Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ya saka hannunsa ya dago kafadarta.

“Idan kina son na zauna sai idan zaki yarda ki zauna da ni zama na har abada”

Ta masa kallon rashin fahimta, sai dai kuma ta kasa tambayarsa abun da yake nufi da haka. Ganin haka ya saka shi yin murmushi ya dauke hannunsa daga fuskarta ya dan ja baya kadan yana kallon harabar gidan.

“Kina son zama da ni?”

Ta sauke kanta k'asa ta kasa cewa komai. He just ask dan ya gane idan tana son zaman da shi ko akasin haka, domin Kaka tana kokarin hada aurensu ne kawai ba tare da lura da suna son junansu ba ko a'a, hadi ne kawai take son tai musu irin na kauye na zamanin baya.

“To ni ina son zama dake, shiyasa nake son Kaka ta bani ke...”

Sai kuma ya kasa karasawa yana ta kallon reaction dinta.

“Na aureki...”

Dagowa tai da sauri ta kalleshi gabanta ya buga da mugun karfi, zuciyarta tai wani uban zillo kamar zata fito daga kirjinta ta fado kasa. Bata san miyasa take jin kamar kalamansa sun mata nauyi ba, alhalin ba a yau ya fara furta mata wannan kalmar cewar zai aureta ba, wacan karon ya ce saboda kar su sabawa Allah ne, har yace idan ta samu wanda take so ko yan'uwanta zai sake yanzu fa? Bayan gashi tana tare da kaka. Ganin ta yi shiru bata ce komai ba ya saka shi zaunawa cikin motar.

“Zan tafi”

Sai ta sake mika masa kudin a karo na biyu.

“Ki koma ki kai mata, idan bata karba ba ki dauka na baki”

Yaja motar ya rufe yai reverse tana tsaye tana kallonsa hawaye na sauko mata, sai da ya juya motar sannan ya sauke gilashin motar ya leko da kansa ya kalleta ya sakar mata murmushi sannan yaja motar ya kama hanya. Tsaye take tana kallonsa tun tana hangensa har ta daina hangosa, sai ta durkushe a gurin ta fashe da kuka ta saka kanta cikin guiwar hannunta tana kuka sosai. Sai da ta soma jin motsin mutane na wucewa sannan ta tashi ta share hawayenta ta shiga cikin gidan kanta a kasa tana tafiya kamar dazun.
  Ko da ta shiga Kaka bata cikin dakin, sai kawai ta hau gadon data kwana a jiya ta rumgume kudin a kirjinta, can kuma ta juya baya ta fara kuka a hankali tana jin zuciyarta na mata mugun zafi.


TALBA POV.

Be taba rabuwa da wani abu ya ji yana marmarinsa ba so soon kamar Aminatu, baronta da yai a can har ya fara jin kewarta. Murmushi yai tunawa da tambayar da tai masa cewar yaushe zai dawo.
Wayarsa ya dauka ya kira Daddy, ringing daya ya daga.

“Ranka ya dade yanzu nake kokarin kiranka”

“Daddy barka da safiya”

“An tashi lafiya fatar ka kamo hanya”

“Gani a hanya Daddy, fatar Momy ta dawo”

“Kun fara damuna da zancen Momy fa, ni ma zan yi yaji na tafi Abuja na yi zamana”

Talba yayi murmushi cike da kaunar Daddy daman san shi da barkwanci.

“Haba Daddy idan ba Momy ai ba rayuwa, dan Allah kace min ta dawo”

“I think dai yau ko gobe zata dawo”

“Gani tafe, zan rakaka ka dauko ta akwai maganar da nake son yi da ku mai muhimmanci kuma ina fatar zaku fahimta”

“Allah ya kawo ka lafiya”

“Ameen”

Ya katse kiran, sannan ya kira Leila kamar yadda ya tsammata bata daga kiran ba, sai ya kira Amal ya gaisa da ita sannan ya kira Momy.

