Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

sukai ma Amadu haka wadancan barayin da suka zagaya gidan Musa suka masa, domin duk wanda ya san yayan Mai Damma ya san wuka ko bindiga bata hudasu, ya sha kuma ba bawa yaransa, ba dan komai ba sai dan kariyar irin wannan ranar, sai dai ayau shan be amfana musu komai ba, ba su kadai ba har da sauran mazan gari da bindiga bata fasawa, sukan kashe su da babur ko dutse, balle kuma Rilwanu da Iro da sukai kwarin suna a garin saboda aikin sa-kai da suke.
Sanusi kam sai yai kamar ya mutum ganin nasa mai sauki ne, domin da babur sauka hau kafarsa dan kawai su gana masa azaba, baya ambatar komai sai Allah, ba a gidan Mai Damma kadai ba, a garin gaba daya haka suka ci suka shude babu wanda ya kawo agaji, suka ci karensu babu babbaka yadda ransu ya so sannan suka bar garin bayan su kwashi abinci da mata cikin har da matan Musa da matar Amadu.



________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
I just published "04" of my story "BAKAR WASIKA". https://www.wattpad.com/1188003519?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=gvBvvJY%2Brh7%2BfdxLjDxcLbTx9rDGdNBA0sMHgr3XMPr%2FqwZ4sIWJ88oZCr4nOa%2BILP0eBQ%2FKRLIQm73M62araHO6%2BoJXjoYprLv7YGhRYyguc1ysae3vRDycS1qvuqiM

*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -4️⃣

“So yanzu ka yarda zaka bata hakuri kenan”

Talba ta girgiza kai.

“Kai no never ni fa ba zan taba ba wanda yake kasa da ni hakuri ba”

Ali ya kalleshi.

“Amman ka ce Daddy yace laifinka ne, kuma kaje ka bata hakuri”

Yayi shiru kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya shafa kansa ya sauke numfashi a hankali.

“Yeah ba wai yana nufin na ce tai hakuri ba, ni yanzu so nake ka kirata ka bata hakuri kuma ka dauke ta ku je yawo ta wayance Shikenan komai ya wuce, amman karka ce ni na ce ka bata hakuri fa”

Ali ya rausayar da kai yana kallon abokin nasa cike da mamaki.

“Miye a ciki dan kace tai hakuri? Ko kuma ka dauke ta kuje yawo, faduwa kai?”

Sai Talba ya amsa masa kai tsaye.

“Yes, taya zaka bawa mace hakuri macen ma wanda take kasa da kai, ni me fa Ali”

“To wai idan kuka yi aure kuka samu matsala, kuma kai kake da laifi...”

Kamin Ali ya karasa Talba ya tari numfashinsa.

“Sai ta ba ni hakuri”

Ta fada da iyakancin gaskiyarta, domin har ga Allah be ga dalilin da zai saka shi bawa wanda ke kasa da shi hakuri ba, kuma mace sai dai shi a ba shi. Ali yayi murmushi.

“Yanzu dai for the sake of Daddy zaka yi”

“For the sake of him na zo har ina rokonka da kai, idan ba haka ba babu abun da zai saka na roke ka ma”

“Look Talba I'm not her boyfriend, ban san kalaman da zan mata ba, kuma ba ni nai mata laifin nan ba”

Talba ya mike, ganin hakan yasa Ali ma ya mike tsaye.

“Fine, amman tare za mu je, kana driving ina baya”

Talba be ce masa uffan ba ya nufi kofar fita, wanda hakan ya tabbatarwa Ali cewar ya yarda kenan. Sai da Ali ya shiga yai sallama da Samira sannan ya fito ya samu Talba a cikin motarsa. A hankali Talba yake tukin har suka fita daga cikin gidan suka hau titi.

“Kirata ka tambaye ta tana ina”

Ali ya masa wani kallo.

“Kiran ma? Talba wai kai zaka bata hakuri ko ni? Just ka kirata ka tambayi tana ina ma you can't?”

Ko kallon gefen Ali Talba be yi ba balle ya tanka masa.

“Fine”

Ali ya fada sannan ya zaro wayarsa ya shiga contact dinsa ya nemo number Amal, domin baya son batawa kansa lokaci tambayar Talba number ta zai iya ce masa baya da ita ma. Ringing biyu ta dauka.

“Hello”

“Hello Lil Sis ya kike?”

Ta yi murmushi jin ya kiranta da sunan da Talba yake kiranta.

“Na'am Ya Ali ina lafiya”

“Good number Leila nake so”

“Okay zan turo maka yanzu”

“Thank You”

Ya aje wayar yana kallon abokinsa tare da mamakin halinsa. In few minutes Amal ta turo masa number, a take ya kira Leila, abun ka da mai jin kai sai da wayar ta yi ringing ta katse bata daga ba, har sai da ya sake kira, wannan karon ma sai da ta kusan yankewa sannan ta daga kuma tai shiru tana sauraren mai kiran, daman can haka take babu yadda za'ayi ka kirata kuma ka yi expecting ita zata fara maka magana, sai da Ali ya saka wayar a speaker sannan ya fara magana.

“Kanwata Leila kina lafiya?”

Jin muryar Ali yasa ta dan sake domin ta san waye shi.

“Ali ya weekend?”

“Alhamdulillah kina ina?”

“Ina gida dari gidansu Madina”

“Okay gani nan zuwa”

Be jira abun da zata ce ba, ya aje wayar ya kalli Talba.

“Idan munje ta fito kai zan bata hakuri sannan na baku guri ku yi magana”

Talba ya masa wani kallo irin really!


*** *** ***

Leila ta aje wayar tana tabe baki.

“Waye?”

Madina ta tambaya tana gyara kwanciyarta.

“Ali wai gashi nan zuwa?”

“To ko ya san abun da ya faru tsakaninku ne?”

“Maybe ai Talba baya boye masa komai”

“Kin gani na fada ya damu fa”

“Ya damu amman be kira ni ya bani hakuri ko ya aiko min da sako ba? Ni I don't think Talba yana so Madina”

“Yana son ki mana Leila”

Madina ta fada sannan ta sauka saman gadon ta kama hannun Leila.

“Zo nan let me show you something”

Gaban madaubin dakin ta nufa da ita ta tsayar da ita gaban madubin.

“Kalli kanki da kyau Leila ki fada min abun da kika rasa”

Leila ta kurawa kanta ido a madabin tana kallon irin baiwar da Allah yai mata ta kyau daidai gwargwadon.

“Kyau?”

Madina ta tambaya sai Leila ta girgiza kai.

“Kudi? Lafiya? Kima, gata ko kuma me?”

“Ba ko daya”

Leila ta amsa.

“Kina da kyau da babu namijin da zaki yi tayin kanki ya ce miki aa ko waye shi kuwa, mahaifinki na da arziki da zai iya siya miki rai idan ana saidawa Leila, kina da kima, ga gata ta ko'ina, kuma duk wannan tarin baiwar da take tare da ke sai zuciyarki ta raya miki Talba baya son ki?”

Leila ta juyo tana kallon Madina

“Za ki iya fada min dalilin da ya saka yake min haka?”

Madina ta yi murmushi ta koma saman gadon ta zauna.

“Saboda Talba, na daya daga cikin irin mazajen nan masu matukar tsada da wahalar samu, kin ga duk wannan abubuwan da kike da su, Talba na da damar da zai iya cewa ba ya son ki idan har baya son ki, kuma ta zauna, domin kin san mutun ne da baya boye abu a ransa idan be masa ba, kuma babu wanda ya isa ya cilastashi, idan har baya son ki kai tsaye zai fada, amman be amsa cewar baya son ki ba ya amince”

Leila ta dan yi sama da ido.

“Haka ne but...”

Madina ta tari numfashinta.

“But Talba yana da matukar tsada Leila, Talba wani irin murdadden mutum ne mai wahala sha'ani, yadda kike takama da kyau yana da kyau, yana da dukiya, yana da duk wani abu da ake so a jikin namiji, yana da arzikin da yake jin zai iya tankwara komai yadda yake so, yana ganin tun da yana da komai dole a bi shi”

“Shi ne matsalarsa ai”

Leila ta fada tana zaunawa kusa da kawarta.

“Yeah ya kasa yarda cewar akwai abun da kudi basa siye, a nan ne kawai yai kuskure”

Leila ta yi murmushi.

