Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kawai Allah yayi tashi na ne ka barni na tafi Zan dawo verysoon Zan na zuwa Muna gaisawa,Uche Yace Alright Be a good Man ya ciro 10k ya bawa Farida yace ajiya gashi asha ruwa,Farida ta karba tayi godiya ta ci gayu cikin lace dinta peach doguwar Riga me kwala dinkin manyan Mata,Shi Kuwa Belloti wata Shadda ya saka ruwan toka an Masa gyaran gashi yayi kyau sosai da gani kasan ya waye ba Kalar Kauye bane.

Har Mota Uche ya rakasu suka tafi suna dagawa juna Hannu,Belloti da Amaryar sa Ana bayan Mota,tafiya tayi tafiya Farida ta kwantar da kanta a kafadar Belloti tana ta bacci, sai da Suka shiga garin Bauchi Belloti ya fita ya siyo musu wani Naman rago gasashe da ruwa da yogurt har driver din nasa daban,Suka ci suka koshi a motar,a Haka har suka dauki Hanyar rugar me shegen nisa Kamar ba a duniya suke ba,Farida ta kalli Belloti Tace sannunku kunyi kokari kowa da inda Allah ya ajiye shi,Murmushi yayi kawai har Suka karasa garin Farida taga gidajen Basu fi Guda Hamsim ba,Tace Lallai Manal ta waye da wuri idan Haka ne to Kuwa ba karamar basira Allah ya Mata ba,kaima Haka my Husband,kalli ikon Allah Wai kana Nan garin a wannan nisan amma har Allah ya kawoka garinmu ka aure Ni,lallai Mijin Aure daban yake,wanda baka taba zato ba Ashe duk wannan haukar da nake kana Nan kauyen ma tuni,da ace a lokacin za a fada min bazan yarda ba Amma gashi ya faru,Belloti yayi Dariyarsa me kyau abinka da Dan Fulani me kyau ga Hanci,Yace Allah kenan ai Allah ba abin Wasa bane abinda ko a mafarki baka zata ba shike faruwa,Farida Tace ko a mafarkina na jaraba ban taba ganinka ba ko me Kama da kai,Suna karasawa kusa da gidan su Belloti Suka hango wasu lafiyayyun motoci Guda biyu da securities tare da Dogarai,Belloti yace ga kanwarki Nan Maybe Manal,Wannan da Alama da mijinta suka zo,Farida gabanta ya Fadi,Belloti yace ki daina damun kanki kina daukarwa kanki karya Farcy,ba a daka ta Dan Adam a rayuwa,idan ka biyewa Dan Adam to a rayuwa ba abinda zaka iya yi,Ki saki ranki,Farida tayi murmushi tare da Furta ba damuwa wancen ne kenan gidan Annatu? Yace yes shine Mana,kannen Belloti Yan Mata da maza ne Suka fito suna ihun murna da oyoyo,Nan take Belloti yasa suka kwashe kayan kaf tare da shigewa cikin gidan da su,gidan su Belloti na Bulon Siminti ne,su biyu ne gida na bulon Siminti kaf garin,Bayan Belloti ya sallami Me Golf ya tafi,Farida Tace to Manal dinfa ya kamata na ganta Kar na tafi Bamu hadu ba,Farida so take Kawai taga wani na gidansu ko zata ji sanyi a ranta,Yan kauyen sai kallonta sukeyi sunga Yar gayu,Ganin ta damu yace Kira Manal din a waya kiji ko da ita aka zo,Farida ta Kira Manal Wayar Bata shiga ba sabo da karancin network,Belloti yace Naga kin damu Jeki gidan Ina jiranki a gidanmu sai kin dawo,Farida da shagwaba Tace Kai da kake Dan gari muje tare,Haka Suka jera suka tafi gidan Annatu.

Farida ce ta gyara handbag dinta tare da shiga gidan da sallama Belloti yace Ina jiranki a waje,Sallama tayi a gidan tunda taga wani shegen chogen takalmi me tsada tasan Manal ce ma,shiga tayi kusa da dakin,can ciki taji dariyar Manal suna magana ko da waye oho sai lokacin ta tuna taga takalman Fuzail masu tsada,ga kamshinsa ya cika ko ina na gidan,Gadon Annatu Me Spring ne yake Lilo Yana Kara kiiii...kiii....Manal tana ta dariya tana cewa prince da zafi fa kaji yanda ka sake Ni a saman bed na fada ka manta da Babynka,Farida ce da masifa tace Wai su waye ne suke dariye dariye Ana Sallama baza su amsa ba sabo da soyayya Haba,Manal tana daga ciki Tace ya naji kamar Aunty Farida kaji muryar prince,Shigo cewar Fuzail Yana Rufewa Manal cikinta da rigarta da ya janye Yana Mata Chakulkuli,Farida ta shiga,Manal ta Mike tsaye Tace laaaaa Aunty Farida yaushe kika Zo? Me ya kawoki kauyen Nan? Farida ta kalli Manal Tace uhm su Manal Wato dai an Zama mayyar miji Allah ya shiryeki yanzu har bedroom din Annatu? Tana Ina? Bata Nan sai anjima zata dawo ita Muke jira Bamu Dade da zuwa ba da Yamma zamu tafi,Farida ta Furta Uhm I can see,to kin manta garin Nan surukai na suke? Manal tace na tuna fa kinzo gaisar da su,yaushe zaku koma? Zanzo gidanki? Farida Tace to munafuka ba yanzu Zan koma gida ba sai na Saba da surukai na sunji dumi na,Dariya ma ta bawa Fuzail,Farida tace Kanina ya gida ya aiki? Bata taba gaisar da shi ba sai yau,Wai kaninta ta ma,Fuzail yace Aunty Lafiya nake,Farida Tace na gani ai,ka daina biyewa Yarinyar Nan wlh tasa kana ta rashin ta Ido a gadon Suruka tam,Fuzail dai Bai ce komai ba,Farida tace Manal Zan tafi gidanmu Zan na zuwa ai Muna gaisawa da Annatu kafin mu tafi,Manal tace hakan yayi zanzo Nima muyi Sallama, Alright Farida ta juya zata tafi,Manal Tace Aunty kinyi kyau wallahi sai kiba kike Yi, to ya na iya komai zam zam ai ko ya kika ce? ,Manal ta Kama Dariya tace Aunty kina Jin Dadi,zanci uwarki nasan Gulmar da kike ta Yi kizo mu sa labile tunda kin matsu kiji in ba munafunci ba mace da mijinta kin damu da matar wani kije kema a Baki Mana ai gaki gashi Nan,Tashi Manal tayi ta biyo Farida har tsakar gida tana karewa Farida kallo tun daga sama har kasa tace Aunty ana harka...harka...harka.....Farida tayi Dariya tace zanyi maganinki ne kin San Halina wallahi kika sake agaban mijinki Zan Baki kunya,Zan fadi kalmar fitsara a gabansa kinga Zaki ji kunya yayarki tayi Maganar banza Gaban suruki kin San Halina Allah idan kina min irin wannan abin sai na Baki kunya,Manal Tace ance Miki kunyarsa nake ji yanzu Ni,Yaya Aunty Hope dai Bellotin akwai Aiki? Hand bag Farida ta kwadawa Manal suna dariya Farida tace Cucumber ai tayi ta fice abinta,Manal tana ta dariya Wai Cucumber.

Dawowa tayi wajen Fuzail Tace idan Annatu baza ta dawo ba mu tafi Dan Allah,akan me? Sai mu koma cikin garin Bauchi mu kwana a hotel gobe sai mu dawo, Fuzail yace sabo da me? Manal ta kwanta a jikinsa da shagwaba tace cucumber zaka bani,Fuzail yayi Dariya yace lallai Yarinyar nan to Ni tawa ba Cucumber bace Cassava ce,Manal ta fara Dariya harda rike ciki,yace karki kashe min yarona da dariyar masifarki,Jin sallamar Annatu sukayi da sauri Manal ta koma kasa saman Tabarma ta bar Fuzail a gefen bed sabo da daki Daya ne irin dakin kauye,Sannu da zuwa Annatu,Yawwa Ashe Kuna ta jirana cewar Annatu tana shigowa sai kunyar Surukinta take ji,a kasa ya zube tare da kwasar gaisuwa ta amsa da fara'a Nan take ta hada musu Fura lafiyayya Anna Ina su Khairan ne?Suna gidan Kakarsu tun jiya,Yaran Ni ban San ya za a saka su a school ba wannan ta kauyen ta Gomnati ce,ko Birni zamu koma da ku? Annatu ta Bude Baki tare da furta Allah ya kiyaye kin San dai ba zaman kaina nake ba,Mijin Annatu ne ya dawo daga Gona ya Iske Ana zancen yace na tafi na barwar wa duk tarin shanu na da sauran kadaronina,Fuzail ne yace to shike Nan Zan samu ayi sabon gidan a Nan din a canja ginin gida,Mijin Annatu ya washe Baki Yana godiya,Annatu ta kalle shi kawai ta tuna Sanda yake dukan Manal Bata Masa komai ba,tace Allah me iko yau Albarkacin Manal zaka ci Kuma,ba irin duka da zagin da baka Mata ba iya yaranka sune mutane to gashi yau arzikin Manal zaka fara ci Wanda ma ba a San iyakacinsa ba sai Allah,Mijin Annatu jikinsa yayi sanyi yace Manal ki yafe min,Kaga rayuwa shi yasa akace da na kowa ne baka San me Jin kanka ba Akan Mahaifiyarki na samu Yara ki yafe min.

Baki Annatu ta tabe Masa tace da Bata yafe ba ai da baza ta bar mijinta ya taimaka maka ba,Manal tace Saudiya Annatu Inshaallah Zaku Yi aikin Hajji Yarima ya biya,Murna Kan murna suka dinga Murna,Manal tafi so su Annatu su koma birni sabo da karatun su Khairan amma ubansu bazai yarda ba sai dai Nan gaba idan sun girma sai suyi karatun a wajenta.

Fuzail yace Gama mu wuce Ummi Inshaallah kafin ta koma Brazil zata Zo ta gaisar da ke Annatu cewar Fuzail,Annatu tana mamaki tace Allah ya kaimu,Ya Riga Manal fita ya barsu suna zance na sirri irin tsakanin Uwa da Yarta,Annatu Tace Ina Dan Uwan naki? Manal tace Yaya Yazed tab ya fada Miki? Baki ga gidan da Malam yake Gina Masa ba na Alfarma wlh sai dai Yaya Bai da matar aure,Allah zai kawo Masa ta gari ne,Shukrah fa an saka bikinta da wani me kudi babban Custome shima da farko wajen Farida yazo ta Masa wulakanci a Hanya ya hadu da Shukrah,Allah kenan Farida anyi banzar yarinya amma tunda kika ga Haka dama can ba rabonta bane Allah yayi duk ciki ba majinta, Allah ya Basu zaman Lafiya da Bellon,Manal ta Furta Ameen ai zaki ga tazo tana garin Nan tazo gaisar da surukanta, Mashaallah cewar Anna,Rumaisa kawarta itama an kusa bikinta Wai Uk mijinta zai tafi da ita can zasu zauna Kuma Anna shima Saurayin Farida ne,Dariya Annatu tayi tace Allah ya kyauta shi Kuma Tanko bawan Allah fa? Yana Nan an Kai kudin Aurensa da wata yarinya Islaha Bata fini ba Baki ganta ba wlh kyakyawa me haske Kuma suna da rufin asiri sosai ba talakawa bane ta kusa Yin candy ma final Exam suke Yi,tana karewa za a daura auren Fuzail ne zaiyi komai,Annatu make manal tayi tace ban hanaki fadar sunan miji gatsal ba,mantawa nayi fa Anna,to tashi ki tafi Yana jiranki,kudi ta ajiyewa Annatu masu yawa Tace gashi inji Shi yace a Baki kayan abincin Kuma Wai na Baban su Khairan ne,Anna Tace to angode Ana ta dawainiya Haka Allah ya Kara Budi,Manal tace Amin ta yafa mayafin Abayarta me kyau da tsada Wata dark green ta fita.

Tana zuwa Suka je da Fuzail tare da gaisar da Iyayen Belloti,Lokacin Farida tana Sallah Manal Tace Bari na jira ta idar Ina Yayan Nawa Bamu gaisa ba,Fuzail sai ya hade girar sama data kasa Kar Manal ta gaisa da Belloti,Sai Kuwa ga Belloti ya shigo Dan saurayi da wankansa na Shadda ta Masa kyau matuka,Manal tayi Murmushi tana kallonsa Suka gaisa da Fuzail,Manal tana Dariya daga kallon Belloti shike Nan Fuzail ya fice waje Yana ta bacin rai,Manal ita Kuma mamakin wayewar Belloti takeyi a ranta tace yo dama Yana Zaune da ogar Daukan wanka ko Bai iya ba ai sai Farida ta gogar da shi bare Kuma Dama a gogensa ta sanshi,Belloti ya fita daban a garin yayi kyau sosai dama gashi ba laifi Yana da kyau,Manal tace Belloti lallai kana hutawa,Belloti Yana dariya yace Hutu ai sai ku kune manya,Farida itama kishi taji ta tuna Belloti yanda yace Yana kaunar Manal ga Manal yanda take da Arnen kyau gashi wani kyau data Kara taci gayu Haka Kawai Belloti yazo yaga muninta gwara Manal ta tafi sai tayi wayo tace Kai Manal kin Shiga uku wallah ki tashi ki tafi kin San dai mijinki Bai son jira ki tafi Yana mota mu ba ruwanmu idan yayi Fushi da ke,Manal zata Yi magana Farida ta katse ta da kin fiye surutu dare fa zai Muku a hanya,Ai cikin garin Bauchi zamu kwana sai gobe zamu bi Flight,to ku tafi sabo da yanzu rayuwa ba yarda duniya ta canja Ana fama da Yan ta'adda.

Mikewa Manal tayi Belloti yace muje na rakaki,Farida tace karfa ka jawo Mata mijinta Yana da kishi,to na Riga na aureki wanne kishi zaiyi yasan dai ai bazan dawo na so Manal ba,Farida Tace zuciya Kashi ne da ita? Belloti Fuska ya Bata Kawai sai Farida ta Shiga hankalinta Kar suyi fada tsoron Belloti take ji,da Manal Suka fita a soro Manal ta bashi 20k tace gashi a kular min da Aunty,Fafur Belloti yaki karba Kuma baida kudi Amma ya rantse bazai karba ba,Manal Tace to shike Nan ka bawa Aunty na,Yace wannan Kuwa Zan Bata kawo ya karba yasa aljihu yace tana godiya.

Ai Fuzail Yana ganin Manal dinsa da tsohon saurayinta sun jero ji yayi Kamar ya hadiyi zuciya ya mutu ya huta,danne bacin ransa yayi Bai Bari Belloti ya Gane ba sukayi Sallama,Belloti ya sake zagawa ta saitin window Manal yace mun gode Allah ya kaiku lafiya kinje gidan Khaltum Kuwa kawarki? Manal tace sai na sake dawowa dai,Okay to ya juya zai tafi Manal ta sauke glass tace ka gaisar min da su Lawi Dan Allah idan na dawo Duk zan neme su,Belloti yace kin tuna cin gyadar ku kenan Manal ta fara Dariya Fuzail Yana gefenta Kamar ya masgeta Haka yake ji,driver ya yiwa magana muje Yana Jan Tsaki,Driver Yaja Suka tafi Belloti ma ya tafi gida Farida gabanta sai faduwa yake Kar Belloti yaga kyan Manal yaji ya tsaneta ita,sai gani tayi ya dawo Yana ma Yi Mata wani kallon kauna,Farida dukkan Yan gidan su Belloti kaunarta sukeyi sunga Yar gayu,gashi wani mutunci da ladabi da biyayya take musu,20k din Belloti ya bawa Farida yace gashi inji Kanwarki,Farida Tace Uche ya bani 10k ta isheni ka rike wannan,Belloti yace a'a bana son gorinku na Mata duk ranar da fada ya hada mu sai kin tuno da kudin Nan naki ba ruwana ki rike abinki kayan Mata kayan gori,mace ta taimaki Miji Amma ba dama yayi katabus sai Gori da cin mutunci bada Ni ba Kar Azo ace Belloti ai na baka 20k kyauta ka biyani abata,Farida ta dinga dariya Tace Allah bazan Yi ba,yace sai dai in ban tashi Kara aure ba duk sai kin Fadi abarki ba ruwana,au zaka iya Kara min kishiya? Ni na Isa Ina Zan Kai matan misali na Baki fa,Indai ba Hali kika canja ba ko wata kaddara ba abinda zanyi da wata Engine Nan naki ya isheni,Farida Tace karka sa na tashi na Fara taka rawa,Belloti Yana dariya yace surukarki zata ganki dakin Nan namu ba sirri gareshi ba,Haka suke hirarsu.

Da Yamma Goggon su Belloti tazo zata fara girkin dare,Belloti yace ki fita ki Taya Goggo Aiki kin San dai Dangin miji,Farida tana Dariya tace to ba musu, aikin da ko uwarta Bata tayawa amma ta yo waje ta dauki tsintsiya goggo tana ki barshi Farida Yara zasuyi daga zuwanki sai Aiki Dan Allah ki huta Haka,Farida tayi murmushi sanye da Hijab dinta Tace barni Goggo na motsa jinina ai Ni na Saba da Aiki dama tun a gida,Goggo tana Murna tace to madalla,Haka Farida duk girman gidan Nan ta share ko Ina ta gyara komai har Ledar tsakar daki ta ko wanne daki sai da ta goge,bayinsu yasha Siminti Nan ma ta sake wanke shi fes ta dawo ta karbi garrin Dawa tana tankadewa Ashe Farida ta iya Iskanci ne yasa basa Yi a gida gashi anzo Ana bautawa Uwar miji.

Manal Kuwa tunda Suka tafi tana kallo Fuzail Yana Fushi Bata taba ganin fushinsa Haka ba,tunawa tayi ko Dan ta kula Belloti ne,a ranta tace Wai wannan wanne irin kishi ne haka mutumin da ya auri Yayarta mene Kuma ai sunyi zaman gari daya tana so ta Masa Magana amma ba fuska,Tsoronsa ma ta shiga Yana can gefen daya Kofar itama tana gefen Daya Kofar,Satar kallonsa takeyi Kawai ya zurawa Hanya Ido fuskar Nan ba Rahma,a tsorace ta dinga lallabo da hannunta Daya sai kace wani wahainiya a hankali ta sa Yatsanta tare da dungurar hannunsa sai kace wani Zaki ta gani,ko kallonta baiyi ba,ta sake Dora Hannunta a cinyarsa tare da girgizawa ko kulata baiyi ba,lafiya My prince? Wani kallo ya watsa Mata kawai tayi Shuru,ganin Haka sai ta ja gefe itama tayi shuru,Har suka je garin Bauchi Bai saurareta ba Kawai wani katafaren Hotel yayi musu Booking,Sauran Securities yace Kawai su tafi da Motocin can gida zasu taho gobe ko jibi,ya sallamesu Suka wuce Manal ta dauki jakar kayansu wacce Guda Daya ce dama Suka hada kayansu ciki,Gaba yayi ya barta ta bishi da sauri,Sama Suka hau aka Basu key din room dinsu,Wani Room and Palo ya Kama musu katon gaske sanyi da kamshi Kawai ke tashi,Toilet ya fara Shiga yayi wanka da brushi ya fito ya shirya a gurguje ya wuce masallacin Hotel din,Manal ma Haka ta shiga tayi wanka da Brush ta fito sai da tayi Sallar Magriba da Isha tayi Azkhar sannan ta shafa lotion dinta ta nemi rigar baccinta ta saka wata maroon me kyau.

Knocking taji anyi ta manta Bata taba shiga Hotel ba Kawai ta tabbatar Fuzail ne ko mayafi Bata yafa ba ga rigar baccin sharara ta Bude kofa Allah yasa Fuzail din ne ransa ya sake mugun baci yanzu da ma'aikacin Hotel ne Haka zai kalle Masa jikinta shike Nan ya kalli banza,a tsorace tace Sannu da zuwa Tsaki Yaja ya hada da ita ya hankadeta gefe yayi gaba,Sharrin Manal sai ta tafi wani luuuuuu ta Fadi Tim a kasa ta fashe da kuka Tace ka dukeni? Fuzail ya tuna da cikinsa ya wani rude yaje ya tashe ta yace I'm sorry ban San Zaki Fadi ba na Dan tureki ban San Baki da karfi ba ne Haka,Manal tana kuka Tace dama kana sani Kuma ai dukana kayi,Ni din na dakeki? Kiji Tsoron Allah Manal Taya Zan daki matata Ni,Gashi Nan akan kana Jin Haushina ka dukeni,Tashinta yayi yace tashi to ya Dagata Tace Ni jiri nake ji wayyo marata Bari zanyi,Cikina ne zai zube,Bari zanyi,Fuzail yace daga Dan wannan faduwar sai ciki ya zube wallahi idan Mala'iku Suka amsa bakinki cikin Nan ya zube bani ba ke,Dan Iskanci sai kice ciki zai zube idan kika fada a dai dai fa,Ana so a furta alkhairi.

Tashi tayi da kyar ta haura saman lafiyayyen bed din sannan ta lullube jikinta,Baza kici abinci ba? Manal tace ae na koshi,Baki da hankali Haka Babyna zai kwana da yunwa,Manal zata Yi magana ya lullube ta da masifa dama haushinta yake ji kadan yake jira,yace dama haushinki nake ji na hanaki Abu kinki ji ko? Ke me taurin KAI ko? Sabo da Ina lallabaki ko? Sabo da Ina Wasa dake ban Isa in fada Miki magana kiji ba?Manal jikinta yayi sanyi tace to kayi Hakuri na daina amma kasan zaman gari Daya ba Wasa ba,Kuma Muna mutunci ne Bai kamata ba sai yace wulakanci ne Dan na auri me kudi,Kuma ma ai yanzu ya rigada ya auri Farida mutunci ya sake kulluwa a tsakani ba yanda zanyi Indai ba zargina kake Yi ba mene abin damuwa sai idan Zarg....karki lalata min aure ya katse ta,Zaki ce Wani abu Nifa nasan soyayyar maza Haka Kawai Kuna Hira Yana Jin Dadi idan Kun gaisa ba shike Nan ba Mene na wani Hira har kina Masa dariya Ina kallo fa kina Kallonsa ko ban ganki bane?

Manal kanta ta dafe tace Wayyo na Shiga Uku Ni na kalli Belloti? Karya ai Zan Miki har cewa kika Yi Yana Jin Dadi Baki kalle shi ba ta ya kika San Yana Jin Dadi? Kun wani jero tare kin San Allah ba Maganar Wasa last warning nake Miki idan ya wuce gaisuwa bana son wata Hira tsakaninku idan Kika sake duk abinda na Miki karki ji haushi,har Yana wani cewa kunci Gyada tare da su Lawi kina yaye Masa hakora wani zan dawo ai ka fada musu, ki koma Ina to wlh kin jawa kanki sai kin shekara baki dawo kauyen Nan ba na fada Miki Kar ma ki sake ce min Zaki je ganin Annatu,Manal Tace to naji ayi Hakuri bazan sake ba Sarkin Mita,nine ma me mitar?Wasa fa nayi maka,Tsaki Yaja ya Mike sanye da Jallabiyarsa ruwan toka zai fita Ina zaka je Kuma? Bai kulata ba ya fice,Saman bed ta haura tare da kwanciya ta shige Blanket sai gashi ya dawo an biyoshi da Abinci lafiyayye a tire,Dakin ya sawa key yace da Manal sai ki sakko kici abinci, idan kunga an damu da ku sai ku tsiri yiwa mutum Iskanci,ance kuyi Abu baza kuyi ba shi yasa maza ke Baku wahala,Manal tayi Shuru dai ta sakko tazo ta duba abincin duka Tace chips zan ci da tea Ni Kuma gashi Naga babu tea din,tun a Muna mota farkon tahowar mu kika dameni ke plantain Zaki ci nasa an kawo Miki da chips kince da Tea Ni bazan iya sake wahalar magana ba,Manal Tace shike Nan zanci haka tasan Idan ta sake magana yanda yake Jin haushinta sai suyi fada again shi yasa taci abinta Haka ta Sha lemo ta wanke bakinta ta kwanta ta barshi Yana ta waya da mutanensa na kasar waje akan business dinsu.

Yana waya hankalinsa Yana Kan Manal dake Shirin Bacci ta rufe Ido yace Cassava din fa ko kin fasa, Dariya tayi tace kazo ka min wani fadan yanda kake Jin haushi na yau, Palo ya fito Yana Wayar a zaune saman kujera Yana kallon wasu wakokin Hausa wata Chanel tana sawa kala kala, Manal jin kidan ta fito palon da lemonta a Hannu tana sha tana rawa
Steps takeyi kala kala tana gani a school friends nasu suna yi tana bin kidan harda Karo Volume,Fuzail Yana waya yace Babyna fa,Manal Tace ba abinda zaiyi Exercise nake masa,ya sake cewa Babyna fa Sunshine karki min asara bakya Jin magana kin fiye rigima idan an toshe Nan ki bula can,Cinyarsa ta koma ta zauna Tace Yaron Nan Yana takurawa rayuwata Allah,Zama tayi a Cinyarsa suna facing juna Yana waya tana tabe tabe a Fuskarsa duk ta hanashi Wayar ma,ta jawo gemu,ta shafa saje,ta koma gashin Kansa ta warwatsa shi,Hannu biyu tasa ta tallafe Fuskarsa ta matseta da Hannu biyu,ta lankwaso Kansa kasa tsaya na maka kitso Yana ta wayarsa cikin Harshen turanci.
Mikewa tayi ta koma ta bayansa ta tsaya tana Masa kitso sai da ta gaji da murde murdenta ta dawo ta sake Zama a cinyarsa Daya kunnen da Wayar Bata jiki ta samu tana ta Masa Wasa da harshenta a ciki tana hura Masa Iska ciki,Zaki sa na kasa Wayar Nan ki Bari na Gama Kinga Cassava ta fara canja yanayi,Murmushi tayi Yana waya tana lashe Masa fuska wuri wuri take bi tana ta iya shegenta da sauri ya karasa Wayar tare da kashe kayan kallon da haske,Suka wuce Bedroom.

Belloti tunda ya dawo ake ta labarin a Kauye Ana zuwa ganinsa yanda ya goge,Haka Farida ta Sha kallo ana cewa Belloti wata Yar gayu ya auro,Baban Belloti ganin Farida yanda take faranta musu Yana Sonta sosai,komai sai yace a kaiwa Farida,Haka Belloti sai abinda Farida take so shi take ci Yana kula da ita ganin Haka sai Dangin Belloti Mata da wasu Maza tare da Goggo Suka tsani Farida sabo da tunaninsu ta mallake musu yaro ita ke cinye Masa dukiya Bayan Basu San tuni kudin Belloti ya Kare ba kudin da Uche ya Basu da Manal shi Farida take bayarwa Yana musu cefane da komai Kuma da su Yan gidan ake cin komai tunda a tukunyar gidan suke karbar abinci.
Wasa Wasa Farida tun abin Bai dameta ba har ya fara damunta komai sai suzo suce Belloti ya Siya musu sai da Dan kudin ya Kare kaf Basu da ko sisi,ga Hajiya tana ta bugo waya Bata da ko sisi a taimaka Mata,Belloti sai cikin abokansa na Birni yayiwa waya ya roke su daya su tura Masa 5k a accnt din Hajiya,Nan take wani ya tura kudin shike Nan aka huta.

Goggo da kannen Belloti sai Suka daina Aiki ko Daya gaba Daya Farida Suka turawa aikin gidan,da Sassafe har Koko ita ke damawa,Haka shara da wanke wanke da girki duk ita keyi sai idan Belloti Yana

Please Login or Register in order to submit comment