Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sosai" a hankali ta ce "Kaima kayi kyau" ya ce "Sure?" ta daga masa kai, ya ce "To ai baki kalleni ba kuma" sai lokacin ta bude fuskarta ta kalleshi sannan ta ce "Da gaske kayi kyau" ya ce "Thank u so much, how is Mummy" ta ce "She's fine" ya ce "Khairiyya na gaisheki, she always asked for you" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Ba kaki kawota ba" ya ce "Sai kinje kin gaishe da Amminta, kinga by then small mum dina ta sanki sai itama in kawota taga Antynta" Rafi'ah ta danyi mirmushi ta ce "To sai wataranan" ya ce "Allah ya kaimu, Amma wannan karan idan Abba yazo zan sameshi na fada mishi" da sauri ta ce "Me?" Ya ce "Ina neman izini a bani ke" tayi saurin rife fuskarta bata ce komai ba, ya ce "Ko wajen Mummy zan kama kafa?" Ta girgiza kai kawai tana murmushi.
Sun kai minti 30 tsaye a wajen suna hira, ita dai Rafi'ah sai uhmm ko murmushi duk shi kadai yake surutun, ya lankwashe kansa irin yadda tayi ya ce "To sai yaushe zamu sake haduwa Baby" ta kyalkyale da dariya ta ce "Aini ba haka nake magana ba" ya ce "Ko, to bari na sake gwadawa" ya dan shagwa6e fuska just like she used to ya ce "Ni dai banaso mu kara kwana 2 ban ganki ba" dariya sosai ta kyalkyale dashi harda sunkuyawa, dai~dai lokacin Jawad ya bude kofar gida ya fito, ya kura musu ido yana kallansu, Yusuf dake murmushi ya ce "Serious haka kike, and i like it" ta tsaya da dariyar da take cewa "That's what u said dai" ya ce "Allah kuwa, sai munyi waya ko, i have to go, zan je gidan abokina" ta ce "Alright safe" Yusuf ya ce "Waye wancen?" Ya karashe maganar yana kallan inda Jawad ke zaune, suna hada ido ya hade rai ya kauda kansa gefe, Rafi'ah ta ce "Dan gidan ne" ya ce "Ohh Mummy tana da rival ne?" Ta ce "Yess, but ya fara auren Mummy kafin mamansu, shi ne babba" Yusuf ya dan daga kafada ya ce "Ohk, yanzu sai yaushe?" Ta ce "Sanda kace" ya ce "To sai munyi waya" ita da kanta ta bude masa kofar motar, bayan ya shiga ta rife sannan ta durkusa tana kallansa ta glass ta ce "Allah ya kiyaye, ka tafi very gentle" Yusuf yayi murmushi ya ce "Thank u LIFE PARTNER" ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta matsa jikin motar tana daga masa hannu ta nufi cikin gidan. Yusuf yayi reverse yana ta dariya, yana juyawa ya dagawa Jawad hannu, dauke kansa ya sake yi ya maida gefe, bayan Yusuf ya wuce ya bi motarsa da wani irin kallon da baza'a kirashi da harara ba. Daga haka ya mike ya shiga cikin gidan, a parlorn Abi ya zauna ya kurawa TV ido, Mami ta fito tana kallansa ta ce "Kai ba abinda zaka dauka ne na tafiyar?" Ya dago kansa yana kallanta ya ce "I'm not going" Mami ta masa kallan kama isa kafin ta ce "Wannan kuma karyane wallahi, kafata kafarka a gidan nan, sai dai idan kaje Abujan kayi ta zama a daki" Tashi Jawad yayi ya fice a parlor, Mami ta bishi da harara ta ce "Wawa kawai, wallahi ba dan a gida na haifoka ba cewa zanyi canzamin kai akayi" daga haka ta koma dakinta tana dialing wayar Abi.


*I'm writing this to the notice of my fans/followers, zan bar typing daga yau sai na gama exams insha Allah.*

_08103810398_

[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_By FATIMA ✍🏻_

_23~24_

______________Jawad ne zaune a parlorn Abi Mami na zaune a kan kujerar dake opposite dinsa, tinda ya shigo parlorn kansa na kasa bai yarda sun hada ido da Mami ba ya zauna akan carpet, bayan Abi ya gama answering call din da yake ya dago kansa yana kallan Jawad ya ce "Why will u not follow them Ahmad? Or do u have something to do?" Ba tare daya dago kansa ba ya ce "Sure, i have alot to do Abi" Mami dake dalla masa harara ta ce "Munafikin Allah, babu wani abinda zakai a garin nan, saboda haka keep this at back your mind, wallahi saika tafi Abuja, i swear to God and i won't regret telling you such" ta karashe maganar tana jijjiga kafarta fuskarta babu walwala, ta dinga hararan Jawad da baisan tanayi bama, Abi yayi gyaran murya yana kallanta ya ce "Iook Hadiza, i see nothing to bother in this case, is Jawad still a kid? ko Ikram bazata zauna nan ba in taga batasan tafiya ballantana Jawad? Pls u keep this issue aside, tinda yace bazai je ba let him stay" Abi na rife bakinsa ya jawo newspaper dake gefensa yaci gaba da karatunsa, kasa daina kallan Jawad Mami tayi, shima kuma yaki yarda su hada ido, caan taja tsaki ta mike ta wuce part dinta tayi banging kofar da karfi, kallan direction din Abi yayi sannan ya girgiza kai yaci gaba da abinda yake, gently Jawad ya mike yana kallan Abi d hankalinsa ke kan newspaper, kallan part din Mummy yayi, caan ya wuce dakinsa ya rufo kofa. Zaro ido Rafi'ah tayi tana kallan Mummy ta ce "Dan Allah Mummy karki gayama Ummina, nifa ba saurayina bane" Mummy dake murmushi ta ce "I can't promise u bazan gaya mata ba, haka zamu zuba maki ido kiyi ta tsayuwa a titi da saurayi sai kace daga wancen garin muke, ai yafi kuyi hirar a gidan auranku, kince sunansa Yusuf ko?" Turo baki Rafi'ah tayi bata ce komai ba, ga kirjinta dake bugawa sosai, babban tsoronta idan Ummi taji wannan zance, ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Mummy dake shirya kayanta cikin wardrobe ta ce "Dan girman Allah Mummy don't let her know, Allah it won't be good for me, zata iya dukana" Mummy ta ta6e baki tana kallanta ta ce "Sai kuma kiyi, baki isa kula samarin bane ko me da zakice zata dakeki, ni shekarata goma sha uku sanda nayi aure, duk karatun danayi a gidan mijina nayi" hawayen daya gangaro a idanta ta goge ta kara turo baki ta ce "To ai ku lokacinku haka ake, ni kuma Abba yace saina gama degree zanyi aure" ba tare da Mummy ta kalleta ba ta ce "U better wipe those tears, dan babu abinda zai hanani bashi dama ya turo magabatansa, dama faduwa ne yazo daidai da zama, kina karasa karatunki kiyi aure, idan yaso daga nan kiga karshen boko, shi kuma ubanki idan bazai aurar dake ba, inada kudin da zan iya miki komai ni kadai na, atooh in baka dashi ne saika jira an maka" Tashi Rafi'ah tayi ta fito parlor ta kwanta kan kujera tana goge hawayen idanta, imagining kawai take idan iyayenta suka saan wannan labarin, what will she even tell Abba bayan kullum burinsa tayi karatu me zurfi, taja dan karamin tsaki tana regretting zuwan Yusuf gidan Mummy.
Umma ce zaune a parlor jidda tayi pillow da cinyarta, kana kallanta kasan taci uban kuka ba kadan ba, idanta duk sun canza kala sunyi jazir, Umma ta dan shafa kanta ta ce "Nace kiyi shiru ko Jiddah?" Cike da karfin hali ta ce "Nayi Umma" daga haka tasa hannayenta ta sharce hawayen daya sakko a idanta, Umma tayi patting bayanta cikin rarrashi ta ce "Ai Jiddah idan baki auri Yusuf ba sai dai idan ba raina, ki kwantar da hankalinki duk kukan nan da kike ki daina, kuma karki nuna masa komai, aure kuma kamar anyi an gama" tashi Jiddah tayi tana kallan Umma cikin muryar kuka ta ce "Allah Umma inasan Ya Yusuf, mutuwa zanyi idan ban aure shi ba" daga haka ta rungume Umma ta fashe da kuka, Ta6e baki Anty Khadija tayi ta tashi ta haura sama, ita haushin Jiddah ma takeji har ranta musamman idan ta tuna akan Yusuf take wannan kukan.
Har dare yayi Rafi'ah bata samu tayi convincing Mummy ba, hakan yasa bugun zuciyarta ya karu, ta jawo ledan drugs dinta tasha sannan ta dake kirjinta ta limshe ido, har kusan karfe 10 tana a haka, jin an bude kofar dakin yasa ta bude idanta, Mummy ta zauna gefenta ta ce "Are u sick?" Ta girgiza mata kai kawai, Mummy ta ce "Tona menene dafe kirji? ko ciwo yake?" A hankali ta kara girgiza mata kai, Mummy ta ce "Then u stand up and take ur dinner" tashi tayi ta zauna tana yamutse ta ce "Tea kawai zan sha" Mummy ta ce "To kije ki hada a kitchen" daga haka ta fita a dakin ta koma dakinta. Sai bayan few minutes Rafi'ah ta janye duvet din dake jikinta ta sakko akan gadon, dogon hijabi ta saka saboda kayan baccin jikinta, daga haka ta fito a dakin, ba kowa a parlorn Mummy hakan yasa ta kashe faan da sockets sannan ta fita main parlor, Sadeeq ne kawai zaune a parlor yana kallo, ta danyi kasa da murya ta ce "Ina yini" a takaice ya ce "Lafiya" daga haka ta wuce kitchen, tana shiga taji kamar ta juya ta fito ganin Ikram da Jawad a kitchen din, kowa kuma harkar gabansa yake, shiga tayi ciki a hankali ta durkusa dai dai inda taga cups ta dauka guda daya da tea spoon sannan ta karasa inda taga flask ta bude zata bebi ruwan zafi, Ikram na gama juye indomie a cikin plate ta dauka tana ta6e baki ta fita a kitchen din. Sugar da milo tasa a cikin tea din, ta dinga bin kitchen din da kallo ko zata ga milk, dai dai inda Jawad ke tsaye ta hango tin din, ta karasa a hankali tasa hannunta zata dauko tin din suka hada ido, sauke kanta tayi kasa ta ce "Zan dauka madara ne" bai sake kallanta ba yaci gaba da abinda yake, ta dauki tin din ta bar wajen, bayan ta zuba ta dauka cup dinta zata fita taji ya ce "Who was that guy?" Juyowa tayi tana kallansa, yana tsaye inda yake kuma bai juyo ya kalleta ba, ta juya a hankali zata fita ya ce "Baki ji bane?" Silently ta ce "A friend" daga haka ta fice a kitchen din, har lokacin Sadeeq na zaune a parlor, Rafi'ah ta ce "Sai da safe" ya ce "Allah ya kaimu" daga haka ta shige part din Mummy.
Washegari da safe Mummy ta shiga kitchen saboda girkinta ne ranar, Rafi'ah najin ta fita ta saka hijabi ta bita suka fara aikin tare da mai aiki, Mummy batai wani aiki ba tana dai zaune tana ce musu suyi wancen suyi wancen, bayan sun kusan gamawa Rafi'ah ta kalli Mummy ta ce "Nifa anjima zn wuce gida Mummy, i have school tomorrow" Mummy ta ce "Ki bari da yamma saina saukeki idan zan fita" girgiza kai tayi ta ce "No, inasan inje islamiyya ne da yamma, kinga jiya banje ba" Mummy dake kallanta ta ce "Ko kuma saurayinkin ne zaizo?" Turo baki Rafi'ah tayi ta ce "Nifa bance ba islamiyya nace miki zanje" Mummy ta ce "Sau nawa kina fashin islamiyyar for no reason, zaki wani fake zakije islamiyya" Ita dai bata ce komai ba banda hade rai da tayi, Hindatu me aiki nata dariya kasa kasa. Bude kofar kitchen din akayi Mami ta shigo, fuskarnan a daure ko walwala babu, sai data dauki abinda zata dauka tazo fita ta ce "Mun kwana lafiya?" Mummy ta ce "Alhamdulilah", abinda yake hadasu kenan a gidan, shima gaisuwan Abi ne yasa Mami tana gaishe da Mummy each and every day, wani lokaci ko Mummy tai mata magana sai taga dama take amsawa, hakan yasa itama tayi watsi da ita dan ita bata iya daukar rainin hankali. Bayan sun kammala komai aka jera akan dinning din Abi, Mummy tasa Rafi'ah ta dibar musu nasu a warmer, plate da cups Mummy ta dauko zata wuce part dinta, Jawad da fitowansa kenan yayi kasa da kansa ya ce "Ina Kwana" ta ce "lafiya Jawad, ya gajiya" ya ce "Alhamdulilah" daga haka ta wuce ciki, Mami sai hararansa take, bayan ta gama dibarwa Ikram abinci ta wuce part dinta ta rufo kofa, Jawad ya dawo kan dinning din ya zauna yayi sarving kansa ya hada tea, sai daya gama sannan ya mike ya nufi part din Maminsa, da sallama ya shiga parlor, Mami ta hade rai ganinsa taci gaba da bawa Ikram tea a baki, zama Jawad yayi yana kallansu ya ce "Take it yourself" ya karashe magana yana kallan Ikram, hannu tasa zata kar6i cup din a hannun Mami, Mami ta ce "Ina ruwanka to? Kai ka sani na bata?" Girgiza kai yayi yana kallanta ta ce "Then u mind ur words, babu ruwanka da abinda nayi niyya a cikin gidan nan" kansa ya kara saukewa kasa ya ce "Amma Mami yanzu Ilkram bazata sha tea da hannunta ba saikin bata, just because ta tashi da zazza6i, ita raguwar inane? shekara 17 fa" Hararansa kawai Mami take harya gama magana, ta ce "To saika hanani abinda nayi niyya tinda kaika haifeni, ko kishin uwarka bakayi ka bude baki ka gaishe da waccen matar, kana gani 'yar kanwata na ganina ina zirya ko sannu bata ce min ba, amma saboda kai kafi kowa ladabi ka gaishe da uwarta" shiru yayi baice komai ba, bayan few seconds ya ce "Kiyi hkr, amma dai kun fasa tafiya yau din?" Ta ce "Inafa tafiya Ikram ta tashi ba lafiya" a hankali ya ce "Allah ya sauwake" Mami ta ce "Yanzu ina zakaje?" silently ya ce "Court" ta ce "Saboda neman suna ko me?" Ya mike yana kallanta ya ce "May b i will just continue my work there, tinda sun bukaci hakan" ta6e baki tayi ta ce "A banza zaka musu aikin kenan?" Ya shafa kansa ya ce "No, ai dama sunce inna dawo zan iya ci gaba kona nema wani waje, end of d month zanci gaba da kar6an salary" beedsheet ta rufawa Ikram ta ce "Allah ya taimaka, Allah kuma yasa da gaske kake, danni yanzu lamuranka tsoro suke bani" murmushi ya danyi ya fita a parlorn ta bishi da harara.
Fitowa yayi a dakinsa cikin manyan kaya, sai kamshi yake ya dauka lab coat dinsa dake kan kujera ya daura akan kayansa, kaan dinning ya zauna yaga babu komai cikin warmers din, hakan yasa ya mike ya shiga daki ya dauko wasu files sannan ya nufi kofar fita hannunsa rike da key din mota, da sauri Jiddah tabi bayansa tana murmushi ta ce "Good morning Ya Yusuf" juyowa yayi yana kallanta ya ce "Morning Jiddah" idanta ne ya ciko tapp da hawaye, tayi kasa da murya ta ce "Dan Allah Yaya mena maka kace ka fasa aurena, ka fadamin koma menene Allah zan daina, i promise u Yaya" ta karashe magana tana goge hawayen idanta, duk jikinsa sai yayi sanyi, shima Allah na gani yana saan Jiddah but tinda Umma taki yarda tun farko ya janye jikinsa, hannunta ya kamo ya bata side hug ya ce "Keep quite" tayi shiru tana kwantar da kanta akan fadarshi taji ya ce "I luv u Jiddah, but i don't like some of ur attitude sometimes" dago kanta tayi tana kallansa ta ce "Na daina Yaya trust me" ya danyi murmushi ya ce "Then zaki aureni?" Ta daga masa kai ya ce "Kinyi alkawari bazaki kara yin abinda na hanaki ba?" Ta kara daga masa kai, ya sake murmushi yana kallanta ya ce "Kenan kinyi alkwari zaki zauna da wacce zan hadaku, but u are my first wife, she will come after u" turo baki ta danyi sannan ta daga masa kai, yayi patting bayanta ya ce "Then stop crying" zame jikinta tayi ta koma cikin gida ya bita da kallo, daga haka ya juya ya wuce parking lot. Da yamma liss Mummy ta sauke Rafi'ah a gida, bayan sun shiga duk da sauri take sai data labartawa Ummi Rafi'ah nada saurayi, Ummi batai wani mamaki ba sabida taga yadda take making calls, sai dai bata ce komai ba, Mummy ta mike tana kallanta ta ce "Na tilasta mata dai ta bani numbersa, tinda gobe ubanta zaizo sai a kirashi yazo suyi magana" kai kawai Ummi ta daga mata, daga haka ta rakata har paking lot kafin ta dawo ciki.
Har dare Ummi bata cewa Rafi'ah komai ba, ita kuwa tinaninta kawai aiki ne ya mata yawa saboda taga tana ta marking, bayan sallan isha ta sakko downstairs daga ita sai 'yar rigar baccinta iya gwiwa, kanta ba dankwali hannunta rike da phone dinta, tana zama ta kalli Ummi ta ce "Gobe Abba da wuri zai iso ko sai caan yamma?" ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce "Sai ki kirashi ki tambayeshi" ta dan turo baki ta ce "Amma Ummi ai zai gaya miki" tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing ta kalli screen din tayi murmushi ganin Yusuf ne, daga haka ta mike ta wuce upstairs Ummi ta bita da harara. Cikin cool voice dinsa yayi mata sallma ta amsa, ya danyi murmushi ya ce "I am happy Babyluv, and it's all because of u" zama tayi gefen gado ta ce "What hapoend Dr" ya limshe idanuwansa kamar tana kllansa ya ce "Mummy just called me, tace Abba zai dawo gobe around 12 na rana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Then what?" Yusuf ya ce "I will come and see him insha Allah, tace min ta mishi magana" kamar zatai kuka ta ce "Pls ka bari ba yanzu ba Dr" Yusuf yayi murmushi yayi hanging call din, dama kawai he just call to let her know, tashi tsaye tayi ta fara zagaye dakin, duk tabi ta rikice, wayarta ta dauka tayi dailing number Mummy taji not reachable, ta kara kiran na Yusuf still d same thing, kwanciya tayi akan carpet ta rasa ta ina zata fara tsayar da Yusuf, Allah na gani batasan hukuncin da Abba da zai dauka ba, jin an bude kofa tayi surin rife idanuwanta kamar me bacci, Ummi ta shigo ta dauko wasu takardu kan stool sannan ta fice a dakin, Rafi'ah ta sauke jiyar zuciya ta mike zaune ta buga uban tagumi.


*Thank u so much for the calls and du'ah, ubangiji Allah ya biya maku bukatanku na alkhairi aduk inda kuke, i so much appreciate the way u people cares, especially when reading ur messages, na gode sosai da sosai* 🥰
[7/29, 6:47 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

_By FATIMA ✍🏻_

_25~26_

Washegari da safe Ummi na kitchen Abdul ya shigo cikin shirinsa na makaranta, ya dafa kafadarta ya ce "Good morning mother" ta ce "Morning, how are u?" Ya ce "Fine" Ummi ta ce "Go and take your breakfast" ya ce "Anty bata fito ba Ummi? And It's almost time" Ummi ta juya ta fita a kitchen din bata ce komai ba, upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi'ah, ta sameta gaban mirror ta gama shirinta tana zaune da dan karamin hijab dinta a hannu, strictly Ummi ta ce "Idan baza kije school din ba Abdul yayi wucewarsa" ta mike a hankali tana kallan Ummi ta ce "Na gama" Ummi ta ce "If u like keep sitting" daga haka ta fita a dakin taja mata kofar. Kamar wacce bata da jini ta zira hijabin sannan ta dauka school bag dinta, har zata fita taga phone dinta dake kan gado tana haske, dago wayar tayi tana kallan screen din, ta6e baki tayi ta kashe wayar ta jefa cikin press hade da jaan karamin tsaki. Tana saukowa downstairs ta samu Abdul har ya gama breakfast dinsa, ta ajiye school bag dinta sannan ta zuna ta hada tea ta fara kur6a, kana kallanta kasan a dole take sha, duk abinda take Ummi na kallanta sai dai bata ce komai ba, bayan tasha half ta mike ta haura stairs ta shiga dakinta, phone dinta ta kunna sannan tayi dailing number Yusuf, yana dagawa ya ce "Why are u not picking my calls Fatima?" Cikin fishi ta ce "Pls don't come to my house i beg u, dan Allah karka zo, i'm begging u for the sake of Allah Dr" fashewa da kuka tayi bayan ta dasa aya, Yusuf dake saurarenta ya danyi murmushi ya ce "But do u want me to break the promise i made to ur Mummy? Or what do u want me to do? so kike nace bazan zo ba kenan, she will take me non serious Rafi'ah, maganar neman aure fa ba wasa bane" sassauta kukanta tayi ta ce "Dan Allah karka zo nikam, if not i will pretend i don't know u" shiru yayi na few seconds kafin y ce "It's ok, bazan zo ba, nasan abinda zance mata, stop crying and wipe ur tears" tayi shiru tana goge idanta da bayan hannunta, ya ce "Kin goge?" Ta daga masa kai, ya ce "Baza kije school bane?" Silently ta ce "I'm going now" ya ce "Ohk safe, say your du'ah and cool down your heart, babu abinda zai faru" ta danyi shiru sai kuma ta ce "Ba kace ka fasa zua ba?" Ya ce "To kije school idan kika dawo zamuyi magana" ta ce "Ohk" daga haka tayi hanging wayar ta ajiye ta fito, tana saukowa a stairs taji Ummi na cewa Abdul "Ku tafi abinku, idan yaso ta hau cab" turo baki tayi bayan ta karaso ta dauka school bag dinta da 500 din da Ummi ta ajiye mata a gefen jakar sannan ta fice a parlorn.
Da sauri da sauri Anty Amina ta tattara magungunan da suka kar6o wajen malaminsu tasa a handbag dinta, duk ta haddace yanda akace tayi, Ikleemah dake kallanta ta ce "Wai Anty Amina tafiya zakiyi?" Ta ce "Ai ina wanka tafiya zanyi ikee, kinga yace da wuri zai taso, jirginsu karfe 9 zai tashi, to ina Abuja ina Kano a tafiyar jirgi" Ikleemah ta mike ta ce "To kona biki ne?" Anty Amina ta ce "Tambayi uwarki idan zata barki, banaso muje tayi ta damuna a waya ki koma, idan zama zama" Ikleemah ta kalli mahifiyarta dake zaune gaban TV, Ikleemah ta ce "Mami bazan bita bane?" Anty Rahama ta ce "Idan kinaso, ni Umma nakeji idan kika tafi, inna fita ita kadai kenan zata zauna" jin haka yasa Anty Amina ta dauki handbag dinta ta shige dakin Umma dan tasan dama ba bari zatai taje ba sai dai idan Umma tayi magana. Tinda Rafi'ah taje school zuciyarta ke bugawa, gashi dai Yusuf yace bazai zo ba amma duk jinta take wani iri, babu yadda Ameerah batai ba amma taki fadin abinda ke daminta, koda akai break a class ta zauna bata fita ko ina ba, ana tashi kuwa Mustapha yazo daukansu, Abdul dake kallanta ya ce "Are u sick Anty?" Ta girgiza kanta ta shiga mota, Mustapha yaja motar yana murmushi ya ce "Hajiya karama Abba ya iso tin sha biyu saura" da sauri ta dafe kirjinta ta ce "Ai nasan zai zo" daga haka ta kwanta ta limshe ido, suna isa gida yayi parking a waje ya ce "Hajiya ta aikeni kasuwa, amin afuwa" Abdul ya ce "Ba komai" Rafi'ah ta dauki school bag dinta ta fito tabi bayan Abdul, ba kowa a parlorn da suka shiga, Abdul ya fara hawa stairs itama tabi bayansa, da sallama Abdul ya shiga parlorn, Ummi ta amsa masa, ya karasa gefen
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment