Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma damu ba. Abin ya bashi mamaki.

Cike da tunani barkatai yahau titi.

****

Kwankwasa kofa sukaji suna zaune suna hira ita da Nana. Ware idanuwa Nana tai kan safiyya.

"Turo"

Safiyya ta fadi. Dan ta dauka yusra ce. Fu.ad ne ga mamakinta. Kallon shi take.

Sanye yake da jeans blue. Sai wata hoodie fara kal. Hular na kanshi. Yaja hannun hoodie din zuwa gwiwar hannun shi.

Yai wani irin kyau. Sallama yai. Ta amsa a sanyaye saboda hakan take jin jikinta ya mata wani irin sanyi.

Da gudu Nana ta tashi taje ta rukunkume fu.ad tana fadin.

"Dady. Inata missing dinka"

Dagota yai jikinshi. Ya sumbaci kuncinta duka biyun sannan yace.

"Princess ta sha kyau yau. Inata missing dinki nima"

Wayarshi ya lalubo cikin aljihunshi da dayan hannun. Dayan na rike da Nana dake faman murmushi bakinta yaki rufuwa.

Camera din ya bude ya daga ya dauke su. Sake rike shi nana tayi yana ta daukarsu.

Sumbatarta yai a kunci yana daukar su a haka. Hannunshi mai wayar yasa yana nuna mata alamar tai kissing dinshi a kumatu.

"Dady zan shafa maka lipstick"

Daquna fuska yai dake nuna bai damu ba hadi da juya mata idanuwanshi. Dariya tayi.

Ta zagaya hannayenta duka biyun a wuyanshi sannan ta sumbaci kumatunshi ya dauke su wajen kala goma. Sannan ya kalli safiyya.

Saurin kauda kai tayi. Dan ta fahimta sarai. Babu abinda zai ja mata daukar hoto dashi. Nana ya kalla yana wani matse lips waje daya.

"Mumy please kizo muyi"

Ta fadi. Ware mata idanuwa safiyya tayi alamar bata so. Nana tace.

"Dady zaka dauki pic da mumy"

"Banda matsala princess. Duk abinda kike so"

Fu.ad ya fadi yana karasa maganar da kallon safiyya. Harara ta watsa mishi wato itace take da matsala.

Mikewa tai. Sai lokacin ya samu damar kallonta sosai. Numfashin shi yaji yana masa wasa wajen fita da komawa.

Ta canza in all the good ways. Kyanta ya fito fiye da da. Kallon da yake mata yasa ta tuna babu mayafi a jikinta. Kallon shi tai taga idanuwan nana basa kanta.

Yanda iya shi kadai zai gani ya fahimta tace

"Bana son kallo"

Daga mata gira yai duka biyun. Ta taka ta karasa inda yake. Duk da bayanshi ta tsaya bai hana kamshin da take ya cika mishi hanci ba.

Mamaki yake sosai saboda collection din smart din daya daina amfani dasu ne saboda suna tuna mishi ita. Shine a jikinta.

Sake baza hanci yai kamshin na tuna masa abubuwa da yawa. Dakyar ya iya daga camera din ya dauke su kala biyu duka safiyya na bayanshi ta wani hade fuska.

Zai dauki na ukkun aka kwankwasa kofar. Tasan wannan karin yusra ce. Da kanta taje ta bude kofar. Aikam yusra ce sanye da doguwar riga fara. Tai rolling farin mayafi. Hannunta dauke da wata jaka.

Da fara.a suka gaisa da safiyya ta shigo ciki. Gaishe da fu.ad tayi ya amsa a dakile. Saida ta zauna sannan tai ma Nana murmushi hadi da fadin.

"Nana"

Murmushin Nana ta mayar mata.

"Ina kwana"

Ta fadi yusra ta amsa. Yarinyar ta mata kyau. Basai an fada mata ba tasan mutumin dake rike da ita shine babanta. Dan ga kamanni nan.

"Gata tazo Nana"

Fu.ad Nana ta kalla.

"Dady sauke ni"

Kallonta yai yace.

"Wacece?"

"Yar jarida"

Lokaci daya idanuwanshi sukai wani irin haske. Sake rike nana yai gam. Baya son yarshi a TV balle duniya ta kalle masa yarinya.

Baya son labarinshi a kunnuwan kowa. Baya son duniya ta kalle shi da matsayin uban daya kasa yima yar shi komai. Saida yaji Nana nason sauka da kanta sannan ya ajiyeta.

Yusra ya kalla.

"Bana son ki dauki komai nata....."

Ya maida hankalinshi kan safiyya

"Ina son magana dake"

A dake tace.

"Seriously fu.ad? Kabari mugama tukunna"

Kara bata mishi rai take

"Ki taso ku muyi a gabanta"

Mikewa tai. Kitchen ya nufa tsabar masifa ce fal a cikinshi. Abin yaso ya bata dariya.

Suna karasawa tace.

"Saika cemun yunwa kakeji drama king"

Dariya tayi saboda yanda yake mata kallon rashin fahimta. Lokaci daya yaji ya sake kulewa. Ya ma zama wani game wajenta.

"kitchen ka kawo mu. Me kake tunanin zan dauka?"

Sai lokacin ya kulla. Yadan dakuna fuska dan ya kasa ganin abin dariya cikin lamarin.

"Bana son yarinyata a TV. Bana son kowa ya kalleta da kalar me zai fada.

Saboda me ma zaki kirasu?"

Hannunta ta dora kan kugu tana kallon ikon Allah.

"Na dauka tun a asibiti na fada maka tana son magana dasu. Kace bakomai"

Kallonta yake dake fassara ashe baki da hankali?

"Na dauka kingane dan a gabanta ne. Bakiga idanuwana ba?"

Yar dariya tai cike da takaici.

"Ka fada mata da kanka"

"Bana son ince kar tayi abinda take so"

Ya fadi. Bata san randa fu.ad zai bar son kanshi ba. Bata ga rana ba. Shi bashida zuciyar dazai ce ma Nana aa sai ita kenan.

Kaman daga sama suka ji ance.

"Dady"

Da sauri suka kalli Nana a tare. Idanuwanta kan fu.ad a kafe tace.

"Na hakura tunda baka so"

Tsugunnawa yai. Ya sa hannu ya tallabi fuskar Nana cikin hannuwanshi.

"Princess bana son maganganun mutane ne. Bana son ki zama abin kallo da magana.

Bana son kowa ya miki kallon something weak and fragile. You are my daughter Nana.

Zuciyata ba zata iya dauka ba"

Tallaban hannuwanshi dake fuskarta tayi da nata. Murmushi tai mishi.

"Ba saika mun bayani ba. Bansan me yasa nake son magana da ita ba. Na hakura tunda baka so"

Sunbatar goshinta yayi.

"Thank you princess"

Dariya tai mishi.

"Kubarni in fada mata da kaina"

Kamun suce wani abu da gudu ta fice daga kitchen din. Suka kalli juna shida safiyya suna sauke numfashi a tare.

*

Zama tai gefen yusra.

"Anty bazan yi ba. Dady baya so. Na hakura. Amman ki tambayeni ko me kike so zan amsa miki indai ba zaki saka a TV ba"

Murmushi yusra tayi mata. Duk yanda take son tasa labarin yarinyar nan baikai yanda ta fahimci babanta ba. Ko itace ba zata so yarta a TV ba sam.

Hira suka danyi kadan da yusra. Tana tambayarta ya akai taga babanta duk ta amsa ta. Rokon Nana tayi sukai hoto tare.

Sannan ta mike ta kalli su fu.ad dake bayansu.

"Nagode sosai. Allah ya bata lafiya"

Suka amsa da amin. Har kofa safiyya ta rakata sannan ta dawo. Fu.ad baice mata komai ba. Wajen Nana yaje ya zauna.

"Zan je unguwa. Idan na dawo zamuje tare dake okay?"

Kai ta daga hadi da fadin.

"A dawo lafiya. Love you"

Wani kumburi zuciyarshi tayi. Saida yai hugging Nana yanajin kaman ya mayar da ita cikinshi kar wani abu ya sameta sannan ya ce.

"Love you more"

Dariyar nan da yake so tai mishi cikin kunnuwanshi sannan ya saketa. Mikewa yai ya sauke idanuwanshi kan safiyya.

Wani irin kallo yake ma safiyya data kasa fahimtarshi. Muryarshi ya saukar sosai. Idanuwanshi na cikin nata yace.

"Zan dai dai ta komai. Zan cika miki wannan alkawarin"

Lumshe idanuwanta tayi. Tana jin yanda yake fama mata tsofin ciwukanta. Hular rigarshi ya cire daga kanshi ya kalli Nana yai mata murmushi sannan ya nufi hanyar kofa.

*

Yana fita daga gidan lukman na kiranshi a waya. Dagawa yai hadi da fadin.

"Lukman....."

"Fu.ad ya ne? Ya nana?"

Saida yai jim ya amsa da.

"Okay i guess"

Yanajin yanda lukman ya sauke numfashi kamun yace.

"Kana gidan ne?"

Girgiza kai yai kaman yana ganin shi.

"Ina hanyar bichi. Bankai da fita daga cikin gari ba tukunna dai. Em' gonna make it right. Duk abinda na bata"

"About time fu.ad. Daka fadamun da munje tare"

Murmushi yai. Har ranshi yaji dadin maganar lukman din sai dai wannan abune da zaiyi shi kadai. Baya son kowa ya tayashi.

Yagaji da yanda tun yarinta lukman da haneef ke share hanyar daya bata. Wannan karin zaiyi komai. Laifin shine shi kadai kuma shi kadai zai gyara.

"Nagode lukman. Nagode fiye da yanda zan iya fada. Kuskure na ne. Ina son gyarawa da kaina."

"Hmm. Be safe. Just be safe fu.ad"

Yar dariya yai.

"Yeah whatever. Ka shafamun kan junior......"

Sai yanzun ya tuna. Yadan daki steering motar hadi da fadin.

"Em such a bad uncle. Nama junior alkawari lukman ko ka tunamun"

Dariya kawai lukman yai ya kashe wayar. Ajiyeta yai gefe ya mayar da hankalin shi sosai kan tukin da yake yi.

Daya dawo anjima zai cika alkawarin nan.

****

Tura dakin ikram yai da sallama. Tana kwance kan gadon ta tana karatun Qur.an. Saida takai ayar sannan ta amsa shi.

Qur.an din hannunta ta rufe ta ajiye gefe a hankali. Da dan murmushi tace.

"Pa?"

Dan tasan ta musu saida safe tun kamun isha.i. Bakuma al.adarshi bane shigowa dakinta babu wani dalili.

Gefen gadon ya zauna. Yana rasa ta inda zai fara.

"Lafiya dai ko? Ina mumy?"

Ganin yanda duk ta rikice yasa shi saurin cewa.

"Komai lafiya ikram. Kawai ina son magana dake ne"

Gyara zama tayi kan gadon.

"Alright. Ina ji"

Saida ya sauke numfashi sannan yace.

"Zan kara aure ikram. An sa rana yau. Nan da wata biyu"

Shiru tayi tana kara tauna maganar shi na tsayin mintina biyar kamun tace.

"Why?"

Tana tsare shi da idanuwa. Dan daga kafadar shi yai.

"Just......"

"Kana son mumy?"

Kai ya daga mata. Dan tana jin tsoro. Taga yanda kishiyar maman kawarta jawahir take basu wahala. In tana bata labari takan gode ma Allah da babansu bai kara mata ba.

Sosai ta kalle shi. Tsoro cike fal da idanuwanta. Hannunta ya kamo. Yana son ya fara zame ma yayanshi aboki da zasu iya magana ba tare da shakka ba.

"Kinsan zaki iya fadamun komai ko? I am your dad. Your best friend ikram"

Kai ta jinjina.

"Kawai ina jin tsoro. I love mum sosai. Kaima haka. What if ta kwace mana kai"

Da wani irin yanayi yace.

"Babu wanda zai kwace muku ni in shaa Allah. Babu abinda zai canza. You will be there for me dake da mum inki dasu umar.

Ba zaku bari kowa ya kwace ni ba.?"

Fuskarta babu wasa tace.

"Sosai ma. Promise komai bazai canza ba?"

Saida yai jim sannan yace.

"In shaa Allah. Kumin addu.a Allah ya tabbar mun da alkhairi. Shi nake bukata"

Sai lokacin tai mishi murmushi. Yasan da wuya ta sake cewa wani abu. Ikram bamai yawan magana bace ba.

Har yakai kofa tace.

"Pa....."

Ya juyo ya kalleta.

"Thank you"

Murmushi jabir yayi. Ya jinjina mata kai kawai ya fita yana ja mata kofar. Numfashi ya sauke yana juya idanuwanshi.

"So awkward...."

Ya fadi kasa kasa. Ya na takawa zuwa dakin su. Jana ya samu inda yabarta tana dudduba wasu takardu.

Idanuwanshi taji suna mata yawo ta dago ta kalle shi sai raba idanuwa yake. Dariya ya bata.

"Ya dai?"

Dan rausayar dakai yayi.

"Kin banni da ikram ni kadai ko?"

Dariya ta sake yi.

"Baga shi harka gama ba. Nace maka ba wani wahala"

Karasawa yai ya zauna kusa da ita. Takardun dake hannunta ya karba ya ajiye gefe daya.

"Lokaci na ne yanzun. A taimakamun a ajiye office work din nan jana"

Shagwabe fuska tayi.

"Nabar ma ayna ai"

Ware idanuwa yai.

"Tun yanzun?"

Dan murmushi tai cike da kishi. Har daci take ji a wuyanta. Ya karance ta tsafa dan haka ya matsa daf da ita sosai.

"Naki ne ni jana. Kinsan wannan ko?"

Daga mishi kai ta iya yi. Duk soyayyar nan a kwanaki sittin da wata zata dinga rabata. Addu.ar ta ci gaba dayi a zuciyarta.

Saida taji wata nutsuwa ta saukar mata sannan ta fara nuna ma jabir kalar soyayyar da take mishi......!

****

Kanshi tsaye gidan su safiyya ya wuce da wani irin yanayi na nasara da yake saka shi murmushi shi kadai.

Da sallama ya shiga. Nana na zaune tana kallon cartoon network. Ta ruga tqna mishi sannu da zuwa.

Safiyya ta fito daga daki.

"Sannu da dawowa"

Ta fadi. Kai yadan daga mata. Yana kallonta hadi dayin murmushi. Komai nasu ya kusan gyaruwa. Zai bata mamaki bada jimawa ba.

"Zamu fita da Nana"

Ya fadi. Kai ta daga mishi. Da gudu nana ta ruga daki ta dauko hijab dinta da takalmi ta dawo.

Safiyya tace.

"Nana ko goodbye?"

Da sauri tana dariya ta karasa wajen safiyya ta rungumeta. Sakinta tai ta juya tana fadin.

"Sai mun dawo"

"Allah ya tsare hanya"

Safiyya ta fadi. Fu.ad ya kamq hannun nana cikin nashi suka fita. Wata ajiyar zuciya ta sauke gidan na mata wani irin shiru.

*

Yana tuqi ne nana tace.

"Dady in rokeka?"

Kai ya daga mata. Dan bayajin akwai abinda zata nema indai zai iya dazai kasa yi mata.

"Ka auri mumy. Dan Allah ku koma aurenku!"

Wani shiru yaji cikin kanshi. Zuciyarshi na tsayuwar wucin gadi kamun ta ci gaba da aiki.

"Please. Tana bukatarka in bana nan. Kana bukatarta in bana nan. Tana sonka sosai. Dan Allah karka ce No"

Zufa ke keto mishi ta ko ina. Nana na tambayarshi abu mai girma. Tana tambayarshi abinda bayajin zai iya.

Bashida abinda zai ba safiyya. Bashi da farin cikin da take bukata. Parking yai gefe yana maida numfashi.

"Nana...."

Ya kira sunanta yana rasa me zai ce. Ta ina zai fara fada mata sakin safiyya dayai yanci ne ya bata. Farin cikin daba zai iya bata vane ya barta ta samu da wani.

Idanuwan nana cike da hawaye tace.

"Ka daina sonta ko?"

Da sauri ya girgiza kanshi. Son da yake ma safiyya bazai taba misaltuwa ba. Sonta yasa yabarta. *Akan so*n da yake mata ya zabi ya barta inhar zata samu farin cikin da shi bazai iya bata ba.

Hawayen da suka zubo mata tasa hannu ta goge. Tana son tagansu sun koma. Tana son hakan fiye da yanda take son lafiyarta.

"Please dady. Bana so inbar mumy ita kadai. Bana so...... Bata da kowa......"

Kuka Nana take yi. Jinshi yake har cikin tsokarshi. Kamo Nana yayi yana tallabar fuskarta yana goge mata hawayenta da sauri.

Dan shi kanshi da zai samu wanda zaima kuka yi zaiyi.

"Ina sonta Nana..... I love your mum. Ita kadai zan so har abada....."

Cikin kuka nana tace.

"To ka aureta"

Cikin rasa yanda zai ce ma Nana yasa shi fadin.

"Banda abinda zan bata. Banda komai dazan bata"

Rike hannuwanshi Nana tayi.

"In tana sonka a haka fa? Zaka aure ta?"

Kai ya daga ma Nana. Son da yake ma safiyya mai girma ne. Yasan bata son shi ta tsane shi yanzun. Ta kuma kara tunda bashida abinda zai bata.

Yaji dadi saboda zai bata mamaki zuwa gobe da safe in shaa Allah. Zai bata abinda yasan tana so. Abinda yai mata sanadin salwantarshi.

"Zan ma mumy magana. Kaji"

Kai ya daga mata. Ya goge mata fuska hadi da fadin.

"Bana son kukanki. In kuma na sake gani zan fasa"

Da sauri tasa hannu ta sake goge fuskarta.

"Na daina. Kayi hakuri bazan sake ba"

Murmushi yai.

"Good girl..... Zauna sosai to"

Gyara zamanta tai ya tayar da motar suna tafiya..........!

*#TeamAS*
[7/9, 1:22 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/9, 1:23 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 40
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


40

*"Turomun number dinta inba mamanta mamaki"* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚
*Wannan maganar make my day.*

*Ayna.u mardiyya (dimples) Allah yabarki da masu kaunarki. Ba saina fadi matsayinki a wajena ba. #ICDWAWFEY*

*Biebie Isa Allah yabar zumunci. You know #AnaTare*

*To the readers ina godiya da yanda kuke biye dani. Da hakuri da rashin update akan lokaci. ILYA😍*

Kwance yake shi kadai a daki. Ya kira number din nuriyya a kashe. Yau kwana uku kenan da rasuwar nawaf.

Bai samu yai magana da ita ba. Yana son yaji yanda take. Shi kanshi dayaga Nawaf na mintina rasuwar ta bala.in tsaya mishi a rai.

Lumshe idanuwanshi yai. Kaman hoton film rayuwarsu ta wani lokaci ta fado mishi.

*Years Back*

Kitson da ake mata tace a barshi haka, zata zo gobe da Safe a k'arasa mata.

Mai kitso tace

"Maman Farhan da kin bari an gama, saura Kadan a gama."

Tace

"Aa, yanzu maigidana ya shaida min yana kan hanyar gida, kar yazo gida ya iske ba na nan, zan dai dawo gobe"

Da sauri ta saka Mayafinta ta fito daga saloon din ta ja Motarta ta nufi gidanta da ke k'asan layi.

**

Zaune yake kan Motarshi, Fuskar shi ba annuri d'aure kamar Lion da ya kwana hudu be ci Abinci ba, tana shiga Gidan Gabanta ya yanke ya fadi ganin shi.

K'irkiro Murmushi tayi ta k'arasa gunshi,

"Welcome Dear you are home Already"

mugun kallon da ya jefeta dashi ne ya sa hanjin cikinta kururuwa.

"Daga gidan Uban wa Kike?"

