Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya mika masa allurar Yusuf ya fara hadawa, Dr. Aryan ya kalleshi still smiling ya ce "Me yasa amma baka za6i field din cardiologist ba {Likitan Zuciya}, kodan ciwanka ma?" Yusuf yayi murmushi ya ce "Not interested, and self medication is not allowed" Dr ya ce "Kuma hakane, Allah ya sauwake, let me get the drugs for u, room dinta shine na kan corner, probably room 4" Yusuf ya ce "Ohk" daga haka yaci gaba da hada alluran. Ummi na fitowa a toilet ta kalli Rafi'ah data juya baya sannan ta dauki sallaya tayi hanyar fita, a hankali Rafi'ah ta ce "Ummi ina zakije" tsayawa Ummi tayi ta juyo tana kallanta ta ce "I want to pray outside Rafi'ah, ina nan corridor ko kinasan wani abu?" Girgiza kanta ta hauyi ta ce "No" daga haka ta limshe idanuwanta Ummi kuma ta fita.
Yusuf na gama hada alluran ya fito a office din Dr. Aryan sannan ya nufi room din da Rafi'ah take, da sallama ya shiga room din ya karasa kan gadon, tana kwance ta juya bayanta idanta a limshe, ya karasa dab da ita ya leka fuskarta, zaro ido ya danyi yana kallanta surprisingly enough, jin kamar motsi a bayanta yasa ta bude idanuwanta ta juyo a hankali, ta zaro ido silently ta ce "who i'm i seeing?" Zama yayi a gefenta ya ce "How are u now?" Ta ce "Much better, how did u know i'm here?" Ya danyi murmushi ya ce "My heart told me u are here" ta saki murmushi me kyau ta ce"It's impossible" ya ce "Bakisan idan zuciya na san ganin abu tana searching ta gano in yake ba?" Ta danyi dariyar daya bayyana with teeth dinta kafin ta ce "So ita ta kawo ka kenan?" Ya ce "Sure! Yaushe kika samu attack" ta fara wasa da fingers dinta ta ce "Immediately i entered my house, so i slept to rest, kawai kuma sai na farajin somehow heartburn" Yusuf dake kallanta tin tini ya ce "Allah ya kara maki lpy, are u sure u are taking ur drugs?" Ta daga masa kai ta ce "Ina sha" daga haka ya mike ya ce "I'm giving u an injection now" ta dan matso bakin gadon ta mika masa hannunta, daga hannun rigar yayi yana kallanta ya ce"Kina tsoron Allaura ne?" Ta danyi smiling ta ce "Not that much, amma fa kar kamin da zafi" yana ta dariya ya goge wajen da spirit sannan ya caka alluran, ya dinga kallan fuskarta to see her reaction, sai ma yaga batai wani raki ba, cotton wool ya saka mata a wajen sannan ya ce "Sorry, insha Allah da safe zan shigo na gaisheki" ta ce "Ohk, thank u" ya daga mata hannu ya nufi hanyar fita, kafin ya bude kofar Ummi ta bude ta shigo, ya danyi kasa da kansa with full of respect ya ce "Ina yini Umma" Ummi ta ce "Lafiya kalau" daga haka ya fita a dakin ita kuma ta shigo tana kallan Rafi'ah da har ta sake kwanciya ta ce "Magani aka baki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Injection" Ummi ta ce "Tashi kiyi sallah sai na hada maki tea ki sha" daga haka Ummi ta daga ta suka shiga toilet.
