Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake yunwa zata halaka yarku Kuna ganin dama kanta Kamar ludayin miya ba ruwana cewar Hajiya Sharifa tayi ficewarta.

Tana fita Manal ta kakaba Hannu zata curo nono ta saman Riga Prince yace No....karki Fara wannan ai rashin sanin darajarsa ne salon ki lalata shi Ni na rasa ba asararki,ki cire rigar Nan tunda Bata da zif,Ga yarinya sai ihu take har sai da ta cire Riga ta saka rigarsa me botin a gaba ta Bude sannan tayi Bismillah ta fara bata,tana Fara Sha tayi Shuru,Sai da ta Sha da yawa sannan ta juya ta Sha Dayan,Manal Gyangyadi ta shiga Yi zata saki Yar a kasa , Prince da sauri yace na shiga Uku 'yata ya taso ya tare wajen da sauri Manal ta Bude Ido yace Dan Allah ki tsaya baccinta yayi nisa kinga har tayi bacci Saura kadan ki jefar da ita,sai da yarinyar baccinta yayi nisa sannan ta kwantar da ita itama ta koma gadonsu Fuzail yace ko za a dawo da ita nan sabo ta danji duminki? to ai ba kyau ka sani Sai a sata a gabanki sabuwar Haihuwa ce idan tayi Yan satikai sai a maidata bed dinta,Dakko Babyn yayi ya dawo da ita Gaban Manal Suka kwanta.
Garin bacci Saura kadan Manal ta danne jaririyar Allah yasa Prince ya farka zaije toilet ya gani da sauri ya dauke yarsa tunda Manal kuruciya ta Mata yawa yana Fitowa a toilet ya maida Babyn gabansa bayansa,Cikin dare Manal ta koma ta makaleshi ta baya .

Yazed Kuwa washe Gari Bai tashi da wuri ba kasancewar bai samu bacci da wuri ba tunda yayi Sallar Asuba ya koma baccinsa,har Raheela ta fito tare da gyara ko Ina na gidan ya dauki sheki da kamshi tana Niyyar Shiga kitchen sai ga Afrah Wato Masatura da Abinci inji Hajiya, Raheela tace Afrah ce shigo Mana,Afrah Tace sauri nakeyi gyaran gida mukeyi ki Gaida Yaya ta juya ta tafi abinta,Raheela Tace na huta har Ina Shirin hada breakfast, Bedroom ta koma Ta da sheka wanka ta zauna ta tsara kwalliyarta me kyau ta shirya cikin wata atamfa sabuwar Riga da skert,tana Fitowa shima ya fito ya dauki wanka Yana sheki,kallonta ya Shiga Yi itama Haka ya fita ya Mata kyau yard din ya Masa kyau,Ina kwana Tace Masa da fara'a yace lfy Alhmdllh ya kika tashi Tace Normal,Hajiya ta Aiko da breakfast,kin huta da girki kenan tace wlh muje ka gani,tana gaba Yana binta a baya har Dining ya duba yaga Chips ne da doya da kwai ga tea da sauransu tana Buda Masa Yana Bayanta Kamar zai shige jikinta kirjinsa Yana gugan gadon Bayanta,wani Shock suke ji Dukkansu,Da sauri ta juyo suna facing juna a hankali ya furta I love you,Shuru tayi yace Baki ji ba? Tace ae,yace I love you ta sake yin Shuru,yace ko bakya ji ne? tace me kace? Ya sake maimaitawa I love you,Ina sonki Ina kaunarki,Banga Alama ba tunda Ni baka nuna min,Ido ya zaro tare da cewa I'm Sorry wallahi Ina sonki Kawai ban taba Yi bane shi yasa nake Jin kunyarki Ina pretending.

Kawai boyewa nake Yi Amma kullum kina Raina,karfa Nan gaba ka dawo kace Magenka ce Tace Dariya yayi yace Wasa nayi Miki ai kema ya kamata ki San nine ba mage ba, nasan kinji ba Dadi kiyi Hakuri duk abinda kike so zanyi ko Mene ki daina shareni please,bana so Naga kina shareni kina Fushi Dani sabo da Ina sonki yasa na aure ki,duk abinda kike so Zan Miki shi ko mene,Kawai Bari nayi Ni sai na aureki sannan zan nuna miki wanne Kalar so nake miki ba Wai nufina ban damu dake ba ki gane,Raheela tace na gane,to Baki ce kina so na ba? Ina sonka,so Kawai ba kauna? Ina kaunarka Honey kafin ta rufe baki Rungumeta yayi a nutse,Yana Shirin kissing dinta ta zille tare da cewa yunwa fa?

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya zauna tayi serving nasa,Bai tsaya cin nasa ba ita ya dinga bawa a Baki tana ci Yana wani lallabata sai dadi take ji a ranta, har suka Gama suka koma Palo ya kwantar da ita a jikinsa, da wayo ya jata bedroom dinsa Suka kwanta a saman bed daga Nan Kuma ya fara canja salo,Ya fara shafa Mata jikinta Yana shafa gashinta,Kissing juna suka shiga Yi Kamar me tana tayashi suna makalkale juna har Suka raba kansu da kayan jikinsu, Albarkatun kirjinta ya Shiga murzawa gaba Daya ya sake rudewa Yana Mata maganganu barkatai kalaman kaunar data jira taji duk ya Gama fada Mata su yau,tunaninta sai dare zaiyi sai taga Yana lalubar Hanya Duk da gushewar hankalinta sai da tunaninta ya dawo jikinta,kamar zata Yi kuka tace Dan Allah ka barni haka, Yazed yana kokarin buda kafafunta da take mannewa yace Dan Allah ki barni na samu nutsuwa please Baby ki bani sweet Shawarma,Haka ya marairaice Kamar ba shi ba Yana roko a bashi Shawarma,Ba yanda ta iya Haka ta bashi Shawarmar ai Kuwa taga hauka Kamar Dan giya,Bata taba zaton zai iya Haka ba yanda yake ji da Kansa sabo da ba Wani Babba bane Yaro ne,Amma sai ga Yaron da take fada ya Bata mamaki taci wahala tayi kuka ta gaji.
Kamar wata kwai Haka yake lilitata har wani kukan shagwaba take karawa.

Manal tun daga wannan ranar da jaririya suke kwana tunda ba
abinda zasu yi,Ummi ta sauka lafiya taga jaririya wannan lokacin Bata takura musu ba sabo da Maimartaba yayi Mata fada,idan tazo ganin Baby sau Daya Bata dawowa tana part dinta ko Fuzail sai dai yaje can,tun kafin Suna Ummi ta maida Manal da Hajiya Sharifa Suka koma part din Manal sabo da Rashin kula da Baby da sukeyi ita da Fuzail shi yasa dole Ummi Tace sai dai Manal ta dinga kwana tare da Sharifa kafin Arba'in ta koyi yanda ake kula da Jariri,Prince yaji haushi amma Haka ya danne fushinsa Kawai sai dai yaje can shima ganin Baby, matan sarki sun cike hudu cuf, Manal taga dinkuna na hauka wajen Fuzail kusan kayanta na sawa ya canja Mata,Jaririyar ma Kaya har fada aka Masa ga na dangi a abokan arzuka kowa da nasa kyautar, har ranar Suna tazo a iya gidan Sarki Kawai ne aka Dan Yin shagali amma ba Wani taron suna an hutar da kowa sakamakon bukukuwa da aka Sha yarinya taci sunanta Minal Haka Kawai Fuzail ya zabi sunan,Sunan matarsa Manal yarsa Minal,raguna Uku da sa Kato aka yanka Yan Aiki sunsha suyar nama,Naman sai da Manal ta aikawa Annatu me shegen yawa,ta aikawa Malam nasa daban,nasu Hajiya da Kannenta daban,na Yazed daban an Kai Masa me yawa Haka Farida har Uwa duniya aka Kai Mata.

Sati biyu da Haihuwar Manal su Annatu,Malam da matansa,Mijin Annatu,Farida,Belloti,Tanko Islaha gaba daya suka keta hazo Maimartaba ne ma ya biya a aljihunsa ba Fuzail ba,Manal kam ba zuwa school ta Haihu Amma ko me aka Yi a school har gida Kawayenta ke kawo Mata ta karanta,a hankali Baby sai girma takeyi tana kiba tayi wani wayo,Hajiya Sharifa ke kula da komai,sati biyu da kwana Uku Manal tayi wankan tsarki jini ya dauke,tunda ta Haihu take Amfani da kayan gyaran jiki Hajiya Sharifa sai tsumata takeyi,Farida ma tana Aiko Mata Kamar sabuwar Amarya, ba dama Manal taje part din prince sai suce Taki tsayawa ta kula da Baby ita Kuma Manal tasan halin Fuzail da maitar sha'awarsa,Suna waya da Farida tace kisa Shukrah ta Miki planning wallahi idan ba Haka ba kafin ki yaye Minal kin samu cikin wata,Manal tace ke Ni bana so na hadu da matsala shi ya dinga Releasing a waje,Farida tayi Dariya Tace ki siyi condom to ki bashi Kawai,Manal tace to,Manal harda siyowa a sirri kwali Guda.

Da dare tana dakinta Hajiya Sharifa tana kwance da Minal sunyi bacci ma da wuri yau,tunda Manal ta samu tsarki take sha'awar mijinta kamar me sabo da Magungunan tsumin da take kurba,tayi wanka kenan ya leko dakin tare da komawa palo,a Haka ta fito daure da towel tana masa Sannu da zuwa,Fuzail ya Zama Kamar maraya Baya Jin Dadi an hanashi matarsa ko rage zafi Bai da damar yi,Manal Tace me zakaci?,Binta yake Kawai da kallo kamar maye,Hannunta ya rike tana tsaye yace Sunshine har yau Baki tsarki ba? Manal tace laaaa nayi tsarki tun shekaran jiya mantawa nayi ban fada maka ba,Kin dauki hakkina hakurina ya kusa karewa romancing dinma kiyi min an hanaki Kuma kin biye musu,Ummi ce fa da kanta prince ya zanyi da ace na bangarena ne Zan iya bijirewa amma taya Ummi zata ce Kuma nace a'a Kai kanka ai Haushina zaka ji,Kamar yanda Zan yiwa Annatu haka zanyiwa Umminka.
Me zaka ci ta Furta tare da Zama a saman cinyarsa,Ke ya furta,Dariya tayi tace nifa me zaka ci nace,Yace ae ai Nima nace ke, naci abinci wurin Ummi yanzu,Manal Tace Allah sarki Prince Dina,Dariya yayi yace Saura kadan na fara kuka,gashi kullum kiyi ta cin kwalliya Ina kallo,sai kiba da kyau kikeyi,Prince mikewa yayi ya ja Hannunta,ta tirje kamar baza ta bishi ba ya Fisgi Hannun nata Suka fada wani bedroom,suna Shiga ya zame Towel din ya jefar Manal tace ka sa key Kar a shigo kaga 8pm Kuma ba part dinka bane fa,Key ya saka Gam.

Har tsoro ya ba Manal yanda ya rude ya haukace Mata Yana Murzata nutsuwarsa ta gudu kayan jikinsa ma sabo da rudewa Yana ta kici kicin cirewa sai da Manal ta taimaka Masa tana Dariya, bakinta ya cafka ya shiga Sha kamar me, saman bed Suka fada Manal ta zage tana Masa abubuwa masu nauyi yanda zata jiyar da shi Dadi,condom ta Mika Masa tare da cewa muyi planning My love Kar na samu wani cikin ban yaye Minal ba,Fuzail yace Allah ya kiyaye Ni banyi Niyyar planning yanzu ba so nake ki sake Haifo min daya sai ki huta amma daga yin Daya Ni ban yarda ba,kuma ma Condom Zan sa nida matata bazan ji dadi yanda nake so ba,Manal kuka zata Masa yace shiiiii....Kawai yaci gaba da sarrafata tana so ta gudu amma ta makara tuni ya samu ya shigeta yaji ta matse Gam Gam,ta matse da yawa kamar Virgin,ita kanta sai data ji jiki,garin tsotsar Albarkatun kirjinta ya zarce da shanye ruwan Nonon Jaririya,Manal ya dinga jajjagewa son ransa Yana sambatu yaji wani matsanancin Dadi data kara na musamman,sai data ji Dan jiki yau a hannunsa,amma ta shayar dashi sweet na mamaki,sake gigicewa yayi a kanta,sai yabonta yake Yana Kara nuna Mata so,Toilet Suka fada Sai da suka tsarkake kansu tare da sake sabon wanka sannan Suka fito,ya shirya ya maida kayansa sannan ya manna Mata kiss a goshi tare da furta Good Night,I love you,Love too ta furta thanks yace suka fita ya wuce part dinsa Manal ta koma daki wajen Sharifa,Hajiya Sharifa ta farka tace har yanzu Baki shirya ba Ina kika fita? Manal tace lna kitchen na tafasa wani magani,Hajiya Sharifa tace yawwa ai gwara da kika nutsu Kinga muna tare har 2months bake ba samun ciki da wuri,Manal tace ai Kuwa dai hakan yafi ta barta Nan.

Tun daga wannan Rana kullum Fuzail sai yazo da dare,Hajiya Sharifa tana yin bacci Manal zata fadawa Fuzail a waya sai yazo su shige wani room su kwashi love,Hajiya Sharifa har mamaki takeyi duk Nacin sintirin Fuzail yanzu baya shigowa sosai Haka Manal ta share Harkar gabanta takeyi.

Wasa Wasa har Manal tayi Arba'in lokacin Kuma ta koma tana zuwa school,a gida take matse nono a feeder a saka a flask kafin ta dawo Baby Minal tana da abincinta,ganin an hanashi sakewa da matarsa yace Abuja zai koma da ita gaba Daya,Ummi ce tace ka Bari Yan uwanta su dawo daka Saudiya sai ku tafi tunda sun kusa, Farida ita kuwa a kasa me tsarki ta fara laulayin ciki Belloti sai murna akeyi yace Haba gaskiya Mana naji Kullum Injin Dap Kamar ana Masa juye,maza ki dinga Shan Zamzam da yawa Jariri ya samu tabaraki.

Bangaren Yazed soyayya suke Sha Kamar me Yayin da Fuzail ya Bawa Maimartaba takardun Yazed aka samo Masa aikin Gomnati a waje me tsokar gaske a iya allowance kadai ya mallaki mota me tsada, Su Afra da Falaqi duk makarantu masu tsada Manal ta canja musu.
Bayan sati Daya su Annatu Suka sauka a Nigeria lafiya,Fuzail har can Suka je Sannu da zuwa shi da Manal,Suka je gidan Farida ma yini Guda Suka yi mata.

Bayan sun dawo taje gidan Shukrah sannan taje gidan Malam,da Prince Suka kaiwa Yazed Ziyara,Manal taga yayanta girma ya fadi sai lallaba mace yake yi tana ta dariya sai kallon Yazed takeyi Wai akan ta sun Iske shi Yana gyarawa Raheela gashi shike nan,Ko a jikinsa baya kunya shi kam,Amma Manal sai Kallonsa tana cewa oh Yaya Ashe kema dai A ne,Dariya Fuzail yayi yace Yayan Guda ma baza a daga Masa kafa ba,kyaleta sai na mareta tukun duk a Kauye ta koyo sa ido,ai ke Manal baza ki waye ba shi yasa,Dariya tayi tace Yaya na tuna Sanda ka dakko Ni a tasha farkon zuwa na birni,Dariya sukayi Fuzail yace ni Sanda na fara ganinki da Botikin awara nake tunawa,Raheela tace gaskiya ku kyale min kanwa Haka,Manal ta Mika Mata Baby Minal tana cewa kyale su Raheela,Yazed yace Mene Haka Raheela Gatsal,to Aunty Raheela shike Nan cewar Manal,sai da Yamma zasu tafi Raheela ta Shiga bedroom Yazed ya bita shima Yana cewa ku jira mu,suna Shiga Bedroom ta kwaso turarukan da zata bawa Manal Yazed yace I miss you yau yini Guda Su Manal sunki tafiya haba,Dariya Raheela tayi ya shiga kissing dinta Suka Rungume juna suna ta fama.

Manal Shuru Shuru Suka ji ba Yazed ba Raheela,Manal tace Wai me sukeyi ne haka a ciki? Ina Zan sani cewar Fuzail,Kai yanzu fa Yaya shima Naga ya susuce sai kallo Raheela yake Kamar maye,Ni wlh mamaki nakeyi Yaya sai ya nuna shi baya ko sha'awa amma kaga ya canja yanzu da zanyi laifi Haka zai dinga min Nasiha shi na Allah bayan Yana murkushe tasa.

Wayyo Minal tana wajensu Kar dai suyi Abu a gabanta,to Iskanci yayi wai da Zaki takurawa rayuwarsa Yana aikin Lada kin dame shi da sa Ido ki kyale shi idan ya Gama samun ladansa zasu fito,ke Sanda kike naki wa ya kulaki,Manal tace Raheela Kuma anga kyakyawan Yayana an makale Masa za a kashe shi da kisisina ai Ina kallonta harda shafawa Yaya wuya shi Kuma yayi Mukus harda lumshe Ido, Fuzail Yana dariya yace Wai ke Ina ruwanki ke wacce fitsarar ce bakya Yi? Manal tace ai dama Ni tun asali ban nuna Ni saliha ba ce dama can Ni na nuna Yar duniya ce Ni kula ne baka Yi ba,da Kauye a jiki na lokacin,Kauye ke tabani amma haba Malam ai mu bama boye boye,shi da yake nuna Mana ustazu ne shi,Fuzail yace to Zo Nima na samu ko Lada ashirin ne,fuskarta yabi da kiss ko Ina sannan ya dire a cikin bakinta sai da ya gaji yace Uhm Kar a kureni a gidan Yaya Guda,Gashi Nan idonka har ya canja,suna Haka sai Suka jiyo tafiyar Yazed suna dariya sun fito fes ba alamar wani Abu ya faru,Manal da sa Ido tace Raheela wanka Kika Yi ne? Naga Kamar fuskarki tayi fresh,Yazed ya gasawa Manal Harara yace zanci Ubanki wallahi kin girma Baki San kin girma ba, Fuzail Yana dariya yanda Yazed ya wani fuske ya bata rai a dole Ustaz yace ayi Hakuri babban Yaya ta tuba,Raheela tace Alwala nayi sai na Gama girkin dare zanyi,Manal tace ba kyau a dinga jinkiri.....kafin ta rufe baki Yazed yazo da Niyyar Marin manal baya son raini,Fuzail da sauri ya Kare yace Haba ya zaka tsargu itafa Wife dinka takewa irin dai fada na Mata,su ai Mata Haka suke har language ne da su sai suyi magana a gabanka baka Gane me suke nufi,ai itama Raheela ta Gane yaren ko? Raheela da sauri Tace ae na Gane Ni,Yazed yace dan Allah Prince dauke ta ku tafi Bata da kunya Zan iya marinta yanzu bana son raini,Yara yanzu sai su dinga Raina babba.

Manal ta Mike tana kunshe Dariyarta Yaya ya tsargu,sai wani bata rai yake,Yazed yace karka sake zuwa da ita sai tayi hankali,Prince yace to Inshaallah,Minal Baby Prince ya Saba a kafada Manal ta Mike tace Yaya baza ka bani komai ba? Wata Harara ya watsa Mata tayi Dariya tabi prince har mota Suka raka su,Yazed prince ya yiwa Allah kiyaye Hanya,Raheela ta bawa Manal kyautarta,Manal tace Raheela kawo kunnenki kiji,Yazed yace baza taji ba ke Kar ki saurareta,Fuzail Yana ta dariya Raheela dai ta window ta mikawa Manal kunne tana daga cikin motar da rada tace ki Bawa Yaya Ginger sosai,ki hada Masa da pepper yaji sosai please,Raheela dai tana Dariya tace to, driver ya jasu Suka tafi,Suna tafiya Yazed yace Manal ta Zama marar kunya wani ba a jinkiri da wanka irin wannan me take nufi? Raheela ta dinga dariya Tace wankan tsarki ai Bata Yi karya ba,Dariya yayi shima yace kin gani dai yanda nake sai a gabanki nake dariya,Muje muyi wanka Raheela ta ja shi Suka tafi tsarkake jikinsu.

Su Tanko sun Riga Prince tarewa a Abujan ma,ya dauki Sani Suka tafi tare da masu Aiki Mata biyu manya Wanda zasu dinga yiwa Manal Aiki,ko da su Tanko Suka ga mahauckacin gidan da Fuzail ya Gina sai da Suka girgiza, Kamar wani shegen Estate me dauke da part Uku,Part Daya na Tanko Daya Kuma na Baki part Wanda yafi kowanne tsaruwa shine na Fuzail ba karya,ba abinda babu na more rayuwa,bangaren Me gadi daban a jikin gate wasu Dakuna biyu kowanne da toilet,Sai wasu na maza biyu masu kula da gidan gaba Daya,Mata Kuwa a can ciki bangarensu yake kusa dana prince,Sani shine Driver na Fuzail yanzu,Sai Yahaya idan Baku manta ba Abokin Farida shima Fuzail ya sama Masa aikin Yi na Gomnati inda ya Dace da shi.
Annatu tuni gidansu an Gama a kauyen ne kyau da shi dagwas yasha tiles Masha Allah.

Manal suna shirye shiryen komawa Abuja dukkan kayansu na bukata tuni an kaisu can suturu da abun bukata,Itama Hajiya Sharifa tana Shirin komawa Kauye Bayan tayi wani kiba tayi haske ta Kara kyau kamar ba ita ba,ta waye ba laifi Ana gobe tafiyar su Manal ta fara amai amai yaki karewa,Yini tayi tana Amai,Hajiya Sharifa tace sai kace me ciki Naga gaba Daya watanki biyu da Haihuwa sannan sai kwana Nan kika koma part din me gida Lafiya? Tsoro ya Kama Manal karfa ace ciki ne,Fuzail ya tafi asibiti da ita suna zuwa aka aunata ciki ne na wata daya da sati biyu,Manal kamar me cikin shege ta fashe da kuka Fuzail ya rasa yanda zaiyi da ita shi murna ma yake Yana ta Jin Dadi amma ita kuka takeyi Hannunta ya rike tare da furta Sunshine kina gani Ana kallon mu let's go,Hannu Manal ta fisge kamar me Aljanu ka daina kulani bani ba Kai har abada,Dariya ta bashi ma yace I'm Sorry muje gida karki fadawa kowa Kawai muyi Shuru dagani sai ke,Manal ta sake tsagewa da kuka ta Mike ta Kama hanyar barin Asibitin wai baza ta Shiga motar prince ba ta tsane shi Yana kallo tayi tafiyarta ta bar asibitin,da mota ya bita Amma tayi sauri ta shige Napep Kuma ta koma gidan maimartabar dai,Part dinta ta wuce tana ta kuka Hawaye yaki karewa,Hajiya Sharifa da take Shirin tafiya gobe tace Manal lafiya me ya faru,Manal Tana kuka Tace ba komai,ko dai cikin ne dake? Manal ta fara sabon Hawaye tace ae Wai,Baki Hajiya Sharifa ta Bude Tace cikiiiiii? Yaushe Nan fa kika ce bakwa haduwa sai kusan wata biyun Nan sabo da Naga Bai zuwa Nan kema Baki zuwa can a yaushe aka Yi? Manal da masifa tace Dan Allah ki Bari naji da abinda yake damuna Wai idan zanyi Abu so kike nazo na fada muku ko me? to Allah ya raba lafiya sai kiyi Shuru kawai Dan wannan abin kunyane,sai kace me cikin shege Dan Allah Aunty ki kyaleni haka, saman bed ta fada tare da lulluba da bargo tana ta faman kuka,Minal tana can wajen Ummi ta goyata,Hajiya Sharifa ficewarta tayi can bangaren Hajiya Babba,tana fita Fuzail ya shigo.



Rashin Lafiya yasa kuka jini Shuru fans.

Masu kirana ta waya,masu nemana online suna tambaya lafiya da masu nemana a groups,da masu Yi min Adduar samun lafiya duk na gani Kuma na gode Ina Matukar godiya da kulawa Allah ya bar kauna.











AsmaBaffa
[1/1, 10:26 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭






DEDICATED TO DUNIYATA AAMNA FANS GP









121-125






Official





By
AsmaBaffa









Page nakI ne

AIDA MAMAN TASNIM

ALLAH ya Kara Miki lafiya da tsawon Rai masu amfani.












Kuka ya Iske Manal na Yi Kamar me ta kudundune a bargo mamaki ya kamashi amma ta wanni fannin sai ya tausaya Mata sabo da Bata Dade da fita daga wahala ba ga wata tazo again,gefen bed din ya zauna yace ki shirya mu wuce Abuja yau na gaji da zama,Ni bazan je ba na fasa Tsawa ya Mata wacce Bata taba sani ya iyata ba ransa a bace cikin karaji yace Get up......sai data tsorata,Now ya sake cewa idan Kinga dama kije ki musu sallama ya fice abinsa,dama duk kayan sawarsu an kwashe Yan kadan ne Suka rage Shiryawa ta shiga Yi tana Yi tana goge hawaye ta Gama da kyar ta Dan wanke fuskarta taje part din matan Sarki,Wajen Badi'at,karshe taje bangaren Ummi kasancewar maimarta yayi tafiya Umrah,Ummi tace yanzu Fuzail ya fada min yau Zaku tafi,Manal Tace ae Haka yace Kamar zata Yi kuka,ya Naga Kamar ba lafiya ba fada Kuka Yi? Manal tace a'a tana murmushin dole,Ummi Nasiha tayi Mata sosai akan Hakuri da zaman tare,Dan Allah Manal karki Bari ku dinga fada da sauran shirme an San Watarana dole a Bata amma a daure a kiyaye Kinga can da gogaggu Zaki hadu karki Bari hakan ya canja Miki tarbiyya karki dauki wani layi marar dorewa,Fuzail Yana sonki da yawa please kar hakan yasa ki dinga Masa ba dai dai ba,ku zauna lfy shima nayi Masa fada sosai.

Inshaallah nasan baza ki samu matsala daga Fuzail ba a yanda na sanshi,Yana da Hakuri karki Bari Kuma yayi Fushi Bai iya Fushi ba,idan kika sake yayi Fushi to sai kin shiga wani hali,ki dauka dama zaman Ibada ne aure ba zaman Jin Dadi Kawai ba,Kar ku tafi muji wani Abu daban duk nasan yanzu Indai ya bar Nan garin to Kuma kasar waje zaku ware tunda Naga ya damu da sai ya koma Abuja nasan Yana da plan, koma Mene karki Bari 6mnths tayi Baku Zo gida ba,idan ba Haka ba Sarki zai sa ku dawo masarauta,anan Kuma Baku da yanci sai abinda akace Kuna under control.

Minal ta dakko wacce ke bacci a dakinta ta Mata wanka ta shirya ta tunda taji Fuzail yace tafiya zasuyi,Manal ta karbi Yarta Yar kubulbul da ita Tasha Kaya sky blue masu kyau,tana karbarta tayiwa Ummi Sallama,Fuzail yasha kananan kaya ruwan toka ya zuba kyau kamar me,Manal cikin Arabian Gown take wata peach ta zuba kyau,takalmi da Jakarta silver,Minal ta Saba a kafada wata Yar aiki tana binta da Jakarta har ta fito taga Fuzail Yana jira a mota,Driver da sauri ya bude Mata ta Shiga ya rufe sannan Yaja mota,tunda Suka tafi Airport ba Wanda yayiwa wani magana sai Fuzail da ya Kira Maimartaba ya sanar Masa sun tafi,Minal ya kalla tana ta wutsil wutsil Manal taki kulata ta kalli window tana Hawaye shaaaaarrrr......Baby dinsa ya dauka Dake saman cinyarta Yana Mata Wasa yace ki

Please Login or Register in order to submit comment