Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

hanya" ya kara kamo hannunta ya ce "Are u angry with me Fatima?" Ta girgiza kanta trying hard not to cry ta ce "Why will i Dr, Allah yasa haka shine alkhairi" daga haka ta zame hannunta ta fito a motar. Tabbas ita kadai tasan abinda taji a zuciyarta a sanda yake mata zancen Jiddah, but ya zatai, a yanzu babu wanda takeso fiye da Yusuf bayan iyayenta, haka Allah ya tsara mata me mata zata aura, so her own is to pray for d best, tana shigowa gate hawayen daya taru a idanta ya gangaro, Jawad dake tsaye a parking lot ya nufota yana kallanta ya ce "What's it? Why are u crying" matsawa tayi gefe zata wuce ya kamo hannunta suka koma gate, lekawa yayi ya hango motar Yusuf daya kusan kaiwa titi, ya juyo yana kallanta ya ce "Meya faru?" Ta girgiza masa kai, ya ce "Tell me, koya maki wani abu ne?" Ta girgiza kai tana saan kwace hannunta amma ta kasa, ya kara jaanta zuwa parking lot suka nufi backyard din gidan, yana rike da hannunta kawai yaji tayi gefe zata fadi, yayi saurin rikota zuwa jikinshi yana kallan numfashinta dake shirin sarkewa, ta dafe kirjinta hawaye naci gaba da sakko mata, yana jiyo yadda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri, ya kai hannunshi bayanta yana patting dinta to make sure she remain calm.


*I'm on my way to Kano now, ur prayer pls*

_08103810398_
[7/29, 6:47 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_30_

Hannunta na rawa tayi saurin janye jikinta tana kokarin mikewa, Jawad ya durkusa yana kallan eyeballs dinta dake fitar da hawaye ya ce "Are you ok Fatima?" Ta daga masa kai tana san tafiya amma jiri takeji bana wasa ba, har lokacin yana rike da hannunta yana kallanta, ta dafa wall ta fara tafiya a hankali ya kamo ta ya ce "You sit down and rest first" girgiza masa kai tayi, ya kamo hannunta ya ajiyeta akan balcony ya ce "Don't u there try to get up, keep quite and remain still" kanta ta kifa akan cinyoyinta ta fashe da kuka, Jawad ya zauna gefenta yana kallanta da mamaki, kusan minti 5 tana kukan kafin ta dago kanta tana kallanshi ta ce "Zan iya tafiya Yaya, i'm not feeling anything" ya ce "Ohk, but what happened" tayi saurin girgiza masa kai ta ce "I'm having headache but no one offended me" daga haka ta mike walking slowly ta bar wajen, har idanuwanta sun kada sosai ta tura kofar parlon su ta shiga tana dafe da kirjinta, ba kowa a parlor hakan yasa ta nufi upstairs, tana gama hawa stairs ta shige dakinta tasa key, zubewa tayi a kasa ta fara kuka me cin rai yadda ba wanda zaiji, da kyar ta karasa kan gadonta ta jawo wayarta ta kira number Ameera, tana dagawa ta ce "Dan Allah Ameera kizo gidanmu, let me tell u ko zanji saukin abinda nakeji" Ameera da hankalinta ya tashi ta ce "What are u saying Fatima? Is Ummi not at home" tsayar da kukan Rafi'ah tayi ta ce "I'm begging u Ameera, dan Allah kizo karna mutu" cikin tashin hankali Ameera ta ce "Ohk gani nan" daga haka tayi hanging wayar. Cikin minti 10 sai gata ta shigo gidan, ta murda handle din kofar ta shigo parlorn, dan murmushi tayi ganin Ummi a parlor tare da Jawad ta ce "Ina yini Ummi" Ummi dake kallanta ta ce "Lafiya kalau Zainab, ya hutu dasu Mamanki?" A hankali ta ce "Duk lafiya suke" kallan Jawad tayi shima ta gaishe shi ya amsa, Ummi ta ce "Gashi kamar ma ta fita fa Zainab, amma bari na kirata a waya" mikewa Ameera tayi ta ce "A'a ita ta kirani, tana sama ina ga" Ummi ta ce "Ohh ta dawo kenan, to ki shiga mana" Ameera ta ce "To Ummi" daga haka ta wuce upstair. Tana murda kofar dakin taji a kulle ta fara bubbuga kofar tana kiran sunan Rafi'ah, tashi tayi ta cire hijabin jikinta sannan ta karasa kofar ta bude, Ameera ta rungumeta ta ce "What is it Fatima? Are u sick?" Rafi'ah ta tura kofar ta kamo hannun Ameera ta ce "Ameera ya zanyi, my Doctor is getting marriage" zaro ido Ameera tayi tana kallan yadda ta fashe da kuka, ta kara rungume Ameera ta ce "Allah inason shi, kema kin sani Ameera, but suddenly yau yake cemin akwai wacce zai aura after then saiya aureni, Ameera my heart is beaten i dont want to have attack" tana magana amma hawaye sunki tsaya mata, Ameera ta shiga share mata idanta ta ce "Kiyi shiru, kinsha magani kuma?" Rafi'ah ta girgiza mata kai ta ce "I took all before u came" Ameera ta kamo hamnunta ta ce "To yanzu ya zamuyi, zaki rabu dashi ne?" Da sauri Rafi'ah ta kalleta zuciyarta na bugawa ta ce "Are u out of ur senses Ameerah, ya zanyi na rabu da abinda zuciyata take so, ai koda mata uku zai aura zanje ta hudu i don't care" Ameera ta dalla mata harara ta ce "And if u don't care why are u crying?" Rafi'ah dake share hawayenta ta ce "Kinsan dai i most...is a most... I repeat a most...a fada maka magana irin haka unexpected ace bakai kuka ba, but ya zanyi Ameera ina san Yusuf fiye da tinanin kowa, amma tinda haka Allah ya tsaramin i will accept my fate and i pray, nasan Allah ya ga zuciyana banajin zan iya rayuwa da kowa inba Doctor ba, he is just a half of me Ameera" tana rife bakinta wasu siraran hawaye suka shiga sauko mata, Ameera ta mike tana murmushi ta ce "That's the best for u Teemah, kiyi ta addu'a kawai, and i will also contribute mine" rungumeta Rafi'ah rayi ta ce "Thank u friend, i luv u" Ameera ta share mata idanta ta ce "Dan Allah ki daina kuka, ai naga kece ma zakije a amarya ba'a tsohuwa ba" dariya ta bawa Rafi'ah, ta danyi murmushi ta ce "Haka ne mana, and nasan Doctor zai iya komai dan ya saki farinciki, kuma hakan da yayi shine adalci daya sanar dake tin yanzu, kinga kinsan da zamanta kenan, koda auransu yazo bazakiji kamar yadda idan baki sani ba, and last last u stop crying dear, i'm begging u" murmushi Rafi'ah ta sakeyi ta ce "Insha Allah i won't Ameerah, nagode sosai" Ameera ta yafa veil dinta ta ce "I'm going, Mama bata gida na bar su Noor su kadai" tashi Rafi'ah tayi ta zura hijabinta ta ce "Bari na raka ki" daga haka suka fito a dakin, suna saukowa downstairs Ameera ta dan rusuna ta ce "Ummi zan tafi sai anjima" Ummi ta ce "To Zainab, ki gaishe da gida" daga haka suka fita Jawad ya bisu da kallo, bakin gate Rafi'ah ta rakata sannan ta juyo, tana shiga parlorn suka hada ido da Jawad, ya dinga kallanta to make sure she isn't crying, ta wuce upstairs da sauri tana turo baki, a dakinta ta samu Ummi na duba abu a wardrobe, ta cire hijab dinta ta zauna bakin gado, Ummi ta gama tattara takardun ta juyo tana kallanta ta ce "Meya samu idonki? Kamar kinyi kuka" ta ce "Abune ya fada min" Ummi ta ce "Ya fita ne?" ta ce "Ehh" daga haka Ummi ta fita a dakin.
Shafa kansa yayi yana kallanta yana murmushi , Ammi ta ce "To meyasa baku shigo na ganta ba?" Ya ce "Zan kawota watarana ta ganki" Ammi ta ce "Ai shikkenan, muna ta bakayi aure da wuri ba ashe kaikam da biyu zaka fara" Farouk dake zaune yayi dariya ya ce "Ammi yanzu nan aka ce maki ba lokaci daya zai auresu ba" Ammi ta ce "Shekara daya kaam ai kamar yau ne Farouk" murmushi sukai duk tasu, Ammi ta ce "Gobe insha Allah zanje naga lefen Jiddan" ya ce "Ohk, amma karkije da Khairiyya bakinta baya shiru" Ammi ta ce "Kanku akeji kuma" da sallama Sameer ya shigo parlorn yana rike da key din motarsa, ya mijawa Yusuf hannu suka gaisa, bayan ya zauna Ammi ta ce "Saura kai Sameer, Yusuf ya kusan zama ango, dama ku biyun nan ku aka sawa ido, yana kaucewa saura kai kuma" Sameer ya daga kafada ya ce "Ni ai da hudu zan fara Ammi" Farouk dai na zaune sai dariya yake, Sameer ya ce "Na bawa Yusuf za6i ya samo min daya, na samo daya da kaina, keda Daddy sai ku samo daddaya" Yusuf ya ce "Aa ba ruwana nikam" Sameer ya mike yana dariya ya ce "Ehh mana, kaga sai ku tayani nema, amma kuma zanfisan waccen zan samo maganar gaskiya" a tare duk suka kwashe da dariya, Ammi ta ce "Ba zancen wasa ba Sameer, da anyi maganar aure saika waske da wasa shekara 34 kana zaune min a gida ga uban ci, gara ma Yusuf baya wani ci, amma kaikam duk wacce ta aureka ta shiga uku da girki" sai murmushi yake ya nufi kaan dinning ya dauki plate, Ammi ta ce "Ka gani ko Yusuf, to ko a office haka yake, yana aiki yana ci" Yusuf dai dariya kawai yake yana kallan Sameer, ya juyo yana kallan Farouk ya ce "Yaushe zaka koma Cyprus Umar?" Farouk ya ce "Next month, hutun dama ba yawa" Yusuf ya ce "Allah ya kaimu" daga haka ya mike yana kallan Ammi ya ce "Zan tafi Ammi" Khairiyya dake kwance jikin Ammi ta ce "Yaya ka gaishe da Anty" ya ce "To zataji, bye bye" daga haka ya daga mata hannu, Sameer ya daga masa hannu ya ce "Sai yaushe kuma?" ya ce "Sai dai kazo kawai" daga haka sukai sallama ya fita a parlor, yana isa parking lot wayarshi tayi kara, ya zaro ta a pocket dinsa yana kallan message din Jiddah kamar haka _"Hello, i just text to tell u that ansa ranar auranmu nan da 1 month, and i hope u will come back soon? Saboda mu nuna farincikinmu, na hada maka favorite food dinka I luv u Yaya"_.


*For the sake of Khadija KK, ga update nan very little 😟 ba dan nacin kiba da bazanyi ba 😄 i'm so tired wallah* .
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_31_

Fifteen minutes ya kai Yusuf gida daga unguwar Rimi, bayan yayi parking ya fito rike da phone dinsa ya rife motar, yana juyawa suka hada ido da Jiddah dake tsaye tana sakar masa murmushi, tayi bala'in yin kyau sai kyalli take, a hankali ya zura hannunsa cikin pocket dinsa ya fara takawa gently har zuwa inda take tsaye, yayi kasa da murya ya ce "U look so cute Jiddah tah" ta kara sakar masa murmushi ta ce "Thank u Yayana, muje ciki kaga abinda na dafa maka" ya danyi murmushi yabi bayanta suka shiga parlorn, ba kowa a ciki sai TV dake ta aiki, ta zauna akan dinning tana kallansa ta ce "Here it is Yaya" ya bude karamar warmer yana kallan vegetable soup din data ji kayan hadi da nama, ya bude dayan yaga tuwon shinkafa, surprisingly ya juyo yana kallanta ya ce "So u have time to prepare this kike barina da yunwa Jiddah?" Ta farfara masa ido ta ce "Ai lokacin ina school ne yanzu kuma nayi hutu" daga haka ta mike ta fara serving dinsa, Yusuf ya dan shafa kansa yana kallanta ya ce "Hope haka zakina min a gidana?" Ta juyo tana kallansa sai kuma tayi murmushi ta ce "Accepted" hannunsa ya wanke ya fara cin tuwan yana kallanta, bayan few minutes ya kara kallanta yaga kallansa take, ya danyi murmushi ya ce "Naje wajen kanwarki yau, and u know what?" Nan da nan ta hade rai ta juya kanta gefe, ya ce "Ya akayi Jiddan Yaya?" Ta kara hade rai ta ce "Ni banasan zancen yarinyar" Yusuf ya wara ido yana kallanta ya ce "Really?" Ta daga masa kai, ya ce "To ai watarana tare zamu zauna, dan banda ra'ayin raba muku gida, kinga tun wuri gara ku saba, Fatima bata da matsala, she's kind and nice to stay with" Yana rufe bakinsa taja wani dogon tsaki, ya juyo yana kallanta ya ce "Why the hiss Jiddah?" A fusace ta ce "Then what's my business with her? nina ce banasan kana min maganarta akwai abinda na hada da ita ne" Yusuf ya wanke hannunsa ya dauki phone dinsa dake kan dinning ya ce "Ai kuwa ke kika hada abu da ita, tinda very soon zaku mallaki miji daya" mikewa tayi kamar zata tashi sama ta bar wajen ya bita da kallo. Kwana uku da faruwan haka Yusuf ya kira Abba ya sanar masa maganar auransa da Jiddah, bayan sun gama waya Abba ya sanarwa Ummi, ta nuna 6acin ranta karara a fili saboda bata ta6a tinanin haka ba, fitowa tayi a dakin Abba duk jikinta a mace ta wuce dakinta, Abdul na zaune yana kallo a laptop dinta, ta rife laptop din ya dago yana kallanta ya ce "Nayi sallah fa Ummi" zama tayi bakin gado ta ce "Kiramin Rafi'ah, kai kuma ka wuce" a hankali yace to sannan ya fita a dakin ya rufo mata kofa, fitowanta a wanka kenan tana goge jikinta Abdul ya shigo, ya tsaya bakin kofa ya ce "Anty, Ummi na kiranki" daga haka ya fice a dakin, cikin sauri ta shafa body lotion ta shirya cikin doguwar riga na atampa sannan ta daura dankwalinta ta fita zuwa dakin Umminsu, gently ta tura kofar ta shiga da sallama, Ummi dake zaune ta ce "Come here" sai da kirjinta ya buga ganin yanayin mahaifiyarta, a tsorace ta karasa ta zauna a kan carpet ta ce "I'm here" Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Da gaske ne Yusuf aure zaiyi?" Rafi'ah ta daga mata kai, Ummi ta ce "And that's what u choose for yourself?" Kanta ta sauke kasa bata ce komai ba, Ummi ta ce "Well, kiyi duk abinda kika ga ya dace Rafi'ah, har nawa kike da zaki auri me mata? Don't u see ur mates? Kowa kokari yake idan ya gama secondary school ya samu admission yaci gaba da karatu but ke aure kika sa a gaba" kanta na kasa duk tana sauraron mahaifiyarta, Ummi ta ta6e baki ta ce "Ya miki kyau, idan kinga haka kikeso fine, nidai addu'a shine nawa, kuma duk abinda ya faru dake mine is to say sorry" a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce "I'm sorry" Ummi ta ce "Noo u haven't wronged me Rafi'ah, ina jiye miki gaba ne, shi aure nutsuwa yake bukata da kwanciyar hankali, nasan kuma indai zakije gidan wata to dole ne zakiyi facing challenges, u are too young for that Rafi'ah, bazaki hakura dashi ba idan kika gama Allah ya kawo miki wani kiyi auranki" sai a sannan ta juyo dai dai saitin Ummi ta ce "Dan Allah Ummi kiyita min addu'a, i don't know what is coming over me, ina sanshi Ummi, kuma ita sun dade tare dashi, na miki alkawarin bazan ta6a neman fadan taba idan har Allah yayi shina aura, i promise u this Ummina, addu'ar ki kawai nake bukata" ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce "Tooo, Allah ya za6a miki duk abinda yafi alkhairi" a hankali ta ce "Ameen" sannan ta mike ta fita Ummi ta bita da kallo.