Da sallama Abba ya shigo parlorn yana kallan Anty Amina dake zaune, ta amsa masa sallamar ranta babu dadi sannan ta ce "Inata kiran wayarka baka picking" Abba ya zauna yana kallanta ya ce "The phone isn't with me, Rafi'ah ba lafiya anyi admitting dinta dazu, so gobe da safe kije ki duba ta" ta dan hade rai ta ce "Zanje gida fa, banje na gaishe da Umma ba, kuma dama akwai abinda tamin inaso kaja mata kunne" Abba ya dago yana kallanta ya ce "But nace maki tana asibiti ko? And goben make sure kinyi branching kin gaisheta" bata ce komai ba ta wuce kitchen ta dauko masa ruwa da cup ta ajiye a gabansa sannan ta koma daki ya bita da kallo ganin fuskarta kamar an kunna wuta. Washegari wajajen karfe goma Anty Amina tazo asibiti, duk ranta a 6ace yake dama ba dan Abba ba da ba zuwa za tayi ba, a hankali ta bude kofar ta shiga ko sallama babu, kan kujera ta zauna tana kallan Ummi ciki ciki ta ce "Ina kwana" Ummi dake hadawa Rafi'ah tea ta ce "Lafiya" Anty Amina ta ce "Ya mai jiki" Ummi ta ce "She's getting better", bude kofar toilet Rafi'ah tayi ta fito, towel kadai ne a jikinta ta karaso ta zauna akan gado tana turo baki, ganin hararan da Ummi ke mata yasa ta danyi kasa da murya ta ce "Good morning" Anty Amina ta mike tana kallan Ummi ta ce "Sai anjima" daga haka ta bude kofar ta fita. Verseline Rafi'ah ta shafa sannan tasa riga da wando ta koma kan gadon ta kwanta, tinaninta Ummi zatai mata fada amma kuma sai taga akasin haka, Ummi ta mika mata tiree me dauke da tea sai bread da chips a gefe ta ce "Tashi kici abinci" Mikewa Rafi'ah tayi ta kar6a tiree din sannan ta faracin abincin, few minutes ta gama ci ta ajiye sannan ta goge hannunta da tissue ta kwanta, waya Ummi ta mika mata ta ce "Ga Anty Halima, jiya ta kira kinyi bacci" kar6an wayar tayi ta kara a kunne ta ce "Mummy" from the orther side Mummy ta ce "Daughter how are u?" a hankali ta ce "Da sauki sosai" Mummy ta ce "To adai dinga kiyayewa, ni dama hankalina bai kwanta ba da kikace zaki raka waccen matar shopping, wallahi badan kar Muhammad yace ina shiga hurumin gidansa ba da babu inda zaki, muka sani ma ko ita ta jawo miki ciwan ya tashi" dariya Rafi'ah tayi ta ce "Sai bayan fa mun dawo Mummy" taja tsaki ta ce "Ke dai kibar mace Rafi'ah, mata akan kishi babu abinda basayi, bari dai na dawo kasar fuskarki ma ba zata gani ba" Rafi'ah ta ce "To Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" daga haka ta mikawa Ummi wayar. Bude kofar dakin akayi Yusuf ya shigo da sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, ya karaso ciki ya dan tsuguna ya ce "Ina kwana Umma" ta ce "Lafiya kalau" ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki, sai godiya" daga haka ya ajiye babban bakin ledan dake hannunsa ya dan kalli Rafi'ah data takure waje daya ya ce "How are u feeling?" A hankali ta sunkuyar da kanta ta ce "Da sauki" daga haka Yusuf ya juya ya ce "Allah ya sauwake, sai anjima" Ummi ta ce "To mungode Allah ya saka" daga haka ya fita ya rife kofar. Ummi ta kalli Rafi'ah ta ce "Who is he?" Dago kanta tayi ta ce "Doctor ne, shine ai wanda yamin injection jiya da daddare" Ummi bata sake cewa komai ba ta nemi waje ta zauna, Gwalalo ido Anty Khadija tayi ta ce "Yusuf nake gani a nan? Naga jiya yace yazo ya kar6i magani, in fact ai ba nan ake zuwa ba" ta wuce Nurse din da suke magana tare tabi bayan Yusuf, cikin few minutes ta karaso shi ta ce "Malam meya kawoka nan? Meyasa bakaje aiki ba?" Yusuf ya juyo yana kallanta ya ce "Nazo na duba abokina ne baiji dadi ba" Anty Khadija ta ce "To bari naje na ganshi, kaga ai zaiji dadi" daga haka ta nufi room din da Rafi'ah take, cikin sauri ya tare ta ya ce "Aiba dole saikin je ba, baima sanki bafa" Anty Khadija ta tsaya tana kallansa, ta karasa bakin kofar da sauri tasa hannunta akan handle din kofar zata bude Yusuf yayi saurin janye hannunta ya ce "Why won't u mind ur own business? Nace maki baima sanki ba".

*SHARIK HAYATI*

Dedicated to Maryam Shehu 🧡

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_15~16_

Kiran da CMD yayi wa Anty Khadija yasa ta juya tana hararan Yusuf ta bar wajen, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke hade da limshe ido sannan ya juya ya fita shima, direct parking space ya nufa ya shiga motarsa ya bar clinic din. Misalin karfe 5 na yamma akai discharging din su Rafi'ah, bayan an gama kai komai mota Abba ya shafa kanta looking into her eyes ya ce "Sannu Mamana, i hope u are not feeling any pain?" Ta daga masa kai tana gyara wuyan hijabinta ta ce "Ehh Abba" ya kalli Ummi dake nade bedsheet din kan gadon ya ce "Let's go Madam" ta ce "Ina fitowa yanzu, akwai sponge dinta a toilet da sauran abubuwa zan dauko" Abba ya kama hannun Rafi'ah suka fita a dakin, sai sannu yake mata har suka isa mota, ya zaunarta a back seat ya durkusa daidai fuskarta yana murmushi ya ce "What do u want to eat?" Ta mayar masa da murmushi ta ce "Nothing Abba" ya shafa fuskarta ya ce "In siya maki Shawarma, i know u like it" ta zaro ido tana dariya ta ce "Abba bayan a asibiti shawarma nayi ta ci, nidai a'a banaso" ya ce "To me kikeso?" Ta ce "Dan~wake, nasan Ummi zata dafamin idan muka koma" Abba ya zaro phone dinsa a aljihu ya ce "Let your stepmother cook, kinga muna zuwa idan kikai wanka sai kici" ita dai murmushi kawai tayi tana kallan Abbannata, yana fada mata bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa, Ummi na karasowa ta shiga front seat Abba ya zagaya mazauninsa yaja motar suka tafi. Cikin 15 minutes suka isa gida, Mustapha ya bude gate suka shigo, bayan Abba yayi parking ya fito yana kallan Rafi'ah dake kokarin bude kofa ya ce "Let me get the food for u" ta daga masa kai tana satan kallan Ummi, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, Ummi dake kallanta ta ce "Which food?" Rafi'ah ta rife kofar motar ta ce "Dama Abba ne yace wai tamin dan wake" Ummi ta ta6e baki ta nufi entrance din gidan, tana danna bell Abdul ya bude yana mata sannu da dawowa, daga haka ya wuce ta ya rungume Rafi'ah yana patting bayanta ya ce "Welcome home dear" ta shafa bayansa itama ta ce "Thank u bro" daga haka ya kama hannunta suka shiga ciki, suna shiga ta kwanta kan sofa tana limshe ido, Ummi ta ce "Get up Rafi'ah" ta dan turo baki ta ce "I just want to rest Ummi i'm not sleeping" Ummi ta ce "Won't u bath?" ta ce "Ba yanzu ba" Ummi ta dagata ta ce "Tashi kije kiyi wanka" tashi tayi dan ba yadda zatai ta wuce upstairs. Cikin fishi Abba ya shigo farlon ya zauna, kana kallansa kasan ransa a 6ace yake, kallan direction din inda yaji footsteps yayi, Ummi ta ajiye flask din hannunta akan dinning ta ce "What are u taking for dinner?" Abba ya girgiza kai ya ce "Ki hadawa Mamana abinda tace tana so, i think tea is ok for me" ba tare da Ummi ta kalleshi ba ta ce "Dama ban jira tamin ba ai, na riga na gama komai ruwa kawai nake jira ya tafasa" Abba ya juyo yana kallanta, ganin ta koma kitchen yasa ya mike ya nufi mosque danyin sallan magrib, ba jimawa Rafi'ah ta sauko cikin sleeping dress dinta iya knees, Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Have u pray?" Ta ce "Yes" Ummi ta ce "Abincin yana kan dinning, and after all ki tabbar kinyi combing gashinki" Rafi'ah ta shafa gashinta dake daure da ribbon tana kallan Ummi ta ce "Dan Allah kimin" Ummi ta dalla mata harara ba tare da tace komai ba. Anty Khadija ce zaune gaban Umma tana mata bayanin inda taga Yusuf, Umma ta numfasa ta ce "To ke a ganinki wajenwa yaje?" Anty Khadijah ta ta6e baki ta ce "Ina xan sani Umma, ai badan CMD ya kirani ba wallahi saina shiga dakin, kuma abin haushi dana gama aiki naje room din na samu ba kowa ciki" Umma na jijjiga kafarta dake kan kujera ta ce "Bari dai yazo, nasan maganinsa kuma" tana rife baki sai gashi ya shigo da sallama, duk cikinsu babu wanda ya amsa, Anty Khadija ta wani hade rai ta juya kai gefe, a hankali ya karaso cikin parlorn ya zauna kan sofa ya ce "Sannu da gida Umma" sai a sannan ta kalleshi ta ce "Ai da wucewarka kayi Yusuf, how many times kake diban kafafuwanka kabar gidan nan ba tare da kaje ka gaisheni ba, sai yanzu zaka wani zubamin jaar fuskarka kacemin sannu da gida, gadin gidan nakeyi?" Tinda ta fara magana kansa na kasa, sai da yaji ta dasa aya ya dan dago kansa ya ce "I'm sorry, almost sometimes banasan naje kina bacci ne na tasheki shiyasa, amma insha Allah bazan kara ba i apologize" Umma taci gaba da taunar chewing gum dinta ta ce "Inaso kuma ka fara hada lefe, saika turomin kudi ta account dina" Cikin sauri ya dago kansa yana kallanta ya ce "Lefe kuma Umma, ni ban tsayar da matar aure ba har yanzu" Umma ta dalla masa harara ta ce "Jiddan uban waye yace yana santa?" Yusuf ya gyara hulan kansa ya ce "It's before Umma, but ni yanzu bani da ra'ayin aurenta, sabida she isn't my type" Anty Khadija ta juyo tana kallansa ta ce "Kama samu zata aureka kenan? Kai har kanada hurumin za6ar matar aure, kaida kake fama da ciwon zuciya mutuwa ko yau ko gobe" nunata Yusuf yayi da yatsa ya ce "Enough Khadijah, don't let me show u d bad side of me, i Yusuf don't fight, but idan kika kara shiga rayuwata i swear to almighty Allah u will regret" daga haka ya kalli Umma ya ce "Saida safe Umma" Umma data hangame baki tana kallansa ta ce "Lalalala karka sake ka kirani da Umma dama, ai zaifi maka ka kirani da Fatima sunan da ubana ya rada min, Khadijan daka fada Aisha ka kira baka saya ba, shekara biyu ta baka a duniya idan baka sani ba yau ka rubuta ka ajiye, wawa kawai" ba tare daya juyo ba ya shige dakinsa ya rufo kofar, Anty Khadija da ranta ya gama 6aci ta mike zata nufi kofarsa Umma ta rikota ta ce "Sa ido kiga ikon Allah Dije, maza kwantar da hankalinki" cije baki Anty Khadija tayi ta koma ta zauna tana huci tana huhhuro hanci.

_Two week ltr_
Rafi'ah ce kwance a gefen Abba tana fada mishi abubuwan da zatai na saukarta, Abba ya dan kalleta yana shafa kanta ya ce "Bafa aure bane Mamana" ta dan turo baki cikin shagwa6a ta ce "But Abba ya kamata amin duk abinda nace gaskiya, nice fa first born dinka" yana murmushi ya ce "Kuma Mamana hakama, to kimin list din duk abinda kikeso" ta washe baki ta ce "Insha Allah, i will do so when i have time" Abba ya ce "Good, are u not celebrating world heart day today?" Ta mike zaune tana kallan Abbannata ta ce "I am Abba" ya ce "What have u done for the day?" Ta saki murmushi tana kallansa ta ce "Nayi addu'a Allah ya bani lafiya, dama duk wanda yake suffering da wannan ciwan, and i thank God for giving me such a loving parents like you, i love u Abbana" daga haka ta rungumeshi, Abba ya shafa bayanta gentle ya ce "Allah ya miki albarka ya kuma baki lafiya, but i think u have to go and celebrate there" ta zame jikinta a nashi ta ce "Zanje Abba, ina jiran Ummi ta dawo a office, because i can't leave you alone" Abba yaja hancinta yana dariya ya ce "Thank u mother, zo ki gayamin me ake a taron naku idan kunje" ta gyara zamanta ta ce "Firstly we introduce ourselves but not all, after then ana bada shawarwari akan yadda mutum zai kula da kansa sabida kar yana samun attack sosai, da kuma what medicine to take idan ka samu attack, after then u rushed for emergency, but the main abinda ake ta fada is heart rest, anaso a kullum mutum ya dinga nutsuwa ya daina sawa kansa damuwa da yawa" Abba ya bata side hug ya ce "Excellent, i hope kina bin duk abinda aka fada?" Ta daga masa kai ta ce "Sosai ma Abba, i really enjoyed this day in life that's 29 of September" Abba ya bata light kiss a forehead dinta ya ce "Proud to have u daughter, gobe insha Allah zan kaiku gidan Umma tinda yanzu kinji sauki sosai" Rafi'ah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Do u mean gidansu Anty Amina?" Ya ce "Of course, Ita kadai ce uwar data ragemana a yanzu" Rafi'ah ta kwantar da kanta akan shoulder dinsa ta ce "Allah ya jikan Baban Kaduna" Abba ya ce "Ameen" ta dago kuma tana kallan Abba ta ce "Wai Abba da Babanka da Umman Anty Amina waye babba?" Ya ce "Babana ne babba, sai Baba Mu'azu sai kuma Umma" Rafi'ah ta ce "Ohk, i was thinking itace Babba fa" Abba ya girgiza kai ya ce "No, just because she a female".
Karfe 3 da rabi Ummi ta shigo gidan, a tare suka amsa sallamarta, Rafi'ah ta mike tayi hugging dinta tana mata sannu da zuwa, Abba ya kalleta ya ce "U are welcome, but u look so tired Ummu Rafi'ah" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Na gaji kam, yau nayi lectures biyu two~two hours, after then mukai meeting sai to 3 muka fito" Abba ya mata sannu sannan ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Call Abdul for me, it's time for prayer" Rafi'ah ta nufi dakinsa tana fadin "Tin da muka dawo a school yau Abdul yake bacci, wallahi Ummi babanki ya zama kasa" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Be careful with me" dariya sosai take ta shige dakin Abdul ta hau kan gadon ta dinga mintsilinsa a baya tana ya tashi, da kyar ya mike ya shiga toilet sannan ta fito tana dariya ta ce "Ummi yau 29 of September, zanje taron heart day" Ummi ta ce "But not alone, Mustapha ya kaiki ya jiraki, sannan karki yarda magrib yayi maki a titi" ta ce "To insha Allah, in kawo maki abinci?" Ummi ta girgiza kai ta ce "I want to bath first" Rafi'ah ta nufi upstairs zuwa dakinta ta shiga wanka, ba dadewa ta fito shafa body lotion sannan tasa peach din doguwar riga, kanta ta fara combing tana ta aush tana 6ata rai kamar an sata dole, bayan ta gama ta saka scarf sannan ta yafa veil din rigar tayi simple make up, woooow!!! fans just say masha Allah here, the beauty can't be describe in one sentence, saina gama page dinma ban gama gaya muku irin kyau din datai ba loooool, turare masu kamshin gaske ta fesa sannan ta dauki flat shoe ta saka ta dauka small side bag ta jefa phone dinta da tissue a ciki sannan ta fita. Tana saukowa downstairs ta samu Ummi zaune nan inda ta barta, ta danyi murmushi ganin kallan da mahaifiyarta ke mata ta ce "Nasan nayi kyau ko Ummi?" Ummi ta maida hankalinta ga TV ta ce "Karki kai magrib Rafi'ah, fatan kuma kinyi sallan la'asar?" Ta ce "Insha Allah Ummi bazan kai magrib ba" Ummi ta ce "Sallan fa?" Ta ce "I'm on period" daga haka ta nufi kofa ta ce "Saina dawo" Ummi ta ce "Allah ya tsare" da Ameen ta amsa sannan ta fita ta kullo kofar, a parking lot ta samu Mustapha yana ta goge mota, yana kallanta ya washe baki ya bude mata back seat ya ce "Kaga turawan asali, Gaskiya Hajiya karama saurayinki yaji dadi, koda wannan kyan aka barshi yaci nasara, bare aje ga hankali, nutsuwa, kyauta, mutunci ga kuma kin fito gidan manya" Rafi'ah couldn't hold her laugh, ta dinga dariya kafin ta ce "Nikam naji dadina da wannan zancen" Mustapha ya ce "Allah kuwa gaskiya nake fada miki hajiya karama, sai wani walkiya kike kina haske ido" Ita dai dariya kawai take yaja motar suka fita a gidan.
15 minutes ya kaisu inda zasuje, bayan yayi parking Rafi'ah ta fito tana kallansa ta ce "Ka jirani anan, ba dadewa zanyi ba" ya duka cikin girmamawa ya ce "An gama kyakkyawa" daga haka ta juya tana dariya ta shiga cikin hall din, everywhere is silent sai muryar mutumin dake kan stage yana magana da loud speaker, Rafi'ah ta samu seat ta zauna ta maida hankalinta gun mai maganar, shawarwari sosai ya bayar ga masu fama da ciwan zuciya, kusan minti 10 yana bayani sannan yayi musu fatan alkhairi ya bayar da loud speaker, mutumin daya kar6i loud speaker ya danyi karin bayani sannan ya kira Doctor Yusuf akan shima ya fito ya bada tasa gudummawar a matsayinsa na likita kuma mai fama da wannan cuta, cikin light steps Yusuf ya karasa kan stage din ya kar6i loud speaker, shadda ce fara ajikinsa tsaha aiki sai hula baka da half shoes dinsa baki, daga hannunsa kuma kana iya hango wristwatch dinsa black colour sai zoben azurfa dake kyalli a yatsarsa ta tsakiya, cikin sweet voice dinsa yayi wa kowa sallama sannan ya fara bayani da english kamar haka "If you are opting to celebrate this day, it is important to try and be more attentive to your own heart health. There are a number of different ways that you can do this. This includes following a healthy diet, quitting alcohol, stopping smoking, and getting involved in physical exercises..." The hall is so quite harya gama bayaninsa in his good and meaningful English, bayan ya gama ya mikawa na gefensa loud speaker sannan ya sakko akan stage din, daga haka the audience break into rapturous applause. Saurin mayar da kanta gefe tayi ganin ya nufo inda take, bayan ya karaso yaja kujera ya zauna yana kallanta ya ce "Hy" ba tare data juyo ba ta ce "Why not salamu alaikum?" Yusuf ya shafa beard dinsa yana kallanta ya ce "I'm sorry, Assalamu alaikum" ta danyi murmushi ta ce "Wa'alaikumus salaam" ya ce "How are u?" Ta ce "I'm fine and u?" Ya ce "Alhamdulilah also" tayi shiru tana kallan mutum dake bayani akan stage, Yusuf ya ja chair dinsa kusan nata ya ce "Is that all for d greeting?" ta ce "What again? Naga ai mun gaisa" ya girgiza kai ya ce "Actually no, wannan karan shine na hudu da muka hadu, i think we have to introduce ourselves to each other" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "Ok, but u start" ya ce "Noo, u start" ta dan turo baki sannan ta ce "Ai kasan sunana" ya ce "Amma kuma na manta" ta dan harareshi ta ce "Ohk Sunana Yusuf Muhammad, I'm the first born of the family, kanina guda daya sunansa Abduljalal, my father works with CBN in Abuja, mother is a lecturer, i'm in SS2 now, ina hadda 5 a islamiyya, Abbana dan Kaduna, shi kadai iyayensa suka haifa, Ummi na kuma 'yar nan Kano ce, su biyu a familyn su ita da yayarta Anty Halima, she is living here in kano also, amma bata ta6a haihuwa ba, Matan Abbana guda biyu ne, so i think this should be my brief history" Yusuf ya saki murmushi yana kallanta ya ce "Nice to meet u Yusuf, hope u are ready to hear mine?" Ta daga masa kai tana murmushi, ya ce "As u know sunana Fatima Muhammad, but they do called me Rafi'ah, ni kadai iyayena suka haifa, sun rasu ta dalilin accident when i was 18 then,
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment