Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun 11pm yazo tashar Yana jira shima a tashar sai da yayi bacci ya tashi sai 1am sannan wata mota ta shigo tashar itace wacce Manal ke ciki,lokacin ta gaji da bacci,Ana zuwa ta fara duba Yayanta rabon da ta ganshi ta manta sai waya,Yana kusa da motar Amma Bata ganeshi ba har Suka Gama Fitowa da kullin kayanta, Yana ganinta ya dinga Murna kasancewar tashar ko Ina haske ne,Hannunta ya rike ta firgita sosai sai da ta kalleshi sosai sannan Kuma ta saki ihu da tsalle ta cikwikwiye shi tana Yaya Kaine? Wallahi Kuwa Yaya Yazed ne cab Yaya Haka ka girma? Yazed Yana dariyar yanda yaga Manal gaba Daya muguwar Yar Kauye ta gaske shigarta kadai abin Dariya ne,Amma ta girma sosai ta Zama Yan Mata,yace Manal wannan girman fa Ina Zaki da shi 16yrs kin wani girma Haka,Manal ta washe Baki kyawawan hakoranta Suka Bayyan Yazed yaga Kanwar tasa ta Kara kyau na azaba sai rashin wayewa,dare yayi da yawa duniya ba yarda yanzu bana son tafiyar dare gwara mu kwana a tashar Kinga duk matafiya gasu Nan zasu kwana da Sassafe sai mu tafi,to Tace kawai,Gaban me gasa nama yaje ya Siya musu tsire me zafi,ya Siya musu pure water da yawa a Leda sai lemo Guda biyu ya jata inda yake safe tare da karbo Tabarma wajen wata me abinci a tashar tare da shimfida musu ya zauna,Manal Tace Yaya na gaji da Zama Allah kwanciya nake so Amma bana Jin bacci,yace kwanta to sai kisa kanki a cinyata,Haka Kuwa akayi Manal ta kwanta ta Mike sosai a Tabarmar tare da dora kanta a Cinyar Yazed,sai da ta huta yace to tashi muci naman sai kiyi Sallar da ake binki ki kwanta.

Ta Mike Kuwa tana cewa Yaya amma Kuna Jin Dadi a duniya ku godewa Allah iya hasken Wutar Nan ya isheni Ni nishadi ma,Tana cin Naman Tace shegiya karya Aradu harda kabeji da Albasa a cikin naman,Dariya ta bawa Yazed yace to bana son surutunki Manal kiyi Shuru mu Gama ci,sai da ta koshi ta Sha lemo da ruwa sannan tayi Alwala tare da Gabatar da sallolin da ake Binta,Yana kallon yanda takeyin ibadar duk kusan da gyara Amma baiyi magana ba,tana Idarwa ta kwanta a cinyarsa sai bacci shi Kuwa jingina yayi da jikin bangon Yana ta baccin shima har gari ya waye sukayi Sallar Asuba sai da gari ya waye Rana ta fito sosai sannan Yazed yace su tashi su tafi gida,Tunda Suka fito daga tashar Manal take kalle kalle tana kallon motoci Iri iri Tace wayyo Yaya Dole kuyi ja kalli garin ba gona sai motoci tana ta nune nune da yatsa har suka shiga Taxi zuwa gidansu.

Suna zuwa Kofar gidan duk taga an wuce gidaje na Alfarma amma su nasu gidan shine ma mafi kaskanci a layin Manal tun anan ta Bata Rai tare da cewa yanzu dama duk Wayar Nan da mukeyi Yaya Yazed a Nan gidan kake? Fuska ya Bata tare da furta wallahi zamu Bata zanci Ubanki Nan ba gidan Ubanki bane,Manal tace Kan uba tana nuna wani katon gida Tace dama can ne gidanmu ai da sauki,a waya idan muna waya Watarana kace abinci nake ci,Watarana wanka nakeyi Sisto,Watarana kace karatu,Watarana kace kana kwance hutawa kakeyi ashe duk a Nan gidan kake, Ni Ina ta hango ka a Aljannar duniya Ashe ina,Allah Ashe akwai Yan Muna birni,idan kana birni baka da kudi gwara na Kauye da Kai, Amma da Ko Malam ya dinga Hawa irin waccan motar ta nuna wata mota,Yazed yace shiga ciki muje ransa a bace,Manal Kamar Amarya tace kafin na Shiga gidan Yaya Bari nayi Addua zanyiwa kaina fatan Alheri, kafar damanta ta zura a cikin Kofar ta daga hannu sama Allah yasa Watarana na ganni irin waccan gidan me kyau,Allah yasa Watarana a dinga tukani a irin Arniyar motar can ko me gindin kwado ce Ina so,Allah yasa Watarana na ganni a jirgi,Sannan Yaya Allah yasa Watarana Dani da Kai mu dauki shatar jirgi mu kadai daga Ni sai Kai da Annatu da Malam.

Watarana mu kwana a hotel mu ajiye motar mu a ciki a rufe Mana ita da Tempol, Yazed ya rike Baki yace kema Irin Farida ce Sis? Manal tace a'a Nifa fatan Alheri nake yiwa kaina,shike Nan bazan yiwa kaina fatan Alheri ba Ni wallahi a wajen Allah nake Nema idan zaka roke shi ka roka da Babban masaki,Ina laifi ko motar Dubu dari hudu na siya maka ko ka siya min,Yazed yayi Dariya Kawai yace Ameen to muje,Ciki Suka shiga Farida ta fara gani.

Manal ta fara karewa gidan kallo tare da furta chab Ashe Birnin duk karyar banza ce,gadar sama da haske shine Kawai abin birgewa amma Ashe ta Gina Bata Shiga bane.
Farida ta San Manal Amma sai ta Mike ta ruga daki da gudu Wai tayi gamo sabo da wulakanci,Hajiya ma tana lekowa taga Manal ta ganeta Amma sai ta kwala Ihu ta banke Kofar ta suna lekowa ta window,ita Manal ma Bata iya Gane su ba sabo da rabonta da su tun tana Yar 7yrs da Annatu ta kawota Hutu.

Yazed ransa ya baci matuka sai kace sunga dodo Haka ya shiga da Manal wajen Malam,Malam ya dinga Murna yace Manal Haka kika girma? Ai kinfi Farida ma girma kamar kece yayarta,Manal ta durkusa tare da gaisar da shi tana tausaya Masa yanda baya iya tashi,Tace Malam ai Farida ita jirani wada ce,Tayi gajeriya da yawa Saura kadan ta Zama wada,Haka ake cewa Irinsu Jirani wada Ina zuwa, Madarar Shanu ce take Aiki a jikina shi yasa na girma Haka,Dariya Malam yayi yace to Alhmdllh ka nuna Mata Daya dakin da ba kowa sabo da ko ka kaita dakin su Farida zata fuskancin matsala gwara tunda da daki daban ka sata ciki,Yazed dama ya gyara dakin har ya sa Mata Yar karamar katifa a ciki da Ledar tsakar daki,Manal ta Ajiye kayanta,Yazed ya kawo Mata sabuwar Ghana must go yace ki shirya kayan sawarki a nan,ki fito kiyi wanka sai na kawo Miki abinci,to Manal Tace tare da aikata abinda yace sannan tayi wanka ta canja wata Yar tsangalalliyar doguwar rigar wani yadi Wanda ya ji jiki green.

Yazed Shinkafa da Miya yaje ya siyo Mata harda Nama yanka Uku,Duk gidan ba Wanda yaci komai ba a Dora girki ba sabo da babu kudi,shima Dan ragowar dari biyu ce Dan kar ya barta da yunwa ta fara rigima shi yasa ya dauke ya siyo Mata abincin har da Pure water Guda uku,Zama tayi ta ci ta koshi tare da rufe ragowar sai zuwa Yamma zata karashe abarta.
Ba ko dankwali a kanta gashin Nan yalala abinka da Yar Fulani har gadon baya,da rigarta me Hannun vest ta fito zata fita waje a Haka Yazed ya daka Mata Tsawa Baki da hankali ne? Nan fa ba Kauye bane,Sai lokacin su Hajiya da su Farida Suka Fito,Hajiya tana tabe Baki tace au Manal ce dama? Farida da su Sa'iha suka kwashe da dariya Kamar mahaukata Wai dama Manal ce Amma Kamar aljana? Farida ta Furta tana dariyar rainin hankali,Ran Manal ya baci gata duk ta fisu girma ma ai Kuwa Masatura tace Allah Kamar wata arandoni ...kafin ta rufe Baki Manal ta daure ta da Mari tare da furta Uwarki ce arandoni ba Ni ba,Dan Uwarki sa'arki ce Ni ko Baku Sanni ba? Duk da cewar na Dade ban Zo ba ai nasan Kun sannni Sarai,Farida ta zuciya an Mari kanwarta ta cakumi Manal zasu Yi kokawa,Manal girman Kauye ce ba yanga,gata yarinya Danya me ji da wauta ai Kuwa Kawai surar Farida tayi Kamar ta dauki tsinke ta bugata da kasa ta zaune a kanta ta shiga dukanta ta ko ina,Hajiya Ihu ta saki da kururuwa.

Tana za a kashe min 'yata,shike Nan Fuzail za a maka asara,wallahi Baki Isa ba mun kusa shiga daula baza ki Rusa Mana mafarki ba,Matar Dan Sarkin kike duka? To Dan sarki zata aura kwana Nan wallahi sai an koreki daga garin Nan idan ta Zama matarsa muguwa,Cak Manal ta tsaya tare da tashi daga Kan Farida tana murmushi ta tambaya Allah da gaske Dan sarki zata aura? Hajiya da Gadara Tace kwarai Kuwa ki daina Raina ta kwana Nan zaizo Zaki gani da idonki,Manal harda ihu tace ai aradun Allah ban sani ba,Sannu Gimbiya ta rike Hannun Farida,Farida ta kwace Hannunta tare da galla Mata harara Baki da hankali Ni Zan hada jiki da ke ki shafa min warin Kauye Salon Yarima yazo yaji Ina tashi,Manal duk ta dauka a gaske ne zata auri Fuzail tace ba komai girmanki ne Allah ya samu a danshinki,Na tayaki murna Yar Uwata,Hajiya ta washe Baki Tace to daga yau ba raini Kuma wallahi kika sake taba ta sai ta sa an koreki daga garin nan,Manal Tace ikon Allah yaushe zai zo zance?Hajiya Tace ya kusa zuwa Kinga ko Aiki sai ki dinga zuwa kina Yi a gidan Surakan Farida,Manal ta rike Baki Tace cab Ni Kuma bauta zanyi? Ina Yar uwarta Ina laifin ma a talauce ta siya min mota ta milliyan goma Haka,Baki Suka Bude Farida tace Baki Isa ba wallahi yarinya ai ko keke tunda Baki da mutunci,Manal Tace Dan Allah Yaya Farida kiyi Hakuri ance da ac a gidan ko iya ac ki lamince min in Dan Sha ko ta kwana biyu ce ko ma ta yini Daya ce.

Yazed da Malam suna jinsu suna ta dariyar Haukar Su har Manal da Bata San duk a mafarki bane,Farida tace sai dai idan daga yau Zaki dinga wanke min kayana kina gyara Mana gidan Nan sannan duk wani Aiki ke Zaki Yi q gidan Nan to idan ya aureni har Makkah Zan sa ya kaiki, bana so a dinga Bina gidan sarauta Ana kunyata Ni,Kun San gidan sarauta basa son Hayaniya kudi Ne da mulki dankare a gidan,Manal tafi tayi tace Allah ya yarda na Yar Uwa shike Nan Dan aikin gidan Nan ai karki damu Matukar ac da nake Jin labarinta naurar sanyi zata fifita Ni ba abinda bazanyi Miki ba.

Karki sake Fatarki ta lalace Yaya Farida,Farida Tace ke dalla Yar Kauye Aunty ake cewa Aunty Farida karki sake ce min Yaya Haka Kawai salon Fuzail yazo yaji kauyancinki,Manal tace gaskiya Anty Ina yinki irin wannan soyayya Haka,Farida tace Yau zamu Fara shirye shiryen ya auren Nan nawa zai kasance,littafi ma Zan siyo zamu rubuta komai,Manal tace ai Yasin hakan yayi ayi sauri a tsara komai sabo da idan lokaci yazo komai an tsara yafi.

Farida kallon Manal tayi Tace ranta min Naira Hamsim idan Fuzail yazo Zan biyaki abarki ba kyauta nace a bani ba,Farida da sauri ta fada dakinta tana murna harda Waka ta dakko Hamsim cikin kayanta ta bawa Farida,Hajiya Tace Masatura karbi maza kuje kanti ke da Falaqi ku Siyo littafin ku dawo,karba suka Yi suka tafi siyo littafin,Manal tana kallo Suka dawo aka dakko Tabarma tare da shimfidawa a gindin bishiyar Dake tsakar gidan har Hajiya,Farida ta rike Biro tace ranar Thursday za a fara bikin Haka na gani a mafarki,Hajiya tace Party ne ranar a Raais Guess palace kin San Nan sai manyan mutane maza rubuta,Farida ta rubuta tare da cewa sai Friday ranar Bridal Shower 8pm,Masatura Tace kamata yayi a Juji palace Kin ga sai Gomnoni ne ke shiga wajen sabo da tsada,Farida Tace haka za ayi,Sunday Kuma daurin Aure da Kai Amarya sabo da kar a ja bikin gwara na hau karagar mulki na Zama Gimbiya cikin gaggawa,a mafarkin Nan Naga ba Delay a Harkar bikin cikin gaggawa aka daura.

Hajiya Tace to yanzu Kinga Muna da munafukai da mahassada a Unguwar nan, mutane suna gulmar mu suna zagina cewar Ina fasa Miki,Ina lalata ki,Baki da tarbiyya,to Dan ubansu rubuta duk Wanda muka sani makiyanmu a Unguwar Nan,Yana aurenki zamu sa aci ubansu,Farida Tace Fire for Fire wallahi duk sai mun Rama zasu ci ubansu.

Masatura Tace Haka Maman Haneef ma ta dinga Mana Dariya Wai Ina Mijin mafarki yake,Da Sauri Hajiya Tace munafuka sai anyi auren su lallabo suce zasu kulla alaka Dan a taimaka musu to karya sukeyi Basu Isa ba,Farida tace waye ya Isa ma yazo Gidan sarautata yace zai dinga nuna min yanda Zan gudanar da zamana a masarauta,Hajiya Tace rubuta Maman Haneef itace a farko cikin Bracket kisa Uwar Gulma sai mun sa an kore su daga garin Nan gaba Daya mun siye gidan nasu na gado da suke takama da shi,Haka Farida ta rubuta Kuwa,Hajiya Tace ta Biyu Hajiya Abu Naga tana min gani gani kwana Nan rubuta ta Dole ta ci ubanta Nan gaba,Nan ma aka rubuta,Hajiya Tace saka Sunan Malam Zikirilla Rannan harda Yi min wa'azi Wai na dinga kula da tarbiyyyarki kaji munafuki yarsa na lalata da zai dameni Dan bakin ciki,Farida ta rubuta Malam Zikirillah prison na shekara goma a gidan yari,Rada Hajiya tayiwa Farida Tace rubuta Manal a ciki tsinanniya na tsaneta so nake Ana auren a dauketa Aiki a gidan,ko Kuma kafin a aureki mu kaita can aikin Bauta,Manal Bata iya karatu da Rubutu ba a gabanta aka rubuta sunanta da duk irin azabar da za a gana mata ba tare da ta Gane ba,ita dai tana mamaki akan za a auri me kudi Dan sarki sai a wulakanta mutane Kuma tun ba ayi Auren ba,Yazed ne ya fito cikin kodaddiyar shaddarsa peach zai fita yace Manal tashi bana son ki shiga wannan haukar wannan Mijin da ake lissafi duk a mafarki ake ganinsa,Manal Tace ban Gane ba? a takaice ya Bata labarin a Gaban Kuma su Hajiya,Manal sabo da dariya harda faduwa a kasa tana kwalla tace Wai dama a mafarki ne? Hajiya ce ta Bata Rai matuka taji haushi Manal Shuru tayi ganin Rai zai baci Tace fatan Alheri nake Miki Anty Farida Allah ya tabbatar.

Yazed Hannunta ya rike tare da janta gefe yace bana son fada,karki Shiga harkarsu bare kuzo Kuna tayarwa Malam Hankali idan aiki ne ko mene idan Basu Yi ba kiyi,gidan Nan kazamai ne idan Baki gyara ba babu me Yi kiyi Hakuri da rayuwa kiyiwa Hajiya Biyayya,itama Faridan ta girmeki ki Mata biyayya,nasan halinki da Shiga abinda ba ruwanki wallahi naji anyi fada dake sai na Miki dukan tsiya a gidan Nan,ba ruwanki,duk abinda zasu Yi ba ruwanki kinji na fada miki,ki jira zanyi kokari na sakaki a makarantar Boko da Islamiyya ko ta Gomnati ce sannan Zan dinga koya Miki karatu da kaina a gida,Manal tana murna Tace to Yaya Inshaallah,Fita Yayi Ita Kuma ta koma dakinta.

Kwanan Manal Daya a gidan ta fara aikin gidan Kamar jaka,komai ita ke Yi ga Yaya Yazed ya hanata Taki yi,Idan baya Nan itace take kula da komai na mahaifinsu Malam,Su Kuwa su Farida shirye shirye sukeyi na zuwan Dan sarki abinsu,Yazed gaba Daya ta Gama Kare Masa da talauci ga ba gonakin Malam yanzu,babu nemowa sai shi,Makarantar ma da yake kurin zai sa Manal sai a ta Islamiyya ya saka ta Kawai Allah yasa har boko Ana koya musu,idan ta dawo gida ta Gama uban aikinta Yazed Kuma zai Sata gaba suyi karatu,a hankali Manal ta fara Dan tsintar wani abu,sannan Yana kokarin hanata yin shigar su ta kauye,Yana Dan sata a Hanya kadan,Su Kuwa su Farida ganin Haka sai Suka Fara bakin ciki Suka tsani Manal ganin sai Kara kyau takeyi kyawunta Yana Fitowa duk Kuwa da irin wahalar aikin da takeyi sati Daya tal ta fara canjawa,tsoro ya Kama Hajiya ta ja Farida Daki tace Dan Ubanki Farida tsoron Kyawun Yarinyar Nan ya kamani,Kinga kyau Haka Kamar aljana to wallahi Ina tsoro Kar Yarima Fuzail yazo ta birge shi,Farida ta buga tsalle Tace wallahi wallahi wallahi Kuwa da sai na kashe Manal har lahira da wuka, yankan rago Zan Mata,Nifa na tsani ma yanda Yaya Yazed yake Mata Yana nunawa sunfi kusanci.


Hajiya cikin rada tace Ni ai kau da Kara ba Wani Abu bane a wajena,Muje wajen Malam Dan Haru ayi Mana fata fata da su,mu rabasu ya tsaneta sannan mu rabata da gidan Nan Kawai shine kwanciyar hankali Amma Matukar Muka kyalesu to zasu ci mu da yaki,satin Manal Uku kacal yau da dare Hajiya da Farida Suka saci jiki sai gidan Malam,Hajiya tace Malam na dawo akan Yaron Nan Yazed kaga duk yanda Muka so mu rabashi da Mahaifinsa abin yaci tura,Talauci ma da muka ce ka Dora Masa ba laifi wannan yayi Amma duk da Haka Malam idan ya fita Yana samowa ai a toshe Masa hanyar samun ko ficika kawai,Malam yace shi fa yake daukan nauyinku idan an hanashi Nema wa zai kula da ku,ai gwara ayi Masa Wanda zai koma sai abinda kika ce,ko Uwarsa ya daina tunawa Kawai sai yanda kika Yi da shi Kinga in ya samo kudin ke zai damkawa,Hajiya Tace Allah ya gani bana son kudinsa Ni da yarinya zata auri Dan sarki me kudi Nan kusa me zanyi da kudin Yazed Wanda Bai wuce na Shan garrin kwakwi ba,Ni bana bukatar biyayyarsa ko kudinsa na kusa Zama me kudi nima,sannan idan nayi kudin shi zai min biyayya Dole, Kawai bukatata ka raba shi da Yar Uwarsa Manal,Yana Sonta Kuma Uwarsu Daya ubansu daya,ko uwarta karka Bari ta tuna shima Haka a Raba su Kawai shi ya zauna tare damu Kamar yanda Muke a baya ita kuma a jefata duniya kawai ta tafi ta bar Mana gida,Kuma mahaifinsu Malam shima Kar ya tuna da wata Manal Kawai a rufe shafinta,Malam yayi dariyar Mugunta yace ajiye dubu goma ki tafi cikin kwana Uku ki dawo ki bani labari,Hajiya duk masifa Bata rasa kudin gidan Malam Haka ta zube Masa dubu goma cash Suka tafi gida.

Tun ranar bayan Kwana hudu tsakani Shi Yazed Haka Kawai yaji Sam ya manta ma Yana da kanwa wata Manal,Malam cikin kwana Uku Sam Bai San wata Manal ba shima,Ita Kuma Manal Sam asiri Bai kamata ba,Allah baiyi tsafin zai ci Manal ba,ita tana hayaccinta,,ba Wani Addini take Yi ba amma ita tasan kowa Kuma tana ganewa ba abinda ya faru da ita,Kawai taga Yazed dinta cikin kankanin lokaci ya canja Mata Sam ya nuna Bai santa ba,tun tana daukan abin Wasa har abin ya dameta,Su Farida Kuma ko kallonta basa Yi sai dai zagi da harara,Idan taje wajen Malam ko Toilet baya Bari ta tura shi,a baya su Farida ko kallon Malam basa Yi Amma ganin yanzu Manal suke son Kora sai komai na Malam ya dawo Hannunsu tare da Yazed sun hade Kai sun ware Manal babu me kulata sai duka da zagi kullum.
Manal Gata yarinya ga kuruciya da Rashin wayo musamman da ta taso a Kauye,tana zaune tayi tagumi Yazed ya shigo da kayan cefane,Da sauri ta Mike tana Yaya Sannu da zuwa,Wata Uwar Harara ya zuba mata tare da hankadeta gefe yace ke wacce irin dabba ce? Na sanki ne? Ko kin Sanni? Yaya Manal dinka ce fa wacce kace na dawo Nan birni na bar Kauye zaka kula da ni Amma Yaya Ni zaka manta Dani? Manal fa ta Annatu Yaya Annatunmu fa? Shuru Yazed yayi ya tsaya tunani yace Annatu munyi waya na tambayeta sunanki Tace Bata sanki ba Itama,ya sunanki ma? Manal ta rushe da kuka tare da zubewa a wajen,Hajiya suna daga daki suna ta dariya da murna ita da Farida,Yazed Waya ya zaro tare da Kiran Annatu ya saka a Handsfree tana dagawa suka gaisa tana Yazed ya Birnin yace lafiya Annata,Kinga Wai kin San wata Manal? Annatu Tace Manal? Manal? Kamar na taba Jin sunan Amma na manta Dan Allah karka dameni na gaji da tambayarka wace Manal ban Santa ba,Manal tana Jin Haka ta sake rushewa da kuka tana Annatu ta nice Manal dinki me tallan Furar fa? Manal da kika saka Ni a mota na taho Birni wajen Yaya Yazed,shi dai Yazed ganin yanda Manal take zunduma ihu sai ta bashi tausayi Haka Kawai duk da Bai Santa ba yanzu sai yaji tana bashi tausayi.

Hannunta ya rike yace kiyi Hakuri wallahi na kasa tunaki Kamar na sanki Amma naji ban sanki ba,Manal gani tayi Kawai Raina Mata hankali sukeyi sabo da wauta bakin ciki yasa ta shiga dakinta ta Hado kayanta kaf a Ghana Must go zata tafi tana kuka kanta babu ko dankwali bare Mayafi,Da sauri ta Shiga dakin Malam ta karewa mahaifinta kallo Yana Wheelchair Yana kallonta ,Baki ya tabe yace bana son a tsaya min a Kai Wai bakuwa ce ke ko Kuwa daga Ina kike? Manal Hawaye ya shiga sintiri a kumatunta taso ace ta iya Rubutu da karatu da kafin ta bar gidan sai tayi Rubutu a takarda ta Ajiye musu Amma Kash Bata San komai ba,Bata Yi nisa da karatun ba wannan ibtilain ya fada mata,sai Kawai ta fito da Jakarta ta fita,Hannunta Yazed ya riko ya Kura Mata Ido itama shi take kallo Dan uwanta abin kaunarta Uwa Daya uba Daya,Hawaye ne suke tsiyayowa a idanuwan Yazed Wanda shi Kansa Bai San na Mene ba,Manal tana ta jira ya furta ya tuna itace kanwarsa Amma Ina sai ya kasa cewa komai sai Hawaye,zobensa na azurfa dake yatsansa na tsakiya ya zaro babu dalili ya cirewa Manal sarkarta karama ya zare Dan kwadon sarkar tare da jefar da Kan sarkar,Zoben nasa na azurfa ya zura a cikin silin zaren sarkar ya sakawa Manal a wuyanta da kansa,zoben nasa ya koma Kamar sarka,Jakar Hannunta ya fisge ya Bude ya dakko wani katon Hijab har kasa ya Mika Mata,binsa takeyi da kallo Kawai da mamaki,Kuma a Haka zai ce Bai Gane wacece ba,har yasan ya Bata zobensa Kuma yasan ta suturta jikinta,a fili tace karya ne kasan Ni wace kana sani zaka Raina min hankali wallahi sai Allah ya saka min kana Dan Uwana na jini ashe baka kaunata Yaya,Shuru ya Mata Yana ta kallonta Yana so ya tuna wace Amma ya kasa,Fisge Jakarta tayi tayi tafiyarta cikin sauri harda gudu,tana kuka Kuma Haka ta bacewa ganinsa.

Su Hajiya suka saki shewa daga daki,Manal na tafiya Yazed ya samu nutsuwa a ransa Haka ma Malam rayuwarsu ta dawo Kamar da a baya kafin zuwan Manal.
Kuka takeyi tana fyalla gudu Bata saurarar kowa tafiya Kawai takeyi Bata San Inda zata je ba,Tana kuka Tace wallahi Nima Annatu babu Ni ba ke tunda kika ce Baki Sanni ba,Har Yamma tayi gab da Magriba Bata daina gudu da tafiya ba har tazo wata Arniyar Unguwa Wanda daga ita sai Allah ya Isa Kuma,Unguwa ce ta masu Hannu da shuni,da gani kasan Bata jigari jigari bace,bacin ran da take ciki shi ya hanata kallon ko Ina,Wasu Mahaukatan Motoci ne na alfarma a kalla zasu Kai takwas Suka fito daga wani mahaukacin gida kirar gidan yayi dan yanayi da sarauta,gaba Daya Motocin number dinsu an Rubuta FUZAIL Amma sabo da Manal Bata iya karatu da Rubutu ba Bata ma San Mene ba,Sam Bata su take Yi ba.
Fuzail dake hakimce a Bayan mota Yana karanta jarida ya dago da Kansa kenan yayi Ido biyu da Manal wata kara ya saki tare da furta Horror Oh my God,Idonsa ya rufe Kam Yana ihu Horror ayi sauri a wuce wajen,ai Kuwa motoci suka fisga da matsiyacin gudu tare da barin layin Kamar zasu tashi sama ta glass a tsorace yake kallon Horror Manal ta Mirror tana masifa ita kadai tana kuka Kuma har nushin Iska takeyi sabo da bacin rai gashi Bata San Ina zata je ba,gani Unguwar ba kowa ga dare yayi sai karnuka ke sintiri a ciki sai ta ja jikinta ta koma Unguwar talakawa inda mutane ke hada hada.














Sharhi Fans.







AsmaBaffa
[1/1, 10:23 PM] Sis Asma: 🧭🧭MAFARKIN FARIDA🧭🧭













MAFARKIN FARIDA IS DEDICATED TO


DUNIYATA AAMNA FNS GP.










7-10












Official













By
AsmaBaffa











Page naku ne

UMMIN SADDEEQ
MMN SADDEQ
MAMAN ILHAM
NANA KHADIJA MAHAMMAD
KHADIJA ABUBAKAR HAMZA
UMMU LATEEPHA
M DEWU
OUM ABULKHAIR














Please Login or Register in order to submit comment