Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manyan mata ne akan tabarma suna zaune sai hira suke, kana kallansu kaga dangin su Ummi ne sai kanwar mahaifiyarsu da ita kadai ta rage musu wacce suke kira da Gwaggo, ko ba'a fada ba kamanni sun nuna, tsugunawa Jawad yayi ya ce "Ina yinin ku" a tare duk suka amsa da fara'a ya mike ya shiga cikin gidan, Ummi ce zaune a parlor da wasu mata biyu, ya zauna akan carpet yana murmushi, Ummi ta ce "Is it you Jawad? Dama kana nan?" murmushi yake yana gyara hulan kansa ya ce "Ina nan Ummi, aiki ne ya min yawa yanzu" ta ce "To Allah ya taimaka" ya ce "Ameen, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah, let me get something for you" daga haka ta mike, gaishe da sauran matan yayi suka amsa masa, ba jimawa Ummi ta fito a kitchen da warmers a hannunta ta wuce parlorn Abba, bayan ta fito ta ce "Ka shigo ciki Ahmad" tashi yayi a hankali ya wuce parlorn Abba ya zauna akan carpet ya fara danna wayarsa. Shigowa Ummi tayi ta zauna ta ce "Kaci abincin ko, bari Rafi'ah ta kawo maka kunu, ko baka sha?" kansa ya dan sauke kasa ya ce "Ina sha, amma dai na koshi da abincin" Ummi ta ce "To bari a kawo maka kunun" daga haka ta fita a parlor. Upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi'ah, a kwance ta sameta tana waya, tayi saurin hanging wayar tana kallan mahaifiyartata, Ummi ta ce "Kije ki dauki kunu ki kaiwa Jawad, yana parlorn Abbanki" a hankali ta mike ta dauki himar dinta ta saka sannan tabi bayan Ummi ta fito, tana saukowa ta wuce kitchen ta dauko flask din sannan ta shiga parlorn Abba, very gentle ta karasa gabansa ta ajiye flask din, suna hada ido tayi saurin dauke kanta ta nemi waje ta zauna gefenshi, a hankali ta ce "Ina yini" ya ce "How are u?" ta ce "I'm fine" ya ce "Ya shirye shirye?" Kanta na kasa ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta mike ta fita a parlor ya bita da kallo. Mug ya dauka ya bude flask din sannan ya debi kunun ya saka cube din sugar guda 2 sannan ya dauka spoon ya juya ya fara sha a hankali. Few minutes ya gama sannan ya ajiye cup din, Ummi ne ta shigo parlor daukan abu, ya danyi kasa da kansa ya ce "Ummi zan tafi Cyprus gobe insha Allah" dagowa tayi tana kallansa ta ce "Tooh zaka kara nisa kenan, daga wajen aiki ne suka tura ka?" Ya ce "Ehh" ta ce "To Allah ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya, are u staying long?" Ya ce "Noo, just 2 months" ta ce "Aida yawa Jawad, Allah dai ya taimaka ya tsare" ya ce "Ameen", daukan abinda zata dauka tayi sannan ta fita a parlor, so yake yace mata yana san yaga Rafi'ah amma ya kasa, gashi he is eager to go home.
After 15 minutes Rafi'ah ta shigo parlor, sai data dan tsaya ganinsa dan a tinaninsa ya wuce, ta sunkuyar da kanta ta wuce dakin dake parlor, ba jimawa ta fito da wani dan bucket a hannunta, Jawad ya ce "Idan kin gama kizo" juyawa tayi ta kalleshi sannan ta fita ta kaiwa Gwaggo bucket din ta dawo, a hankali ta karasa inda yake ta zauna, ya mika mata envelope din ya ce "Mummy ta bayar a baki" ta kar6a sannan ta ce "Thanks" daga haka ya ciro box din da cheque ya mika mata ya ce "And this is for you" ta dago ta kalleshi sannan ta kar6a, kallan cheque din ta dinga yi, ta kara kallansa ganin 100k ajikin cheque din, sauke kanta tayi kasa ta bude box din a hankali, ta dan zaro ido ta ce "Azurfa?" Ya daga mata kai ya ce "I hope it will size you?" Murmushi tayi ta fara zira ring din a hannunta na dama, ta juyo hannun tana kallansa ta ce "Yayi kyau sosai, thank u so much" kallan dogayen fingers dinta kawai yake, ta cire ring din ta maida shi box dinsa sannan ta ce "I'm so much greatful, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" a hankali ya dago yana kallanta ya ce "I know u have more than that, so no need to say thanks, and i'm wishing u a happy marriage life, try your best and be the best wife ever" a hankali ta ce "Insha Allah" still looking at her ya ce "Gobe zan tafi Cyprus bazan samu daurin auran ki ba" duk jikinta sanyi yayi ta ce "Allah ya kiyaye, ya kaika lafiya" ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya dauki key din motarsa, tashi tayi tabi bayansa har suka fito a gidan, ta rakashi har mota tana mishi Allah ya kiyaye, silently ta tsaya a bakin mota ta ce "I'm lost of words Ya Jawad, nagode sosai da sosai, Allah ya saka, i'm happy with the gift" murmushi ya danyi ya ce "Ba komai, thanks too" rife motar tayi sannan ta shiga gida shi kuma ya tada motar ya bar layin. Tana shiga compound Gwaggo ta ce "Shine angon ne Fatima?" Turo baki tayi tana kallan kakartata ta ce "Ba shine bane fa Gwaggo" Gwaggo ta ce "To shi wannan din waye? angon baizo ya gaishe niba fa, baisan kanwar kakarki tazo bane" dariya ta danyi ta ce "Keda zamu tafi tare, ai an maki dakinki" daga haka ta wuce ciki ta barta a tsaye.
Washegari da sassafe Jawad ya gama shirinsa na tafiya Abuja, daga caan karfe 10 na dare zasu tashi zuwa Cyprus Mami na tsaye ta gama hada masa komai ta ce "Yanzu sai kaje Abujan zaka karasa kenan?" Ya ce "Ehh" ta ce "To saura karkaje ka gaishe da mutanen gida, nasanka yanzu zaka ce aiki ya maka yawa" murmushi ya danyi ya ce "Ai a caan zan sauka tinda yau zan wuce" ta ce "To Allah ya kiyaye, ya kuma tsare hanya" ya ce "Ameen", Sadeeq ne ya fitar mishi da komai zuwa mota, bayan sun fito parlor Mummy ta fito da dambun namanta cikin dan karamin bucket ta ce "Allah ya tsare Ahmad, ga dambun naman" kar6a yayi ya ce "Nagode Mummy" ta ce "To Allah ya tsare" daga haka ta koma part dinta Mami ta bita da harara, shi dai sauke kansa yayi kasa ya fice a parlor, Mami tabi bayansa ta ce "Dambun naman ne bazan iya maka ba sai ka fadawa duniya an maka" dan murmushi yayi ya ce "It's nothing ai Mami, duk daya ne" harara ta 6alla masa ta ce "Allah ya tsare" daga haka ta koma cikin gida ba tare data ga tafiyarsa ba. Da Yamma liss aka fara shirin waleeman da Mummy ta hada, ita ce komai akan gaba, karfe 4 mai make~up tazo ta fara yiwa amarya, Ameera na gefe ta gama make~up dinta tana daura dankwali, bude kofar akayi Mummy ta shigo ta ce "Wai har yanzu baku gama ba?" mai kwalliyan ta danyi murmushi ta ce "An gama Hajiya" Mummy ta kalli Rafi'ah dake kyalli ta ce "Masha Allah" daga haka ta fita a dakin, by 4:30 sun gama komai da komai, a compound din cikin gidan aka jera kujeru akai decorating wajen, Babbar malama aka dauko ta wa'azantar da mutune akan rayuwar zaman aure, da yawa mutane sun karu ba kadan ba, bayan ta gama aka fara cin abinci sannan aka raba snacks, daga karshe akai hotuna kowa ya watse. Da dare musalin karfe 10 Rafi'ah na zaune a dakinta ita da Ameera da wasu friends dinsu na islamiyya su biyu, Mummy ta shigo ta ajiye musu warmer din abinci ta ce "Rafi'ah Gwaggo tace bata ganki ba tin bayan waleema" limshe idanuwanta tayi ta ce "Ina daki, bayan dazu data ganni da make~up tace min abu kamar aljana" dariya Ameera ta dinga yi tana kallan Rafi'ah, Mummy ta ce "Ai kadan da aikin Gwaggo, Yusuf din ya aiko kayan da zaki sa goben?" Rafi'ah ta ce "Yace zai kawo da safe" Mummy ta ce "Ok to shkn, zaizo ne ayi kamun dashi" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Yace dai zaizo muyi pictures" Mummy ta ce "To ba damuwa na zata ai bazai zo ba ne danaji baki maganar ba" daga haka ta fita, Rafi'ah ta kalli Ameera ta ce "Ai sai yazo wajen kamun nan, ai da bikin matarsa shima yaje" Ameera ta dan yi murmushi ta ce "Kishi" duka Rafi'ah ta kai mata ta kauce tana dariya. Washegari ya kama friday, gidan biki ya cika da jama'a kowa nata hidima, Rafi'ah dai tattara nata nata tayi ta koma gidansu Ameera saboda mutane. Bangaren su Umma kuwa, mutane kadan ne a gidan, dan batayi wani gayya ba, gaba daya abin duniya ya isheta, sau biyu Jiddah na zuwa mata tana kuka, haka dai Umma ke lalla6ata ta koma gida. Gidan Ammin Khairiyya kuwa acaan duk 'yan uwa suka sauka, gidan ya cika da mutane kai kace a gidan Yusuf ya girma. Anty Amina ce zaune a dakinta tare da Anty Rahama, ta dan yatsune fuska tana kallan Anty Rahama ta ce "To ya zanyi Maman Ikleemah, kina gani dai abun nan yana nan ba'a tone ba" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "To sai asan abinyi a gaba ai, ba wai zuba ido zamuyi ba, su kuma 'yan uwanmu da basu iya zuwa birni ba duk sun cika gida, gidan Umman ma acike yake, kema naki acike, nifa idan na gaji kaaf mutanen parlorn nan saina koresu wallahi" Anty Amina ta gyara zamanta ta ce "Ga kazanta kamar ta fito fili, shima Yayah Muhammad din a hotel yace zai kwana yau" Anty Rahama ta gwalalo ido ta ce "Anya mun ta6a bikin da akai taro irin wannan kaf zuri'ar mu kuwa? Har Abban sunma ya rasa wajen kwana a gidansa sai hotel?" Anty Amina ta ce "To shine abinda yake damuna, gashi shi Mutumin Umma cewa yayi ko taro baza'ai ba gashi har gobe daurin aure" Anty Rahama ta ce "Mudai zuba ido, ba kince yana nan ba a binne?" Kai ta daga mat, Anty Rahama ta mike ta fita tana kallan mutanen parlorn da duk yawanci 'yan uwansu ne ta ce "Kuma wallahi duk matar data ci abinci ta share, haka kawai kun cikawa kanwata parlor da 'ya'ya 'yan kauye" wata 'yar uwarsu ce ta mike tana kallansu ta ce "Ke Rahama ki kiye bakinki, gidankine da zaki finga yiwa mutane iyayi kina fada musu magana" Anty Rahama ta ce "Amma ai gidan kanwatane kuma gidan Yayana" matar ta mike tana tafa hannu ta ce "Indan ta wannan ne muma ai dan uwanmu ne, saboda haka duk inda muka ga daman zama a gidan nan zama zamuyi" wata mata ce ta tashi tana kallanta ta ce "Dan Allah Safiya kiyi hakuri kibar kulata, ita har tanada bakin magana, shekararta nawa a gida babu aure, ga zandareriyar budurwar 'yarta banda rashin kunya bata iya komai ba" Cakumeta Anty Rahama tayi ta ce"Har ni zaki cewa bazawara, yanzu sai naci kaza-kazanki a gidan nan wallahi" mutanen dake zaune a parlor suna ta bada hakuri, da kyar dai Anty Rahama ta saketa ta shige daki tana zage-zage.

_08103810398_
[8/5, 7:38 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_38_

Zaune take akan sallaya tana addu'a misalin karfe 10 na safe, juyawa tayi jin ringing din wayarta, ta dago wayar tana murmushi ganin Yusuf ne, a hankali tayi picking call din ta kai kunne hade da sallama, on the orther hand Yusuf ya ce "How are u Baby?" A hankali ta ce "I'm fine" ya ce "I saw ur make~up yesterday, kinyi kyau sosai, i hope yau kifi jiya kyau" a hankali ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah" ya ce "Zanzo na kawo miki kayanki anjima" ta gyara zamanta ta ce "I'm not at home" da mamaki ya ce "Kina ina?" ta ce "Gidansu friend dina Ameera, bayan layin mu ne" ajiyar zuciya ya sauke har sai data jiyoshi, ya danyi shiru sai kuma ya ce "Caan gidansu zanzo kenan?" Ta ce "Ehh, ina ga" ya ce "Alright, u send me the address, take care" ta ce "Ohk bye" hanging call din tayi taci gaba da addu'a, bayan ta gama ta mike akan carpet ta dan limshe ido dan bacci takeji bana wasa ba, daren jiya batai baccin kirki ba tai ta sallah tana addu'a hopping for the best marriage in her life. Jiddah ce zaune a parlornta tana share hawaye, tinda taji Yusuf yana waya kuka ya dinga cinta, bata samu sauki ba saida tayi kukan, tana nan zaune ya fito daga daki, ta gefen ido ta dan kalleshi, sai da kirjinta ya buga ganin kyan da yayi, sai sheki yake kamar shima am masa dilka lol, ya sha farar shadda da babbar riga sai ya fito as the groom he is, banda kamshi babu abinda yake, bude warmers din kan dinning yayi yaga babu komai, ya juyo ya kalleta tayi saurin dauke kanta, yana murmushi ya karasa gefenta ya bata side hug ya ce "Why the mood first wife?" fashewa tayi da kuka ta ce "Aure zakiyi ka kyaleni ko Yaya?, dan Allah ka fasa auran nan Allah zan iya mutuwa" limshe idanuwansa yayi jin yadda tayi collapsing a jikinshi, ya dinga shafa bayanta cikin rarrashi ya ce "I told u everything yesterday night Jiddah, alkawari nayi zan zauna daku biyun har karshen rayuwana, all i want is peace, ba aure zanyi dan hankalina ya tashi ba, and ba wai zanyi aure bane saboda bana sanki ba, ina sanki babu abinda kika gaza yimin a zamana dake, duk da ma satin nan kaff da yunwa kike barina amma dai na yafe miki" kara fashewa da kuka tayi ta ce "Bayan yarinyar rainin yawo ne da ita, gata karama amma sai rashin kunya, wallahi idan ta shigo gidana she will regret" ta karashe maganar tana share hawaye, rungumeta yayi tsam tsam cikin lallami ya ce "Amma ai tin farko na riga na gaya miki tare zaku zauna, sannan jiya da aka zo jere u did wrong, kin 6atamin rai kawai banyi magana bane saboda banasan hayaniya, ya za'ai ki rife kofar parlor bayan kinsan ta nan zasu shigo?" Rife idanuwanta tayi ta ce "To meyasa baka mata nata kofan ba?" Strictly ya ce "That's my wish, ba gidana bane? don't make me angry now, kuma yau kam kije gida, da daddare idan an kawo amarya u can come back, idan kinga dama ki kwana in kina so" kara fashewa tayi da kuka ta ce "Ni bazanyi attending auranka ba wallahi, bazanje gidan ba, sai dai na tafi gidan Anty na" zameta yayi a jikinsa ya ce "I don't permit u, idan baza kije gidanmu ba u can stay at home" daga haka ya dauki key din mota da kayan Rafi'ah a leda ya fita a parlorn, yana fita ta rushe da kuka ta durkusa akan carpet tana ta shiga 3. Umma ce zaune a gaban Malaminta sai zufa take, ya juyo kwaryar dake cike da ruwa yana nuna mata ya ce "Da karfe nawa ne auran?" Cikin rawar jiki ta ce "Yau Juma'a da karfe 2 idan an idar da sallah" girgiza kansa yayi yana kurawa ruwan ido ya ce "Ba lallai a daura auran ba" Umma ta share zufa tana kallansa ta ce "Alhamdulilah" da sauri ya dago ya kalleta ta ce "Allah gafarta Malam" ya juya jajayen idanuwansa ya ce "Mutanenmu na bukatar wata gudumawar Hajiya, saboda aiki sabo zasu yi" cikin sauri Umma ta ciro dubu 50 ta ajiye masa a gabansa ta ce "Indai aiki zaiyi ko nawa ne zan bayar Allah gafarta Malam" yayi wata kalar dariya ya ce "An gama Hajiya, sai dai ki zuba ido" mikewa Umma tayi tana murmushi ta ce "A huta gajiya" daga haka ta debi takalmanta a hannu ta fita a dakin.
Anty Amina ce zaune a dakinta ta buga uban tagumi, duk jikinta yayi sanyi ganin awanni ya rage a daura aure , gashi so take ta tono abin tagani yana nan din amma gidan cike yake da jama'a ta ko'ina, duk ta rasa inda zata sa ranta gashi Anty Rahama ta koma gidan kawarta wai sai an fasa auran zata dawo tayi dariya, bude kofar dakin d akai yasa ta dago kanta, Ikleemah ta karaso dakin da kumburarrun idanuwanta da sukai jaa, zama tayi a gefen gado tana kallan Anty Amina ta ce "Saura awa 3 fa Anty, kunce min dani za'a daura amma har yanzu banji ana ango yace bayayi ba" fashewa tayi da kuka tana kallan Anty Amina. Ajiyar zuciya ta sauke ta kamo hannayenta ta ce "Kiyi hakuri mu zuba ido mu gani, ai yadda kika sha dilka da gyaran jiki dole ke zaki shiga gidan Yusuf, kima daina daga hankalinki muna nan zakiji komai anjima" cikin kuka ta ce "Fatana kenan Anty, dan idan na rasa Yusuf mutuwa zanyi Anty Amina, sai dai Ammina ta dauki gawana ko ku... " rife bakinta Anty Amina tayi ta ce "Kina hauka ne Ikleemah, menene na zancen daukan gawa kuma" share hawayenta tayi ta jingina kanta akan gado tana kuka kasa~kasa.
Simple make~up Rafi'ah tayi ta saka atampa Ameera tayi mata daurin, sosai tayi kyau, sai kamshi take duk inda ta gifta, Ameera dake kallanta ta ce "Anya Doctor zai bari ki dawo gida Fatima? Masha Allah kin yi kyau" 'yar harara ta 6alla mata ta ce "Ina dai Babanku baya kasa?" Ameera dake dariya ta ce "Jiya fa nace miki yayi tafiya, amma anjima zai dawo, dan yace min zai iya samun daurin auranki" ta dauka veil dinta ta yafa ta ce "Ameera kaina ciwo yake" dafa goshinta tayi ta ce "To bakya bacci Fatima, taya baza kiyi ciwan kai ba" a hankali ta dan limshe ido ta ce "To ya zanyi Ameera, dole ne nayi addu'a sosai na roki Allah yasa a gama bikin nan lafiya, gaba daya na gaji so nake a gama kowa ya huta" Ameera ta danyi murmushi ta ce "Dama haka hidima yake ai, insha Allah lafiya kowa zai koma gida" a hankali ta ce "Ameen" tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing, ta bude idanuwanta dake limshe tayi picking call din, Yusuf ya ce "I'm outside" ta ce "To" daga haka tayi hanging wayar tana kallan Ameera dake gaban mirror ta ce "Bari naje Khadija, su Maryam Sa'eed basu zo ba har yanzu" Ameera ta juyo tana kallanta ta ce "Soon zasu zo, dazu da kina bacci munyi waya, wai tailor ne bai karasa musu dinkin ankon ba" Rafi'ah ta ce "Alright, sai na dawo" Ameera ta ce "Ki gaishe sa" da toh ta amsa sannan ta fita a dakin, kannan Ameera ne kawai a parlor suna kallan power rangers samurai, ta danyi murmushi ganin yadda suke gaisheta ta ce "How are u people?" Suka ce "Fine" daga haka ta fita, tsaye suke shida Aliyu a jikin motarsa, ya dinga kallanta harta karaso inda suke, ta dan kalli Aliyu ta ce "Ina yini?" Ya ce "Lafiya kalau Amaryar mu, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah" Yusuf ya gyara zaman hularsa yana murmushi ya ce "Ina yini Baby" rife idanuwanta tayi da veil dinta, ya ce "Kinyi kyau Allah, i feel like stealing you and run" harara Aliyu ya 6alla masa ya ce "Doctor ka daukeni karshen layin nan idan ka gama, zan shiga wajen Mukhtar" Yusuf ya ce "Ba damuwa" daga haka Aliyu ya kalli Rafi'ah ya ce "Amaryarmu sai anjima ko" ta ce "To nagode". Bude back seat Yusuf yayi ya ce "Pls enter Baby" ta sauke kanta kasa sannan ta shiga motar, zagayawa yayi shima ya shiga back seat yana kallanta ya rife kofar, ya jawo ledan kayanta ya ce "Ya miki kyau?" Ya zaro rigar yana warewa a hankali, ta dinga kallan hadaddiyar gown din ta ce "Yayi kyau sosai, thank u" ya ce "Mention not, meyake damunki?" tayi saurin sauke kanta kasa ta ce "Me kaga?" Maida rigar yayi cikin ledarta ya ce "Your eyes, bakya bacci ko?" Ta girgiza masa kai a hankali, kamo hannunta yayi murya caan kasa ya ce "Pls tell me dear" silently ta ce "I'm just having headache" Yusuf ya dinga kallanta with lots of disturb ya ce "Have u take any medicine?" Ta girgiza masa kai kanta na kasa, limshe ido yayi yana matsa hannunsa cikin nata jiin zafin jikinta, iya hannunta daya rike kawai yaji jikinta da zafi, dago kanta yayi yaga idanta tap da hawaye, ya kai hannunsa face dinta zai tare tayi saurin janye fuskarta ta ce "I'm not crying" ya ce "You are" ta ce "Kawai ina tinanin Ummina ne idan na tafi" jinginar da kansa yayi ajikin kujera yana kallanta, ji yayi kamar ya jawota jikinshi ya rarrasheta, ya sake hannunta ya ce "Are u taking ur drugs?" Ta ce "Ehh, dazu ma nasha" ya ce "Abinci fa?" Ta ce "Naci" ya ce "Allah ya kara miki lafiya, but don't stress yourself pls, u know ur condition more than anyone else, nasan dole zakiyi kewar Ummi but do a little Baby, kar ki bari ki samu attack today pls" tana ta jujjuya yatsunta ta ce "To" ya danyi murmushi yana kallan Henna hannunta ya ce "It's looks beautiful" ita dai bata bari sun sake hada ido ba, ya ce "Waya maki?" Ta ce "Wata ce" ya ce "Ohk, anjima da dare zan gani sosai da sosai" turo baki tayi ta kara sauke kanta, ya ce "Take ur clothe, Allah ya sauwake, but make sure kinsha panadol sai ki kwanta kinga yanzu is 12 idan an daura auran i will call u" boye fuskarta tayi a jikin kujera tana murmushi ya ce "Yess i will be the first to tell u insha Allah" bude kofar tayi ta fito, ta dan saci kallansa ta ce "Thank u" ya fito shima yana kallanta ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ta daga masa hannu ta koma cikin gida.
Mami ce ta shigo gidan da Ikraam a bayanta, suka dinga wuce mutane a tsakar gida suka shigo ciki, Gwaggo ta kalli daya daga cikin 'ya'yanta ta ce "Waccen ba kishiyar Halima bace?" Anty Salma dake kallan Mami ta ce "Itane mana Gwaggo" Gwaggo ta ce "Shine ta wuce ba gaisuwa, aiko bata sanni ba tana ganina taga jinin su Halima" ita dai Anty Salma shiru tayi taci gaba da danna wayarta, Ummi na shirin fitowa a parlor suka ci karo da Mami, ta danyi murmushi ta ce "Sannu da zuwa Hajiya" ba yabo ba fallasa Mami ta ce "Sannu" Ummi ta juya ta ce "Ku shigo ciki" daga haka ta wuce dasu dakinta dake sama inda Anty Halima da kayenta suke, sosai Mummy tayi mamakin ganinta, dan tanaji da safe Abi na mata fada jiya bata zo gidan biki ba, Mummy ta ce "Sannunku da zuwa" Mami ta gaisa da kawayenta, ta ce "Ina Amaryar?" Ummi dake jera musu abinci agabansu ta ce "Tana nan neighbors dinmu" Mami ta ce "To ya hidima?" Ta ce "Mun gode Allah" kallan Ukraam Mummy tayi ta ce "Ke bakya gaisuwa ne?" Mami ta dan hade rai sai kuma ta ce "Haka take ai" Ikraam ta gaishe da mutanen dakin sannan ta koma bayan uwarta ta lafe, bayan minti 10 Mami ta mike tana kallan Ummi da shigowanta dakin kenan ta ce "To ni zan wuce ga wannan ba yawa" ta nunawa Ummi food flask da bedsheet din da suka kawo, Ummi ta ce "Allah ya saka da alkhairi, mun gode, Jawad ma bana kusa ban mishi gidiya ba ya wuce, Allah yasa ya tafi a

Please Login or Register in order to submit comment