Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dauki waya ta kira Yayansu ta fada masa abun da ya fara sannan ta dada masa cewar tana son abi mata hakkin yarta.

“Aa Umma ba a haka ko dan saboda zumunci”

Cewar Alhaji Alfa daga can cikin wayar, sai Umma ta rufe shi da masifa.

“Shi be duba zumuncin ba yai mata abun da yai? Ga ta da ciki yai mata wannan duka haka ga kuma cin mutunci saboda wasu karuwan banza a waje, ba zan lamunta ba idan kai ba zaka iya ba ni zan dauki mataki da kaina, domin ba zan lamunta aci zalin yata ba bayan bakin talauci sannan kuma ya hadota da saki bayan ya mata duka”

“Zan yi wani abu akai Inshallahu, aman ita ma ki bincike ba zai yiyu haka siddan Faruq yai mata haka ba ba tare da wani dalilin ba, Faruq ba irin mazan nan ne ba Umma, amman yanzu zan yi wani abun inshallah”

Da haka suka yi sallama, sannan Baturiya ta tashi ta shiga dakin Umma tana kuka kamar gaske, tana shiga ta bude jakarta ta dauko wayarta ta akashe ta saka wayar karkashin gadon Umma.

“Kuma cikin nan Wallahi zubar da shi zan yi, ina zubar ba na cika idda na auri saurayi kai kuma kai ta fama da talauci auren ma sai ya maka wahala”

Ta fada tana wani cika, sai a yanzu take jin zafin sakin da yai mata kukan na gaske da gaske ya zo mata.



26

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*


Madina ce take ta mata zaben tufafin da zata saka, daga atamfa zuwa abaya da shadda da kuma lace ta daukar mata kusan kala 25, ban da talkami da hijab da veil. Suna zuwa gurin biya kamin su yi wani yunkuri ta mika atm dinta. Talba ya kalleta.

“i can pay”

“Dan Allah ka bari na yi wannan aikin ladar”

Be saki cewa komai ba, ya kalli Aminatu.

“Muje mu jirata a mota”

Ba musu Aminatu ta mika masa hannu ya rikata tana takawa a hankali suka fice, kamar dazun a yanzun ma front seat ya zaunar da ita sannan ya zagaya ya zauna a side dinsa.

“You got lucky ba yayanki kadai yake son hidima dake ba, har da Kawar Matata”

Kallonsa kawai tai ta sauke kai kasa, shiru ne ya biyo baya har Madina ta fito tare da masu rika mata ledodin kayan Talba ya bude musu bayan motar suka saka, sannan ta rufe ta bude back seat din ta zauna, yana kokarin yin reverse ta mika masa box din agogon hannu that worth 150k.

“Zan yi farinciki idan ka karbi wannan kyautar daga gareni”

Kallonta yai sai kuma ya kalli Amintu.

“Shalele karba min”

Aminatu ta karba ta rike ba tare data buda ba, har suka isa gidansu Madina be karbi agogon ya duba ba, balle yai mata godiya, hakan da yai sai yasa ta ji wani iri, yanzu kam ta tabbatar akwai babban aiki a gabanta, domin samun abun da zai burge Talba a take ko kuma ya dauki hankalinsa ba abu ne mai sauki ba.
A harabar gidan ya faka motarsa, ya mika hannu ya budewa Aminatu.

“Ki taka da kafarki ki fita, kuma ki rika tafiya ke kadai ba sai an rika ki ba”

Ta lake kafada tana dan turo baki, sai dai bata ce masa komai ba kuma bata yarda ta kalli inda yake ba. Shi kam sai kallonta yake yana ayyana irin shagwabar da take a gaban iyayenta domin kana ganinta ka san shagwababbiya ce, dan farin ma wani yai shagwaba balle auta autar ma ta maza.

“Yaya Madina zaki rika ni ko?”

Ta fada tana jiya fuska ta kalli inda Madina take tsaye tana mikawa hadiman gidan ledidin hannunta.

“Eh”

Ta fada sannan ta nufo inda Aminatu take zaune ta rikata, sai da Aminatu ta aje masa agogon sannan ta fita Madina ta rufo masa motar.
A tunaninta zai mata godiyar siyayyar da tai ma Aminatu amman bata ji hakan daga bakinsa ba, ta san kuma hakan ya masa dadi ko da ba a fada ba, sai a yanzu ta tabbatar da miskilacinsa ya wuce inda take zato.
Sai da suka shige cikin main house din sannan ya ja motarsa ya bar gidan, at first restaurant ya so ya tafi ya ci abinci even though baya son cin abinci a waje sai dole, but yana son ya kaurace ma cin abincin Momy saboda ta fahimci be jidadin abun da tai masa ba, sai dai hakan ba zai saka shi gaba da ita ba, kamar yadda dazun ma be kasa kiranta a waya yai mata barka da safiya ba, bayan kuma ya saba da shiga part din ko wace safiya ya gaishe ta. Kamin ya karasa restaurant din kiran Amal ya shigo wayarsa, sai yai picking call din ya saka wayar a hands-free ya aje ta kusa da shi.

“Lil Sis”

“Yaya”

Ta amsa masa cikin kuka, ya san halinta da shagwaba sometime kan sily abu sai tai ta kuka, hakan yasa be tashi hankalinsa ba.

“Waya taba ki me kike yi ma kuka?”

“Momy ce ta yi fada da Daddy, kuma har ya sake a ta debi wani tufafinta ta bar gidan, ta bar mu ni da Leila tun dazun sai kuka muke”

Wani irin faduwar gaba ne ya same shi, sai yai sauri sauka daga titi ya faka motar gefe, ya dauki wayar ya kai kunnensa.

“Ba a wasa da irin wannan maganar Amal”

“Wallahi da gaske nake”

“Miya faru?”

“Ni na yi komai, Ya Kabir ya fada min abun da ya faru ni kuma na fadawa Daddy, shi ya zo bangaren Momy yana ta masifa and Momy ta kiraka da tsintacciyar mage, shi kuma yace ba zai dauka ba, shi ne ya saketa...”

Be ce mata komai ba ya yanke wayar, ya shiga kiran Daddy, amman har wayar tai ringing ta gaji ta tsinke Daddy be daga ba, Talba ya sake kiransa nan ma the same thing, tun yana kira yana sa ran zai dauka har ya cire rai, hakan ya tabbatar masa da cewar ran Daddy ya bace sosai, domin abu ne mai wahala yai masa two miss calls be daga ba, amman a yau ya jera masa 11 miss calls be yi picking ba. Sai ya sake kiran Amal.

“Yana gida?”

“Aa ya fita”

Ya yanke kiran sannan ya duba agogon hannunsa biyu saura kwata ya gani, take hau titi ya fisgi motar kamar zai bar gari, cikin yan mintuna sai gashi Harabar ma'aikatar su Daddy, ko fakin din kirki be yi ba ya fito da sauri ya shiga cikin ma'aikatan, kusan ya san mutane da yawa a ciki kamar yadda mutanen gurin ma suka san shi saboda yawan fadarsa da Daddy yake da kuma zuwa gurin, sai dai be tsaya gaisawa da kowa ba daman ba gaisuwar yake so ba, saboda ta zame masa kamar ta dole ce kasancewar su abokan mahaifinsa. Kai tsaye ya nufi bangaren da office din Daddy yake yana ta zuba sauri. Sai dai yana shiga sakariyar ta hana Talba ganin Daddy.

“Yace baya son a dame shi kowaye ya zo kar a bari ya shiga ciki”

“Kin san waye ni kuwa?”

Talba ya nuna kansa.

“Na sani dan Allah kai hakuri, aikina nake yi”

Ta fada cikin damuwa, sai ya wuce ta ya karasa gurin office din ya bude ya shiga ita kuma ta biyo bayansa da sauri tana kokarin dakatar da shi.

“Duk kika yi kuskuren taba ni sai na mareki Wallahi”

Ya furta yana nuna ta da yatsansa, babu alamar wasa a fuskarsa. Daddy dake tsaye yana kallonsu ya ce.

“Amman na tabbatar da kai ne, korarta zaka yi, yanzu kuma kana kokarin hanata aikinta, you can go Hannatu”

Sai ta juya da sauri ta fice. Daddy ya kalleshi.

“Ya akai?”

“Haba Daddy miya saka zaka yi haka?”

“Hey my friend, control your tongue, I'm your father and you're my son, so ni zan tambayi dalilin da zai saka kai wani abu ba wai kai tambaye ni ba”

Talba ya karaso kusa da teburin Daddy cikin yanayin damuwa.

“Daddy please, be kamata ba Wallahi, da girmanku ace kun rabu? Mu ya kake son ku yi? Baka duba Amal da Leila ba? Baka duba ni yadda zan ji ba? Da wane ido zaka kallemu? And baka yi tunanin yadda Momy zata ji ba?”

“So a idonku nine mai laifi? Ni baku ayyana yadda zan ji ba?”

“Ni kullum a gurina kai ne mai laifi daddy, kai namiji ne ya kamata ka rika kawarda ido, amman sai ka rika biyewa Momy da take mace? Hankalinta da tunaninta ba daya ba ne da naka”

Daddy yayi murmushi ya nuna masa kujera.

“Have a seat my friend”

“No ni ban zo nan domin zama ba, kawai na zo na dauke ka ne mu tafi da kai ka bawa Momy hakuri ka dawo da ita”

“Have a seat”

Daddy ya maimaita wannan karon ya fada tare da zaunawa. Sai da Talba ya sauke ajiyar zuciya sannan ya zauna.

“Fada min gaskiya, ban san ka da karya ba Son, abun da Amina tai be bata maka rai ba?”

“I feel bad, amman be kamata ya saka ka yanke wannan hukuncin ba”

“Ban yanke hukunci saboda ta kori yarinyar daka kawo ba, na yanke wannan hukuncin ne saboda ta kira ka da tsintacciyar mage”

“Fushin zuciya... ”

Daddy yayi saurin dakatar da shi with serious face ta hanyar daga masa hannu.

“No, bari na baka wani labari da ban taba fada maka ba. A cikin wani babban gida mai rufin asiri mata har hudu, kowa a wannan gidan yana da manyan y’ay’a da kanana, ko wace mace a cikin matansa ta haihu shida wata tara wata goma sha daya, sai karamar matarsa ce kawai ta haifi yaya biyu maza wanda ta kasance karama ce kuma ita ce ta hudu, tana tsaka da rainon yayanta sai mutuwa ta sallamo mata, yaya da kanensa suna daji gurin noma, ka zo kiransu aka fada musu cewar mahaifiyarsu bata da lafiya, sai dai kamin su kawo rai yai halinsa, ita ce karama kuma ita ta riga tafiya ta bar kananan yayanta guda biyu, haka yaran biyu suka tashi cikin yan'ubanci da kuma kyara ta matan uba, idan uban ya dawo sai a nuna ana son su kamar za a hade su, idan kuma ya saka kafa ya fita abinci ma sai sun yi bara su ci, wata rana kwatsan wannan mutuwar ta sake kwankwaso kofar mahaifinsu, kuma ta dage sai da ta tafi da shi, daga lokacin sai rayuwa ta kara zame musu abun tausayi, domin a gidan da suka taso gida ne da babu hadin kai a ciki, kowa kansa ya sani kuma ga kishi da nunawa uba aka hada ba uwa ba, idan aka dafa abinci masu ake bawa, ba marasa uwa ba, idan sallah ta tashi sai dai yan'uwa mahaifiyarsu su yi musu dinki, wani lokacin abinci ma a can suke zuwa su ci, suna cikin wannan rayuwarsa sai yayan ya fara bin shanu yana rakiyarsu zuwa inda ake saidawa sai masu shanun su biyashi, sai kuma ya shiga daji yai itace sai ya shiga gidaje ya bada itacen a bashi abinci sai kawo wa kanensa, kudin da yake tarawa kuma idan kanensa yana jin yunwa ko rashin lafiya ta kama shi, zai siya masa magani ne, da haka ya fara faskare, da duk wani aikin karfi da yan'uwan mahaifiyarsa suka samu labari sai suka zo suka dauke su suka tafi da su gurinsu, sai dai hakan be kashe guiwar yayan ba, da yan kudin da ya samu ya saka kenansa a makaranta, kullum kokarinsa na yadda dan'uwansa zai gina kansa ne, da wannan tunanin ya tsallaka zuwa birni yana achaba, daga nan ya fara zuwa kudu, idan ya samu kudi sai yace a bawa Mu'azu, a siyawa Mu'azu abu kasa, a biya masa kudin makaranta, sannu sannu dan'uwansa yana ta karatu shi kuma yayansa yana ta neman kudi saboda rayuwar kanensa ta inganta, achaba da yake a can sai ya karbe shi har ya zamana yana zuwa siyen wasu abubuwa daga nan arewa ya kai can, wani abun kuma sai ya siyo ya zo da shi nan, kamin a ankaro kudi suka taso masa kofafin arziki suka bude masa, sai ya dawo a nan yai aure, ana zaune kalau kanensa yana zuwa makarantar kwana a birni idan hutu ya samu sai ya dawo gida, sai matar yayan ta fara nuna bata son kanensa tana hana shi yi masa wasu abubuwan daya kamata, ganin haka yace ba zai iya sake dan'uwa ba, amman zai iya canja mata, sai ya sake ta ya auro wata, ita ma da ta zo sai ta fara nuna wannan halin, a take ya sallame ta ya auro wata, bayan ya jaddada nata cewar shi kam a duniyar nan be da kamar dan'uwansa, sai matar nan ta rike kenan da mutuncin da amana, shi kuma ya maida hankali gurin kasuwancinsa, har ya zamana yayyunsa da suka wofintar da shi a wacan lokacin suka dawo suna neman ci a karkashin inuwarsa, wasa wasa ya fara siye gonaki da gidaje irin na kauye yana saidawa yana samun riba, kamin kace kwabo ya zama daya daga cikin masu kudin kauye na wacan lokacin duk da kasancewar yana da samarta ba tsoho ba ne, da haka ya fada siyasa sai kuma abun ya karbe shi kofofi suka bude masa, yai taraka kuma ya cinye, sai dai har kanensa ya gama karatu ya tafi jami'a Allah be bawa yayansa haihuwa ba, yana cikin karatun ya hadu da wata a jami'ar suka yi aure, yayan ya siya masa gida a birni suka zauna, ana wata na uku da saurensa ya samu aiki a babban gurin saboda yayansa babban dan siyasa ne na taraiya, a kuma wannan lokacin matar yayan ta samu ciki, a kullum wakensa idan ta haifa masa namiji za a saka sunan kanensa, idan kuma mace ta haifa za a saka sunan mahaifiyarsa, ashe Allah be yi ba zai ga abun da zai haifa, wata rana aka samu wani gurbi na babban matsayi a Lagos, sai ya dage akan sai kanensa za a bawa saboda yana da takardu da duk wani abu da ake bukata, sai dai abu na yan siyasa su ma wadancan suna so, bayan ya bada sunan kanensa da takardunsa, sai abokin hamayyarsa yace ya saurari abun da zai same shi matukar be janye kudirinsa ba, be fada masa baki da baki ba, amman ya fada ta inda zai iya ji kuma ya ji, amman be janye kudirin ba, abun ka da mutanen kauye ana zaune kalau kafarsa ta fara kumbura har ya zamana baya iya zuwa majalisa, har ta kai ko gidansa baya iya fita, cikin sati jikinsa ya kumbura kamin wani makon ya dawo ya ce ga garinku, haka muka ta jimamin rashinsa musamman ne kuma mutuwarsa bata hana Allah hukuncinsa ba na dora ni a wannan matsayin, ashe kuma wani kukan yana tafe a gaba, a lokacin da muke ta murna matarsa ta shiga watan haihuwarta zata haifa mana da ko ya, ashe ban kwana take ta mana ba mu sani ba, ranar da ta haihu aa fiti ana da lafiya kalau mahaifiyarsa kuma ta koma ga Ubangijinta... ”

Tun da Daddy ya fara bawa Talba labarin be mumfasa ba sai da ya kai aya.

“Ka san waye wannan yaya da kanen Mu'az...?”

Talba ya kalli Daddy hawaye na sauko masa, kamar yadda suke saukowa Daddy.

“Kai ne kanen Daddy shi ne Yayanka... ”

Daddy ya girgiza kai yana cige bakinsa da karfin sosai yake yakar zuciyarsa yana hanata kukan dake son gabato masa da shi, daya wuce na zuciya har yake neman muhalli a bakinsa.

“A haka kaka tunanin wata macen zata kalli kwayar idona ta kira dan 'uwana na jini da jini da tsintacciyar mage kuma na kasa fusata na kasa yin komai? Macen da take karkashin ikona da kulawata? Ina raye wata mace tana nuna min tafi son yayanta da dan'uwana na jini? Ina jin sonka a cikin jinina Mu'az, ina jin wani irin son a jini da zuciyata, bana jin akwai wani uba da yake son dansa kamar yadda nake sonka, ko kadan bana son na ji wani abu da zai bata maka rai, zan iya daukar komai ban da a taba ka”

Talba ya mike tsaye hawaye na sauko masa ya nufi windows din office din Daddy ya tsaya. Sai Daddy ya dauko tissue ya goge hawayensa yana kallon Talba.

“Ban taba baka labarin nan ba, saboda bana son ka ji a ranki cewar kai maraya ne, alhalin ina raye”

Talba kamar jiran kalaman Daddy yake, sai ya fashe da kuka marar sauti irin na maza ya jimke hannunsa zuciyarsa na sosuwa da labarin da Daddy ya bashi. Da hannunsa na dama ya share hawayensa sannan ya juyo ya kalli Daddy yana jin wani irin shaukin kaunarsa.

“Ka yi duk abun da ya kamata Daddy, shiyasa ban taba jin maraici ba, kuma ban taba tambayar labarin iyayena ba, ka bani gata ka nuna min kauna wanda ba ko wane mai uba ke samu ba”

“Abun nan akwai ciwo Mu'az, saboda ni ma na taso a maraici, kana ji kana gani abu ya gagareka, kana gani a nun maka abu nan ba naka ba ne, idan aka bata maka rai, babu uwa ko uba da zai rarrasheka ya baka hakuri, musaman ma uwa, shiyasa ba zan taba bari kai maraici ba, idan har kaga ka rasa sai idan bana raye, ko da ma ace na mutu na ginaka kuma na bar maka abun da zai taimaki rayuwarka ba zaka taba rasa komai ba, ba zaka taba kukan rashin uwa ko uba ba, musamman uwa”

Talba ya gyada kai wasu hawayen na sauko masa.

“Kamar yadda na ji a yanzu nan Daddy, amman duk da haka Ina rokon Alfarma a yafewa Momy, ita ma ta rike ni kamar danta, na taso ban ta wata uba ba bayan ita, dan Allah Daddy ka dawo da ita”

“Of course zan dawo da ita, do you think I can live without Amina? Zan dawo da ita amman sai ta karbi hukuncinta, ni ma ina fatar za a daga min kafa”

Talba yayi murmushi idonsa na cika da wasu hawayen.

“Ina kaunarka Daddy, Allah kara maka lafiya”

“Amin Allah ya maka albarka”

“Amin”

Ya amsa sannan ya dauki tissue ya gyara idonsa, sannan ya nufi kofar fita.

“Mu'az ina ka kai yarinyar nan?”

“Gidansu Madina”

“Ka dawo da ita gida”

“A can din ma ta fi sakewa, Madina tana sonta”

“Baka da inda yafi gida, kuma be kamata akaita ko'ina ba, bayan ga inda kake da iko”

“Na ji, amman sai ka fara dawowa da Momy”

Daddy yayi murmushi yana daga masa hannu alamar ya tafi, shi ma murmushin yai kadan ya fice yana jin zuciyarsa wani iri, samun kansa yai a motarsa yana ta sauke ajiyar zuciya, be taba jin irin yadda yake ji a yau ba. Sai dai babu wanda ta fado masa a rai sai Aminatu, shi da be taba ganin iyayensa ba, be san su ba amman a yau yaji yana marmarin ganinsu yana kewarsu balle ita data rayu da iyayenta ta girma tare da su ta san dadinsu ace an raba ta da su lokaci daya, kuma a gaban idonta, ya tabbatar abu ne da ba zata taba iya mantawa da shi ba, ba kuma zai gogu a zuciyarta da idanuwanta ba. A masallacin gurin yai sallah azahar sannan ya fito yana ta tukin ba dan ya san inda zai je ba, baya tunanin zuwa gida a yanzu, dan baya jin zaman gidan zai masa dadi, but ina zai je? Office? No baya bukatar komawa can, gurin Ali? Nope zai fara damunsa da maganar Leila, haka yai ta yawo idan ya gaji da tukin sai ya saka motarsa ya zauna a motar, uku da rabi ya nufi gidan marayunsa be fito ba sai hudu da rabi. Kai tsaye ya nufo gidansu Madina domin zuciyarsa ta bukaci ganin Aminatu, be kira Madina ya fada mata gashi zuwa ba, balle ta san da zuwansa, he just want go ba tare daya sanar mata ba, sai da ya isa gate din gidan sai kuma ya ji wani iri, kar mutanen gidan su ce ya cika zuwa, tun da dazun ma ya zo, gashi yanzu baya cikin yanayin na walwala. Amman ya kamata ya koma b tare da ya ga Aminatu ba? Bayan ya kudurtawa kansa son magana da ita? Hannu ya kai ya dannn horn sau biyu mai gadin ya leko ya ganshi sai ya koma ciki ya bude masa gate din. Tun kamin ya karasa harabar gidan ya hango Aminatu zaune a parking lot sanye da daya daga cikin rigar da suka siyo dazun picking color, bakinta ya sha man lebe har wani sheki yake gashin kanta kuma ya sha gyara, an basa mata shi ya sauko har bayanta, sai wata yar karamar farar hula wanda ke bayyana gashin tsakiyar kanta da kasan gashinta, sai a lokacin ya tuna dazun be kaita gurin gyaran gashin ba, and now he think Madina ta kaita ko kuma ta gyara mata. Tana zaune kan kujera kusa da wata mota, sai dan karamin teburi a gabanta mai cike da littafai textbooks hannunta rike da biro. Ana bude gate din ta dago tana kallon motarsa har ya karaso kusa da ita ya faka motar ya sauke gilashin motar yana kallonta. Ita ma kallonsa take har ya bude motar ya fito ya rufe a hankali ya karaso kusa da ita cikin yanayi na damuwa.

“Ina wuni”

“Lafiya kalau, me kike a nan ke kadai?”

“Na gaji da zama ciki ne shi ne Ya Madina ta fito da ni tace wai na sha iska, ta bani abun rubutu”

“Kin iya rubutu ashe?”

“Ajami ba”

Ya kai hannu ya dauki littafin da take rubutu akai.

_Ina samun natsuwa a kalamanka, kamar yadda ganinka ke kwantar min da hankali, rashinka yana nufin mutuwata, samunka kuma farincikina_

Yayi murmushi bayan ya gama karantawa, sannan ya kalleta.

“Ashe kin iya kalaman soyayya”

Sai tai kasa da kanta tana murmushin daya kara bayyana kyauta da hasken bakar fatarta.

“Ina rubutawa wani saurayina shi kuma yana rubuto min, idan zan tafi talla sai ya ba ni ta shi, ni kuma na a shi tawa, duk da ajami muke rubutawa, kamin rayuwarmu ta canja, ni na dawo nan shi kuma ya tafi inda ba a dawowa”

Ta karasa idanuwanta na cika da kwalla. Sai ya risina gabanta yana kallon kyakkyawar fuskarta.

“Kin rasa abubuwa da yawa, kina da juriya na injina miki, yanzu fada min ya kike ji?”

Ta dago ta kalleshi.

“Ba dadi, sabawa da mutanen da baka sani ba, abu ne mai wahala, na kasa manta iyalina”

“Na fahimta”

Ya fada yana kallon wani gurin dabam, hakan ya bata damar kare masa kallo, fari ne fes irin farin nan mai kyau da daukar ido, ga wani dogon hanci da sauko masa gashin kansa ma sai sheki yake, abu ne mai wahala a iya yi masa kallo daya a kawar da ido. Ba kyaunsa ne kadai abun da idanuwanta suke nuna mata ba, har da damuwar dake fuskarsa domin bata taba ganinsa a haka ba.

“Kai ma kana da damuwa...?”

Ta tambaya cikin tsoro da fargabar irin amsar da zai bata, juyowa yai ya kalleta sai tai arba da kyakkyawan Murmushin daya fadada fuskarsa.

“Ya akai kika gane?”

Ta yi shiru tare da sauke idonta kasa.

“Ina ce miki Shalele kin cancanci sunan, saboda kin rayu da iyeyenki kin jin duminsu, kin san muryarsu, kin san farincikin da damuwarsu, a karon farko yau na ji ina kewar mahaifiyata duk da kasancewar ban taba ganinta ba, amman ina jin kamar na kirata ta amsa min, kamar tace Talba be
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment