kudi? Ga alhazawa Yan siyasa da Yan kasuwa ki samo Daya ciki,ki hakura Amma wallahi Manal ko mun hakura mun daura gaba ta har abada da Manal,babu mu ba su cewar Farida,Hajiya Tace har abada tsakinmu da su Manal sai Sharri Bamu ba su, kyaleta da Fuzail bala'in gidan sarauta ma ya isheta,Kuma wallahi Har Fuzail da Yan Uwansa Matukar zasu Zo gidan Nan ba mutunci cewar Hajiya,Farida Tace Hajiya wallahi kaunar Fuzail nakeyi da gaske yanzu ba kudinsa nake so ba,ko bashi da kwandala Zan aure shi da Zan samu,Hajiya tana lallaba Farida tace na sani...na sani Farida ta kiyi Hakuri shi so danne shi akeyi har ya bar zuciyarka.
Gaki kina da kyanki ba laifi Kawai fa sai dai akan Manal ace Miki Mummuna amma kyakyawa ce Kuma kin iya wanka.

Mazan yanzu ai duk kyalkyal banza suke biyewa su dai suga Yar wanka Yar gayu tana kamshi,su ganta da shape,duwaiwaka mashaallah,aga kirji tullukwikwi to ko ciko tayi sai kiga an aureta da wuri da gaggawa,Yanzu kitson Attach Zaki koma ko yaushe,ga Mai me kyau ki dau haske,wannan Duwawun na ciko da ya shigo Wanda Zaki ga Dan wando ne Amma an Masa soso da ciko mata shi suke sawa a ciki su daura skert a Kai Malam kiga duwawu Kamar zai Fado maza Ana kallo Ana yaye baki duk karya ce daga masu Shan kwaya sai masu sa wandon ciki,Farida Tace ga Manal Nan nata ita Haka yake Kato,Ke banza irinsu Basu da yawa a duniya a gari daya baifi ki samu mace Daya ko biyu ba masu na Allah da Annabi a birni Kuwa kaf layi duk girmansa ba afi a samu Mata goma ba idan ma sun kai,su dama maza Yanzu sun lalace da sai fara,Fara ko na Mai ne sai kiga Namiji zai hada babban hatsari a kwalta sabo da kallon Budurwa.

Hajiya Dan ta kwantarwa da Farida hankali ta tsaro karya tana cewa Rannan ma wata taci Mai Ni ko birgeni ma Bata Yi ba duk ta karce fatarta ta tashi daga aiki Dole sai ta koma baturiya tana tsaye a gefen titi me Hannu Daya wasu Trailer Guda biyu sun taho Daya daga can Hannu Daya daga wancen Hannun duk garin kallon Yarinyar Nan me Mai Suka hadu Suka Yi Karo da Karo Munga tashin hankali ranar,kana Nan motoci su biyar suka zo suka shige cikin Trailers din Nan wayyo akan yarinya Wanda farin nata ma bana Allah bane aka Yi asarar rayuwa haka,sabo da Haka duk munin mace Bata rasa miji yanzu babin daukan wanka zamu bude Kawai duk layin Nan sai dai a kalli sabon yayi a jikinki a kwaikwaya.
Farida tace to Allah na tuba da Sanda Muna Talauci ma Mukayi bare yanzu da muke da harka,shege Tela na ma na daina bashi dinki na yanzu ya Zama tsohon yayi,Hajiya Tace ai sabon Yayi za a dinga kaiwa,sun Dade suna tsare tsarensu,Manal tana can ta dukufa akan Littafanta da su Masatura suna ta koya Mata abubuwa.

Washe Gari ma Fuzail shi ya Kai Manal school Tanko ne Driver,Yanda ya Kai Manal har class Haka ya sake kaita Kuma ya dakkota,Islamiyya Kuma Tanko ne ya kaita shi daya,zuwa dakkota aka dakkota da Fuzail suna bayan Mota sai rike riken Hannu suke suna wasanni da hannayen juna,Tanko Yana satar kallonsu yace Ana soyayya a Nan Nima da waccen me gashi kamar Isgar arnan zata tallafa min ai da na more Amma tunda yanzu taga ba auren Prince zata Yi ba babu mutunci tsakaninmu,Tanko ya Saba ganin gashin Farida sabo tana Dan yin dauri Wanda zai fito Tum tum daga baya.

Suna mota Fuzail yace Annatu Tace ki shirya gobe gidan miji ko ba Taya,Manal Tace Amma Wasa kake? yace da gaske wallahi ko da kafar katako sai an kaiki Inshaallah jibi ma Kamar yanzu a cikin jinya kike kina ta kuka na Miki fata fata na hangoki Allah sarki ya fada da tausayi.

Manal tace ban yarda ba ko dangina ai Basu Zo ba,Fuzail yace muje gida kiga su Annatu wallahi sunzo da Yagwalgwal Dinku da Goggo mutum biyar nasa an dakko su,Dangin Malam Kuma mutum Uku harda Hajiya Sharifa,Manal Tace a Ina kasan wata Hajiya Sharifa Yar Uwar su Malam? Fuzail yace to a gidanta ma aka saukeni da naje,Allah kaje kauyen su Malam bayan na Annatu? Idan Yaya Yazed yazo ki tambayeshi Kuma su Malam ma sun dawo da Yazed yanzu suna gida idan Baki sani ba yarinya.

Manal sai Kuma ta fara kuka yanzu Dan Allah gobe za a kaini gidanku? Ko ba tayar mota ma cewar Fuzail,Manal jikinsa ta fada Wai ta Suma Tace na mutu kawai aje a fara Haka kabari na tawa ta Kare,Dariya Fuzail ya dinga Yi yace wallahi nasan sai kinji a jikinki Dole ne,Da kyar Abban Ameer fa ya shawo Kan Memartaba,a Haka ma Ummi Bata San za a kawoki gobe ba,Amma Ameer yau zai fada Mata da dare,Kuma Tace ko an kawo ki Ma'aikata zata zuba a part dinki da part Dina Bamu Isa munyi wani Abu ba za a sanar da ita,tsaro za a bamu sosai Wai baza mu kwana tare ba.

Manal Tace ga shawara,Ina jinki,Kawai ka koma ka Tara Family dinka kaf kace dama ba so na kakeyi ba Wani rashin mutunci na maka shi yasa ka aure ni Dan ka nuna min iyakata,ka tsarasu yanda kowa zai tabbatar ba son juna mukeyi ba kaga za a Dan rage Mana masu tsaron idan Muka hadu a boye muyi hirarmu,Idan da mutane a wajen tsakaninmu gaba ce Kawai ko ya kace? Idan anyi hakan zaiyi Kuwa? Manal tace sosai ma kuyi shawara da Ameer kaji.

Dan iskancin Manal sun Gama hirarsu Amma suna sauketa a gida da kuka ta shiga da uniform dinta,Da Yazed suka ci Karo yace ke Kuma lafiya? Wai gobe za a kaini? Sosai ma an Gama komai ma dazu ma Mijinki ya turo Driver da wasu Bayi sun tafi da duk wasu kayanki Annatu ta hada musu Wanda kika ware tun Ana biki kika Ce da su Zaki tafi,sauran idan kin shiga ku karasa da su,Kuma an kawo lefenki Maman Ameer da wasu matan Suka kawo ki je ki gani daki Guda abin yayi yawa,Ga su Farida can Kuma suna ta zage zage karki kulasu.

Manal iya lefenta data gani sai da ta tsorata akwatuna sun Kai talatin Banda wasu jakankuna,gaba Daya kayan Wanda ya shafi English wears,Inners,Arabian,Indian, cosmetics Dukkansu a turai Fuzail yayi Order,Kayanmu laces,Shadda,atamfofi da wasu materials kadan sune Kawai aka siya a Nan,mutane sai turuwar kallon lefen ake zuwa ana dauka a waya,ganin za ayi surutu Annatu ta kulle dakin a daren Tace Fuzail ya turo a kwashe kayan a kaisu gidan Manal,ai Kuwa Manal tana kuka tana Kara hada abin bukatunta aka tafi da su,Malam ma yayi gara ta gani ta fada.

Shukrah tana gaba da ita ake komai Kuma Amarya sai da aka sake gyarata komai anyishi Dake akwai kudi,kayan kamshi na musamman duk Shukrah ta karbi kudi Hannun Fuzail anyiwa Manal,washe Gari Kuma Haka taje school har Islamiyya Tanko ne shi Daya ya kaita ba Angon,Tana dawowa abinci Kawai taci sai wanka,Sabon Wani shegen White and Golden lace aka Bata ta Sanya Riga da zani irin na Amare dinkin Fuzail ne ya Aiko da shi na musamman,kyan da Manal tayi ya baci,Me makeup ce ta Mata sama sama me kyau har daurin tayi Mata me kyau,ta ko Ina Manal kamshi takeyi.

Takalmin da jaka tare da Mayafin Golden,Dama tayi Alwala nafila tayi tare da Adduointa sosai,Shukrah Kuwa wata Shadda ta Sha dark purple ta zuba kyau ta Sha makeup,su Annatu Kuwa gaba daya dangin uwa Dana uba daga karkara suke ko wacce a hargitse Kamar korarru a Haka Kuma sun Sha gayu,Hajiya Sharifa ce ma ta Dan fita daban cikinsu.

Malam ne ya shigo da kafafunsa sauki Yana ta samuwa sosai yayiwa Manal Nasiha,Haka Annatu da Dangi,Hajiya Kuwa lekowa tayi tace to dai Kar aje aga an shiga daula a dinga cin mutuncin Yan gida sakinki za ayi ato,Harara Malam ya galla mata ta juya ta tafi,Farida Kuwa sabo da bakin ciki barin gidan ma tayi gaba Daya Dan Kar Malam yace ta shirya a Kai amarya da ita.

Su Falaqi Kuwa da su Masatura Dukkansu Yazed ya musu dinki matan su Uku atamfarsu me tsada ta Sha dinki gasu dama da iyayi musamman Masatura data Fara Zama Budurwa 14yrs,Su da su za aje rakiyar Amarya.
Falaqi Dan yaro Tasha shaddarsa yayi kyau shi Yana da haske ma,Yace Allah yasa yanzu Malam Yana da kudi da Sanda bashi da kudi ne Allah Aunty Manal zanbi na koma gidanta a sa min gadona kusa da nata,Dariya aka dinga yi,Oga Yazed ma fadansa daban yayiwa Manal,Manal sai kuka akeyi Kamar zata mutu,Yazed yace kinji na fada Miki bana son kawo Kara,babu yaji,Banda Raina Iyayen Miji da Yan Uwan miji duk da nasan Baki da matsala,Banda kawaye barkatai a kwashe sirri Ana fada musu.

Kwata kwata mutanen da zasu raka Amarya ba Sufi mutum goma ba Amma sai da Fuzail yasa aka kawo mota Guda ashirin Kamar za a dauki Yar Shugaban kasa,kowa motarsa shi kadai ya shiga har Falaqi zaba yayi tasa Guda ya kame a baya,ga securities ga Dogarai da Kuma wasu suna binsu a dokuna Wai Dole sai an San Yarima ne yayi aure, Mutane sun Sha

Please Login or Register in order to submit comment