Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din dake gefe ya sha. Mika ma safiyya yai. Ta girgiza masa kai. Ajiyewa yai.

Ya janyo ledar fruits din ya sha kankana sosai. Ya ci ayabar dake ciki takai goma sannan ya mike.

Cikinshin safiyya tabi da kallo cike da mamakin ganin duk lodin dayai mishi yana nan a shafe.

Expression din fuskarta ya sa shi yar dariya. Rabon daya jishi shidin ta bangaren cin abinci harya manta.

Yau jinshi yake wani normal. Ya dawo fu.ad dinshi. Duk wani abu da yake tunanin ya rasa ya dawo.

Bude baki yai zai magana wayarshi tai ringing. Hakan ya tuna mishi da yana bukatar sake fita.

Dauko ta yai kan kujerar daya tashi. Wani iri yadan ji. Sam bai shirya jin wani dogon zance ko nasiha ba.

Dagawa yai ya kara a kunne. Haneef yace.

"Fito"

Kan ya amsa ya kashe wayar. Ajiyar zuciya fu.ad ya sauke hadi da fadin.

"Just when i thought yau babu wani drama........!"
[7/1, 7:31 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/1, 7:33 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 22
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

22

*Do include a bro in your du.a. Mustapha may His soul rest in peace. Waya sani ni ko ku wani zai bukaci hakan anjima ko gobe. Allah ya saukaka mana tamu tafiyar. Amin*

Safiyya ya kalla yace.

"Barin ga haneef a waje"

Kai ta daga masa. Ya fice da sauri. Tun daga nesa daya hango haneef jingine jikin mota. Jikinshi sanye da manyan kaya ya daga hannuwanshi alamar surrender.

Yana karasawa ya wani yi rau rau da idanuwa hadi da fadin.

"Dan Allah kace ba fada zakaimun ba. Wallahi iya ba jiya ma nayi sub din wata biyu"

Haneef bai san lokacin da dariya ta kubce masa ba. Fu.ad ya wani dafe kirji dai dai inda zufiyarshi take yana sauke numfashi.

"Hankalina ya kwanta. Ina wuni"

Daure fuska haneef yai. A ranshi yana fadin. Dole ka gaishe dani tunda baka da gaskiya.

Idanuwa kawai ya zuba mishi. Abinda yasan baya so. Gara kai masa masifa a wuce wajen.

Cike da kosawa yace.

"Alright kamun fadan...."

Shirun dai ya sake masa.

"Please..... "

Hakan yasa haneef fadin.

"Bansan me zance maka ba fu.ad. Kome na fada ta gefen kunnenka zai wuce"

Da sauri yace.

"Zai tsaya ciki. Da gaske nake amman karkamun fushi. In babu kai bazan iya fuskantar su abbah ba"

Yanayin daya karasa maganar da wani sanyi yadan taba haneef din. Kallon shi yai da kyau.

"Bakajin magana. Abinda kai ba karami bane ba. Bance bazai yafu ba. Auren da aka gina ta hanyar da ya dace ma yana zuwa da matsala fu.ad.

Ballantana naku da babu amincewar iyaye ballantana albarkarsu.

Kasan rayuwarta ta gama canzawa kenan?"

Cikin ido ya kalli haneef yace.

"Nasani. Ina sonta sosai. Bani da wani zabi ne shisa"

Sai da haneef ya sake gyara tsayuwa tukunna yace.

"Na yarda baka da zabi. Amman kana da son kanka da yawa. I really hope zaka so ta rabin yanda kake son kanka"

Dariya fu.ad yai.

"Em' noh' dah' selfish fa. We good?"

Girgiza kai haneef yai.

"Not even close"

Mota fu.ad yaga yana niyar shiga ya riko masa riga da sauri.

"Fu.ad meye haka kaman yaro. Sakemun riga karka dakuna mun...."

Haneef ke fadi yana kiciniyar kwace fu.ad dayake rike dashi dam.

"Allah sai kace we good sannan"

Ikon Allah haneef ya ware ido yana kallo.

"Wai kai bakasan ka girma ba? Kana da aure fa yanzun. Haka zakai yara kai kanka yarinta bata gama sakinka ba"

Rigar haneef ya saki ya wani dakuna fuska yana fadin.

"Banda wajen yara a zuciyata. Naku kawai sun isheni....."

Girgiza kai kawai haneef yai yana bude murfin motar. Sake riko shi fu.ad yai.

"Please mana. I need mi' bro"

Sauke ajiyar zuciya haneef yai. Shi kanshi yasan bazai iya wani fushin kirki da fu.ad ba.

"We are good. Tana sonka fu.ad karkai mata butulci please"

Murmushi yai sosai sannan ya daga hannunshi alamar salute yace.

"Yes sir"

Dariya haneef yai ya shiga motar. Ta window din fu.ad ya tsaya yana fadin.

"Na siya gida fa. 3 bedroom ne. Barin dauko maka takardun ka ajiye mun a wajenka.

Please ina son siyan furnitures da za.a saka anjima. Inzo muje tare"

Girgiza kasa kai haneef yai.

"Nope. Allah ya sanya alkhairi. Ka dai kara addu.a sosai daukomun takardun sauri nake"

Da sauri ya je ya bude motarshi ya dauko takardun ya kawo ma haneef. Wani langabe fuska yai.

"Inzo muje?"

"Ku tafi da lukman mana"

Haneef din ya fadi yana tada motarshi.

"Fushi yakemun"

Kallonshi haneef yai ya daga gira alamar 'matsalarku ce'. Sannan ya maida hankalin shi kan motar yana janta.

"Thank you"

Fu.ad ya fadi yana kallonshi harya fice. Wani sanyi yaji.

"Saura lukman. Sannan su abbah"

Ya fadi yana komawa cikin gida. Inda yabar safiyya ya sameta. Ya karasa kan kujerar da take zaune ya zauna daf da ita.

Yana kallon yanda jikinta yai wani iri alamar tana son matsawa. Basarwa yai dole ma ta saba dashi.

"Fita zan sakeyi. Saikin mun hakuri kadan. Komai zai dai-dai ta in shaa Allah"

Ba fitarshi bace ta dameta. Yanda take jin hucin fitar numfashinta dab da ita.

Zuciyarta a kwance take yana zama ta soma tsalle tsalle. Manyan idanuwanta ta sauke masa kan fuska.

Kasa daurewa yai. Hannu yasa ya taba kuncinta. Tadan janye fuskarta. Hakan yasa shi sauke hannunshi.

"Bara in tafi sofi"

Mikewa yai. Tabishi da idanuwa. Abinda ke cikin idanta ya fisgeshi. Komawa yai ya tallabi fuskarta da hannuwanshi duka biyun.

Pecking dinta yai a goshi. Sannan ya mike ya fice. Hannuwa tasa ta taba inda nashi hannun yabari.

Ta lumshe idanuwanta tanajin yanda har lokacin dumin hannunshi baibar wajen ba.

*

Kai tsaye gidansu lukman ya wuce. Yako yi sa.a yana dakin shi a zaune yana cin abinci.

Da sallama ya shiga ya karasa. Amsa shi ya sauke idanuwanshi kan takalman da ya shigo dasu.

"Takalmi fu.ad...."

Inda yake tsaye ya tsaya. Nan ya cire takalmin yabarsu tsakiyar dakin ya karasa.

Zama yayi. Lukman ya ci gaba da cin abincin shi yana danna waya kamar ma fu.ad din baya dakin.

Wayar ya karba ya sakata a key ya ajiye gefe. Kallon lukman yai sosai.

"Kayi hakuri. I know em' a shitty friend. Hell ion' even deserve aboki kaman ka.

But ina bukatar abokina. Dan Allah kayi hakuri"

Cokalin ya ajiye cikin plate dinshi ya dago ya maida hankinshi kan fu.ad daya wani yi rau rau da idanuwa yace.

"Kasan dai zaka iya tarata da kowanne irin magana. Bance ko yaushe kake abinda ya kamata ba.

Ban kuma damu da ka saurari shawarwarina duk sanda na baka su.

Imagine fu.ad zaka yanke hukunci irin wannan ba zaka fadamun ba"

Hannuwanshi ya hade alamar neman afuwa tare da cewa.

"Na riga da nayi. Kayi hakuri"

Murmushi lukman yai. Fu.ad yace.

"Menene na murmushi cikin maganata"

Daga gira lukman yai duk biyun hadi da fadin.

"Dan dawo baya kadan. Kaman hakuri naji kanata bani"

Dariya fu.ad yai yana daukar pillow din kujerar dayake kai ya jefa ma lukman.

"Shut up"

Dariya sukai gabaki daya. Kamun cikin serious voice lukman yace masa.

"Safiyya ta maka abinda bakowacce mace zata iya ba.
Ko da nine a matsayinta bayan abubuwan da suka faru sai dai sonka ya kasheni wallahi.

Dan Allah ka riketa"

Dafe kai fu.ad yai.

"Seriously. Me yasa kuke fadamun abu dayane wai. Ina sonta. Kun kasa ganewa and zan rike ta in shaa Allah"

Daquna fuska lukman yai.

"Naji sarkin soyayya. Shahid kapoor. Ba saika gartsamun cizo ba daga fadar gaskiya"

Dariya kawai fu.ad yayi. Yasan indai lukman da haneef na tare dashi zai winning kowa a hankali.

Hira suka shiga yi. Fu.ad din na bashi labarin yanda komai ya faru da maganar gidan da ya siya.

Nan ya jira lukman din bayan yagama cin abinci. Yaje yai wanka ya fito sannan. Saida suka biya ta wani shagon saida wayoyi.

Ya basu wayarshi ya dauki wata karamar HTC da kudin. Inba dole ba yafi son ya siya wayarshi acan.

Lukman ya tayashi zabar wa safiyya wata Tecno mai kyau. Sannan suka wuce wajen furnitures.

Pictures aka dinga dauko musu fu.ad na fadin basuyi mishi ba. Shi sam baya son kayan katako.

Wasu ya zaba. Na black silver. Lukman ne yai magana dasu suka gama cinikin komai.

Tare da wanda motocin kayan suka tafi har gidan. Da yake in kana bukata su zasu hada maka komai su jera.

Haka aka jera musu komai. Lokacin magrib tayi. Daga shi har lukman a gajiye suke.

Sun dawo sallar magrib ne fu.ad ya kalli lukman a gajiye yace.

"Wai daman haka hada gida yake da wahala?"

"Ni kaina ban san da wahala haka ba. Kuma har yanzun akwai abubuwan da babu fa"

Dan yamutsa fuska fu.ad yayi.

"Babu tv..... "

Girgiza kai lukman yai.

"Ba wannan bane kadai. Akwai abubuwan da babu"

Sauke numfashi fu.ad yayi.

"Zan kira pha.iza hopefully ita batai fushi ba. Sai tazo tagani ko?"

Jinjina kai lukman yayi alamar yarda da abinda fu.ad din ya fadi.

Kulle gidan sukayi. Sai da ya sauke lukman gida. Ya sake biyawa ya hado musu takeaway sannan ya nufi gida.

*

Tayi kallo harta gaji. Tunani kala kala a ranta. Da taga tunanin su inna da ko ya suke ciki na neman haye mata yasa ta ture su gefe.

Dan wata irin kewar inna ke damunta. Lumshe idanuwanta tayi tana tunanin fu.ad.

Yanda take mafarkinshi da yanda take ji akanshi. In yana gabanta tafi jin hakan sosai.

Goshinta ta sake tabawa kaman zata dangwalo peck din dayai mata dazun a jiki.

Taga ya dade sosai dai. Take addu.ar Allah yasa lafiya. Ta tashi ta leka kofa yafi a kirga mussaman yanzun da dare yayi.

Sallar isha.i taje tayi. Ta sake watsa ruwa duk da sanyin shi dankam ko gida takan dafa wasu lokuttan.

Tai alkawarin in fu.ad ya dawo zata tambaye shi dankam ruwan akwai sanyi da kuma bokiti tagaji da wahalar nan.

Wata riga ta saka doguwa fara. Ta daura dankwalin akanta. Tana bukatar inner wears. Suma tafi bukata fiye da kayan sakawa.

Tunanin fadama fu.ad kawai sai da wata kunya mai karfin gaske ta kamata. Ta dawo falo ta zauna kenan taji sallamar shi.

Wani murmushi ya kwace mata. Ta amsa ta mike ta karasa inda yake tana karba ledojin daya shigo dasu.

"Sannu da zuwa. Ka dade sosai.... "

Kallonta yake. Rigar ta wani mata kyau. Da murmushi ya amsa da.

"Sorry nasani. Munata siye siye ne fa da lukman. Saura kadan in shaa Allah.

Babu dai zazzabin ko?"

Kai ta daga mishi. Dan garau take jinta. Banda damuwar dake danne kasan ranta.

Karasawa sukai ya zauna kan kujera. Kasa ta ajiye kayan data karba hannun fu.ad ta nemi wata kujerar ta zauna.

"Sofi kaina ciwo yakemun fa"

Cike da kulawa tace.

"Sannu. Daka je ka kwanta kadan huta. Ko in dauko maka magani?"

Girgiza mata kai yayi hadi da fadin.

"Stress ne kawai. Bari inyi wanka inzo muci abinci. Ko kina jin yunwa?"

Tanajin yunwa sai dai kawai ta tsinci kanta dason ta jira fu.ad din ya fito. A hankali tace

"Kaje ka fito"

Wucewa yazo yi ta gabanta hakan yasa tace.

"Umm kaji...."

Juyowa yai da duk hankalinshi akanta.

"Ya dai sofi? Menene?"

Yanda ya zuba mata idanuwa da dukkan nutsuwar shi ya sata jin wani iri. Kanta ta sadda kasa.

"Ba wani abu bane babba fa"

Waje ya samu ya zauna gefenta.

"Komun kankantar shi. Ina jinki"

Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi tana kin yadda idanuwanta su hadu da nashi sannan a hankali muryarta can kasa tace.

"Ruwan wanka. Sanyi gare shi sosai kuma babu bokiti sai dai inta tarowa da hannu"

Ware idanuwa yai da mamaki yace.

"Bokiti kuma sofi? Ruwan ina kike wanka dashi?"

"Ruwan daka kunna mun nai alwala"

Baya so ya yarda da maganarta sai ya tabbatar. Mikewa yai yana fadin.

"Ta so ki nunamun"

Babu musu tabi shi har zuwa toilet din. Fanfon dake wajen alwala ta danna kaman yanda yai sannan ta kalle shi tace

"Kaganshi. Ruwan sanyi sosai"

Baisan lokacin da dariya ta kubce masa ba. Dariya yake sosai har da dafe ciki.

Kallon shi take da murmushi a fuskarta. A kunyace tace.

"Nayi kauyanci ko?"

Girgiza mata kai yake ya kasa daina dariya har lokacin. She is just too much ya fada cikin kanshi a fili kuma yace.

"Sofi......"

Kasa magana yai saboda wata dariyar dayaji ta sake kubce masa. Dakyar ya samu ya nutsar da kanshi sannan yace mata.

"Zo ki gani"

Nuna mata yanda zata hada ruwa bathtub din yayi. Da inda zata cire ruwan ya tafi.

Sau uku ya nuna mata tana kallo. Tun a karo na farko ma ta rike komai dan wahala dai kayi abu a gabanta. Tsayawa yai tayi yagani.

Da murmushi a fuskarshi yace

"Good girl"

Murmushi ta mayar mishi a kunyace.

"Barin yo wankan ko?"

Kai ta daga mishi. Tare suka fice yai dayan bedroom din ita kuma tai zamanta a falo. Kawai dariyarshi take ji cikin kunnuwanta da yake sata murmushin data kasa fahimtar daga inda yake fitowa.

Tana nan ya fito. Sanye da three quarter loose mai wasu igiyoyi daga kasan milk sai riga fara data kama shi.

Idanuwanshi take kallo. Har yanzun mamaki suke bata. Ta maida dubanta kan gashin shi. Yanayin askin shi na kara bata mamaki tun jiya.

Ya wani aske gefe da gefe da bayan kan. A tsakiyar kan nan gashin yake yayi wani coil.

Tsaye yai yana kallon yanda idanuwanta ke yawo a fuskarshi zuwa kanshi. Hakan na mishi dadi. Kula tai da yaga tana kallon shi.

Ta sadda kanta kasa a kunyace. Yai murmushi. Ya karasa ya zauna kan kafet. Daga jiya zuwa yau cin abinci akan kafet na mishi dadi.

Yanzun din ma shinkafar taci. Dan ta dazun ma ta mata dadi ta sha ruwa ta koma saman kujera tana kallon yanda fu.ad ke cin abincin shi.

Yana gamawa ya bude ledar wayarsu ya dauko tashi ya bude. Ya ciro charger din da wayar daman tun acan shi ya saka sim dinshi a ciki.

Dan saida ma aka kunnata yai tura abubuwan shi yai wiping dayar kamun ya basu. Ta safiyya ya dauko. Ya bude ya saka mata sim din daya siyo mata da memory card sannan yasa battery din ya mika mata.

"Ga wayarki"

Ware idanuwa tai da mamaki. Ta sa hannu biyu ta karba tana jujjuya wayar. Daga ganin kyanta tasan tana da tsada sosai.

"Nikam wannan wayar ai tayi tsada"

Dariya yai. Ta dora da fadin.

"Gashi ban iya ba...."

"Karki damu zan koya miki. Kawo asa a charge kamun mu tashi kwanciya ya cika"

Bashi tai. Yasaka da tashi da tata din ya koma kan kujera ya zauna suna kallon arewa24 tare.

Shi kadai yake kallon wata drama data burgeshi ta dadin kowa. Ita kam safiyya tai shiru.

Ba kallon take ba tunanin rayuwa take. Oh da yanzun tana gidan ado. Ta wani bangaren wani sanyi taji. Dan bata son ado ko kadan.

Ko kamun kaddara ta hadata da fu.ad dinma bata son shi. Tsanar shi ta karu ne bayan haduwarta da fu.ad.

Inda wani yace mata rayuwarta zata juye haka ba zata taba yarda ba. Kalli kudin fu.ad. Ita kanta tasan ko da wasa bata dace dashi ba.

Sam bataji yana mata magana ba. Lumshe idanuwanshi yai. Baya son tunanin nan da take yi. Inda take zaune ya koma.

Bataki karasowarshi ba sai fuskarta data ji ya tallaba cikin hannayenshi. Da sauri tasa nata hannuwan kan nashi tana rikewa dam.

Hannuwanta yabi da kallo yana jin su har cikin ranshi. Idanuwanshi ya maida cikin nata. Fuskarshi babu walwala yace mata.

"Bana son tunanin nan sofi. Bana so ko kadan"

Wani rauni taji na daban. Hawayen dake cikin idanuwanta suka zubo. Cikin rawar murya tace.

"Kayi hakuri. Zan bari. Ina kewar su inna ne kawai......."

"Shhhhhh......"

Ya fadi yana goge mata fuska da hannayenshi. Amman kaman kofar fitowar wasu hawayen yake bude mata.

Gani yai bazai mishi ba. Rikota mata hannuwa yai ya matso da ita gab dashi. Rungumota yai jikinshi yana lallashi.

Kuka tai sosai. Sai da yaji tayi luf sannan a hankali yace.

"Komai zaiyi dai dai. Komai zai gyaru in shaa Allah"

Kai ta daga masa a hankali take kokarin zamewa daga jikinshi dan nata jikin duk ya mutu. Sakinta yai ya mike ya duba wayoyinsu.

Duk sun cika. Cirewa yai ya karasa wajen safiyya ya kama hannunta yaja ta sukayi bedroom din tare. Sai da tahau ya ja mata blanket din tukunna ya zagaya ya zauna kaman jiya.

Wayarta ya kunna yace mata.

"Matso kigani"

Duk da tana jinta wani iri bai hanata yin abinda yace ba. Bayan duk wannan nan da nan din dayake da ita gudun zama kusa dashi shine karshen abinda zatai.

Ko ba komai ba haram bane tasan da hakan. Kawai ji take jikinta ba daukar wani dumi ga zuciyarta ba dokawa sosai.

Shima matsawa tai sosai kusa da ita. A hankali yake nuna mata yanda zatai da wayar. Inda zata danna tai kira da sauran abubuwa.

Mika mata yayi. A hankali take tabawa kaman wadda hannunta zai makale a ciki. Mamaki wayar take bata.

Data taba sai taga komai ya wuce. Muryarta dauke da excitement tace masa.

"Ana daukar hoto?"

"Sosai ma. Kawo ki gani"

Mika masa wayar tai. Hannunta ya rike wayar na ciki. Yasa dayan hannunshi yakai camera din ya kunna flasher ya danna.

"Kai..... "

Ta fadi cike da mamakin ganin yanda ya dauki hoton dakin. Yanayinta na bashi dariya. Sakar mata hannu yai yana kallonta.

Mikewa yai zaune kafafuwanta mike kan gadon. Daukar hoton ta sake yi taga yayi. Tai wata dariya.

Saita fu.ad tai da camera din ta dauka. Hasken kawai yagani. Ya zaro Idanuwa ta Sakina daukar shi.

Dariya yake yakai Hannu yana karewa.

"Sofi daina daukata duk fuskata tayi maiko kina mun hoto......"

Tana dariya ta sake daukar wani. Hannuwanta ya riko duka yana janyota ta fada kan cikinshi.

Dariyar da take yi ta dauke lokaci daya. Wani numfashi taja daya sa shi fadin.

"Fuck me...."

Cikin kanshi. Idanuwanshi ya kafa mata. Gabaki daya jikinta ya mutu. A hankali muryarta kamar wadda aka shaqe tace.

"Yi hakuri na daina"

Saida yai gyaran murya dan jinta take ta makale. Shi kanshi abinda yake ji na neman kwacewa daga control dinshi.

"Tsayawa zakiyi in rama"

Ganin ya sake mata hannu yasa ta mike daga jikinshi tana maida numfashi ko zuciyarta zata dan rage gudun da takeyi.

Hasken wayarshi taji cikin Idanuwanta yana daukarta hoto. Dariya tayi ya Sake daukar wani.

Pillow ta janyo tana karewa a dole bata so yana daukarta. Ci gaba yai da dauka yana jinshi wani so light.

Gajiya tai ta cire pillow din ta kwanta. Sannan ya sauke wayar yana duba hotunan daya dauketa.

Juyowa yai ya nuna mata yaga bacci ya dauketa. Dariya yai. Ya zare wayar dake hannunta ya ajiye gefe. Kanta ya daga ya gyara mata kwanciya.

Ya kara ja mata blanket din sannan yakai hannunshi ya kashe musu wutar dakin. Addu.a yai musu su dukansu sannan ya kwanta da wani kwanciyar hankali na daban a zuciyarshi.

Hannunta ya laluba ta cikin blanket din ya rike dam. Lumshe idanuwanshi yai a hankali ya ce.

"I love you sofi...........!"

Kamun wani bacci mai nauyi ya dauke shi.

*#TeamAS*
[7/1, 7:33 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:13 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 23
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


23

Ya riga safiyya tashi. Sai da yai wanka yai alwala ya fita mota ya dauko kayan da zai sake.

Baya son ya ajiye su cikin gidan sam. Dan in son samun shi ne kar su wuce yau ba su koma gidansu ba.

Komawa bedroom din yayi. Yanda safiyya ke baccin ta hankali kwance yasa yaji kaman kar ya tashe ta.

Gefenta ya zauna ya zuba mata idanuwa. Baya son hannunshi yakai jikinta saboda alwalar dayake da ita.

Gefen gadon yadan bubbuga. Ta bude idanuwanta cike da bacci ta sauke su akanshi.

"sofi sallah"

Ya fadi da murmushi yana mikewa daga kan gadon. Saida ta gama addu.ar tashi daga bacci sannan ta mike zaune.

Tana kallon fu.ad ya fice daga dakin. Dafe kai tadanyi. Duk da yau zuciyarta a shirye take da tashi tare da fu.ad bai hanata jin wani iri ba.

Ga kewar su inna. Mikewa tai ta shiga bandaki. Saida ta fara yin brush da fu.ad ya ajiye mata sannan tai alwala.

Sallah ta gabatar. Addu.a sosai tayi bayan ta idar na Allah ya bama su inna zuciyar yafe mata ya kuma basu zama mai inganci da fu.ad.

Dan shi kadai yasan me yake shimfide kan titin kaddarar daya dora su. Tana nan zaune kan kafet fu.ad ya dawo daga masallaci.

"Ina kwana"

Ta gaishe dashi. Cikin fuska ya kalleta.

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah. Kaifa?"

Dariya yadanyi.

"Kina kusa dani. Komai dai dai sofi"

Kunya taji ta sadda kanta kasa. Fu.ad din ya dora da fadin.

"Yau ba wanka da ruwan sanyi ko?"

Dariya tai.

"Yanzun ma zanyi wankan ai"

Kallonta yai yana wani ware idanuwa. 'Yana da kyau' zuciyarta ta fadi.

Sake dakuna fuska yai alamar bai gane abinda ke sata murmushi ba.

Hakan ta karanta yasata mikewa. Kamun tai wani abu maganar zuci ta kubce mata.

"Kana da kyau"

Hannu tasa ta rufe baki. Dariya ta bashi sosai. Da gudu ta nufi bandaki ta rufo yana fadin.

"Sofi dawo nan......zaki fito ki maimaita mun in sake ji"

Dariyarta ya jiyo daga bandakin. Fita yai daga dakin saboda baya son abinda tunanin tana wanka yake mishi.

Yau akwai abubuwa da yawa da yake sonyi. Ga ball yana son zuwa amman yasan bashida wani lokaci. Dole zai hakura zuwa gobe in komai yai settle.

Yana nan kwance bacci ya dauke shi.

*

Wata doguwar rigar ta sake mayarwa. So take ta wanke kayayyakinta amman ta rasa sabulun wanki. Wankan ma da wani abune cikin roba da batasan ko meye ba.

Sai kamshi ga kumfa yana dashi. Fita falo tayi ta duba fu.ad bata ganshi ba. Daya daga cikin bedroom din ta tura.

Don tana bukatar sabulun wanki. Ganinshi tai kwance yana bacci. Har zata fice taja masa kofar idanuwanta suka hango kayan kan wani table.

Karasawa tai cikin dakin. Kayanshi ne duk daya cire daga zuwansu zuwa yau. Dauko su tayi ta ja masa kofar a hankali.

Bandakin bedroom din ta koma. Dabara ta fado mata. Tunda dai babu bokiti. Ruwa ta tara a bathtub din ta zuba shower gel din ciki ta kada yai kumfa.

Kayan fu.ad ta soma wankewa. Duk rigunan ma fararene. Harda singlet dinshi da boxers. Saida ta wankesu ta dauraye.

Sannan ta wanke jeans din da three quarter daban ta dauraye suma. Nata ta wanke da tazo dasu da hijab dinta sannan ta wanke dogayen rigunan datai amfani dasu.

Karfen data gani cikin bandakin ta shiga yarfe kayan tana shanyawa akai.

*

Ya jima da tashi. Wata kasala dai yake ji yasa shi kin sakkowa daga kan gadon. Wayarshi ya lalubo ya duba agogo.

Takwas da rabi. Mikewa yai safiyya na manne a zuciyarshi. Baisan sanda bacci ya dauke shi ba.

Daga dan hutawa kamun gari yadan waye ya fita ya siyo musu abin da zasuyi breakfast da.

A hankali kaman wanda bayaso ya sakko daga kan gadon. Haka ya tako zuwa falo bao ganta ba.

Bedroom din da yasan tana can ya nufa. Da sallama ya tura kofar ya shiga.

Tana cikin bandaki tsaye tana yarfe hijab dinta. Da mamaki yace

"Sofi? Me kike yi haka?"

Da sauri ta juyo. Ta lumshe idanuwanta ta bude su akanshi. Tsoro yadan bata saboda bata ji shigowarshi ba.

A sanyaye tace.

"Allah yasa dai banyi barna ba. Babu sabulun wanki da wannan ruwan nayi"

Girgiza kai fu.ad yai yana sauke numfashi sannan yace.

"Banna bama karama ba"

Rau rau tayi da idanuwa. Shisa da kaman tabari ya tashi daga bacci. Dan dai tana zaune ba wani aikinyi.

Amman tasan wannan ruwan da tsada da ganinshi. Murya na rawa tace

"Kayi hakuri dan Allah. Wallahi babu sabulu shisa. Bansan da tsada ba amman......."

Katse ta yai da fadin.

"Damn the shower gel. Bannar da kikamun kinsa hannunki a ruwa.

Kina so kiyi mura ne sofi? Duka yaushe zazzabi ya sake ki? Kinzo kina wani wanki"

Ajiyar zuciya ta sauke. Ta dauka barna tayi.

"Ba abinda zaimun. Wankin ma ba yawa"

Karasawa yai sosai bandakin. Zaro idanuwa yayi ganin harda kayanshi.

"Haba mana sofi. Harda kayana fa. Za azo a wanke ai"

Shiru tayi dan batasan me zata ce masa ba. Ita a wajenta wannan ba wani aiki bane. Ko dauda kayan basu dashi.

Yanda fu.ad din yakeyi saikace ta wanke kaya kala talatin ba kwarori ba. Hijab dinta ta karasa shanyawa.

Karasawa yai gefen gado ya zauna yana wani bata fuska. Baiji dadin ganin tayi wanki ba sam.

Kawai jiyai bayason tayi kowanne aiki. Yafison komai ayi mata. Ta zauna ta huta karta wahala.

Fitowa tai daga bandakin. Muryarshi can kasa yace.

"Bana son ki kara yin wanki sofi. Bana so"

A sanyaye tace.

"Na daina. Kayi hakuri"

Kai ya daga mata kawai ya mike yana fadin.

"Bara in siyo mana abinda zamuci"

"Allah ya tsare hanya"

Ta ce. Ya amsa da amin yana ficewa. Gyara zama tayi ta sauke numfashi. Kawai yanda yanayinshi yayi bataji dadi ba.

Duk kokarin da yake akanta. Karshen abinda zatayi shine ta bata mishi rai.

*

Take away ne yayo musu na kwai da dankalin turawa sai yoghurt. A bedroom sukai zamansu suka ci.

Sannan yace mata zai fita ya karasa siyayyar komai. Saida suka je falo ya kunna mata kallo sannan yai pecking dinta a goshi ya fice.

Ganin maigadi ya bude masa gate ya tuna mishi da cewar yana bukatar maigadi shima. Da kuma yar aiki.

Kasa yai da glass din

Please Login or Register in order to submit comment