Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jawowa kaina, Ummi dan Allah ki yafemin, bansan haka zai faru dani ba, i'm tired with this misrable life na gama gajiya" shiru ta danyi jin an bude kofar dakin, ta dago kanta a hankali ganin wanda zai shigo.

*Gashi harda na jiya 🤗 Sorry for keeping u waiting.*

_08103810398_
[8/11, 1:23 PM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_42_

A hankali Jiddah ta tura kofar dakin ta rufe, ta kama kugu tana murmushi ta ce "Dama duk macen da tasan inda yake mata ciwo bai dace ta shigo gidan wata ba, gashi kin shigo banda azaba babu abinda kike sha" kwashewa da dariya tayi tana tafa hannu, Rafi'ah ta kauda kanta tana share hawayen idanta, Jiddah sake cewa "Gara ki tattara naki ya naki kibar mana gidanmu kafin abu yayi tsanani, dan yanzun nan ya gama gayamin ya tsaneki fiye da kowa a duniya" tana fadin haka ta juya ta fice a dakin. Tsabar bakin ciki kasa kuka tayi ta kifa kanta akan gado numfashinta yana neman sarkewa, a hankali ta jawo wardrobe din dake gefenta ta dauko drugs dinta, bayan ta balla ta mike ta dauki guntun pure water ta hadiye maganin, komawa kan gadon tayi ta kwanta tana addu'a ko zata samu saukin abinda take ji. Washegari da tinda ta tashi ta gama abinda za tai ta shirya tana jiran Yusuf saboda clinic da zata je, shiru yana dakin Jiddah ko lekowa baiyi ba, Rafi'ah na zaune a parlor Jiddah ta fito da plate din abincin a hannunta, sai rakwarkwasa take tana murmushi, bayan ta ajiye plate din ta koma part dinta tana dariya, shiru har bayan azahar Yusuf bai fito ba, Rafi'ah dake kwance ta jawo phone dinta tayi dialing number Ameera, yana shiga ta dauka ta ce "Amarya, how are u?" Cikin sanyin murya Rafi'ah ta ce "Fine, where are u now?" Ameera ta ce "I'm at home, do u need something?" Limshe ido Rafi'ah tayi ta ce "I want to see u Khadijah" Ameera ta ce "To bari nazo yanzu" hanging wayar Rafi'ah tayi ta share hawayen idanta ta koma ta kwanta. Bayan minti 15 taji ana knocking, ta mike ta fita a dakin, tana bude kofar Ameera ta rungumeta ta ce "I missed u friend, how are u?" Murmushi kawai Rafi'ah tayi ta kama hannunta ta ce "You're welcome" daga haka suka shiga part dinta, har dakin Rafi'ah ta shiga da ita suka zauna, Ameera dake kallanta ta ce "Kinyi rama and kin kara fari, is anything wrong?" Tare hawayen idanta takesan yin amma hakan bai yuwu ba, ta rungume Ameera ta fashe da kuka ta ce "I'm tired Ameera, na gaji da zaman auren nan kuma" zaro ido Ameera tayi tana kallanta ta ce "What are u saying Rafi'ah? Indai matsalar Jiddah ce ba sai kin shiga harkarta ba" Rafi'ah ta hau girgiza kai cikin kuka ta ce "No it's Doctor, Ameera bansan da wani ido zan kalli Ummina na fada mata na gaji da auren Yusuf ba" kara fashewa tayi da kuka ta sulale kasa ta zauna akan carpet, Ameera ta sauko itama tana kallanta ta ce "Pls explain further, ban gane abinda kike fada ba". Share hawayen idanta tayi ta ce "Ameera Doctor ya tsaneni, tin satina biyu a gidan nan nake ganin ba dai dai ba, baya min magana, baya cin abincina, baya min komai da kika sani, ko dakina baya shigowa yanzu" daga haka ta fashe da kuka ta turo baki ta ce "Wannan ma shiya dama ai, ni babban damuwana daina min magana da yayi, i'm in pain Ameera, my heart is always beaten, it hurts me morethan u know Ameera" ganin yadda take kuka yasa idan Ameera ma ya ciko da hawaye, gaba daya ta shiga damuwa itama, ko a mafarki bata tinanin Yusuf zaiyi abinda Rafi'ah ta fada ba, amma gashi a zahiri tin aure na wata daya matsaloli iri iri, lallai yau ta yarda maza abin tsoro ne.
Share hawayen daya gangaro mata tayi ta dago Rafi'ah dake kuka kamar ranta zai fita ta ce "Have u tell anyone?" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "Noo, dan Allah karki fadawa kowa banasan hankalinsu ya tashi, and beside that inasan mijina, no matter how zan zauna dashi har karshen rayuwata" Ameera ta shiga share mata hawayenta ta ce "No Fatima, u have to tell someone ko zaki samu mafita, u can't be hurting yourself this much, bayan haka ma bakya tinanin ciwanki ya tashi" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Dan Allah promise me u won't tell anyone, Khadija kar ki bari wani yaji zancen nan, pls keep my secret only u Ameera" fashewa ta karayi da kuka jikinta na rawa, Ameera dake kuka itama ta ce "Ohk i promise u that i will keep this secret alone, amma meya kamata muyi yanzu?" Rafi'ah ta saketa ta fara goge hawayen idanta ta ce "U help me praying Ameera, nasan dai tinda nake ban ta6a cutar wani ba, so Allah ba zai bari a cuceni ba nima" Ameera ta ce "Insha Allah zan taya ki da addu'a, kuma zaki cinye wannan jarabawar da yardar Allah" Rafi'ah ta share mata idanta ta ce "Nagode Ameera, dama inasan in baki hand card dina na asibiti, sai ki kar6omin drugs dina, zan kira Doctor Hisham na gaya masa" Ameera ta ce "Ohk ba komai zan kar6o maki yanzu" tashi Rafi'ah tayi ta dauko hand card dinta cikin jaka ta mikawa Ameera ta ce "Zakiga office dinsa da sunansa a jiki, zan kirashi sai na masa bayani" ta ce "To shikkenan, kinci abinci ne?" Girgiza kai Rafi'ah tayi ta ce "Zan dafa anjima naci" Ameera ta yafa veil dinta ta ce "Ohk saina dawo" daga haka ta fita a dakin, kwanciya Rafi'ah tayi ta kira Dr. Hisham, bayan sun gama wayar taja blanket ta rufu har kanta, dan wani sanyi take ji yana ratsata har cikin jikinta. Tana nan kwance har Ameera ta dawo, Rafi'ah na jin an bude kofar ta mike zaune, Ameera ta karasa kusanta ta ce "Are u ok?" Ta daga mata kai kawai, Ameera ta ajiye mata ledan drugs din ta ce "Yace kinsan yadda kike sha ko?" Ta daga mata kai ta ce "Yes i know" daga haka Ameera ta mika mata wani leda mai takeaway a ciki ta ce "Ga abinci na siyo miki, u don't have to cook" murmushi Rafi'ah tayi ta ce "Thank u so much" Ameera ta mike ta ce "I'm going Fatima, Abbana ya kirani da ina hanya, idan kina bukatar wani abu u call me, ko Sajeed zan bawa ya kawo maki" Rafi'ah ta kamo hannunta ta ce "Thank u so much Khadijah, i don't know how much to thank u friend, nagode sosai" Ameera ta ce "Mention not, sai anjima" daga haka ta fita a dakin, tana fita Rafi'ah ta share hawayen idanta sannan ta koma ta kwanta. Ba ita ta shi ba sai kusan la'asar, ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, gaban mirror ta zauna ta shafe jikinta ta tashi tasa kaya, tayi kyau sosai sai dai kana kallanta kaga rama sosai da damuwa a tattare da ita, takeaway din da Ameera ta siyo mata ta bude, tana kallan abincin ta fara yatsina fuska, spoon ta dauka ta debi fried rice din ta kai bakinta, da sauri ta zubar jin yadda zuciyarta ke tashi, ta rufe takeaway din ta ajiye a gefe sannan ta mike ta shiga toilet ta wanke bakinta ta dawo ta kwanta.
Da dare kasa kwanciya tayi saboda yunwa dake daminta, ta fito a blanket ta dauka himar dinta ta saka ta fita a dakin, ba kowa a main parlor sai dai tana juyo muryarsu a parlorn Jiddah, ta dan turo baki ta shiga kitchen, tsayawa tayi tana bin kitchen din da kallo ko zata ga abinda ranta yake so, flour ta duba taga babu, ta tsuguna tayi tagumi, babu abinda take kwadayi taci sai dan wake, mikewa tayi ta bude fridge ta dauki fanta da glass cup ta koma part dinta, ta kai minti 6 tana kallan Fantan kafin ta zuba a cup ta dauka ta kai bakinta, tin kafin ta hadiye ta fara kakarin amai, tayi saurin zubar dana bakinta sai sauke numfashi take tana kallan sauran fantan dake cikin cup din, mikewa tayi ta shiga toilet ta wanke bakinta sannan ta fito ta dauki bottle din fantan ta jefar ta window, sauran na cup dinma ta zubar dashi sannan ta ajiye cup din akan drawer ta neki waje ta zauna.
Haka Rafi'ah take ta faman shan wahala ita kadai har tsawon sati uku, wani lokaci ta samu abinda takeso wani lokaci idan babu ta hakura tayi kuka ta share ko kuma ta kira Ameera, kullum sukai waya da Ummi ko Mummy bata ta6a fada musu abinda ke faruwa, laulayi take sosai amma ko kadan bata kawowa kanta ciki ne da ita ba, ga mungun zazza6i da take kwana dashi duk dare, duk ta kara ramewa tayi mungun haske, ita kanta batajin nauyin jikinta saboda ramar da tayi. Ranar Monday da Yamma tana zaune a bakin gado ta buga uban tagumi, damuwarta bai wuce kiran da Mummy ta mata ba na cewa zata zo, duk sanda ta tuna sai kirjinta ya buga, tana nan zaune wayarta ya fara ringing, ganin Mummy ce yasa ta danyi jiim kafin ta dauka, Mummy ta ce "Kina jina Fatima?" Ta ce "Ehh Mummy" ta ce "Kiyi hakuri na fasa zuwan, kinga Ikram ne ba lafiya yanzu haka muna hanyar asibiti" wani 6oyayyen ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce "Ohk ba komai Allah ya bata lafiya" Mummy ta ce "Ba damuwa ki gaishe da Yusuf din" daga haka tayi hanging call din, tana nan zaune aka danna bell, ta mike a hankali ta zura hijabi har kasa sannan ta fita ta bude kofar, Khairiyya ta rungumeta ta ce "Anty" Rafi'ah na murmushi ta ce "You and who?" Ta ce "Driver ya kawoni" Rafi'ah ta tura kofar ta kama hannunta suka shiga ciki, a parlor suka zauna Khairiyya ta ce "Ina yini Anty" Rafi'ah ta ce "Fine, how is Ammi?" Ta ce "She's fine, tace na gaisheki wai yaushe zaki sake zuwa" Murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ita gidansu ma sau biyu kawai taje, Khairiyya ta ce "Anty jiya na gama exams dina, jss3 zan shiga next term" Rafi'ah ta gyara mata himar dinta ta ce "Good, Allah ya sanya alkhairi, kiyi karatu sosai" Khairiyya ta ce "Sure, i want to be a medical doctor just like Yah Yusuf" Rafi'ah ta ce "Allah yasa to" mikewa tayi ta ce "Let me get something for u" Khairiyya ta ce "Anty indomie zanci" Rafi'ah ta juyo tana kallanta ta ce "Can u cook?" Ta ce "Yess ina dafa indomie, white rice, spaghetti, macaroni and also..." Da hannu Rafi'ah ta nuna mata kofa ta ce "To kije ki dafa, banasan surutu" Khairiyya ta danyi murmushi ta mike ta ce "Anty are u sick?" Ta girgixa mata kai kawai, tana fita Rafi'ah ta rufe kofar dan babu abinda ta tsana kamar aroma din indomie, kwanciya tayi akan gado taja blanket ta rufe duka jikinta. Bayan minti 10 taji Khairiyya na kiranta, ta janye blanket din jikinta ta ce "What khairiyya?" Phone dinta ta mika mata ta ce "Ana kiran wayarki kuma number ne" kauda kanta gefe tayi saboda kamshin indomie daya bugi hancinta, Khairiyya ta ce "Should i pick the call?" ganin yadda Rafi'ah take yasa ta matsa baya tana kallanta ta ce "Is like u are not well Anty" da sauri Rafi'ah ta mike ta sauko a gadon, kafin ta karasa toilet ta fara kwararo amai a kan tiles din dakin, ta durkusa a wajen taci gaba da kwararo shi kamar zata fitar da kayan cikinta. Khairiyya da jikinta ya gama sanyi ta ajiye plate din indomie ta nufi inda take ta tsuguna gabanta ta ce "Sorry" kwanciya Rafi'ah tayi a kasa tana sauke ajiyar xuciya, Khairiyya ta mike ta fita a dakin da sauri, tana fita parlor Yusuf na shiga part din Jiddah, tabi bayansa da gudu ta ce "Yaya" juyowa yayi yana kallanta ya ce "When did u came?" Ta ce "Tin daxu, Anty bata da lafiya fa" Yusuf ya juya ya shige parlorn Jiddah tabi bayansa, akwatuna ne guda 4 manya manya a tsakiyar parlorn, Jiddah ta fito a daki tana kallan Yusuf ta ce "I think we have to go, kayi abinda Umma tace maka?" ya zura hannunsa a aljihu ya dauko karamar paper ya ce "Here it is" Jiddah tayi murmushi ta ce "To akwatinan a kai parlor, bayan nan ka bata takardar ka sameni a mota" ita dai Khairiyya na tsaye tana kallansu, Jiddah ta wurga mata harara ta ce "Ubanwa kika tsaya kalla anan?" khairiyya tayi saurin jaa baya ta ce "Ni bake nake kalla ba" sai kuma ta kalli Yusuf dake jan akwatina zai kai waje ta ce "Yayah i'm talking to u, Anty Fatima bata da lafiya" ko ya daga kai ya kalleta, tabi bayansa har ya fito balcony, ya bawa mai gadi yace a sa a mota sannan ya koma ya dauko sauran ma ya kawo masa, Khairiyya ta kama hannunsa ta ce "Yayah" cikin tsawa ya ce "What.. What do u want?" Ta fashenda kuka ta ce "Anty bata da lafiya, she's vomiting yaya, kazo ka ganta pls" fisge hannunsa yayi ya shiga parlorn sannan ya wuce daki, tana nan kwance ga amai a gabanta kaca~kaca gaba daya tayi weak ko hannunta bata iya motsawa, Khairiyya ta kalleshi ta ce "Kagani tun daxu tana kwance a kasa" tsugunawa Yusuf yayi yana kallanta ya ce "I'm leaving Fatima, i can't stay with u anymore, kinci amanata ba kadan ba, na soki tsakani da Allah but u betrayed me, mena maki da zaki saka min da haka, ba dan Jiddah ba da tin tini kin kasheni, so i want to tell u that i hate u, Jiddah kadai nakeso, na tsaneki Fatima, i will go far away from u, i will distance my self from seeing this ur ugly face" ita dai kallansa kawai take ta kasa magana, Khairiyya ta durkusa tana kuka jin abinda yake cewa, a hankali ya zura hannunsa ya ciro takarda ya bude hannunta na dama ya saka mata a ciki ya ce "Finally u take this, the only solution kenan da zan samu peace of mind" daga haka ya mike ya fita a dakin, sai lokacin hawaye suka dinga sakkowa a idanta, ta mike a hankali tana kallan paper hannunta, jikinta na rawa ta bude paper, bayan ta gama karanta content din two lines ta saki kara ta fadi a wajen sumammiya, Khairiyya ta mike ta karasa wajenta tana jijjigata amma ko motsi batayi, tana kuka ta dauki wayar Rafi'ah ta fara dailing number Mummy. Kallan Jiddah Yusuf yayi ya ce "Where are we heading to?" Cike da isa ta ce "Kaduna mana, su Umma suna caan suna jiranmu, gobe da safe kuma mu keta hazo" Yusuf ya danyi murmushi yaci gaba da driving ya ce "I so much luv u, Umma, and Khadija, u mean alot to me, bansan ya zan saka muku ba" Jiddah tayi murmushin gefen baki ta ce "We love u too Yusuf Muhammad"

_08103810398_
[8/12, 10:27 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_43_

Ummi ce zaune a room din da akai admitting dinta, drip ne a hannunta na dama dayan hannun kuma tissue ne a ciki, lokaci~lokaci tana goge hawayen dake sakkowa kumatunta. Kusan awanta 5 da tashi kenan amma har yanzu Rafi'ah bata farfado ba, jin an bude kofar yasa ta daga kanta tana kallan direction din kofar, Abba ya shigo dakin ya zauna gefenta, kana kallan idanuwansa kasan shima yayi kuka, ga rashin jin dadi a fuskarsa karara, karfin hali kawai yake a matsayinsa na babba wanda ya yarda da kaddara either good or bad. Kamo hannun Ummi yayi ya ce "Ya jikin?" Ta share hawayen idanta ta ce "Da sauki" Abba yayi shiru yana kallanta kafin ya ce "It is a test from God Zainab, babu kuma wanda ya isa ya wuce kaddararsa a rayuwa, idan Allah ya rubuta zai faru definitely it might happen, amma dan Allah ki daina kuka haka nan, nasan abin da ciwo, it really hurt us, musamman keda kika haifeta" Ummi tayi shiru kawai tana ci gaba da goge idanta, Abba ya juyo yana kallanta sosai ya ce "Itama ta tashi yanzu, amma dan Allah idan kikaje kar kiyi kuka, pray for her, u are a mother, don't make her to give up in life, encourage her, support her, karki bari ta tsaneni aure at this her age, it's a destiny" a hankali ta ce "Insha Allah, kun kira shi dinne?" Abba ya ce "I called him, ya kuma ce ya saketa so muyi hakuri kawai, nata kaddarar kenan" Ummi ta kara share hawayen idanta ta ce "She's pregnant fa Abbu Rafi'ah, wallahi bazan yafewa Yusuf ba, dama tun farko abinda nayi gudu kenan" Abba ya girgiza kai ya ce "That should not be a problem, fatana Allah ya raba lafiya, ko guda 100 zata haifa i can take care of them, kawai kici gaba da addu'ah, soon komai zai zama tarihi, shi kuma watarana zaiyi nadama" Ummi ta ce "Hakane, Allah ya bamu ikon cinye wannan jarabawar" ya ce "Ameen" daga haka ya zare mata drip din hannunta ya ce "Ki daure ki mata sannu don't forget all i said" Ummi ta gyara hijabinta kawai ta nufi kofar fita walking slowly, dan ji take kamar zata kara faduwa, kamata Abba yayi har suka je dakin da Rafi'ah ke kwance, Abba ya bude kofar suka shiga, Mummy ce tsaye a kanta tana rarrashinta, sai maganganu take anyhow komai yazo bakinta fada take, dayan side din kuma Ammi ne tsaye da Khairiyya sai share idanta take da hijabi, Anty Amina dasu Anty Rahama ma suna tsaye, sai goge hawayen munafirci suke, Mummy ta dago jajayen idanuwanta da suka kumbura tana kallan Ummi ta ce "Sannu" Ummi ta daga mata kai tana kallan Rafi'ah dake kwance, a hankali ta karasa kusanta ta ruko hannunta, jikinta zafi gaau, tana kallan Ummi ta zabura ta mike ta rungumeta, fashewa tayi da kuka tana fadin "Ki yafemin Umminah, ya sakeni for no reason, ban masa komai ba sai ma shine yake cutana for almost 2 months, ban ta6a fadawa kowa ba, pls Ummi kuce karyamin haka, never thought i will be divorced at this my age" saketa Ummi tayi ta fita a dakin saboda kuka da take itama, Mummy ta kama hannun Rafi'ah ta zaunarta akan gado ta ce "So u haven't heard all i said Fatima" cikin kuka ta ce "Naji Mummy, but u people should let me cry, idan banyi ba bazanji dadi ba, Allah ya Allah idan mafarki nake kasa na tashi yanzu" rungumeta Mummy tayi ta dinga jijjigata tana fada mata kalaman da zasu mata dadi, bayan kusan minti 30 tayi shiru tana bin kowa na dakin da kallo, Mummy ta kwantar da ita ta ce "Kiyita addu'ar dana fada maki dazu, dan Allah u stop crying, kinsa Umminki na caan tana kuka, so kike BP dinta yayi raising ne?" Ta girgiza kai a hankali hawaye na sakko mata ta ce "Indai a kaina take kuka nima na daina, kice mata bazan kara ba Mummy" Mummy ta ce "To karki kara, ki kwanta kiyita addu'a" mikewa tayi ta kwanta tana kallan Abdul dake share hawaye yana zaune akan kujerar dake opposite din gadon da take. Mummy na fita taji hawaye masu zafi na sakko mata, ta share idanta sannan ta karasa dakin da Ummi take, tana zaune Abba na gefenta ya hada mata tea, Mummy ta shigo dakin tana kallansu ta ce "Zakici abincin ne?" Ummi ta girgiza kai ta ce "Na koshi" Mummy ta ce "Allah ya sauwake". Bata wani jima a nan b ta koma dakin da Rafi'ah take, tana nan kwance bakinta na motsi tana ta addu'a, kujera taja ta zauna itama, duk dakin yayi shiru sai numfashinsu kakeji a hankali, jin an turo kofar yasa Mummy ta daga kanta tana kallan Mami data shigo, Mummy ta ce "Ya mai jikin?" Mami na kallan Rafi'ah ta ce "Ai taji sauki, cikinma ya daina ciwan, sun sallamemu yanzu, ya jikin Rafi'ah?" Mummy ta ce "Da sauki itama" Mami ta kara kallanta ta ce "Bari mu wuce gida ga dare yayi, gobe na dawo" Mummy ta ce "To Allah ya kara sauki, a mata sannu" Mami ta fice a dakin bayan tayiwa su Ammi sallama. Karfe 11 na dare Abba ya shigo dakin da Daddynsu Khairiyya sai Abi dan tin dazu da sukazo aka hana kowa shiga wajenta sai data tashi, sun tausaya mata matuka ba kadan ba, Daddyn Khairiyya ya dinga mata addu'a da nasiha iri iri, haka Abi ma yayi ta mata kafin sukai musu sallama, Ammi ta kalli Mummy dake zaune ta ce "Hajiya zamu tafi, Allah ya kara mata lafiya" Mummy ta ce "Mungode Allah ya tsare" Khairiyya dai sai kallan Rafi'ah dake kwance take har suka fita a dakin, ba jimawa Abba ya dawo dakin, ya kalli su Anty Amina dake zaune ya ce "Bari na maidaku gida" kamar jira take ta mike tana kallan Mummy ta ce "Allah ya sauwake" Mummy ta ce "Yauwa Amina mun gode" Abba ya kalli Abdul dake zaune ya ce "Kaifa?" Ya girgiza kai ya ce "Zan zauna anan Abba" Abba ya ce "To shikkenan, bari in kaisu, Umminsu ma gida zata kwana sun sallameta" Mummy ta ce "Ehh yafi kam taje ta huta, Allah ya tsare hanya" Abba ya ansa da Amin kafin ya fita a dakin. Ta6e baki Anty Rahama tayi ta ce "Kawai kinsamu zaman asibiti kamar dole, wallahi da niyyata sanda Umma da Ikleemah zasu tafi muma mu wuce" Anty Amina ta ce "Haba Anty, idan ban zauna ba ai zasuce murna nake, bakiga yadda na dinga kakalo kukan karya ba?" Har Anty Rahama zatai magana sai tayi shiru saboda Abba data hango yana tahowa da Ummi, Anty Amina na kallansu ta dauke kai, bayan sun karaso ya bude lock din motar Ummi ta shiga gaba su kuma suka shiga baya yaja motar suka bar clinic din.
Daren ranar kwana Ummi tayi tana salla tana kai kukanta ga Allah, tayi kuka ba kadan ba a daren nan, kafin safiya ita kanta tasan ta rame tsabar damuwa, tana idar da sallan asuba ta shiga kitchen tayi dan~wake da kunu sannan tasa a basket, sama ta koma dakinta tayi wanka ta shirya, tana gamawa Abba ya dawo daga masallaci, bayan sun gaisa ya kalli agogon dakin ya ce "Karfe 7 saura yanzu, kinyi breakfast ne?" Ta girgiza masa kai ta ce "Idan naje caan zanci" Abba ya ce "No, kafin na shirya kiyi breakfast"daga haka ya juya ya koma dakinsa, half cup na kunu kawai ta iya sha, shima turawa tayi ta shanye bawai son ranta ba, bayan ta gama ta ajiye cup din ta

Please Login or Register in order to submit comment