Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bread with tea" ya ce "Meyasa kike shan tea da rana" ta ce "Ni ko yaushe ma idan inasan sha" ya ce "To bari na hada miki" daga haka ya kwantar da ita akan kujera ya fita a parlor, kamshi yaji a kitchen hakan yasa ya nufi nan, Jiddah ce tsaye a gaban gas tana soya kwai, ya rungumeta unexpected tayi saurin juyowa, suna hada ido ya manna mata kiss a kumatau ya ce "How are u, dazu da safe naje na samu kina bacci" ta ce "Fine" daga haka taci gaba da abinda take, yana rike da ita harta gama ta kashe gas din, a hankali ta ce "Zan wuce parlor na ka sakeni" ya danyi murmushi yana kallan egg din hannunta ya ce "Nima zanci" ta hade fuska ta ce "To muje parlor" ya ce "Noo, sai dai ki zuba min nawa" kallansa ta dingayi kafin ta sauke kanta, ya ce "Bazaki bani bane?" Ta ce "Nifa banci komai ba tin safe gashi yanzu karfe 2 ne, kuma idan na zuba maka baxai isheni ba, dama kai zaka ci saina baka, amma wallahi bazan hada abinci wata banza taci ba" Yusuf ya matseta a jikinshi ya ce "Yanzu dai bazaki bani ba kenan" ta ce "Na fada maka ai" ya ce "Zanje eatery na siyo mana abinci yanzu sai mu kara" make kafada tayi ta ce "Nifa bazata ci abincina ba" kin saketa yayi saima kansa daya kwantar a wuyanta, Tana kokawar kwacewa Rafi'ah ta shigo kitchen din, hakan yasa tayi collapsing a jikinshi tana dallawa Rafi'ah harara, ko kallansu batai ba ta wuce ta dauko flask da mug ta fito a kitchen din, kasa hada tea din tayi ta tsaya rike da mug din a hannunta, jin motsi yasa tayi saurin bude flask din zata debi ruwa Yusuf ya ce "What are u doing?" Kin kulashi tayi ta zuba ruwanta sannan ta rufe ta dauka liptopn akan dinning ta saka a ciki, daukan mug din tayi zata wuce part dinta ya riko hannunta ya ce "Sugar fa" juyawan da zatai ta zubo ruwan zafi a kafarta, ta saki kara ta jefar da cup din ya tarwatse a wajen, da sauri Yusuf ya dagata ya ajiyeta kan kujera yana kallan kafar, Jiddah ta dinga hararansu tana murguda baki, cikin rarrashi Yusuf ya ce "Sorry dear, bari na gyara wajen muje mu siyo abinci" hawayen idanta ta share ta ce "Bayan kasa na xubar da tea dina" dariya ya danyi jin ta kirashi da tea, ya san ko me za'ai ba iya sha zata tai ba, ya dagata suka nufi part dinta ya ce "Keda baki da lafiya menene naki na hada tea kuma" a hankali ta ce "Ba kabarni da yunwa ba kaje wajen matarka, meyasa bazan hada ba" ta turo baki ta kwanta akan kujera, murmushi yayi ya fita a parlor ya share inda mug din ya fashe sannan yayi mopping wajen, karasawa yayi gefen Jiddah ya ce "Zamuje eatery me zan kawo maki" girgiza masa kai tayi ta ce "Ni banasan komai" ya bata light kiss ya ce "I know u like shawarma, ita zan siyo maki" bata ce masa komai ya koma part din Rafi'ah, a tsaye ya sameta harta sa hijabi, ya ce "Bafa dake zanje ba" cushion din gefenta ta wurga masa ta ce "Kuma saina bika, ai jiya ma daka fita baka dawo da wuri ba" ya danyi murnushi ya ce "Zance naje ai jiya" ta kara turo baki ta nufi kofa ya bita da kallo yana murmushi, baisan meyasa idan yana tare da ita baya gajiya da kallan abubuwanta ba, key din mota ya dauka ya fita, a parlor ya sameta tsaye tana jiranshi, tayi saurin kama hannunsa ta ce "Harda yawo ma zamuje ko Doctor" ya ce "Eh" rungumeshi tayi tana murmushi ta ce "When are we coming back?" Ya ce "Till night" ta danyi tsalle ta ce "Yess" daga haka suka fita zuwa parking lot Jiddah ta bisu da harara. Sai lokacin Anty Khadija ta koma gida, bayan tayi parking ta shiga parlor da sallama, Umma dake kallanta ta ce "Sai yanzu" ta ce "Ehh na biya clinic ne" Umma ta ce "To ya kukai?" Anty Khadija ta ajiye veil dinta akan kujera ta ce "Kamar dai yadda Malam ya fada hakan take, suma inaga da abinda suka kulla a kasa, shine ya hadu da wanda muke ya kasa bada result me kyau, gaskiya Umma sun mungun tsanar yarinyar" Umma ta danyi murmushi ta ce "Barka, kinga yanzu haduwarmu dasu, zasu bar komai a hannunmu, sai muyi yadda mukaga dama" Anty Khadija ta ce "Hakane, kuma Umma baza suyi tinanin sake wani abun ba, balle su toshe mana hanyar namu aikin" Umma ta danyi dariya ta ce "Dama Malam yace min bamu kadai bane" daga haka Anty Khadija ta mike ta haura upstairs.
Yau ya kama sati 2 da bikin Rafi'ah, tin sassafe ta tashi ta shirya saboda Yusuf ya mata alkawari zai kaita gida yau, sosai tayi kyau ta yafa veil dinta akai, gefenshi ta koma ta zauna ta ce "Doctor" ya dauke kansa akan laptop ya juyo yana kallanta, ta ce "Pls na kwana mana kaji" dan zaro ido yayi ya ce "I can't sleep here without u, sai dai idan zaki bari jibi kwanan Jiddah sai kije ki kwana" kwantar da kanta tayi akan kafardarsa ta ce "Banaso" ya ce "To ba kwana, da daddare zan dauko ki" a hankali ta ce "Na yarda to, kuma sannan ni..." Shiru tayi ta fasa cewa komai, ya bata side hug ya ce "Now tell me, me zaki ce?" A hankali ta ce "Matarka ta daina shiga harkana tinda bataso mu zauna lafiya, kagani dazu na jona ruwa a kettle shine ta juyemin, hakama jiya ta daukemin Apple dina akan dinning kuma nayi magana tace wai in kwata idan zan iya" shiru yayi yana kallan lips dinta dake motsi, ta kai hannunta kan botton din rigarsa ta ce "Kuma Ummina tace karna sake nayi fada da ita, so kace itama ta daina min haka" bakinshi ya ajiye akan nata ya ce "Ai jiya na mata fada sosai, bazata kara ba" ta ce "To ai yau..." Shiru tayi jin bakinshi cikin nata, tayi saurin janye fuskarta ta matsa a gefensa ta ce "Ba yanzu zamu tafi ba" jinginar da kansa yayi akan gado ya limshe ido, kamar zatai kuka ta ce "Karfe 9 fa yanzu Doctor" bude idanuwansa yayi ya kamo hannunta ta dawo kusa dashi ya ce "Zanyi missing dinki Baby, i so much luv u, banasan naji bakya jikina" daga haka ya rungumeta tsam tsam a jikinshi, cikin rarrashi ta ce "I will miss u too, but ni kam ka tashi mu tafi" ya danyi murmushi ya ce "Tona tashi" ta kama hannunsa ta ce "Let's go" kashe laptop din yayi ya dauki phone dinsa da key din mota sannan suka fita. Jiddah na zaune a parlornsa tana shan tea, ya ce "Zan kaita gida na dawo" ta juya musu keya bata ce komai ba, har zasu fita ta ce "To meye damuwana da sai ka gayamin, aikin banza kawai" Rafi'ah ta juyo da sauri jin abinda ta fada, sai kuma tayi shiru, Yusuf ya bude kofar suka fita, yana jiwo tsakin da tai amma baice mata komai ba, har sukaje parking lot baiyi magana ba, bayan sun shiga ya tada motar Rafi'ah ta kamo hannunsa ta ce "Dan Allah ka daina fishi Doctor, i apologize on behalf of her" juyowa yayi yana murmushi yaja hancinta ya ce "I'm not angry dear" ta ce "But you're not smiling" ya ce "Ai nayi" ta ce "Ai saida nayi magana" shiru yayi ya danna horn gateman ya bude sannan suka fita, bayan sun hau titi ta dan kalleshi ta ce "I'm soryy to say ur wife doesn't have manners of talking".


_08103810398_



[8/10, 8:46 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_41_

Shiru Yusuf yayi ya ci gaba da driving dinsa, bayan few minutes ta dan kalleshi sannan ta ce "I'm sorry if i hurt u" still baice komai ba, sai bayan minti uku ya ce "Not at all, i don't feel like talking anymore" jinginar da kanta tayi jikin kujera ta limshe ido, har sukaje gida babu wanda ya kara magana a cikinsu, a kofar gida yayi parking yana kallanta ya ce "Come down" ta ce "Why not kayi parking a ciki to?" Ya girgiza mata kai kawai, ta ce "But Abba zaiyi magana yana nan fa" ba tare daya kalleta ba ya danna horn, bayan Mustapha ya bude gate din ya shigar da motar sannan yayi parking. Fitowa tayi tana kallansa ta ce "Bari na fadawa Ummi tare muke" ya girgiza mata kai, kamo hannunsa tayi cike da damuwa ta ce "My Doctor is anything wrong with u? Kona maka laifi ban sani ba" limshe idanuwansa yayi ya ce "Uhm~uhm, baki min komai ba, kawai naji banasan magana ne, may be..." Shiru yayi ya bude idanuwansa yana kallanta, ta kai hannunta face dinsa ta ce "May be what?" ya girgiza kai ya ce "I'm having Headache kuma haushi nakeji" murmushi tayi ta rungumeshi ta ce "Allah ya baka lafiya" a hankali ya ce "Ameen" tana dago kanta ta hango Anty Amina da Anty Khadija suna tahowa, sai shewa suke suna tafawa, yadda take kallansa shima Yusuf haka yake kallansu, har suka karaso inda suke Rafi'ah na rike da hannun Yusuf dake zaune, ta dan sunkuyar da kanta ta ce "Ina kwanan ku" Anty Khadija ta washe baki tana kallanta ta ce "Amarya har kin fara fita ne?" Kafin tayi magana Anty Amina ta ce "Haba sati biyu fa, ai yaci ace tazo taga mutanen gida" Anty Khadija ta karasa wajen motar tana kallan Yusuf ta ce "Bashi da lafiya ne?" Rafi'ah da kanta ke kasa ta dan sake hannunsa ta ce "Ehh, kanshi ne yake ciwo" sai lokacin ya dago kansa yana kallansu ya ce "Good morning" a tare suka amsa gaisuwar, Anty Khadija ta ce "To Allah ya sauwake" daga haka suka nufi inda motarta take, murya caan ciki ta kalli Anty Amina ta ce "Kingani ko, alamu sun nuna abin ya fara aiki, aina fada miki daga yau komai zai dai dai ta" Anty Amina ta kamo hannunta ta ce "Gaskiya babu abinda zan iya saka miki dashi Khadija, Amma dama nayi alkawarin idan komai ya dai daita akwai filina da zan mallaka miki, nasan dai watakila kinfi karfinsa amma ai kyauta da dadi" Anty Khadija tayi murmushi tana kallanta ta ce "Gaskiya naji dadi sosai, yanzu dai ki koma komai ake ciki zan kira ki" Anty Amina ta daga mata hannu sannan ta koma apartment dinta ba tare data kalli inda su Rafi'a suke ba, dago kansa yayi ya ce "Move, zan rife kofar i'm going home" ta marairaice ta ce "Baza ka gaishe su ba?" Ya girgiza kai ya ce "Some other time, i can't stay here" matsawa tayi ya rufe kofarsa sannan ya tada motar yayi horn, juyawa tayi duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinsu, tana hawa balcony ta juyo taga harya fita a gidan, bell ta danna sannan taja gefe ta tsaya, bayan minti 2 aka bude kofar, kallan budurwar data bude kofar tayi sannan ta shiga parlorn, Rafi'ah na murmushi ta rungume Umminta dake zaune akan kujera, Ummi ta shafa bayanta ta ce "How are u daughter?" a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce "I'm fine Ummi, ina Abba?" ta ce "He's upstairs" daga haka ta mike ta ce "Abdul fa?" Ummi ta ce "Yana dakinshi" upstairs ta wuce tana murmushi ta ce "Let me see Abba first" tana shiga dakinsa ta sameshi yana zaune akan stool, Abba yayi murmushi ganinta ya ce "Is this my Mum?" Itama murmushi tayi ta zauna a kan carpet ta ce "Ina kwana Abba" ya ce "Lafiya kalau Mamana how are u and everyone?" Ta ce "All fine Abba, tare muka zo amma kanshi na ciwo shine ya wuce gida" Abba ya ce "Subhanallah, i will call him ltr, Allah ya sauwake" ta ce "Ameen" mikewa tayi ta ce "A huta gajiya Abba" ya ce "Alright Mother" tana fitowa a dakin ta shiga dakinta, yana nan yadda ta barshi sai kamshi yake, ta kwanta akan gadon tana murmushi ta ce "I missed u bed" daga haka ta mike ta fita a dakin ta sauko kasa. Abdul na gefen Ummi yana taya ta arranging papers, ya dan zaro ido ya ce "Anty" ta rungumeshi ta ce "Ya kake, tashi min a gefen Ummina" dariya Abdul ya dinga yi yana kallanta ya ce "Ai ke mun kyautar dake, yanzu ni kadai ne ko Ummi?" ta shafa kansa ta ce "Exactly Babana, tashi dai ka bata wajen tinda ita bakuwa ce" turo baki Rafi'ah tayi jin ance mata bakuwa, Side hug Ummi ta mata ta ce "So ya kuke, i hope everything is going fine?" A hankali ta Jinginar da kanta ajikin mahaifiyarta ta ce "Lafiya kalau, amma ba shida lafiya ne" Ummi ta ce "Subhanallah, meya sameshi?" Cike da damuwa ta ce "Ciwan kaine, dama fa akan da yamma idan yazo daukana zamuje gidan Mummy" Ummi ta ce "Ki bari next time sai kije kawai" a hankali ta ce "Toh, mai aiki kika dauka Ummi?" Ta ce "Ehh, ko karna dauka" Rafi'ah tayi murmushi ta ce "A'a ai aiki zai maki yawa" Ummi tayi murmushi tana shafa kanta ta ce "I hope bakya saan jikin ki nan" ta ce "Noo, da sassafe nake komai Ummi" Ummi taja hancinta ta ce "Good kici gaba da haka kinji first born, watarana zaki ga amfaninsa" a hankali ta ce "Insha Allah" daga haka ta mike ta wuce kitchen.
Da yamma Rafi'ah na zaune a dakinta duk ta shiga damuwa, ta kira Yusuf yafi a kirga amma ko daya baiyi picking ba, bude kofar dakin akai, tayi saurin juya kanta saboda idanta duk yayi jaa sakamakon kuka data yi, karasowa kusanta Ummi tayi ta ce "Idan bazaki tafi ba in kira Abbanki in fada masa, sau uku ina aiko Saudatu ta kira ki amma kinyi zamanki" mikewa tayi a hankali ba tare da kalli Ummi ba ta dauki Hijab har kasa cikin sauran kayanta sannan ta nufi hanyar fita, Ummi dake kallanta ta ce "Wait Fatima, wani abu na daminki ne?" A hankali ta girgiza kai, Ummi ta ce "Toh Allah ya kiyaye kije Mustapha ya kaiki, Abba kuma kya kirashi dan dawowarsa sai dare" slowly ta share hawayen daya sakko mata, ga zafin barin gida, ga damuwarta na halin da Yusuf yake ciki, gani take kamar yana nan kwance ba lafiya, cikin muryar kuka ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya, na tafi" cike da tausayin Rafi'ah Ummi ta ce "Allah ya kiyaye" daga haka ta wuce dakinta. A hankli ta sauko a stairs din ta fita zuwa parking lot ta shiga mota, Mustapha yaja motar suka tafi, har sukaje gida ba tai magana ba, sai da yayi parking ta ce "Thank u" daga haka ta fito ta shige gate. Da sauri ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar, still ta tsaya tana kallan Yusuf dake kwance yayi pillow da cinyar Jiddah, tayi saurin kauda kanta duk suka bita da kallo harta wuce part dinta, tana shiga ta turo kofar ta durkusa a wajen ta fara rera kuka, kusan awa daya tana zaune a bakin kofa kafin ta mike ta shige dakinta ta rufo kofa, tana nan zaune har akai magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah har akai isha tana zaune akan sallayar, ta mike tayi isha sannan ta dauki towel ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta samu Yusuf a bakin gado yana zaune da laptop a gabansa, sauke kanta tayi ta nufi inda kayanta suke ta dauki night dress sannan ta koma toilet ta shirya, scarf ta saka bayan ta fito sannan ta karasa gefenshi ta zauna, a hankali ta ce "How are u now?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Better" tayi shiru tana kallansa, dago kansa yayi suka hada ido tayi saurin sauke kanta ta ce "Dan Allah kayi hakuri idan na maka laifi Doctor" girgiza kai ya danyi kafin ya ce "How many times zance miki bakimin laifi ba, ko kin daina fahimtar magana ne" hawaye ne tap a idanta jin yadda yayi maganar, cikin muryar kuka ta ce "U never shout at me, meyasa zakamin tsawa yau" hannunta ya kamo ta matso kusa dashi ya rungumeta very light, dan bai bari sun hada jiki sosai ba, ya ce "I'm sorry, i don't know what comes over me, haushin kowa nakeji yau, especially..." Shiru yayi yana rike da ita, ta dan sake shi tana kallansa ta ce "Ni ko?" Daga haka ta fashe da kuka, matsowa yayi ya kara rungumeta sosai ya ce "Bance ba, but haushi nakeji kawai" cikin kuka ta ce "Kayi addu'a mana" ya ce "Nayi" daga haka ya saketa ya kwanta akan gadon, share hawayen idanta takeyi tana kallansa ta ce "Or is it because nace matarka bata iya magana ba da safe?" Shi dai kallanta kawai yake, caan ya mike ya dauki pillow ya koma parlor ta bishi da kallo, duk yadda taso ta hakura karta bishi kasawa tayi, bayan 30 minutes ta leka parlorn ta sameshi saman kujera har yayi bacci, a nan wajen ta sulale ta fara kuka sosai.
Washegari da sassafe ta tashi ta hada masa breakfast sannan tayi wanka, tana shigowa dakin ta sameshi ya shirya, ta danyi kasa da kanta ta ce "Good morning" kai kawai ya daga mata, daga haka ya dauki briefcase dinsa da statescope zai fita ta ce "Breakfast din yana kan dinning" ya girgiza kai sannan ya fita a dakin, bin bayansa tayi har suka fito main parlor, ya gama saka takalmi sannan ya dauki komai nasa zai fita ta ce "Doctor breakfast din fa" ba tare daya kalleta ba ya fice ya rufo kofar, Jiddah dake zaune akan dinning ta sheke da dariya, duk yadda Rafi'ah taso kar tayi kuka amma hakan bai yuwu ba, ta fashe da kuka ta koma part dinta, jikinta har rawa yake ta zube aKan gado tana kuka me cin rai. Haka Rafi'ah taci gaba da hakuri, tin daga ranar duk maganar da zatai masa sai dai ya daga kai koya girgiza mata kai sai kace kurma, amma idan da Jiddah ne sukanyi hira wani lokaci, wani lokaci kuma zai kulata amma ba sosai ba, Rafi'ah kuwa babu abinda yake hadasu, yanzu a parlor ma yake kwana indai a dakinta yake, wani lokaci tayi kuka harta godewa Allah, wani lokaci kuma tayi hakuri amma ko kadanne saita zubar da hawaye, a haka har ta cika wata daya a gidansa duk ta kara ramewa tayi farii sosai saboda damuwa, kuma koda wasa bata gayawa kowa a gida ba. Ranar Saturday da yamma tana zaune a main parlor aka fara knocking, ta mike a hankali ta karasa kofar sannan ta bude, rungumeta Khairiyya tayi ta ce "Oyoyo Anty" itama rungumeta tayi tana kallan Ammi ta ce "Sannu da zuwa Ammi" Ammi ta shigo parlorn tana murmushi ta ce "Sannu Fatima" Rafi'ah na rike da hannun Khairiyya ta ce "Have a seat Ammi" Ammi ta zauna akan kujera, zama Rafi'ah tayi a kan carpet ta ce "Ina yini?" Ammi ta ce "Lafiya kalau Fatima, fatan duk kuna lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah Ammi" mikewa tayi ta shiga kitchen Khairiyya ta biyota, abinci ta kai wa Ammi da fruits sai dambu da Mummy ta aiko mata jiya, bayan ta gama jere mata ta dauko fanta guda biyu da cups ta ajiye mata, Ammi ta danyi murmushi ta ce "Sannu da kokari" ita dai murmushi kawai take kanta na kasa, Khairiyya ta zuba abincinta ta fara ci, Rafi'ah na kallanta ta ce "Yaushe zaki zo mana hutu?" Khairiyya ta ce "Soon Anty, muna gama exams zanzo, jss3 zan shiga fa" Rafi'ah ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Masha Allah, i wish u all d best"
"Shiru Rafi'ah baku zo mana ba muma bamu zo ba" dagowa tayi jin muryar Ammi, with smile on her lips ta ce "Ammi ai yanzu baya dawowa da wuri sai yamma sosai shiyasa, kuma har weekend fita yake" kafin Ammi tayi magana aka bude kofar, ya shigo yana kallansu sannan ya nemi waje ya zauna, silently ya ce "Sannu da zuwa Ammi, ina yini?" Ta ce "Lafiya kalau, yanzu nake tambayarka ai, baka kaita ba kai baka zo ba muma kuma shiru" dan shafa kansa yayi yana murmushi ya ce "Wallahi Ammi aiki ne yamin yawa yanzu, amma insha Allah zamu zo" ta ce "To Allah ya kaimu" Khairiyya na kallansa ta ce "Yaya ina yini" ya ce "Lafiya Ammina, karfa ki cinye mana abincin mu" ta danyi murmushi ta ce "Ai Anty Fatima zata dafa maka wani" kallan Rafi'ah dake zaune ya danyi sannan ya dauke kai ya ce "Sai dai ke ki dafa min ai" ta danyi murmushi taci gaba da cin abinta, Yusuf ya ce "Ammi ke ba xaki ci abincin ba?" Ta ce "Alhamdulilah Yusuf na koshi" ya ce "Sameer ya tafi ko?" Ta ce "Ya tafi Dubai sai bayan wata biyu kuma" Yusuf ya ce "Ayyah, ya sameni a office jiya ai, so munyi sallama" ta ce "Haka yake cemin, shine nace ai yau bari nazo tinda kunki zuwa" cire hular kansa yayi ya ce "Zamuzo Ammi, Jiddah taje gida za tayi kwana biyu" Ammi ta ce "To Allah ya dawo da ita lafiya, na zata ai tana ciki ta ki fitowa ne" ya dan zaro ido yana murmushi ya ce "Never, ai ba zata jiki tayi shiru ba" Ammi ta ce "Hakan kake gani" daga haka ta kalli Khairiyya ta ce "To idan kin gama ciye~ciyen ki tashi mu tafi, dan idan magrib yayi driving wahala yake min" Yusuf ya ce "Har yanzu Ammi" ta ce "Har gobe kuwa Yusuf bana samun nutsuwa" daga haka ta mike, tashi Rafi'ah tayi ta ce "Mungode Ammi" Ammi ta ce "Ba komai, sai kunzo din" Khairiyya ta kama hannun Rafi'ah ta ce "Anty sai na zo hutun" Rafi'ah ta ce "Sai kinzo" Hijab dinta ta dauka akan kujera ta saka sannan tabi bayansu, har mota suka rakasu, Yusuf nata murmushi har suka tafi, juyowa yayi zai koma cikin gida suka hada ido, sai da kirjinta ya buga tayi saurin dauke kanta, ita tama manta raban da yayi mata murmushi ko magana, kusan sati uku da kwanaki kenan, sai daya shige ya rufo kofa sannan ta shiga itama. Da dare Yusuf na kwance a parlor ta fito sanye da Hijab ta zauna gefensa, a hankali ta ce "Doctor" ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce "Gobe zanje follow up clinic, maganina ya kusan karewa" sauke idansa yayi a kanta ya ce "Wa zai kaiki?" Sai yau ya mata magana bayan sati uku da suka wuce, ta kauda kanta gefe hawaye taap idanta ta ce "Cab" maida kansa yayi gefe ya limshe ido, ta tashi ta koma daki tana goge hawayen idanta, dama tasan yanzu duk duniya ba wanda ya tsaneta kamar Yusuf, babu abinda yake 6ata mata rai irin rashin magana da yake mata, fashewa tayi da kuka ta jawo wayarta akan drawer zata kira Mummy, kawai kuma ta fasa ta gefar da wayar a kasa, kuka sosai take tana kiran sunan Abbanta, da tasan haka rayuwar aure yake da tin tini bata yarda da Yusuf tayi aure ba, gaba daya yanzu ta tsani kanta da komai nata, cikin kuka ta ce "Nina

Please Login or Register in order to submit comment