Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajenta na samo tawa matar,gashi sanadin ta an yanta Ni na Zama mutum na canja wa zaice Tanko ne? Belloti yace ai Ni nasan me nake gani na Alheri tunda na Aurota kullum ci gaba nake samu, ta bani Sako ma tace na fadawa Maimartaba kowa ya sheda ita kadai ce ba kishiya,aka kwashe da dariya,Maimartaba yace Kai dai shakiyi ne, Farida Tace ba ruwana bani nace ba,Manal tayi zaraf tace Ni Nace da Fuzail to shine Bai fada ba babu kishiya Maimartaba,to Uwar kishi cewar Yazed ana dariya,Prince yace to sarki yaji Amma sai abinda Dansa Prince yace in ya kawo wata maraba idan Bai kawo ba fine,idan ma kasar waje zai koma da Zama ya koma abinsa,Da sauri sarki yace wannan Kuma baka Isa ba,kaima ka fake da isar da sakonka kenan aka Yi Dariya,Ummi Tace Mashaallah sai a yafi juna,Yazed harda cewa a rufe taro da Addua a saka matata Raheela ciki Allah ya sauke ta lfy ta kusa Haihuwa Edd dinta ya cika, Malam ya fara zazzago Addua aka shafa,Sai ga waya kishiyar Hajiya ta bugo tace suna asibiti da Raheela ta Haifi mace.

Ana ji aka Taya Yazed murna,Manal Tace Yaya Sunana za a saka Mata,Farida tace Yaya nafi Manal Albarka duk ta jikina Suka samu dacewa Sunana za a sa Mata sabo data gado Ni,Prince yace wlh Baki fita Albarka ba Kawai Manal za a sa,Hajiya tace sunan Annatu zai mayar karku damu mutane,bayan dai an Gama nishadi Nan maimartaba ya sallami kowa,Tanko yace shi sai jibi zai dawo Abuja shi da sani,Prince ya dauki matarsa Suka bi jirgi,Farida ma da Belloti Haka cike da murnar kyautar sarki,Farida tace sai na bude kanti da kudin na sa yaro ciki ko ya kace? Belloti yace hakan yayi sai mu duba me zai kawo ciniki sai a zuba sauran kudin ki siyi kadara,Farida tace motar Kuwa gata Nan kaga yanzu motocinmu har uku cikin ikon Allah.

Bangare Fuzail Kuwa lafiya Suka Isa gida suna zuwa sabo da ba gajiya a jikinsu fita Suka Yi yawon shakatawa ya kaisu wani katafaren wuri Sabo da Minal zata Sha Ice cream, Ameer Yana Hannun Manal Yana wasansa,Minal Kuwa dama kullum sai wajen prince abinta,Prince yace Minal fa next week Zan Sata a school dinku,Manal ta tsuke Fuska Uwa da ya a school Daya,ita Yar tana pre nursery Uwa tana Ss1 bazai yuwu ba ta rainani ace makarantar mu Daya gaskiya a'a,Prince yace to wlh Nan Zan kaita,ai Kuwa bazan kulata ba,karki kulata ai yarki ce,Kika sake ma Ameer sai ya iskeki Manal ta turo Baki gaba.

Sati Daya tsakani aka saka Minal a pre nursery da uniform dinta itama Manal Haka tare prince yake kaisu school Uwa tayi ajinsu bayan ta Kai Minal har class dinsu,ga sunansu kusan iri Daya,mutane ai ta kallonsu Kuma kamarsu Daya sak,Kamar ya da kanwa,idan an tashe su Haka zasu fito Manal ta rike Hannun Yarta Azo a dauke su,Watarana sani yazo Driver,Watarana prince da kansa.
Yau ma Monday sani ne ya dakko su sai gasu sun shigo tare Manal rike da Hannun Minal suna Sallama Salamu alaikum Daddy mun dawo Fuzail ya dago ya kalle su Yana dariya harda hada Baki su fada a tare,Yace sai kuzo ku cire Uniform ayi wanka aci abinci babbar tazo room Dina karamar Kuma tayi wajen Nanny Ameer Yana jiranta suyi Wasa,Minal tace Yeeeee Babba da Babba yaro da yaro bari muje yeeeeee.... tayi sama da gudu harda faduwa Manal tana ganin Minal ta Kule ta fada jikin Prince tana dariyar Babba da Babba yaro da yaro shima Dariya yayi yace tashi ki Kora Yarinyar Nan wajen Nanny wallahi wayon jaraba ne da ita Kar ta dawo kin San dai halinta da labe,yanzu sai ta labe tace zata bani tsoro kin San tanayi,ai Kaine kake Wasa da ita ba Dole ba.

Manal tana zuwa tajita a Bayi Wai wanka takeyi tana Shiga toilet din taga tayi dama dama Shaving cream din fuzail,Fitowa tayi Tace prince Zo kaga yarka abinda takeyi idan na daketa kace na cika rashin Hakuri,lekawa yayi ya ganta yace Baby bakya ji ko? wannan bana wanka bane,karki sake Zan zaneki,yanzu Nan fada ka Mata? Matsa Manal ta banke Fuzail ta wuce ciki da sauri ya ruko ta calm down ki dinga fada da yarki zata rainaki fa,Ka gani gwalo take min ko Allah sai na duketa yau,Fuzail ya rike Manal tana ta wutsil wutsil sai ta kwace ta Zane Minal,Minal Dariya tayi harda tafi tace Daddy ya rike Mum wullu baza ta zaneni ba wullu....tana zarowa Manal harshe,Manal tace ai Kuwa Zaki gani yau baza kici abinci a gidan Nan ba Ameer ne zai ci,Kuma bazan Miki wankan ba kije wajen Nanny,ai na Iya cewar Minal,Bana son surutu Baby girl, Dad zo kayi min wankan gobe Kuma akwai Ishlamiyya.

Manal tafiya tayi itama tayi wankanta Fuzail Ne ya yiwa Minal wankan ya shiryata sannan yace remain what? food ta bashi amsa yace to Jeki wajen Ameer Yana wurin Nanny kice ta Baki abinci karki dawo Nan sai dare Lokacin za ayi karatu,Okay Dad yau ma da fruits Zan Sha? Yace yes idan an Gama cin Heavy sai a Sha fruits banda Shan Juice ko sweet sabo da hakoranki Kar su samu matsala suyi cin Zuma,Dariya tayi tana tsalle Ni bana cin Zuma fa wayyayi (wallahi) alright naji Jeki,har ta tafi ta dawo tace a Kara min perfume ba a fesa min wancan ba,ya dakko ya fesa Mata yace Oya go,Naje gidan Aunty Islaha zanga Dan Jariri,Fuzail yace no babu time wurin Nanny nace kije fa idan kika dawo sai na zaneki,Bacci zanyi karki tashe Ni,idan kinje kice a kunna muku cartoon ke da Ameer, har ta tafi ta dawo Tace Daddy yigar (rigar)Nan ta tangaye(tsangale) min,Haka take to Yar Kauye karki dawo tafi,tafiya tayi da gudu yace be careful, tooooo tace tayi gaba.

Manal ce ta shigo tare da sawa kofa key da abincinta a plate da lemo a Hannunta yace Ameer fa ya kamata a bashi nono duk da yasha madararsa,za a bashi Amma sai a kyale Uwar Ameer taci nata ko,Zama tayi a Cinyarsa yace Ni dai duk sai Kun karasa ni yanzu Minal ta tafi gaki kema anjima Ameer Zaki kawo min,Mene aikinka to? Mika Cassava,ai Ni a ka'ida Kawai na bada Cassava,Dariya ta dinga Yi yace kawo na Baki abincin kiyi sauri kizo na baki abarki fita zanyi yau sai 12pm Zan dawo Ina da meeting da wasu Doctors Akan Hospital din Dana Gina a Nan.
Manal tana Dariya tace to kaje Mana idan ka dawo sai na karba cassava din,so nake naje Meeting cikin nutsuwa so kike naje Ina can Ina tunaninki na kasa komai na dawo,tana Gama cin abincin Suka Fara buga harka,lokacin yana tsaka da Beltal uba Yana wani Nishi da gurna'ni,Manal ma tana ta sambatu Minal ta hauro sama da gudu tana knocking Shalama'alaykum Mummy a akko min Chocolate dina,Mummyyyyyyyyy......Manal tana ji tace karka kulata ci gaba,Minal ta koma sauran bedroom din ta duba ba kowa ihu ta saki ta kwanta tana ta birgima wannan Bai sa sun saurareta ba sai da suka samu nutsuwa Manal tana maida kayanta tace wannan Kai ta gado a rigima,Ke dai yarinya ai kece har yanzu bakya jin magana.

Jallabiyya ya saka sannan ya bude Kofar Manal tana kwance Wai bacci takeyi,Minal tana ganin Daddy ta daina kukan tace,tashinta yayi tsaye tare da daga sama Yana shillata tana kyalkyala Dariya,Daddy Dan Allah a bani sweet ko Daya ce,na Hana Shan sweet ke Baki San kadan ba,Ina Mummy na? Bacci takeyi ta gaji shine kuka kulle ofa Ni kuka barni,Ido Fuzail ya zaro yace tafi wajen Nanny kice ta rakaki wajen Aunty Islaha kice Muna gaisheta maza idan kinyi Sallar Isha kice ta kawo ki gida,Yeeeee Bari inje muyi Wasa bye,ta tafi Dake Islaha kulata takeyi suna Wasa tare shi yasa take so taje can.

Tana tafiya Suka Yi wanka tare Manal ta sake gyara bedroom din sannan ta karbo Ameer lokacin ya tashi a bacci ma,Bayan ya dawo daga masallaci Sallar Isha Manal ta idar da Sallah taci kwalliya ta fito palo tace na kawo ma abincin? Yaushe Kika Yi girkin ko Yan Aiki?ai kasan sai idan Ina makaranta nake cewa su dafa min Abu kafin na dawo, lokacin da ka tafi masallaci na dafa, Me Kika dafa sharp sharp Haka? Faten dankali da kifi,shi yasa kika Gama da wuri ya furta Yana ta kallonta tayi kyau cikin kana Nan Kaya Riga da wando sun Mata kyau sosai,Kinyi kyau ya Furta Yana binta da kallo,Zama tayi a gefensa kafin ta kwantar da Ameer Fuzail ya kwanta a Cinyar ta,yayi matashi da Cinyar Manal,yace waye zai ce kina da Aure bare Kuma harda 2kids kullum kyau kike karawa Sunshine,Manal tayi murmushi Kawai tana Jin Dadi an yabe ta.

Minal ce ta shigo da jakar kayan wasanta tace Aunty Islaha ce ta siyo Mana tace kullum zamu dinga Wasa,Manal tace lallai tana biye Miki da yawa,Minal ganin Fuzail yayi matashi da Cinyar Manal ta fashe da kuka tazo ta sa Hannu biyu tana dage Kansa na rantse cinyata ce ka tashi min,Fuzail yace na kwace ta daga yau, ihu ta fara tana cire Kansa yace Ni din? kanta ta Dora a saman na Fuzail dole sai ya tashi ita ta kwanta,Zan mareki Sa'anki ne shi cewar Manal,to ya tashi min a cinya,Mikewa Fuzail yayi yace kawo min abinci naci na shirya na tafi,Da Sauri Minal tace Ina zaka je Daddy? Nayi Fushi barin gidan zanyi bazan dawo ba,to kayi hakuyi bazan sake ba,yace bazan hakura ba na daina kulaki.

Ka dawo Dad kayi kwanciyarka,yace bana so,Dariya Manal tayi ta kawo Masa abinci Minal ma Tace zata ci aka zuba mata nata,Yana gamawa ya shirya cikin wata farar suit ya zuba kyau kamar a jikinsa aka dinka, lokacin Minal tayi bacci tuni ya fita,Sai 12am ya dawo Kamar yanda yace,Manal ya Iske tana karatu ta Masa Sannu da zuwa ya cire kayansa ya Shiga wanka,bayan yayi Shirin bacci yace an Gama karatun ne? Manal Tace a'a sai 1am, wa zai kyaleki dalla rabu da su da karatun iskar Nan ya dauke littafin ya jefar da shi gefe can ya dauki Manal cak suka kwanta tare da kashe light,Manal Taji cucumber a Mike Tace lafiya? Muna meeting muna kallon wani Adventure movie gaba Daya film din Sai sex akeyi kuru kuru ba boyewa,Manal tayi Dariya tace to ya kukayi? Kowa Fuskewa yayi kamar Bai San anayi ba,ba sai ku canja Channel ba,ai iskancin Nan dadin kallo gareshi,Manal ta dukeshi kadan a baya tace to yanzu mu sake kwashe dadinmu blanket ya rufa musu sosai Suka Fara kashe Boss.



ALHMDLLH

NAN NA KAWO KARSHEN MAFARKIN FARIDA,ALLAH YA SAKE SADA MU A SABON NOVEL NAN GABA WANDA SHIMA FREE BOOK NE DON JIN DADIN FANS DINA .


JINJINA DA GODIYA TA MUSAMMAN GA FANS DINA MASU BIBIYAR NOVEL DINA.

DUBUN GAISUWA ZUWA GA MASU SHARHI KUNA DA YAWA BAZA KU IRGU BA,DANA GROUPS DINA DANA GROUPS DABAN DABAN HARDA WANDA SUKE GROUPS DIN DA BANA CIKI MA INA GODIYA.

WANDA SUKA YI MAGANA KO SHARHI BAN SAMU DAMAR MUSU REPLY BA DA WANDA SUKA YI SHARHI NA SHA'AFA BAN BASU KYAUTAR PAGE BA INA BADA HAKURI SOSAI A DAN YI MIN UZURI.

INA GODIYA GABA DAYA FANS DA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANSU BA GODIYA DUBU.


COPY BY ZAINAB BUTALAWA












ASMABAFFA

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment