Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bita da kallon mamaki, kallan leman tsamin ta dinga yi kafin ta dauka ta wanke sannan ta dauki wuka ta yanka shi biyu, tana matsawa cikin tea din wasu hawaye masu zafi suka shiga sakko mata, yanzu har itane za'a ce bazata ta6a waje ba kar ta shafa musu cuta, to cutan me take dashi bayan ciwan zuciya? Shikuma tasan heredity ke kawoshi mostly, dan itama a familyn Abbanta ta gada, Jin kamar footsteps a bayanta yasa tayi saurin goge idanta ta dauka tea spoon, tana juyowa suka hada ido da Jawad, tayi saurin sauke kanta kasa tabi ta gefensa ta fita. Tana kaiwa Mummy tea din wayarta ya hau ringing, ta ciro a jaka sannan ta daga call din, "Ok" kawai tace sannan ta kalli Mummy ta ce "Yazo" Mumny ta ce "To ki shigo dashi parlorn Abi ba sai ya shigo ciki ba" ta ce "To" sannan ta zura hijabinta ta fita, a bakin gate ta sameshi ya jinginu da motarsa hannunsa rike da key, yaci manyan kaya yayi kyau sosai, ta sauke kanta kasa ta ce "U are welcome" ya ce "Thank u Baby, what's wrong with ur eyes?" Ta ce "Daxu abu ya fadamin" ya ce "Ayyah sorry, hope ya fita?" Ta daga masa kai, ya ce "Alhamdulilah", ta dan kalleshi ta ce "Ka shigo ku gaisa" ya ce "Ohk" daga haka ya bude mota ya ciro carton din Malt da leda cike da Apple, yana shigowa gate man ya kar6eshi, da sallama suka shiga parlorn, gate man ya ajiye abubuwan sannan ya fita Yusuf ya zauna kaan carpet yana kallan hoton Jawad dake manne a wall, ba jimawa Mummy ta fito Rafi'ah na biye da ita, tana murmushi ta zauna, ya sauke kansa kasa ya ce "Ina yini Mummy?" Ta ce "Lafiya Yusuf ya aiki kuma" ya ce "Alhamdulillah, ya karfin jiki?" Ta ce "Jiki yayi sauki, Allah ya saka da alkhairi" a hankali ya ce "Ameen" sannan ya ciro maganin ciwon kafan ya ajiye mata a gefe. Sun dan jima kafin Mummy ta shiga ciki, Rafi'ah ta zagayo ta zauna kusa dashi ta ce "Ya Anty Jiddah fa?" ya ce "Tana nan lafiya, yaushe zamuje wajen Ammi ne, ta damu kije mata" a hankali tayi murmushi ta ce "Ko ranar Monday inna dawo a school" ya ce "To Allah ya kaimu" mikewa tayi ta nufi fridge din parlor ta bude ta dauko mirinder da coke sannan ta dora akan tray ta dauki glass cup, tana juyawa Mami ta fito daga part dinta, ta dinga kallanta kafin ta ce "Ke wai wacce irin dabbar yarinya ce, ba ance miki karki sake ta6a mana fridge ba" still tayi waje daya jikinta na rawa, Mami ta kar6a tray din hannunta ta ajiye akan dinning ta ce "Haba, mace kamar mayya, aiko maye yana gane magana wani lokaci" Yusuf dai na zaune yana bin Mami da kallo, Rafi'ah ta koma ta zauna a hankali duk jikinya a mace, ganin sun hada ido da Mami ya ce "Ina yini" ta dalla masa harara, Yusuf ya mike yana kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "Dear, i'm going" daga haka ya nufi kofa, kallan Rafi'ah Mami tayi ta ce "Dama karuwancin naki ba iya gidanku ya tsaya ba harda gidan mutane?" Caak Yusuf ya tsaya jin abinda ta fada, nan da nan hawaye suka shiga sakkowa a idan Rafi'ah, Yusuf ya juyo a hankali yana kallan Mami ya ce "Mama niba mazinaci bane, kuma abinda kika fada saam bai dace ba, saboda baki da shaidar abinda bakinki ya furta" Mami ta ta6e baki ta ce "Idan kai ba mazinaci bane ai ita kowa yasan nata, to tinda tare na ganku ai zance duk kanwar ja ce" Yusuf ya dinga kallan Mami with much surprise ya ce "Mama!!!", bude kofar akai Jawad yayi sallama, Mami ta saki kuka ta zauna akan kujerar dinning, Jawad ya karasa kusanta da sauri ya riko hannunta ya ce "What's wrong Mami?" Ta dago fuskarta hawaye sha6e sha6e ta ce "Wallahi wannan bawan Allan ne Jawad ya cimun mutunci, daga gani ma shaye~shaye yake, saboda kawai nace bako baka gaisuwa ne" nan da nan Jawad ya mike ya daga hannu yayi kaan Yusuf, Rafi'ah ta fashe da kuka, dai dai nan Mummy ta fito a part dinta da sauri har kamar zata fadi...

[7/29, 2:12 PM] My Imaan: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_32_

Rike hannunsa Yusuf yayi yana kallan eyeball dinsa da sukai jaa ya ce "How there you?" Jawad ya kwace hannunsa ya cakumi wuyansa yana huci, salati Mummy ta saki tana kallansu ta ce "Na shiga uku, Jawad me nake gani haka?" ganin Mummy yasa Yusuf baiyi attempting ta6a shi ba, Mummy ta janye Jawad gefe tana kallansa ta ce "Maiya faru ne Ahmad?" Juyawa yayi ransa a 6ace ya shige dakinsa, dan shima indai a gaban Mummy ne he can't do anything, Mummy ta kalli Rafi'ah dake kuka sosai sannan ta ce "Ikon Allah, me yake faruwa ne haka?" ganin hankalinta ya tashi yasa Yusuf ya gyara wuyan rigarsa yana kallanta with a little smile ya ce "Ba komai fa Mummy, Allah ya kara sauki" daga haka ya juya ya bude kofar parlorn ya fita. Mami ta dago kanta tana dariya kasa~kasa ta shige part dinta Mummy ta bita da kallo, saam ita kanta ya kulle, she is totally disturb to know what's happening, kama hannun Rafi'ah tayi suka shiga part dinta, Mummy ta ce "Ki rifemin baki ki fadamin meya faru?" Goge hawayenta ta shigayi sannan ta bata labarin abinda ya faru tin zuwanta kitchen da zata hada tea har zuwa karshe, Mummy da ranta ya gama 6aci ta dauko wayarta tayi dailing number Abi.
duk ilahirin gidan na zaune parlor kowa ransa ba dadi musamman Jawad da har yanzu idanuwansa basu dawo dai dai ba, Mummy ce ta fito Rafi'ah na biye da ita a baya, caan gefe ta samu ta zauna kanta a kasa, Mummy ta zauna gefen Mami dake taunar chewing gum tana girgiza kafa, Abi yayi gyaran murya yana kallan Rafi'ah ya ce "Repeat what u just told me Fatima" a hankali ta dafe kirjinta jin zuciyarta na bugawa, Abi ya ce "Talk now" a hankali ta kara fadan duk abinda ya faru kamar yadda ta fada masa a farko, Jawad ya dago with shock yana kallanta sanda tace Mami tace mata karuwa, bayan tayi shiru ta dinga goge hawayen idanta da veil dinta, Abi ya juyo yana kallan Mami data juya masa keya ya ce "Amma kinsan girmanki ya fadi a gaban 'ya'yanki ko Hadiza?" kin juyowa ta kalleshi tayi, Abi ya ce "Ai duniya ce watana u will regret all this, kin kira 'yar mutane da karuwa, kin tafka abin kunya a gaban 'ya'yanki wanda nasan har abada wancen yaro bazai miki kallan uwa me daraja ba, you hurt me today Hadiza, saboda haka kije gida saina nemeki" daga ita har 'ya'yanta suka kalli Abi with shock, Jawad kadai ne kansa na kasa ya kasa cewa komai, Mami ta mike kamar zata tashi sama ta shige part dinta, Abi ya girgiza kai ya ce "Allah ya kyauta" daga haka ya mike yana kallan Mummy ya ce "Zan fita" ta ce "Allah ya kiyaye" mikewa Sadeeq yayi ya ce "Bari in sauke ka" daga haka ya bi bayansa suka fita, mikewa Jawad yayi ya wuce dakinsa, Ikraam dai na zaune banda kuka ba abinda take, caan ta mike ta wuce part dinsu, Rafi'ah kam duk jikinta yayi sanyi, musamman hukuncin da Abi ya dauka, idan ta tuna a sanadinta ne sai ta fashe da kuka, bayan awa daya Mami ta fito da katoton akwatinta Ikraam na biye da ita suka fita a parlorn. Ranar dai haka suka kwana duk gidan shiru, hatta ita Mummy jikinta yayi sanyi, ballantana Jawad, kwana yayi baiyi bacci ba yana tina abinda Rafi'ah ta fada, kuma duk ba wanda yaji bazai faru ba, yasan Maminsa zata iya aikata abinda yafi haka ma, ya dafe kansa yana addu'ah ciki ciki, da asuba yayi alwala ya wuce masallaci, tare suka dawo da Abi amma ko magana basuyi ba, ko daya gaisheshi ciki ciki ya amsa, hakan ya tabbatar masa Abi yana fishi dashi sosai. Tinda ya dawo dakinsa ya kwanta yake juyi, gaba daya ya rasa
abinda yake masa dadi, sai kusan karfe 8 sannan bacci ya daukeshi. Zaune take akan kujera duk ta takure waje daya, Mummy dake kallanta ta ce "Ki tashi kiyi breakfast" girgiza kanta tayi ta ce "I'm going home, banasan cin komai" Mummy data lura duk a tsorace take ta ce "To shikkenan, ga 500 kan kujera ki hau cab" a hankali ta mike ta dauka kudin, ta wuce daki ta dauko jakar kayanta sannan ta fito ta ce "Sai anjima" Mummy ta ce "Ki gaishe su" tana fitowa a parlorn ta sami Sadeeq zaune akan kujera yana waya da Mami, ta sauke kanta kasa ta ce "Ina kwana" ya amsa mata sannan ta bude kofar parlorn ta fita, a tsorace ta dinga tafiya a compound din harta iso bakin gate ta bude kofa, komawa baya tayi da sauri ganin Jawad tsaye a wajen, ta juya zata koma ciki ya kamo hannunta, kuka ta farayi tana kallan idansa da suka kumbura alamar dai yayi kuka, cikin kuka ta ce "Dan Allah kayi hakuri Ya Jawad, i caused all this, ni bansan haka zai faru ba da wallahi bazan fadi gaskiya ba" limshe idanuwansa yayi kafin ya budesu a kanta ya ce "Keep quite now" tayi shiru tana goge hawayen idanta, ya ce "U caused nothing, dama haka Allah ya tsara koda bakya nan may b zata tafi, And i don't want to see that guy in this house again, let him be on his own, ya kuma kyaleki idan kina gidan nan" a hankali ta daga masa kai, ya ce "Ina zakije?" Ta ce "Zan tafi gida ne" ya ce "Let me drop u" daga haka ya sake hannunta ya bude motarsa dake waje, ajiyar zuciya ta sauke dan a tinaninta dukanta zaiyi da farko, ta bude front seat ta shiga yaja motar suka tafi. Suna hawa main road ya ce "How old are u?" A hankali ta juyo ta kalleshi, shiba kallanta yake ba sai driving kawai yake idansa akan titi, yana juyowa tayi saurin juyawa ta ce "17" baice kara cewa komai ba har suka iso gida, yayi parking yana kallan wayarsa dake haske, ganin Mami ke kira yasa ya rage volume ya kifa phone din, ta sauko a motar ta ce "Nagode" daga haka ta wuce cikin gida, sai daya ga ta shige sannan yaja motarsa yayi gaba. Tana shiga cikin gida ta ajiye jakar a parlor ta gaishe da Ummi sannan ta wuce kitchen ta hada tea ta dawo ta zauna, bayan ta gama ta dauki jakarta ta haura upstairs zuwa dakinta.
Karfe 2 Jawad ya tashi daga nauyayyen baccin daya daukeshi, wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya, sunyi masa kyau sosai, ya dauki key din motarsa da phone dinsa ya fito a dakin, yana bude kofar parlorn suka ci karo da Abi, yayi saurin ja baya yana shafa gashin kansa ya ce "Sannu da dawowa Abi" Abi ya zauna kan sofa ya ce "Come back here" Jawad ya koma ya zauna akan carpet Abi dake kallansa ya ce "Where are u heading to?" Silently ya ce "Gidan kawu" Abi ya ce "Ohk, and i'm sorry with the decision i take, gara taje gida ta huta kafin ta dawo" a hankali ya ce "Toh" Abi ya ce "Ka kuma rage wannan gashin naka, ko kunya bakaji a cikin bokanka da wannan gashin" ya dan shafa kansa yana murmushi ya ce "Insha Allah" daga haka ya mike ya fice a parlorn, parking lot ya nufa ya bude motarsa ya shiga sannan yayi horn aka bude gate ya fita. Minti 20 ne ya kaishi gidan kanin baban Mami, yayi parking a waje sannan ya fito ya shiga gidan, ba kowa a compound din gidan sai mota kwaya biyu, knocking kofar ya farayi a hankali yana kallan flowers, bayan an bude ya wuce ciki ba tare daya amsa gaisuwar da me aiki ke masa ba, dakin dake farko ya bude, Ikram ce ciki sai Muhibba, kafin su gaishe shi ya ce "Ina Mami" Ikram ta ce "Tana dakin Mama, ina yini" ya ce "Lafiya" daga haka ya fice a dakin ya shiga dayan, Mami ce kadai a dakin tana waya da Haj. Kareema, ganin Jawad yasa tayi hanging wayar tana masa wani kallo, ya zauna a bakin gado ya ce "Ina yini" a fusace ta ce "Ban wuni ba, aida ubanka yace na taho gida bakai wani abu a kai ba, ko ayi hakuri baka ce ba, sannan nayi ta kiran wayarka baka dauka ba, tin sassafe Sadeeq yazo ya gaisheni amma kai da yake asara ta maka yawa sai yanzu kazo karfe 3 saura" limshe idanuwansa yayi yana jin haushin yadda take daga murya duk ilahirin gidan suna ji, ya sauke murya caan kasa ya ce "Kiyi hakuri, i don't mean to hurt u, bacci ne ya daukeni saboda jiya banyi ba" ta wani hade rai ta ce "Uban me ya hanaka baccin?" Juyowa yayi yana kallanta kafin ya ce "Abinda naji" ta ce "Bangane ba" ya ce "Abinda Fatima ta fadawa Abi, Mami this isn't fair, kinsa na aikata abin kunya kuma..." a mungun fusace ta ce "To ka dokeni Ahmad, yimin shegen duka sannan ka min fadan, ai fada kadai ba zai maka maganina ba" Haj. Fatima matar Kawu ce ta shigo dakin da sauri, tana kallan Mami ta ce "Lafiya Hadeeza kike ta ihu haka?" Cikin 6acin rai ta ce "Wannan wawan ne mana yakesan 6atasan rai bayan wanda ubansa yamin" Haj. Fatima ta ce "Kiyi hakuri dan Allah ki daina fada haka, da kannensa fa a gida" Mami ta nuna masa hanyar waje ta ce "Get out now" shi dai kansa na kasa yana zaune, Haj. Fatima ta ce "Jawad jeka kawai anjima ka dawo" tashi yayi a hankali ya nufi kofa Mami taja tsaki ta ce "Sai anyi magana yayi ta sauke kai kamar baya magana, nan kuwa idan ya fada miki magana sai kinyi mamakinsa" shidai bai juyo ba ya fice a dakin ya rufo mata kofar.
Da yamma Rafi'ah na zaune akan dinning wayarta ya hau ringing, murmushi tayi ganin Yusuf ne tayi picking call din hade da sallama, ya ce "How are u Baby?" Ta ce "I'm fine" ya ce "Zaki iya fitowa ina waje" ta ce "Ohk ina zuwa" hanging call din tayi ta mike ta haura sama, dakinta ta shiga ta saka Himar dinta sannan ta wuce dakin Ummi, a hankali ta bude dakin ta shiga, Ummi ta ce "What's it?" ta sauke kanta kasa ta ce "Doctor ne ya kirani wai yana waje" Ummi taci gaba da abinda take ta ce "Don't stay long" ta ce "Ok" sannan ta fita a dakin, wayarta ta dauka akan dinning bayan ta sakko sannan ta fita a parlorn, yana tsaye kamar yadda ya saba suna hira da Mustapha, ya sakar mata murmushi ya ce "Kinyi kyau" Mustapha ya shige ciki yana cewa "Ai oga taka ce insha Allah" murmushi Rafi'ah tayi ta ce "Kaima kayi kyau, ya shiye shirye?" ya ce "Alhamdulilah, how was yesterday nasan kinyi kuka sosai ko?" Ta sauke kanta tana wasa da fingers dinta ta ce "Not much" ya ce "To ki dinga hakuri, ita rayuwa haka take, u don't bother much" ta ce "Hakane" ya ce "And shi kuma wannan yaran ya fita a rayuwana, dan wallahi idan ya kureni he won't feel good, na tsane shi i really hate him with passion saboda haka let him not come into my life again" kallansa kawai Rafi'ah take jin yace yaro, tasan dai idan Jawad bai girmeshi ba to there are age mates, hancinta yaja ya ce "I luv u" tayi saurin janye fuskarta tana murmushi ta ce "Same to u" ya ce "Dama Invitation card na kawo wa Abba na daurin aure, dazu dana kira na gaishe shi yace he will come on Thursday" kar6a card din tayi tana jujjuya shi ta ce "Alright" ya ce "I'm going, zanje caan gidana Umma na kirana" ta ce "Safe, Allah ya kiyaye hanya" ya ce "Ameen" ya bude motarsa yana kallanta ya ce "Ya jikin Mummy?" Yana rife bakinsa Jawad yayi parking a gefensa, har lokacin idansa basu dawo dai dai, gashi Mami ta kuma 6ata masa rai, dauke kanta tayi akansa ta kalli Yusuf ta ce "Taji sauki ma sosai" ya ce "Haka akeso, sai munyi waya" daga haka ya shige motarsa ya kunna ya fara reverse, fitowa Jawad yayi yana kallan Rafi'ah ya ce "Ummi na ciki?" shiru tayi ganin Yusuf yayi parking ya nufo inda suke tsaye yana yiwa Jawad wani shegen kallo...

_08103810398_
[7/30, 9:03 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_33_

Gently Yusuf ya karasa inda suke ya kalli Rafi'ah sannan ya ce "Go inside" ta juya duk jikinta a sanyaye ta shige gate, dan murmushi Jawad yayi bai ko kalli inda yake ba yabi bayan Rafi'ah, tana nan tsaye bakin gate tana lekawa to see if they will quarrel, saurin ja da baya tayi ganin Jawad ya turo gate din, ta sunkuyar da kanta ta fara kame~kame ta ce "I'm...looking for my....for my earring...it just fall down here" durkusawa tayi ta dinga bin interlock din da ido, Jawad ya dinga kallanta kafin a hankali ya ce "Fatima" dagowa tayi ta kalleshi ya ce "U are just 17 and i'm 35 so don't think zaki iya min karya ban gane ba, and don't forget my profession, daga yadda mutum yayi magana i know if he's lying, kawai kice kina kallan wancen mutumin ne" dan zaro ido tayi ta ce "Laa nifa ba shi nake kalla ba, na leka ne naga ko zaka shigo" murmushi Jawad yayi yana kallanta ya ce "This is strictly no, bani card din hannunki nagani" mika masa tayi sannan ta sauke kanta kasa tana ta wasa da zoben hannunta, sai daya karatanta tass sannan ya mika mata ya ce "And u are happy ko?" Ta girgiza kai sai kuma ta ce "That's God plan" Jawad ya dinga kallan pink lips dinta dake motsi a hankali lokacin da take magana, shafa kansa yayi ya dauke idansa a kanta ya ce "Haka dai kika za6awa kanki, but ai there's a way out, u can leave him and find another love" noke kafada tayi ta dan turo baki kafin ta ce "No, ni dai a'a" Jawad ya dinga kallanta with passion, juyawa yayi ya nufi cikin gida tabishi da ido kafin ta kara turo baki tabi bayansa. Ummi na zaune a parlor Abdul yayi pillow da cinyarta Jawad ya shigo da sallama, Ummi ta daga Abdul a jikinta tana murmushi ta ce "Barrister" murmushi shima yayi ya zauna akan carpet, dai dai lokacin Rafi'ah ta shigo da card a hannunta ta wuce upstairs, ya sauke idanuwansa daga kallan Rafi'ah ya ce "Ina Yini Ummi" ta ce "Lafiya kalau Ahmad, how is work? kwana biyu baka leko mu ba" shafa kansa yayi yana murmushi ya ce "Aikine yanzu yakemin yawa" ta ce "To Allah ya taimaka ya bada sa'a" ya ce "Ameen", kwalawa Rafi'ah kira Ummi ta shiga yi, bayan ta sauko ta tsaya bayan kujera ta ce "I'm here" Ummi ta ce "Ki kawowa Ahmad abinci" juyawa tayi zata nufi kitchen Jawad ya mike ya ce "Zan wuce ne dama" Ummi ta ce "Abincin fa?" Ya ce "Fitowana naci abinci, and na samu call daga court" Ummi ta ce "To nagode Jawad, Allah ya saka maka da alkhairi, kana da kokarin zumunci keep it up" murmushi yayi ya fita a parlorn byan ya sake mata sallama.
Shirye~shirye Umma keta yi baji ba gani, kai kace Anty Khadija ce me yin auren, komai ta gani tace za'a raba a biki, musamman da yanzu biki ya rage saura kwana biyu, sai dai duk abinda take siya aljihun Yusuf ne yake yin kuka, kuma ko kadan baya nuna gajiyawarsa dan dai su rabu lafiya. Sai ranar Friday su Abba suka dawo Kano saboda aiki daya masa yawa, Mustapha ne ya daukosu a airport, bayan sun dawo yayi parking ya ciro karamar jakar Abba a boot ya nufi cikin gida, Anty Amina ta wuce apartment dinta, da sauri Ikleemah ta fito ta rungumeta ta ce "Anty gidanma ba wani datti fa, harna sallami me aikin ta tafi" Anty Amina ta ce "Uwarki bata zo ba ko?" Ikleemah ta ce "Sai anjima tace zata zo" daga haka Anty Amina ta kama hannunta suka wuce ciki. Rike da hannun Abdul Abba ya shigo parlor, Ummi dake kitchen ta fito tana murmushi ta ce "Ur welcome" ya ce "Thank u Madam, how is everyone?" Ta ce "All fine, sannu da hanya" daga haka ta daga masa cushion din kan kujera ya zauna, kan Abdul ya shafa ya ce "Babana ka fara tara gashi ko?" Abdul ya danyi murmushi ya ce "No, zanyi aski anjima" fitowa Rafi'ah tayi a kitchen ta dan zauna akan carpet ta ce "Sannu da dawowa Abba" hannunsa ya mika mata ta saka nata a ciki sannan ya ce "Come close Mamana i missed u, how are u?" Kanta na kasa sosai ta ce "Fine Abba, ya hanya?" Ya ce "Alhamdulilah" daga haka ya bata side hug, duk sai taji kunya sosai, bayan ya saketa ta koma gefe ta ce "Abba baka siyo mana Apple din nan ba" ya ce "Na siyo mamana, ki duba boot inaga basu fito dashi ba" har zata fita Abba ya ce "Come back, let ur brother go" daga haka ta dawo Abdul ya mike ya fita, kiran da Ummi ke mata yasa ta fasa zama ta wuce kitchen. Ummi ta mika mata carrot ta ce "Ki gyara sai ki hada komai ki kai dinning, after then sai ki daura wancen naman" turo baki tayi dan tin safe take aiki a gidan nan, duk ta gyara ko ina tayi mopping sama da kasa, kafin ta gyara kitchen suka dora abinci, Ummi dake hararanta ta ce "Idan ba zakiyi ba u let me know, ai ba yau na saba yin komai da kaina ba" daga haka ta fice a kitchen din, turo baki ta karayi ta dauko chopping board ta fara yayyanka carrot din, ta kusan gamawa kenan mistakenly ta yanka yatsanta na hagu, ta saki kara sosai ta jefar da knife din a kasa, da sauri Ummi ta shigo tana kallanta ta ce "What's that shouting for Rafi'ah?" Rafi'ah ta fashe da kuka tana nuna mata yatsanta, Ummi ta dinga kallan yatsan da yankan ma is not that deep, jinin ma dan kadan ne ta fito, wukar ta dauka ta ci gaba da gyara carrot din bata kulata ba, Abba ne ya shigo rike da newspaper ya ce "Ya akai ne?" Ummi ta ce "Ba komai, ta tsorita ne" Abba ya juya ya ce "Alright, be careful Mamana" harara Ummi ta maka mata ta ce "Fita min a kitchen"

Please Login or Register in order to submit comment