Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

zai kawo min kaji?”

“Ah gaskiya idan fa yana da shi yana yi”

“Idan yana da shi kika ce, ke dai zauna na kawo miki ruwa”

Baturiya ta mika mata kujerar da take zaune dazun, ita kuma ta karba ta zauna tana karewa gidan kallo kamar bakonta, ko gaisuwar da Sultan yake mata bata ji.

“Baturiya kenan duk kyau nan naki kika kare a gidan nan”

Baturiya ta aje mata ruwan a cup tana fadin.

“To ya iya, kaddara rayuwa ta kawo ni nan”

“Kika dai kawo kanki, ke kika so ai”

“Hmmm Wallahi Ramlee babu irin cin mutunci da ban masa ba, amman yaki ya sake ni”

“Ina ko zai sake ki, tun da be da kudin auro wata, kuma ya san yadda kike da kyau nan kina cika idda wani mai kudi zai aureki”

“Da gudu ma, ni Wallahi ban taba zaton zan yi rayuwa a haka ba, bawan Allah nace masa idan mun yi aure zan cigaba da karatu yace ya yarda zai dauki nauyin komai, sai gashi abincin ma wannan wahala yake mana”

“To miya hana shi?”

“Ai lokacin da na aureshi karatu yake, ni na dauka, yana gama karatu zai samu aiki mu fancama yadda muke so, ashe ashe wahala ce ke kirana, gashi gurin auren ma sauki aka masa tun da auren gida ne, kawaye da muka gama secondary school a tare daga mai aure wani shege sai mai aiki a guri kaza ni ina nan zaune a wani shegen gidan duk yabi ya rugube, kuma na haya”

Tana kai aya Ramlee ta saka mata dariya.

“Ke kika so Baturiya, tsabar kyau fa Baturiya ake ce miki, gashi manyan mutane suna son farar mace, Wallahi ba ki ga yadda mutumen ya haukace daga ganin hotonki ba”

Baturiya ta nufi namanta ta juya tana fadin.

“Ke ni fa Ramlee duk iskancina ba zan iya zina ba”

“Su kuma manyan mutane ai sun fi son matan aure saboda sun fi Sirri, wasu kuma ba sai kin fada musu cewar kina da aure ba, ki ga abun da be wuce 30-1hour ba an baki kusan 500k ko 300k”

Baturiya ta juyo tana kallonta tana zaro ido.

“Da gaske wai?”

“Wallahi kuwa, ke auren ma ba rufi asiri ba ne a gareki, wanda ta haihu har wani tsoron fadawa maza take ma, kara ma budurwa ace ko dan gaba, amman ke fa? Kuma ko kudi aka ganki da shi za a ce na mijinki ne”

“Tab humm ai sun san bakiri nake aure, shi kansa idan ya gan ni da wannan kudi sai ya tambaya ina a samo”

“Ki ce tallafi ne kika samu, daga nan sai ki kirkiri sana'a ki fara yi, kin ga idan ma wasu sun shigo ba za a zarge ki ba, Wallahi cikin Shekara daya Fee'ah har makka sai kin je, kuma duk abun da kike so zaki siya a duniyar nan”

Baturiya ta dawo kusa da ita ta zauna.

“Amman su wani irin kudin banza ne da su haka?”

“Masu kudi fa aka ce miki Baturiya, kina irin wannan area ko'ina kwata ai dole ki yi mamaki, da zaki yarda zan hada ki manya manyan yan kasuwa da yan siyasa, kuma ba haka nan ake zuwa musu ba ai, sai an gyara ki an shirya, ta yadda zai ji kamar be taba kusantar wata mace ba”

“To shi zunubin zaki daukar min?”

Baturiya tai mata tambayar rainin wayo. Sai Ramlee tai murmushi tana mikewa tsaye.

“Baki ji matsi ba ne yarinya, kin san da Allah kika chat da maza a facebook? Har kina haduwa da su kina karbar kudinsu”

“Wannan ai dabam, ban aikata ba sai dai na yi musu dadin baki”

“To yayi kyau ki cigaba”

Ta saka hannunta a jaka ta ciro 10k ta mikawa Sulta.

“Sultan a siye minti ka ji, ni bari a dauki naman tun da ba za a min ta yi ba”

Ta karasa gurin naman ta saka hannu ta dauka ta kai bakinta, Baturiya ta yi murmushi.

“To ai ke dince kika dauke min hankali ”

Bata sake ce mata komai ba ta nufi kofa, Baturiya sai kallo tsadadden lace dinta take, sai da ta fita sannan ta juyo.

“Ni baki ma fada min ina kika samu nama ba, ko wani aka yaudara”

“Wannan karon roka na yi”

“Uhm wata rana dai zasu roki abun da baki so”

“Ai da zarar na ga mutum da ruwan haka, sai na zubar da shi na kama wani”

Ramlee ta yi dariya ta juya ta kama Hanya Baturiya kuma ta rufe gidan ta nufo gurin yaronta Sultan ta karbe kudin da Ramlee ta bashi.

“Karka fadawa Daddy ka ji?”

“Toh”

Ya amsa ta yana kai hannu ya dauki cinyar kaza. Sai bayansa sallah isha'i Faruq ya shigo gidan, ba laifi ya samu masu haske har ya hada 500, tun da ya ji kofar gidan a bude ya tabbatar matarsa na cikin nishadi, domin idan tana jin rashin mutunci wani lokacin rufe gida take saboda yai ta wahalar kwankwasa a waje.
Bayan ya shigo ya maida kofar gidan ya rufe, kamin ya karasa falon ya so ma jin waka ya tashi, ko kwankwato babu matarsa na cikin nishadi a yau. Sallama yai ya shiga ta amsa masa kamar ba ita ba.

“Sannu da zuwa”

Ya dan tsaya kallonta kamin ya amsa.

“Yauwa, ya gidan”

“Alhamdulillah”

Ya zauna saman kujera yana kallonta.

“Mun samu wani abu ne kike ta nishadi haka?”

‘Tun da a sanadinka aka samu ai za a sammaka’

Ta fada a ranta a fili kuma sai ta mike tsaye tana fadin.

“Uhm wasu yan kudi ne na samu shi ne na siyo kaji na soya mana”

Daki ta shiga ta debo masa a platecikin wanda ta soya ta kawo masa ta aje a gabansa.

“Ina kika samu kudi?”

Ya tambaya yana kallon naman da zai rabin kaza.

“Allah ya ba ni”

Ta amsa masa bayan ta zauna.

“Haka kawai Allah zai baki kudi daga sama ba ta dalilin wani ba?”

“Allah ne ya ba ni”

“Ki dauke namanki, ki kawo min abinci, ba zan ci abun da ban san inda aka samo shi ba”

“Matsalar talaka kenan ai, ga talauci ga girman kai, yaushe rabon da mu ci nama a gidan nan?”

“Ba mu kadai ne a cikin wannan halin ba Rafi'ah, mutane da yawa suna ciki, mutane da yawa a da da kika san suna ci uku a wuni wssu yanzu biyu suke wasu daya, amman idan muka yi hakuri komai zai wuce, na san kina cikin hali Rafi'a, saboda kina ganin yan'uwanki da kawayenki a ciki wadata, hakan ba yana nufin Allah ya manta da ke ba, da ya ga dama da sai ya aura miki wanda yafi kowa kudi a duniya, amman ya jarrabaki miyasa ba zaki yi hakuri ba?”

“Faruq kenan, yanzu duk hakurin da na yi na shekara biyar baka gani ba?”

“Kin yi hakuri na sani, amman fadar sirrin gidana yafi komai yi min ciwo, idan na ci ko ban ci ba wani ya sani abun na min ciwo, bana son ki fada wani hali saboda halin da muke ciki dan Allah ki yi hakuri”

“Ai dole kace na yi hakuri kam, ban da hakuri me kake da shi da zaka ba ni Faruq? Yanzu dan na samu kudi na siye nama na ci ya zama laifi? Ka san ina da ciki ina kwadayin abubuwa amman kai zargina ma kake, ni wannan cikin ma zubar da shi zan yi Wallahi, dan ba zan haihu ba ka yanka min bunzuru, wata kila ma ba zaka yanka min komai ba ka bar ni kyari da ido kamar kwaruru baki salab kamar Salamatu ina kallon yan barka ayi ta mana tsigumi”

“Allah da yai masu kudi be manta da ni ba Rafi'a, ban san wace irin macece ke ba, idan na fita waje ina cikin damuwa da bakinciki a maimakon idan na dawo gida na samu nishadi sai na tarar bakinciki gida yafi na waje yawa, har fargabar shigowa nake”

“To ka sake ni mana, ko zama da ni dole ne? Kai wai kana ganin Allah ba zai hukuntaka yadda kake azabbatar da mu da yunwa?”

“Kika sake furta wata magana sai na mareki Wallahi”

Ya fada cikin bacin rai, da muryar dake nuna da gaske yake. Ganin hakan yasa dole tai shiru domin ta san halinsa idan ya fusata be iya ba.




TALBA POV.

Zaune yake saman carpet yaran na zagaye da shi, sai kallonsu yake yana murmushin. Farincikin yara musamman marayu na daga cikin abunda yafi komai faranta masa rai, hakan ne yasa shi bude gidan marayu, kuma yana kai ziyara lokaci zuwa lokaci, wani lokacin kuma yana zuwa gurin ya wuni tare da su, ko ya dauke su ya fita da su zuwa gurin shakatawa.
Ya kalli agogon hannunsa sannan ya daga yarinya dake cinyarsa da bata wuce 5 years ba ya mike tsaye. Sai yaran ma suka mike tsaye suka bi bayansa har zuwa gurin motarsa, ya saba musu idan zai tafi yana raba musu kudi ko alawa wani lokacin kuma chocolate. Sai da ya shiga cikin motar sannan ya mika hannunsa baya ya dauko ledar sweet ya bude ya fara raba musu, hannu biyu suke sakawa suna karba kamar yadda ya koyar da su, hayaniyar yaran yasa Ali dake driver side ya bude ya fita yana waya. Da dai daya Talba ya bisu yana basu, idan ledar ta kare sai ya bude wata, har sai da ya raba musu duka sweet din da ya zo da shi, sannan ya kwantar da kujerar motarsa ya kwanta yana jiran Ali dake waje yana waya.
Bayan Ali ya kare ya dawo cikin motar ya rufe yana kallon abokinsa.

“Ka gama da su?”

Talba ya kalleshi kamar be ji abun da ya tambaya ba.

“Har yanzu tunanin abun da kai ma Leila kake yi?”

“Saboda Daddy da Momy na yi, kuma zan cigaba da yin hakan matukar hakan zai faranta musu rai”

Yana rufe baki sakon Leila ya shigo wayarsa.

“Ka zo ka kai ni shopping yanzu”

Ya dauke idonsa bayan ya gama karantawa.

“Leila tana ganin hakan ba zai saka na tsane ta ba? Ina son girmamawa Ali, ai ya kamata tace Yallabai, but look how she text me kamar wani direbanta”

“Tana da gaskiya, ya kamata ka koyi girmama mace”

“Ba macen da take kasa da ni ba, wannan ranar ba zata taba zuwa ba, ba zan taba zama wawa akan mace ba, sauke ni gida”

Ali yayi murmushi yayi ma motar key, har suka isa gidan idon Talba a rufe, hannyensa kuma rumgume a kirji. Harabar gidan Ali yai farkin Talba be ce masa komai ba ya bude motar ya fita ya nufi kofar falon, kananan kaya ne a jikinsa, sai kamshin turare yake. Yana isa ya danna door bell din ya tsaya jikin kofar, cikin kankan lokaci aka bude masa kofar domin yanayin yadda yake danna door bell din dabam ne, da yasa ake gane shi ne. Dagowa yai a hankali ya kalli Baaba wanda ta bude masa kofar hawaye na sauko mata. Dan fuskar Mama yai domin ta saba idan ta bude masa zata masa sannu da zuwa angona, sai yai mata murmushi ranar da yan kwarai suke a kai kuma zai soma taba wasa da ita ko ya amsa mata. Shigowa yai cikin falon yana kallon Leila dake tsaye kusa da sofa ranta a bace, sai kuma ya juyo ya kalli Baaba.

“Miya faru?”

“Babu komai ranka ya dade”

Baaba ta amsa masa sannan ta fara tafiya. Binta yai da kallo kamin ya maida dubansa gurin Amal dake tsaye upstairs tana zayyana masa abun da ya faru.

“Ya Leila ce ta mareta”

Talba ta kalli Leila.

“Baaba ta ho dan Allah”

Baaba ta juyo ta dawo kusa da shi ta tsaya cikin damuwa.

“Bata hakuri”

Talba ya fada yana kallon Leila, wani irin kallon mamaki tai masa, Momy na jin haka ta fito daga kitchen.

“Ita fa tai min laifi”

“Kin sani sarai bana maimaita kalma”

“Baka san abun da ya faru ba”

“Bana son na sani”

Ya fada yana matsawa kusa da ita, kana kallon cikin idonsa ka san ransa ya bace. Sai da ta kalli Momy sannan ta kalli Baaba ta ce.

“Ki yi hakuri”

“Babu komai ya wuce”

Baaba ta fada sannan ta nufi kofar fita falon zuwa BQ inda dakinta yake. Sai da ta fice sannan Momy ta karaso inda Talba yake tsaye tana fadin.


“Wannan be kamata ba sam, taya zaka wulakanta yar'uwarka a gaban yar aikin?”

“Be kamata ta dauki hannu ta mareta ba Momy, no matter what Baaba tai mata, ta yi jika da ita”

“Gaskiya ka ci mutunci Leila, ka tauye mata hakki Talba, na yi shiru ne kawai saboda bana son na yi magana a gaban Baaba”

“Kin san inda na fito Momy? Gidan marayuna, yaran da suke can basu da uwa ba su da uba, wasu ma a titi aka dauko su aka kawo su nan, wasu kuma danginsu basa iya kula da su, amman Leila Allah ya ba ta komai, kudi, uwa, uba, ilmi, dukiya, sai dan na saka ta ba da hakuri ne zai zama cin mutunci?”

“Wannan kuma ai dabam ne, akwai tazara mai fadi mai tsawo tsakanin mai kudi da talaka, akwai abun da be kamata ayi agabansu ba, ko kuma a saka ayi musu, musamman inda muke da gaskiya”

“Wannan zarar da kike magana, ban tana ganinta ba, kuma ba zan taba ganinta ba, ban taba jin na fi wani dan yana talaka ina da arziki ba, sai dai na ji nafi shi saboda yana kasa da ni a aiki ko a shekaru, ko kuma saboda ni ina miji ita tana mata, amman ba zan taba iya cin mutuncin wanda ya haife ni ba, wasu talakawan sun fi mu a gurin Allah”

Yana gama fadar hakan ya nufi kofar fita a fusace. Momy ta bishi da kallo tana kada kai.

“Finally, gatan Daddynka ya saka har ni kana iya tsayawa ka fadawa magana... ”

Be juyo ba dan be ji akwai abun da zai sake ce mata. Balle kuma ta kuma ya kula Amal dake zayyana masa abun da ya faru daga can inda take tsaye.

“Ya Leila ce ta kawo mata ruwa shi ne, gurin mika mata carpet ya tadeta ruwan ya zuba a jikin Ya Leila sai ta mareta...Shi ne abun da ya faru Ya Talba ko baka tsaya ba na fada maka, Ya Leila ce bata da gaskiya”

Ta karasa ita da Leila suna watsawa juna harara, daman can haka suke kamar ba yan'uwa ba, basa shan inuwa daya.



________

Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai, muna da kwalli mai karfin gaske (Mujarrabun sadidan) Akwai na farin jini for yan mata da Zaurawa. Akwai wanda ba a bawa mai kishiya, akwai na mazajen da kr neman mata, muna da rantse baki da kishiya, muna da back to virgin, for yan matan da kaddara ta fadawa, ko Zaurawan dake son zama yan mata, akwai jigida mai kyau, muna da man ayu 100% natural. Akwai na maza masu hannun Dambe.
Hajiya sai n gwada akan san na kwarai, ba cuta ba cutarwa, duk wanda kika siya sai kin dawo.

Ga masu bukata za su iya tuntubar number na 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.
*💔 BAKAR WASIKA 💔*


By Khadeeja Candy


Page -7️⃣

Bayan Baba ya sauke wayar ya kalli Inna cikin yanayin damuwa yace.

“Bashiru ne yake mana maganar komawar mu can”

Inna ta girgiza kai.

“Babu inda zanje, ba a tserewa mutuwa a ko'ina take”

“Na san da haka amman dai ya kamata mu bar garin nan saboda ance akwai yiyuwar su dawo, kuma kina gani kullum mutane barin garin nan suke”

“Babu inda zanje Malam, na fi son mutuwata ta same ni a inda nake”

“Ai kaji matsalarki kenan, shi kansa abun da yake ta magana kenan a lallaba masa ke”

Inna bata sake cewa komai ba, har Baba ya ci ya shude. Duk abun da suke Aminatu na dama furar tana saurarensu, bayan ta gama ta kawo ma Inna ta zauna kusa da ita ta fara bata a hankali tana sha, Inna bata hana Aminatu shayar da ita ba, duk kuwa da kasancewar zata iya sha da kanta. Sai da ta tabbatar ta koshi sannan ta rufe furar ta koma gurin girkin da take. Har ta girka ta gama bata cikin walwala da sakewar zuciya, ba na rashin yan'uwa ba, na tunanin kalaman da Inna tai mata? Ta ya zata rayu babu Inna? A hannu waye zata zauna ma? Ba ita kadai ba Baba ma ya zai ji idan suka wayi gari babu Inna? Ko da ace tana da aure rayuwa ba zata taba mata dadi babu uwa ba, balle kuma a yanzu da take tare da ita, Saurayinta Maniru ma yana cikin mutanen da yan bindigar suka kashe, bayan ta gama ta zubawa Baba nasa ta zubawa Isah a inda ake saka masa sannan ta kwashe sauran a Samira babba, ta debi ruwa ta shiga bandaki. Sai da ta cire komai na jikinta sannan ta zauna saman dutsen da suke zama idan zasu yi wanka ta fashe da kuka.
Kuka tai sosai sannan tai wanka ta fito idonta a kumbure, ta dora alwala ta shiga dakinsu tai sallah, bayan ta gama ta d hannayenta sama tana rokon Allah.

“Ba ni da gata sai naka Allah, ka dauke yan'uwana a lokacin da ka so, ka sauya rayuwata zuwa yadda ka kaddara min, Allah ka yafe min ka jikan yan'uwana, ka ba mahaifiyata lafiya ka bar ni da ita Allah”

Ta karasa hawaye na sauko mata, sannan ta shafa addu'ar ta mike tsaye, ta fito waje, sai da ta zuba ma Inna ruwa a buta sannan ta rika ta, ta kaita bandaki bayan ta fito ta taimaka mata tai alwala sannan ta shimfida mata abun sallah.

“Allah ya miki albarka Auta”

Inna ta fada tana kokarin gyara zamanta, domin a zaune take sallah a yanzu. Aminatu ta kalleta kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta amsa.

“Ameen”

Ta mike tsaye.

“Bari naje na yi itace yamma ta yi”

Kai kawai Inna ta daga mata, ita kuma ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka ta ta dauki zaren da take daure itacen idan ta yi, sannan ta saka talkaminta ta fice, ba ita kadai ba kusan duk yan matan garin da ma matan aure suna zuwa daji ne su yi kara da yamma saboda dafa abinci, abu ne mai wahala ka ga gidan da ake siyen itace a yanki, yawanci duk a daji suke yin kara.
A da ta saba idan zata tafi yin kara akan biyo mata ko kuma ita ta biyawa wasu, sai dai tun bayan da aka tarwatsa rabin garin take tafiya ita kadai, saboda an tafi da wasu yan mata, wasu kuma sun yi gudun hijira, sauran da suka rage kadan ne. A gurin da ta saba tsayawa ta tsaya ta shimfida zanen sannan ta aje zaren a gefe, kana ta shiga tsintar karan, tana yi tana tuna yadda suke yi a da, ita da kawayenta, har tigengen suke cikin nishadi da walwala, sabanin yanzu da suka bar ta da kewa.
Sai da tai rabin sannan ta samu kanta da mugun faduwar gaba, marar misaltuwa, a take ta nade wanda ta tara a daure ta dauka ta nufo gida da gudunta, kowa sai kallonta yake, kamin ta iso har hawaye ya fara sauko mata, bakin kofa ta jefar da karan ta rugo da gudun gurin Inna da ke kwance tana bachi ta taba ta.

“Inna...Inna.... Inn”

Bata karasa ba, Inna ta bude idonta da sauri tana kallonta.

“Lafiya Auta?”

Sai ta fashe da kuka, wanda hakan yasa Inna ta tashi zaune.

“Tsoro nake ji Inna, gabana faduwa yake”

“Tsoron me? Miya faru?”

“Ban san ni ba, bana son na yi nisa da ke”

“Auta kenan, kin isa ki tare min mutuwa ne? Da wani na tarewa wani mutuwa ai da na tarewa Yayana, kin san babu uwar da za a kashewa yaya a gabanta kuma ta kyale alhalin tana da ikon yin wani abu?”

Maganar da Inna tai ya isa ya tabbatar da cewar ta fi jin bakincikin kashe mata yaya da akai fiye da keta mata haddi da aka yi. Aminatu ta yi kasa da kanta tana kuka sosai.

“Kina kuka da wuri, ki adana kukanki saboda gaba”

Ta kalleta.

“Miyasa kike min fatan kuka Inna?”

“Saboda zaki yi kuka mai yawa Aminatu, dole zaki yi kuka, ranar da zaki bude ido babu ni, ranar da zaki ga wata uwar idan kika tuna da taki dole ki yi kuka, ranar da kika ga wasu yan'uwa kika tuna da naki dole ki yi kuka, ranar da kika nemi wani abu kika rasa dole ki yi kuka, ni na riga na gama tawa rayuwar har na yi jikoki kuma na yi Auta, ke kuma yanzu rayuwarki take kan ginuwa, ta fara miki a haka, me kika tsammani a gaba? Dadi? Dadin yana tafe bayan wuya amman, yanzu na fi tausayin rayuwarki fiye da ta kowa Aminatu”

Ta share hawayenta, ta kara matsawa kusa da Inna ta kwanta jikinta, ta lumshe ido, tana maida numfashi a hankali.

“Allah ga yata, Allah ka zame mata gata”

Inna ta fada a ranta hawaye na sauko mata, ba tana kalamai ba ne domin ta daga mata hankali, a a har ga Allah tana fadin abun da take jin ya kusa tabbatuwa a gareta ne, kuma tana jin nata mai kiran ya kusa kiranta, jikinta da mafarkanta suna bata haka, domin tana jin wani kalar yanayi na dabam a jikinta wanda bata taba jin irinsa ba, sai dai a kusa? Ko a nesa? Yau ko anjima? Shi ne abun da bata da tabbaci.
Bayan sallah Magariba, Baba da Isah suna daki sun saka Inna a gaba suna ta kokarin convinced din Inna akan ta amince da magabar Bashiru su ma su yi hijira su bar garin amman ta ki, Aminatu kam tana zaune waje sai kallon hadarin dake haduwa take, ita kanta bata san na yi ba, tafiyar ko zaman? Inna tana da gaskiya idan sun tafi ba za su tserewa mutuwa ba, sai dai barin garin zai taimaka Inna ta manta wata damuwar, domin a cikin abubuwan da suke bata mata rai har da zaman gidan da take ganin an kashe yayanta kuma tana ganin a kowa ne dare kamar za su shigo ne su yi mata sallama kamar yadda suka saba, yadda rayuwa take a baya.
Sai da akai kiran sallah isha'i sannan Baba da Isah suka fito waje, sukai alwala suka yi haramar zuwa masallacin.



TALBA POV.

Ya kusan minti ashirin a cikin motar sannan ta fito, kamin ta bude motar ta shiga ma wani aiki ne, ba karamin kufula shi tai ba, domin ya tsani jira ya tsani a bata matsa lokaci.
Sai dai ko kadan be nuna mata ransa ya bace ba, ya ja motar suka fita fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Mai gadin be yarda ya tsaya jiran sai Talba ya danna horn sannan ya bude masa ba, tun a lokacin da ya ga ya shiga motar yai hanzari bude gate din ya tsaya, be bar gurin ba har sai da motar Talba ta fice daga gidan.
Be kalli inda take ba, tukinsa kawai yake yana sauraren fm din dake gabatar da wani program, sai dai ita lokaci zuwa lokaci tana satar kallonsa, duk kuwa da kasancewar bata son su hada ido gudun kar ya ga tana kallonsa.
A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin titi, ya zata yi ta canja Talba? Shine tambayar da ta zo mata a rai, gata a mota daya da shi amman baya nuna mata wata alamar kauna, Baya ma son kallon inda take kamar ba masoyinta ba.

“Na fasa zuwa shopping din take me home”

Sai a lokacin ya kalleta tare da kiran sunanta.

“Leila...”

Ta kalleshi Irin duban nan na fusata, sai dai kwarjininsa ya hanata nuna masa fushinta.

“I'm not your
DOWNLOAD
DOWNLOAD

1 Comments On BAKAR WASIKA
avatar
aisha-7-1

6 months ago

Reply

Nice novel

Please Login or Register in order to submit comment