Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta goge hawayen idanta ta ce "Ummi zafi yakemin fa" cikin tsawa Ummi ta ce "I said get out here, dama aiba niyyar yi kikayi ba" tana fita a kitchen din Abba kuma ya shigo ya ce "Wai lafiya dai?" Ummi ta ce "Wai yankewa tayi shine takemin kuka, dama dai ba niyyar yin aiki tayi ba, banga abin kuka ba a wannan wajen" Abba ya kalli Rafi'ah data kifa kanta akan kujerar dinning, karasowa cikin kitchen din yayi ya ce "Pls u stop shouting at her, kiji tausayinta mana, after ciwan dake daminta kiyi ta mata tsawa, haba Ummu Rafi'ah, let her rest pls, ke kinki kuma a nemo mai aiki" Ummi dake sauraronsa ta ce "Allah ya baka hakuri, mai aiki ne banaso, sai dai idan aure tayi" Abba ya danyi murmushi ya ce "Nifa ba fada nazo muyi ba Madam, kinbi kin hade rai" a hankali ta ce "To ai kaine sai kaita nunamin kamar bani na haifi Rafi'ah ba" Abba ya ce "Pardon, amma u have to see her condition" ta ce "To" fitowa yayi a kitchen din jin phone dinsa na ringing.
Jiddah ce zaune a high table wajen Kamu, tayi masifar yin kyau, make~up very light aka mata amma kamar ka saceta a wajen, hall din babbane sosai kida nata tashi, a gaba gaba tawagar Umma take, manyan mata sun sha tsadadden lace dinsu yawancinsu da gold a neck dinsu, Anty Khadija ma ta cakare sai hotuna suke da friends dinta maza da mata, ganin Jiddah ta hade rai yasa Anty Khadija ta fara takawa steps din har inda take zaune ta ce "Ke dalla ki kwantar da hankalinki sai kace bakisan halinsa bane, Umma ta kirashi yanzun nan zakiga ya karaso" Jiddah ta marairaice ta ce "Anty dan Allah kiyi iya bakin kokarinki, Allah yaya zai iya kin zuwa ko waye ya kirashi" tashi Anty Khadija tayi ta kira number Aliyu, yana dauka ta fice a hall din saboda karan kida ta ce "Ali kuna ina ne? anata jiransa gashi har time ya tafi" Aliyu ya ce "Hajiya Anty yanzun nan zaki ganmu, muna jiran wani abokinmu ne" Anty Khadija ta ce "To kuyi sauri dan Allah, gashi karfe 7 time dinmu zaiyi expire su gyara wajen wasu zasu shiga by 8, Aliyu ya ce "Don't mind Antyn mu gamu nan" daga haka yayi hanging call din yana kallan Yusuf dake zaune ya limshe idanuwansa, tin jiya yake kiran Rafi'ah a waya amma wayanta a kashe, Aliyu ya dafa shi ya ce "Kaifa ake jira Yusuf, sai kirana ake wallahi" Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce "I'm not going Aliyu, sai da nace ni banason wannan kidan amma sai da akai" Aliyu ya matso kusa dashi ya ce "Yau ne fa kawai Doctor, pls entertain her baza taji dadi ba idan baka je ba" yana rife bakinsa wasu friends dinsu su shida suka shigo dakin, daga haka dai har sukai convincing dinsa yace zaije amma ba dadewa zaiyi ba, canza kaya yayi cikin milk gezna, tayi bala'in mishi kyau sosai, ga beard dinsa sun kwanta saman farar fuskarsa sai kamshi yake, daga haka suka shiga mota suke wuce shida Aliyu, sauran motoci hudun kuma suka bisu a baya. Ba karamin farinciki Jiddah tayi ganin Yusuf ba, gaba daya ta kasa dauke idanta a kansa, ta dinga murmushi tana kallansa harsu Aliyu suka rakoshi gefenta sannan suka koma table dinsu, sosai aka ci aka sha a wajen, aka cashe sosai musamman Umma da kawayenta, da kyar Yusuf ya tashi ya manna mata 'yan 500, sannan ya juya ya mannawa Jiddah ma, Anty Khadija na rawa har zuwa wajensu ta dinga watsa musu kudi tana video, ba jimawa Ammin su Sameer ta fito itama ta dinga watsa masa kudi tana tsokalarsa, duk 'yan uwa da abokan arziki saida suka manna masa kudi, musamman Sameer yafi kowa watsawa dan uwansa kudi, jin an kama hannunsa yasa ya juya, ya sakar mata murmushi ya ce "Khairiyyan Yaya" ta washe masa baki ta ce "Yaya banga Anty ba?" Ya ce "Wa?" Ta ce "Wannan faran, Anty wama sunanta? but you used to called her Fatima" a hankali yayi murmushi ya ce "Her name is Rafi'ah, she's not here" Khairiyya dake kallansa ta ce "Why Yaya? Ba kace she's ur best friend ba, why is she not presence at ur marriage?" A hankali ya ce "Soon zakiga tazo" a hankali ta sakeshi ta koma dai dai saitin kofa tana kallan masu shiga da fita ko zataga Rafi'ah amma babu, ganin Yusuf da abokansa sun fita a hall din ta 6ata fuska kamar zatai kuka, dan tasan an gama event din kenan.
Da dare Rafi'ah nasan kunna wayarta amma taki sabida batasan kiran Yusuf ya shigo mata, haka nan ta hakura har bacci ya dauketa. Washegari ya kama Sarurday, sassafe ta kunna wayarta ta masa text sannan ta kashe wayar ta sauko dan taya Ummi aiki. Yusuf na zaune a dakin Aliyu text din ya shigo, ya gama karantawa sannan yayi murmushi, ji yake duk duniya babu wacce yakeso irin Rafi'ah" Aliyu dake kallansa ya ce "What's that" Yusuf ya ce "She send me message now, that i shouldn't worry, ta bani time ne nayi hidimar aure naji da baki" Aliyu ya ce "Yanzu hankalinka ya kwanta kenan? Sai kayi baccin da bakayi da daddare ba kafin lokacin daurin aure yayi" Yusuf ya ce "But ba haka naso ba, i need to hear her voice, i missed her much" Ali ya ta6e baki ya ce "Kasan dai bazaka je wajenta a yau ba kam, ba kuma gobe ba, ba jibi ba, sai dai ko gata" Yusuf ya kai masa duka ya ce "Karka kaini har gata Malam, jibi zanga abata" daga haka ya kwanta yana murmushi jin answer da Aliyu ya bashi. Karfe 10 Abba ya fito cikin shirinsa na alfarma yayi breakfast sannan yayi wa Ummi sallama zai tafi daurin auren Yusuf, ta masa Allah ya kiyaye sannan ta ci gaba da gyaran dakinta. Jawad ne tsaye a kofar gidansu Aliyu ya jinginu da motarsa, Aliyu ya fito ya mika masa hannu ya ce "Barisster always behaving somehow, tinba yau ba muke tare amma sai kazo kayi parking a waje, kuma wallahi Mama jiya sai data tambayeka" Jawad ya danyi murmushi ya ce "Zanzo na gaisheta but gobe insha Allah" Aliyu ya ce "Allah ya kaimu, zakaje daurin auren Yusuf ne?" Harara Jawad ya dalla masa ya ce "Kai din dai daya zame maka dole, over my dead body" Aliyu ya dinga dariya ya ce "Pls, yana ma ciki yana shiryawa, kaga kaima kaci manyan kaya kuma kayi kyau sai dai ba babban riga" Jawad ya bude motarsa ya ce "Pls let me go Ali, nima daurin auren wani zanje, tare mukai masters" Aliyu ya ce "Friend dinka?" Jawad ya kalleshi sannan ya kunna motarsa ya ce "Kasan banda friends, i only have good mates" Aliyu na daga masa hannu yana dariya ya ce "Allah ya shiryeka kai dai, still dai friends din ne" Jawad baice komai ba ya juya kan motarsa ya nufi gidan Kawu daga nan ya wuce. Karfe 11:30 aka daura auren Yusuf Muhammad da Hauwa Sa'eed (Jiddah), uncountable people sun shaida dauruwar wannan aure, bayan nan akaci akasha sannan kowa ya watse. Yinin Ranar Rafi'ah a daki tayi shi tana kallo, duk da abin na damunta but she's just trying to calm herself musamman da taji muryar Abba ya dawo, lokaci lokaci Ummi kan lekata taga kallo take hankali kwance, nan kuwa ita kadai tasan abinda ke daminta deep down. Bayan isha aka shirya amarya tsaf dan kaita dakinta, Umma tayi mata fada sosai da sosai a gaban jama'a, Jiddan na kuka haka aka tafi da ita gidan Yusuf, gidan yayi kyau sosai komai sabo ga kamshin turaren wuta dake tashi. Yusuf na zaune dakin Aliyu Sameer da wani abokinsu Mukhtar suka shigo, Sameer ya mika masa ledan kaza da fresh milk ya ce "Karfe 10 saura fa Yusuf, muje mu raka ka mu wuce gida" Yusuf ya mike suka fita, shima kansa jikinsa duk yayi weak, gani yake kamar Rafi'ah fishi take dashi. Har karfe 12 Rafi'ah batai bacci ba, da taji motsin Ummi zatai pretending kamar bacci take, har Ummi ta rufeta da blanket ta fita ko motsi batai ba, Ummi na fita ta mike ta zauna, sai a sannan hawaye ya gangaro idanta, tayi saurin sharewa sannan ta mike ta shiga toilet tayi alwala ta dawo tasa himar ta tada sallah. Washegari wajajen karfe 10 Jawad ya fito daga dakinshi ya nufi dakin Abi, yana nan zaune da newspaper a hannunsa yana karantawa, Jawad ya durkusa ya ce "Ina kwana Abi" Abi ya ajiye newspaper hannunsa ya ce "Lafiya kalau Ahmad, yau bazaka fita bane?" A hankali ya ce "Zan fita amma sai da yamma" Abi ya ce "Masha Allah, yau na kira Kawunka nace Maminku ta dawo" murmushi ya danyi ya ce "Allah ya saka da alkhairi Abi, Allah kuma ya kara kiyaye gaba" Abi ya ce "Ameen" shafa kansa Jawad yayi ya rasa ta ina zai fara wannan maganar, caan dai yayi karfin hali ya ce "Abi dama inaso muyi magana ne" Abi dake kallansa ya ce "Go on Son i'm all ears"...

_08103810398_
[7/31, 10:43 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_34_

Shiru Abi yayi bayan Jawad ya fita, he can't believe this is what Jawad is seeking for, in dai kuwa hakan ya tabbata zaifi kowa farinciki, tashi yayi yana kallan clock din dake jikin wall sannan ya wuce dakinsa. Jawad bai tsaya ko ina ba sai gidan Kawu, bayan ya shiga gidan parlorn Kawu ya fara shiga ya gaishe shi sannan ya wuce dakin Mama, suna zaune ita da Mami bayan sun gama breakfast suna dan hira, Jawad na shigowa Mami ta hade rai kai kace ba ita ke hira tana dariya ba, a hankali ya zauna a kan carpet yana kallan Mama ya ce "Ina kwana" ta ce "Lafiya kalau Ahmad, ya mutanen gidan?" Ya ce "Kowa lafiya" daga haka ya dan kalli Mami ya ce "Good morning mother" ciki ciki ta ce "I'm fine" ya ce "Masha Allah" Mikewa yayi Mama ta kalleshi kafin ta ce "Bari Muhibba ta kawo maka breakfast" dan shafa kansa yayi yaja baya ya ce "Nayi breakfast Mama, zan wuce kawai" ta ce "To Allah ya kiyaye" daga haka ya kalli Mami ya ce "Sai anjima" bata amsa shi ba saima harara data bishi dashi harya fita a dakin, Mama ta ce "Bafa hake ake yiwa d'a ba Hadiza, jaan sa zakiyi a jiki amma ba ki dinga masa fada haka ba, yanzu fisabilillahi Jawad me shekara 36 dinne zaki zauna kina masa fada kamar Ikram" Mami ta ta6e baki tana kallan Mama ta ce "Kinga shi Jawad idan damuwa ya shiga bazai ta6a fada min ba, sai yayi ta shiru shiru ke kyace na Allah ne, wani lokaci sai ya gayawa matar ubansa abu ni bai fadamin ba" Mama ta ce "The best solution kawai yayi aure" Mami ta dan zaro ido ta ce "Aini bana tinanin yana hira ma wannan yaran, tinda nake da Jawad bai ta6a kawomin wata yace ta gaisheni ba, ke ko a waya ne, kinga kuwa ai watakila an sa mana hannu, amma idan ba haka ba yaro shekara 36 ace har yanzu shiru, ba aiki ya rasa ba, ga gidansa nan a gine sai aikin yin gyara ba mata a ciki, aini lamarin Ahmad yan firgitani Anty Fatima" shiru Mama tayi tana kallan Mami, caan ta danyi murmushi ta ce "Idan kin koma gida sai muyi magana" Mami ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Toh". Cikin shirinta na islamiyya ta fito tana kallan Abdul dake kwance saman kujera yana bacci, dogon hijabi ne har kasa a jikinta sai nikab a hannunta, jin footsteps yasa ta juya da sauri, juyowa tayi ta kara kallan Abdul dake kwance ta ce "Ummi why is he still sleeping?" ta kamo hannunsa taji da zafi, Ummi ta ce "Bashi da lafiya, ki tafi kawai" duk jikinta sai yayi sanyi, ta durkusa tana kallan fuskar lovely brother dinta, saam itama bataso taga bashi da lafiya, Ummi dake kallan idanta daya kowo ruwa ta ce "Don't cry here Rafi'ah, ki tashi ki wuce Islamiyya" a hankali ta dafa goshinsa ta ce "Ummi what's wrong with him, ba'a je clinic ba kuma" Ummi ta kamo hannunta tana murmushi ta ce "Stop crying daughter, insha Allah he will recover soon, munje clinic kina bacci" Rafi'ah ta share dan guntun tears dinta ta ce "Zazza6i yake yi Ummi?" Ta ce "Ehh, amma da sauki kinga yayi bacci ma yanzu" a hankali ta mike tana turo baki ta ce "Kuma baki tasheni naje ba" Ummi ta ce "To kiyi hkr, yanzu dai ki tafi karki makara" calmly ta ce "To" daga haka ta dauka jakarta akan sofa ta fita zuwa parking lot.
Sai karfe 12 Jiddah ta farka daga baccin daya dauke ta, ta dinga bude ido a hankali harta ware su duka, bata ga kowa cikin dakin ba sai dai kuma taji karar ruwa a toilet, ta mike a hankali ta zauna tana tino incident din jiya, limshe idanuwanta tayi tana jin kaunar Yusuf har cikin ranta, tana nan zaune harya fito a toilet da towel daure a waist dinsa, Jiddah tayi saurin komawa ta kwanta ganin sun hada ido, gently ya karasa kan gadon yana shafa fuskarta ya ce "How are u Jiddan Yaya?" Boye fuskarta tayi a kirjinshi tayi shiru, ya bata light kiss a forehead dinta ya ce "Thank u wife, you make me feel comfortable yesterday night" sai a lokacin ta dan dago kanta tana kallan fuskarsa ta ce "Kafa jikani da ruwan jikinka Yaya" rungumeta yayi ya dinga shafa mata sauran ruwa dake hannunsa, ta danyi murmushi ta ce "Zan rama ai" hancinta yaja yana smiling ya ce "Zamuyi dambe kuwa" ta danyi dariya ta ce "I know how to deal with u" matsowa jikinta yayi ya kai bakinshi dai dai kunnenta ya ce "And u cried yesterday night, why didn't u deal with me" boye fuskarta tayi a jikinshi tana dariya kasa kasa, ya dagata yana kallan fuskarta ya ce "Go and bath" sauka tayi akan gadon ya dinga kallanta harta shige toilet, bin bayanta yayi ya bude toilet din yana kallan yadda ta yamutse fuska ya ce "What's that" a hankali ta ce "Yaya my lap" ya kamo hannunta ya ce "Sorry dear, bari na hada maki ruwan zafi" daga haka ya hada mata just like he did before, bayan ya gama ya juyo yana kallanta ya ce "Ai kinga yadda mukai dazu, so u do exactly, kar kuma ruwan yayi sanyi" ta ce "To" daga haka yaja mata toilet din, few minutes ya shirya cikin kananun kaya ya dauki key din mota, yana shirin fita ta fito a toilet, kallansa ta tsaya yi kafin ta ce "Where are u going?" Ya ce "I want to get us something for breakfast" daga haka ya fice a dakin tabi shi da kallo, haka kawai kuma ta tsargu dashi, gani take kamar wajen Rafi'ah zaije, duk jikinta babu kwari ta shirya, tana shiryawa ta koma kan gadon ta kwanta, phone dinta taji yana ringing a kan stool, ta mika hannunta ta dauka sannan tayi answering call din, Anty Khadija ta ce "Ke bazaki kira mutane ki musu ya gajiyar biki bane? Tin da asuba nake kiran wayarki baki dauka ba" Jiddah ta kumburo fuska ta ce "Ban tashi bane lokacin" Anty Khadija taja tsaki ta ce "To sai ki tashi yanzu, anjima zanzo" ciki ciki ta amsa sannan tayi hanging call din, bayan nan ta kira layin mahaifiyarta, tana dagawa ta fashe da kuka ta ce "Anty kinji wai Anty Khadija zata zo min gida, dan meyasa bazasu barni na huta ba, kwana na daya fa" Mahaifiyarta da suke kira da Anty ta danyi murmushi ta ce "Yi shiru Auta, kyaleta tazo, watarana da kanta zata dauke kafafuwanta a gidanki, yanzu aka fara" Jiddah ta share hawayen idanta ta ce "Shi kuma kinga ya fice ya barni, kuma nasan watakila wajen yarinyar nan zaije" Anty ta ce "To yaje mana, nace miki yanzu aka fara wasan" Jiddah tayi shiru tana jin zuciyarta na zafi, Anty ta tausasa murya cikin rarrashi ta ce "Haba Auta, kiyi hakuri na dan lokaci ne, yanzu ki koma kiyi baccinki, kima saki jikinki gida naki ne miji naki ne" murmushi ta danyi ta ce "Toh Anty nah" daga haka sukai sallama. Duk yadda taso ta koma bacci kasawa tayi, bayan minti 30 Yusuf ya shigo rike da ledan take away, bata amsa sallamar da yayi ba saima juya kai da tayi, ya shigo dakin yana murmushi ya ce "Na siyo miki favorite dinki love" juya kai gefe tayi ta danja tsaki, ya ce "What? Na miki laifi ne?" Kin kulashi tayi ta mike ta dauka wayarta zata fita falo ya jawo hannunta ta fado jikinshi ya ce "who are u hissing" kallansa ta dinga yi kafin ta kara hade rai ta ce "Sai kaje ka rungume ita wacce kaje wajenta" da mamaki yake kallanta jin abinda tace, ya ce "Ko kin fara hauka ne Jiddah? What are u saying?" zame jikinta tayi a fusace ta ce "Abinda kaji shina fada, kuma ni ba hauka nake ba tinda banyi abinda za'a kirani da mahaukaciya ba, kaida kaje wajen wata da auranka ai kai ya kamata a kira da wannan sunan" daga hannunsa yayi zai wanka mata mari sai kuma ya sauke kasa ya zauna bakin gado, ficewa tayi a dakin hade da jan tsaki ya bita da kallo, bayan few minutes ya fara karanto Al~qur'an kasa kasa saboda ya samu saukin abinda yake ji.
Bayan mintina kalilan ya mike ya fita parlor, zaune ya sameta a kan kujera tana kallo, ya zauna gefenta ya ce "What comes over u Jiddah? u just change all of a sudden" a hankali ta juyo tana kallansa sai kuma ta ce "Kaje wajen yarinyar ai nasani" ya kamo hannunta ya ce "What is ur evidence? Ina san ganinta kam banyi karya ba, but ai yanzu lokacinki ne, i can't leave u at this condition" harara ta balla masa ta zame hannunta cikin nasa, tana juya kanta ta fara hawaye, ya rungumeta ta baya ya ce "Sorry if i hurt u" juyo da ita yayi yana kallan fuskarta camly ya ce "This is our first day as couples Jiddah, pls don't let shaidan deceive u" a hankali ta kwantar da kanta akan kafadarsa tana sheshekar kuka, ya dinsha shafa bayanta yana rarrashinta, ita a duniya yanzu babu wadanda takejin haushinsu irin su Anty Khadija, idan ta tuna kullukan maganin da suka bata sai taji zuciyarta na zafi, itama yanzu dama ce ta samu kuma dole tayi amfani dashi, babu abinda zaisa ta yarda su shanye Yusuf ita ta tashi a babu, kara shigewa jikinsa tayi tana limshe ido, ya dan bubbuga bayanta ya ce "Are u not hungry?" ta girgiza masa kai, dago da kanta yayi yana kallan idanta ya ce "Why? Tin jiya bakici komai ba" ta sauke kanta a kirjinshi ta ce "I will eat ltr" ya kara dago kanta ya jawota jikinshi sosai ya ce "Then we will eat together ko?" Daga masa kai tayi, ya kai bakinsa kan nata ya fara bata hot and romantic kiss...
