Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

shiga dakin Saudatu mai aikinta, tana zaune akan sallaya tayi shiru itama, duk da ba wani zama tayi da Rafi'ah ba, jiya data ganta sai da tayi kuka, haka kawai takeji tana san yarinyar, jin an rufe kofar tayi saurin jaa baya tana kallan Ummi ta ce "Ina kwana Ummi" Ummi ta ce "Lafiya kalau, jiya mun dawo kinyi bacci" ta ce "Ehh nayi bacci, ya Anty Rafi'ah da jiki?" Ummi ta ce "Da sauki, yanzu zamu koma, da rana ki dafa komai ma kici, ba sai an kai asibiti ba" Saudatu ta ce "Toh, Allah ya kara mata lafiya" daga haka Ummi ta mike ta ce "Ameen" tana fita a dakin Abba na sakkowa, ta dauka basket din suka fita zuwa parking lot, Mustapha ya musu ya mai jiki sannan ya bude gate suka fita, sosai Abba ya dinga kwantarwa Ummi hankali a mota, ba irin misalan da bai mata ba dan hankalinta ya kara kwanciya, kuma Alhamdulilah ta rage fargaban da takeji sosai. Bayan sunyi parking ta dauko basket din suka shiga ciki, Abba ne ya bude kofar dakin ya shiga Ummi ta bishi a baya, kan gadon duk suka nufa, tana nan zaune da hijab a jikinta, da alamu salla ta gama idarwa, Ummi dake kallanta ta ce "How are u daughter" ta dan goge hawayen idanta ta ce "Alhamdulilah Ummi" daga haka ta kalli Abba da shima kallanta yake ta ce "Ina kwana Abba" ya ce "Lafiya kalau Mamana, ya jikin ki?" Ta ce "Da sauki Abba" nan suka gaisa da Mummy ma, Abdul ya gaishe dasu shima, Rafi'ah dai na zaune akan sallaya ta lula duniyar tinani, idan ta tuna abinda Mummy ta fada mata sai ziciyarta ta buga, wai itane dauke da cikin Yusuf, jin Ummi na ta6a ta yasa tayi saurin zabura, lokaci daya hawaye ya shiga zirya a idanta, Ummi ta sauke ajiyar ziciya ta ce "Ko so kike na koma gida?" Ta girgiza kai a hankali tana share hawayen idanta, she can't believe that she's pregnant, ta kara rufe idanta da hijab dinta ta fara kuka tina ko shekara 18 bata cika ba, saura two months ta cika shekara 18, bayan Abba ya fita tare da Abdul Mummy ta ce "Aiba a kanki aka fara saki da ciki ba, kinganta harta yi shiru tindana gaya mata tana da ciki ta daga hankalinta" Ummi ta shafa kanta cikin rarrashi ta ce "Stop crying daughter, duk abinda kika gani jarabawace daga Allah, watarana sai labari, ki daina damun kanki ko dan cikin dake jikinki ma" rungume Ummi tayi ta ce "Ina kokarin yin hakan Amma Ummi bana iyawa" Ummi ta ce "Zaki iya Rafi'ah, just forget about Yusuf, ki manta da kin ta6a rayuwa dashi" kwanciya tayi liif a jikin Ummi tana sauke ajiyar zuciya. Karfe 8 Ammi ta karaso asibitin da warmers din abinci, sosai taji dadi ganin Rafi'ah nacin dan wakenta sosai, kunu ne dai bata wani sha ba, da azahar Mami ma sukazo ita da Sadeeq, minti 10 sukai suka koma gida, wajajejn karfe 2 su Umma dasu Anty Rahama suka iso, carton din maltina Umma tasa aka siyo aka ajiye musu. Kwanan Rafi'ah 3 a asibitin aka sallameta bayan an bata magunguna sabi, by now ta dan sake saboda kullum Ameera na zuwa asibiti ita da mamanta, anan take kara kwantar mata da hankali, Mami ma kullum sai tazo ta kawo abinci, haka Ammima itakam safe rana dare sai ta kawo abinci duk da hanata da Ummi take amma bata fasawa, kafin a sallameta 'yan uwa da abokan arziki su kaita zuwa dubata, Yusuf ya sha tsinuwa a gun Gwaggo ba kadan ba, motsi kadan saita tsine masa. Washegarin randa aka sallameta tana zaune a daki ita da Ameera, gaba daya ta damu dan Ameera sallama ke mata zata tafi zaria makaranta ta samu admission, Rafi'ah ta fashe da kuka ta ce "Zanyi missing dinki Ameera, Allah bazanji dadi ba" Ameera ta share mata idanta ta ce "Duk bayan sati biyu zan ringa zuwa, nidai kawai ki daina damuwa ki kula da kanki sosai" Rafi'ah ta kamo hannayenta ta ce "Insha Allah friend, Allah ya bada sa'a yasa ki fara a sa'a" Ameera ta ce "Ameen Fatima" duk jikinta sanyi yayi ganin yadda Rafi'ah ke share hawaye, jin hawaye na zuwa mata tayi saurin daga mata hannu ta fita a dakin, a corridor ta goge idanta sannan ta sakko downstairs, tayi wa Mummy da Ummi sallama, Ummi ta mata fatan alkhairi sannan ta bata leda me dauke da tirare da sleeping dress, da kyar ta kar6a sannan ta kara musu sallama ta tafi, Ummi ta kalli Mummy dake zaune ta ce "Anty bazaki koma gida ba, ai jikinta yayi sauki?" Mummy ta ce "Anjima zan tafi Zainab, Jawad ma yau zai dawo" Ummi ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya", tashi Ummi tayi ta ce "Bana leka Rafi'ah ko zata ci abinci" Mummy ta ce "Ohk to" daga haka Ummi ta dauki warmer da plate ta haura sama.


_ALHAMDULILAH, anan na kawo karshen littafin *SHARIK HAYATI* part one, ina rokon Allah ya yafemin kuskuren danayi ya kuma bani ikon rubuta abinda shine dai dai_ 🙏🏻

_Special thanks to the members of my Groups, wallah u people are the best, ina sanku sosai da sosai 💞💞_ _And again my Kk 🥰 i luv u so much sweetheart, u are always supporting me right from the beginning, billahil azeem ina sanki Dije ta, my Jiddah soyayyarki is endless_ 😍, _AISHA SHEHU can't forget with u sister, Fatima is thanking u again and again Allah ya raya Na'eem ya bashi ilimi me inganci_ 😇, _Then my FANS 😇 Billah ina sanku a duk inda kuke sisters, only God knows how much i luv u people, ina muku fatan alkhairi duniya fil akhirah 😘_ .

_08103810398_
/n An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya


Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment