Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke gutsura? Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba i'm going to deal with u honestly, ke ba kya shiru ne a rayuwarki? Must u talk? and let me hear u talk again kiga ikon Allah" shiru tayi ta kifa kanta akan kujera, deep down her kuma tayi alkawarin indai taje baza ta musu aiki ba, ba kuma za'a zageta ta kyale ba. Suddenly phone dinta dake ajiye kan sofa ya hau ringing, Ummi ta dinga kallan screen din ganin an rubuta Dr. Yusuf, tashi Rafi'ah tayi daga inda take ta dauka wayar sannan ta nufi upstairs Ummi ta bita da kallo. Direct dakinta ta shiga bayan tayi picking call din ta zauna bakin gado, Yusuf ya ce "How are u dear?" Silently ta ce "Fine" ya ce "Why the mood?" share dan guntun hawayenta tayi ta ce "Wai saina je gidan Umma ne" Yusuf ya shafa gashin kansa yana murmushi ya ce "Who said so? And who is Umma" a hankali ta ce "Kanwar Kakanmu ce" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "To meyasa bakinsan zuwa? Is she not ur grandmother?" Sake share idanta tayi ta ce "She is, but basa sona ai" Cikin rarrashi Yusuf ya ce "Kiyi hakuri to kije kinji Baby" ta dan turo baki ta ce "Ni banaso" ya ce "I know but for the sake of ur parents, ai lada ma zaki samu idan kikaje, kinga kinyi ziyara" ta ce "Uhm, uhm" ya ce "Bakisan ladan Baby?" Ta ce "Inaso" ya ce "Then smile" ita kanta batasan lokacin data saki murmushi ba, ya ce "Alright, i will call u ltr ina driving ne" ta ce "Allah ya kiyaye" ya ce "Won't u say bye~bye my love" ta danyi dariya kawai, ya ce "Oh na baki dariya kenan?" ta ce "Something like that" ya ce "ko?" Ta ce "Ehh" ya ce "To zan kiraki anjima, bye bye love" saurin rife ido tayi ta janye wayar a kunnenta tayi hanging call din, tana juyawa sukai ido hudu da Ummi, sai da zuciyarta ya buga at first, Ummi ta ce "Who's that?" Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa, Ummi ta ce "I'm i not talking to Rafi'ah?" A hankali ta dago kanta tana kallanta ta ce...


_I LUV U FANS_ 😄

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_21~22_

Karfe uku da rabi Ummi ta shigo dakin Rafi'ah ta tashe ta a bacci, tayi mitsi~mitsi da ido tana kallan Ummi ta ce "Abdul din bai dawo ba shine na kwanta" Ummi dake kallanta ta ce "Abdul Baffa ya kirashi, ki tashi ki shirya Mustapha ya kaiki, shi yaje daga baya" turo baki tayi ta janye duvet din jikinta ta ce "But Abba said we should go together" Ummi ta wurga mata harara ta ce "To karki shirya ki sauko, continue arguing with me" tana dasa aya ta fita a dakin taja mata kofar, Rafi'ah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta mike ta shiga toilet, few minutes ta fito da towel a jikinta, ta zauna gaban mirror ta shafe jikinta sannan ta bude press dinta ta dauko atampa ta saka, das~das dinkin ya zauna a jikinta, tayi combing hair dinta sannan ta daura head tie dinta ta saka hijabi iya knees dinta, babu ko powder a fuskarta amma tayi kyau sosai, ta dauka side bag dinta da phone sannan ta sauko downstairs. Ummi ce kadai a parlor da laptop a gabanta, Rafi'ah ta zauna gefenta ta ce "Na shirya" Ummi ta dago tana kallanta ta ce "Ko powder ba zaki shafa ba Rafi'ah?" dan bakinta ta turo ta ce "Ni haka nakeso" Ummi ta ta6e baki ta ce "Ga turare ki kaiwa Umma, my regards to them" ta karashe maganar tana mikawa Rafi'ah ledan da turaren yake ciki, kar6a tayi ta mike ta ce "Sai na dawo" Ummi ta ce "Ki gaishe su, bayan Magrib zai koma ya dauko ki" a hankali ta ce "Toh" sannan ta fita a parlor. 10 minutes with some seconds ya kaisu gidan Umma, Mustapha yayi parking a waje ta masa sallama sannan ta fito ta shiga gidan, ba kowa a compound din sai mota kwaya daya a parking lot, ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar ta shiga da sallama, babu wanda ya amsa mata sai ido da suka zuba mata duk tasu, dan basuyi zatan zuwanta gidan ba, dama mostly da Abba suke zuwa. A hankali Rafi'ah ta karasa cikin parlor ta zauna a kan carpet ta ce "Ina wunin ku?" Ba yabo ba fallasa Anty Rahama ta ce "Lafiya kalau" Anty Amina kuwa kota daga kanta ta kalli inda take. Bayan 10 minutes Anty Rahama ta kalli diyarta dake kwance kan sofa ta ce "Ikleema tashi kuje ki nuna mata toilet dina ta wanke min" with surprise Rafi'ah take kallan Anty Rahama, tashi tayi tana gyaran wuyan hijab dinta ta ce "Dama Abba cewa yayi nazo na gaishe da Umma, ga wannan inji Ummina a bata" daga haka ta nufi kofar fita, Ikleema ta ce "Ai gara da kika tafi gayyar tsiya" Rafi'ah ta juyo tana kallanta ta ce "Ga tsiya kam ai kina cikin ta" ganin Anty Rahama ta taso tana kunduma zagi yasa taja musu kofar da gudu ta nufi gate ta fita, cikin sauri ta karasa bakin titi ta tsare me Napeep ta shige, sai sauke ajiyar zuciya take tana huci, bayan minti 2 mai Napeep din ya juyo yana kallanta ya ce "Ina zakije 'Yammata?" A hankali ta fada mishi inda zai kaita sannan ta kifa kanta tana kokarin dai dai ta numfashinta. Bayan ta iso gida ta cire 500 a jakarta ta bashi ya bata change sannan ta shiga gida, tana bude kofar parlor Ummi ta ce "Zo nan Rafi'ah" baya ta dan ja ta ce "Wallahi Ummu ba abinda na musu" Ummi da ranta ya gama 6aci ta ce "Of all abinda na fada miki baki jiba Rafi'ah sai da kikaje kika jawomin magana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "I swear Ummi ni ban ce musu komai, bafa dasu nake ba, nida Ikleema nake" Ummi ta ce "I'm that kind of mother who doesn't talks but kika kaini karshe billahil azeem u will regret" Rafi'ah dake tsaye bakin kofa ta share guntun hawayenta ta ce "Ai dama nasan Abba zasu kira suce na zagesu, kuma wallahi ni ba dasu nake ba, Ikleemah ce ta fara cemin gayyar tsiya" daga haka ta fashe da kuka ta tsuguna a wajen, Ummi taja tsaki ta ce "Tinda kinsan dama neman fada suke data zageki ai saiki mata shiru, gashi nan yanzu sun hada karya da gaskiya sun gayawa Abba, sai kuma kisan abinda zaki ce masa ya sauko" daga haka Ummi ta mike ta shiga kitchen, tashi Rafi'ah tayi ta share idanta ciki ciki ta ce "Wallahi duk wanda ya hadani da Abba shida Allah" Ummi da fitowanta a kitchen kenan ta ce "Ke dai kika sani kuma, and don't involve me in this case, ko sunana ban yarda ki kira ba, banasan abinda zai 6ata min rai ina zaman zamana" Rafi'ah ta sake tare hawayen idanta ta wuce dakin Abdul.

_Two weeks ltr_
Ummi ce Zaune a kitchen tana hada coleslaw cikin bowl Abdul na 6are maggi a gefenta, bayan ya gama ya mika mata ta ce "Keep it there" a kan drawer ya ajiye ya dawo gefenta ya zauna, dai dai lokacin Rafi'ah ta shigo kitchen din, ta dan tsaya bakin door ganin sun gama aikin da suke, karasawa ciki tayi tana kallan Ummi ta ce "Wai meyasa bazata sauka anan ba Ummi?" Ummi ta ce "Da gidanta dan meyasa zata sauka a gidanku" Ta dan turo baki ta ce "To nidai caan zan tafi" a takaice Ummi ta ce "Abba yace babu me zuwa, tinda zasu kai karfe 12 kafin suyi landing, kuma itama cewa tayi ku zauna gobe da safe zata zo" Rafi'ah dake kallan Ummi ta ce "Har sai gobe zamu ganta" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Keep shut quite now, ke bakisan tara ki nake bako Rafi'ah? tinda muka fara aikin nan kika tafi kika kata waya baki dawo ba sai yanzu, kinzo kuma kin isheni da surutu, better mind ur words, bari kuma Abba ya dawo ki masa bayanin da uban wa kike waya da bazaki gayamin ba" a hankali ta sunkuyar da kanta ta ce "Kiyi hakuri" Ummi bata ko kalleta ba taci gaba da abinda take. Bayan ta gama ta hada komai cikin basket ta bawa Mustapha ya kai gidan Mummy da yake akwai mai aikinta a gidan. Ganin ba kaisu caan gidan za'ai ba yasa Rafi'ah tayi sallan ishanta ta shiga daki ta kwanta, harta fara bacci phone dinta ya fara ringing, ta dauka a hankali ta kara a kunne hade da sallama, Yusuf ya dan zaro ido jin muryarta ya ce "Are u sleeping Baby?" Ta dan turo baki ta ce "I'm tired that's why" ya ce "Sorry, kinyi wa Mummy abinci ne?" Ta danyi murmushi ta ce "Sure" ya ce "Ohk let me leave u rest" ta ce "Uhm, till tomorrow" ya ce "Byee" tana hanging wayar ta kasheta duka duka ta koma baccinta. Washegari tinda Rafi'ah tayi sallan asuba tayi wanka, bayan ta shirya tayi dialing number Mummy, bata dauka ba har kiran ya katse. Karfe 7:30 Mummy ta iso gidan, Abdul ya mike jin horn ya leka ta window, dan murmushi yayi yana kallan Ummi ya ce "It's Mummy" daga haka ya bude kofar ya fita da sauri, rungumeta yayi yana ta bubbuga bayanta looking happy ya ce "You are welcome mother" Mummy ta kama hannunsa ta ce "How are u, ya sai tsayi kake?" Abdul ya danyi dariya yana kallan saurayin dake tsaye jikin motarsa ya ce "Ina kwana?" Cike da fara'a ya ce "Lafiya kalau and u?" Abdul ya ce "Also fine", Mummy ta juyo tana kallansa ta ce "U come in Jawad" daga haka suka nufi entrance din gidan tana rike da hannun Abdul, Suna shiga ciki Ummi ta rungumeta ta ce "Sannu da zuwa Anty, ya hanya?" Mummy ta ce "Alhamdulilah, ya muka sameku?" Ummi dake murmushi ta ce "Lafiyar kowa kalau" sai lokacin Jawad ya tsuguna bakin kofa ya ce "Ina kwana" Ummi ta ce "Lafiya kalau, Jawad, kaine yau a gidanmu" ya danyi murmushi yana shafa kanshi, Mummy ta ce "Ai ba zaman kasar yake ba, shima day before yesterday ya dawo daga Ukraine" Ummi ta ce "Ayya, kayi masters kenan" ya daga mata kai yana murmushi, Mummy ta ce "Yanzu zai ci gaba da aiki ba" Ummi ta ce "Masha Allah that was great, yasu Mamanku?" Yayi kasa da kansa ya ce "Suna nan, gobe zasu wuce Abuja" yana rife bakinsa Rafi'ah ta sauko a guje ta rungume Mummy kam kam, Mummy ta shafa bayanta ta ce "How are u daughter?" A hankali ta dago kanta ta ce "Fine Mummy, ya hanya?" Mummy ta ce "Masha Allah" daga haka ta kara rungume Mummy tana murmushi, Ummi ta mike tana kallan Jawad ta ce "Ka zauna kan sofa mana" Rafi'ah ta dago kanta jin an kira Jawad, suna hada ido ta dauke kanta tana kallan Mummy ta ce "Abbana ma ya kusan dawowa, saura kwana uku" Mummy ta ce "Munyi waya ai jiya, ga Jawad baku gaisa ba" Rafi'ah ta dan turo baki ta ce "Shida bayawa mutane magana, in munje sai yayi ta hade rai da fishi" Mummy ta dan zaro ido ta ce "Wai hakane Jawad?" Shidai baice komai ba yayi murmushi yaci gaba da danna phone dinsa. Breakfast Ummi ta jera musu akan dinning ta ce "Anty Halima ga abinci, Jawad u come forward". mikewa Mummy tayi ta koma dinning ta zauna, Rafi'ah ta dawo gefenta ta ce "Let me serve u Mummy" daga haka ta dauka plate ta fara zuba mata abinci, few minutes Mummy ta gama breakfast dinta, ta mike tana kallan Jawad dake danna waya har lokacin ta ce "Bismillah Jawad" ya tashi a hankali ya ce "To" Mummy ta wuce upstair tana fadin "Ina Zainab din take ne".
Jawad na zama akan dinning ya kalli Rafi'ah dake cin chips and egg ya ce "Can't u great?" Ta dan 6ata fuska ta ce "Bayan baka ma mutane magana a gidanku" ya ce "To ai yanzu gidanku nazo" a hankali ta ce "Morning" ya ce "How are u?" Ta ce "Fine", kusan minti 10 basu kara cewa komai ba, Jawad ya ajiye cup din tea yana kallanta ya ce "Ya jinki kuma?" With surprise ta dago tana kallansa, taya yasan bata da lpy to? Jin tayi shiru yasa ya ce "Allah ya kara sauki", suddenly phone dinta dake gefensu ya fara ringing, Jawad ya kalli screen din sannan ya kalleta, daukan phone din tayi ta wuce kitchen, bayan tayi picking tayi sallama, Yusuf ya ce "How are u Baby? I just saw ur text now" ta danyi murmushi ta ce "Yanzu ka tashi kenan?" Ya ce "Of course, fatan sun iso lpy?" Ta ce "Ehh Alhamdulilah" limshe idanuwansa yayi murya caan kasa ya ce "I want to see u Baby" ta sunkuyar da kanta tana murmushi ta ce "Ohk, anjima zanbi Mummy gidanta sai kazo caan" cike da farinciki ya ce "Woow thank u luv, mezan kawo maki?" Ta saki murmushi ta ce "Nothing" ya ce "No say something pls" a hankali ta ce "Khairiyya" ya dan zaro ido ya ce "Ba yanzu ba, but i promise she would come one day" turo baki ta danyi ta ce "Pls Doctor, inasan na ganta ne?" Ya ce "I promise u zan kawota watarana kinji Baby" ta ce "To" ya ce "Hope you're not angry" ta kara sakin murmushi ta ce "No" ya ce "Alright by what time zanje caan din" ta dan juya idanta kamar yana gabanta ta ce "I think after Asr" ya ce "Ohk, which area?" ta fada masa sunan anguwan da kuma house number, Yusuf ya ce "Understood, thank u so much love" rife fuskarta tayi da tafin hannunta ta ce "Sai anjima" ya ce "Bye" daga haka yayi hanging wayar, tashi yayi ya janye duvet din jikinsa ya tsaya gaban mirror, farar riga ce a jikinsa sai tree quarter ash colour, comb yasa ya taje gasjin kansa sannan ya dauki laptop dinsa ya fito a dakin, Da sauri ya tsaya ganin Umma a parlor da Anty Khadija suna ta daddaga kayan da umma ta siyo na lefe, Yusuf ya dauke kansa ya ce "Ina kwana Umma" cike da fara'a ta ce "Lafiya Yusuf, kaga dai kayan dana fara siyowa" ba tare daya kalli kayan ba ya ce "Sunyi kyau" Umma ta taso da wani tsadadden lace a hannunta ta ce "Kaga wannan ai yayi kyau ko Yusuf, ko kuma kafisan red color?" A hankali ya ce "It's ok" Umma ta koma ta zauna ta ce "Atoh, jidda fara ce idan aka tara mata jaa ai ba kyau zatai ba" shidai bai ce komai ba ya wuce kitchen ya hada tea sannan ya fito ya koma daki, Anty Khadija ta kalli Umma dake jera kayan cikin akwati ta ce "Umma wai fara'ar me kike tayi ne?" Umma tayi murmushi ta ce "Khadija kenan, ke bakisan idan ana son buri ya cika sai an saki fuska ba, kema dai ki lalla6ashi ku shirya, hanya daya kenan da jidda zata samu ta shiga gidansa ba wata caan daban ba" Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce "Ai wallahi bai isa ya auri wata caan daban ba, kisha wahalar rainonsa sannan yaje ya auri wata ta moresa" Umma ta ce "Kema dai kya fada, gara ya auri za6ina ta yadda zata bini sau da kafa mu mallakeshi" murmushi Anty Khadija tayi ta mike tana kashewa Umma ido daya ta nufi dakinsa.
Mummy ce zaune a dakin Ummi suna hira, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Amma tin daga ranar bai kara tashi ba" Mummy ta ce "Allah ya kara mata lpy" Ummi ta mike ta ce "Yanzu kenan Maman Jawad Abuja zasu koma?" Mummy ta ce "Haka ta tsara masa wai zasuje hutun sati biyu kafin a koma school" Ummi ta ce "Allah ya kyauta, ya kannen Jawad din?" Ta ce "Duk suna nan, sai shegen taurin kai da rashin kunya irinna uwarsu, nidai bana shiga harkarsu dan kakkarya yara ba abu me wahala bane a wajena, Jawad ne kawai me hankali a cikinsu, Sadeeq kam ba'a magana, ita kuma wancen sa'ar Rafi'an rashin kunyarta yafi karfinta, ana gobe zamu dawo ma sai da uban yayi mata dukan tsiya" Ummi dake saurarenta ta ce "Allah ya shirya mana" Mummy ta ce "Ameen" daga haka suka hau hirarsu ta yaya da kanwa.
Karfe uku Mummy tace wa Rafi'ah ta shirya zasu tafi, ta dauka handbag me dan girma tasa kayanta kala hudu aciki, Ummi dake kallanta ta ce "Kwana nawa zakiyi ne?" Ta ce "Sunday zan dawo da daddare, kwana 2 kenan" Ummi ta ce "Ki fadawa Abba dama, and make sure u don't forget ur drugs" ta ce "To", bayan ta gama shirya kayanta ta kira Abba ta fada masa, ya mata Allah ya kiyaye, har bakin mota Ummi ta rakasu, Mustapha ya bude motar Rafi'ah ta shiga, suna tsaye bakin motar Anty Amina ta shigo gidan, ta kauda kanta gefe tayi apartment dinta, Mummy ta bita da kallo ta ce "Ita dan kiban ma da matan manya suke ita batayi, daga ina take kuma?" Ummi ta ta6e baki ta ce "Ina zan sani Anty" Mummy ta ce "Allah ya kyauta" daga haka ta shiga motar Mustapha yaja suka bar gidan. Minti 15 ya kaisu gidan Mummy, suna horn aka bude gate din, Mustapha yayi parking suka fito sannan ya musu sallama ya juya, bin bayan Mummy Rafi'ah take har suka iso entrance din gidan, Mummy ta murda handle din ta shiga Rafi'ah tabi bayanta, Abi ne zaune a parlonsa yana kallo, ya danyi murmushi ganin Rafi'ah ya ce "Future Barrister" ta boye fuskarta tana dariya, dan bata manta sanda take haukar ita lawyer ce, har zare take daukowa tana daurawa mutane a kafa wai shine handcuff, Abi yayi dariya ya ce "Ina dai baki fasa zama barristern ba?" Zama tayi a kasa still smiling ta ce "Ina yini Abi" ya ce "Lafiya kalau Fatima, how are u and them" a hankali ta ce "Kowa lafiya" ya ce "Ya jikinki kuma?" Ta ce "Da sauki sosai" ya dan kalli Mummy ya ce "Ya kuka samesu?" Ta ce "Duk lafiya suke" tana rife bakinta mahaifiyar Jawad ta fito daga side dinta, ta wani hade rai, Rafi'ah ta ce "Ina wuni" ciki ciki ta ce "Lafiya" Mummy ta kalli Rafi'ah ta ce "Tashi ki shiga ciki Rafi'ah" mikewa tayi ta shiga bangaren Mummy, Abi ya tashi yana gyara babban rigarsa ya ce "Madam zan fita fa" ta ce "Zuwa ina?" Ya ce "Nace Sadeeq yazo muje shopping, naga ba komai ne akwai a gidan ba" ta ce "Allah ya kiyaye hanya" daga haka ta ya fita ita ma ta mike ta shiga bangarenta.
Bai fi 10 minutes da fita ba Jawad ya shigo gidan hannunsa rike phone sai car key dinsa, direct side din Maminsa ya nufa, Ikram ce kadai zaune a parlor tana kallo a system, ta dan dago kanta ta kalleshi ta ce "Sannu da dawowa Yaya" ya ce "Sannu, ina Sadeeq?" Ta ce "Sun fita da Abba" mikewa yayi zai fita yaji maganar Mami ta bayansa, ya juyo yana kallanta ya ce "I thought kin fitan ai" ta dalla masa harara ta ce "Ka sameni a dakina yanzu" daga haka ta juya ta koma ciki, kusan minti biyu yana tsaye kafin ya zura hannayensa cikin aljihun wandansa ya nufi dakin ta, yana shiga ya tura kofar ya rufe ya tsaya jikin mirror, ta ce "Sai nace ka zauna kenan?" zama yayi akan stool din dake wajen, Mami da ranta ya gama 6aci ta ce "Maimakon da ka kai matar uban naka ka dawo ka kaini saika nemi waje ka zauna" ya dago kansa yana kallanta ya ce "Naje court ne Mami, na samu urgent call around 9, Anty kuma Abi ne yasa ni na sauketa a gidan kanwanta" Mami ta ce "Ai dama kai duk inda zakai suna nan kake xua, da yace ka sauketa why not go and leave her, in yayi magana kace ka manta" a hankali ya ce "Kiyi hakuri" taja tsaki sannan ta mike, shima mikewa yayi ya ce "Zan kaiki din ne?" Ba tare data kalleshi ba ta ce "Zaman jiranka zanyi, Sadeeq dake neman lada ai ya kaini" sunkuyar da kansa yayi ya ce "Sai anjima" daga haka ya fita a dakin.
Yusuf ne tsaye gaban mirror yana gyara zaman hular kansa, farar shadda ce ajikinsa tayi bala'in masa kyau, sai kamshi yake, ya dauki key din motarsa da wayarsa ya fito a dakin, Anty Khadija ce kwance a parlor tana gyangyadi, jin kamshin turarensa yasa ta zabura ta bude ido, sai da ta saki murmushi kafin ta ce "Doctor daga nan kuma sai ina?" Ya dan kalleta sannan ya dauke kai ya ce "Somewhere" bai jira cewarta ba ya fice ya jawo mata kofar, yana zuwa parking lot yasa key ya bude motarsa ya shiga, kunnata yayi yana jira tayi warming dan yau tun safe ba inda yaje, ko sallar juma'a ma a unguwa yayi baiyi nisa ba. Jiddah ce ta shigo gidan duk a gajiye, kana kallanta kasan daga school take, suna hada ido ta saki murmushi ta karasa inda yake ta ce "Yaya sannu da dawowa" a hankali ya ce "Sannu kema" ta ce"Umma tace ka bada kudi a fara hada min lefe nago..." Kallan daya watsa mata yasa tayi shiru tana kallansa, ya ce "Akai forcing dina dai, tin farko ai nunawa sukai basa so, saboda haka nima na hakura, u go and find someone but not Yusuf" Kallansa kawai Jiddah take with expression, she's just lost of words, nan da nan idanuwanta suka kawo ruwa ta ce "Amma kasan ina sanka Yaya, wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba" jaan motarsa yayi ya wuce ya barta tsaye a wajen, kuka me karfi ta saki ta nufi cikin gida da gudu tana kiran Umma.
Sai da Yusuf ya tsaya yayi sallan la'asar sannan ya karasa gidan Mummy, dai dai kofar gidan yayi parking bayan ya duba house number, bayan yayi parking ya fito ya jingina jikin motarsa ya fara kiran wayar Rafi'ah, suna zaune ita da Mummy suna hira kiran ya shigo, ta mike ta dauka wayar sannan ta shiga daki, ya ce "I'm outside dear" ta ce "Alright gani nan" daga haka ta ajiye wayar ta daukar well ironed himar dinta ta saka, powder kawai ta shafa da lip stick sannan ta fito rike da wayarta a hannu ta ce "Mummy bari naje waje" Mummy ta washe baki ta ce "To ya shigo compound mana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Kaiii Mummy class mate dina ne fa" Mummy ta ce "Hmmm, shi class mate din ba zai shigo cikin gida ba sai ya tsaya a bakin gate" ita dai Rafi'ah bata ce komai ba ta fita a parlorn, tana fitowa ta samu Ikram a parlorn Abba tana zaune, suna hada ido kowacce ta dauke kai Rafi'ah ta nufi kofar fita. Tin fitowarta Yusuf yake murmushi yana kallanta, bayan ta karaso tasa tafikan hannayenta ta rife idanta ta ce "Ni kadaina kallo na" ya danyi murmushi ya ce "U look more beautiful in hijab, kinyi kyau

Please Login or Register in order to submit comment