“Talba”

“Momy barka da safiya”

“An tashi lafiya”

“Lafiya kalau Alhamdulillah”

“Ance ka baka kwana a gida ba, ina kaje?”

“Waya fada miki?”

“Amal”

Yayi murmushi mai sauti.

“Allah ya shirya Amal ba zata daina gulma ba, naje kauye ne”

“Amman kasan hanyoyin nan ba su da kyau Talba”

“Nan ai da sauki abun be kawo ba, kuma gani hanyar dawowa, ina fatar kin dawo Momy”

Ta yi shiru.

“Rashinki ne ya saka muka bar gidan nan, gaba daya gidan baya mana dadi, kuma ina jin babu dadi idan na tuna cewar saboda ni komai ya faru”

“Zan dawo ai, kuma ba laifinka ba ne komai ya wuce”

“Zan zo anjima na daukeki”

“Aa sai next week”

“Momy do this favor for me dan Allah...!!!”

“Shikenan”

Yayi murmushi.

“Thank Youu Momy ashe kina so na”

“Wannan wace irin magana ce Talba? Bana son ka nake zaune tare da kai? Na taba cutar da kai a tsawon zaman da na yi da kai? Ta ya uwa zata zauna da tun yana jariri har ya girma a hannunta kuma ta ce bata taba son dan nan ba, bayan kuma yaron nan be mata komai ba? Engineer ya riga ya dasa maka wani mugun ice na kiyayata a zuciyarka shiyasa har kake min wani kallo na dabam”

“Ko kadan Momy, ban taba kallo wata mace a matsayin uwata ba sai ke, ban san wata uwa ba sai ke, kuma Daddy be shimfida min komai ba a zuciyata sai kaunarki, ke da shi kun kasa fahimtar juna ne kawai, kina ganin kamar ya zurfafa a so na, shi kuma yana ganin kamar baki so ni a yadda ya kamata ki so ni ba, kuma duka na fahimcinku, fatar za a yafe min”

“Baka yi komai ba, Allah ya maka albarka”

“Ameen”

Ya amsa da murmushi sannan ya kashe wayar, ya cigaba da tukinsa yana tunanin yadda zai gabatar da Daddy da Momy maganar Kaka.
Ko da goma tai har yayi wanka ya canja tufafi, be tarar da Daddy a gidan ba haka ma Amal tana makaranta Leila ce kawai a bangare sai Kabir dake karyawa a dinning.
Kallo daya Kabir yai masa ya dauke ido domin a yanzu be da makiyi kamar Talba, Leila kuma ta kura masa ido ta kasa daukewa har ya karaso kusa da ita ya zauna, sai gabanta ya buga da karfi, duk yadda take son hana zuciyarta soyayyar Talba sai ta kasa musamman ma idan yana kusa da ita wani lokacin har jin take kamar ta rumgume shi, sai dai gudun zubar da class dinta ya saka bata nuna masa haka, dauke idonta tai tana ganin wani uban kyau daya kara kamar an shafa masa hoda.

“Ya kike?”

Ta mike tsaye sai ya kalleta.

“Can we talk”

Tsayawa tai sai dai bata juyo ta kalleshi ba, kuma bata ce masa komai ba.

“Zauna mana”

Ta koma ta zauna.

“Akwai abun da kike so ne?”

Ya tambaya feeling some how kamar he's out of words, haka yake a duk lokacin da yake tare da Leila, duk kalmar da zai kama yai magana ta fahimta da ita sai ya ji kamar ba zai iya ba, except ta fada masa baka magana ne ko kuma ta masa wani laifi, on that point kam ya san abun da zai fada mata. Mikewa tai tsaye ta nufi upstairs sai ya bita da kallo yana ta kokarin hada kalmomin da zai yi mata magana ta fahimta amman ya kasa har ta haye sama. Tashi yai ya nufi kofar fita Kabir ya bishi da wani banzan kallo har ya fice, bangarensa ya koma ya dauki keys dinsa ya fito ya shiga motarsa. Ko da ya isa gate har sun bude masa. Yana fita ya fisge motar da karfi ya dauki hanyar da zata kai shi gurin da Daddy yake aiki. A harabar ma'aikatar ya faka motarsa ya fito ya nufi ciki da saurinsa yana kiran Daddy a waya.

“Daddy gani shigowa zan muje mu dauko Momy yanzu”

“Bana gida”

“Yeah na sani office dinka nake nufi”

“Bana office, ina gidan Hajiya Yana, na yi marmarin abincin Doctor ne shi ne na zo na yi breakfast, amman idan na gama zamu dawo gida yanzu”

Talba ya tsaya cak yana mamakin yadda Daddy ya fishi hikima da wayo, wato a can ma ya karya a maimaikon ya jirashi su tafi tare, and yes yayi abun da ya dace, daman shi yana son saka Daddy a gaba ne saboda yana ganin kamar baya son dawowa da Momy ne.

“Fine sai kun iso”

Ya fada sannan ya juyo ya dawo yana murmushi ya nufo motarsa. A ranar be yi maganar da Daddy ba, duk da kasancewar Daddy ya tambaye shi amman sai ya dauko wani zancen, ba dan komai ba sai dan ganin a ranar Momy ta dawo be kamata yai maganar ba, washe gari ma be yi maganar ba, har sai da aka kwana uku da dawowar Momy a gidan. In all these three days yana kiran Kaka a waya idan ta daga ta ji muryarsa sai ta kashe, last kiran da yai mata ma ya bukaci ta bawa Aminatu wayar amman bata ko tsaya saurarensa ba ta kashe wayar.
  Sai da Amal ta tafi makaranta Kabir ma ya fita Leila kuma ta koma dakinta, sannan ya kalli Momy ya ce.

“Momy ina son magana da ke da Daddy,  ko zamu iya zuwa can?”

Momy ta kalleshi daman tun da suka zauna karin kumallon ta lura da babu abun da ya ci sai kofin tea yake ta juyawa.

“Miya faru?”

“Magana ce mai muhimmanci kuma ina son na yi ta ne tare da ke da Daddy”

“Okay gani zuwa”

Sai ya dauki tea din ya mike tsaye ya nufi kofar fita, Ta kofar gaba ya shiga bangaren Daddy a babban falonsa ya zauna yana shan tea a hankali. Sai ga Momy ta shigo ta kofar ciki,

“Baka shiga ciki ba?”

“I think yana karyawa”

“Let me talk to him”

Ta nufi hanyar karanin falon, sannan ta wuce bedroom dinsa. After like thirty minutes Daddy ya fito Momy tana bayansa, a karamin falo ya zauna sai Momy ta kira Talba.

“Talba...”

“Na'am”

Ya amsa sannan ya tashi ya nufi falon, a kasa ya zauna Momy kuma na zaune kusa da Daddy, dukansu sun tattara hankalinsu guri daya suna kallonsa musamman ma Daddy da ya fahimci akwai damuwa a tattare da dansa.

“Kana da wata matsala ne? Na ga ko breakfast ba ka yi ba”

Momy ta fada, sai Daddy ya cire gilashin idonsa.

“Mu'az akwai wata damuwa ne?”

Sai da ya hade yawun bakinsa sannan ya ce.

“Matsala ce kuma ba matsala ba”

“Wani abun ne?”

Momy ta sake tambaya. Sai Talba ya fere musu daga buri har wutsiya akan kudirin Kaka da kuma irin yadda ta dauki fushi da shi. Ba abun da kaka tai ne ya bawa Momy mamaki ba kamar jun cewar Aminatu yar'uwarsa ce, Daddy ya yunkuro yana kallonsa shi ma da mamaki.

“Wato baka rabu da yarinyar nan ba Talba? Har da daukarta ka kaita gurin Hajiya, da ba yar'uwarta ba ce acan zaka aje ta kenan?”

Cewar Momy cikin wani irin bakinciki na jin abun da Talba ya fada, sai Daddy ya daga mata hannu domin shi ba wannan ne damuwarsa ba.

“Taimako ai abu ne mai kyau, babu laifi a abun da Mu'az yai, ki tattara wannan abun ki aje gefe daya, ki bari mu ji da damuwarsa. Kai kana son yarinyar”

Daddy ya karasa yana kallonsa with serious face. Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai ce.

“I don't know yet”

“That's mean baka son ta, and no one can forced you shikenan”

Daddy ya karasa masa domin yasan waye Talba idan yana son abu zai fito kai tsaye ne ya ce yana so, haka ma ida baya so zai fadi cewar baya so.

“Ya ma za'ayi ya so ta? Yarinyar ai bata dace da shi ba, imagine an yi raped dinta kasan iya mutanen da sukai mata wannan aika aikan? And waya sani ko tana dauke da wata cutar, lastly Talba ba mutum ne mai son hayaniya ba bana tunanin zai iya zama da mata biyu”

“Wannan ba matsala ba ce, da ace yana sonta za a iya bincikar lafiyarta kuma i will support him ya aureta, amman tun da baya son ta ba zai aureta ba”

Daddy ya fada, gaba daya sai jikin Talba ya mutu kalaman bakinsa suka kare, domin ya san duk juyin duniyar nan da za'ayi Daddy ba zai yarda ya aureta tun da har be nuna cewar yana sonta ba, and yes shi kansa be san yana sonta ba, all what he know is yana tausayinta.

“Amman... Kaka...”

Talba be karasa ba Daddy ya tari numfashinsa.

“Zan kirata zan yi magana da ita a waya, zan fahimtar da ita, yaushe rabon duniya da ayaraye, ai an daina wannan abu a wannan zamani, ko da ma ana yi ni ba zan bari ayi maka ba”

Daddy na kawai nan ya mike tsaye ya nufi bedroom dinsa, daga Talba har Momy binsa sukai da kallo sai da ya shige sannan Talba ya mike tsaye da zimmar tafiya sai Momy ta dakatar da shi ta hanyar tsayar kiran sunansa.

“Talba”

Mikewa tai tsaye ta karasawa gurinsa tana kallonsa fuska a hade.

“Karka kuskura ka bari Leila ta ji wannan maganar, domin akan 'ya'yana, bana da mutunci, bana da ragowa, bana son abun da zai daga musu hankali, idan ma ka fara son yarinyar nan ka bullo da maganar ta wannan hanyar to ka cireta a ranka tun wuri, kana gani ai, ni kadai nake a gidan mijina, haka ma yayana zasu zauna har karshen rayuwarsu, ko da wasa kar ka yi kuskuren hada soyayyar Leila da ta wata macen ko da ba wannan ba, balle kuma wannan kazamar da bandits suka gama wulakantawa, yarinyar da ingiyar aurena ta rabu saboda ita”

Kallonta kawai yake da mamaki, kamar ba ita ce ta gama fada masa cewar tana kaunarsa ba, and yanzu ya gane halin Momy tana sonsa but when it's comes to her children bata saurarawa kowa. She got lucky ita ce ta fada masa haka b Leila ba, da Leila ce zai iya fada mata bakar maganar da har ta mutu ba zata taba iya mantawa da ita ba, but Momy ce ya zai yi bayan ya saka mata ido. Har ta yi gaba sai kuma ta dawo ta sake kallonsa.

“And for the very last time karka sake shiga safgar yarinyar nan”

“Yar'uwata a yanzu, ko a da na taimake ta balle a yanzu da bata da kowa sai ni sai Kaka”

“I don't care, rayuwar kowa bata dame ni ba, ka haka rame ka binne maganar nan a inda aka yi ta, idan ba haka ba zan baka mugun mamaki Talba domin ba zan yarda a taba kimar yata ba...!!!”

A falon ta bar shi tsaye ta nufi babban falo cikin fushi ta karasa kofar fita falon wanda zata sadata da bangarenta, shi kam binta yai da kallo har ta shige ta turo kofar sannan ya fito babban falon ya zauna yana tunanin yadda zai fuskanci Kaka, anya zata fahimta kuwa? Idan ta fahimta falillahil hamdu, daman haka yake so, sai ya cigaba da daukar dawainiyar Aminatu, sai dai idan kuma bata fahimta ba fa? Ya zai yi? Ya shafa kansa yana sauke ajiyar zuciya.
Ya kusan awa daya a zaune, sannan ya tashi ya nufi bangarensa yana amsa wayar Ali, a tsanake ya labarta masa komai sannan ya nufi gadonsa ya kwanta ba dan yana jin bachi ba, sai dan ya rasa abun yi. Yana rufe ido wayarsa tai ringing sai ya kai hannu ya dauka ba tare daya bude idon ba, power button ya danna sai yai picking call din ya kara kunnensa.

“Na cilasta maka aurenta ne da zaka turo ubanta ya rufe ni da fada, yana kokarin nuna min cewar ina son yi maka auren dole ne? Lallai Mu'azu ka nuna min ban isa da kai ba, kuma yanzu na gane dalilinka na watsar da mu da kake, saboda mu talakawa ne ko? Toh na shata layi daga yau kowa ya tsaya matsayinsa, yarinyar da kake kyama har ubanka yana fada min akwai banbanci tsakaninka da ita gata can ana mata karin ruwa, idan ta mutu aikowa ya huta”

Sai a lokacin ya bude idonsa ya tashi zaune da sauri.

“Bata da lafiya ne Kaka? Zata iya magana?”

“Ban sani ba, na dai fada maka kar kaka sake turo min ubanka ya dame ni da wata maganar banza, idan abun da yake ganin yana bani ne yana daukar nauyina ban cilasta shi ba, kuma ba a yunwa ya gan ni ba”

“Kaka dan Allah ki kwantar da hankalinki, daman na yi magana da Daddy ne saboda ya fahimtar da ke, ban yi tsammanin abun zai kai ga haka ba, na yi alkawari zan aureta”

“Ba zan aura mata miji irinka ba, kaje can ka auri yar masu arziki, ai daman kishi yake taya yarsa, har yana nuna min cewar kuna da banbanci”

“Zan shigo garin Maradu yau ko gobe kuma Wallahi sai kin aura min ita”

Yana fadar haka ya ji ta mikawa wani wayar tana fadin.

“Karbi kashe min, waya sani ma ko zagina zai yi yanzu kuma, bayan ubansa ya gama nasa”

Dit... Ya ji ankashe wayar, sai ya mike tsaye ya fice daga dakin da zimmar zuwa bangaren Daddy, sai ya same shi waje direbansa ya bude masa mota yana kokarin shiga. Sai dai hangoshi da Daddy yai ya saka ya dan jinkintar yana jiransa. Ya karaso gaban Daddy a natse.

“Daddy aka yi magana da Kaka ne? Ta kira ni tana ta masifa”

“Na yi magana da ita, ina kokarin fahimtar da ita ta kasa fahimta, sai maganar take saboda anga ita talaka ce shiyasa nake mata haka, kuma wai ina taya yata kishi for god sake ya za'ayi na taya Leila kishi ni ba mace ba? Ba wai bana goyon bayan auren nan ba ne saboda Leila, Wallahi bana goyon bayan auren nan ne saboda baka so”

“Amman Daddy idan yin zai zama mafita why not...”

“No baka so ba za'ayi ba, that's it”

“Idan kuma ina so fa...”

“No baka saba yi min karya ba, ni kuma ban saba canja kalamaina ba, ba zan yarda kai abun da baka so ba, kuma ba zan bari ka yi abun da zaka zo kana nadamarsa ba, ba za'ayi auren ba karka sake yi min maganar nan”

Daddy na kaiwa nan ya shige motarsa, Direban ya zagayo ya rufe matsa sannan ya koma ya shiga driver side ya ja motar. Sai da Daddy ya fice daga gate din gaba daya sannan Talba ya koma bangarensa ya canja tufafin jikinsa ya dauki wallet dinsa da keys ya fito da sauri ya shiga motarsa sai da yai reverse sannan ya hango Momy dake tsaye a backyard tana kallonsa fuska a hade, dauke kai yai yaja motar yana danna horn da karfi kamar mai tsere. Sai da yai nisa da unguwar sannan ya kira Ali ya fada masa abun da ya faru.

“Yanzu miye abun yi?”

“Oho ni yanzu hankalina ma ya koma can gaba daya, saboda Kaka tace min gata nan ana mata karin ruwa waya sani ma ko wanda ke mata karin ruwan be wani kware ba, kuma wata kila ba a bincika ciwonta ba”

“If ka damu da ita da lafiyarta Talba, be kamata ka nunawa Daddy baka son aurenta ba, kasan Daddy ya fika son abun da kake so, kuma yafi ka tsanar abun da kake ki, yanzu ya zaka yi kenan?”

Talba yayi jimmm sai kuma ya sauke ajiyar zuciya.

“Aurenta zan yi, ba zan yarda zumuncin dake tsakanina da Kaka ya lalace ba akan abun da ina da iko da shi ba, kuma ba zan yarda Daddy ya samu matsala da Kaka ba”

“Then ya zaka yi convinced din Daddy ya yarda ka aurenta? Kasan ba zai taba yarda ba, aje maganar Daddy a gefe ma, ya zaka yi da Momy da Leila?”

“AUREN SIRRI no one would know, har sai komai ya daidaita, and i think Aminatu deserved a better life zan dawo da ita gidan nan”

Ali yayi saurin mikewa tsaye daga zaunen da yake yana girgiza kai.

“No karka yi haka Talba, zaka cutar da kanka kuma yarinyar zata cutu”

“Sai dai ni na cutar da kaina, amman ba zan bari a cutar da Aminatu ba, kuma ba zan cutar da ita ba”

“Maimakon haka, ai kara ka samo wani dabam ka aura masa Aminatu a matsayinta, saboda ba lallai ne ma idan a aureta ka iya zaman aure da ita yadda ya kamata ba”

Talba yayi murmushi yana tuna kalaman Momy na dazun.

“Saboda me? Saboda wasu mazan sun wulakantata? Ali bari na tambaye ka, idan kanwarka zaka so wani aureta? Ita ta kaddarowa kanta wannan abun ya faru da ita? Miyasa ake kyara mutanen da irin wannan kaddarar ta fada musu? Wallahi wannan abun ya fara min tausayinta kuma ya karfafa min guiwar aurenta, saboda ta cancanci zama da namiji irina, bayan ni a yanzu ban san wanda zai aureta ya zauna da ita da zuciya daya ba, and ba zan iya yaudarar Kaka tana kallon ni na aureta sai kuma na saka wani yayi? Ita kanta Aminatu ba zata ji dadi ba, and idan hawayen yarinyar ya zuba saboda ni ba zan taba yafewa kaina ba”

Ali yayi murmushi.

“Na taba fada maka lokaci zai da idonka zai rufe ka taka kaya ka jita kamar lad'a, kana son yarinyar nan believe me, zaka iya yaudarar Daddy da Momy da Leila amman ba zaka iya yaudararta ba, and you are telling me idan hawayenta ya zuba saboda kai ba zaka yafewa kanka ba... This is Love Talba, Welcome To the club”

Talba ya natsu yana nazarin abun da ya fadawa Ali, did he say something wrong? No gaskiya ya fada masa ai abun da ke ransa. A hankali ya sauke wayar ya cigaba da tukin yana tunanin halin da Aminatu take ciki.




LEILA POV.

Tana fitowa daga dakin ta shiga dakin Momy, bata same ta a ciki ba, sai ta sauko kasa ta shiga kitchen nan ma bata ciki.

“Ke Mairo ina Momy”

Ta tambaya tana wani yatsinar fuska kamar wanda tai arba da kashi.

“Tana sama”

Mairo ta amsa mata ba tare da ta kalleta ba.

“Wai Mairo har wani ji kike da kanki a gidan nan, Wallahi idan baki yi hankali ba sai na karya ki, ba ki san halina ba ne”

Kallonta kawai Mairo ta yi ta dauke kai ta cigaba da abun da take, ita kuma ta juyo ta fito daga Kitchen, kai tsaye ta nufi upstairs kamin ta karasa Momy ta sauko rike da atamfa.

“Momy ina kika shiga ban ganki ba”

“Ina backyard”

“Gurin me?”

Leila ta tambaya da mamaki domin ba kasafai take shiga can ba.

“Gurin kallon Talba, ashe har yanzu yarinyar nan tana ransa?”

“Me yace ne?”

“Ba komai kawai na lura da yanayinsa ne”

“Yauwa Momy daman ina son na yi miki magana akanta, ki bincikar mana shi inda ya kaita dan Allah ko ma ki saka ya dawo da ita gidan nan if possible”

“Saboda me?”

“Madina ta ba ni shawarar mu samu wani mu biya shi ya aureta, kin ga ai mun huta, to na yi da bugun cikin Ali be fada min komai ba, sai ma ya nuna min kamar be san inda Talba ya kai yarinyar ba”

Momy ta yi shiru tana nazari.

“Indai haka ne, Madina ta kawo shawara mai kyau, amman akwai wani sirri da baki sani ba”

“Minene?”

“Wannan yarinyar da kakanta da kakar Talba yaya da kane ne”

Leila ta gwalo ido waje tana bude baki cike da mugun mamaki.

“What'? That's mean cousin dinsa ce kenan? How how Momy how? No ba gaskiya ba ne kina min wasa ne”

A take idonta ya cika da hawaye jikinta ya fara rawa, sai Momy ta rika hannun ta koma sama da ita.

“Shiiiiiiiiiii zo nan ki ji”

Momy taja hannunta har cikin dakinta, hawaye kam sai sallama yake yi ma idanuwan Leila tana amsa masa da gaggawa.
34

*Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith bank, then send the evidence via 08036126660*

AMINATU POV.

Tana jin muryar Talba sai ta bude ido da sauri, domin tabbatarwa idan kunnuwanta daidai suka jiyo mata, tsaye ta ganshi a kanta yana ta kallon kyakkyawar fuskarta cikin damuwa. A take ta zabura ta tashi zaune.

“Ina wuni”

Sai ya zauna kusa da ita yana kallonta cike da kulawa.

“Ya jikin?”

“Alhamdulillah”

Ta fada tana jin kamar an yaye mata ciwon an aje gefe daya. Hannunsa ya kai ya taba wuyanta sai ya ji shi da dan sauran zafi. A nan ya kalli Kaka.

“Wane irin magani aka bata?”

“Wanda ka kawo mata”

Kaka ta fada masa tana wani tsuke baki, ta dauke kai kamar wata yar yarinya wai ita ala dole fushi take da shi.

“Haba Kaka”

Sai kuma ya kalli Aminatu.

“Shalele wani irin magani aka baki?”

“Mai dacin nan na malaria da na ciwon kai, sai kuma ya saka min ruwa, kuma ta min allura”

Ta fada a shagwabe idonta na cika da kwalla ji take kamar ta fashe masa da kuka tunawa da zafin allurar da akai mata gashi kullum
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment