Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koyi yanda ake abin itama Tace to,a gidan tayi wankanta sannan ta maida kayan jikinta, Haka su Shukrah Suka ebi nasu Suma Manal ta taho gida da abinta harda siyo lemo Cock da ruwa Faro.

Tana zuwa ta ebarwa su Hajiya Nasu sannan ta ajiyewa Yaya Yazed da Malam sabo da sunce suna Hanya Suma,ganin Magriba ta kusa Manal tayi sallar Magriba yanzu ta iya Sallah babu gargada ta koyi abubuwa da yawa na Boko Dana addini ba laifi sannan ta Dan goge an fara samun canji zuwan Shukrah ya jawo.

Cikin kayan da Shukrah ta bata ta dauki atamfa wata Brown and Black Yar dubu Uku da dari biyar ce Amma sabuwa duk wannan Shirin Ameer ne aka ce size ne ya yiwa Shukrah kadan shine ta barwa Manal,Dinkin Riga da skert ne,Shukrah Bata San Manal ma a Haka ake rainata Amma a jikinta tana da kauri kayan da kyar suka shige ta musamman wajen Kirjinta da Hips dinta ta cika su fam kadan suke jira jip ya Balle Kuma duk kayan kala Uku atamfofi sai lace Daya Haka dinkin yake Kai Daya,ta zuba kyau,cikin kayan kwalliyar nata da Shukrah ta Dan Bata ragowar nata ta shafa powder tare da zizara tozali kadan yanda Shukrah ta koya mata,Sai Maroon jambaki ta Dan shafa sama sama shike Nan ta hakura gudun kar ta Bata fuskarta,Dan Ragowar Body spray dinta ta Ajiye a gefe tare da dakko mayafin da Shukrah ta bata Guda Daya Baki da takalmi me Dan tudu Baki shima duk sababbi ne Amma aka rainawa Manal hankali Wai wani a kwance suke,Ita Kuma ganin kayan Yan Birni fes sai ta yarda.

Ameer ne ya sa Fuzail a gaba Yana ta dariya an Kira tela ya Gama auna size din Fuzail zai Masa dinkunan Shadda da yadika,Fuzail ya zabo colors da yake so kala bakwai,Yace Masu Araha nake so,Yadin ya zabi gaba Daya Ishurunka Maraya Shaddar Kuma me mugun Araha Suma Ana gani anga na talakan Dan gayu,Ameer ya dinga cewa Talakan Dan gayu,cikin shaddojin masu Araha tela ya dinka Kala Daya wata dark Arsh shima dinkin aka Yi shi wani na takakawan samari dai Amma yayi kyau musamman anyi shi dai dai jikinsa cif cif,tela ya kawo kala dayan Guess House yace sauran sai jibi Zan Gama dinkawa na kawo,Ai Kuwa tela ya washe ya samu kudi a wajen Fuzail da yawa,Babu Wanda yasan me su Fuzail suke kullawa da Ameer, Ameer yace ka taso muje na saka a Taxi wannan gyaran naka ya Isa Haka kayi kyau,karka fesa turare sai Dan kadan zaka goga,turaren ma marar kamshin kirki ya shafa kadan,aka Dora sabuwar Hular gashi Amma wannan gashin Bai Kai na farko yawa ba Haka gemu da sajen ma kadan aka kara sai yasa Face mask Kalar Shaddar tasa,Kyan da dinkin ya Masa ya Isa sai dai me Araha ne, Takalminsa yasa normal Black Slifas yanda ba Wanda zaice Yana da kwandala,Bakar ledarsa ya dauka da sakon Manal a ciki,Ameer ne yayi Driving nasa zuwa Gefen kwalta ya tare Masa Taxi sabo da shi baya son Napep Bai iya hawansa ba sai Dole.

Lokacin Farida ta fito da Kaya Niki niki a Hannunta tana gefen hanya gashi Ana wahalar mota ga dare Yana yi tana ta faman jiran Napep ko Taxi,Fuzail ya hangota a duniya baida wacce ya tsana irin Farida,tunawa yayi Yar Uwar Manal ce ko ya auri Manal sai ta dinga zuwa wajenta zumunci sai yace da Me Taxi ya tsaya ya dauke ta.

Farida Bata lura ba tana ganin Taxi Tace da sauran masu jiran mota ku taho mu shiga waccen ai Kuwa aka ruga da gudu,Farida ta Fada mota abinta Kawai kayan nata ta Dora a saman cinyar Fuzail yaji uban nauyi,Murya ya canja yace Malama kin Dora min Kaya,Farida da bala'i ta kalle shi sai taga Farooq ne,wani tsanarsa taji tare da Jan mugun Tsaki sai da kowa ya kalleta,ko a jikinta tace ka tarewa mutane waje a Ina kake so na Dora kayan Nan motar Haya ce idan kayi zuciya ka siyi taka,Tunda baka da motar ai Dole kayi Hakuri da halin daka tsinci kanka Malam da Allah Miko min Daya Ledar Nan, aka Miko Mata ta sake jibga Ledar a Cinyar Farooq,Ransa ya baci ya kusa loosing Control Kawai ya danne da kyar,Driver da Kansa yace Amma ke Baki da tarbiyya shi yace a tsaya a dauke ki Ana wahalar mota amma sai ki Masa Haka a mutane banza dakikiya dalla fitar min a mota na fasa daukanki.

Farida ta sake Jan Tsaki tace yo da ace nasan shine ma yace a dakko Ni ai bazan shiga motar ba,wannan banzar motar ma an fada maka Nan gaba wannan zata gagereni ne?kazo Nan da wata Daya nayi maka alkawari Ni Zan siya maka Motocin da Suka Fi wannan tsada na baka irinsu goma kaci gaba da haya a ciki kana kawo min balance,Driver ya Mata up and Down yace a hakan? Amma kike faman yawo a kasa da motar haya ke dalla fita Mahaukaciya gaja dake,Uwarka ce gaja ta furta tana fita a motar tana sani ta sa Hannu ta hankada Kan Prince Fuzail ba zato ji kake Kummmm....a jikin glass din Window, badan sumarsa ba da yau sai gefen goshinsa yayi kulu Allah yasa tudun gashin ya Dan tare kadan ya bige,Wajen ya Sosa tare da jinjina kai,Farida ta fice tare da banko Kofar da karfi,Driver ya fito Wandonsa 3qtr Yana sabulowa gaba Daya Rabin duwawunsa a waje yake tsabar tashanci shi ko Boxers baya sawa Haka yake barin Rabin Duwawunsa a waje,Matakan tsaro Indai Suka gani sai sun Masa nasiha Amma yaki ji,Haka ya fito tare da tsayawa a Gaban Farida yasa hannu a hantsar Wandonsa ya tattaro gaba Daya harda Sandar girman tasa yayi sama da su ya samu Farida ya kwada Mata Mari yafi biyar sai da aka rike shi da kyar amma har yasa kafa ya fatalar da ita gefe zai taka Mata ciki aka rirrike shi,Fuzail ya gyara kwancinyarsa a mota Yana kallo Yana Jin Dadi.
A ransa yace Inama yarinyar Nan tasan waye Ni na samu nasa a kaita a garkame shegiya a prison na gidan sarauta kullum ta dinga kula da dokunan gidan Sarki gaba dayansu duk yawansu wallahi har wanka sai ta dinga musu tana brushing musu jiki.

Driver ne ya shigo motar ya bar Farida a gefen kwalta tana tsala ihu wasu da Basu San me ya faru ba suna ta Bata hakuri aka sa ta a mota,a ranta tace wallahi akan Manal Zan Rama zaka gani yau Indai can zakaje wallahi Nima yau sai na Bata maka Rai shege da shaddarsa Yar Dubu biyar talakan banza.
Driver Kuwa passengers suka cika a motar aka matse Fuzail Dan sarki Guda a lungu yana manne da Jikin Kofar mota numfashinsa Kamar zai dauke ya Saba idan a turai ne duk inda zaka je a taxi to Kai kadai za a dauka komai nisa,a Nan dinma Farida ce ta jawo masa wajen Kiran sauran mutane suzo ga mota.

Ga goslow kafin azo ma ya Gama jigata a mota Shaddar tasa duk ta yamutse,Ana zuwa ya mikawa driver 1k zai bashi canji yace barshi Kawai,Driver ya dinga godiya ya wuce,da bakar ledarsa ya karaso Kofar gidan su Manal wacce lokacin ta Gama shirinta tsaf,Falaqi Yana waje ya Gane Farooq da gudu ya shiga gidansu Yana kwalawa Manal Kira ga Wannan mutumin Nan da kika taimakawa me gashi da yawa,Manal a fili Tace baiyi Aski ba kenan,Mayafinta ta yafa tare da lekowa ta hango shi Kuwa a gefe yayi wata tsaiwa ta manyan Yara a tsaye an harde kafa,Manal ita dai wankan Nan ya Gama tafiya da Imaninta Allah sarki Bata Raina ba ai ita gani tayi ma ya Gama kure karshen wanka a duniya,sai da ta Kare Masa kallo sannan ta fito gaba Daya tana takawa inda yake da kyar take tafiya sabo da Bata Saba da sa Kaya damammu ba,bayan Haka ma sun so suyi Mata kadan,Fuzail sai kallonta yake yanda ta zuba kyau Kamar a sace ta a fece,Shi Bai ma San ta Kai Haka ba sai yau,har kunya taji yanda yake Kare Mata kallo a ranta taji Dadi tasan ta Gama haduwa tayi kyau tunda ta Zama abar kallo a Wajensa da duk Wanda ya kalleta.

Tana zuwa gabansa yace Sannu da zuwa Kareena Kapoor Yaya su Salman Khan suna lafiya dai ko? Dariya Manal ta dinga Yi tana boye Fuska Tace wannan ai tsokana ce.
Daga soron gidan nasu ta shimfida musu Tabarma ya zauna shi dai Yana kallo ta kawo Masa kayan ciye ciye yayi mamaki dama ta iya irin wannan snacks haka,ta kasa magana sabo da kunya sai Dariya takeyi ita kadai ta rasa inda zata saka kanta,Yace ya akayi ne wannan murmushin fa? Manal ta sa Yatsa a bakinta tana ta faman gwigwiya,Hannu yasa tare da zare Mata Hannun yace sai kin cinye min yatsan Kuma? Dariya ta sake Yi tana daga zaune tayi kasa da kanta,Yace Ikon Allah,Ina kwana au Ina yini ta furta,I'm Good and you? Tace Alhmdllh,Kinyi kyau fa yarinyar nan,idan Baki aureni ba kika yaudareni sai mun koma makiya da ke,Manal ta kyalkyale da dariya tace Haba dai ai bazan yaudareka ba,Idan Malam yace bazai bani ba fa? Manal tace karma ka Fara Malam bazai hanaka Ni ba Indai Ina so,to a gidanku basa kaunata da wa Zan Kama kafa? Manal ta nuna kanta da yatsa Tace ai Kai ka Riga ka Kama dahir ba ruwanka da wani kamun kafa.

Yace Farida fa Wai me na Mata ne? Karfa ta kawo cikas a aure na dake? Manal tayi yanda Yan tauri keyi ta Kai wani Suka gefe Tace akanka Zan iya sara Suka,Dariya ta bawa Fuzail Suka dinga dariya,a ransa yace kallo ya bar Ameer yau.
Ledar hannunsa ya Mika mata,Tace Mene? Bude ki gani mana,tana budewa taka wata sabuwar Wayar Tecno spark 5 wacce ta ninka waccen tsada da komai,Baki ta Bude tare da tambaya Ina ka samu kudin? Na siyar da gonar gadon ai an tura min kudin shine naji Wayar Taki ta lalace na canja Miki wacce ta fita tsada,Manal tace to Kai Kuma fa? Shi Kuma ya nuna Mata wata Vivo karama yace ta isheni nafi damuwa da ke nafi so Naga matata ta fito,Manal Taji wani kaunarsa sabuwa, ta shiga jero Masa godiya da adduoi,wacce ta lalace ta Mike zata dakko Masa ya bi Bayanta da kallo yanda ta dame komai ya fito,Fuzail a ransa yace wow Zan huta,Amma wannan Shukrah ta dame min Baby da yawa za a rabawa maza a titi su gani Ina bazai yuwu ba Dole a Kara Size din Ashe katuwa ce haka.

Wayar ta kawo Masa yace me zanyi da ita ki siyar da ita idan za a siya ki kashe kudin,Fafur Manal Taki yarda Wai sai dai ya tafi da ita Dole ya karba,Lemon ta Bude Masa ya karba ya Sha Yana cin snacks din yaji Dadi yace ke kika Yi? a Ina kika koya? Manal tace ai kawata ce Shukrah da Mamanta suka koya min,Kai ya jinjina yace wow yayi Dadi kina da brain,kaci da yawa Kai nayiwa akwai wani ma da yawa nayi zaka tafi da shi kaga sai Ameer ma ya ci da Dan uwanku,Thanks My love,Murmushi tayi Kawai yace Haka Zaki ce You are welcome,idan ance kinyi kyau kice Thanks,Manal ta amsa da to,Karar Napep taji a Kofar gidansu Tace Ga su Yaya Yazed Nan ma na sani...kafin ta rufe Baki taga keken Guragu Yazed ya turo Malam a kai,Manal Tace ba a Dace ba kenan,magani baiyi ba,suna shugowa sai taga Malam Yana sarrafa Hannunsa yanda yaga dama ba irin a baya ba,Manal mikewa tayi da sauri cike da kunya Wai tana zance da saurayi an ganta.

Yazed ganin bako tare da Manal yayi mamaki ko a waya Bata taba bashi labari ba duk surutunta,Sallama Malam Yayi Fuzail da sauri ya zube gwiwoyinsa a kasa ya Shiga gaisar da Malam Yana Masa ya jiki,Malam ya amsa da fara'a da sakin fuska yaji Hausar Kuma ta saurayin Bata fita da kyar ma yaji wani abin,Fuzail Mikewa yayi tsaye tare da mikawa Yazed Hannu,Yazed ya karba da fara'a Suka gaisa ya Masa ya Mai jiki ya amsa da sauki,Manal tana ta murna Fuzail ma Haka ya samu Shiga.

Manal ce tace Yaya Yazed yau baka rike min ko Hannu ba ka daina so na ta furta da shagwaba,Murmushi yayi kawai,Malam shi tuni su Falaqi Suka fito da gudu Suka gungura kekensa cikin gidan,Manal Hannun Yazed ta rike Tace Yaya kayi kyau Kamar ba Kauye kaje ba kalli yanda kayi Dan kumatu ta Kai Hannu zata taba da wasa yace Zan mareki,Uhmm Yaya baka min fada ba kaga Ina zance,Ya zanyi Dake Manal idan na hanaki zance Ni Zan aureki? Ciki ya shige ta bi bayansa zata tafi,Fuzail ya sa Hannayensa a hips dinta tare da jawo ta baya da sauri,Sai ga Farida ta shigo da kayanta fuskarta ta kumbura,taga shigowar Su Malam shi yasa Bata saurari su Manal ba ita ta tsaraba takeyi tukun Amma ta tabbata kafin Farooq ya tafi yau sai ta Kona Masa Rai.

Tana shiga gidan Malam Kawai ta gaisar a tsaye tace babu Yar Ayabar Hanya ne? Ko Dan Orange,Sa'iha Tace Aunty Kinga Malam Hannunsa yanzu Yana komai Yaya Yazed ma yace Yana Dan takawa da kafafunsa kadan kadan,Farida tace Good Haka ake so Ina tsarabar? Harara Malam ta gasa mata tayi Shuru.

Hajiya Kuwa ta rasa inda zata sa kanta sabo da Murna Dama ita kullum Sha'awa ce ta dameta gashi Malam baya nan shi yasa take murna tunda ya dawo zai biya Mata bukatarta ba Wai lafiyarsa ce ta dameta ba, Manal tasan yau ta Gama tafiya da Imanin Fuzail yanda yake nacin kallonta, yace je ku gaisa da su Malam sai ki dawo,Kida sukaji ta cikin gidan Farida ta kunna Blootooth speaker a dakinta ta cika gidan,Malam yasan ko yace ta rage baza ta rage ba,Yazed ma ko ta kanta baibi yasan Bata Jin magana Manal ta Mike tare da juya baya zata shiga gida abinka da karamin gida sai kidan ya cika ko Ina har waje Kamar kayi rawa,Manal kidan taji me Dadi gashi yau a cikin murna take step daya tayi tare da juya hips dinta a Gaban Fuzail tayi cikin gida ko juyowa Bata Yi ba,Fuzail Kansa ya Kama kaikayi sabo da yanda Manal ta tafi da Imaninsa ya nutsa a hannunsa a cikin sumarsa me uban yawa ya Sosa sai yaji Kamar Bai Sosa ba ya sake sosawa Karo na biyu sai lokacin ya tuna Ashe hular gashi ce a kansa,Murmushi yayi tare da daukan ruwansa me sanyi ya kwankwada ji yake kamar Kar ya tafi ya bar Manal.

Dakin Malam ta shiga tare da durkusawa ta sake sabuwar gaisuwa Tace Malam ya jikin? Malam da fara'a yace Alhmdllh ai Hannuna yanzu Ina sarrafa su sosai sannan tafiya ma Ina Dan takawa kadan me maganin yace a hankali Zan dawo dai dai,Manal ta dinga Murna,Baba yace Manal Ina kika samo wannan me gashin Haka? Bai Jin Hausar ma tamu fatan ba Arne bane? Dariya Manal tayi a kunyace tace ba Arne bane Malam Dan Niger ne yazo Nan na Dan taimake su ne lokacin da sukayi hatsari shine muke mutunci,Malam Yayi murmushi yace Uhmmmm a Haka sai na ganshi Kamar Yana da nutsuwa da sauri Manal tace sosai ma Sai ka zauna da shi ma,ai kasan Malam wallahi Hankali ne da shi,Ni Indai bana kirki bane ma ai bazan kula shi ba,Malam yace gashin nasa ne yayi yawa,Manal tace yo ai liman ne a unguwarsu Malam,Dariya ta bawa Malam yace a Ina kika sani? Kuma Liman ne zai hada Suma a Kansa haka? Yo Malam ai koyi yake da Larabawan Madina,Malam yace Hakane dake a Madina aka haife shi ko? Kunne Manal ta Sosa tace idan an tashi auren ba sai ayi Bincike ba kuji,Baki Malam ya bude yace au kika ce mutunci kukeyi, Malam Allah mutumin kirki ne ko a addini ka kirashi kaji sai Kun tafka mahawara da shi nasan ma shi zai lashe Mahawarar, Ma'ana dai kina sonsa Ko? Karatun fa? Nayi ko secondary ce a dakinsa bayan aure sauran jami'ar na karasa abata a kitchen,Malam yace dama na lakanci bakya son Ilimi Manal mazan yanzu wallahi idan Suka lallaba Suka kaiki shike Nan kin Zama nama,Mikewa Manal tayi Tace Malam ka huta kayi wanka kunyarka nake ji ni ta fice fit Dan Kar ma ace ta hakura da Aure.

Tana fita taci Karo da Yazed ya gasa Mata Harara Dariya tayi tasan zancen ya ganta tana zance yafi so tayi karatu wajen Fuzail ta koma abinta Suka ci gaba da Shan Hira,Fuuuuuuuu Farida tazo ta wuce su sanye da Hijab dinta.

Tana fita wajen wani tantirin abokinta Me suna Yahaya Uban daru ta je, Hannu ta Mika Masa Suka tafa a bainar jama'a ga hasken wuta a wajen,Yahaya Yace Yan Mata ya akayi ne? Akwai labari uban daru Zo mu wuce ta wani dafa kafadar Yahaya suka Yi gefe can Suka Gama zancensu suna Yi suna dariya suna tafawa,Farida ta koma gida abinta 9pm Fuzail ya karbi Snacks dinsa zai tafi gida sun fito da Manal zata raka shi Yahaya Uban daru me takama da Rashin kunya yazo har Gaban su Manal ya tsaya Manal ya kalla tare da kashe Mata Ido daya Baby ya akayi ne,Ran Manal ya baci ita Bata sanshi ba ma,Tace na sanka ne?Murmushi Farooq ya saki yasan Farida ce Kawai ta hada,Fuzail ya kalli Yahaya yace Kai Kuma fa? Yace Yahaya kenan ko baka taba Jin sunan ba? To suna ne Wanda Allah ne ya rada shi da kansa,Ya fadawa Annabi zakariyya zai haifi da Dan Kuma sunansa Yahaya,
Fuzail ya danne Dariyarsa yace to ai ba yahayan gaskiyar bane,ai ba Kai aka radawa ba mutum me daraja aka radawa,Wanda aka radawa sunan daban Kai photocopy ne, a photocopy din ma Kai photon-photon-photon copy ne sau dubu dari dari ma na gaske kuwa,Ba Manal ba Har Yahaya Dariya ya koma Yi Kamar me,Ba musu yace gaskiya ka fada tunda a wancan zamanin Ana ta yin masu suna Yahaya na kirki suna shudewa har zuwa wannan zamanin da muke ciki Kuma Ni a cikin wannan zamanin ma cikakken Dan Iska ne ban gaji me sunan ba,Manal tace Kai ka sani Kuma.

Yahaya Uban daru yace shike Nan ke Manal Saurayinki ya bani Dariya na hakura na bar masa,Hannu ya mikawa Fuzail,Fuzail ya Mika Masa Hannu Suka gaisa yace kayi Murna yaro da kasan waye yau sai ka kwana baka Yi bacci ba,Yahaya yace karka min kuri Malam Dan na hakura ka samu bakin magana,kasan me aka turo Ni nayi Kuwa? Fuzail yace sai ka fada.

Yahaya yace cewa akayi nazo Kawai na rungumeta a gabanka, Kawai kwar jini tayi min kaima Dana kalleka naji idea ta gaba Daya ta gudu,Fuzail yayi dan gajeren murmushi yace Allah ya rufa maka asiri baka aikata ba wallahi kaji Ina cewa rantsuwa ko sai kayi Prison,batar da Kai zanyi sai an manta da Kai a duniya,Dariya Yahaya yayi Yana ganin Karya ne kuri Kawai Fuzail keyi yace shegiya karyar samari ba a Gane mun iya karya sai Muna Gaban Budurwa wannan karyar taka ta hau wallahi Ni ka Zama abokina ma daga yau ga Hausar taka sai a slow Wai Ina cewa Rantsuwa hhhh uban daru ya sake dariya,Fuzail Kuwa ko murmushi baiyi ba Kallonsa Kawai yakeyi,Yahaya ya sake mikawa Fuzail Hannu Suka tafa yace shege mutumina da Allah Indai kazo ka tabani ko ta wajen zamanmu ne ka gashi can muje na nuna maka wajen, wallahi kayi min da gaske nake ka birgeni Haka Kawai naji kayi min,Fuzail yace na gode Yana mamaki yanda ya girmi Yaron amma sabo da ya ganshi ba kowa bane harda wani maida shi sa'ansa Wai shege mutumina,Kai ya girgiza Kawai Manal ta Masa rada a kunne kayi Hakuri,shima da rada yace Soyayya ta jawo min Ina cin ubana a garin Nan Gaskiya,Dariya suke ta yi,Yahaya yace style din gashin Nan naka ya birgeni kaga Nawa Ina ta tarashi Dan banza Taki taruwa gaba daya,Gaskiya wankan Sumar Nan taka yayi Nima irinsa zanyi Verysoon,Fuzail ya tsaida Manal yace koma gida to can maza ne,Kana zuwa gida ka kirani kaji?yace to Kuna da wuta kinsa Wayar a charge? Tace ae tare da juyawa tayi gida abinta.

Shi Kuma Suka tafi da Yahaya,suna tsaye zai shiga taxi Motocin Maimartaba sarki sukayi parking da sauri kusa da Fuzail ko a jikinsa yasan babu Wanda zai Gane shi,Yana mamaki me Sarki zaiyi a Nan sai yaga wasu Motocin Suma da yawa sun tsaya Gaban Motocin sarki Sai lokacin ya Gane Ashe Babban Aminin Mai martaba ne Gomnan Kano,Yahaya yace Uhm Harkar ta manyace Allah ya Isa kudin mu a kasar Nan ba Wani me gaskiya Kawai zaluntar mu akeyi.

Kaga Tsinannun sarakunan Nan Suma mugun yashe kudin kasar Nan sukeyi,ai ba azzalumai irin sarakuna wallahi daga su sai yayansu,gasu da tsumulmula basa kyauta Yan Bura.....Fuzail Yana ji yace ai Basu da kirki Sam,Yahaya yace ae Mana Yan Iska asararru muna fama da yunwa kalli Motocin da suke Hawa matsiyata,gasu duk mazinata ne manema Mata sai bariki Suka iya,Fuzail yasan har ubansa aka hada sai yace a dinga Yi musu Addua dai yafi,Uban waye zai Bata lokacinsa wajen Yi musu addua? Yau dan Uwa da kyar Muka ci abincin Rana Ni da Kaka ta,Kaga Sai nayi sati ban rike dari biyar tawa ba,ba Dole mu haukace ba mu tada Hankalin kasa,wallahi Dole na Shiga kwacen Wayar mutane a titi,Baki Fuzail ya Bude yace Amma kake zagin shugabanni bayan kaima bana kirkin bane? Dan Uwarsu ai su suka koya Mana,Ni wallahi ma duk nafi tsanar Yan masarauta musamman wannan Sarkin namu ya fiye son Kai,daga shi sai yaransa,Shi idan ba Wani bane ma a kasar Nan ko Mu'amula bayayi da mutum bare taimakon talakawa sai dai a siyar Mana da filaye da gonaki yaransa su Shana daga shi sai su,Haka yaransa Yan Iska ance basa ganin kowa da kima sai Dan sarauta,su duk kudinka ma Matukar baka gaji sarauta ba babu ruwansu da mutum.

Fuzail yace Allah? Wallahi cewar Yahaya ai wani Dansa da aka Haifa a turai ko Fuzail yake ko wa? Shi ance Daban yake ba ruwansa da wannan Sarautar da wani iyayi,safgar gabansa yake Yi kawai ko Sarkin ma Bai Isa yasa yayi wani shirmen sarauta ba,ba ruwansa guy din Yana birgeni kaga dai ban taba ganinsa ba ko? To Ni labarinsa Kawai yasa naji ya min a rayuwa,Kai da Zan ganshi ma wallahi sai mun gaisa da shi Dole duk yanda zanyi mu gaisa sai nayi Hannu da Hannu da shi,Fuzail a ransa Yana ta dariya sai ya mikawa Yahaya Hannu yace mu sake gaisawa ai gani a madadin Dan sarki,Yahaya ya sheke da wata Dariya yace Kai dalla matsa wa yake takai Kai Nifa wankanka ne Kawai ya min sai fatarka da gani kana kula da ita,Amma ka Isa ka Kama kafar Fuzail.

Fuzail Yana dariya yace wallahi karka sake cewa wanka na ya maka ko skin Dina sai kace wani Dan Gay dan Luwadi Zansa a maka duka,Yahaya yace a'uzu iskancina Bai Kai Nan ba wallahi ba nufina kenan ba Kawai Ni ka Gane Ina son Dan wanka ne ba Wani Abu ba,karka Bata min Rai da Allah Malam,Fuzail ya sake Bude Baki da mamaki yanda Yahaya yake cin ubansa a ransa yace Bai San waye Ni ba babu komai.

Suna Haka sai ga sarki da Fadawa an lullubeshi zai shiga mota,Yahaya yace kalli da Allah asararru sai kace wani

Please Login or Register in order to submit comment