Horn Abi yayi Mustapha ya bude gate yana daga masa hannu, bayan ya shigo yayi parking sannan ya fito, da ladabi Mustapha ya gaisheshi sannan ya tambayi Abba, Mustapha ya ce "Bari a masa magana" daga haka ya nufi apartment din Anty Amina, ba jimawa Abba ya fito sukai musabaha, yana ta murmushi ya ce "U are welcome Honorable, bismillah ka shigo" daga haka suka nufi BQ, a parlor suka zauna sannan suka kara gaisawa, Abba ya ce "Bari a kawo maka abin sha" Abi ya ce "Alhamdulilah Engineer, ba dadewa zanyi ba i have an important meeting" Abba ya ce "Ohk ba damuwa, dama 'yan siyasa are always on meeting" Abi ya danyi murmushi ya ce "Dama wata magana ce ta kawoni, and i wish u will be happy with it" Abba ya ce "I hope so Honorable" Abi ya gyara babban rigarsa ya ce "Dama yau da safe d'an wajena Ahmad yazo min da magana ta cewa yana son 'yarka da aure, so shiyasa naga nazo na fara maka magana kafin komai" still Abba yayi yana kallan Abi with shock jin abinda yace, ya danyi murmushi ya ce "That is not a problem Honarable...

_08103810398_


*Hello everyone 🤗 i hope u are all fine? if so that's my wish 🥰 Many people suna complain akan na rage yawan page, but u too should notice that da ina page biyu ne yanzu kuma guda daya nake saboda yanayin time,so kunga page daya ai bai kai page biyu yawa ba, that is it 😇 sannan masu comment are like sisters to me, i luv u so much cus d comments are melting my heart billah, Allah ya bar zumunci yasa mu karu da juna 🤲🏻 ku huta lafiya* .


*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_35_

Abba ya danyi murmushi ya ce "That is not a problem if i didn't made promise to someone, na riga nayi wa wani yaro alkawari and i'm sorry to say so Honorable" murmushi Abi yayi ya ce "Don't think u did bad, cika alkawari ai abu ne me kyau, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" Abba ya ce "Ameen, Ameen" tashi Abi yayi ya ce "To yallaboi zan wuce, a huta gajiya" Abba ya bi bayansa with respect ya ce "Allah ya kiyaye a gaida iyali" Har mota Abba ya raka shi sannan sukai sallama, bayan ya shigo ya apartment din Anty Amina. Mami ce zaune a dakinta tana shirya kayanta cikin press, daga kai tayi dan ganin wanda zai shigo, Ikram ta zauna bakin gado ta ce "Mami kinga Ya Sadeeq ya kwacemin phone dina" Mami ta ce "Let him give u, ina Yayanku?" ta ce "Yana cin abinci a parlorn Abi" ta ce "Call him for me" tashi tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo ta ce "Yana zuwa" sannan ta juya ta fice. Few minutes Jawad ya shigo da mug a hannunsa yana jujjuya tea din da spoon, Mami ta ta6e baki taci gaba da abinda take, zama yayi a bakin gado ya ce "Gani" ta ce "Magana nakeso muyi" ya ce "Ohk i'm all ears" zama tayi tana kallansa ta ce "I want u to get marriage" da sauri ya dago kansa yana kallanta, ta ce "Yes, ka samo mata aure zakiyi" sauke kansa yayi yana kallan tea din hannunsa ya ce "Ohk" harara ta dan 6alla masa ta ce "Not just ok Ahmad, na gaji da zamanka a gidan nan, ga gidanka caan kaima kayi aure ka koma" a hankali ya ce "Insha Allah" tashi tayi taci gaba da abinda take shima ya mike ya fita a dakin ta bishi da harara. A hankali Jiddah ta mike a jikin Yusuf ta dauka scarf dinta ta saka, dago kansa yayi yana kallanta ya ce "Ina zakije?" Ta ce "Zan bude kofa, baka

Please Login or Register in order to submit comment