“Ni kuma zan gyara masa wannan kuskuren, sai na nuna masa banbanci da sauran mata, dole ne ya san cewar ina da kima da daraja, kuma dole ya koyi yadda zai yi rayuwa da ni, all those four years of dating, ni nake bashi hakuri ko da ni ce da gaskiya, ina binsa kamar wani sarki da baiwa, all those years ni nake masa text how are you, so so so this, idan ya bar kasar nan ni zan kira shi na tambayi lafiyarsa, ko na masa sako, amman ko da rana daya Talba be taba daga waya ya tambayi ya nake ba! Idan na yi kwaliya be taba ce min kyau ba, be taba replied sakona ba, be san yai min kyauta irin ta masoya ba, balle har ya dauke ni muje yawo, ba zan taba yarda na aure shi a haka ba, now it's my turn, dole ne ya canja”

Ta karasa yana yawo da idonta a dakin. Madina ta kama hannunta.

“No Leila mutane irin Talba suna da wahalar sha'ani, kuma suna da shaukin kai ga wanda ya iya zama da su, kar garin gyara ki ballo wata barnar, idan kin bashi hakuri a inda kike da gaskiya ai ba laifi ba ne”

“No dole ne ya gyara, yana son soyayya amman be san yadda zai nuna ta ba? Be san yadda zai biya ta ba? Ban taba kiran sunansa a gaban idonsa ba sai na sakaya, amman shi be taba gwada kirana da suna mai dadi ba”

Ta karasa tana murmushi.

“I'm such a fool”

Ta kai dubanta gurin wayarta da ta soma ringing. Hannu ta kai ta dauki wayar sannan tai picking.

“Hello?”

“Kanwata ga mu harabar gidan”

“Okay”

Ya mike tsaye ba tare da tunanin komai ba ta nufi kofar fita.

“Talba ne?”

“Ali dai Uhm Talba zai zo nan?”

Ta fada tana mere baki sannan ta fice, hango Motar Talba harabar gidan ba karamin mamaki ya bata ba, domin ko a mafarki bata taba saka ran zai zo ba, kuma bata zaton Ali ya aro motarsa ne. Tun kamin ta sauko entrance din ta canja tafiya, kamar wata hawainiya haka ta rika takawa kamar bata son karasawa kusa da motar.
Da gangan tai haka domin ta san a cikin abubuwan da Talba ya tsaya akwai jira, ko bata masa lokaci for nothing, mutum ne da yake daukar lokacinsa da muhimmanci sosai, dakika daya ko biyu idan ka kara, zai iya rushe ko miye a tsakaninku, hakan yasa yana girmama lokacin wani da ra'ayinsa.
Kamin ta iso Talba ya cika har ya kusan fashewa, ba karamin jihadi yai ba na bawa zuciyarsa hakuri har ta iso. Ali dake front seat ne ya sauke gilashin motar yana murmushi, Talba kam ko inda take be kallo ba sai taba wayarsa yake kamar his life depends on it. Kallo daya Leila tai masa ta dauke kai tana amsa gaisuwar da Ali yake mika mata.

“Lafiya Kalau”

Ta amsa tana kokarin juyawa. Sai Ali ya bude motar ya fita.

“Ina zaki je?”

“Ciki zan koma, baka fada min tare da wani zaka zo ba”

Kallon mamaki Ali yai mata, ganin ta yi abun da bata saba ba. Wani irin tafasa zuciyar Talba take kadan ya rage ta kone, bude motar yai ya fito a fusace ya zagayo inda take tsaye.

“Na zo nan ne, saboda Daddy ya saka ni, ba dan ra'ayina ba, na fi karfin daukar wulakancin mace ko wace iri ce, na fi karfi na bawa na kasa da ni hakuri wannan ranar ba zata taba zuwa ba...”

Ali ya rasa inda zai saka kansa, sai kawai ya koma cikin mota ya zauna, shi da ya zo sasanci sai kuma a sake yin fada a gabansa. Talba na gama fada mata haka ya juyo ya dawo cikin motar yadda ya rufe ganbun motar kadai ya isa ya sanar da bacin ransa.
Kamar wanda akai wa gorin tuki haka yai ribas ya rika danna horn, Mai gadin ya bude masa gate da sauri, ya firgi motar kamar wanda ya shirya bakuntar lahira.

“Wannan wace irin soyayya ce Talba me ke damunka, wai anya kana son Leila kuwa?”

