Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji ana knocking ba?" ya ce "To ke zakije?" Zama tayi ta dan 6ata fuska ta ce "Ai nasan Anty Khadija ne" ya ce "Let me check" daga haka ya fito a dakin ta biyo bayansa, yana bude kofar parlor Anty Khadija ta shigo tana kallansu, Yusuf ya danyi murmushi ya ce "Welcome sis, have a seat" ta zauna akan 2 seater tana kallan Jiddah dake tsaye bayan Yusuf, a hankali ta zauna ta ce "Ina yini" Anty Khadija ta ce "Lafiya kalau, ya amarci?" Jiddah ta ce "Lafiya" Anty Khadija ta kalli Yusuf ta ce "Doctor ya amarci, ya kuma kwanan amarya?" A hankali ya ce "All fine" daga haka ya wuce daki. Yana shiga Anty Khadija ta kalli Jiddah ta ce "Dama sauran maganin nan na kawo miki, shine zaki hada shi dana bakin leda" tana rife bakinta ta ciro kullin magani ta mika mata, Jiddah ta dan yamutse fuska kafin ta kar6a ta ce "Ohk nagane" Anty Khadija ta ce "Yauwa, idan lokacin yayi zanyi alerting dinki" Jiddah ta daga mata kai ta ce "Ohk ba damuwa ki gaishe da Umma" Anty Khadija ta mike tana lankaya hand bag dinta ta ce "To sai anjima" daga haka ta fice a parlor Jiddah ta bita da harara hade da tsaki, jujjuya maganin ta dinga yi sannan ta ta6e baki ta mike ta cusa shi kasan cushion ta koma ta zauna, tana zaune taji Yusuf ya rungumeta ta baya, a hankali ya ce "What are u thinking?" Ta ce "Nothing" daga haka ya saketa ya dawo gefenta ya zauna, kwanciya tayi ta dora kanta akan cinyarsa tana kallan TV ta ce "Yaushe zan koma school" ya shafa kanta ya ce "Next week i think" ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ta limshe ido.
Anty Amina ce zaune a parlor'n ta tana ta sheka dariya, Ikleemah ta fito a daki tana kallanta ta ce "Anty Lafiya?" Mika mata wayar Anty Amina tayi, Ikleemah ta dinga kallan pic din Yusuf da Jiddah na aure, duk sai taji ba dadi, ga wani haushi daya tsaya mata a wuya, ta kalli Anty Amina ta ce "Da gaske ne aure yayi?" Anty Amina ta kara shekewa da dariya ta ce "Aure mana Ikleemah, zanso naga fuskar waccen yarinyar" ta6e baki Ikleemah tayi, ita dai taji dadi ko banza Rafi'ah ta shiga kunci, ta wani bangaren kuma haushi taji, dan a yadda mafarkinta ya nuna mata ita kadaice mata a gurin Yusuf, ajiye wayar tayi ta koma daki tana jaan tsaki.
Da sallama Anty Khadija ta shigo dakin, Umma ta amsa sannan tayi hanging wayar da take ta ce "Khadija kin dawo ne?" Ta ce "Na dan jima ma ina daki ne" Umma ta ce "Kin kaiwa Jiddah maganin dai baki manta ba ko?" Zama tayi a bakin gado ta ce "Na kai mata, kinga a hankali a hankali aiki zaina tafiya" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To saura kuma ke, dama jira nake na gama da Yusuf, ki fito da miji kema kiyi auranki" Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce "Umma kenan" Umma ta ce "Ba batun Umma kenan ba, shekararki fa 37 Khadija, ga Yusuf da yake 35 yayi aure ai yanzu kam kema sai ki tafi" Anty Khadija ta ce "Zan tafi ai, akwai lokaci" Umma ta ce "To Allah ya kaimu, ga Jiddah me 25 ma tayi auranta" tashi Anty Khadija tayi tana kallan Umma ta ce "Nifa har yanzu ban samu wanda raina ya kwanta da shi ba, ni inasan mijin da yake da Kudi na gani na fada, kyau, kuma wanda zai soni kamar ya mutu" Umma ta ce "To Allah ya kawo miki" ta ce "Ameen" daga haka ta fice a dakin. Rafi'ah ce zaune a gefen Abdul tana kallan yadda yake limshe ido yana juyi, ta kamo hannunsa ta ce "Abdul ko zaka ci abinci?" Ya girgiza kai, juyawa Rafi'ah tayi tana kallan Ummi ta ce "Ummi yaci abinci dazu ne?" Ummi dake kallansu ta ce "Yaci, ku fita waje ko zai dan sake" Rafi'ah ta kama hannunsa ta taimaka masa ya mike sannan suka nufi kofa Ummi ta bisu da kallo, tin dawowan ta a islamiyya bata tashi gefen Abdul ba, da yayi motsi zata tambayeshi koda abinda yake so, kana kallan Rafi'ah kasan ba karamar damuwa tayi akan rashin lafiyar luvly brother dinta ba. Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike ta wuce upstairs. Kujera Rafi'ah ta ajiye musu a balcony suka zauna, lokaci lokaci ta kan bashi labari ko kuma ta nuna mishi abu a waya duk dan ya dan sake, kuma alhamdullilah hakan ya masa dadi sosai, juyawa tayi jin footsteps a bayansu, ganin Ikleemah ce yasa ta juyo taci gaba da bawa Abdul labarin da take,
"To shi dama mutumin shi kadai mamanshi ta hai..." Shiru tayi ganin Ikleemah ta tsaya akansu ta kama kugu, Rafi'ah ta kauda kanta ta ce "Malama Lafiya?" Dariyar karfin hali Ikleemah ta fara yi kafin ta ce "Nazo ne na miki jaje game da abinda ya faru" Rafi'ah ta ce "Wane abu kuma?" Ikleemah ta kara fashewa da dariya ta ce "Wai kina nufin baki da labarin auran Yusuf?" Sosai zuciyarta ya buga, ta juya kanta taki kallan inda Ikleemah take, Ikleemah ta ce "To sai ayi hakuri a nemo wani, dama nasan wahalar banza kike Yusuf ba tsarar auranki bane" tashi Rafi'ah tayi cikin fishi ta ce "Mind your words Ikleemah, meye hadina dake daza ki dinga min irin wannan maganar" Ikleemah ta ce "Ai dama bance na hada abu dake ba, Allah ma ya kiyaye in hada jini da dangin cuta" tass, tass, ya sauke mata mari biyu a kumatun ta, Ikleemah ta zaro ido tana kallan Abdul dake tsaye a gabanta yana huci, yayi pointing dinta da yatsa ya ce "This should be the last zaki kira mu da dangin cuta, and idan cutan ne ai daga familyn ku ta fito, and let me keep this warning to u, Antynah isn't ur mate, u stay far away from her, idan ba haka ba u will know the bad side of me" yana kai karshe ya dauki wayar Rafi'ah ya wuce cikin apartment dinsu, kai kace bashi ke nishin rashin lafiya yanzu ba, daga Ikleemah har Rafi'ah kallansa suke, Rafi'ah ta wuce ciki itama ta bar Ikleemah dafe da kuncinta a tsaye.
Tana shiga ta samu ba kowa a parlor ta wuce dakin Abdul ta murda handle din ta shiga, tsaye ta sameshi gaban mirror da towel a hannunsa, strictly ta ce "Why did u slapped her?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Because she insulted u" Rafi'ah ta ce "Don't u ever try to slap her again, bata girmeka bane? or are u stupid" baice komai ba saima kayansa daya fara cirewa, ta ce "Kuma kasan Abba won't take it likely ko? Yanzu da abinda ya faru da wanda bai faru ba zasu fada mishi, so kake kullum yana yiwa Ummi fada, zai ce fault dinta ne" idanta taap cike da hawaye ta karashe maganar, ita babbar damuwarta bai wuce fishin Umminta ba, shiyasa yanzu komai zai faru ta hakura zata shanye akan Abba yayi wa Umminta fada, rungumeta da taji yayi ne yasa ta dawo daga tinanin data tafi, Abdul ya kai hannunsa idanta ya ce "Pls don't cry sister, insha Allah babu abinda zai faru" a hankali ta ce "But u slapped her Abduljalal, why?" Bayanta ya hau bubbugawa calmly ya ce "Not when they're insulting u sis, bazan iya ganin ana insulting dinki nayi shiru ba, bama zagi ba, wallahi ko kallan banza aka miki bazan bar mutum ba, did u know how much i luv u Aunty?" Rungumeshi itama tayi tana murmushi ta ce "Idan kana sona ta kaida abinda banaso" ya ce "Ohk" daga haka ta sakeshi ta fita jin an bude kofar parlor.
Tinda Abi ya turo Sadeeq ya kira shi ya kasa nutsuwa, ya dinga kai kawo yana tinanin abinda zaije yaji, bayan minti 10 Sadeeq ya kara knocking dakin ya shigo, tsayawa yayi yana kallan yayan nasu ya ce "Abi yana jiranka fa Yaya" kai ya daga masa sannan ya bi bayansa suka fita, parlor ya fita ya zauna akan carpet yana kallan Abi ya ce "Sannu da dawowa" Abi ya ce "Yauwa son" shima shiru yayi ya rasa ta ina zai fara masa bayani, caan dai ya dago yana kallan Jawad da kansa ke kasa ya ce "Naje gidan su Fatima dazu, sai dai kuma the answer wasn't funny saboda an riga da an yiwa wani alkawari, so u don't worry son, kayi fatan Allah yasa haka shine alkhairinka, ya kawo maka wata da ban" tinda Abi ya fara magana Zuciyarsa take bugawa non stop, a hankali ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya nufi dakinsa just trying to control himself, yana shiga dakin wasu hawaye masu zafi suka sauko masa, yayi saurin gogewa saboda raban da yayi kuka harya manta a rayuwarsa, ya zauna bakin gado ya kama kansa yana karanto addu'o'i, bayan few minutes aka bude kofar dakin, dagowa yayi suka hada ido da Mami, yayi saurin sauke kansa ya ce "I'm having headache"

[8/3, 7:09 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_36_
*THE PAGE IS DEDICATED TO THE WHOLE MEMEBERS OF ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* 💞

Shiru Mami tayi tana kallansa kafin ta ce "Since when?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Two hours ago" juyawa tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo da bottle water sai cup hade da panadol, zama tayi gefensa ta 6alla masa maganin ta mika masa sannan ta zuba masa ruwa a cup ya hadiye, mika mata cup din yayi ya ce "Thank u" Mami ta kar6a sannan ta mike ta ce "U rest first, idan bai daina ba sai muje clinic" kai ya daga mata sannan ta fita a dakin ta jawo masa kofa. Bayan sati daya da bikin Yusuf, Rafi'ah na kitchen tana kwashe shinkafa cikin warmer wayarta ya fara ringing, ta fito cikin nutsuwa ta dauka wayarta sannan ta koma kitchen Ummi ta bita da kallo, picking call din tayi hade da sallama Yusuf ya ce "How are u Baby?" a hankali ta ce "I'm fine" ya ce "Good, zanzo yau da yamma" dan murmushi tayi me kyau tana gyara zaman phone din a kunnenta, dan tinda yayi aure sai yau zata ganshi, waya dai kwana 3 da aure suka farayi, cikin cool voice dinsa ya ce "Or are u not happy? I missed u more than u know Baby" cikin sanyin murya ta ce "I also misaed u Doctor" ya ce "Worry not u will see me insha Allah" murmushi tayi ta ce "Allah ya kaimu" ya ce "I will call u ltr when i'm home, ina driving" toh kawai tace sannan tayi hanging call din tana murmushi. Bayan ta gama komai ta wuce upstairs zuwa dakinta ta tattaro hijabs dinta na hadda ta wuce backyard ta saka a washing machine, tana zaune tana chat da Ameera harya gama sannan ta dauraye tayi spinning ta fara shanyawa, tana gamawa taji anyi parking mota, lekawa tayi taga Mummy na shirin fitowa, ta karasa da gudu ta rungumeta tana murmushi ta ce "You're welcome mother" Mummy ta shafa kanta ta ce "Thank u daughter" handbag dinta Rafi'ah ta kar6a sannan suka wuce ciki.
Haka Rayuwar Rafi'ah ya kasance watarana dadi watarana kunci, babu abinda yake daga mata hankali face idan ta kira Yusuf Jiddah ta dauka, dan dole haka ta dinga avoiding call dinsa ko zata samu sauki, dan kwana biyu ciwanta ya kan tashi but not that serious, hakan yasa tayi concentrating akan karatunta ta watsar da shi itama, duk da shi yana kokarin zuwa ya ganta amma saam bata wani sake masa yanzu, musamman yanzu da take shirin yin Waec dinta, Khairiyya ta kan zo gidan sosai wajen Rafi'ah, ko Yusuf ya kawota ko kuma driver ya suketa, sosai Rafi'ah take ji da yarinyar har cikin ranta. Bangaren Jawad kuma tin da aka saka bikin Rafi'ah ya daina zuwa gidan, kullum wajen aiki yake yini sai dare yake dawowa gida, idan ka ganshi zaka rantse bashi da damuwa, har wani kiba ya danyi ya kara haske, ya watsar da duk wani abu da zaisa ya shiga damuwa, Mami ma idan ya gaisheta da safe ya fice sai tayi bacci yake dawowa. Ba karamin tashin hankali Anty khadija da Ummanta suka shiga ba ganin maganinsu baya tasiri a jikin Yusuf, duk da dama malamin yace a hankali aiki zaiyi amma gashi dai babu changes tsawon wata 8, ita kuwa Jiddah tinda tayi 6ari ta shiga damuwa saboda har yanzu shiru ne babu alamun wani ciki a tattare da ita, suma suna nasu maganin ita da Auntyn sai dai suma babu abinda ya canza, dama da zarar Anty Khadija ta kawo magani Jiddah zata tattara tasa a handbag dinta idan ta fita school ta zubar a titi, haka ta dinga musu tin farkon bikinta har zuwa yau, wani lokaci idan ta tuna auran Yusuf sai ta fashe da kuka, haka zaiyi ta tambayarta amma ta masa banza. Anty Amina ma kullum taje gidansu sai an hado ta da magani, wani lokaci tayi amfani dashi wani lokaci ta ki, dan ita yanzu babbar damuwatarta bai wuce ta hana auren Rafi'ah ba, wannan karan da kanta ta kar6o magani tayi amfani dashi da sunan Rafi'ah ta bunne, bata ta6a shiga tashin hankali kamar ranar da aka kawo lefe ba, ko Jiddah batai haukan da tayi ba, yini tayi tana zarya a parlornta, karshe data kasa hakuri taje ta tono layoyin taga sunan nan inda suke, sake rufe wajen tayi sannan ta koma apartment dinta cike da damuwa, gashi Abba tinda biki ya rage saura sauti 2 ya dawo gida, baya bari ta fita ko ina saboda kullum Ikleemah sai tazo, watarana ta kwana watarana kuma ta tafi. Ranar Saturday Rafi'ah ta gama Neco, tsabar dadi ranar yini tayi tana bacci, washegari kuma Mummy ta taho da mai gyaran jiki aka fara mata, a BQ aka sauki matar saboda safe da yamma ake mata dilka, tin tana marmarinsa harta gaji, ga warinsa daya isheta, ji take kamar tayi amai wani lokaci, ana saura sati daya biki tana kwance a daki taji ana knocking ta danyi shiru sannan ta ce "Waye?" Abdul ya turo kofar ya ce "It's me, ana jiranki a BQ" tashi tayi tana turo baki ta zura himar dinta sannan ta fito a dakin zuwa downstairs, Ummi kadai ta samu a parlor, ta sunkuyar da kanta ta ce "Bacci nayi shiyasa ban fito ba" Ummi taci gaba da abinda take bata kulata ba, fita tayi ta wuce BQ, ta shiga parlor da sallama, Mummy ce da mai gyaran jikin a zaune suna magana, karasowa tayi ta zauna tana dan yatsine fuska ta ce "Wai yaushe za'a gama ne Mummy?" Anty Halima ta ce "Ranar da aka fara biki mana" kamar zatai kuka ta ce "Dan Allah daga yau a kyaleni banaso nikam, Allah ji nake kamar zanyi amai" harara Mummy ta dalla mata ta ce "Wallahi baki isa daga yau a daina gyaran jiki ba, ina laifin ranar Wednesday, Thursday ki huta friday a fara biki" tagumi Rafi'ah tayi tana kallanta kafin ta ce "Ni gaskiya i'm tired Mummy" Murmushi me gyaran jiki tayi cikin rarrashi ta ce "Kwana hudu fa kawai ya rage Amarya, ki kai hakuri kusan sati 3 ma balle kwana 4" dan turo baki Rafi'ah tayi ta cire hijabin jikinta sannan ta dauka zanin da take daurawa ta wuce daki.
Da daddare Rafi'ah na zaune a parlor tana shan tea Abba ya shigo parlor, ta mike a hankali ta kar6a ledan hannunsa ta ce "Sannu da dawowa Abba" ya ce "Yauwa Mamana, how are u?" Silently ta ce "Fine Abba" daga haka ta wuce kitchen, ajiye ledan hannunta tayi ta ce "Ummi, Abba ya dawo" daga haka tayi saurin ficewa dan ma kar a sata aiki, Ummi ta bita da harara sannan ta wanke hannunta ta fito parlor. Rafi'ah na shiga dakinta taga missed call din Yusuf har 7, kafin ta sake kira wani kiran ya shigo, a hankali tayi picking ta kai kunne, ya ce "Where have u been Baby?" ta ce "Bana kusa ne" ya ce "I'm outside" toh kawai tace sannan tayi hanging call din, babban himar dinta ta saka har kasa, sai kamshi take ga fatar jikinta dake sheki, ko powder babu a fuskarta amma tayi bala'in yin kyau, ta jima a tsaye tana rike da staircase, gashi tana san fita amma kuma su Abba na parlor, ganin call din Yusuf na kara shigowa tayi karfin hali sannan ta sauko ta nufi kofa, Ummi dake yayyanka Apple ta dago tana kallanta ta ce "Ina zakije?" Tsayawa tayi cikin cool voice ta ce "Waje" daga haka ta bude kofar ta fita, as usual yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannu, Yusuf ya dan zaro ido ganin yadda ta canza sosai, gaba daya street light din ya haskata, ta sauke kanta tana wasa da fingers dinta ta ce "You're welcome" ya ce "Thank u wife, kinga yadda ki kai kyau kuwa? anya nima bazanje amin ba" boye fuskarta tayi tana murmushi ta ce "Kai ai namiji ne" ya ce "To ai banaso ki fini kyau" dariya ta danyi ta ce "How are u?" Ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce "I'm fine love, ya jikin ki, ina bakya damuwa sosai" kai ta daga masa sannan ta ce "Ehh" ya ce "That's good" bude mota yayi ya ciro IV card da yawa cikin bakin leda da kuma key ya mika mata ya ce "Take this, key din na gidan ne" ta kar6a tana murmushi ta ce "Thank u, ai basu tambayi key ba" ya ce "Mummy ta tambaya dazu, ki kai mata" kai kawai ta daga masa, ya ce "To ya kamata ki shiga gida, dare yayi" ya karashe mganar yana kashe mata ido daya, murmushi tayi kawai ta ce "To, saida safe" ya ce "Alright Baby" daga haka ta shige ciki shi kuma ya koma mota yayi reverse sannan ya bar layin. Anty Khadija ce zaune gaban Umma duk sunyi jugum har abin tausayi, Anty Khadija ta mike tana kallan Umma ta ce "Nifa gani nake kamar Jiddah yaudararmu take bata amfani da duk wani magani da muke bata, inba haka ba yau wata kusan 9 labari bai canza ba" Umma ta ta6e baki ta ce "Haka dai kika gani Khadija, idan hakane ta ina zata so a mata kishiya? dole dai tana amfani da magungunan nasara ce babu, gobe kuwa zan koma inji ya ake ciki" Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "To Allah ya kaimu" daga haka ta fice a dakin. Karfe 12 na dare Rafi'ah ta tashi ta danna wayarta dake gefenta, missed call din Yusuf ta gani guda 3, ta danyi murmushi ganin text dinsa a saman wayar ya rubuta "I love you" hasken wayar ta kunna sannan ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta tada sallah, har kusan karfe 3 kafin ta kwanta anan kasa nan da nan bacci ya dauketa, washegari ya rage saura kwana 4 biki, 'yan uwan su Ummi sun fara sauka a gidan maza da mata, ba karamin tashin hankali Anty Amina ta shiga ba, dan a cewar malaminta ko taron bikin baza'ai ba, gaba daya ta shiga damuwa har wani rama takeyi gashi ta kasa nutsuwa, kusan kullum sai kaji Abba na mata fada. Da sallama ya shigo dakin hannunsa rike da makullum mota, ya zauna bakin gado yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mami gobe fa zan tafi Cyprus" tashi tayi ta zauna tana kallansa ta ce "Ai na zata ka fasa tafiyan da naji ba kai magana ba" ya dan shafa gashin kansa ya ce "Ehh, da ba yanzu bane, to amma sun kirani ne" Mami ta ce "To Allah ya kaimu, da yushe zaku tashi?" Ya ce "Karfe 10 na dare, idan na kwana a Abuja sai mu wuce" ta ce "To Allah ya kaika lafiya, kana dawowa kayi auranka kaima ka zama mutum, ga masu cuta ma suna aure ballantana lafiyayyu" shiru yayi kansa akan wayarsa yana dannawa, Mami ta ce "Wannan karan bakasan kilishi ne? naji bakai maganar ba" dagowa yayi yana kallanta ya ce "Inaso" daga haka ya mike ya fita sannan ya ja mata kofar. Direct part din Mummy ya shiga da sallama, ya zauna akan kujera yana kallan TV, fitowa tayi tana kallansa ta ce "Jawad kaine?" Ya ce "Ehh" dan raban daya shigo mata harta manta, sai dai idan sun hadu a parlorn Abi su gaisa, Mummy ta dauko masa malt da cup sai ruwa ta ajiye masa a gabansa ta ce "Dan kai yanzu ka zama bako Ahmad, bama ganinka baka ganinmu" murmushi ya danyi yana shafa gashin kansa ya ce "Aiki ne Mummy" ta ce "Haka dai kace, kaikam idan ka zama shugaban kasa sai dai muyi hakuri da kai, kullum aiki aiki baya karewa, ai naga a court dinma ana hutu ko?" Murmushi ya sakeyi ya ce "Zan tafi Cyprus ne gobe" Mummy ta sake baki tana kallanshi ta ce "Cyprus Ahmad?" Ya ce "Insha Allah" ta ce "Amma kasan zan aurar da Rafi'ah ko?" A hankali ya ce "Ehh, amma kiyi hakuri daga court din ne suka nemi a turani, wata biyu zanyi a caan" Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai shikkenan, Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a, bari na aike ka ka kai musu sako" daga haka ta shiga daki tana fadin "To dambu kake so ko meat pie zan maka sai kana soyawa?" Fitowa tayi da envelop a hannunta ta mika masa ta ce "Dan Allah ka kai musu yanzu Jawad, tin dazu nake kiran Abduljalal yazo ya kar6a baizo ba gashi yamma ta kusa" very gentle ya mike ya dauki malt din yana kallanta ya ce "To saina dawo" ta ce "Ka gaishe su, baka fadi me zan makan ba" ba tare daya kalleta ba ya ce "Dambu nakeso" ta ce "Ba damuwa" daga haka ya fita a parlorn Mummy, Sadeeq kadai ya samu yana cin abinci, ya wuce shi ya fita a parlor ya nufi parking lot, yana kunna motar ya danna horn, gate man ya bude sannan ya fitar da motar bayan ya amsa gaisuwar mai gadin, yana fita yayi parking ya bude envelope din, kananun IV card ne aciki na kamu na Mummy tayi organizing, ya ciro guda daya yana kallo, bayan ya gama karantawa ya maida ciki ya rufe sannan ya tada motar ya bar kofar gidan.
[8/4, 2:59 PM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_37_

A bakin gate yayi parking as usual, dashboard ya bude ya dauko chequebook da biro yayi rubutu sannan ya yage paper din yasa a pocket dinsa, wani dan karamin box ya dauko sannan ya dauki envelope din ya fito a motar ya rufe, gently ya karasa bakin gate din ya tura sannan ya shiga, few people ne a tsakar gidan kowa da abinda yake wasu na zaune akan mat, wasu kuma nata backyard ana girki, wasu

Please Login or Register in order to submit comment