Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Buri ace ya zabe ta,Yana gamawa ya Mike ya bar part din gaba Daya zuwa sashen me martaba.

Sarki Yana ta murna yasan ma a cikinsu Dole ya zabi daya, Fuzail ya shigo Sarki da murna yace you can speak English today,Fuzail da hausarsa ya fara kokarin magana Dole fa shi sai ya koya yace Babu,Sarki yace ban Gane babu ba? Zancen kurame yayiwa sarki Wai ba wacce tayi,ran sarki ya baci yace duk kyawunsu? Fuzail yace Yeah Babu, sarki masifa ya shiga Yi masa,Fuzail shima yace ya daina turancin a Haka zaina magana,ai Kuwa da zancen kurame ya nunawa sarki Kirjinsa yace One of them is too big,da zancen kurame ya gwadawa sarki idan suna bacci Boobs dinta zai dameshi,Sarki ya rufe Baki da sauri sabo da kunya ta Gama kamashi,da sauri ya canja zancen yace sai wace tayi Kuma shima ya Masa da Maganar kurame,Fuzail yace daya...no shape, she is like 1, Sarki yasan Kawai bayaso ne shine zai Masa tsari yace cikinsu babu wacce tayi? Ya tambaya da turanci,Fuzail ya furta capital YEAH,shima da turanci yace a bashi lokaci zai samo da Kansa,Sarki Bai matsa Masa ba,ya yiwa matan kyauta Suka koma gidan Iyayensu gwiwa ba kwari.

A Haka Matan sarki da Yan Uwan Fuzail sai tallan mata suke kawowa Fuzail amma Sam Bai zaba ba yace duk Basu Yi ba,har an gaji an kyale shi,Yau Sarki ya matsa Masa sai yaje ya zauna a fada yaga yanda ake mulki,kayan sarauta aka sashi ya saka Dole yaje,Yana zuwa ya Iske masu busa Algaita suna ta busawa sarki sabo da Dole ne kullum sai anyi ta a Gaban sarki da safe,ai Kuwa Fuzail yaji kida yaki karewa gashi Yana tausayawa masu Algaita yanda suke kunburo kumatunsu,tun Yana kallo Yana danne zuciyarsa har ya kasa ya daka musu Tsawa tare da mikewa tsaye Yana masifa a Fadar yace Wai sai Kun cire kumatunku? Nawa za a baku please ku bari Nan,ba ruwansa ya kunyata Sarki a Gaban manyan masu sarauta,Ba shiri Me matarba yace yaje inda zai je ba sai ya zauna ya ga wani yanda ake mulki ba.

Kuma shi Fuzail ba ruwansa da wasu Fadawa Bayi da kuyangi duk Fadawan Nan maza Hannu yake mika musu suna gaisawa,matan Kuma Hannu yake daga musu,an Masa fada yace shi bazai iya ba Ana gaisar da shi Yana share mutane sannan musulunci yace ayi musabiha da Sallama Dole aka barshi Nan ma.
Akwai abokinsa Guda Daya Dan gidan Kanin Mai martaba Kuma wazirin sarki Ameer,Ameer Dan Waziri ne tare Kuma sukayi University da Fuzail sabo da Haka a Nan Baida Abokin da ya wuce Ameer,Shima Ameer Yana da sarauta,shi Kuwa Fuzail yace Bai so shi Business man ne ko a can Yana da Company shi Karan Kansa me kudi ne Bai dogara da kudin Iyayensa ba,akwai shi da son Neman na kansa tun Yana yaro Hajiya Ayusha Umminsa ta dorashi a Harkar Business dinta har ya girma Kuma ta bashi jari me yawan gaske Haka Sarki ya Kara Masa shine yake Harkoki da dama na Business masu kawo kudi,Yana da shares a wani katafaren Mall Dake Korea Republic,sannan Yana da shares a wani Company na kera motoci,Haka Yana shares a hukumar kwallon kafa ta wani team dake Brazil,ko ta Ina kudi shigo Masa sukeyi dama sai da kudi ake Neman kudi,sai kaga Kamar baya neman kudi Kuma a Haka millionaire ne na gaske duk yafi Yaran Sarki kudi sosai sabo da a waje akwai Harkoki na samun kudi idan kana da jari.

Ameer ne zaune a palon Fuzail,Cikin Harshen turanci Fuzail yace Ina son Inga rayuwar talakawa,tunda na taso rayuwa kala daya nayi ta masu kudi,ban San Daya bangaren talakawa me suke ciki ba,Ina so Naga irin rayuwarsu,Ameer yace ya kamata Kuwa amma Kai Mene damuwarka Allah ya baka kudi Ina ruwanka da su,idan taimako zakayi kayi Kawai amma ta ya zaka ga wani rayuwarsu.
Na fa tambayi Me martaba zanyi tafiya nace Masa Zan je yawon Bude Ido a Nan Nigeria Zan Shiga kauyuka zanyi Kamar 1 to 2 weeks sannan yace indai ba tare da Kai zamu tafi ba bazai barni ba,Amma Indai dakai zanje ya Amince ko gobe zamu iya tafiya.

Dariya Ameer ya dinga Yi yace Shikenan Prince ban Isa na kasa bin umarninka ba yaushe zamu tafi? Fuzail yace gobe amma fa kasan baza muje a Haka ba,ka samo Mana kayan talakawa mu saka sannan Ni gaskiya sai na canja ma fuskata Zan saka hular gashi ta maza me uban yawa sannan na Kara da gemun karya kaga idan mun Shiga mutane babu me ganewa su waye ko ya kace? sannan Suma talakawan baza su gujemu ba tunda munyi iri Daya da su cewar Ameer tafawa Suka yi suna ta shirye shiryensu.

Washe gari da zasu Yi tafiyar cikin shigarsu ta Alfarma sukayi Sallama da kowa Suka fita,suna barin gidan Sarki Wani Guess House Suka shiga me kyau anan Ameer ya saka wani dogon wando jean Wanda yaronsa ya tura layin Yan gwanjo ya siyo musu kayan aka wanke su tas,Ameer Dogon wando ya saka jean black duk ya Dan kode da ka gani kasan na talaka ne,t-shirt dinsa wata Grey me karamin Hannu shi Bai rufe Fuskarsa ba.
Fuzail Kuwa Wandonsa blue jean ne 3qutr da t-shirt me dogon Hannu wata me zanen layi layi red and Black,Wani hular gashi me uban yawa na maza ya saka a Kansa sai kace a Kansa aka halicceta,babu Wanda zai Gane sawa yayi yayi wani kyau abinka da me kyau,Gemu dogo ya Kara a kasan nasa da saje duk Fuskarsa ta Kara Rufewa da gashi duk Wanda yasan Fuzail to ba shakka bazai taba Gane shi ba duk da yayi kyau,skin dinsa ce Kawai ta nuna Hutu,suna kallon kansu a mudubi suna ta dariya,Ameer wankan Tarwada ne shi,Bai Kai Fuzail tsayi ba amma shima ba baya ba ya hadu.

Fitowa sukayi Suka jawo wani tsohon machine da Ameer ya siyo a wajen wani bakaniken machine,Dariya ce ta kamasu Suka dinga yiwa kansu Dariya Musamman Fuzail Bai taba Dariya ba irin ta yau ba Ameer har mamakinsa yakeyi yanda yake nishadi,Ameer ne zai tuka machine din Fuzail ya hau bayansa Yana dariya ya daki kafadar Ameer yace let's go man.

Ameer Yaja machine cike da kwarewa,Fuzail Cikin turancinsa yace a fara zuwa unguwannin Talakawa sai mu shiga kauyuka baza mu koma gida ba har Jigawa state sai munje,Ameer yaci gaba da tafiya Yana bin unguwannin Talakawa na garin suna kallo wani abin ya Basu tsusayi wani ya Basu Dariya da sha'awa,Wani abin ya Basu haushi,Har Yamma suna yawo gaba Daya yunwa ta kamasu,lokacin Kuma Farida taci Uwar kwalliya cikin wani lace dinta Dan dubu goma fari tas ta tafi gidan Sarki yau ta rantse sai taga masoyinta Fuzail.

Tana tafiya a layinsu tana yanga,Manal Kuwa tana gida yau ma tayi Awara da yawa gashi ba Wanda yazo ya Siya har Yamma tayi ganin zata sake tafka asara sai Kawai tayi wanka ta Sanya doguwar rigar atamfarta Leda wata maroon and milk tayi kyau dake me kyau ce Manal fara tas ga kyan sura ko Bata Yi kwalliya ba kyau takeyi,gashi Yazed da Malam Basa Nan ya tafi kauyen su Malam za ayiwa Malam maganin Hausa ko za a dace sai sun kwashe sati biyu kafin su dawo.
Dole ta dauki katon botikinta na Awara ta fito da Niyyar ta zaga ko zata samu masu siye,tana tafiya a layinsu Kamar zata Yi kuka ba mutane ko mutum Daya a layin Kamar ba kowa a layin nasu Haka take tafiya ita daya.

Farida Kuwa juyowa tayi ta hango Manal da bokitin Awara ta dinga dariya ko kallon hanya Bata Yi tana faman yiwa Manal Dariya,Kawai Su Fuzail Suka yanko kwana sai ganin mace sukayi a gabansu,Fuzail ya saki Kara,Ameer ya firgita garin zai kaucewa Farida Kawai ya daki jikin katanga da machine din Suka Fadi gaba daya,Farida tsorata Kawai tasa ta Fadi a kasa Amma ba abinda ya sameta ta Mike da sauri tana Tsaki tana goge jikinta tsayawa tayi akan Su Fuzail Wanda basa ma Hayyacinsu Amma ta dinga zunduma musu ashar ta uwa ta uba,tana shegu matsiyata talakawan banza,Kun jawo min yanzu sai na koma gida na canja kaya sannan zanje ganin masoyi na.

Allah ya Isa tsinanannu talakawa matsiyatan banza Yan Iska Shegu,Juyawa tayi zata koma gida ta kalli Ameer Ido cikin Ido Tace sai kunci Uwarku yayan mayu ta tafi abinta,Fuzail Yana numfashi sama sama yace kaga wannan Bata taimakemu ba sai fada takeyi,Kamar naji zagi take Yi? Ameer yace ban taba ganin marar tarbiyya irin wannan ba kaji Kuwa zagin da take Mana,Fuzail yace na Gane ai,yau Fuzail ya koyi zagi da hausa a wajen Farida Kamar karatu ya rike a Kansa dama Bai iya Zagi ba, sosai duk zagin data musu ya koya,Ya kalli Ameer yace Matsiyata let's go,kasa tashi sukayi sunji rauni,Manal ta hango abinda ya faru tana nesa sosai Amma Haka ta shararo da uban gudu Kamar zata tashi sama,Botikin awarar ma gaba Daya sakinsa tayi ya tarwatse a wajen tana karasowa wajen su Fuzail ta daura hannaye a Kai ta fara yaren fulatanci itama Hausar Bata ishetaba, karshe tace Hodijam taga Ameer yafi Jin ciwo sai Kawai ta tafi zata cakume shi Fuzail yasa hannunsa da kyar ya ture ta gefe,Manal tunaninta zallan bahaushe ne taga yaki magana tayi zaton rauni ne yai rauni tace Sannu bawan Allah Sannu kaji me tubu tubun gashi Allah gashinka kamar dakin Girkin Annatuna Allah sai an maka Aski sai kace dakin bukkar rigar mu,Bawan Allah idan kayi Aski ai sai kaji dadin kanka.

Me Napep ta tare da sauri ya fito Kuwa ya taimaka Mata aka saka su a ciki ta tafi da su asibiti,ta manta ma Bata da ko sisi.
Amma Haka tasa aka kaisu asubitin Gomnati, Likita Yana dubasu yace babu matsala Yar buguwa ce Amma Ameer sai ya zauna a Hospital na sati Daya shi Kuma Fuzail yau za a sallame shi,Manal Tace Alhmdllh dama Bata da kudin da zata biya,ta rasa yanda zata Yi gashi an Rubuta allaura da magani,Suna kwance a gadon asibiti ta kallesu duk bacci sukeyi ta fita da gudu,Fuzail shi ba bacci yakeyi ba yaga Sanda ta fita a baya ya bita a hankali har wajen Asibitin ya hangota tana bara Manal tana a taimaka min bayin Allah ga Kati marasa lafiya ne Dani Bamu da halin daukan nauyinsu,Haka yaga tana bin mutane tana bin duk wata mota da tayi parking,mamaki ya kashe Fuzail dama akwai mutane irin Haka tayi bara Dan ta taimaki wani,to me yasa ma ta nace sai ta taimake su,Wani me kudi ne ya karbi katin Guda biyu a Hannunta Yana kallo Suka tafi Chemist na Asibitin aka siyo Mata magungunan,Fuzail Kuwa ya koma ya nannade a Gadonsa,sai gata ta dawo da sauri tana murna Tace Alhmdllh na samo kudin maganin gashi an siyo komai har kudin cin abinci ya bamu Allah ya biya,.

Likita ta Kira aka zo aka musu abinda ya kamata,Fuzail a gadon bayansa yayi wani mugun kujewa wajen Babba sai jini yake Yi,shi Kuwa Ameer a kafa ne da goshinsa yasha wahala shi yasa yafin Jin jiki.
Zazzabi ne ya rufe Fuzail sosai ga yunwa gashi Bai Saba da wannan Harkar wahalar ba,Kuma sabo da Rashin gado ga marasa lafiya da yawa a kasa a Haka aka sallami Fuzail,Fuzail Yana Rawar sanyi da turanci yayiwa Ameer rada a kunne tare da tuna masa Wai yayi amfani da Atm card ya kula da kansa,Ameer ya amsa a boye duk Manal Bata kula da me sukeyi ba.
Fuzail da kyar yake tafiya Tana rike da Ledar magungunansa ganin Yana tangadi Bata San yunwa ba ce,tausayinsa taji ta rike hannunsa,tsigar jikinsa ce ta tashi yarrrrrr.....ganin Kamar bazai iya tafiya ba ta juya Bayanta tare da tsugunawa a kasa tare da furta hau na goyaka,Dariya ta bashi sai da yayi Dariya Bata sani ba,mikewa tayi ganin Bai hau ba ta rike shi sosai suna tafiya a Haka har gefen hanya,har ga Allah zazzabi ne me zafi ya Kama Fuzail Yana ta Rawar Sanyi,Napep Suka shiga tana tambayarsa Ina ne gidanku? Fuzail Yana Jin hausa ba can ba amma ya rasa me zai ce Mata yanda zai Bata bayani me gamsarwa,long story,labari is tsawo,Dariya Manal tayi Tace labari is tsawo? Kalmominsa Kawai yake Dan hadawa da dabara ya kwaba da turanci,Manal tace Ina ne Unguwar ku? Da kyar yace Kauyen nisa,My Money my Everything yan Fashi karbewa,babu ko Mai,ba iyaye,Ba kowa sai Family can kauye,Manal taji wani tausayinsa ma'ana talakawa ne bashi da kowa ya Tara yan kudinsa Yan fashi Sun kwace,sannan Maraya ne shi sai Yan Uwa a can kauye me nisa,Manal ta furta Allah sarki Ashe irin rayuwar mu Daya,Tace Neman kudi kuka Zo Nan garin? Yace ae Bamu da kowa talauci ne.

Tunda naji halin da kake ciki sai naji na samu Dan Uwa,sai naji ka Zama wani garkuwa a wajena sabo da rayuwar mu ta talauci tazo daya,Manal ma ta bashi Dan gutun labarinta na talauci da wahala yanda zai gane,shi karya ya Mata Amma sai Kuma da yaji nata da gaske sai ta bashi tausayi sosai.

Tace yanzu kaga Mahaifinmu yana can kauye Ana Masa magani Yayana Baya Nan suna tare Zan kaika gidanmu tunda yanzu baka San Inda zaku je ba,idan aka sallami Dan uwanka sai ku tafi tare,Shi dai Yeah Kawai ya Furta sabo da zazzabi da yunwa sun Gama kashe Masa jiki.
Farida Kuwa Bayan ta koma gida Kaya ta canja Kawai ta dauki Hanyar Gidan Sarki a Taxi,sai da taje wannan saurayin nata Bafade yace ai kinyi rashin sa'a Yarima yayi Tafiya yau da hantsi,shi yasa nace kizo da wuri kafin ya fita Kuma sai Nan da sati biyu zai dawo gashi yanzu yayi tafiya,Jiki a sanyaye Farida ta juyo gida tana Hawaye da kukan bakin ciki matsiyata talakawan sun jawo Mata Bata ga masoyinta ba Allah ya hadani da matsiyatan Nan wallahi tunda Suka cuceni sai na musu abinda har abada baza su manta ba,Har Farida ta dawo gida tana kuka tana Bawa Hajiya labarin sannan tana tunanin Ina zata sake ganin Wanda Suka bata Mata lokaci Bata ga masoyinta ba ta samu ta musu wulakanci na gaske tunda sune suka kusa Kade ta.

Manal Kuwa gidansu ta shigo da Fuzail Yana zazzabi,gashi Yazed ya garkame dakinsa,ta bayan dakin ta koma dashi tare da shimfida Masa tabarwa,sabo da tsabar sanyin da yake ji Haka ya kwanta Yana karkarwa yace Blanket,Bata Gane turanci yace Bargo,da sauri ta tafi dakinta ta dakko bargonta tare da lulluba Masa tana Masa Sannu, Bayan dakin ta Bari ta fito lokacin dare ma ya fara ta hango Farida a zaune ta zuba tagumi tana Tunanin Fuzail dinta,Manal Tace Dan Allah Farida Kinga ke Babba ce Zaki fini iya kula da marar lafiya Wanda Suka Fadi a machine dazu kin tuna su Wanda Saura kadan su bigeki,ai nayi tunanin Zaki taimaka musu sai Baki iya hakan ba,yanzu Guda Daya ciki Yana gidan Nan Dayan Yana asibiti Dan Allah kije akwai maganinsa ki tayani bashi ki Dan zauna da shi,so nake Zan koma asibiti na siyawa wancan abinci na Kai masa,Farida a ranta taji Dadi dama wanted take nemansu sabo da ta huce haushinta,sai Tace to zanje na kula da shi,Manal tana murna ta fice da sauri tana komawa asibiti da take away dinta na shinkafa da Miya da salat Wanda a wajen wata makwaftansu ta Karba suna mutunci, Sai ta Iske wani Mutum Yana jinyar Ameer,Ameer Yana cin abinci yaji sauki yace wani bawan Allah ne yake jinyar Dan Uwansa yaga ba kowa a wajena shine yazo ya taimaka min,Manal sabo da godiya har da tsugunawa Bata San mutumin Yaron Ameer bane,Tace to tunda Naga da sauki kana cin abinci Bari na koma gida sai gobe Inshaallah,da sauri ta fito tare da shiga Napep ta koma gida.

Farida a lokacin ta tafi da ruwanta botiki Guda sabo da maralafiya baya son ruwa,sai da ta ebo me sanyi sannan tazo Fuzail Yana kwance tazo ta fisge bargon tana Danna Masa ashariya ta shiga sheka Masa ruwan a jikinsa me sanyi sannan ta dinga kwada Masa Botikin a bayansa,Fuzail ya kasa kwakwaran motsi sabo da azaba,Ya fara kokarin tashi da rarrafe Yana kokarin guduwa Amma Farida tana watsa Masa kasa,Hajiya ta fito tana kara masa Dan Iska talakan banza yazo ya cuce mu,Manal ce ta shigo da gudu tana ganin abinda Suka Masa Tace Farida kinci Amana ta kin yaudareni yanzu bawan Allah bashi da lafiya kina gani,wallahi wulakanta Dan Adam baida Dadi baka San waye ba a duniya,Dan Adam daraja ce da shi Manal ta furta harda kuka wiwi,Hajiya da Farida Suka ja tsaki Suka Yi hanyar dakinsu suna Furta ai ke tsiya a gindinki ta Kare,ba Kya kula kowa sai banza wofi,Manal Bata kulasu ba ta rike Hannun Fuzail da karfinta ta taimaka da kyar ta jashi dakinta Yana cewa Sanyi,Tana kaishi dakin ta dawo da gudu ta dauki bargo da Tabarmar,Allah yasa tana da ruwan zafi a flask sai ta zuba a wani Dan baho ta sirka ta kawo dakinta,Yana Zaune a kasa ya dunkula waje daya.

Kayan Yazed wata t-shirt da dogon wando Wanda bayan ya tafi ta wanke Masa ta Ajiye su ebo a Jakarta,rigar data jike ta taimaka ta cire masa,rauninsa na Baya ta kalla ba abinda ya same shi ai Kuwa da ruwan dumin ta goge Masa jikinsa tas da Dan towel dinta me Kama da Handkerchief,sai da ta gama Kuma yaji Dadi sosai,I wanna shower my self ya Furta,Manal ba a fahimta sai gwada Mata yayi da zancen kurame,Haka ta fita makwafta gidan wata Amarya da suke mutunci ta samo ruwan zafi me kyau ta hada Masa a bokitin ta Kai toilet sannan ta sake rikeshi harda bashi Sabulu Giv,Hajiya suna ta ce Mata karuwa dama kwartonki ne,Bari Yazed ya dawo,ko kulasu Manal Bata Yi ba ta rakashi har ciki,ya rasa yanda zaiyi yayi wanka,gaba Daya kyankyami yake ji,Haka ya lallaba Kawai ya danyi ya fito da sauri kamar an Koroshi duk da tsaftar bayin.

Tana kallonsa Sai ya fuske Kawai ya nuna normal ai shi ya Saba ma da irin wannan talaucin,kayan Daya cire ta wanke tas ta Shanya tana shiga ta Iske ya saka kayan Yazed Kuma yana Sallah a zaune,Yana idarwa ta zauna a gefensa tare da Mika Masa Ledar take away da Abinci ciki shinkafa da Miya da salat babu ko kifi ,ga Pure water Guda uku.











Sharhi fans pls


AsmaBaffa
[1/1, 10:24 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭












MAFARKIN FARIDA IS DEDICATED TO

DUNIYATA AAMNA GP

















16-20









Official










By
AsmaBaffa










Page naku ne

Rahma
~A
Sophie
Ummy Manga
Xara
Preyaa
Asmie
Minerh
Sadiya
Hauwa J
Ummin Iklas
Khadija











Yunwa yake ji matuka karbar abincin yayi zai Bude tace baka da lafiya kawo na Bude maka,Tana magana ya kafe ta da Ido Yana mamaki Wai dama da mutane Haka a duniya,Karba tayi ta Bude abincin ta sa spoon ta ebo zata bashi a baki,mamaki ya Kama Fuzail Amma ya fuske sabo da yunwar da yake ji ya Bude bakin ta zuba Masa ya ci yaji shegen yaji a ciki ya fara jan yaji,Pure water ta Mika Masa ya karba da sauri ya Sha yunwa tasa ya daure ya dinga karbar abincin Yana ci sai da ya cinye tas ya Sha ruwa, Magungunansa ta dakko ta bashi kwayoyin ya sha badan Yana so ba,Kallo yake Binta da shi tana bashi mamaki a yanda kasar Nan take Dan tsabar ganganci da Rashin wayo ta yarda da su,yaji tausayinta ganin irin talaucin da suke ciki,Tace Wai baka Jin hausa ne? Kai ya daga Mata tare da Furta kadan kadan,sai da yayi minti biyu Shuru ba Wanda yayi magana sannan yace Ina ji,bana iya magana da hausa da yawa,Manal tace Ni Kuma gashi bana Jin turanci banyi makaranta ba Kamar yanda na baka labari Yaya Yazed ya saka Ni a makaranta kaddara tasa na bar gidan Nan Dana dawo Kuma babu kudin da Zan na zuwa makaranta da kyar dai Ina zuwa Islamiyya asabar da lahadin,Mene Islamiyya?murmushi tayi tace makarantar addinin musulunci,Okay ya furta tare da Fadin Nima babu kudi poor man ne Ni,Manal ta Gane nufinsa tayi Dariya Kawai,yace bakiyi Sallah ke babu Sallah? Bana Yi ne jiya Allah yayi girma ya same ni na fara Haila,Aunty Farida Tace period ake cewa da turanci,Yesterday Ni Manal fara period,My ciki ciwo karfin Hali nakeyi ma,Fuzail ya Gane me take nufi shi kanshi yaga yarinya ce sosai shi yasa take abun yara,Murmushi Kawai yayi Bai San me zai ce ba,yace Baki Jin turanci Ina kika San My,Is etc? Yaya ne take koya min na fara iya karatu da rubutun hausa ma.

Ganin talaka ne Dan uwanta ta Mike ta dakko pad dinta data siya jiya Tace ka gani Anty Farida ce tace Dole sai na siyo Ina amfani da ita mugun tsada gareta Naira dari biyu har da Hamsim da kyar na dauki jarin Gyada ta na siyo,Ya Gane wasu kalmar wasu Kuma Bai Gane ba Kawai ya girgiza Kai irin ya Gane din Nan,Jikinsa da yasha duka wajen Farida duk ciwo yake Masa da kyar ya lallaba ya haura saman Yar katifar Manal ya kwanta abinsa.

Ni a Ina Zan kwanta kenan Manal ta tambayi kanta a ranta tana kallo ya fara bacci hankali kwance,Tace yau Dole dakin su Farida Zan koma na kwana ai bai Dace na kwana da Namiji a daki Daya ba amma Bari na jira baccinsa yayi nisa sai na tafi, Haka ta zauna a gefen katifar tana jira baccinsa yayi nisa Wutar dakinta ta kashe dakin ya dauki duhu,Gyangyadi ta fara har ta fara bacci Bata sani ba itama sabo da gajiya bacci ne yayi awon gaba da ita a Haka a zaune, har ta kwanta a kasa kusa da katifar Bata sani ba ta manta da wani bako ma.
12am sanyi sanyin da ake Yi yasa tana bacci Bata San ma ta koma jikinsa tana furta Annatu na,kanta ta daura a saman kirjinsa tare da Rungume shi sosai ta kankame shi,shi dai cikin bacci yaji wani dumi me Dadi da jiki me laushi a jikinsa sabo da Haka baccin ya Masa mugun Dadi,a Haka suka ci gaba da bacci abinsu Manal kwance a jikinsa wani kamshi na Fitowa daga jikinsa na musamman me Dadi kasa kasa.

Basu farka ba sai da Rana ta fito sannan bugun Kofar Manal da ake faman yi ya tashe su a bacci,Da sauri Manal ta janye jikinta Dake cikin nasa a kunyace duk ta rasa inda zata sa kanta sabo da kunya tana mamaki ya akayi ta zo saman katifar ma,Da sauri ta bude Kofar tare da leka iya kanta waje taga Farida ce,Dariya Farida tayi Tace kwartuwa oh Manal an San kwana da gardi a daki,ko kunya Baki ji ba ki rasa Wanda ma Zaki kula sai wannan talakan marar asali Wanda ba'a San asalinsa ba,Mahaukaciya a rayuwar yanzu masu kudin ma ya suka Kare to wallahi duniyace take so ta tashi Nan gaba ance Kafin kiyama ta tsaya sai an shiga tsananin Talauci kasa zata daina yin noma da yawa za a rasa abinci Kinga mu da muke Yan karshen zamani ai idan Muka auri masu kudi mun tsira daga wannan ko da lokacin ya riske mu.

Amma ki duba Malam yanda yake Talaka duk danginmu babu Wanda zai dauke Mana matsalar dubu goma,Rance ma babu Wanda zai bamu bare ya iya daukan nauyinmu,Kalli Manal Malam da mu yaransa yanda muke karbar Cable ta ko Ina Talauci yana ta zanemu da cable ta

Please Login or Register in order to submit comment