Da mugun karfi Talba ya taka burki, he got lucky babu motoci da yawa a titin.

“Fitar min a mota”

Ya fada ba tare da ya kalli Ali ba. Ba sabon abu bane gurin Ali ya saba nasa haka idan ransa ya bace ko suka samu tsabani, sai dai baya hana anjima ya neme shi.

“Kana da matsala Wallahi kana da matsala, wannan mugun fushin ban san inda zai kaika ba”

Ali ya fada cikin bacin rai.

“Ka san bana son ana min ihu”

“Mtsssss”

“And i hate tsaki”

“Ba zan fita daga motar ba”

Ali ya fada yana gyara zama. A take Talba ya bude motar ya fita ya barta kunne, ganin hakan yasa Ali yai saurin fita ya zagaya driver side ya cigaba da tukin yana mamakin rayuwar Talba.
Gefen Titi Talba ya dawo ya tsaya, a ganinsa kaskanci ne ya shiga napep balle kuma ya hau babur zuwa gida, not just that even tsayin da yake a gafen titi ba girmansa ba ne, wayarsa ya ciro ya kira direban gidansu.

“Ka zo ka dauke ni zan turo maka location ta whatsapp yanzu”

Shine kawai abun da ya fada ya kashe wayar ya kunna datarsa ya shiga whatsapp dinsa ya tura masa location din, sannan ya maida wayar aljihu yana kallon titi, har lokacin zuciyarsa zafi take masa saboda Leila ta kira shi da wani, how on earth zata kira shi da wani?
After like 15 min direban ya iso, da kalle kalle har ya hango inda yake ya faka masa motar, Talba ya bude ya shiga ba tare da yace masa komai ba, shi ma direban be yi kokarin yi masa magana ba domin ya san Talba baya son yawan gaisuwa da kuma kallo, idan kuma kana son bata masa rai to ka cika shi da surutu.
Suna isa gida ya bude motar ya fita ya nufi bangarensu, wato shi da Kabir sai dai kowa side dinsa dabam, kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya jefar da wayarsa kan gado ya cire rigarsa da agogo ya shiga bathroom, sannan ya ciri jean din dake jikinsa ya kunna shower ya tara jikinsa yana kallon kansa a katon madubin dake facing dinsa a bathroom din, kamin ya dukar da kansa yana kallon zanen sunansa da tattoo dake kirjinsa wanda babu wanda ya san da shi sai shi kadai, can kuma ya dago ya lumshe ido.



AMINATU POV.


Kusan ko wane gida dake garin an taba, wasu an kashe wasu an kwashe duka da dabobi, wasu an tafi da yayansu da mata, wasu kuma anyi ma matan fyade, sai dai ba kamar gidansu Aminatu ba, domin wulakancin da akai wa mahaifiyarta ya wuce na kowa mutum goma shadaya a lokacin daya, kuma aka kashe yayyayunta hudu, aka kona rumbun hatsinsu, aka raunata wasu, aka kora dabobinsu.
Ba gidan kadai ba garin gaba daya tsit yai duk kuwa da kasancewar barayin sun yi iya barnar da zasu yi sun tafi, amman tsoro ya hana kowa fitowa, sai kuke kuke kake ji a gidanje, sai dai gidansu Aminatu ya fita dabam da baka jin kukan kowa, har asuba Aminatu na boye karkashin gado, mahaifiyarta kuma tana zaune a bakin kofar idonta a bude amman bata iya komai kamar an zare mata lakka a jiki haka take ji, Sanusi kuma na tsakar gidan a sume. Kamar macijiya haka Aminatu ta fito karkashin gado, ta janyo zanen gadon dake kan gadon karfe dan bono na Inna ta nufi Inna dake kwance tsirara tana kawar da idonta tana kuka har ta karasa kusa da ita ta kulluba mata zanen. Sannan ta juya ta koma inda fitilar kwai take ta dauka ta kara haskenta, ta taka kamar mai koyon tafiya ta fito waje. Wani rawa jikinta ya fara yi hango rumbun abincinsu na ci da wuta, sai kuma ta juya a hankali ta sauke idonta kasa ta kalli gawar Iro, da ta Amadu, ga kuma Sanusi shi ma dake kwance, kafa na zubar da jini, gaba daya ilahirin jikinta ne ya fara rawa kamar yadda bakinta ma yake yi.

“Ya... Ya... Ya.. Ya..”

So take ta kira sunan daya daga cikinsu amman ta kasa, hawaye sai aikinsu suke a fuskarta. Ta saki fitilar numfashi na fitar mata da karfi, wani kuma na shiga da sauri. Juyowa tai ta kalli Inna dake kwance bakin kofar har lokacin idonta na zubar da hawaye, sai wulakancin da akaiwa mahaifiyarta ya fado mata a rai, komai ya zame mata sabo.

“Me muka musu?”

Ta tambayi kanta tana wani irin kuka na fitar hankali, sai kuma ta ruga da dugu gurin yayanta Sanusi ta taba shi. Sai kuma ta juya ta kalli yayanta Amadu dake kwance kai a fashe, take ta girgiza kai.

“Ba da gaske ba ne aa, wannan be faru ba, yan'uwana ba su mutu ba, ba ayi ma mahaifiyata fyade ba, wadandan nan mutanen ba su zo ba, komai be faru ba”

Ta tashi da sauri ta ruga da gudu daki ta koma gurin kwanciyarta ta kwanta taja abun rufa ta lullube ta kame guri daya ta runtse ido, da gaske so take ta farka daga bachin, so take komai ya zama mafarki. Sai a lokacin Inna ta samu kuzarin motsawa ta fashe da kuka.

“Allah ka isar mana ga bayinka Allah....”

Ta fada tana kara fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ta taba zuciya. Jin kalamanta ne yasa Aminatu ta saka hannayenta ta toshe kunnuwanta ta kara runtse ido ta kwara wani irin ihu da muryar da bata taba sanin tana da ita ba.

“Aaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa”

Ba makotansu kadai ba, har gidan dake tsakaminsu dashi gida biyar ne sai da suka ji ihun Aminatu.



>>>>>>>>>>
Anya Leila zata kai labari kuwa na cewar sai ta koyawa Talba darasi?

Nikan nace Ali yana hakuri da wannan aboki nasa mai wuyar sha'ani da jin Kai😕😠😡

Allah sarki Aminatu, ko da yake mahaifiyarta ce abar tausayi. 😭😭😭


________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
https://www.wattpad.com/story/283871769?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_reading&wp_page=reading&wp_uname=KhadeejaCandy&wp_originator=ZCqcO2wXIv6pkkxIr3do4ng1%2BTHhzoVPTPFtpfDcb1ftHOVsldMflpG2lAwd5aYtrehJ12WEeerjWSVNDZunKAH9QpxhI0A%2BzJsYI6RrshbTOZsoLUXljeZDCPaDNtKr


*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -5️⃣

Sai after sallah isha'i ya fito harabar gidan ya zauna a inda aka jera kujerun zama domin hutawa, kusa da garden, sai kamshin turare yake kamar sabon ango, fuskarsa cike da annuri, sai dai babu walwala ko kadan a tare da shi.
A hankali ya hade yawun bakinsa ya daga kansa sama yana kallon taurarin dake samaniya, kamin ya juyo yana kallon Amal dake sanye da kayan bachi tana nufo inda yake.

“Ya Talba”

Ya dan sakar mata murmushi kadan.

“Lil Sis ya kike?”

Ta zauna a kusa dake kusa da tashi tana amsawa.

“Lafiya kalau”

Sai kuma ta yi shuru tana kallonsa.

“Kina bukatar wani abu ne?”

Ta girgiza kai ta soma wasa da yatsun hannunta.

“Talk to me Lil Sis fada min damuwarki”

Ya fada yana kallon yanayinta dake nuna akwai damuwa a tare da ita.

“Yaya ka sake yin fada da Ya Leila ne?”

Fada suka yi? Ya zai fada mata? Abun da suka yi fada ne ko aa, shi be ma tabbatar ba, all what he know is ta kira shi wani shi kuma ya fada mata magana, sincerely speaking ma ya manta me yace mata.

“Yeah Maybe”

Ya fada yana dan tabe baki.

“Miya faru?”

“Ta dawo gida tana ta kuka tun dazun, yanzu kuma kuma Daddy ya shigo yai ma Momy fada ita ma kuka take?”

“Why?”

“I don't know, kawai dai na ji Daddy yana cewa babu wanda ya isa ya wulakanta masa d'a, kuma wai ya zaba maka Leila ne saboda kar kaje neman auren wata a wani gidan ace ba za a baka ba saboda yadda kake behaving, amman a gidansa yana da iko da Leila”

Talba ya cika ma bakinsa iska ya busar.

“Ina Momy?”

“Tana dakinta...”

Amal ta karasa tana kallon Kabir daya doso inda suke zaune ta kofar gaba, kana ganinsa ka san a fusace yake.

“Look Talba, ba zaka Leila kuka saboda bakin halinka and now ka saka Momy kuka ba okay? I won't tolerate this, dole ne sai ka auri Leila ne? Idan ba ka canja hali ba ba zaka taba aure ba a rayuwarka”

Daga inda yake zaune ya dago yana yi ma Kabir wani banzan kallo.

“Ka sani ba a amin tsawa ba a nuna ni da yatsa”

“To sannu ubana, sannu Sarkin Arewa, girman kai zai kashe Mtssssssssss”

Kabir ya karasa yana jan wani dogon tsaki. Amal ta yi saurin kama hannun Talba.

“Ya taso mu bar mishi gurin gaba daya”

Uffan Talba be sake cewa ba ya bi Amal dake rike da hannunsa, har sai da suka shigo cikin falon sannan ya saki hannunta.

“Je dakinki zan yi magana da Daddy”

“To amman karka ce masa ni na maka gulmar”

Yayi murmushi ya juya zuwa bangaren Daddy. Daman can duk wata gulmar gidan gurin Amal ake jinta. Cikin natsuwa da kamala ya shiga bangaren Daddy, yai sallama Daddy ya amsa masa tare da kai hannu ya dauki remote ya kashe plasma dake kunne. Talba ya zauna kasa kusa da kafafuwan Daddy.

“Daddy yau na kawo maka karar kanka”

Daddy yayi murmushi.

“Na taba Momy ko?”

“Eh Daddy ka san bana son hawayen Momy”

“To ai laifinta ne, taya Leila zata yi laifi na yi mata fada kuma tace zata shigar mata”

“Amman Daddy Momy tana kare Leila ne kamar yadda kake min, kuma tun da har Momy ta shigar mata na yarda ni ne ba ni da gaskiya, domin Momy kullum tana side dina ne”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“I will try my best na ga na zama Romantic, zan zama yadda Leila take so indai hakan zai faranta ran kowa, yanzu abu daya nake so Daddy ka je ka bawa Momy hakuri?”

Daddy ya nuna shi da yatsa.

“Hey i talk to your mom na mata fada, kuma ita ya kamata ta ba ni hakuri saboda rai na ya bace”

“Amman Daddy ai kai kayi mata laifi”

“Really? Kasan da wannan amman idan kai ma Leila laifi sai ka sa bata hakuri”

Talba yayi murmushi.

“Daddy wacan yana da banbanci da wannan, ita Leila ai yarinya ce, wannan kuma ba zaka iya da yayanta ba, yaranta ba za su yarda kai mata haka ba”

“Leila ma wata rana uwar wasu ce, kuma yaranta ba za su dauki abun da kake mata ba, kamar yadda a yanzu kake jin rashin dadi, and tell me, you take your Mom side”

Talba ya sake yin murmushi.

“No Daddy kullum ai ina side dinka, amman dai ina son Momy ta daina bacin rai please”

“Shikenan zan kirata ta zo nan na bata hakuri”

“No Daddy ka tafi dakinta mana, zata fi daukar abun da muhimmanci Please”

Daddy ya masa kallon mamaki.

“So that's mean kasan yadda ake lallaba mace, duk abun da kake yi da gangan kake yi kenan?”

Talba ya mike tsaye yana dariya kamar ba shi ba, Daddy ma murmushi yai mai sauti yana binsa da kallo cike da kauna irin ta Uba da D'a.
Bangaren Momy ya dawo, kai tsaye ya nufo dakin Leila, be tsaya knocking ba ya tura kawai ya shiga, sai ya same ta zauna gaban mirror tana duba fuskarka. Tsaye yai cak kamar an dasa shi, ta ina zai fara? Me zai ce mata? Sorry? Shi da kansa? Yace mata sorry? After ta kira shi wani? Taya ma zai ce mata haka? For the sake of Daddy, wata zuciyar ta raya masa, but duk da haka be jin zai iya ce
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment