Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta ce "Why Doctor" ya ce "U look more beautiful in hijab" rife fuskarta tayi da gyalen rigarta ta ce "Kaima ai manyan kaya yafi maka kyau" ya ce "To ai jiya nasa" ta ce "Yeah, nima kuma nasa Hijab" ya ce "Keda baki tsaya mun gaisa ba, kishi ya rufe maki ido" harara ta dan masa ta ce "I don't want" yana dariya ya ce "Ur wish is my command Hajiyata, is Abba at home?" Ta juyo tana kallanshi ta ce "Me zaka mishi?" Ya ce "Zance asa ranar auranmu ne" dan zaro ido tayi sai kuma ta ce "This is impossible" ya zura hannunsa a pocket dinshi yana kallanta ya ce "Fatima Abbanki mutumin kirkine, after Abbana he's the second person i can trust, he's a nice person i ever seen, he welcomed me happily, ya saurari bayanai na from d beginning till end and kinsan abinda yafi birgeni dashi?" Girgiza kanta tayi tana murmushi, Yusuf ya ce "He promised that..." Shiru yayi ganin mota tayi parking a gefensu, ya dan kalli Rafi'ah da itama motar take kalla, ganin Mummy ta fito a ciki yasa Yusuf ya karasa kusanta yana murmushi, har kasa ya durkusa ya ce "Ina yini Mummy" cike da fara'a ta ce "Lafiya kalau Yusuf, how is work?" Ya ce "Alhamdulilah" ta ce "Masha Allah" daga haka ta wuce cikin gida, tashi Yusuf yayi yana kallan Rafi'ah ya ce "Dear, i think i have to go, ko zaki zo muje shopping?" Ta dan girgiza kai ta ce "So kake Ummi ta kakkaryani?" dariya ya danyi ya ce "We are not going far" ta noke kafada ta ce "I'm not going anywhere" har lokacin Jawad na cikin motarsa yana kallansu ta cikin tinted glasses dinsa, after some seconds ya bude kofar motar ya fito, da fara'a Yusuf ya mika masa hannu, shima hannu ya mika masa suka gaisa, sai dai bai kalleshi ba, ya zame hannunsa ya nufi gate, Rafi'ah ta ce "I'm not saying i won't follow u anymore, watarana ai zamuje shopping din but not now" juyowa Jawad yayi ya kalleta kafin ya tura gate din ya shige. Yusuf ya ce "When is that time?" Ta ce "Idan na gama exams dina, and we are going with khairiyya" ya ce "Sure, zan kawota ranar Saturday ta gaisheki" cike da farinciki ta ce "Yess thank u Doctor" ya ce "Mention not, bana tafi dan naga kinfi son Khairiyya akai na" murmushi tayi me kyau kafin ta ce "And it's impossible, after Abbana da Ummina, Mummyna then it's you" daga haka ta boye fuskarta ta nufi gate ya bita da kallo yana murmushi, sai data shige sannan ya shiga motarsa ya bar layin.
Da sallama ta shiga parlor'n tana kallan Mummy ta ce "Sannu da zuwa" Mummy ta ce "Yauwa Daughter" kallan Jawad tayi dake magana da Ummi ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya" Ummi ta kalli Rafi'ah dake kokarin daukan laptop ta ce "Ki kawowa Jawad abinci Rafi'ah" toh kawai tace ta nufi kitchen, Mummy ta mike tana kallan Ummi ta ce "Kuma baima ci abinci ba tinda safe" shi dai sunkuyar da kansa kawai yayi, Ummi ta ce "A dinga kula fa Jawad, are u not afraid of Ulcer" ya danyi murmushi kawai baice komai ba, Ummi ta ce "A dai kiyaye gaskiya" daga haka tabi bayan Mummy suka haura upstairs. Warmers din abincin ta dauko a kitchen ta dora akan dinning, ta koma kitchen ta bude fridge ta dauko drink da table water, tana fitowa ta sameshi zaune akan dinning din, ta ajiye abubuwan hannunta zata juya ya kamo hannunta, with shock ta juyo tana kallansa, idansa na kan warmers din abincin ya ce "Saurayi zaki bi ya kaiki shopping mall ko?" zame hannunta tayi cikin nasa ta ce "And so" Jawad ya dago kansa yana kallanta ya ce "Wannan mutumin da kike gani is just here to spoil ur life and use you, baso na tsakani da Allah yake miki ba, and ki bar ganin yana kaiki shopping malls stop thinking he will stop there, one day he will request for something else" zama tayi akan kujerar dake gefenshi ta ce "Ni bai ta6a kaini wani waje ba, and this is the first time he's asking me to go for shopping, i trust him and he's more than kind " bayan tayi shiru ya ce "So be careful with guys most of them are of that intention of spoiling young girls, ba kuma a cewa an yarda da mutum, the person very close to u can deceive you, so u take very good care of yourself" sauke kanta tayi kasa a hankali ta ce "Thank u" har zaiyi magana phone dinsa ya fara ringing ya ciro wayar a pocket dinsa yayi picking call din hade da sallama, Mami ta ce "Ai sai ka kira kaji ko mun isa lafiya ko? Amma shiru~shiru ba call, or are u happy for my absence Jawad?" A hankali ya ce "No, aiki ne ya min yawa ko gida ban koma ba, but you're on my mind to call" Mami tayi shiru kafin ta ce "To ka tafin gidan Kawun?" Ya ce "Till tomorrow ai ban koma gida ba har yanzu" ta ce "To shikkenan gobe da sassafe ka tattara ya naka ya naka ka bar gidan" silently ya ce "To Mami, a huta gajiya" ta ce "Yauwa, Allah ya kare min kai" daga haka tayi hanging wayar. Kallansa kawai Rafi'ah take jin karyar daya zuka, ya dago kansa yana kallanta ya ce "So is an advice" tashi tayi ta dauka laptop dinta dake kan sofa ta ce "Thanks for d advice" daga haka ta wuce sama ya bita da kallo.


*Barka da sallah fans, fatan anyi sallah lpy, anci nama lpy? Ina jiran nawa raban nima 😄 lol, Barka da sallah once again.*

08103810398
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_29_

Murmushi Aliyu yayi yana shafa beard dinsa ya ce "Then what decision did u take?" Yusuf ya danyi shiru kafin ya ce "That's what i'm thinking Aliyu, ita Umma ta dage saina fara auren Jiddah, to bansan kuma ya zan fara fadawa Fatima hakan ba" ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yana kallan Yusuf ya ce "Wait Yusuf.... Wane shaidan dinne yake zugaka ka auri mata biyu?" Yusuf ya shafa gashin kansa ya ce "Haka Allah ya tsaramin Aliyu, but before ba haka naso ba" Aliyu ya ajiye glass cup din hannunsa ya ce "To Allah yasa haka ne alkhairi" Yusuf ya ce "Ameen, yanzu ya kake gani za'ayi" ya ce "Kawai tinda Umma ta dage ka fara auren Jiddah, sai ka lalla6a Fatima ka gaya mata ta hanyar da zata fahimta" Yusuf ya danyi murmushi ya ce "Thanks for saying something Aliyu, nagode sosai" Aliyu ya ce "You mention not Yusuf, i think that is the best solution". Gently Jawad yake tahowa inda suke zaune, duk da hasken wutan dake compound din Yusuf ya dinga kallansa to confirm ko shidinne, ganin shine yasa Yusuf ya mike yana mikawa Aliyu hannu ya ce "I'm going Ali" Aliyu ya tashi yana bashi hannu ya ce "Till tomorrow, gobe da wuri zaka shiga clinic ko?" Yusuf ya ce "Insha Allah" daga haka ya dauka key din motarsa dake kan table ya ce "Night" yana juyawa suka hada ido da Jawad, Yusuf yabi gefe ya wuce parking lot.
Harya fita da motarsa Jawad bai ko kalli inda yake ba, bayan sun gaisa Aliyu ya ce "Yaushe ka dawo 9ja Ahmad?" Jawad dake danna wayarsa ya dago yana kallansa ya ce "Waye wannan wanda ya tafi yanzu?" Aliyu dake zuba masa drink cikin glass cup ya ce "Wai Yusuf? Friend dina ne" Jawad ya sauke kansa kasa ya ce "I need to know more about him" kallansa Aliyu keyi kafin ya ce "Ka san shi ne?" Jawad ya ajiye phone dinsa ya ce "Can i have my answer then?" Aliyu ya jingina da kujera ya ce "To nidai bansan komai a kansa ba, friend dina ne, a asibiti daya muke aiki sannan school daya mukai masters a Italy amma ya rigani gamawa, that's all i know" Jawad ya limshe idanuwansa ya ce "Is he married?" Aliyu ya ce "No, but ya kusa" da sauri ya bude idanuwansa yana kallan Aliyu kafin ya ce "Wa zai aura?" Aliyu ya dan zaro ido ya ce "Kaiii Barisster, what's all this question for?" Jawad ya kara limshe idanuwansa ya ce "Answer me pls" Aliyu ya ce "Cousin dinsa zai aura" Jawad ya ce "Alright yayi kyau" Aliyu ya matso da kujerarsa kusa dana Jawad ya ce "Kasan shi ne?" Jawad ya girgiza kai ya ce "No" Aliyu ya ce "Meyasa kayi parking a waje" Jawad ya ce "Is because i'm not staying long, na tsaya salla nan masallacin kusa daku, then i decided to branch and see u" Aliyu ya ce "Good, ka kyauta but not more" Jawad ya daga kafada alamar i don't care ya ce "Zan wuce ka gaishe da Mama" daga haka ya mike tsaye, Aliyu ya ce "Ko ruwa baka sha ba" ya girgiza kai ya ce "I'm full, kuma sauri nake, zan mayarda Mummy gida" tashi Aliyu yayi suka jera suna tafiya harya rakashi mota sannan sukai sallama ya shigo gida Jawad kuma ya tada motarsa ya bar layin. Slowly yake tafiya yana tina maganar Aliyu "cousin dinsa zai aura" Jawad ya danyi murmushi ya kara speed din motar, few minutes ya kawoshi gidansu Rafi'ah, yayi horn gate man ya bude sannan ya shiga yayi parking ya nufi entrance din gidan, da sallama ya shiga parlorn, Rafi'ah dake kwance ba dan kwali tayi saurin mikewa ta dauka scarf dinta ta saka, Ummi da fitowanta a kitchen kenan ta ce "Ka dawo kenan Jawad, bari a kawo maka abinci" shi dai baice komai ba sai murmushi da yake, Mummy ta ce "Naga shiru baka dawo ba" ba tare daya dago ba ya ce "Nayi branching wajen friend dina ne" Mummy ta ce "Ohk, to kaci abinci mu tafi nasan Abi yana dab da komawa gida" ita dai Rafi'ah na zaune tana kallon wani indian film a laptop, ta dan daga kanta ta kalli Jawad suka hada ido, a tare duk suka sauke kansu kasa, Ummi ta ajiye masa abincin akan center table sannan ta jawo shi gabansa ta ce "Bismillah" daga haka ta dauko masa table water sai cup ta ajiye a gefen plate din, gefen Rafi'ah ta zauna tana tattara papers din da tai making, Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Laah Ummi, Abba bai bani 5k dinba kuma ya shiga apartment din Anty" Ummi ta ta6e baki ta ce "Then u leave it till tomorrow" turo baki tayi ta ce "To ai ba lallai ya tashi da wuri ba" Ummi dai bata kulata ba taci gaba da abinda take. Jujjuya abincin kawai Jawad yake, shi dama cin abincin dare bai wani dameshi ba, bayan ya dan ci ya mike yana kallan Ummi ya ce "Thank u Ummi, sai da safe" Ummi ta kalli abincin kafin ta ce "What have u eaten Ahmad? Banga kaci komai ba" ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce "Naci ai Ummi" ta ce "To Allah ya kyauta" tashi Mummy tayi tana kallan Rafi'ah ta ce "Ba rakiya ne Fati" Tashi tayi tabi bayan Mummy suka fita zuwa mota, Mummy dake kallan ta ta ce "Yaushe zaku gama exams din?" A hankali ta ce "Friday" ta ce "To sai kizo ki tayani zama ko" ta ce "To" daga haka ta ce "Allah ya kiyaye" Mummy ta ce "Ameen" juyawa Rafi'ah tayi ta koma ciki sannan Jawad yaja motar suka fita gate din.
Washegari bayan su Rafi'ah sun gama shirin makaranta sunyi breakfast tace wa Ummi zataje wajen Abba, da kai ta amsa mata sannan ta fita a parlorn su ta nufi apartment din Anty Amina, tana murda handle din tayi sallama, Abba dake zaune a parlor yana kallan news ya dago yana kallanta ya ce "Come in Mamana" Canvas din kafarta ta cire sannan ta nufi wajen Abba ta zauna gefenshi, sosai uniform din yayi mata kyau tana ta kamshi, a hankali ta ce "Good morning Abba" ya ce "Morning sweetheart how was ur night?" Ta ce "It was fine Abba, dama jiya ka manta baka bani 5k din ba" Abba dake kallanta ya ce "Ohh na manta, muje na saukeku kawai, tinda i'm doing nothing" murmushi kawai take ta mike tsaye, Abba ya ce "Jeki gaishe da Antynki a kitchen kafin na dawo" daga haka ya nufi upstairs, gently ta karasa kitchen din ta bude, a tare duk suka juyo suna kallanta, ta danyi kasa da murya ta ce "Good morning" juya kai Anty Amina tayi ta kalli Ikleemah dake hararan Rafi'ah ta ce "Jeki rufemin kofa" Rafi'ah najin haka ta juya ta bar wajen, Ikleemah tayi banging kofar tana jaan tsaki ta ce "Wai Anty dan jaraba da safen ma sai anzo miki, naga Abban a gidanki yake" Anty Amina ta ce "Yanzu haka uwarce ta turota, nidai nafi karfin kowa ba maganin da zasu barbada yayi tasiri akaina" Ikleemah ta ta6e baki ta ce "Sai kace aljana wallahi, anya bata bleaching Aunty? Gashi sai kyau take" Anty Amina ta ce "Caan nasu kuma". Abba na saukowa ya wuce Rafi'ah na biye dashi har suka iso parking lot, ta shiga ta dauko school bag dinta sannan suka fito ita Abdul suka shiga mota Abba yaja suka fita, dama tuni mai gadi ya wangale gate, sai da suka hau saman titi Abba ya ce "Mamana u take good care of yourself, be a daughter of a respected man, calm yourself dear, insha Allah u won't regreat in life Fatima, and never get tired to praying, idan zaku kwanta ku ringa alwala, tashi sallan dare even if it isn't everyday, and u two should never get tired of reading qur'an" a tare duk suka amsa da "Insha Allah Abba" Abba ya ce "Allah ya muku albarka" suka sake amsawa da "Ameen".
Anty Khadija ne zaune a dakin Umma tana bubbude kayan lefen da Umma tace ta gama hadawa, bayan ta gama budewa ta dago tana kallan Umma ta ce "Yanzu sai saka rana kenan" Umma ta ce "Insha Allah, na kira kanwar uwarsa ma na fada mata tazo taga kaya kar tace an wareta" Anty Khadija ta ta6e baki ta ce "Umma amma dai kin kara masa lokacin da yace zai auri yarinyar caan? Gara abar Jiddah taci amarcinta hankali kwance" Umma tayi dariya ta ce "Ke dai mun gama magana, ya auri Jiddah tukunna, ita kuma waccen ko bata aureshi ba sai tayi nadamar saninsa, dan Yusuf sai ya zame mata bala'i da tashin hankali a cikin rayuwarta" Anty Khadija dake murmushi ta ce "Yesss, nasan tinda kika fada saiya tabbata Umma, wayaga idon yarinyar taab" daga haka ta kwashe da dariya harda tafawa.
Ranar Friday Rafi'ah ta gama exams dinta a ranar ne kuma Abba ya kira Yusuf ya sanar masa ya bashi auren Rafi'ah, kar kuga murmushi da farinciki wajen Yusuf, sai dai idan ya tuna Rafi'ah bata saan da maganar auransa da Jiddah ba sai zuciyarsa ta tsinke, amma ya dauki alkhawari dole zai gaya mata ko zai samu nutsuwa ta wannan bangaren, ranar Saturday da yamma Rafi'ah na zaune a dakinta wayarta ya fara ringing, murmushi tayi ganin Yusuf ke kira sannan tayi picking call din hade da sallama, ya amsa mata sannan ya ce "I'm outside dear, ga kuma Khairiyya na kawo maki" cike da murna ta ce "Ohk im coming out now" daga haka tayi hanging wayar ta mike ta dauka dogon himar dinta cikin press ta saka, phone dinta kawai ta dauka ta sauko downstairs, ta danyi shiru tana nazarin me zata cewa Ummi, kamar daga sama taji muryarta tana fadin "Where are u going?" Tayi saurin sauke kanta kasa ta ce "Amm...dama..dama Doctor ne yazo yana waje" Ummi ta juya ta koma kitchen ta ce "Don't stay long" murmushi Rafi'ah tayi ta zura flat shoes dinta sannan ta fita a parlorn, cikin nutsuwa take tafiya harta fito gate, Khairiyya ta fito daga front seat tayi hugging dinta ta ce "I missed u Anty" Rafi'ah taja hancinta tana gyara mata scarf dinta ta ce "I missed u khairiyya, how are u?" Ta ce "I'm fine, Yaya yace i'm spending the day with u" sai lokacin ta kalli Yusuf dake kallanta ko kiftawa babu, ta sauke kanta kasa ta ce "Ina yini Dr" ya ce "Fine sweetheart, ya hutu?" Ta ce "Alhamdulilah" ya ce "SS3 zamu shiga ko?" Tayi saurin rife fuskarta tana murmushi ta ce "Ni ka daina tsokala na" ya ce "No i'm counting my days" zaro ido tayi ta ce "So soon?" Ya ce "Ehh mana, aiba yawa lokacin" ita dai murmushi kawai tayi, ya sake kallan fuskarta ya ce "Bayan awa biyu zan dawo na dauketa, and i want to talk to u idan na dawo" a hankali ta daga masa hannu ta ce "Ohk till u come back" ya ce "Thank u" daga haka yayi reverse ya bar unguwar, Khairiyya ta kalli Rafi'ah ta ce "Anty kawai sai ki boyeni mu kwana" Rafi'ah ta zaro ido ta ce "So kike yau Amminki tazo ta zaneni" Khairiyya tayi murmushi looking happily, Rafi'ah ta kama hannunta ta murda handle din suka shiga, kallansu kawai Ummi take har suka karasa shigowa, Khairiyya ta zauna a kan carpet tana kallan Ummi ta ce "Ina yini" Ummi ta ce "How are u?" Ta ce "I'm fine" kallan Rafi'ah tayi dake daukan abu akan dinning ta ce "Who is she?" Kanta na kasa ta ce "Cousin din Dr ce" Ummi ta ce "Ohk, tashi ki zauna kan kujera mana, what's your name?" A hankali ta ce "Fatima Zarah, amma Ammina da Daddynah used to call me Khairiyya" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Good". Bayan Rafi'ah ta gama hada mata fruits salad ta mika mata ta ce "U take this Baby, and what will i cook for u" Khairiyya ta kar6a bowl din tana murmushi ta ce "Na koshi da abinci Anty, but i like this" daga haka ta dauka tea spoon dake gefen bowl din ta fara sha, Rafi'ah na zaune harta gama shanyewa, ta mike ta ajiye bowl din akan dinning, Rafi'ah dake kallanta ta ce "Ko in kara maki?" Ta girgiza kai, kama hannunta Rafi'ah tayi suka haura upstairs, bayan sun shiga dakinta Khairiyya ta limshe ido ta ce "Anty is this ur room, very neat and it's smelling nice" Rafi'ah dai murmushi kawai tayi, Khairiyya ta daga kanta tana kallan hotunan Rafi'ah dake jikin wall tin tana 'yar karama har izuwa yanzu, Rafi'ah ta ce "Khairiyya ko in kawo miki fried rice?" Zaro ido yarinyar tayi ta ce "Anty nifa bana cin abinci sosai da dai Yaya Sameer kika ce, shine Ammi tace ko a office ci kawai yake, shi kuma Yaya Faruk wai bayacin spaghetti" murmushi kawai Rafi'ah take tana kallanta, ta sake cewa "Allah Anty Yaya Sameer yana da ci, zai iya cinye abincin cikin gidan nan" Rafi'ah na dariya ta jawo laptop dinta ta ce "Which cartoon do u want to watch?" Cike da farinciki Khairiyya ta ce "Yess Anty, i love watching Angelina ballerina" Rafi'ah ta shiga YouTube tayi searching sannan ta saka mata, bayan ta fara kalla ta mike ta ce "I'm coming dear, just 5 minutes" daga haka ta fita a dakin.
A awa biyun da Khairiyya tayi wajen Rafi'ah taga kulawa sosai, duk abinda tace tanaso Rafi'ah zata bata, har 500 ta bawa Mustapha ya siyo mata chocolate, bayan Yusuf ya kira yana waje Rafi'ah ta kashe kallan tana kallan Khairiyya ta ce "Yaya is outside Khairi" Khairiyya ta rungume Rafi'ah ta baya ta ce "I will miss u Anty" kama hannunta tayi suka fita ta kaita har dakin Ummi ta ce "Zata tafi Ummi" Ummi ta bata packet din sweet sai ribbom da bead, ta dan rusuna tana dariya ta ce "Nagode" Ummi ta shafa kanta ta ce "A gaishe da Mama" da toh ta amsa tana ta dagawa Ummi hannu, bayan sun fito a dakin Rafi'ah ta ce "Wait here" daki ta koma ta dauko mata ledan chocolate dinta sai dan karamin tirare cikin wani kwali, ta hada mata chocolate da sweet din waje daya sannan tasa mata tiraren cikin ledan bead din ta ce "The perfume is also for u" Khairiyya ta wara ido ta ciro shi tana shinshinawa ta ce "Anty irin kamshin dakinki da jikinki, i love it, thank u Anty" shafa kanta Rafi'ah tayi sannan ta kama hannunta suka sauko downstairs, bayan sun fita a parlorn suka nufi bakin gate, yana tsaye jikin motarsa as usual, Khairiyya ta shiga nuna masa abubuwan hannunta, ya kalli Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Thanks for everything love" ta danyi murmushi ta ce "Mind not, i will miss her much" Yusuf ya dan shafa kansa ya ce "To muje ki rakani mu kaita gida" ta ce "No, kaje dai ka dawo" ya ce "Pls, aiba nisa ba kince kinsan area ba" a hankali ta ce "Toh" ya bude mata front seat yana murmushi ta shiga, daga haka ya zagayo seat dinsa yayi wa motar key suka wuce, 5 minutes ya kaisu gidan Ammi, Yusuf ya juya yana kallan Khairiyya ya ce "Kije ciki Khairiyya zan maida Anty gida" kamo hannun Rafi'ah tayi ta ce "Thank u Aunt, baza kuje nima kiga Ammina ba?" Ta ce "Noo, some other time Khairi, zanzo kiyi ta bani labari" daha haka ta sauka a motan tana daga musu hannu ta shiga gate, juyowa Yusuf yayi yana kallan Rafi'ah dake murmushi. Jifa jifa suke hira har suka kusa isowa gida, ya samu dai dai kasan wata bishiya yayi parking ya juyo yana kallanta, nan da nan kirjinta ya hau bugawa, ya sakar mata murmushi ya ce "What?" Ta ce "Naga kayi parking a nan, and the street is very quite" Kamo hannunta Yusuf yayi yana kallan idanta ya ce "I want to say something Fatima, but pls don't judge me wrong" dago kanta tayi tana kallanshi, ya ce "Sure nasan u are my happiness, u cause alot of changes in my life Fatima, i don't know how much i luv u, and insha Allah i will continue caring till my last breath" sauke kanta tayi kasa tayi shiru, ya kara kamo dayan hannunta silently ya ce "Kafin na hadu dake akwai wacce nake soyayya da ita, she's in my house, her name is Jiddah, and i promise to marry her too" kanta na jikin kujera tana jinsa amma ko dago kanta ta kalleshi bata yi ba, ya matsa kusa da ita ya ce "I hope zamu zauna tare dukkanmu?" Daga masa kai tayi, ya ce "Noo, u speak" a hankali ta ce "I'm hopping for d best, Allah yasa shine alkhairi" baisan lokacin daya rungumeta ba, tayi saurin janye jikinta tana turo baki, bai ta6a tinanin iya abinda zata ce ba kenan, ya kamo hannuta yayi kissing soft hand dinta ya ce "U are d best Rafi'ah, ke dabance a cikin mata, i luv u so much Fatima" murmushi ta danyi ta juya tana kallan waje ta cikin glasses din motar, ya tada motar yana kallanta ya ce "Bari mu wuce kar Ummi ta neme ki" daga haka yaja motar, har suka iso gida bata ce komai ba, sai da taga yayi parking ta ce "Nagode, Allah ya kiyaye
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment