Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

mata sorry.

“Idan wani abu ya faru a tsakaninmu, ki bar shi a tsakaninmu ba zai wani ya ji ba”

Ya fada sannan ya juya, sai kuma ya juyo.

“And if you need something, lemme know”

Yana fadar hakan ya juya ya fice ba tare da ya rufe mata kofar ba. Tabe baki tai ta mike tsaye ta isa gurin kofar ta rufe ta juyo ta dawo gaban madubin ta zauna. Har ga Allah tana son Talba, kuma ta san yana sonta amman abun da yake mata is yayi yawa, girman kansa da jin kansa yayi yawa, that's why dazun ta fadawa Daddy cewar bata shirya aurensa a yanzu ba sai nan gaba, Momy kuma ta goya mata baya ganin kullum ita ake kwaruwa, but this time around Momy ta goyi bayanta.
Jin wayarta ta yi kara alamar sako yasa ta mike tsaye ta isa gurin da wayar take ta dauka ta duba sakon.

“Good Night”

Shine rubuce da number Talba, ba shiri ta zauna tana mamaki. Da gaske shi ne ya turo mata sakon ko wani dai? Dan murmushi.

“Duk sai na rama abun da kai min, it's my turn”

Ta fada tana jin wani irin dadi, juya ido tai.

“Ya kamata ya san ina da tsada”

Ta fada sannan ta kwanta saman gadon.


*** *** ***
Kamar jiya Saturday, yau kuma Sunday, kowa yana zaune a teburin cin abinci ban da Daddy da zai karya bangarensa da kuma Leila da take dakinta.

“Ina Leila?”

Talba ya tambaya yana kallon Amal.

“Tace zai ba zata fito ba”

“Why?”

“Just”

“Hada nata breakfast din na kai mata dakinta”

Ba Momy da Kabir ba, ko Amal har Baaba mai aikinsu sai da ta kalleshi.

“Kamar dai ba kai Talba”

Kabir ya fada, sai Talba yayi murmushi kadan.

“Sounds funny, right?”

“No sounds new”

Momy ta yi murmushi.

“Ban fada muku ba? Wata rana Talba zai canja”

Ya mike tsaye ya shiga hada ma Leila nata abun karyawa.

“I didn't change, ina yi ne for the sake of you and Daddy”

“So na dan ra'ayin kanka kake ba, kenan baka farinciki da abun da kake, doesn't make sense”

Kabir ya fada yana tabe baki. Talba dai be sake ce masa komai ba har ya cirewa Leila komai ya dauka ya nufi upstairs. Amal ta mike da sauri ta bi bayansa ta rigashi karasawa gurin kofar ta bude masa saboda hannayensa duka biyu suna dauke da abu ne. Yana shiga Amal ya janyo kofar ta rufe, har gefen gadonta ya aje mata komai sannan ya dago ya kalleta.

“Good Morning”

Ya sake gaisheta duk da kasancewar ya aika mata da sakon gaisuwa da safe kuma bata masa reply ba, which is pain her. Bata amsa masa ba sai kallonsa take.

“Ga breakfast dinki, idan kina bukatar wani abu ki fada min”

Yana fadar hakan ya juya, sai da ya kusa isa kofa sannan ta ce.

“Anjima zaka kai ni shopping”

“Idan kin shirya ki kirani”

Ya fada ba tare da juyo ba, sannan ya fice ya ja mata kofar. Yana saukowa downstairs be koma dinning din ba sai ya nufi kofar fita, yana fitowa ya tsaya bakin kofar falon ya kira Ali. Kamin Ali yai picking Kabir ya fito ya tsaya daidai inda yake tsaye.

“Kasan mi ye Talba?”

Talba ya kalleshi yana kokarin yanke kiran Ali da yake.

“Kai dan'uwana ne, ba zan so ka cutu ba, kamar yadda ba zan so Leila ta samu matsala, ni shawarar da zan baka karka auri macen da baka so, domin zaku yi ta samun matsala ne kawai, ji abun da kake yi a yanzu saboda Momy da Daddy kake yi ba wai dan ka faranta ranta ba, kuma ba dan kana so ba, hakan kuma zai haifar da kiyayya da tsana a tsakaninku”

Talba ta saka wayar aljihu yana kallon Kabir.

“Ina sonta Kabir...”

“No, maybe dai kana sonta saboda baka san miye so ba, ko kuma kana sonta saboda baka son ka bawa Daddy kunya, ko kuma kana sonta saboda kana son ka yi aure, amman na san wata rana zuciyarka zata so wata wata kila Leila ce ko wata dabam, a lokacin da zata maka laifi kuma na bata hakuri Wallahi baka ko sani ba, wanda zaka so faranta mata a karan kanka, idan tana cikin damuwa kai ta kokarin ganin ka cireta, idan tana kuka karika jin hawayenta kamar mutuwarka ne, duk wannan shan kunun da kake yi ita zaka sake mata ka rika neman tai maka murmushi kana mata dariya, idan zuciyarka ta fara wannan son, duk son da biyayyar da kake yi ma Daddy ko Momy idan suka muzantata sai ka ji ba dadi kamar kai aka yi ma, daga lokacin ne rayuwarka zata fara canjawa...”

“Noo Kabir, you know i don't believe in love, so wannan daren ba zai taba zuwa ba balle har na kwanta na yi wannan kalar mafarkin, ku ne da kuke karance karance da kallo fina finai kuke dauka irin wannan soyayya gaskiya ce, even if gaskiya ce ma ni bana cikin irin wadannanhawayen mazan...”

Yana fadar hakan ya fara sauka entrance din. Kabir ya bishi da kallo yana murmushi.



AMINATU POV.

Sai da haske ya fara bayyana sannan mutane suka leko gidan, duk da kasancewar kowa yana fama da nasa jimamin. Duk wanda ya shigo ya tararda gawar su Amadu sai ya zubar da hawaye, daman can kowa ya saka ran sai ayi musu ta'asar da tafi ta kowa saboda suna da yan sa-kai har biyu da da barayin yankin suke matukar tsoronsu, domin basa yi ma barayi da sauki musamman idan sun hadu da su a wani gurin. Da taimakon yan tsirarun garin da suka rage aka dauko zage aka rufe gawarsu, Sanusi kuma aka dauke shi kan babur zuwa babbar asibitin shimkafi, a lokacin ne Inna ta fahimci har da Musa aka kashe, kuma aka tafi da matansa biyu bayan matar matar Amadu, cikin yaranta da suka tsira Aminatu ce kawai ita ma dan ba su ganta ba ne, sai kuma Isa da ya tafi kai Baba gurin ganin Gwaggonsu, sai kuma Bashiru dake kasuwancinsa a birni tare da iyalansa.
Karfe bakwai da yan mintuna Baba ya iso cikin gidan, domin labarin abun da ya faru ya same shi a can garin da yake gurin kanwarsa, yana shigowa cikin gidan ya kasa rike kansa, tsayi ma ya kasa duk da kasancewarsa namiji sai gashi ya zube kasa yana kuka da idonsa, Inna kam zaune kawai take tana kallon komai, hawayen sun dauke mata. Da dai daya Baba ya fara bin gawar yayansa har hudu yana dubawa, Isah ma kuka yake sosai, ya ga Amadu da ka fashewa kai, sai kuma Rilwanu, da aka takewa wuya da babur, haka Musa na da dutse aka fashe masa kai. Iro kam gawarsa bata wuce ta karamin jariri ba domin gawarsa ta kone kurmus daker aka samu aka hada dan abun da yai saura gudu daya aka lullube da zanen Inna.
Baba ta fadi zaune ya fashe da wani irin kuka yana dora hannu saman kai.

“Allah ka hana zalinci, Allah ka sani mutanen nan ba mu musu komai ba, Allah ka isar mana”

Baba ya fada cikin wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya, sai kuma ya juyo ya kalli dansa Isah da shi ma kukan yake ya ce.

“Isah ka gani an kashe an yan'uwanka...”

Daga inda Inna take zaune ta amsa.

“An kashe su Malam, d'a hudu, ni na haifi yarana kuma a gaban idona aka kashesu, yaran da ba su wuce sa'an yayana ba suka keta min haddi har su goma sha daya, a gaban yata, suka kone muna abinci, suka kora mana dabbobi, saboda kawai zalinci, titin kwarai ba mu da shi a garin nan, ba mu damu da cigaban zamani ba, taki ma sai an ga dama a bamu, duk wani cigaba ko aikin taimako ba mu san shi ba, da hakkinmu muke tara komai, yanzu kuma zaman lafiya da farinciki ya gagaremu...”

Inna na gama fadar hakan ta mike tsaye da sauri jin kamar numfashinta zai fita, ta dora hannunta a kirji tana kuka tana neman agajin Allah.

“Innalillahi, shikenan sun raba ni da murmushi sun raba ni da dariya, kuma sun keta rigar mutunci na”

Safa da marwa ta fara yi cikin gidan hannunta akai tana kuka tana jijjiga. Duk abun da ake a kunnen Aminatu, domin bachin da take son ya dauke ta ta sake farkawa a rayuwar zahiri be dauke ta ba, har lokacin kuma jikinta be daina rawa ba, kamar yadda kunnuwanta ba su daina jin karar binga, haka idanuwanta ba su kawar mata da ganin da tai ana yi ma mahaifiyarta fyade ba.

“Ina Auta? Ko sun tafi da ita?”

Baba ya tambaya yana kuka sosai, sai wata matar dake tsaye kusa da Inna tana kokarin bata hakuri ta ce.

“Aa tana daki”

Duk wanda ya ji ko ya ga ba aje da Aminatu ba ya san da cewar ba su ganta ba ne, yadda suka kwashi matan garin suka tafi da su babu abun da zai hana su zuwa da Aminatu. Baba ya tashi da sauri ya shiga dakin, sai ya same ta a inda ta saba kwanciya tana lullube, ba jikinta kadai ba, har hakoranta kana jin kara yadda suke haduwa da juna tsabar yadda jikinta yake rawa. Baba ya kai hannu ya janye mayafin sai ta tashi da sauri idonta a kumbure ta kalleshi.

“Baba...Baba... Baba... Baba”

Baba ya sake fashewa da kuka.

“Baba wasu mutane ne suka zo.. Ba mu musu komai ba Wallahi, ba mu musu komai ba... Sun... Sun... Sun... ”

Ta kasa fada sai ta fashe da wani irin kuka ganin cewar da gaske ne komai ya faru ba mafarki ba.

Ba ko wace gawa ta samu sallah da sutura yadda ya kamata, saboda yawan gawarwakin, ashe ma samun sutura da masu yi ma gawa sallah da kuma binne ta kamar yadda addini musulunci ya tabadar wani abu ne da ba kowa yake samu ba, domin wasu da tufafin jikinsu ake saka su a cikin ramen, wani ramen kuma sai a hada mutum hudu guri daya.
Bayan an binne gawarwarkinsu ne, Bashiru ya iso, hankali tashe, yana shigowa shi ma ya fara nasa kukan, na rashin yan'uwa. Aminatu kam tana can gefe daya zaune ta ki yarda ta zauna cikin mutane ko kallon mutane bata so, kuma ta ki cin komai. Sai da ta ji Baba yana maganar zai tafi asibitin gurin Sanusi sannan ta mike tsaye da sauri.

“Baba dan Allah ka tafi da ni”

Ta fada cikin kuka, wani irin tsoro take ji ganin take kamar sake dawowa zasu yi, gaba daya a firgice take, a dayan bangaren kuma tana son ganin halin da dan'uwanta yake ciki.

“Aa Auta ki zauna a nan, asibi ce fa”

Ta yi saurin rike rigarsa ta fashe da wani irin kuka.

“Dan Allah Baba ka tafi da ni, ka taimaka min dan Allah Baba ka tafi da ni”

Idon Baba ya sake cika da kwalla.

“To saka talkaminki mu tafi”

Ta saka talkamin dake kusa da ita, bata tsaya neman nata ba, haka suka fito cikin gidan tana rike da rigar Baba, Baba ya nuna mata wani babur.

“Ki hau Babur din Buba, ni zan hau na Isah”

Sai ta girgiza masa kai tana kuka ta rumgume shi.

“Aa Baba Baba dan Allah karka sake yin nisa da ni”

Gani take kamar idan yana nan babu abun da zai faru, gaba daya ta rasa gane kan komai, kwakwalwarta ba zata iya dauka ba.
A dole babur daya suka hau ita da Baba, dan motsi kadan sai ta ji kamar zuciyarta zata fado tsabar tsoro, har suka isa idon a rufe yake domin ganin take idan ta bude ido mutanen zata gani.
Ko da suka isa sun tararda asibitin a cike, domin a kauyensu ko a gidansu kadai akai ta'asar ba, an kawo mutane da yawa, wasu sai ihu suke wasu kuma suna zaune suna jiran a gama da wasu a duba su. Baba da Aminatu waje suka tsaya Isah ya shiga ciki, ganin ya dade yasa Baba ya shigo cikin emergency tare da Aminatu, gaba daya ta kara firgicewa ganin yadda wasu ke zubar da jini. Kamin su karasa inda suke zaton dakin da Sanusi yake ne, Isah ya fito yana kuka.

“Lafiya?”

“Baba babu Sanusi, Sanusi ya tafi sai dai idan mun isko shi, Allah ya jikanka Sanusi...”

Ya fada yana kuka, sai ga gawarsa an fito da ita. Aminatu bata san lokacin data saki rigar Baba ba ta ruga da gudu gurin gawarsa, duk ita duk tsoron gawa da take yau ta manta da wannan.

“Wayyo Allah na shiga uku, Ya Sanusi”

Sai kuma ta juyo da gudu gurin Baba dake kuka ta rike shi.

“Baba kai yi wani abu dan Allah Ya Sanusi ya tashi”

Baba ya girgiza mata kai yana wasu irin hawaye masu zafi.

“Ba ni da rayuwa Aminatu, sai hakuri”

Sai ta sulale kasa ta fashe da kuka.

“Wayyo na rasa Yaya mai sani dariya, yayana mai tsokanata, Yayana mai so na”

Baba ya duka kamar zai mata magana sai dai shi ma bashi da zuciyar yin haka a yanzu, sai ya kara fashewa da kuka.

“Allah ya Isar mana Allah ka isar mana”

Isah ya fada yana kuka, duk wani mai sauran imani da tausayi sai da idonsa ya cika da hawaye saboda tausayi. Zunbur tai ta tashi tsaye.

“Baba ku duba kila be mutu ba...”

Rugawa tai zata tafi gurin gawar sai Isah ya riketa, wani irin tsalle tai tana son ta kwaci kanta daga rikon da yai mata amman ta kasa, ta fisgi kanta ta fisga ta sake fisga ta sai fashe da tana jin kamar ace yau akwai abun da zata iya yi ta dawo da rayuwar Sanusi.



>>>>>>

If you want to subscribe pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, and send the evidence to 08036126660, zan yi adding dinki paid group In-sha-Allah.


________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -6️⃣

Bakincikin mutuwa, da damuwar rasa rai, wani irin bakinciki ne da yake ma kansa muhalli a zuciyar bawa, baki yayi kadan ya bayyana yadda zuciyata take ji, haka zuciya ma ba zata iya daukar abun ita kadai ba har sai da taimakon idanuwa da gangan jiki.
Taya Aminatu zata fadawa kowa yadda take ji? Taya zata rasa yayyu biyar maza kuma ta kasa kuka? Taya za a maida garinsu da gidansu kamar kufai kuma ta kasa kuka? Taya za a keta haddi mahaifiyarta a gaban idonta kuma ta kasa kuka?
A tsakanin rasa yan'uwanta da kone musu abinci da keta haddin mahaifiyarta bata san wani yafi wani zafi ba. Anya zata iya dauka?

“Duk ni kadai?”

Ta furta wasu hawaye mazu zafi na sauko mata, kana ganin yanayinta da kuma jin kalaminta kasan bata cikin hayyacinta, ruwan hawayen dake mata zuba har ya canja launin fatar idonta, ya kumbura mata ido, kwayar idon kuma ta mata ja sosai.

“Auta dan Allah ki yi hakuri, haba kowa ba yana da tabon mutane nan a garin nan”

Anty Aina'u matar Bashiru ta fada tana kai hannu ta dafa ta. Aminatu ta kalleta kamar tace mata shiga zuciyata ki gani, sai kuma ta dauke kai ta hadeye yawu.
Har aka yi gaisuwar kwana uku aka watse Amintu bata daina kuka ba, kukan da ta sha ko Inna bata yi ba, domin Inna ta bar komai a zuciyarta ne, idan ta yunkurin kukan ma baya zuwa mata, sai dai bata iya komai ko bandaki zata zagaya sai an rikata. Idan kuma ta zauna ta sanda kai kasa bata iya dagowa sai an rika kan nata an dago da ita. Kana ganinta ka san kukan zuci take wanda ya fi na ido illa.
Washe garin Ranar da aka watse Aminatu na tsakar gida tana wanke wanken kayan abincinsu, sai kawai ta fashe da kuka, rayuwarsu take tunawa kwana hudu zuwa biyar da ya wuce, a da idan tai wanke wanke kowa zubawa ake, amman yanzu daga ita sai Isah da Inna da Baba kawai suke ci, ba kamar da ba. Tunawa da tai da maganganun da mutane suke mata cewar ta yi hakuri ko dan ta karfafawa mahaifiyarta guiwa yasa tai saurin share hawayen. Ta cigaba da wanke wanke bayan ta gama ta dauki kayan ta kai a inda suka saba ajewa ta aje. Sannan ta fara sharar gidan, tana yi tana ta ganin inda aka aje gawarwakin yan'uwanta, ta kasa daina ganin abun a idonta.
Bayan ta gama sharar ta dauko tabarma ta shimfida daga bakin kofar sannan ta shiga ciki ta riko Inna dake kwance.

“Inna muje waje ki sha iska”

Daman zaman dakin ya fara isarta, sai ta yunkura, Aminatu ta taimaka mata ta mike tsaye tana takawa a hankali har suka fito, Aninatu ta zaunar da ita a hankali, sannan ta koma ciki ta dauko filo ta jingina mata a jikin ginin na kasa, ta jinginata. Take Inna ta sauke wata irin sanyayyiyar ajiyar.

“Allah ya miki albarka”

“Amin”

Aminatu ta amsa hawaye na sauko mata ganin yadda rayuwata ta sauya mata ita da mahaifiyarta a lokaci daya. Inna ta sakar mata murmushi sannan ta soke kai kasa. Madafa Aminatu ta nufa ta kunna wuta ta dora tukunya ta zuba ruwa. Sannan ta koma ta auko shimkafar da yayanta Bashiru ya siyo musu ta fara tsinta.

“Ji dan Allah ko tsintar shimfar bata iya ba...”

Ta lumshe ido da sauri tunawa da yayanta Sunasi da tai, yana yawan tsokanarta komai take sai yace bata iya ba. A hankali ta daga kai tana kallon ginin da yai domin yana daf da aure shi da Isah. Duk yadda ta so ta tana kanta hawaye sai ta kasa, hannunta ta saka ta share hawayen tana jin kamar wani nauyi a zuciyarta.

“Ashe haka ake ji idan aka rasa rai”

Ta furta a hankali tana kokarin tsayar da kukanta, sai kuma tai murmushi da yafi kuka ciwo.

“Mutuwa bakin takobi mai raba uwa da daya, ta raba yan'uwa ta raba mata da miji, kin maida mana gida kamar kufai”

Ta damki shimkafar a hannunta wasu hawayen na sauko mata kamar ba gobe, a dole ta aje gyaran shimfara saboda hawaye ya hana ta ga komai.

“Auta...”

Ta juyo da sauri jin kamar muryar Inna ta kirata, sai dai ganin kanta a noce ya tabbarta mata ba kiranta tai ba, muryar dai ce take jin kamar ta Inna. A take ta fashe da kuka ta bar gaban murhun ta mike tsaye wanda hakan yai sanadiyar barewar shimkafar da ke jikinta ta nufo inda ta gudu ta fada jikinta tana kuka. Sai Inna tai saurin lumshe idonta da sauri tana jin kukan Aminatu har cikin ranta, tana son tace mata yi hakuri amman bakinta ya mata nauyin da take jin kamar maganarta ta kare a duniya, sai kawai ta daga hannunta ta dora a jikin Amimatu tana shafata alamar rarrashi.

“Miyasa wani zai ji bakinciki da farinciki mu? A kauye muke zaune amman muna jindadi rayuwarmu, miyasa za su ruguza farincikinmu? Na kasa saba da rashin Yaya Sanusi Inna, Inna yanzu waye zai sake tsokanata? Yaya Amadu mai min fada baya nan, yaya musu mai bamu abinci baya nan, sun kashe Yaya Rilwanu da Yaya Iro...”

Inna ta bude idonta ta saka hannu ta kama fuskar Aminatu.

“Zan tafi na barki Aminatu, yar Autana, ina son ki saba da hakuri, akwai kalubale a gaba, mace da ta tashi a cikin gata da soyayyar uwa da uba da yan'uwa irin ki, duniya ta sauya mata lokaci daya? Dole zata ji ba dadi kuma zata fuskanci kalubale, amman zan fada miki wani abu, ina son ki rike ki rika maimaitawa, a duk lokacin da kika tsinci kanki a damuwa ko kika ga wani abun tashin hankali bakinki ya saba da furta Innalillahi Wa'inna Ilaihirraji'un, ri rike wannan kin ji”

Aminatu ta kalli Mahaifiyarta hawaye na sauko mata.

“Inna idan kika mutu kuma zai ki yi tsammani ni zan rayu? Wannan wace irin magana ce?”

“Zaki rayu Autarta, dan na mutu ba shi yake nufi ki mutu ba, Allah be raya wani dan wani, kuma be kashe wani dan wani, da ya bar yayana dan ni, ko kuma ya bar su dan ke, yadda ya so haka yake”

“Inna maganar da kika fada min yanzu, ta fi min ciwo fiye da rasa rayuwar yan'uwana, kada Allah ya nuna min ranar da zaki tafi ki bar ni, sai dai ni na tafi na barki”

Ta fada cikin kuka sannan ta rumgumeta. Inna ta sake runtse ido tana jin wani kololon bakinciki yana mata yawo a zuciya. Suna haka Baba ya shigo rike da yar ledarsa ta dawo (Fura) ganinsa yasa Aminatu ta tsagaita kukanta ta daga jikin Inna tana fyace hancinta.

“Kukan dai ne be kare ba”

Ya fada yana zaunawa kusa da Inna kana ya aje mata ledar furar.

“Ga fura Auta ta dama miki na san ba iya cin wani abua kike ba”

Kallon furar kawai tai ta dauke ido.

“Baba sannu da zuwa”

Aminatu ta fada da muryarta ta kuka, wai Baba yai mata murmushi irin na su na manya domin shi kansa juriya kawai yake irin ta maza amman ya ji zafin mutuwar yayansa, da kuma keta haddi matarsa. Hannu biyu Aminatu ta saka ta dauki ledar furar ta nufi gurin da suke aje ruwa ta dauko kwanon ruwa ta zuba furar ta fara damawa da nono. Daga Inna har Baba kallonta suke, ta ba su baya amman hakan be hana ta jin abunda suke tattaunawa.

“Ko ya rayuwa zata kasancewa Aminatu idan bana raye?”

Baba ya kalleshi da sauri jikinsa yayi mugun sanyi, Aminatu kuma ta juyo ta kalli Inna hawaye na bin fuskarta.

“Rayuwa zata kasance mai wahala Inna, zan zama marar gata marar yanci, dan farinciki da yai saura a rayuwata zai tafi ya bar ni, iskar da zan shaka ma sai na yi kamar na mutu sannan na same ta, Baba dan Allah ka yi mata magana ta daina irin wannan maganar”

Ta karasa tana duban mahaifinta, Baba ya kasa cewa komai domin jikinsa yayi sanyi sosai idonsa har sun cika da hawaye, Inna ta kalleshi tana murmushi ita ma hawayen ne a idonta.

“Yayanka sun fika jarumta Malam”

“Wannan ba maganar Jarumta bace, magana ce marar dadi, kuma da na san abun da zaki fada kenan da ban shigo gidan nan yanzu ba”

Ya karasa yana kai hannunsa aljihu ya ciro wayarsa dake ringing. Ya kara wayar a kunne tare da sallama sai dansa Bashiru ya amsa ta dayan bangaren...




BATURIYA POV.

Tana tsugune gaban murhu tana suyar naman kajin suka ji an kwankwasa gida. Ta kalli danta shi ma ya kalleta.

“Ko Abba ne?”

A take ta daka masa tsawa.

“Ban ce ka daina cewa Abbah ba?”

Sultan yayi saurin rufe bakinsa.

“Daddy”

“Good”

Ta mike tsaye tana mita.

“Wata kila ma yaran nan su Saifu sarakan kwadayi tun da sun ji an soyar abu kamshi ya kawo musu, shiyasa zama irin wannan area ta talakawa sai dole Wallahi”

Ta kai hannu ta bude kofar sai arba tai da kawarta Ramlee, a take ta washe baki, Ramlee ta sakar mata murmushi tana wani irin kamshin turare irin na manyan masu kudi.

“Yau gidanmu?”

“Sai kace ban saba zuwa gidanmu ba”

Ta fada a yayinda Baturiya ta kauce mata ta shigo.

“Ki ce yau na shigo a sa'a kaji ma kuke ci, lallai Faruq yayi abun kai”

Ta fada ta zigar zolaya da bugun ciki tana kallon Baturiya. A take Baturiya da bata shaye rada ta tsire baki tace.

“Kina magana kamar baki san wa nake aure ba, Faruq din ne
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment