Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa'a kuma" ciki ciki Mami ta ce "Ameen" daga haka ta dan kalli Mummy ta ce "Sai kin dawo" bata jira cewarta ba ta kama hannun Ikraam suka fita a dakin, gaba daya mood dinta ya canza, leda Ummi ta samu ta juye musu snacks din da basu ciba, Abdul da shigowansa kenan ta ce "Kaima Mamansu Jawad kafin su tafi, kace mun gode" cikinsa ya fara shafawa yana kallanta ya ce "Yunwa nakeji Ummi" ta dalla masa harara ta ce "Ba aiken ka nayi ba, nima babu abinda naci tin ruwan lipton dana sha da safe" juyawa yayi ya fita a dakin, da sauri ya fita gate ya samu tana shirin ta tada mota, mika mata ledar yayi ya ce "Ina yini" taja motarta ta bar kofar gidan, kallan hannunsa ya dingayi yaga ba abinda ya sameshi dan dama da sauri ya janye, ya koma cikin gida ya zauna kusa da Gwaggo dake balcony akan tabarma ya fara cin snacks din. Karfe 1 aka dinga tafiya babban masallacin juma'a dake unguwar dan anan za'a daura auran. Rafi'ah na daki taci kwalliya sosai suna ta hotuna kiran Ummi ya shigo mata, tayi picking call din ta fito a dakin saboda hayaniyar friends dinsu, a hankali ta ce "Ina yini Ummi" ta ce "Lafiya, kinci abinci ne?" Ta ce "Ehh, naci" Ummi ta ce "Kina addu'a dai ko Rafi'ah?" A hankali ta ce "Inayi" Ummi ta ce "Never get tired of praying daughter, ko me kike ki dinga addu'a, make sure kina kiran Allah a duk kan lamarinki" silently ta ce "Insha Allah Ummi" Ummi ta ce "Good, Ga Mummynki" kar6ar wayar Anty Halima tayi ta ce "Kina jina Rafi'ah?" Ta ce "Eh" Mummy ta ce "Ku shirya ayi kamun nan da wuri a kaiki kafin dare yayi sosai, kowa saiya dawo gida cikin nutsuwa, karfe 4 kuna wajen nan dan Allah" ta ce "To zamu shirya" Mummy ta ce "Allah ya tsare yasa a gama komai lafiya" a hankali ta ce "Ameen" sannan tayi hanging call din ta koma daki, gefe ta zauna tayi shiru tana kallan time, karfe 2 harda minti 15, ta kifa kanta akan gwaiwoyinta tana karanto ayatul qursiyyu, Maryam ta juyo tana kallanta ta ce "What's wrong Fatima?" Sai a lokacin duk hankalinsu ya kai wajen, suka koma gefenta suna tambayarta menene, Ameera ta ce "Ko ciwan kanne?" girgiza musu kai tayi ta ce "Ba komai" daga haka ta fashe da kuka, Ameera da gaba daya ta rikice ta ce "Wai menene Fatima?" Cikin kuka Rafi'ah ta ce "Abbana, i will miss him" Ameera taja dan karamin tsaki tana murmushi, ita a tinaninta ma wani abin ne ya faru, daga haka ta rungumeta tana kallan agogon dakin ta ce "Kinga time kenan? Ai hamdala ya kamata ki farayi not crying Teemah" Rafi'ah ta share idanta ta ce "Na fada ai" su Maryam dake kallansu suka kwashe da dariya, harara ta musu ta turo baki tana juya kai gefe, wayarta ne ya fara vibrating tayi saurin kallan screen din, daga call din tayi kirjinta na bugawa da sauri~da sauri, Yusuf ya danyi murmushi ya ce "You are now my wife" limshe idanuwanta tayi tana murmushi. Karfe 2 da rabi 'yan daurin aure suka fara dawowa, Anty Amina ta fito tsakar gida ko zata ji wani labari amma taga kowa hidimar gabansa yake, Ikleemah na biye da ita har suka karaso wajen apartment din Ummi, juyawa tayi sai ga Abba ya shigo gidan, tayi karfin hali ta kakalo murmushi ta ce "Abban Rafi'ah har kun dawo?" Ya ce "Ehh an daura aure, ki samo min abincin mutum 10 akai guest house dina" da ido kawai ta bishi yana magana, juyawan da zatai taji faduwar Ikleemah a kasa, Abba da har ya fara tafiya ya juyo da sauri yayi kansu, Anty Amina ta saki kara tana jijjigata ta ce "Na shiga uku Ikleemah dan Allah ki tashi" dai dai nan Anty Rahama ta shigo, tayi kansu da gudu tana ta shiga uku, daga Ikleemah Abba yayi ya nufi bakin gate da ita Anty Amina tabi bayansu tana kuka.


*I dedicated this page to the members of my groups, i love u all and thanks for d comments i appreciate sisters 🥰*
_08103810398_
[8/7, 2:53 PM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_39_

Anty Rahama na tsaye rike da hannun Ikleemah a ward din da akai admitting dinsu, lokaci~lokaci ta kan jijjiga hannunta tana kiran sunanta ko zata tashi, Anty Amina dake tsaye bakin kofa tana kallansu ta ce "Anty Rahama ki bar jijjigata tunda sunce very soon zata tashi" dago kanta tayi tana kallan Anty Amina kafin ta fara magana kamar haka "Na rantse da Allah, na rantse da wanda ya halicci uwata da ubana Rafi'ah bazata zauna a gidan Yusuf ba, sai tayi nadamar auransa a rayuwarta, sai ta dandana bakin ciki kamar yadda tasa Ikleemah" a hankali Anty Amina ta karaso inda suke ta dafata ta ce "Kamar anyi an gama, amma yanzu hankalinmu ya dawo wajen Ikleemah kafin komai" tana rife bakinta wani Doctor ya bude kofar dakin Abba na biye dashi a baya, Abba ya karasa kan gadon yana kallan Ikleemah dake kwance kamar gawa ya ce "Allah ya baki lafiya" Anty Rahama ta ce "Ameen" Doctor na gyara mata drip din hannunta ya ce "Soon zata tashi, so karku daga hankalinku ba wani damuwa" Abba ya ce "Fatanmu kenan, amma menene yake damunta Dr" kallan Abba yayi kafin ya ce "We can talk in my office yallaboi" Abba yabi bayansa suka fita zuwa office dinsa, bayan sun zauna Doctor ya kalleshi ya ce "How are u related with her? Naga kamar kaine mahaifinta" Abba ya ce "Yess i'm a dad to her but not biological father" Doctor ya ce "Do u have any heridity of Heart Attack either family dinku kona mahaifiyarta" Abba ya ce "Yess we have" Doctor ya ce "Allah ya karawa masu shi lafiya, i'm sorry to say itama ta kamu dashi" Abba ya danyi jiim kafin ya ce "What the next thing now" Doctor ya ce "Eh insha Allah zata tashi anjima, zamu daurata akan magani, amma ina ga ba lallaima ta kwana ba" Abba ya mika masa hannu ya ce "Mungode sosai" Doctor ya ce "Allah ya bata lafiya yallaboi" daga haka Abba ya fita a dakin ya wuce masallacin dake asibitin, bayan an idar da sallan la'asar ya dawo ward din da suke, a zaune duk ya samesu sunyi jugum Abba ya kalli Anty Rahama ya ce "Ko zaki kira mahifinta ki sanar masa" ta hade fuska ta ce "Sai dai idan an sallamemu kuma, mutumun da ko nemanmu baya yi" Abba ya ce "Koma menene u let him know, uba ai uba ne, kuma rabuwa ba hauka bane, dole ne yasan abinda yake damin 'yarsa" Anty Rahama da idanta ya kawo ruwa ta ce "Menene yake damunta Ya Muhammad? Dan Allah ka fadamin ina ba mutuwa zatai ba" Abba dake kallanta ya ce "Ba kuka zakiyi ba, kiyita mata addu'a kawai" Anty Rahama ta goge idanta ta ce "Menene yake damun Ikleemah Yaya" Abba ya ce "Itama ta kamu da ciwan zuciya, yace zai sata akan magani idan ta tashi, so dont worry about Allah ya basu lafiya baki daya, zanje na sallami bakina da suka zo daurin aure" daga haka ya fita a dakin Anty Rahama ta bishi da kallo, yana fita ta rushe da kuka tana jijjiga Ikleemah ta ce "Na shiga uku na, Ikleemah ciwan zuciya? Nida nakewa wasu dariya yau gashi a jikin 'yata na shiga uku Umma ya zanyi inasan 'yata wallahi" Anty Amina dake kuka itama ta ce "Mun shiga uku, dan Allah suce ba gaskiya bane". Haka suka dinga rusa kuka har saida Doctor ya shigo ya musu magana sannan suka sassauta kukansu. Parking Abba yayi a kofar gida ya fito sannan ya shiga ciki, wayar Ummi ya kira yace ta sameshi a parlorn shi, ba jimawa ta shigo cikin shigarta ta alfarma, kana kallanta kaga uwar amarya sai kamshi take da gold dinta a wuya da kunne, zama tayi a gefen Abba ta ce "Ya jikin Ikleeman?" Ya ce "Da sauki, wai ciwan zuciya ne itama" Ummi ta dan zaro ido ta ce "Subhanallah, Allah ya bata lafiya, anyi discharging dinta ne?" Abba ya ce "Noo, sunce dai may b anjima, an kai abincin da nace akai guest house?" Ta ce "Ehh, an kai dazu" Abba ya mike ya ce "Bari naje na sallami baki, sannan ku hakura da wannan event din da zakuyi" Ummi ta ce "Nifa bani zanyi ba, Anty Halima ce ta hada musu" Abba ya ce "To kice mata a barshi kawai, akwai marar lafiya a gida" ta ce "To Allah ya sauwake" daga haka ya fita a parlorn.
Da kyar Ummi ta shawo kan Anty Halima aka fasa kamun nan, dan cewa tayi ita ba ruwanta da ciwansu sai anyi kamu, wai idan sune da yanzu suna abinda yafi haka. Duk da haka sai da Mummy ta kira mai hoto sukai ta hotuna a compound din gidan bayan anyi decorating dinsa, sosai Rafi'ah tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, ganin Yusuf da friends dinsa sunzo yasa Ummi ta koma cikin gida, Mummy kuwa hotunansu suka sha da Yusuf har kusan Magrib sannan suka tafi, daga haka kowa ya watse, Aliyu ne ya dauki su Rafi'ah ya maidasu gidansu Ameera.
Umma ce zaune a gefen Ikleemah tana bata tea a baki, Anty Rahama da idanuwanta suka kumbura tsabar kuka tana gefe a zaune kamar marainiya, bayan Ikleemah ta koshi Umma ta kalli Anty Amina ta ce "Yanzu dai rashin lafiyar Ikleemah shine gaba da komai, idan ta samu sauki na tabbata komai zai tafi dai dai rannan zasu gane banbancin aya da tsakuwa" su dai suna zaune ba wanda yace kala a acikinsu, kowa da abinda yake sakawa cikin ransa musamman Anty Rahama gani take kamar su Ummi dariya zasu mata.
Da damuwa Anty Khadija ta shigo dakin da Ummanta take, bayan ta zauna ta ce "Umma mahaifiyarta tana da kishiya, sai dai kuma tafi zama a Abuja akan a nan, inaga kafin su koma zuwa gobe ni zanje" Umma ta ce "Hakan za'ai, shima Malam da mukai waya cewa yayi baisan me faru ba aikin yaki yi, yana da tabbacin aurin ba zai dade ba" Anty Khadija tayi wani murmushi ta ce "Ai dama bai cancanta ya dade ba, ai Yusuf Umma bazai ta6a samun kwanciyar hankali ba" Umma ta mike ta fita a dakin sakamakon kiran Malam daya shigo wayarta.
Karfe 9 bayan sallan isha su Mummy suka shirya Rafi'ah tsaf, tinda aka fara shiryata take hawaye, bayan an gama Mummy ta kama hannunta zuwa dakin da Ummi take, Mummy ta damka hannunta cikin na Ummi ta ce "And pls don't cry daughter" daga haka ta fita a dakin, silently Ummi ta kira sunanta, ta dago idanta da suka cika da hawaye ta ce "Ki yafemin Ummi na" rungumeta Ummi tayi trying hard not to cry ta ce "Allah ya miki albarka daughter, Allah yasa auranki ya zama abin kwatance, i will miss u daughter" Rafi'ah ta fashe da kuka ta kankame Umminta, bude kofar dakin akayi Abba ya shigo, ya zauna gefensu ya fara magana cikin rarrashi, sosai ya lalla6a Rafi'ah hade da mata addu'an samun sa'ar aure, bayan nan shida Ummi suka mata nasiha sosai da sosai, a karshe suka mata addu'ah, duk sai jikinta yayi mungun sanyi, ta rungume Abba tana kuka, da kyar ya raba ta da jikinsa ya fita a dakin, Ummi ta kama hannunta suka fito, Mummy ce ta lullu6a mata alkyabbar jikinta suka sauko downstairs har lokacin kuka take da haka suka wuce da ita.
Minti 14 ya kaisu gidan Yusuf, aka shiga da Rafi'ah har dakinta, zuwa karfe 10 kowa ya watse sai Mummy, Gwaggo da Anty Salma, sosai da sosai suka kara mata nasiha, da zasu tafi gwaggo harda kukanta, Rafi'ah na kuka haka suka tafi suka barta, koda suka fito Jiddah na zaune aparlor taci uban kwalliya tana kallo, ko kallansu batai ba bare susa a rai zata gaishe su, Gwaggo sai mita take har suka fita, Mummy ce ta jasu zuwa gidanta dan a caan zasu kwana. Karfe 11 Yusuf ya shigo gidan, ajiye dayan take away yayi ya shiga da daya, a kwance ya samu Jiddah tayi rub da ciki, ya hau kan gadon ya dagota ya ce "How are u?" Ta fashe da kuka ta kankameshi, a hankali ya ce "Ga abinci na kawo maki, amma ai kinmin alkawari u won't cry ko?" hawayenta ta share ta koma gefe ta zauna, Yusuf ya kara matsawa inda take ya ce "Take ur food, and stop crying" kai kawai ta gyada masa, ya ajiye mata take away din akan bed side drawer ya ce "Good night" da ido ta bishi harya fita ya rufo mata kofar, ta fashe da kuka tayi wurgi da take away din. A kan dinning ya dauki ledan daya ajiye ya shiga part din Rafi'ah, tana zaune a parlor tana kallon wani series, tayi saurin dago kanta tana kallanshi, bude hannayensa yayi ta taso da sauri tayi hugging dinsa, ya rungumeta shima yana shafa bayanta ya ce "This was my dream always" Rafi'ah ta sake shi tana kallansa tayi murmushi, ya bata side hug yana kissing forehead dinta ya ce "I luv u" ta ce "I luv u more" hannunta ya kama suka shiga cikin daki, ta zauna akan stool ta dan turo baki ta ce "I'm missing my parent Doctor" durkuswa yayi ya kamo hannayenta biyu ya ce "Not when u have me dear, tashi muyi sallah" make kafada tayi ta ce "Ai nayi sallah a gida" ya ce "I know, wancen da wannan ba daya bane" ta ce "To amma ai nace maka nayi" ya ce "Kinyi kuka ba, ur eyes are red" sauke kanta tayi ta daina kallansa ta ce "I'm hungry kuma" babban rigarsa ya ajiye a gefenta ya ce "Idan kikai sallah sai kici abincinki" ta dan kalleshi sai kuma ya ce "Sai bacci" ta dan turo baki ta ce "Kafana ciwo yake i can't walk" tashi yayi ya dagata kamar Baby suka shiga toilet, da alwala suka fito yaja su sukai sallah sannan ta jawo take away din ta fara cin kazar dan yunwa takeji bama wasa ba, shi dai kallanta kawai yake yana murmushi harta gama, ta mike ta dauko cup ta sha fresh milk sannan ta shiga toilet tayi brush ta fito tana kallansa ta ce "Doctor" ya ce "Matar Doctor" tayi saurin rife fuskarta ta ce "Banaso" ya ce "Nine bakyaso" ta dan kalleshi sai ta ce "Tsokalan ne i don't want" ya kamo hannunta ta zauna gefenshi ya ce "Gist me, meyasa aka fasa event din?" Rafi'ah ta kwanta a jikinshi ta ce "Ikleemah ne ba lafiya" ya ce "Waye ita?" Ta ce "Wacce ta kai maka abinci first time kazo gidanmu" yaja hancinta ya ce "Kice wacce kike kishi da ita" ta dan yatsine fuska ta ce "Ni ina ruwana da ita" bakinshi ya daura akan nata tayi saurin komawa baya ta ce "Are u not sleepy?" Ya ce "Of course, kwana zamuyi muna hira yau" ta dan zaro ido ta ce "Oh oh, ni bacci nakeji" ya ce "Ni banajin bacci to, ya zamuyi" ta dan bude hannayenta alamun bata sani ba ta ce "Nasan kuma kanaji" ya ce "Banaji, i can spend the whole night without sleeping" dariya ta danyi ta koma baya ganin yana kokarin kamota, ya jawota jikinshi ya ce "Sai munyi hira fa" tana dariya ta ce "Then let me sleep sai na baka labarin" ya kara rungumeta ya ce "Bacci zakiyi" ta ce "I won't" kwantar da ita yayi yana jaan hancinta ya ce "Good" tayi shiru tana saan kwace jikinta ya ce "Wait,,, let me show u something" tsayawa tayi tana kallan phone dinsa da yake dannawa, kashe hasken wayar yayi sannan ya kashe wutan dakin, ta dan zare ido ta ce "Doctor" sai kuma ta yatsine fuska kamar xatai kuka ta ce "Pls stop".


*Thank u all for d du'ah nagode sosai* .
[8/8, 9:48 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_40_

Bayan kwana 3 da bikin Yusuf Anty Khadija tazo gidansu Rafi'ah, dai dai gate din tayi parking sannan ta fito ta shiga ciki, Mustapha ne kadai a compound din yana wanki caan gindin pampo, ganin bakuwace yasa ya wanke hannunsa ya karaso inda take tsaye, cike da ladabi ya ce "Ina yini Hajiya" a hankali take chewing gum din bakinta, kamar ba zata amsa ba ta ce "Lafiya, ina ne apartment din Amaryar gidan nan?" Mustapha ya nuna mata part din Anty Amina ya ce "Wancen ne Hajiya" ba tare data yi magana ba ta fara takawa zuwa apartment din, bayan ta hau balcony ta danna bell taja gefe ta tsaya. Few seconds aka bude kofar parlor, Anty Khadija ta dinga kallan Ikleemah data dawo kamar skeleton, dan ba karamin rama tayi ba, dan yatsine fuska tayi ta ce "Matar gidan na nan?" Ikleemah ta daga mata kai sannan ta bata hanya ta huce, bayan sun shiga ta turo kofar ta ce "Tana ciki bari na mata magana" daga haka ta haura upstairs Anty Khadija kuma ta nemi waje ta zauna. Da sallama ta bude dakin ta shiga, Anty Rahama dake kwance tayi saurin tashi zaune ta ce "Ikleemah bance karki hawo bane, kina ganin yadda ake fama amma ke bakyajin magana" karasawa tayi gefen mahaifiyarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, dafe kirjinta tayi a hankali ta ce "Ammi kirjina, wayyo Allah na" cike da damuwa Anty Rahama ta rungumeta ta ce "Allah zai baki lafiya Ikleemah, amma menene na haurowa bayan kinsan nima yanzu zan sauka" silently ta ce "Anty Amina ne tayi bakuwa" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "Koma wacece karki kara yin gangancin haurowa ba tare dani ba, bazaki kwala min kira ba" tana rife bakinta Anty Amina ta shigo dakin da phone dinta a hannu, karasawa wajensu tayi ta ce "Subhanallah, lafiya dai ko?" Anty Rahama ta ce "Ina lafiya Amina, daga kinyi bakuwa wai ta hauro sama kiranki, tana gani jiya sai da muka koma asibiti aka bamu wasu magungunan" Hannun Ikleemah Anty Amina ta kama ta ce "Haba Leemah, so kike ki kara jawo mana wani abun ne, ai yau kam jiki yayi kyau, maza muje kasa a dafa miki abinda kikeso" dagata tayi suka nufi kofar fita Anty Rahama tabi bayansu, a hankali suka dinga saukowa a stairs din saboda Ikleema, bayan sun shigo parlor Anty Amina ta dinga kallan Anty Khadija dake zaune tana danna wayarta. Kwantar da Ikleema tayi akan kujera ta zauna ta ce "Sannu da zuwa" Anty Khadija kallesu ta ce "Yauwa sannu" zama Anty Rahama tayi ta ce "Wa kike nema?" Anty Khadija ta danyi murmushi ta ce "Fatan an gama biki lafiya" harara Anty Rahama ta balla mata ta ce "Malama kinyi kuskure, ai ba anan akayi auran ba da zaki zo mana ban gajiya" murmushi Anty Khadija tayi ta ce "Nasani, nazo ne muyi magana da matar gidan nan" Anty Amina dake kallanta ta ce "Wace irin magana?" Anty Khadija ta gyara zama ta ce "To da farko sunana Khadija Bello, nice yayar Yusuf wanda ya auri 'yar gidan nan" dan murmushi Anty Amina tayi, bata san Anty Khadija ba amma tanajin labarinta dan ita tayi sanadiyyar raba Yusuf da Nusaiba, a hankali ta ce "Sannu da zuwa Hajiya Khadija, bari a kawo maki abin sha" daga haka ta mike, cikin saurin Anty Khadija ta ce "No, No, karki damu, ba zama nazo yi ba, nazo ne daman muyi magana, nasan kina daya daga cikin makiya auran nan" Anty Amina ta koma ta zauna tana kallan yayarta ta ce "Aiba ni kadai ba, kinga dani da yayata da 'yarta da Ummanmu da wasu daga cikin danginmu duk ba so muke ba, dalili kuwa shine basu dace ba, ga kuma cuta dake cin yarinyar" Anty Khadija tayi crossing legs dinta tana jijjiga key din mota ta ce "To kun samarwa kanku mafita?" Anty Rahama dake kallanta ta ce "Tukunna dai" juyowa Anty Khadija tayi ta kalleta sannan ta ce "Tukunna fa kika ce?" Anty Rahama ta ce "Ehh, bakiga muna da marar lafiya ba, wannan yarinyar da kike gani sanadin auran nan ta shiga wannan hali" Anty Khadija ta kalli Ikleema sannan ta ce "Allah ya kyauta, to muma dai ta bangarenmu basan auren muke ba, taya za'ai shekara daya da auran 'yar uwata ya mata kishiya, kishiyarma yarinya karama da bata san ciwan kanta ba, to ni ba dogon magana nazo yi ba, harka ce ta samu yadda zakuji dadi muma muji dadi, idan kun yanke shawarar ga card dina da komai ajiki" tana rife bakinta ta dauko card din ta ajiye akan kujera sannan ta mike ta ce "Sai anjimanku" Anty Amina ta ce "Allah ya kiyaye". Tana fita Anty Rahama ta kalleta ta ce "Anya kuwa yayarsa ce? Naga basa kama" Anty Amina ta ce "Ba iyaye daya suke ba, inaga a gidansu ya girma, amma kinsan mubi matarnan komai zai tafi dai dai" Anty Rahama ta ce "Nima naga alamun nasara, amma kinsan baza su so Ikleema ta shiga gidan ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To shine autan maza? Mu dai idan Rafi'ah zata fito na har abada ai ko ba komai mu mukai nasara, wallahi Ikleema ki kwantar da hankalinki namiji sai kin zama amma ki manta da Yusuf" shiru Ikleema tayi tana kallan Anty Amina, caan ta danyi murmushi ta ce "Na hakura Anty indai itama xata fito, wallahi a yanzu bani da burin daya wuce naga ta gama wulkanta" Anty Rahama ta ce "Gaskiya mu yarda kawai, kuma idan auran ya 6alle sai dai kinga tai ta zama a gida, daga nan suyi rayuwarsu muyi tamu" Anty Amina ta dauka card din tana kallan address din gidan ta ce "Zanje gobe na sameta nima" Anty Rahama ta ce "Bari naje na kira Umma na fada mata komai, daga haka ta mike ta wuce sama tana murmushi.
Gently ya dinga daga kafarsa yadda baxata ji footsteps dinsa ba, juyowa yayi yana kallan Rafi'ah dake kwance akan kujera, mistakenly kafarshi ta bugi center table tayi saurin mikewa tana kallan parlor, komawa yayi bayan kujera da sauri ya buya, ta dinga bin parlorn da kallo jin motsi, mikewa tayi ta leka bayan kujerar suka hada ido, ta turo baki ta koma kan kujera ta kifa kanta ta fara kuka, with lots of disturb ya tashi yana murmushi ya zauna gefenta ya ce "Yanzu fa zan dawo, i just want to buy something akan junction" kwace hannunta daya rike tayi ta ce "Nasan ai wajen matarka zakaje" jawota yayi jikinshi ya rungumeta ya ce "Noo, zan samo mana lunch ne" ta kara turo baki ta ce "Ni bazanci irin na jiya" ya shafa bayanta ya ce "What do u want then?" A hankali ta ce "Egg and

Please Login or Register in order to submit comment