Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Zan Mata na siyeta har Botikin,Islaha ta kalli Tanko ita sai taji Tanko ya birgeta,Dai dai din wani a karkacen wani.

Islaha ta bashi du Ya biya kudi gaba Daya,Tace Kai me kudi ne gaskiya,Tanko Yace Allah sarki Mission na fito Yi wallahi ba karya wani Aiki zanyi Amma da kike ganina Me Gadi ne a gidan Sarki,Islaha murna ta kamata tace wayyo Dan Allah a gidan Sarki kake Aiki?Tanko Yace Uhm Bayi ba mu a bauta Muka taso,Islaha Tace cab wallahi ai Kai ba bawa bane,ai yanzu an daina bauta tun zamanin Jahiliyya aka Yi wannan,Ya sunanka Kai? Tanko Yace Iliyas harda gyara suna Iliyas Ana ce min Tanko,Wannan Kaka ta cuceka wallahi ka canja suna gaka kyakyawa Ana ce ma Tanko Kawai ka koma tk,Tanko Yace No T&K ko? Islaha tace da yafi kasan Ni Ina son Inga mutum Dan wanka,sai ka birgeni,Tanko Yace lallai darajata ta karu,Nan take yace kina da waya? Islaha Tace Rannan ta Fadi,Tanko ya karkace ya zaro wata karamar wayarsa Tekno Yar Dubu Hudu ya zare Layinsa yace gashi Islaha Sarkin kyau na Baki kyautarta ki sa layinki,Islaha tace bazan karba ba Haka Kawai sai kace Yar Iska,Nifa Malam ba karuwa bace Ni,Baki Tanko Ya bude yace nayi Miki kala da Karuwiii Ni?Dariya Islaha tayi Tace Karuwii wai? Tanko ya nace Sai da Islaha ta karbi waya,yace Kai Me Napep bani aron Biro da takarda,Me Napep ya bashi ya rubutawa Islaha Number dinsa sannan ya sauka dauke da Botikin Alawar madararsa.

A ransa Allah Allah yake yaga Farida ji yake kamar Ana ruru Masa wutar kaunarta a zuciyarsa duk ya rasa dalili sai tunaninta yake ko wanne time,Haka ya karasa Kofar gidansu tare da Bawa Me kanti Ajiyar Alawar Madararsa,Farida ko kwalliya Bata Yi ba ta fito fit sanye da Hijab me Hannu,tana zuwa Tace Algungumi cire Takunkumin face mask da ka saka da wannan munafukin rawanin daga nada Wato Ashe Tanko ne ai Allah ya Toni asirinka,Tanko Ga Kaunar Farida ta Masa yawa gashi an kure shi,Haka ya tsaya sololo Farida ta Gama ci Masa mutunci sannan Tace bani ba Kai,Malam ne ya dawo yaji irin maganganun da Farida take watsawa Tanko,Malam yace ai Baki Isa ba Tanko sai kin aure shi ba abinda zai hanani daura muku Aure ko Zaki mutu Ni Iliyasu Ina kaunarsa yayi min,Malam ya kalli Tanko Yace ka turo Magabatanka,Tanko Yana ta murna da godiya ya kalli Farida ya zaro Mata harshe Wai gwalo sai ya tsaya a Gaban Malam yace Ni talaka ne har ga Allah Tanko ne me aikin su Fuzail,Malam ya washe Baki yace Ni kayi min Tanko karka damu ka turo manyanka.

Tanko Alawar Madarar ya karbo ya mikawa Farida yace gashi a rabawa su Falaqi da su Alhaqatu idan Kuna da su Aliflamin ma ki raba musu su sha yanzu karya ta Kare Tanko Kiri Kiri kina gani shi Zaki aura,Farida ta fashe da kuka tare da yin ball da Botikin Alawar Madara Tace wallahi bana sonka ta shige gida da kuka,Hajiya da gudu ta fito tana lafiya? Farida sai lokacin ta kwashe komai ta sanarwa Hajiya,Hannu Hajiya ta Dora a Kai Tace wayyo na shiga Uku na lalace gashi Malam Dan Haru yayi aiki,Farida ta sake rushewa da kuka tace Hajiya kin cuce Ni kinyi Gaggawa da kika tafi wajen Malam Dan Haru gashi wallahi tsafi yake Yi,Hajiya tace ai shine yasa ma Malam yace sai ya Baki Tanko dole,Yanzu ya zanyi? Farida Tace mu koma a karya asirin me zanci da Tanko.

Wajen Malam Suka koma suna zuwa Farida sai Rusa kuka take Tace Malam kayi min Rai wallahi Dan karya ne ba Mai kudin bane,Tanko ne me gadin gidan Sarki Fuzail,Wallahi Dan karya ne Bawa ne,Shi Kansa Malam Dariya ce ta kwace Masa ya shiga kyakyata Dariya ba ji ba gani,Haushin hakan yasa Hajiya ta daga hannu ta zuba Masa Rankwashi sun Kai biyar da bala'i Tace wallahi idan baka karya ba sai na Kira maka Yan Sanda sun Kamaka na tona maka asiri,Malam yace wallahi bazan karya ba sabo da Ni ba Allah bane da za ace komai Zan gani,Dan haske ne aka haska Mana muke ganin wani abin sauran mu fassara da kanmu,Kuma mu Aljanu ke Mana hidima muma Muna musu,tunda Baki da mutunci da girmana Zaki rankwashe Ni wallahi bazan karya ba,duk abinda zakiyi kiyi,Hajiya ta shiga bashi Hakuri tana wlh saurin Hannu ne dani ko yarana Haka nake dukansu kayi Mana Rai Dan Allah ka karya asirin Nan,Malam Dan Haru yace dama ai duk me Hali irin namu karshemu nadama,Ni dama nasan sai sa'ar gaske Zan tuba,sabo da Haka wallahi bazan karya ba,sai mun hadu a wutar Jahannama Ranar da Shedan zai taramu ya Mana General Assembly ya karanta Mana Wala ta lumuni wa lumu anfusakum,Ma'ana karku zargeni ku zargi kayukanku,ku tashi ku bani waje Malam ya daka musu Tsawa,ba shiri suka fito Farida sai kuka Hajiya tana Bata hakuri.

Malam dagewa Yayi lallai Tanko ya turo,Wanda hakan yasa Hankalin Farida yafi na San Huda tashi,Gaba Daya ta rasa sukuni ta daina komai sai Kuka za a Mata auren dole,ga Tanko ya dage kusan kullum sai yazo zance duk Kuwa da irin wulakancin da take Masa ,Tanko ya fadawa Babarsa ya samu matar aure shi Kam,tsohuwa ta dinga Murna ta samu Yan Uwan Mahaifin Tanko tare da sanar musu suje a Kai kudin aure,Ai Kuwa Dubu dari Suka kawo kudin auren Farida Ranar Farida tayi kuka ta godewa Allah,ta rasa sukuni ta rasa Wanda zata samu ya taimaka Mata,Hajiya duk kokarinta tayi akan Malam Kar ya Amince da Auren Amma Malam yaki yarda,Hakan yasa Farida tayi wanka ta shirya tace Wajen Manal Zan je ta taimaka min ta hadani da mijinta ya sa baki wallahi bana son Tanko gwara ko waye a bani akan na auri Tanko,Yazed Yana ji yayi Dariya yace Amaryar Tanko dama Manal zasu Miki Rana? Fuzail yanzu Baki ji kunya ba zuwa Neman Alfarmarsa? Ko gidan Manal Baki taba zuwa ba sabo da Hassada da bakin ciki yanzu Kuma Zaki tafi sabo da bukatarki?Ko kinje Malam bazai fasa ba sai idan Tanko ne yace ya fasa da kansa.

Farida Bata kula Yazed ba ta dauki Hijab harda sa Hijab sabo da aji tausayinta ta fice tana zuwa gate din farko Sani yace kin daki gurbi sahibin naki ya fita yanzu ya tafi kasuwa zai Fara rage kayan lefenki jiya ma Akwati biyu manya aka siyo suna Nan,Farida ta Harari Sani tare da wucewa ciki,Tunda ta shiga iyakarta gate din farko ba a Bari ta Shiga gate na biyu ba bare ma ta Isa ga Wajen Iyalan sarki,ta Dade a tsaye sai lokacin ta tuna ta Kira Manal,Wayar ma tana Hannun Fuzail Yana Bude Mata Wasu Media,Aunty Farrrrrrr....yaga an sa tana kwance a saman kujerar da yake ta Mike kafafunta a saman cinyoyinsa tana kallo,Wayar ya daga tare da karawa Manal a kunne,Manal ta Mike zumbur Aunty Farida lafiya mutuwa akayi? Tsaki Farida ta ja tare da furta malama Ina gate din farko an hanani shigowa wajen ki,Manal Tace Bawa masu gate waya,suna karba Manal da Iyayi wai Tace Princess Manal ce sai da Fuzail ya kalleta Yana dariya,Me kula da gate na biyu yace wa? Ta sake cewa Mrs Fuzail da masifa,Sai lokacin Dogarin ya fara kirari Yana bada Hakuri,Farida tana kallo tana Ina ma ace nice,Nan take aka Bata izini taje har bangaren Maimartaba Nan ma Sai da Manal tayi magana sannan Farida ta samu ta Shiga,Saude Manal ta turo Direct part dinta aka wuce da Farida,Farida ta Zama wata Yar kwaya,gaba Daya ta chake sabo da kyau da Haduwar da take gani,mamaki ya isheta Wai Manal ce a cikin Nan.

Tana zaune a palon kasa taji takun Manal da sauri ta kalli sama inda taji motsi Fuzail ta gani yasha wankan wani danyen Yard blueblack Kamar zai je party,ya zuba kyau ya Kara kyau,kiba da haske,Manal tana bayansa ya goyota ta matse cikin kana Nan Kaya wani matsiyacin Bumshort fari ,ya kamata Gam ya Mata kyau matuka,sai Yar t-shirt wata maroon,gashinta ya Sha gyara suna zuba kamshi,Farida jikinta sai yayi sanyi gaba Daya sai ta shiga tausayawa kanta,Manal tana wani mahaukacin kamshi tazo tare da Rungume Farida Aunty Farida oyoyo,Farida tayi wani saraaaaa sannan tayi karfin Hali tace ya gida ya Jin dadi? Manal ta koma ta zauna tare da Furta Alhmdllh tana murmushi,Tace ya su Hajiya su Malam,sati biyu kenan har yanzu ban samu na shigo ba makaranta ce tayi zafi,ga Kuma Prince idan nace zanje sai yace na fiye zuwa gida,sannan na Kira Hajiya nayi nayi a kawo min su Falaqi Hutu Taki wlh,Ko kwana biyu da sun min,Farida wani bakin ciki taji da ba ita bace Manal ce a wannan gida,da wannan Mijin nata hadadden gaske.

Fuzail Ganin dama ba shiri suke ba Kuma tana kallonsa Bata Masa magana ba sai yace Sunshine Zan fita ni,da sauri Manal tace Ina Kuma zaka je Bayan Ummi sai Dare zata dawo,muna da inda zamuje ne da Ameer,Okay Allah ya dawo min da Kai lafiya,Ameen ya furta,ganin zai fita ko kallon Farida baiyi ba Manal ta Mike da sauri ta rike shi tare da janshi gefe tana cewa Dan Allah Aunty ce fa,Auntynki ko Amma Ni Bata girme Ni ba Bata Isa na gaisar da it ba,Manal tana rada tace za muyi fada fa,yau bazan Zo tayaka kwana ba,Shagwaba Manal ta fara Masa tana kukan shagwaba tare da rike hannayensa tana doka kafafu, Fuzail yace Dan Kinga Ina Wasa dake ne Manal baki Sanni ba shi yasa,ture Manal yayi tare da ficewarsa abinsa.

Farida Baki ta tabe tare da cewa Nifa akwai abinda ya kawo ni,Manal abin Sha Dana ci iri iri ta kawo mata Amma Farida abinda ke damunta yasa ko ruwa Bata kurba ba,ta zauna tare da Bawa Manal labarin Tanko Amma Bata ce asiri Suka Masa ba Wai Tanko ne ya makale mata, Karshe Farida tace ki fadawa mijinki ya ja Masa kunne wallahi,Kuma ba ruwan Fuzail da rayuwata da har zai bada motoci da kudi a yaudareni,Ni ba Yar Kauye bace da za a Raina min hankali Kamar yanda aka Miki,Ki fada Masa yasa Tanko ya janye wallahi nafi karfin gadar zarensa,Manal haushi ya kamata tace ance Miki Fuzail ne ya tura shi? Shi da na rokeshi akan ya yiwa Tanko Fada lallai ya janye shine Zaki ce Fuzail ne yasa,nayi zaton ma abin arziki ya kawoki to baza a sa Tankon ya janye ba kiyi abinda Zaki Yi idan isarki da gadararki ce zata sa ya janye sai kizo ki sa ayi dole,duk abinda ake Miki bakya gani Allah ya shiryeki wallahi Ciwon Hassada ne da ke ki fara addua Allah ya yaye miki,Bafa tsoronku muke ji ba Kawai Dan a zauna lafiya muke hakura burar'ubar Nan fa muma mun iyata,Idan Zaki canja Hali ma ki canja wannan ba inda Zaki je,Fuzail baida time dinki wlh kallo baki isheshi ba albarkacina kike ci amma wallahi badan ni ba irin abinda kika Masa sai yayi maganinki ,Farida tsayawa tayi Kawai tana kallon Manal.

Ganin damarta zata kwace sai ta sassauta Tace to Ni dai ki San yanda Zaki Yi Baku Isa na auri Tanko na zauna a karkashiinku ba,Murmushi Manal tayi Tace Dama nasan Haka ce zata sa ki tsani Tanko Haka amma Tanko wlh ba mummuna bane kowa ya sani,Kawai tun farko kice sabo da nine Kawai,Ae wallahi akan na zauna a bangaren bayi gwara na auri me yasar Masai, zabin Allah Zaki Nema Aunty,Farida Tace a'a mutum ma Yana zabawa Kansa ai da zuciya ake Aiki sabo da Haka Ni nasan abinda yafi dacewa da Ni Allah ya bani ko waye Banda Tanko,Shike Nan ga abinci Nan ki ci,mu wacce Kaza ce Bamu ci ba ai ba sune Suka kawo Ni ba,Ki Gaida gida Farida Amma Nima gidan Nan Allah ne ya kawo Ni ba zabi na ba,Zanci uwarki wallahi kika zabawa kanki dai Zaki min Iyayi shegiyar Yarinya sai Iyayin jaraba Nan kika dinga Kuka sai an aura Miki shi sannan kice ba zabinki bane,Dariya Manal tayi tare da juyawa a Gaban Farida tace Aunty ya kika ganni Dan Allah Dan Mijina me Dadi,Dariya Farida tayi tace to anji kina Jin Dadin abin ba sai kin fada min ba,Manal tace to muje kiga saman,Baki Farida ta tabe tare da furta Dan an nuna min wai kina Jin Dadi ko? To baza a kalla ba Tanko Kawai zaku sa ya daina so na daga Nan Zan dawo kulaki,Mikewa Farida tayi tace Kinga Tafiyata,Ki tsaya na dakko Miki kudi,Banso dubu Darin Tanko ta isheni Kuma wallahi asara zaiyi Dan ko ya fasa baza a biyashi duk abinda ya kawo ba sabo da shine tukwicin Karyarsa.

Haka Farida ta koma Gida tana zuwa ta Iske wata tsaleliyar Mota Malam Yana ta murna Fuzail ne ya siya masa me tsada me kyau motar tayi matuka duk inda ka Shiga sai an San ka hau mota,Farida Ita ko murna bata Yi ba sabo da ta kanta take Yi.

Bayan Farida ta tafi Sai Dare Fuzail ya dawo bayan Manal ta bashi abinci yaci ya koshi sunyi Shirin bacci suna saman bed Manal tana jikinsa a kwance ta fara rada Masa magana a kunne Dariya yake kyalkyalawa shi Daya,Wai Ashe labarin Karyar Tanko take bashi da yaje ya dankarawa Farida Fuzail yace Tanko anyi Yan iska,Fuzail yace ah wallahi bazata ta auri Tanko ba koma Mene sabo da wannan idan tazo gidan Nan kin Shiga uku fada zaku Yi tazo tayi ta kishi da ke ko ta ce zata taba min ke Ni Kuma ba abinda zai Hana ban kulleta a kurku na gidan Nan ba insa Dogarai su Mata Illa,a baya Ina goyon Bayan Tanko Amma yanzu Sam Sam baza ta yuwu ba Farida a Nan gidan Ina,duk da idan ta auri Tanko to dole Tanko Zai daina Gadi wlh Zan samo Masa aiki me kyau Kuma bazai zauna a gidan Nan ba yanci zai samu na gaske amma bana son fitina dole Tanko ya janye .
Manal ta dinga Murna Tace ai ko Ni da nake Yar Kauye bazan auri Tanko......kafin ta karasa Fuzail ya saka bakinsa cikin nata yace Ina ruwanki da Tanko ma,kin San Allah ku daina haka,Ina ruwanku kowa Yana da baiwarsa Dan Kawai Ana cewa Bayi ne Kun jawo ma wallahi sai na maida Tanko Mutum verysoon Tanko Zai shaki Iskar 'yanci.

Bana bakin ciki amma Ni dai tunda Farida Bata so a hanashi,shi Kuma idan Yana so fa? Sonkai ne fa ko shi ba mutum bane? Ya kaga Farida da Tanko duk wankan Nan a Tanko ta Kare da ranar Har Dinner Zan hada musu lafiyayya suje su cashe cewar Fuzail,Ai wlh abin kunya ne ace yayar matarka tana auren Bawa,Babu kunya aure fa kika ce ke Nifa gidan Nan Zan Bari jira nake ki samu ciki Kawai na Gama da Ummi shike Nan,Manal cikinta ta shafa tace naji alamarsa ya kusa tahowa cikin taba Nan kaji daga daidai Nan kaji tauri tauri inaga Shine a Nan,ta daura Hannun Fuzail a gefen cikinta can kusa da baya,Dariya Ya Kama Yi yace ciki a Nan ai sai asibiti cuta za ace ba ciki ba,maidata yayi samansa tare da furta zo na dubaki yanzu a bani kayan dadi.

Manal da shagwaba Tace pls style din jiya ya bani wahala Allah yanda ka lankwasa min Hips ya kusa ballewa zafi yake min,Ina wajen? Ta nuna Masa ya dan latsa wajen ta kwalla Kara,yace Kai karfa ko da gaske kinji rauni ko kashinki ya goce,ai Kaine kasan ban Saba ba ban iya style din a kace sai anyi ai gashi Nan Kuma Kaine ka Danna min wajen da karfi sai da ya lotsa ciki,Sorry rashin Excersise ne Amma idan kin Saba shike nan,sai ka Kira me gyara ta bangaren mata ta duba wajen Allah Jurewa nake Yi da kyar nake tafiya, Knocking Suka ji sun San Ummi ce Baki ya toshe Mata Suka Yi shuru,tana bugawa Daya biyu ta ja tsaki Tace Bai dawo ba Allah yasa ba wajen Yar iskar can yaje ba, Jin ta tafi Manal Tace Kai ungo Jerusalema dinka,Faridanku Bata da kirki itace take cewa Haka,Manal tana Dariya kasa kasa Tace a wajenta na ji nima,daga Nan suka shiga murza juna yanda ya kamata,Dalibar tasa ta koya gaba daya ta Gama kashe shi da salonta hankalinsu ya gushe kalmomi masu Nauyi suke Furtawa juna.

Belloti ya goge sosai ya kile ya Zama wani Dan birni gashi matashi me tashe Dan Fulani,Yana samun kudi a gidan giya shi yasa yake daukan wanka,Ubangidansa Uche machine ya Siya Masa Kago sabo dal Belloti Yana shanawa,a gari har yanzu Bai waiwayi kauyensu ba anyi Neman anyi Neman har an gaji Iyayensa sunyi kuka sun gode Allah Belloti Kam yace bazai koma ba sai da motarsa Sabuwa zai je suga yayi kudi.
Christmas ce take karatowa Uche yace Belloti ya shirya zai rakashi Nasarawa Yayansa Emeka da matarsa a can suke da Zama wajensu zai je yasha biki,Belloti kullum Manal tana ransa Jin ance Nasarawa ai sai Belloti ya sa sabon layi ya Kira abokinsa Lawi,Lawi yaji ance Hello Belloti ne,Lawi ya dinga ihu da murna yace Haba Belloti Ko kaima kungiyar Yan ta'adda ka Shiga ne? Ya kamata ka dawo gida,Belloti yace sai nayi kudi har yanzu kudin Basu Kai ba,Sauri fada min Address din gidan su Manal Dake Nasarawa idan da Hali ma ka bani Address din gidan mijinta,kasan Kuwa wa ta aura? Dan sarki ne,Kai dalla matsa fada min Ni,lawi yace ban San gidan mijinta ba Amma nasan gidansu Nan ya bashi Address din gidan su Manal,Yana bawa Belloti ya kashe wayar tare da cire layin gaba daya Dan ma Kar a nemeshi.

Bayan Kwana biyu Fuzail Tanko ya Nemo yace ya janye Neman auren Farida da yake Yi,Tanko Bai da ikon yiwa Fuzail musu Amma Kuma asiri yasa bazai iya Jin Maganar kowa ba akan wannan,Tanko rasa me zaiyi yayi sai Kawai Idonsa ya cika da Hawaye ya fara kuka sabo da bala'in da yake ji a ransa idan Matukar aka ce ya bar Farida shi Kam bazai iya ba,Mamaki ya Kama Fuzail da Manal,Yanzu har son Faridan ya Kai Haka? Tanko Kamar yaro ya daga Kai Wai ae,Tausayin Tanko ya Kama Fuzail sai kace tsafi Namiji da kuka Haka Kuma akan soyayya,Manal Itama sai taji Tanko ya Bata tausayi Yana tsugune a kasa Gaban Fuzail,ganin Haka duk sai suka kasa sake Yiwa Tanko zance Fuzail yace wannan wacce Jarabta ce Tanko,Tanko da Hawayensa yace Nima ban sani ba wlh ban San dalili ba,kana Addua Kuwa? Tanko yace Sosai ai ni kasan dama bana Wasa da Ibada,Azkhar kullum baya wuce Ni,jeka Kawai Fuzail ya furta,Tashi yayi ya fita da sauri,Manal ta kalli Fuzail tace Ni Kuwa baka min irin son nan sai dai in mutuwa nayi kayi kuka,Dariya ta bawa Fuzail ya gimtse ya fada jikinta ya fara Mata kukan karya,Ummi ce ta shigo ba zato ta Kama Fuzail dumu dumu ai Fuzail sai ya zarce da kukan gaske Kamar na gaske ya koma yi harda shesheka,Manal ta Bata Rai tare da tureshi Ni daga Ni baza kazo ka ci min mutunci ba sannan da masifa ta samu tace ka isheni,Ni Nace ka sa Hannun Jarin a can,Ummi tace Kai...Kai..wallahi ku kiyayeni Hannun Jarin ubanku tun kafin na karaso naji dariyar ku shine Zaku raina min hankali,Wannan shigar da kika Yi uban wa kika yiwa idan bakwa tare? Na Dade Ina zarginku dama Ana fada min Kuna tare kullum Amma ban taba Kamaku ba sai yau shi yasa na Kyaleku,Yau sai ka sake ta tunda baka da mutunci,Fuzail yace saki Kuma? Manal tana ji tace Ni magana ta Allah zuwa yayi ya fada min tsautsayi yasa yayiwa Yar Aiki ciki shine nace sai na fada muku shike Nan fa ya Kama kuka ba Dariya kika ji ba Ummi.

Tsoro ya Kama Ummi ke karki min karya wallahi Zansa a daure ki,Manal Tace ki bincika a gidan Nan kiji ta Mike tare da saka Hijab ta fice daga part dinsa Yana cewa kiyi Hakuri karki fada Dan Allah,au da gaske ne Fuzail? Ummi ta tambayeshi Mukus yayi Yana alamar rashin gaskiya,fita Ummi tayi zuciyarta fal da damuwa tana rokon Allah yasa ba Haka bane,a ranta Dariya tayi Tace so suke su Raina Mata hankali ta kwantar da hankalinta ta koma sashenta.
Ganin Farida ta dage baza ta auri Tanko ba Malam ya Kira Tanko cikin gaggawa yace idan ya shirya a sa Rana,Tanko gidan Sarki ya sanar inda za a sanarwa Maimartaba,Umarni sarki ya bayar a wucewa Tanko gaba ko yaushe a sa Rana a shirye suke,Yan Uwan Tanko da wakilan Sarki Suka je Malam ya matsa shi Nan da Sati biyu za a sa Rana,Haka aka tsaida ranar aure,Farida ta haukace ihun kuka take Kamar Mahaukaciya ta Kira Manal a waya ta zazzageta Wai duk itace ta hada Mata mugunta gashi Nan za a aura Mata Tanko,duk wani shiri Malam Yayi shi Dake akwai kudin ya Gama komai,Farida ba Wanda ta fadawa Haka ba Shirin da ta Yi,Farida Bata San Iyaye suna da power Haka ba sai yau,Kawarta Walida Tace ta gudu ta bar gida Farida Tace ba inda zanje Kuma ba Wanda ya Isa ya kaini gidan Tanko wallahi sai in gawata za a Kai,da a aura min Tanko gwara a bani ko waye a duniya,Walida duk da Yar bariki ce sai da Tace ke Farida ki daina cewa kowa,Farida Tace na ce Haka.

Belloti Allah ya kawo su Nasarawa Lafiya gidan Emeka yayan Uche suka sauka gida hadadden gaske daki Guda aka bawa Belloti,girki dama ya Saba da cin abinsu shi yasa ko Uwar me Suka dafa Belloti ci yake,Abinci ya Sha Snail aka kawowa Belloti ya kwashi gara,sai da yayi kwana biyu a garin Yana yawo Yana shakatawa sannan ya nemi gidan su Manal,Ai Kuwa har gidan aka Nuna Masa yazo a Galleliyar Motar Uban gidansa Uche,Yasha kana Nan Kaya yayi kyau Belloti akwai kyan diri,Yaci sa'a ya samu Yazed,Yana Fitowa ya Gane Belloti amma ya waye yayi kyau ya kile ya zama Dan gayu,Yazed yace ba Kai naji ance ka bace ba,Dariya Belloti yayi Suka tafa irin shegen Nan yace wlh Neman kudi kawai Kano nake neman arziki kasan bazai yuwu a rayuwa ka zauna kana kallo a fika kudi Kuma a fika nishadi ba, Ina karka sake idan baka da kudi ka nemawa kanka nishadi,Yazed yayi Dariya yace Haka yake dama Yazed baifi Mate din su Belloti ba,dakinsa ya sauke shi tare da kwalawa Farida Kira ta kawo Masa abinci,tana Fushi ta kawo sabo da tana Jin haushin Yazed an hada Baki da shi za a Mata auren dole,Belloti yaga Farida Yar gayu Malam irin wacce suke mafarkin samu wayayya, Farida ganin Belloti ya dau wanka Dan matashi sai ya birgeta Tace dama shi aka aura min da yafi,Belloti Dan Karya harda cewa af na manta ban kulle motata ba,Jin da mota yazo sai ta Kara Jin kaunarsa,Fita yayi Yana bin Farida da kallo,Yana dawowa yaji Yazed Yana zancen auren Farida,Belloti yace Nima na shigo sahun Yan takara,Saura kwana shida fa bikinta kace ka shiga ciki kaima ai ba Nema cikin Nema,Belloti yace na yarda da kaina Allah Yana so na Yana bani abinda nake so ni Haka nake da sana'a ta, aiki nake a babban Super market inji karyar Belloti yace da gidana a Kano Rufin asiri Ina da shi,Yazed yace baka da hankali,Belloti yace wallahi na shiga cikin Yan takara babban Yaya,Fuzail yace to maji ma gani ci abinci,Belloti shi sai yaji girkin ba Dadi sabo da ya Saba cin na Igbo akwai su Snail da su kwari kala Kala.



Please Login or Register in order to submit comment