Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

akan dinning idan zaka ci" ya mike yana kallan Khairiyya ya ce "Muje muci tare, Mami Daddy baya nan ne?" Ta ce "Bai dawo ba, we are expecting him on Wednesday by God grace" ya ce "Allah ya dawo dashi lafiya, when will u visit me Zarah?" Ya karashe magana yana kallan Khairiyya dake zuba musu mango juice cikin glass cup, ta dago tana kallansa ta ce "Idan an bamu mid~term break zanzo Yaya" ya ce "Ohk, what was ur last position?" Ta ce "2nd, kuma Yaya Sameer yace zai siyamin tablet but har yau shiru" Yusuf yayi murmushi ya ce "May b kin masa laifi ne?" Ta ce "Noo, i just wake him up the other day, wai ashe he's having headache, shine yaji haushina" ya ce "To kinga? Ke kika jawa kanki ai".
Bayan sun gama cin abinci ta kama hannunsa ta ce "Yaya mu tafi ko?" ya ce "Not yet Amminah, we still have much time, sai da la'asar zamu fita" daga haka ya bata side hug suka zauna suna kallan TV.
Karfe 12 da rabi Mustapha ya dauko su Rafi'ah a islamiyya, suna shigowa gida ta ajiye side bag dinta tana kallan Ummi ta ce "I'm so tired Umminah" Ummi ta ce "Go take a shower, i think u will feel better" ta mike a hankali ta ce "Abba fa?" Ummi ta ce "Yana apartment din Antyn ku" turo baki tayi ta wuce upstairs, Tana shiga daki ta lankaye bag din sannan ta jawo towel ta shiga cire kayanta dan yin wanka, minti 10 ta dauka a toilet kafin ta fito, ta zauna gaban mirror ta fara combing kanta sannan ta shafa lotion ta mike ta saka kaya, riga da skirt na atampa tasa, dinkin ya zauna mata das das, ta daura dankwalinta sannan ta sauko downstairs, direct kan dinning ta nufa ta fara cin abinci, after all ta dawo gefen Ummi tana taya ta recording marks.
karfe 2 da rabi Abba ya shigo parlon da sallama, Rafi'ah ta dago kanta tana amsa sallamarsa ta ce "You're welcome Abba" ya ce "Zo nan Rafi'ah" ta dan zaro ido tana kallansa, dan duk sanda ya kirata haka tasan akwai babban laifin data aikata, ta karaso gefensa a hankali ta ce "Gani" ya ce "Sit down" ta zauna kanta a kasa, sai lokacin Ummi ta dago kanta ta kallesu, Abba ya ajiye wayarsa ya ce "What did i told u in the morning before u left for Islamiyya?" Taso tayi pretending like she didn't recall amma ganin reaction din Abban nata yasa ta ce "Kace naje na gaishe da Anty" ya ce "And why didn't u go?" Ta kara sauke kanta kasa tana wasa da azurfan hannunta, ya ce "I'm i not talking to u" a hankali ta ce "Nothing" ya ce "Saboda ban isa na sakaki ba ko kuma bata kai kije ki gaisheta ba" girgiza masa kai ta hauyi a hankali, ya ce "To tashi kije ki gaisheta, and never let this kind of foolishness happens again, i can't tolerate, idan kin dawo kizo kuma ki dauka veil dinki zaki rakata shopping" kamar zatai kuka ta mike a hankali ta fita a parlor, kamar me counting steps dinta take tafiya harta isa apartment din, ta murda handle din sannan ta shiga parlorn da sallama, ko amsa sallamarta batai ba ballantana ta amsa gaisuwar data mata, Rafi'ah ta juya ta fice a parlorn, haushi duk ya cikata, tana shiga parlornsu Abba ya ce "Kije kuma ki rakata shopping now" ta kara turo baki ta wuce upstairs tana bubbuga kafa, tana shiga dakinta ta fashe da kuka ta jawo wayarta tayi dialing phone din Mummy, bugu biyu ta dauka tana "Yau an tinoni kenan?" Jin kamar kuka yasa ta ce "Subhanallah, are u crying Rafi'ah?" Cikin kuka ta ce "Koba Anty Amina bace" Mummy ta ce "Menene kuma ya faru? Tazo ne?" Hawayenta ta share kafin ta ce "Jiya sunzo da Abba, kinga yanzu ya gama min fada wai banje na gaisheta ba, danaje kuma na gaisheta tana kallona taki amsawa, wai kuma Abba yace saina rakata shopping, gaskiya ni i can't, i so much dislike her Mummy, kinga fa ita bata zo ta gaishe da Umminmu ba amma Abba yake tilastamu mugaisheta" Anty Halima ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Wipe your tears, ina dalili zaki dinga kuka akan kishiyar uwarki, ki barta caan da mungun halinta, tinda Abbanki ne yayi magana ki rakata, amma idan ta miki ki mata kema, ban yarda ki raga mata ba wallahi, duk wannan asarancin na Zainab ne, ita dan fadan nan ma na mata bata iya ba, wallahi ban yarda kiyo halinta ba, ina dalili keda gidan ubanki a dinga takura miki" Rafi'ah ta turo baki ta ce "Ni banma san dalilin da zaisa na raka taba" Mummy ta ce "Makirci ne irinna mata, ki dai kula da duk wani takunta, aniyarta ta bita caan, kuma koda wasa karki daukar mata kaya ai ke ba 'yar aikinta bace, idan na dawo ma kika koma gidana kikai auranki ina zata ganki" Rafi'ah tayi saurin hanging call din ta tashi ta fito a dakin, da Ummi taci karo zata shiga dakinta, ta 6ata rai ta ce "Ummi kinji wai sai in rakata shopping" Ummi ta ce "And so? Wani abu ne zai ragu ajikinki ko me? wallahi da nasan bakije kin gaisheta ba da sai ranki ya 6aci a gidan nan, ina zaman zamana kin jawomin magana yana fadin ninake kyaleki, saime idan kin gaisheta" ta ce "Ummi to ita gaisheki take?" Ummi ta daka mata tsawa ta ce "Kindly disappear here, wallahi zan 6ata maki rai Rafi'ah" barin wajen tayi hawaye na zuba mata. Bayan ta sauko ta wuce Abba dake zaune a parlor ta fita compound din gidan, ta karasa parking lot ta jingina da mota ta wani hade rai. Kusan ten minutes tana tsaye kafin ta fito walking slowly tana ta chewing gum, an sha kwalliya kai kace gidan biki zata, Mustpha yayi saurin bude mata back seat jikinsa na rawa, bayan ta shiga ta ce masa "Ka cewa wannan yarinyar ubanta baice mata tare zamu tafi bane?" Rafi'ah ta dago kanta da sauri jin abinda tace, ta kara folding hannayenta tana tsaye jikin motar Abba, Mustapha ya karasa kusanta a hankali ya ce "Hajiya karama ke ake jira" ta dalla masa harara ta juya kai gefe, Abba ta hango ya fito da waya kare a kunnensa yana answering call, hakan yasa tayi saurin shiga motar tana ta turo baki Mustapha yaja suka wuce.
Tafiyar minti 20 sukayi kafin suka iso shopright, bayan Mustapha yayi parking suka sauka suka karasa ciki, ita dai Rafi'ah sai binta take tana dalla mata harara ta gefen ido, almost 1 hour suna zagaye amma abu guda 4 kawai ta dauka, kuma ita da kanta ta rike basket dinta, ta dan saci kallan Rafi'ah ta ta6e baki ciki ciki ta ce "Sai kin gaji da yawo yau munafuka" suna tsaye a wani waje wani dan saurayi yazo wucewa, ya danyi murmushi kafin ya ce "Excuse pls Madam" Anty Amina ta matsa tana binsa kallo ya shige, juyowa yayi ya kalli Rafi'ah sannan ya kara kallanta, hade ran da tayi yasa ya juya ya tafi abinsa dan da niyyarsa ya mata magana.
suna tsaye awajen sukaji ance "Fatima" Rafi'ah tayi saurin juyowa tana murmushi, wara manyan idanuwanta tayi ta ce "Doctor" yana rike da hannun Khairiyya ya karasa gabanta ya ce "How are u?" Ta ce "Fine, is this your sister?" Ya danyi murmushi yana kallan Khairiyya ya ce "Yes, she is" Khairiyya dake rike da Baby doll dinta ta ce "Good Afternoon" Rafi'ah ta shafa kanta ta ce "How are u little girl? U are so cute" Yusuf ya cusa dayan hannunsa a pocket dinsa as usual ya ce "Thank u, are u leaving now?" Ta girgiza kai ta ce "Actually no, and i came with driver" ya ce "Alright, that's good" sai lokacin idansa ya sauka akan Anty Amina dake gefen Rafi'ah tana rike da basket, tin zuwansa ta kura masa ido ko kiftawa babu, kallan Rafi'ah yayi a hankali ya ce "Are u together with her? I mean the lady besides u" Rafi'ah ta daga masa kai ta ce "Yess, my housemaid" jin haka yasa Anty Amina ta gwalalo ido tana kallan Rafi'ah ta ce "I don't understand, who's your housemaid here?" Ta kallai Yusuf sannan ta kalli Anty Amina ta ce "Let's move from here pls" Yusuf ya dan matsa gefe sannan tabi bayansa itama, sororo Anty Amina tayi tana kallan Rafi'ah, daga haka ta cije baki ta saki basket fin hannunta fuuuu ta bar wajen cikin sauri. Dariya sosai Rafi'ah ta kyalkyale dashi harda kama ciki, sai yanzu abinda ta fada yayi mungun bata dariya, Tsayawa kawai Yusuf yayi yana kallanta with confusion, ta kai minti 5 tana ta kyalkyala dariya kafin ta kalli Yusuf ta ce "Anywhere thank u much" ya danyi shiru sannan ya ce "Are u sure she's your housemaid?" Ta ce "Of course, kasan idan suka waye sai a hankali, wai yanzu fishi tamin, dama tana ta rokona kar watarana na copsa mata", Yusuf yayi murmushi ya ce "And u did?" Sake dariya tayi ta ce "Why will i not Doctor" ya sauke ajiyar zuciya yana kallanta,
Sweet da chocolate ta kwasarwa Khairiyya ta biya kudin sannan suka fito, sai bayan sun fita ta mika mata ledan ta ce "This is yours little Baby?" Khairiyya ta kalli Yusuf sannan ta kar6a ta ce "Thank u" Rafi'ah ta kama hannunta ta ce "What's your name?" A hankali ta ce "Fatima Khairiyya" Rafi'ah ta dan wara ido looking smiley ta ce "Woow ashe namesake dina ne" dai dai lokacin ta kalli inda sukai parking taga ba motarsu a wajen, Yusuf dake kallanta ya ce "Where are they?" Ta ce "May b they've gone" ya ce "Ohk, let me drop u home" tabi bayansa har suka isa inda motarsa take, back seat ya budewa Khairiyya bayan ta shiga ya budewa Rafi'ah front seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa ya sawa motar key, suna hawa saman titi ya kalli Rafi'ah dake murmushi ya ce "Who's she? I mean the woman?" Ya kara tambaya for d second time, silently ta ce "Stepmother" tana rife bakinta ta sheke da dariya tana kai kanta kan cinyoyinta, surprisingly enough Yusuf yake kallanta ya ce "Do u mean your Daddy's wife?" Ta daga masa kai still laughing ta ce "Nima ramawa nayi, haka kawai ta fito dani just to make me angry, munkai awa muna zagaye amma wadannan abin daka gani a basket su kadai ta dauka" ta kara turo baki ta ce "Ai dani take wallahi" Yusuf couldn't hold his laugh, yayi dariya kafin ya ce "Zaki sha fada wajen Daddy ai" ta ce "Ba fada ba? Aini ba yanzu na saba jin fada ba" yayi nodding kansa ya ce "Kin saba kenan?" Ta ce "Noo" ya sake kallanta ya ce "Since from the first day i saw u nayi noticing u are stubborn" ta danyi murmushi ta ce "And it isn't true, ina rama abinda akamin ne kawai that's all" ya maida hankalinsa ga tuki ya ce "Wane area kike?" Ta ce "Hotoro GRA" daga haka ta fada mishi house number din.
Anty Amina na komawa gida apartment dinta ta nufa ta kasa zaune ta kasa tsaye, ita abinda Rafi'ah ta fada bai dameta sosai ba kamar kamannin Yusuf, tabbas bazata ta6a mantawa dashi a rayuwa ba, amma da dukkan alamu bai gane taba, a hankali ta ce "Kaddai saurayin Rafi'ah ne?" Daga haka ta lalibo wayarta cikin hand bag dinta ta fara neman phone din Abba. Bugu daya ya dauka ya ce "I will call u ltr i'm busy now" daga haka yayi hanging call din, a bakin titi Rafi'ah tace Yusuf ya ajiyeta, tayi masa godiya sannan ta shafa kan Khairiyya ta ce "Bye little girl" Khairiyya ta daga mata hannu sannan ta juyo tana kallan Yusuf ta ce "My house isn't far from here, so nagode sosai" ya danyi murmushi ya ce "Mention not" daga haka ta shiga cikin layin walking very slowly tana auno fadan da Abba zai mata, tasan duka kam is impossible tinda ba ta6a mata yayi ba. Cikin sauri Anty Khadija taja birki ganin Rafi'ah, if she could recall itace yarinyar da Yusuf ya kai mata office dinta, kafin tayi parking ta fito tuni Rafi'ah ta tura gate ta shige gida, ta dinga kallan dankareren gidan kafin taja motarta tayi gaba, motar Yusuf ta gani akan junction ya tsaya suna gaisawa da wani, lokaci daya jikinta ya bata cewar shi ya ajiye Rafi'ah yanzu, ganin yadda yake ta fara'ah suna gaisawa da mutumin ya tabbatar mata da cewa Yusuf yana cikin farinciki, abinda ta tsana ta ganshi a ciki kenan, tayi mungun tsanar ta ganshi yana murmushi, taja wani dogon tsaki sannan taja motarta ta tafi a wajen ta ce "Ba dai naga gidansu ba, muje dai zua" daga haka ta kara speed din motarta tayi hanyar gida.

_SHARIK~HAYATI_

*Remember update is 2 days per week, And the page is dedicated to my luvly, sweet, mint, bread, sugar, honey 🙄 what again? Time bom, big bom 😂 My ILHAM 🧡 stay blessed Jiddah ta*
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_13~14_

Cikin quick light steps ta shigo compound din nasu, ta dan kalli apartment din Anty Amina sannan ta ta6e cute mouth dinta ta nufi entrance din gidan, Ummi ce kadai zaune a parlo tana kallo, Rafi'ah ta saukar da kanta ganin irin kallan da Ummi ke mata, ji tayi ta ce "Where are u from?" Wani katan abu daya tsaya mata a wuya ta hadiye kafin ta ce "Shopright" Ummi ta dinga kallanta sannan ta ce "And why did u came back alone? didn't u know that they spent more than 20 minutes before u came in" a hankali ta ce "Naje daukan perfumes ne, so kafin na dawo na samu sun taho" Ummi ta ta6e baki ta ce "Is ok" daga Rafi'ah ta wuce upstairs da fargaban abinda zai faru idan har Abba yaji tacewa Antinsu mai aiki ce. Direct dakinta ta shiga ta kwanta akan bed tana sauke ajiyar zuciya, calmly ta danne side din da zuciyarta yake saboda heartburn data faraji, ta limshe idanuwanta to make sure it's not taking long, ji tayi kamar an kara mata wanda takeji akan da, ta fashe da matsanaicin kuka tana kwalawa Ummi kira, juyi ta farayi tana yarfe hannu, dayan hannunta kuma yana kan heart dinta dake mata zafi kamar zata fasa kirjin ta fito. Tin tana hawaye harta dawo she's crying loud calling Ummi and Abdul. Ummi na zaune a parlo taji kawai she's not comfortable with her daughter's absence, tasan the next abu da zatai to bacci ne, hakan yasa ta mike ta nufi upstairs, Immidiately tana gama hawa Rafi'ah ta saki wani irin kara hade da kiran Abba, Ummi ta bude dakin da saurin tayi kanta tana salati, dagota tayi jikinta tana kallan idanta dake limshe ta ce "Rafi'ah!" tana bude idanuwanta hawaye suka shiga gangaro mata, a hankali ta dago hannun Ummi ta dora akan chest dinta ta ce "It's hurting me Ummi" daga ta tayi kamar baby girl ta rungumeta suka fito a dakin, suna fitowa sai ga Abba da hawowansa kenan yana waya, cikin tashin hankali ya ajiye wayar akan sofa yana furta "Subhanallah" daga haka ya kar6eta in a hurry ya fara sakkowa steps da ita, komawa daki Ummi tayi ta dauko hijab dinta sannan ta sakko. Ko kafin ta fito har Abba yasa Rafi'ah a mota, bayan Ummi ta shiga yaja motar suka fita a gidan zua Clinic din da suke zuwa. Suna isa cikin gaggawa aka turo bed aka daurata akai sannan aka wuce da ita ciki.
Dr. Saleem, Dr. Aryan da kuma wasu turawa biyu ne a kanta to make sure they give her quick assistance, Aspirin doctor Aryan ya saka mata a baki, as usual ta fara chewing a hankali harta hadiye sannan aka bata nitroglycerin ta sha, after then aka mata injection din papaverine to reduce the pain and discomfort beyond her chest to orther part of her upper body, few minutes da mata alluran ta samu tayi bacci, Dr. Aryan ya kalli sauran doctors din dake kanta ya ce "I think it's successful" wani bature a cikinsu ya ce "By God grace" daga haka suka fita gaba dayansu suka jawo kofar to let her rest. Suna fitowa Abba ya karasa wajensu ya ce "How is she Doctor?" Doctor Aryan ya cire hand gloves din hannunsa yana kallan Abba ya ce "It was successful, insha Allah within 1 hour zata tashi" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Thank u" daga haka ya koma inda Ummi ke zaune, daka ganta kasan tana cikin tashin hankali, Abba ya kamo hannunta yana massaging just to make her calm ya ce "Relax please, kiyi ta mata addu'a" ta goge dan hawayen dake makale a idanta ta ce "I don't want to loose Rafi'ah Yallaboi" ta karashe maganar cike da damuwa, Abba ya ce"The best thing is du'ah Ummu Rafi'ah, u know God plan the best, it is a test from God, kuma ina fatan zamuci wannan jarabawa insha Allah" a hankali Ummi ta ce "Allah yasa".
Anty Amina ce zaune a parlorn ta tana shan fresh yoghurt sai yayarta dake zaune a gefenta tana sauraronta, bayan ta dasa aya matar ta zaro ido hade da kundumo ashar ta ce "Baki fasawa yarinya baki ba? Ita har tana da bakin da zata kiraki da 'yar aiki? Wallahi tallahi Amina kinyi asara, ko uwarsu ce ta fada miki haka bakya tsigale taba ballanta wannan taniniyar yarinyar" Anty Amina ta ajiye glass cup din hannunta ta ce "Nifa Anty Rahama wani abun mamaki na gani that's why i totally forgot her speech, nifa tsohon saurayin Nusaiba na gani ya mata magana" Anty Rahama ta ce "Wacece Nusaiba?" Gyara zama Anty Amina tayi ta ce "Kawata da muka gama karatu tare, wallahi tana sanshi yana santa ingaya maki wata 'yar uwarsa ta shiga tsakani suka rabu, ni kuma dama fa.. Tin kafin nayi aure kyau yakemin, fatana dai ba saurayinta bane, wallahi Anty Rahama bakiga kyansa ba, kamar shi yayi kans... " tsawa Anty Rahama ta daka ta ce "Lallai Amina na yarda kin fara hauka, ina ruwanki da wani saurayi caan da mijinki" ta 6ata rai ta ce "Anty Rahama hauka kuma?" Ta ce "Hauka mana Amina, da kinsan irin tuggun da muka hada nida Umma akan Ya Muhammad ya aureki da baki fadi haka ba, ina gashi muna 'yan wansa na jini amma akace ya nemeni yaki, haka na hakura nayi wannan tsinannen auren da babu komai a cikinsa sai wahala, me za'ai da talauci Allah na tuba" Anty Amina sai kallanta take bata ce komai ba, Hakan yasa Anty Rahama ta kamo hannunta ta ce "Ko kin manta da Ummanmu da mahaifinsa uba daya suke, to haka mukaita kai kawo kauyen Masko har Allah yasa da kansa yaje ya sami Gwaggo Allah ya jikan rai yace yana sanki da aure, ke wahalar da muka sha wallahi bazai misaltu ba, amma gaki shekara 3 har yanzu ko 6ari baki ta6a yi ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To Anty kikasan ko shine baya ai... " katseta Anty Rahama tayi ta hanyar cewa "Kuul dama!!! da baya aihuwa ya haifi Rafi'ah da Abduljalal? Ki dai zauna dai, kina gani duk dukiyar nan su kwashe su barki da dan karamin fili" Anty Amina ta mike ta ce "To ai haihuwar ta Allah ce, duk magungunan da kike kawomin ina sha amma shiru har yanzu" Anty Rahama ta ce "Maza bani abinda zan samu in wuce na bar Umma ita kadai Ikleemah ta fice" daki Anty Amina ta shiga ba jimawa ta fito da sarkan gold ta mikawa Anty Rahama ta ce "Ga dai wannan" Anty Rahama ta washe baki ta ce "To barka, sai a siyar aci gaba da nema maki maganin haihuwa, ina dalili shekara 3 fa kenan babu labari" daga haka tayi kasa kasa da murya ta ce "Ni inaga ma wannan kishiyar taki ce tasa miki hannu, dan taga dake ake tafiya Abuja a barta a Kano" Anty Amina ta ce "Nima dai abinda nace kenan, amma koma menene yazo karshe" Anty Rahama ta nufi kofar fita ta ce "Muna nan dake zakiji labari, to nidai na tafi" Anty Amina ta daga mata hannu ta ce "To sai anjima" daga haka Anty Rahama ta fita ita kuma ta dawo ciki.
kwance take jikin Ummi tana ta faman sauke ajiyar zuciya, Ummi ta kamo hannunta tana kallan idanta ta ce "How are u daughter?" A hankali ta ce "Da sauki" Ummi ta gyara mata scarf din kanta ta ce "Allah ya baki lafiya", bude kofar dakin akai Abba ya shigo Abdul na biye dashi, suka karasa kan gadon suna kallanta cike da tausayi, jikinta Abba ya ta6a ya ce "Mamana, ina ke maki ciwo yanzu?" Silently ta ce "My chest Abba, amma kadan kadan yake" Abba ya durkusa dai dai fukarta ya ce "Soon zai daina Mamana, zanje gida na dawo me zan kawo maki?" Ta danyi smiling sannan ta ce "Shawarma Abba" ya shafa kanta ya ce "To Insha Allah" Abdul ya kamo hannunta na hagu yana kallanta ya ce "Get well soon Anty, Allah ya baki lpy me daurewa" kallansa tayi trying hard to control herself ta ce "Thank u love" limshe idanuwanta tayi dan ita kadai tasan abinda takeji deep down, damma da aka mata alluran ya rage mata radadi da ciwo, Abba ya kalli Ummi ya ce "Lie her down and pray Madam, after then itama tayi sallah tayi addu'a sosai kinji Mamana?" Kai ta gyada masa ta ce "To" Ummi ta kwantar da ita ta ce "Allah ya kiyaye, amma Abdul kar ya dawo ya zauna kawai tinda kaima komawa zakayi ai" Abba ya ce "Me zai hana muzo tare mu koma, ai shima yanaso yaga condition dinta" Ummi ta ce "To sai kun dawo" daga haka suka fita ita kuma ta shiga toilet danyin alwala. Yusuf ne zaune a office din Dr. Aryan, bayan ya mishi bayanin abinda ya kawo shi Dr. Aryan ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya kira Dr. Hisham ya sanar masa yadda sukai, on the other side Doctor yace ya kar6a test din nasa sannan ya rubuta masa sabbin magani, after yayi hanging wayar ya kalli Yusuf sannan ya ce "Let me have the test" Yusuf ya mika masa test din, bayan ya duba ya ce "Allah ya sauwke, bari nayi ma wata patient injection idan na dawo saina rubuta maka drugs din, nasan by now she's awake" Dr. Aryan ya karashe maganar yana kallan agogon dake manne a bangon office din, mikewa Yusuf yayi dan sauri yake ya wuce gida, gaba daya he looks so tired, Dr. Aryan ya ce "Can't u wait?" Yusuf ya ce "Let me have the injection saina mata i'm also a medical doctor" daga haka ya ciro ID card dinsa ya mikawa Dr. Aryan, kar6a yayi yaga sunansa, asibitin da yake aiki da year din daya fara aiki sai field dinsa daga karshe, murmushi Dr yayi ya ce "Masha Allah, ashe ina tare da babban likita ne, nice to meet u Yusuf" daga haka
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment