Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allansu aikin banza zo mu matsa baya yanzu Fadawan Nan sai suzo su fara shaudawa mutum Bulala akan mun tsaya kusa da sarki,ai kafin Yahaya ya rufe baki Kawai sunji ruwan Bulalu a jikinsu ta ko ina Musamman Fuzail da yaki guduwa,Shi Yahaya tuni ya fece,Fuzail Kuwa Ana ta tafka Masa ruwan Bulalai ta ko Ina,Kuma yaki guduwa,Har Allah yasa sarki ya gani da sauri ya sa dogari ya musu magana su daina,aka dinga musu fada,Sarki ta Glass window na motarsa yake ta faman kallon Wanda fadawa Suka rufe da duka,ikon Allah ya furta kaga wani Kamar Fuzail Dina,Kai lamarin Allah da yawa yake,Shi wannan ya Tara gashi ne Kawai gashi talaka Amma komai iri Daya har dirin da yananyin skin din,sarki kasa daurewa Yayi yace a Kira Masa Yaron, Dogarai Suka zo gabansa Sarki Yace ayi maka Iso dai dai lokacin Kuma ya tare Taxi ya shige abinsa yayi tafiyarsa ya barsu Nan sabo da takaici.

Yana motar Yana masifa sabo da zafin bulalar doruna ta ratsa Fuzail yace ai Dole a zagi Sarki wallahi banga laifinsu ba,wannan wanne irin zalunci ne,shi talaka a kasar Nan Baida yanci, bayansa ya Sosa yasan ma an fasa Masa baya da duka duk manal ce ta jawo min ya Furta Yana tsaki yau ko na koma bazan kirata a waya ba wallahi sai gobe,ko ta Kira bazan picking ba.

Sarki Kuwa a ransa baiji dadin rashin zuwan Saurayin Wajensa ba,yaso ya Masa Alheri me tsoka sabo da Kawai sunyi Kama da Dansa,Kuma yaso ya bashi Hakuri sabo da yayi Kama da Dansa sabo da son Kai irin na sarki,idan baiyi Kama da Dansa ba shike Nan sun daki banza kenan.
Manal ita Kuwa Yazed Bai Mata maganar Saurayin ba Itama Bata Masa ba,da dare tana ta jiran Kiran Fuzail amma Shuru,tsoro ya kamata lokacin Fuzail Yana gida ya shiga Toilet Yaga yanda jikinsa yayi rudu rudu da bulalar Dogarai,jikinsa ya gasa Yana ta Jin haushin sarki da Manal yace laifinsu ne,Manal ta jefa shi a halin canja shiga,shi Kuma sarki baida Adalci Bai San darajar Dan Adam ba.
Wanka yayi da Sallah sannan ya kwanta a makeken Gadonsa ko Riga Bai sa ba sabo da Kar bayansa ya sake rurucewa Haka ya kwanta,lokacin Manal tana ta kiransa a waya yaki dagawa Yana Fushi da ita.

Wayar tana ta Kara ya kalla yace baza a daga ba kin Sa mutum sai wahala yake Sha Ana ta dukana tunda na fara sonki dai dai ranar da bazanci zagi da duka ba,abin haushi yau Dogarai yarana Yan aikina da Hannunsu suka zaneni a gefen Titi Gaban mutane,ai na ganeku su Tanko ne zaku Gane kurenku wallahi bari komai yayi settling zaku San kun Zane Prince.
Manal ce ta sake Kira ya kalli Wayar yace baza a daga ba aikin banza ya juyawa Wayar baya,har 1am Manal ta kasa bacci ta Hana Fuzail bacci da nacin Kiran masifa sai taji ko lafiya,Gajiya yayi ya daga tare da kumbura Baki Wai Fushi yake Yi Kamar Yaron yaye yace Hello....Manal Ajiyar zuciya ta sauke tace wallahi hankali na ya tashi kaje gida lafiya? Fuzail Direct yace a'a ba lafiya naje gida ba,Ido ta zaro me ya faru?yace Yaran sarki ne akan sarki zai Shiga motarsa suka Hadar min da zanewa, Manal ranta ya baci tace Allah ya tsine musu tsinannu Shegu har Sarkin Azzalumi,in Banda zalunci Kawai sai yasa a zaneka me ka musu aikin banza aikin wofi Ni wallahi shi yasa ko me Unguwa bana so wani Nawa yayi sabo da zaluncinsu,Fuzail yace idan kika samu Dan sarki fa zai aureki nasan guduna Zaki Yi? Manal da sauri Tace Dan Allah rufa min asiri Dan Sarkin banza ina da Kai wa yake ta wani Dan sarki,Kai Nifa irin wannan biyayyar ta gidan sarakai bazan iya ba,Ni Allah ma ya taimakeni Mijina Bai da hadi da azzalumai,Ni wallahi kasa Sarkin Nan ya Gama sire min ko motarsa na gani sai na zagesu.

Fuzail yaji za a zagi babansa yace karki zagesu ba ruwanki ko so kike ki zama Farida kema? Ba Haka na sanki ba,Manal Tace to Kawai sai su zane min Kai,Kar dai ki zage su na fada miki,to shike Nan tunda kace a kyalesu,Hira Suka ci gaba da Yi har 2am Yazed ya fito zaije fitsari yaji Manal tana ta waya,Kai ya girgiza yace sai da safe zanyi maganinki Manal Naga canji Zaki amsa tambayoyinki idan da Rabon kinci duka ne to.

Sai bayan sun Gama Wayar sannan Fuzail yace Sarki ba ruwana Kai ka jawowa kanka gashi Nan surukarka ta zageka baka sani ba,Ni Kuma bazan hanata ba tunda Kai ka jawo,Haka da safe Ameer Yana zuwa wajen Fuzail ai ya bashi labarin dukan da yaci da komai ma har abinda Farida da Yahaya Suka yi,Ameer ya dinga dariya kamar mahaukaci.

Fuzail Kuwa wanka ya dauka na karshe cikin kana Nan kayansa Brown and white ya zuba kyau gashinsa na asali Yana uban sheki yasha wani Aski na gagara,cikin Fushi Ya wuce part din Maimartaba Yana zuwa ba ko gaisuwa ya dinga masifa Taya za a dinga zubar da mutuncin sarauta yanzu na gani a media yanda Dogarai suke Zane bayin Allah Haka Kawai,Ya kamata ka tsawatar musu ai mulki ba Haka ake Yi ba,ba dama ance mutum ya tsaya kusa da ku da glass a Fuska ko kuma idan Kun tsaya Dole sai dai mutane su bar wajen ko su durkusa wannan ba dai dai bane.
Sai da Fuzail ya Gama masifarsa Sarki yace to Ubana Sannu Mahaifina,Shuru Fuzail yayi ya zauna a kujera,Sarki yace kayi hankali Zansa a kulle min Kai wlh, duk sauran yarana ba Wanda nake magana da da shi direct sai Kai ka kiyayeni,Sarki ya kalleshi yaga ransa a bace, sai yace Naga wani yaro jiya Kuna Kama naso Yaron yazo da na hadaku.
Shuru Fuzail yayi Yana ta Fushi sai da sarki ya lallashe yace za a kiyaye zai yiwa Dogarai magana su daina hakan sannan Fuzail ya daina fushin.

Washe gari Yazed dakinsa ya Kira Manal bayan ya tanadi Bulalu masu kauri jira yake yaji Abu ba dai dai ba taci ubanta a gidan,ita Kuma ta kulle a ranta Matukar Yazed yace baza a Mata aure ba to wajen su Malam Salahu yayan Babansu zata tafi ta Kai kararsu Dole sai an Mata aure Kuma tasan Annatu dama tana so Yarta tayi aure Bata da matsala Yazed ne uban Iyayin karatu.








Dole nasan aci dariyar dukan Fuzail,nayi Dariya Kamar me wallahi.



Masu Sharhi Ina godiya musamman
Hajiya Khausar
Ummi Deejat
Hauwancy cool life
Etc










AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭 MAFARKIN FARIDA🧭🧭








IS DEDICATED TO

DUNIYA TA AAMNA FANS GP.