Shirye~ shirye sosai Umma take na bikin Jiddah, gidansu ma kansa saida aka masa paint from head to toe. Almost everyday Jawad ya kanje ya gaishe da Ummi, wani lokaci ya kawo Mummy su yini, duk da ba'a gida yake kwana ba duk safiya saiya biya ya gaishe da Mummy da Abi kafin ya wuce wajen aiki, ta bangaren Yusuf kuwa tinda ya gama gyaran gidansa Umma ta sa shi a gaba, yau tace ya kawo dubu dari, gobe tace ya kawo dubu hamsin, haka dai kullum, ko kadan kuma baya nuna gajiyawarsa akan hakan, duk abinda suka tambaya ya kam basu, sosai da sosai kuma yake kula da Rafi'ah, baya kwana biyu baije sun gaisa ba, waya kuwa kullum cikin yinta suke hakan kuma na kona raan Jiddah ba kadan ba, idan tayi magana sai yace ai ita kullum suna tare, a haka har biki saura sati daya, a ranar ne kuma Mamin Jawad ta dawo daga Abuja saboda Ikram zata koma school.
Zaune take a gaban mirror tana waya aka bude kofar, tayi still tana kallan wanda zai shigo, ganin Ameera yasa ta sauke ajiyar zuciya dan a tinaninta Ummice, da yanzu ta hau fada, Ameera ta tsaya gabanta ta ce "Matar Doctor Yusuf" Rafi'ah ta danyi murmushi tayi hanging wayar ta ce "Matarsa na gidansu ai" Ameera ta ce "Kema very soon zaki zama ai" Rafi'ah ta sake murmushi ta ce "Daga ina kike" Ameera ta ce "Jiya bakije islamiyya ba, shiyasa nazo naga ko lafiya, kuma dazu nayi ta kiran wayanki baki dauka ba" Rafi'ah ta ce "Ohh, wayan na silent ne, kinsan Doctor used to called much, kuma Ummi fada take tayi wai ina waya da yawa, nikam kawai sai nasa a silent idan ya kira nayi ta wayana, yanzu ma akan idan na gama zan kiraki ne" Ameera ta ta6e baki ta ce "To aikuwa kamar a bakin Ummi" Rafi'ah nata dariya ta ce "Kamar da gaske". Hira sosai sukayi kafin Rafi'ah ta rakata har bakin layi sannan ta dawo gida, tana dawowa ta samu Ummi a parlor ta dawo a aiki, ta zauna tana kallanta ta ce "Sannu da dawowa" Ummi ta ce "Sannu, Anty Halima nata kiranki wai baki dauka ba why?" Rafi'ah ta duba phone dinta aikwa taga 6 missed call dinta, ta ce "I don't know she called" Ummi ta ce "Tinda yau saturday ki shirya Mustapha ya kaiki, batajin dadi ki tayata zama, gobe saiki dawo" dan zaro ido tayi ta ce "Meya sameta?" Ummi ta ce "Zazza6i take, yanzu nayi branching na duba ta" sama Rafi'ah ta wuce ta samu handbag din Ummi me dan girma ta saka kayanta da drugs dinta a ciki sannan ta canza hijabi ta sauko tana kallan Ummi ta ce "To zan tafi sai da safe" Ummi ta ce "Safe, zan kira Abba na fada masa" daga haka ta fita zuwa parking lot.
Mustapha na zaune a balcony din Anty Amina yana kallan idan film a wayarsa, dama nan yake zama indai tana Abuja, Rafi'ah ta karaso kusanshi ta ce "Zaka kaini gidan Mummy yanzu fa" ya mike yana nade tabamarsa ya ce "To Hajiya karama, wallahi wani film nake kalla, yarinyar cikin film din kamar ke, har kama kuke Hajiya" Rafi'ah ta dan juya ido ta ce "Taya za'ai ina Nigeria kace ina kama da Indians" ya ce "Allah kuwa Hajiya, hancinku ma iri daya ne" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "To zan hadaka da Doctor kuwa" Mustapha ya washe baki yana dariya ya ce "Allah sarki, ai jiya ma daya zo kafin ki fito hira muka sha, ya bani dubu uku, gaskiya kinyi sa'a Hajiya karama, akwaishi da kyauta, gashi fari kaal dan gaye, amma dai bafulatani ne ko?" Rafi'ah na shiga mota ta ce "Sai dai ka tambayeshi idan yazo" Mustapha ya ce "Ai mutumina ne bari ya sake zuwa, anya ba tattarawa zanyi idan anyi aure ba in koma gidanki" Rafi'ah ta ce "Zakawa Abba butulci kenan?" Ya saki murmushi yana jaan motar ya ce "Ai Abba ubane Hajiya karama, tinda nake ban ta6a ganin mutum me fahimta irin Alhaji ba, Allah ya biya shi da gidan Aljannah" a hankali ta ce "Ameen" sannan tayi picking call din Yusuf.
Few minutes ya kaisu gidan Mummy, bayan yayi parking ta masa sallama sannan ta tura gate din gidan ta shiga, a hankali ta sauke kanta ganin Jawad na zaune akan farar kujera dake kan balcony, sai da ta iso dai dai saitinsa ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau" daga haka ta shige ciki, Mami na zaune a parlorn da wata kawarta Hajiya Kareema, Rafi'ah ta dan rusuna ta gaishesu, Hajiya kareema ta amsa tana kallanta harta shige part din Mummy, a hankali ta zaro ido ta ce "Wannan yarinyar fa?" Mami ta ta6e baki ta ce "Diyar kanwarta ce, ni wallahi baso ma nake tana zuwamin gida ba, ciwan zuciya ne fa da ita" Hajiya Kareema ta zaro ido ta ce "Ciwan zuciya kuma? 'yar yarinyar nan dako 18 inaga bata cika ba" Mami ta ce "Atooh, ni dai cewa nayi ma ko HIV ne da ita suke boyewa, kiganta fa a bushe sai farar fata, gashi idan ciwan ya tashi saita fita a hayyacinta, batasan ma waye a kanta ba, ni tsorona kar tazo ta ya6a mana wani kalan cutan mu shiga uku, kinga wancen zuwanta ma Ikraam kwana tayi da zazza6i" Haj. Kareema dake sauraron Mami ta ce "Ai gara kuyi nesa da ita" Mami ta ce "To kinga, ina dalili zata dinga min zarya a gida kaalan ta cuci 'ya'yana ta ya6a musu ciwo".
Rafi'ah na zaune gefen Mummy tana matsa mata kafa ta ce "Doctor yace zaizo gaisheki, kuma wai zai kawo maki maganin ciwan kafa, inaga wanda kike shafawa zaki barshi ki gwada wannan" Mummy ta mike zaune ta ce "To Allah ya kawo shi, Yusuf akwai hankali da nutsuwa dan Allah Rafi'ah karki watsa masa kasa a ido, ya soki tsakani da Allah, ki zauna da matarsa zuciya daya, ba ruwanki da kishiyarki ce kiyi iya kokarinki a kanta, i know u are good in caring but pls ki dage kinji Mamana" tana murmushi ta daga kanta ta ce "Insha Allah Mummynah, mezan dafa miki?" Mummy ta ce "Yanzu dai tinda nayi wanka ki hadamin tea, amma lipton kawai da lemon tsami banda sugar" Rafi'ah ta ce "To bari naje" daga haka ta mike ta fito a parlorn Mumny, yanzu kam ba kowa zaune a parlorn Abi, ta wuce kitchen ta dauka mug ta dauraye sannan ta debi ruwan zafi a flask tasa liptopn, tana bude fridge Mami ta shigo, cikin sauri ta ce "Ke dakata" Rafi'ah ta dago kanta tana kallanta, Mami ta rufe fridge din ta ce "Ba kowa ake bari ya bude fridge dinba, ga cututtuka sunyi yawa a duniya, kowa saiya da6a hannunsa a handle din ya bude, irin haka ai sai a dauki cuta" gefe Rafi'ah ta koma tana kallan yadda take goge handle din Fridge din da towel, bayan ta gama ta gefar da towel din ta bude fridge din tana kallan Rafi'ah ta ce "Me zaki dauka?" A hankali ta ce "Leman tsami" Mami ta dauko leman tsami daya ta ajiye mata a kan drawer ta ce "Dama daga yau kina kiyayewa duk abinda kikasan in kin ta6a wani zai ta6a wajen ki barshi kawai, ga mai aiki ki sata tana miko miki" sauke kanta tayi cikin cool voice dinta ta ce "Mami nifa banda wani cutar da za'a dauka" wani kallan rashin mutunci Mami ta mata ta ce "A hakan, ki kalleki fa, to nidai bazance komai ba, amma dai ki kiyaye duk abinda na fada miki, ciwan zuciyar da akace idan mutum yana dashi ka ta6a guminsa kaima saika kwasa fa?" tana rife bakinta ta fice a kitchen din Rafi'ah
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment