Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me yawa,Manal taci gaba da zubawa Hajiya Naira tana Dariya sabo da Hajiya Shokin ta sake Ebowa da Hannu biyu ta watsawa Manal wannan karon Hajiya harda gwalo ta hadawa Manal,Su Annatu da suke kallo ma duk ta kwaso ta watsa musu,Farida ta shigo Itama kusa da Hajiya Suka Fara kwasowa tare suna watsawa Manal Shoki,Harda sa musu wakar Shoki ahh Shoki,Su Sharifa Suka ce Ana zuba bariki a wajen nan, su
Yahaya da Basu San ramuwa ake Yi ba suka ce Hajiya Haka akeyi Bari ki gani Suka shige Suka dinga cashewa suna girgiza da Murguda Kugu Kamar Mata,Hajiya Tace Uwaku ba rawa nazo Yi ba.

Fuzail da kishinsa ya koma gida,Ummi tana kallonsa duk ya kasa sukuni,Tace akan Allah baiyi Tanko ya auri Farida ba ko wa take? Sai ka zauna ka damu kanka akan me,tunda ka shigo kake kunci an rasa me aka maka,Yarinyar Nan ce ta min fitsara Dan taga naje gidansu Ina ruwana da safgarsu da har zata gaya min magana,Dariya Ummi tayi tace tukunnama Indai matsiyaci ne,wa yace kaje,kace ba kulata kake ba me ya kaika? Baza ki Gane ba Ummi,Ummi tace Ni dama wallahi Ina son magana da Kai naji a gidan Nan Ana gulma kana bibiyar Kuyanga yanzu Fuzail abinda zaka min kenan akan kayi lalata da Kuyanga wallahi gwara ka kula matarka Ummi ta fashe da kuka,Fuzail yace Ni karya ake min me zanyi da wata Kuyanga,wallahi idan ta tabbata ko kayiwa wata Kuyanga ciki a gidan nan ba Ni ba Kai Kuma kasan Maimartaba sai ya daureka wallahi Dan Allah karka ja min abin kunya,Fuzail yace tukunna ma Sai Manal tayi ciki kunji ance Kuyanga ce kwayi bayani,a fili yace Allah Yana bayan me gaskiya,Allah ya tona asirina Indai Ina kula kuyanga,kwafa Ummi ta ja tace ai Allah Yana gani ta fice a fusace.

Fuzail ta matarsa yake,kasa nutsuwa yayi 2pm ya ci abinci lafiyayye ya sheka wanka ya fito cikin wata jallabiya Fara tas Kamar wani Balarabe Yana kamshi,bayan yaje Sallar la'asar yace Tanko yazo ya kaishi gidan su Manal,Tanko ne yayi Driving dinsa, har can lokacin Ana ta cashewa,Manal ya hango tana ta zirga zirga gyalenma babu ta ajiyeshi Haka suke yawonsu dukkan su matan,daga nesa yasa Tanko yayi parking Yana ta kallon Manal ransa ya Kara baci ya hasala sosai sai zirga zirga sukeyi tare da Yan Mata su Shukrah,duk ta fisu yarinta,Tanko Yana satar Kallon Fuzail Yana dariya a ransa yace jaraba sai kace shi kadai ne me Mata duk ga Mata Nan wajen ma da matane mazan Basu da yawa duk ya damu Kansa,Tsaki Kuwa Fuzail ya ja yafi kwando Guda,Ya Kira Wayarta Kuma a kashe Bai San ta kasheta ba ta bawa Annatu Ajiya Kar me Dan Hali ta sace mata.
Tanko Yana sani yace Ranka ya Dade Kira maka ita za ayi ne? Da bala'i ya kalli Tanko Yace a Haka zaka je wajenta ka ganta,yo gani na nawa Kuma Tanko ya furta a ransa,Gajiya Fuzail yayi Akan ya barta a Haka gwara Tanko ya Kira Masa ita, Tanko kira ta kace tazo Tafiya gida zamuyi kace tazo mu tafi ka fada a Gaban Annatu dole zata Koro min ita,Tanko yasha yadinsa milk duk cikin kayan da Fuzail ya dinka Masa yayi kyau harda hularsa ka rantse ma Abokin Prince din ne,Yana tafiya sai ga Islaha da Dan farin Hijab dinta da Leda a Hannunta ta auno Madara ta yin Alawar Madara,tana kallonsa ta Gane Tanko da karfi Tace laaaaa Iliyas ? Tanko ya tsaya da dariya yace lallai kinyi kokari da kika Gane Ni Haba taya bazan ganeka ba tab Sannu Ina yini?Tanko yace lafiya Alhmdllh,Fuzail sai masifa yake a ransa ganin Tanko ya ma manta da aikensa ya Kama Hira da wata yarinya.

Ina kika je Haka? Madara na siyo ta gobe,kaga wayata tana ta aikinta gaskiya me kyau ce kaji idan na Kira Goggota muryarta a cikin rangadadau, Tanko yace ba karamin Aiki na bane In Baki babbarta Islaha ta fara Masa fada wai Kai wallahi ka kiyayi wannan kyautar taka Yan Mata yanzu kulaka zasu dinga Yi su maidaka gara,ai Ni me kaunata nake Bawa abina,Ni kaina kana birgeni da ka bani Wayar Kuma sai naji wani tausayinka naji ka sake birgeni,Ai kyauta Dadi gareta cewar Tanko,ai Kuwa dai Nima naji,da Kamar Kar na karba,da tuni kin cuci kanki Tanko yace Yana kallon fuskar Islaha kyakyawa da ita me haske, yace kina da kyau duk masu suna da L masu kyau ne,Islaha tace uhm ai ni Zan fada maka Haka Ni da nake ganinsu a makarantar safe,Hmm Ni dai Zan tafi gida,Tanko tuni yace muje na rakaki a Ina kike ko a Nan Unguwar kike? Fuzail Yana Shan mamakin rainin Hankalin Tanko yanda yabi Budurwa ma ya manta da shi sun tafi suna ta Hira suna dariya,Islaha tace Allah ya kiyaye min zama a wannan Unguwar lalatacciya,Fuzail a fusace ya Kira wayar Tanko,Tanko ko duba Wayar baiyi ba Islaha ta tafi da shi tuni sun bar layin ma.

Yana kallon Amarya da Yan Mata suna ta nishadi,Fuzail yayi Dariya shi kadai yace Allah ya tsare Allah ya jishe mu Alkhairi,Yana Haka sai ga Ango da wasu Yan matasa irinsa Wanda a garin zuwansa Suka Saba a wata majalisa,Motarsa ya kotse tare da parking Suka fito da kudaden liki Suka yiwa Amarya Liki Wanda abokan nasa ma Belloti ne ya Basu kudin likin sabo da su rufa Masa baya,Amarya ta Shiga,Belloti har zai taka rawa sai ya fasa Kar a ganoshi Dan Tasha ne,ya nuna nutsuwa da da'a sosai Farida ma Bata nuna zakewa ba ta nuna itace Amarya,Manal ta fito da wani kudin zata Yi liki tana cewa Ango ya shiga? suka Kama Fulatanci da Belloti lokacin data shiga tana Masa liki ta Gama ta fito,Belloti Bayan ya fito yaje wajen Manal Yana fada Mata su Lawi sunce a gaisheta suna Dan tuna gida suna Dan magana abinka da Yan gari Daya an taso tare gashi Kauye kowa yasan kowa dole a gaisa ayi Hira,shi Fuzail Bai San wannan ba,ransa yayi tsananin baci Kamar ya fashe Haka yake ji,zuciyarsa kamar ta fito sabo da kishin bala'i ne da Fuzail matuka.

Nan take Idonsa ya canja yayi wani ja,farcensa yasa a Baki Yana kwankwasa hakorinsa da shi,Yana kallo gab da Magriba Manal suka shige gida sai gata sun fito da Mayafi sun Mike layinsu sun Kara gaba ko Ina zasu oho,dama Haka Mata ke biki wasu Indai Suka fito biki to fa shike Nan ba ruwansu ko Ina zasu iya zuwa Kuma a layin Haka da masu aure da marasa aure Haka basa yafa ko mayafi baza ka Gane matar aure ba.
Basu Dade ba yaga sun dawo a Napep da ledoji a Hannunsu alamar wani abin Suka siyo ma.

Bangaren Manal kuwa bata ma San Yana wajen ba,Unguwa da suka fita kayan Amarya suka karbo Wanda zata tafi da su ta Kai wajen wanki shine Suka karbo da Kuma sababbi da ta bayar a goge Mata,Tana Shiga Ciki taji Hajiya Sharifa da ta shigo yanzu tana cewa ke Manal Naga mijinki wallahi ki hirya daukanki yazo mun dawo daga makwafta muka ganhi Yana Alwala,Manal a ranta tace tab bikin ma baza a bar mutum ya huta ba idan na tafi Amaryar wa zai shirya Mata kayanta ga kawaye duk kwana zasu Yi ana Shan shafta ai bazai ganni ba,Shuru tayi tace Ina zuwa ta koma dakin Yazed ta buya a ciki,Fuzail gajiya yayi da jiran Tanko ya tura wani yaro gidan ace Manal ta fito anzo Daukanta,Su Annatu ba inda Basu duba ba ba'a ganta ba,an nemi Manal an rasa,Ana fadawa Fuzail yayi Dariya a ransa yasan buya tayi Ana Haka Sai ga Falaqi da su Masatura Dukkansu sun taho Wajensa sun Sha gayu,Yace duk kune Haka wannan wanka Haka,Yaya Fuzail Makeup Muka je Aunty Manal ce ta Bamu kudin,Malam yace zai canja Mana sunaye masu Dadi da Ma'ana,Fuzail yana murmushi yace Good ni Zan sake siyo raguna kowa ya ci Dadi, Falaqi yace dazu na ganta a dakin Yaya Yazed Tace Kar na fadawa kowa tana ciki Wai bacci zata yi,Fuzail yace Good je ku nunawa Annatu inda take sannan kuce Sauri nakeyi ta fito.

Falaqi ya tafi da Gudu,Fuzail ya Basu sababbin kudi Yan Hamsim Hamsim yace kuje kuyi liki Kuma,Masatura suna godiya Suka tafi yace karfa ku Hana Falaq,to ai zamu bashi.
Falaqi Yana Shiga ya Iske Annatu tana ta masifa Ina Manal ta tafi,yace tana dakin Yaya Yazed Kuma Yaya Fuzail yace tayi sauri su tafi,Annatu suna Shiga Suka ga Manal a katifar Yazed tana Danna Wayarta,Annatu tace to Hakima taso wallahi ko yanzu na mammakeki,Falaqi ta Harara tace zaka sani idan anyi hutu baza Azo gidana da Kai ba,Dariya yayi yace naji,Kayanta ta hada ba Wanda ta fadawa zata tafi tayi tafiyarta cikin fushi,tana zuwa motar ta Balle ta shiga tare da jefa Jakarta ta zauna tana hawaye,Fuzail yace tashi ki koma a kwana lafiya,Ba kunya Manal ta dauki Jakarta tana murmushi Tace na gode I love you ta juya zata tafi,a fili yace Kaiiiii Baki Bude,Juyowa tayi tare da shigowa cikin motar ta manna Masa kiss a kumatu Tace sai gobe ko jibi? Fuzail ya kalleta ransa a bace yace Baki San laifin da kika min ba? Laifi Kuma? Ni din? Baki ga Ina Fushi ba? Au Fushi kake Yi ? Dan Allah? ai ban sani ba wallahi Yi Hakuri ta dawo Tace me nayi? Au Baki San ma me kika Yi ba?

Au na tuna me yasa ka tafi dazu bayan Kuma Kai ka kirani ai Ni ya Dace ma nayi Fushi da Kai,kasa na fito Kuma kayi tafiyarka Allah ka bani haushi gaba Daya badan na Bawa zuciyata Hakuri ba yau bazan kulaka ba kwata kwata ai Ni baka kyauta min ba,sannan yanzu kazo na tafi gida gaskiya banji Dadi ba, ka nuna min iyakata,ka kunyata Ni a Gaban mutane kaga Kuwa yanda ake sha'awar mu Ana yabonka ka iya kiwo yanda na canja na Yi kiba nayi kyau,sai dai kaji ana ta cewa wannan Yaron Dan Albarka ne,ai Yaron Nan Yaron arziki ne,ai Manal ta Dace,ai koriyar shinkafa yake bata tana ci,ai ac ta sanyayata ai Baku ga yanda yake shagwabata ba,Yana ji da ita,Yana lilitata,Manal tana Jin Dadi,Manal ta Fuzail,Manal din Yarima,Yariman Manal,Ni Kuma Ina yanga Ana fasa min kai ai dole Haba tayi girgiza da kirji a motar Jin wani kida sabo Yana tashi,Tace Ni Kai zanwa Rawar tawa,Oya Fara liki,duk masifar Fuzail Daya kwaso sai ta hanashi magana ma ta sashi nishadi Nan take ya manta da fushinsa yabi Manal da kallo Yana dariya marar Sauti ganin tsakaninta da Allah Rawar takeyi a zaune Kuma kidan take bi,Yanda yake kallonta yasa taji kunya ta fada jiinsa tana Dariya,Yace yanzu dai yau baza ki koma ba? Manal Tace please ka barni kwana Daya Dan Allah duk Yan matan kwana zasuyi,ku dinga yawo ba Mayafi a layi ko? Kuna Hawa Napep Kuna zuwa yawo,Kuna kula mazan wasu Kuna musu surutu Kuna dariya,a Haka Zan barki? Kin tambayeni da Zaki hau Napep ki tafi unguwa? Manal tayi Mukus tace Ni din? Harara ya watsa mata tace to kayi Hakuri kaji ta fada Masa inda Suka je,Fitowa ba Mayafi Kuma na daina Inshaallah, Karki sake ban so na sake ganinki da Belloti a tsaye kinji na fada Miki Ni bana so wlh,Tsohon saurayinki ne fa,har yanzu nasan Yana sonki,Kuma zaina fakewa da gaisawar zumunci Yana kallonki Yana Jin Dadi,Baki Manal ta Bude tace Allah sarki Belloti yayi Aurensa Ina ruwana da shi,kinji ko har Allah sarki kike cewa ai kema wa ya sani ko har yau Yana ranki,Na shiga Uku manal ta daura hannu a Kai tace Sharri zaka min Kuma? Ke kika sani kuma,sabo da Annatu Zan barki ki kwana,Ki kunna wayarki Kuma ki samu room ke daya 2am Oral xxx zamuyi,Manal ta zaro Ido ni dai Allah a'a, Alright sai kizo mu tafi gida,No na yarda sai ka kira,ta yunkura zata fita a motar yace Zauna ai Hira zamuyi zance na Zo sai 10pm Zan tafi.

Manal Tace tunda ka barni na kwana ba damuwa,Ya fito daga motar itama ta fito ya daurata a saman bayan motar daram,Shima ya Dane gefenta ya zauna suna ta hirarsu ta masoya.
Farida da sauran Yan biki suna hango su,sai da aka Gama Dj Suka koma ciki bayan sunci abinci suka Yi wanka aka zauna Ana kwasar shafta da Rashin kunya iri iri, Walida tace wannan guy din fa na Kanwarki Farida Yayi wallahi gashi Yana Sonta da yawa,irin Mijin da nake so me kwarzabar jaraba,ya dinga nace min Yana Nuna min caring, idan anzo harkar bed Kuma ba sauki,Shukrah tace ai suna son juna,Farida Jin ba ita bace sai ta canja zancen da cewa idan Ina Kano sai yaushe zaku Zo to? Rumaisa tace Bayan Amarci yayi sauki,Farida Tace kin tuna min ma ta Mike tare da dakko zumarta da tarkacen magunguna tana Sha.

Sai 9:30 Tanko ya dawo,Ganin Fuzail Yana ta zuba Hirar love da matarsa sai ya koma gefe da Alawar madararsa a Leda da yawa Islaha ta bashi kyautarta,Sai bayan 11 sannan Fuzail yace zai tafi,kiss ya Mata a saman goshinta, Tanko da sauri yazo tare da mikawa Manal Ledar Alawar Madara,Manal ta duba ta dinga Murna Kamar taga Mama,Tace na gode Tanko wallahi kamar kasan ita nake nema,Fuzail yace sai kace me ciki,kudi ya Kara Mata kudin liki ya rakata ta shige gida sannan ya dawo Yana sane da Tanko,Tanko yazo ya Shiga mota ya jashi suka tafi, Fuzail Yana gidan baya yace wace wannan Yarinyar Kuma? Tanko yayi Murmushi ya bawa Fuzail labarin Islaha,Fuzail yace me yasa baka ce na rakaka zancen ba?yaushe zamu je? Tanko yace bazan je da Kai ba wlh Haka Kawai tana Dan ganin kyawuna ka jawo min ta daina gani Tace dama Kaine Saurayin nata,ba ruwana baza ka jawo min ba,sai dai na tafi da Sani tunda nasan nafi Sani Kyau,ai ba a tafiya da me kyau zance,Dariya Fuzail yayi yace shike Nan Allah ya tabbatar da Alkhairi,Tanko yace Ameen a sa Mana Albarka daga nesa.

Tunda aka fasa auren Tanko yasha jaje wajen abokan aikinsa.
Hajiya Kuwa a gidan ta kwana a dakinta tare da Yan uwanta Mata tunda bikin Yarta akeyi sai an Gama zata barwa Malam gidansa.
Washe Gari da wuri Belloti yace Amarya ta shirya zasu Kama Hanya,Duk iya kayanta na sawa da komai an shirya,Yana zuwa a bayan motar aka shirya komai aka rufe,Malam da Yan uwa sunyiwa Farida Nasiha daidai gwargwado,Har Hajiya an Mata fada yanda ya kamata sai kuka takeyi Haka aka sata a Bayan mota sabo da Belloti yace zai dauki Ubangidansa a gaba,shi kadai Yaja Amaryarsa Ana daga Mata Hannu Suka tafi,a Kofar gidan Yayan Uche yayi parking,Uche ya fito da kayansu shima aka sake lodawa a motar sai lokacin ya kula da mace,Bai San Belloti aure yayi ba,yace Me kanayi da Mata ga Wannan cikin mota? Belloti yace muje Zan maka bayani Oga,Uche ya Shiga karewa Farida kallo wacce ke lullube da mayafi tana shesheka,Shi dai Uche ba tare da yadda ba ya shiga mota Belloti Yaja Suka dauki Hanya.

Sai da suka danyi nisa Bayan sun hau babban Hanya Uche ya sake cewa cikin hausarsa da Bata fita we Ina Wana Mata za shi? Bana Gane ba,Beloti karka jawo nayi loosing Control baza kaji da kyawu ba ehem chike nan.
Farida kuka ya tsaya tana zare Ido,Matsiyaci Belloti sai da ya tabbatar sun shiga daji sosai sannan yace Amarya tace,aure aka Daura min,Uche yace I don't Understand you aure like how? Aure daka sani wallahi kaji karshen rantsuwar mu kenan,Uche yasan idan Belloti yace wallahi to da gaske yake, Hannu ya daura a ka Yana ihu yace ewoooo.....ewoooo.....tunda kayi ransuwar masallaci irin naku fa to fa nasan da gaske ne,Ke wannan yaro baka da ankali,ya Kuna aure Kamar wasan kanan kananan Yara? Yaushe ka fada soyayyar Belloti? Yaushe kasan Hali nasa? Aiki Nasa duk baka sani ba ka yarda just like that,yace Yana sonka ka Amince kace yes wannan yaro baka da ankali wooooo Hausa people wooooo,Farida ya sake juyowa ya kalla ta zazzaro ido,Uche ya sheke da dariya yace abeg no vex kaso mijinka wooo ba ruwana,bani Zana dau nauyinka ba Ina fada maka gaskiya ne baka Yi hankali ba,ko baka da Iyaye ne? A street ya ganka? Farida ta fashe da kuka Kawai,Uche ya Bude Baki yace I'm Sorry Baby sunanka Ummee? Belloti yace sunanta Farida,chaii da Ummee yayi Kama a hausa people,karka yarda da wani Farida kafi dacewa da Ummee,Uche idan ya kalli Farida sai ya kwashe da dariya yace zaka ci Ubanka yaro dakinku Daya tal a gidana.
Kidansu na church Wanda akayi da yaren Igbo Uche ya kunna,ya saki kidan ba Dadi Ana ta ambatar Jesus Ana gwalan gwalan din yare,Belloti duk ya iya wakokin sabo da Zama da su Uche sai bin wakar yake Yana tuki Yana shara uban wuta,Idan aka Ce Jesus sai ya daki sitiyari ma,Farida mamaki ya kamata,Sai ga Belloti ya zaro Wiwi ya kunna tare da furta Sorry Masta,Uche yace Miko min Daya Nima,Suka bulbule Farida da Hayakin Wiwi gashi sunki sauke ko glass,Farida dama ba kunya gareta ba Tace Dan Allah ku sauke glass kana uban shara gudu kana Jan wiwi ga Kun kulle ko Ina zaku sa min ciwon Kai ko tsoron mutuwa bakwa yi? Belloti yace kowa ya mutu kwanansa ne ya Kare Aljanna ta me Rabo ce Yana sheka dariya,Uche yace kai yarinya ka daina damuwa idan an mutu chike nan bacci akeyi me dadi a kabari ba Wanda zaiyi Disturbing naka, yana Kora wata Yar giya a karamar kwalba,Belloti yace ah Oga Ashe akwai ragowar Votka? Kwana Guda kenan ban Kora ba,ya motar kayan nan hope ba a Kama Mana ba? Uche yace Kaya suna Nan sunje tuni shi yasa na matsu mu koma akwai sabuwa an fitar da kwalaba karama Amma tafi ta Votka girma,Belloti yace Nice very very nice....akwai harka kace suka tafa,Farida taga ko kulata Basu Yi ba,Harkar gabansu Kawai sukeyi sauraronta ma basa Yi,Sai da aka Yi nisa Belloti ya juyo yace ke dama kina ciki ne? Ai na manta Dake wallahi,Farida ta harareshi tare da furta ta sama na tashi ai,karfa ka Raina min hankali wallahi nafika tijara,idan kanka Yana hayaki Ni wuta ke tashi a ciki,Uche Yana ji yace wuta na tashi a kanka zaka rasa gashi yarinya gashi wajen mace akwai Chau ,Tsaki Farida tayi Kawai,Belloti yace Zaki San kinwa uban gidana Tsaki Zan ga Tijarar da kika fini,wallahi kika min Iskanci a dajin Nan Zan tsaya na jefar dake,bana son Rashin kunya wlh ki kiyaye karki jawa kanki Baki Sanni ba bani da mutunci cikakken tantiri ne Ni,Bari muje gidan Zaki gani da idonki,ba wata Yar birni data Isa ta Raina min hankali yanzu,Aurenki nake Yi ki Lallabani ko ki Zama sakin Wawa kwananan Nan,Shuru Farida tayi Tace Amma kasan nayi maka Adalci ko zuwan farko na Amince na soka,da kika ga Baki da mafita ba ai dole ce tasa Kika aureni Amma da Wanda ya fini yazo ko kallona baza kiyi ba,wanne darene jemage Bai gani ba,wallahi duk abinda kikaga ya samu gafiya jelarta ce da ta Bari a waje,ki Lallabani mu zauna lafiya,bani da Burin zaluntarki ko Dan sabo da Manal,Darajar Manal zakici Amma idan kinyi Hakuri da abinda Zaki gani mun zauna lafiya,Ni soyayya nake bukata,idan Zaki min ba abinda bazan Miki ba,Bana Neman Mata shi yasa na aureki,Zaki ga abubuwa daban daban,idan kinji ki kinki gani mu zauna lafiya Idan kinki kince shishigi Zaki min Kuma jikinki zai fada Miki.
Idan Baki yarda ba idan munje sabon Hari ki Shiga cikin bariki ki tambaya waye Belloti,Sabo da Manal kadai Zan Dan dinga raga Miki.










Ina Matukar godiya masu sharhi.





AsmaBaffa
[1/1, 10:25 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭





DEDICATED TO
DUNIYATA AAMNA FANS GP







81-85






Official





By
AsmaBaffa






Page naku ne

Bilyn Nas
Nafee
Leela
Tajra lollipop
Mom Aneesah
Maryam Adamu
Teema
Malakso
Fatima Bature Ali Mmn Muh
Amina Baba






Tafiya sukayi me Dan Nisa Belloti ya sake juyowa yace kina ciki ne?Farida tsoro ya kamata tace Dan Allah mu koma a dakko Yaya Yazed muje da shi yaga gidan,Belloti yayi Dariya yace kin fara tsorata kenan? Kin manta Sanda nace Zan dakko muku motar haya guda daya aje ko da kawayenki ne Hajiyanki tace ai tunda nace baza a Kai kayan jere ba komai na zuba a gidana ba damuwa,in Bari daga baya za a hada dangi suzo suga gidan daban tunda ba a shirya ba,ba uban Wanda nake Jin kunya a danginki tunda an rigada an daura magana ta kare,Malam Yana cewa zai hada dangi a Basu mota ke da Hajiya kuka zakalkale Kuna cewa da su Annatu Yan Kauye za a tattara a Kai Miki gida zasu lalata Miki gida,akan a kwashi Yan Kauye suje sai dai a tafi Dake ke Daya,Malam yace shi Kuma baza aje da kawaye ba sai dai danginsa idan Baku Amince ba kibi Ango ke Daya,kika biyo Ni,ai ban Miki dole ba,in Banda ke shashasha ce ance Miki aure Wasa ne? Dan kin San gidan Iyayena Ni kika sani? Kuma a kauyen nake? Ke Farida ban San Baki da hankali ba sai Dana aureki ke da Hajiyan Taki duk kwakwalwar tinkiya ce da ku,a Haka Kamar wayayya Ashe banza ce ai gwara Yan kauyen da ke,ke a jahilan ma kinfi jahili Jahilci wallahi har kina da bakin zagin Yan kauye? Uban me kuka Tara? Nawa ne da ku?

Tasan laifinsu ne ita da Hajiya sukace baza a Kai musu Yan Kauye ba, ba bakin Kare Kai sai Tace an kusa zuwa ne? Belloti yace sa takalminki...Farida taga anyi tafiya tafi ta 1hr, Uche Yana wakarsa Yana cewa sa min wakar Emenyi Wanda yayi a France Church,Belloti yace wayyo kalbina wakar tana min Dadi duk da ba addini na ba,Baki Farida ta tabe tare da kwanciya a Bayan kujera ta rufe Fuska da mayafi,Belloti yasa Hannu ya dage mayafin tare da cewa gashi Nan nayi Budar Kai tunda ita kike bukata a dakko dangi suyi miki, kin rufe Fuska kamar Munafuka,Farida Bata ce komai ba,Uche yace Amarya kayi Chau,ka kula da mijinka wooo Everytime Beer,Consumer ne ni a Kira giya cewar Belloti,Waka Suka canja ta Yan Naija suna bi da bakinsu sun cika motar da Hayaniya,Farida a ranta Tace komai akayi da jaki sai yaci Kara,dama mutumin Kauye Ina zai waye,Belloti yaji tsakinta yace kwantar da hankalinki Amarya munyi nisa a tafiyar Nan bazan gaji ba Muna zuwa akwai Fresh Cucumber, sabo da Ni kin San Cucumber aka min ba Banana ba,Banana ta Yara ce ai ni Belloti Rabajas,ga katuwar Katifa sai ki juya sau Uku Baki Fado ba ba irin ta dakinki ba, Juyawa Farida tayi ko kulashi Bata Yi ba.
Suka ci gaba da tafiya yunwa ta kwakwule Farida amma Suka ce su baza su tsaya ba giyarsu ta ishe su,Farida Tace Dan Allah karku kashe mu a mota kuna ta Shan Kayan Maye,just Ordinary Alcohol ce fa Cewar Uche,Belloti yace Kai rabu da ita cocaine Muka Sha Dan Uwarki.

Shuru Farida tayi taga abin nasu ba arziki,Sai lokacin Farida ta tuna da Innalillahi wa innailayhirrajun....ga yunwa ga gudu bana Wasa ba,ga Shan giya suna ta tafiya faaaaaaaaaaa Haka Farida ta bude Jakarta kazar maganinta na Mata da Walida ta saka Mata a Leda Tace Kar taci sai sunje gidan Belloti yunwa tasa ta dakko abarta ta Shiga yaga tana ci tana Shan Malitinar Dake jakar ta,Belloti yace kaza Haka ba bismillah? Farida ta dauke abarta daga saman cinyarta ma ta rike a Hannunta sai da ta cinye abarta tas har Kashin sannan ta jefar da Leda ta goge Hannunta yace Kara wuta ja muje kowa ya mutu kwanansa ne

Please Login or Register in order to submit comment