36-40










Official









By
AsmaBaffa










Page naku ne Yan Albarka

TAMORMIE
AYNAH
AISHA UMAR
MAMAN AMAL
ABIDA ALI
HINDU MOHA
CWT FAUXAH












Da Sallama ta shiga dakin tare da Zama a gefen katifarsa ta Furta Yaya gani,Kayan jikinta na Jiya su ta maida yau kallo ya Kare Mata yace Ina kika samu wannan kayan? Duk Naga kin canja tafiyar sati biyu me ya faru ne Haka?bana so fa naji abinda ba dai dai ba Manal fada min a Ina kika samu kayan Nan Naga kin canja ma gaba Daya ban Gane ba,sannan wannan saurayinfa daga Ina Naga kin bashi matsayi da yawa.
Zama Manal ta gyara tun bayan tafiyarsa duk har haduwarta da su Fuzail sai da ta kwashe ta bashi labarin komai ba abinda ta boye masa karyarta Daya Bata ce ya taba kwana a dakinta ba,sannan Bata ce ta taba kwana a gidan da ta Nema musu su zauna ba Tace ai a waje take tsayawa su fito su karbi abinci ta juya gida,sai labarin kayan da Shukrah ta bata da kawancensu da karatun da take koya mata,har abinda su Hajiya sukayi Mata sai da ta fada masa.

Sai da ya Gama ji sannan hankalinsa ya kwanta yasan Manal Bata karya komai zata fada idan har ta boye abu to tasan fadarsa zai iya jawo matsala,To Yanzu dai Shukrah ta kyauta na gode data Dan koya Miki karatu,shima Saurayin naki yayi kokari Daya koya Miki wasu abubuwan,Manal ta fara dariyar murna Tace Yaya Kuma nafi Gane karatunsa ma,Ae ai dama Dole ki Gane Nasa cewar Yazed,da ace naji abin tsiya wallahi yau sai kinci duka a gidan Nan,ka tambaya kaji idan karya nake Allah Yaya gaskiya na fada maka,Na yarda ai yanzu su Hajiya Haka Suka Miki?Manal tace kyalesu Ni wallahi Farida da Allah zai kawo Mata Prince din nata ma a Mana auren tare kowa ya huta da jaraba.

Yazed ya kalli Manal yace Wai ke ban Gane ba karatunfa? Ni wallahi Yaya ka bar zancen Nan,
Tab Aiki Babba taso mu tafi ayi zancen Nan a Gaban Malam,Manal ta Mike tare da cewa ae aje...aje.
Suna zuwa Malam da Yazed Suka Fara lallaba Manal akan Kar ta Yi aure sai tayi karatu,Malam yace Manal mu maza ne gaskiya muke fada miki gwara ki zauna kiyi Ilimi ki fara Aiki kina samun na kanki mijinki ma Sai yafi rikeki da amana,Mazan yanzu kana da ilimin ma ya aka cika bare wannan Saurayin naki wlh da gani ba kunya ce da shi ba,Yazed yace ai Ina Kallonsa Naga a waye yake Kar,Kuma bako ma Wanda ba a sansu ba haba Manal auren bako fa hatsari ne a rayuwar nan,na rasa jarabar da yasa ma daga taimako ta manne masa,Su Malam suna ta Yi har Suka Gama.

Manal tace Nima a bani dama nayi magana,Muna jinki cewar Yazed Manal tace da kuka Ce sai nayi karatu ai yace zai sani a school,Kuma Bayan Haka ko nayi makaranta Ni bazanyi Aiki ba bana so,Aiki ko wahala Indai mijin zai min komai ba matsala Balle ma Yana da zuciya,Nawa ne basa Aikin Kuma sunfi masu aikin komai da komai na Jin dadin rayuwa sabo da mazajensu suna da rufin asiri,idan yayi kudi ba kasar da bazan jeba,ba motar da bazan hau ba Indai Allah ya azurta shi Ilimi Kuma zai saka Ni yace,sannan Malam Kai ma fa ba Bokon kayi ba Kuma gashi kayi aure gamu,sannan shi duk da bako ne to na kirki ne ayi Bincike Nan gaba Ni Ina da tabbaci Inshaallah baida matsala,Yazed yace Malam Yaron ya hure Mata kunne ya samu dama Bama gari ya Gama hure Mata kunne wallahi ko me zamu ce baza ta yarda ba,Dan Ubanki za a miki auren Amma ki sani Bamu da kudi sai dai Annatu ta siyar da shanunki a Miki Nima Nawa shanun Fili Zan siya sabo da Haka tunda bakya Jin shawara ayi Miki da ragowar shanunki Malam Baida kudi.

Manal tace ba komai ai na fadawa Annatu ma munyi magana a waya,Yazed ya girgiza Kai yace Wato itace ta Baki goyon baya ko? To Wai dama da a Kauye aka barni da tuni yanzu ba a min aure da Belloti Allah ya taimakeni na samu Wanda nake so sai ace sai nayi karatu wallahi Allah idan baza ku yarda ba Kara zan kaiku wajen Kawu Salahu wallahi ai ba laifi nayi ba.

Haushi ya Kama Yazed yace je ki Kai karar mana yaro yazo ya hure Miki kunne ya yaudareki da kudi kalli Wayar hannunki fa,karya kike wannan kayan duk shi ya Siya Miki,Manal Tace naji ai Ina Kauye kasa sai na dawo wajenka na maka biyayya na dawo kace duk abinda nake so zaka min shine yanzu ka canja sai na koma wajen Annatu gaba Daya,ki koma mana ai Kinga dai yanda mijinta yake Miki Jeki tunda Baki da hankali.

Kuka Manal ta fashe da shi baza a Mata aure ba,Malam tsoro yaji ko sha'awa ce take damun Manal Kar ya jawo ta lalace,Bai San Manal ita babu ma Wannan a ranta Kawai soyayya ce ta kwashe ta da Kuma kuruciya,Malam yace tashi kije zanyi tunani,Kafin ta fita Ashe Hajiya tana labe ita da Farida suna Jin komai ai wuf Hajiya ta Fado dakin Tace wallahi bazai yuwu ayiwa Manal aure ba sai an fara yiwa Farida sabo da itace Babba Dole Manal tabi layi ehe,Manal tana Hawaye tace layi Zan bi? Ah Kawai a makarantar kwana nake naje karben abinci,ko banki naje Karbar kudi? Hajiya tace Baki Isa ba yarinya kinyi kadan
Malam Yace idan kika sake sa min Baki a Maganar auren Manal a bakin aurenki na gaji da halinki,Mukus Hajiya tayi tare da ficewa Kamar Iska.

Kasa zaune suka Yi suka kasa tsaye Farida Tace ko wajen Malam zamu koma a Kori Saurayin Nan mu wargatsa zancen auren? Hajiya Tace Baki da hankali ai gwara mu kyaleta ta auri talakanta taje tayi ta Shan wahalarta,idan Muka watsa abin kika sani tazo ta samo wani me kudin gashi ke har yanzu Prince yaki zuwa wannan Mafarki naki fa na fara gajiya da shi gaskiya wallahi tallahi kwana Nan Zan fara dirka Miki duka cikin dare mun gaji da Jin sunan Fuzail Cikin mafarki yaki zuwa,Abu yaki ci yaki cinyewa gashi Dan kudin zuwa wajen malamin ma ya gagaremu komai babu.

Farida Tace zaizo ne Hajiya Haba zaizo ne karki damu daula ta kusa zuwa Kuma ai yanzu ma na daina mafarkin nasa gaba Daya na rasa dalili,tunda Farooq Dan Iskan Saurayin Manal ya bige Ni da tsuran machine dinsa ban sake mafarkin Fuzail ba ko da Wasa ,Hajiya Tace Allah yasa dai yazo Amma gaskiya na fara tsorata da lamarin Nan gata mayayyar Yarinyar asiri baya cinta,mu barta ta auri talakanta su karata ta fara zube Yara bala'i ya musu yawa,rabu da su mu koma gefe mu Sha kallo Ana Yi Muna kyalkyala Dariya.

Yazed da Bai yarda da Auren Manal ba Amma Jin hassadar su Hajiya karara sai yace a ransa za ayiwa Manal auren mu bita da Addua mu gani,idan ya kasa riketa ya sakar min kanwata Kawai,Manal kuwa dakinta ta koma ta kulle da key take ta Rusa kuka baza a Mata aure ba,tana kuka tana zagin karatun Boko.
Su Falaqi ne suka taho da gudu suna fadawa Malam Aunty Manal fa tana ta kuka tana zagin karatun boko,Malam hantar cikinsa ta kada gwara ayi Mata auren kawai,Da Kansa sukayi shawara da Yazed.

Yau da dare Farida so take ma ko a mafarki ta sake ganin Fuzail Amma abin ya gagara,ta daina mafarkin Sam,Farooq ta dinga tsinewa duk shi ya jawo Mata,Kwanciya tayi saman katifarta tare da danne fuskarta da pillow tana cewa Fuzail yau kazo Dan Allah,Zo Nayi mafarkinka Fuzail,Zo Mana kaji ta sake rumtse idanunta tana wutsil wutsil da kafafunta saman katifarta tana Yeewwww.......Zo......Fuzaillllllll.......Zo nan Nayi Mafarkinka, Hajiya ce ta leko Jin Surutun Farida,Tace da tausayi na cire Rai ba lallai yazo ba ko a mafarkin,Ina tsoro kar arzikin Nan ya wuce Ni,Farida Tace ai Kuwa da Bola Zan koma da Zama na haukace Kawai,Hajiya ta bude Baki tace karfa Muna Nan muji zaiyi aure? hmm ai Kuwa kabari ne yake kiran ko wace Amaryar wallahi da wata ta aure shi gwara ayi min daurin Rai da Rai a gidan yari yafi,ko Kawai ku Haka Ramin Kurege ku binne ni Haka a ciki,Hajiya Baki Bude Tace kina da hankali Kuwa? Idan kin mutu Ni fa? Farida Tace ga su Sa'iha ne,kuka Hajiya ta saki yau Ni na shiga Uku nasan da gaske kike Farida ta juya tayi cikin dakinta,Farida Dariya tayi ta sake yin Mika tana cewa Wayyo Fuzail ka rungumeni ko a mafarki ne Haka Farida tayi bacci Bata Yi ko mafarkin Tanko ba bare Fuzail.

Washe gari Manal kwana tayi tana kuka a dakinta ta kashe Wayarta gaba Daya, Yazed ya buga Mata kofa ta Bude Ido jage jage da Hawaye,Tsaki Yaja yace ke yanzu Baki ji kunya ba?Manal ta daga Kai Wai ae Bata ji ba,ai shike Nan kice idan da gaske yakeyi Malam yace ya turo manyansa bayan sunzo zamuyi Bincike muma,Manal sai kuka ya tsaya cak Nan take ta washe bakinta tare da Furta to Allah ya bar zumunci Yaya,Allah ya Kara Mana son junanmu,shi yasa Nake ji da Kai, ko kulata baiyi ba yayi tafiyarsa.

Tsalle tayi tare da fadawa saman katifarta sabo da Murna, Wayarta ta jawo ta Kira Fuzail,Lokacin Suna tare da Ameer a part din su Ameer, Yana dagawa yace ranki ya Dade,Dariya tayi tare da furta tare da naka,ka tashi lafiya? Nayi Fushi sai yanzu Zaki kirani tun safe Ina kiranki Baki picking ba,Kayi Hakuri Muna meeting da Yan uwa ne, Alright Yaya Yazed din me yace a kaina? Manal Tace ka lashe zabe nawan,Allah? ya tambaya, Tace sun dangwala maka Yaya Yazed ya maka Signing,Malam Ma Ya manna maka stamp a Office dinsa,Dariya Fuzail yake tare da furta Good My love, ai in fada maka shi da Malam sunce idan da gaske kake Yi ka turo manya,Kawai kice na Zama Ango, Ameer ya kalleshi tare da tabe Baki a hankali ya Furta sai kace wata Babbar Budurwa ji yanda yake murna kamar me,Fuzail yace kice gobe za a kawo kudin aure,Manal Tace Ina laifin ma Jibi ko Nan da kwana uku,Ameer yace ka nuna fa da gaske kakeyi ka fitar da yarinya kunya Kawai a barshi jibi za a zo,Fuzail yace Ameer yace Jibi yayi kice Jibi za a zo,Manal Tace to tare da kashe wayar ta fita domin sanarwa Yazed.

Yazed yace to ba damuwa,Fuzail ya sake Kira yace ta tura Masa number Yaya Yazed Bata San Mene ba ta tura Masa dai,Fuzail ya kalli Ameer yace yanzu ya za ayi kenan? Ameer yace karya ta Kare a aure dai kasan ba karya babu Wasa sabo da Haka yanzu yakin zamu tunkara Kawai ayi ta Kare,mu samu a sirri a fadawa Yazed komai,ita Kuma Manal Kar ta sani sai an daura muku aure wallahi idan ta sani zaku Yi fada ne kasan karya ba Dadi Kuma mun Raina Mata hankali,to ai munyi ne da kyakyawar manufa Banga abin damuwa ba,kasan fa Manal da sauran Mata ma yanda ta ganka tana so a Haka take sonka ba ruwanta da kudi,Ni na fada maka Manal sai an Kai ruwa Rana da ita Amma duk bala'i idan an Riga an daura shike Nan Igiya na hannunka sai yanda kaga dama,kaga Umminka da Sarki tare da Yan uwa Dole su kyaleta idan an daura yanzu Target dinmu Yazed da Malam su zasu sani a sirri farko kenan sai masu Kai kudin Aure kaga Abba na baida matsala Waziri Kanin sarki kasan duk aure idan ya taso shi ne akan komai Kuma an wuce wajen nayi Masa bayanin komai a nutse ya fahimta yanzu dama ai ba da Memartaba za a Kai kudin ba,manya ne maza,Abba nasan zaiji da komai tunda mun Gama komai,Fuzail ya kalli Ameer Yana Kora lemo yace kana so na da yawa Dan Uwa,anything for you Bro shima Ameer yace.

Washe gari Fuzail waya sukayi da Yazed yace zaizo gidan zasuyi magana shi da Malam,Yazed yace sai kunzo,washe gari Manal Bata sani ba ma Bai fada Mata ba, Shukrah tazo wajenta suna tsakar gida a zaune Manal,Sai sallamar maza ta ji,tana daga kanta suka Yi Ido hudu da Fuzail tare da Ameer Dukkansu Yardi Suka sa Ishurunka Maraya,Ameer nasa fari,Fuzail Kuma Sky,duk da Haka sunyi kyau,Shukrah ta kallesu Sam Bata Gane Ammar ba Wanda ta gani da gashin Bob merly wannan gashi ne Kawai normal,A ranta tace shi dai wannan Ameer abokansa duk masu uban gashi,Manal ta kalli Shukrah Tace shine fa saurayina me gashin,Shukrah dai tunda taga yadin jikinsa tasan Manal cikin wahala zata jefa kanta kawai Amma sai tayi Shuru da bakinta.

Anci Sa'a Hajiya Bata gidan sun tafi yawon Maula wajen danginta tare da Yarta Kuma kawarta Farida,Manal tashi tayi ta dakko sabon Hijab dinta data Siya me hannu maroon ta saka,duk tunaninta akan kawo kudin aure ake wannan meeting.

Shukrah Tace ko duk akan kudin Auren ake wannan shawarar? Me kika gani? Manal ta tambaya,No ba komai nasan dai idan mutum Bai da Hali sai kiga akan dubu goma Ana ta shawara a kanta,Fuska Manal ta bata tace Wai ku Yan birni meke damunku ne Haka? Kowacce kudi -kudi shi yasa aurenku baya karko,je Kauye ki gani wallahi yarinya tana mugun Shan wahala Amma ko yaji Bata taba Yi ba,Kuma yanda takewa miji biyayya sai ki rantse duniya yake Bata gaba Daya,ta dauki aure Ibada ne,ta hakura da Jin dadinta,wasu mazan ma zaluntarsu suke Yi Kawai Amma kiga tayi zamanta ta hakura,wasu ma su ke ci da kansu duk sun fice a hayyacinsu amma babu bazawara matashiya,Indai Kinga bazawara matashiya to mutuwa mijinta yayi ko kuma wata babbar kaddara Amma badai akan abin duniya ta fito ba.

Kije ki gani yanda butar me gida daban,kwanon abinci,ba a Isa ko Dansa yaci abinci a kwanonsa ko cokalin megida daban ne sabo da ganin darajarsa da mutuntuwa,Ana bashi girmansa komai sai da izininsa akeyi, Kawai kice Farooq talaka ne zasuyi shawara Bai da kudin kawowa Zaki min wani kwane kwane to a Haka nake sonsa ai ba ke Zaki zauna min ba,Shukrah ta zaro Ido tare da Furta Allah ya Baki Hakuri daga Wasa,Ameen wannan ba Wasa bane cin Fuska kika min ku dama Haka kuke Baku iya magana ba sai Kawai ku kwabowa mutum magana,shi yasa Wasu idan Suka Yi aure suke fada da mazajensu sabo da Rashin iya sarrafa harshe, a koma baya a duba rayuwar Iyayenmu ai ba Haka Suka Yi ba,ko a Bayan Ido mace ta zagi mijinta gani akeyi kamar ma Allah ta taba,Mukus Shukrah tayi.

Rannan Ina jinku kawayenki Yan wajen akinku sunzo kuka hadu Kuna ta zagin Mijin Yusrah,Kuma itama wawiya harda ita tana tsinewa mijinta tana zaginsa akan zai Mata kishiya Kuna tayata ita Kuma ta saki Baki tana ta tonawa kanta asiri wallahi ku gyara halinku barikin Nan da Iya shege muma fa mun iyata,kudin Nan mun San dadinsa hakura mukeyi Kawai Zaki fada min magana Ina ganinki Babba da hankalinki Ashe kema gososuwa ce? Shukrah tace to jaraba naji Haba wannan masifa Haka akan Farooq,Murmushi Manal tayi tace ai kece Ni Ina da zafi gaskiya,to Afwan cewar Shukrah.

Ameer shi ya samu tiryan tiryan ya kwashe labarin komai ya Bawa Yazed da Malam sabo da mamaki kasa magana sukayi sai da ya cire gashin ma suka tabbatar,Nan take Malam da Yazed murna ta kamasu Kuma Manal ta birgesu, hankalinsu ne ya kwanta da Auren,karshe Suka ce a sirrinta auren,Yazed da Malam Suka Fara tunanin mafarkin Farida da yanda abin ya faru Wato Farida Akan Manal take mafarkin,gashi ita ta fara haduwa da shi Amma ta wulakantashi ta samu dama,Malam a ransa yace iko sai Allah Farida tayiwa kanta Ashe da gaske ne mafarkin nata amma ta gudu ta bar ladanta ita da uwarta mafarki ya Kare Kam,Yazed zai Basu labarin mafarkin Farida Malam Yayi sauri ya canja zancen ya Hana a fada musu,Fuzail yace sisi baza ku kashe ba a bikin,Sannan kafin bikin Inshaallah za a canja ginin gidan nan,Yazed Ma Idan ka karbi takardunka ka sanar min,Yazed shi dai mamaki yakeyi wata azurtawa ta Allah dare daya,a wajen Yazed dare daya ne mana,Malam sai murna da farin ciki yakeyi ,Su Fuzail suna gamawa Suka fito Har Yazed Sai Manal taga Yazed Yana ta murna,Sai taji wani sanyi,Amma gogan Fuzail ko magana baiyiwa Manal ba shi a Dole ya Gama hayewa,Yazed ne yace baza ki raka su ba?Manal Tace to ya kulani ne? Kee Yazed ya daka mata tsawa...mikewa tayi tare da tafiya rakiya,Shukrah ta zauna sai faman satar kallon Yazed takeyi ita dai akwai son me kyau,gaba Daya tunda taga Yazed ta nacewa zuwa gidan tana fakewa da Manal.

Manal tana fita soro inda su Ameer suke Ameer

Please Login or Register in order to submit comment