Dankwalin kanta ta zame, Baki na rawa tace

"daga gidan kitso nake, kuma ai na maka text"

Gashin kanta ya damk'a, Ta sandara ihu Zafi ya sa ta kiran sunanshi,

"Muhammad Don Allah kayi hakuri, you are hurting me"

Be saurareta ba ya jata har Parlo inda ya yasar da ita a k'asa kamar Gabage.

Kuka takeyi sosai, ga Zafin kitson ga kuma na jan Gashi, Belt ya shiga Zarowa, ta san dawan Garin, tayi sauri tashi zata gudu ya sa k'afa ya tande ta, ta fadi k'asa, wani ihu ta saka.

Muhammad be ji tausayin ta ba haka ya shiga lafta mata wannan belt din kamar Allah ya aiko shi sai da ya gaji don kanshi kafin ya barta.

****

Straight Islamiyyar su Farhana ya nufa, ya ci ko sa'a sun tashi, dama abunda baya so ya zo yayi ta jira, da gudu ta k'araso gunshi tana fadin

"YaYa Farhan, ina ta jiranka"

Murmushi yayi yace

"Sorry muje Gida"

*

Tana jin dawowar su tayi saurin tashi don shiga dakinta, bata kai ga shiga dakin ba taji Farhana a jikinta.

"Mummy, me ya sameki?"

Rasa abun da zata ce mata tayi, ta fara kame kame.

Daga nesa Farhan ya k'are mata kallo, fuskarta duk bruises ya matso kusa da ita a nutse yace da k'anwarshi;

"Farhana je ki cire Uniform dinki"

Ba gardama ta dauki jakkarta tayi daki.

"Mummy, Daddy ya sake dukkan ki ko?"

Ta shiga girgiza kai ta rasa ansar da zata bashi, a fusace yace

"For how long zaki cigaba da enduring dukkan da yake miki?"

Jiki a sanyaye tace

"Kayi hakuri, zai bari"

A fusace yace:

"Till when zai daina dukkanki? Sai kin aurar damu? Mummy shekaru na Sha takwas, tun ina Shekara 4 nake ganin yana Abusing dinki, Allah kadai yasan tsawon lokacin da kikayi cikin wannan halin, Mummy put an end to this please.

Ki kai shi K'ara, befi k'arfin Hukuma ba, akwai Agency na Women Rights and Child Abuse, he's been Abusing us all for quiet a Long time, Mummy i hate seeing you like this"

Murmushin takaicin tayi tace

"Farhan i cannot, Ni ba kowa bace face Marainiyar Allah, banda kowa, banda wanda zai tsaya mun, Kai da k'anwarka ne Farinciki na, i can endure all this for you, so everything is going to be fine"

Takaici ya hana Farhan magana, ya saba jin wannan maganar daga gun Mahaifiyarsa, haushi ya sa shi fita daga Parlorn.

****

Wayarshi datai ringing ta katse mishi tunanin da yakeyi. Ya dauko ya duba. Dan guntun tsaki yaja ganin bakowa bane yan mtn ne saikace zasu bashi wata tsiyar.

Mikewa yai da wani nauyi a zuciyarshi ganin lokacin sallah yayi. Yana son yin wani abu wa matan dake cikin rayuwar domestic abuse saidai baisan ta inda zai fara ba.

Da wannan tunanin a zuciyarshi ya fita masallaci.

****

Yana rike da hannu nana da sallama suka shiga babban falon a tare. Momma ta amsa su.

Kwace hannunta Nana tayi daga cikin na fu.ad ta ruga da gudu tana fadin.

"Granny...."

Da fara.a momma ta riko Nana jikinta. Fu.ad kam yarinyar dake zaune kasa tana wasa yake kallo. Ta mishi kyau ba kadan ba.

Karasawa yai yasa hannu ya dauketa ya kwantar da ita kan kafadarshi. Ya hada fuskarshi da ta yarinyar yana rocking dinsu a hankali.

Yanda tai luf yake jin abin har cikin zuciyarshi. Lumshe idanuwanshi yayi yana jin kamshin yar yarinyar da baisan na menene ba. Powder ce ko turare.

Muryarshi can kasa yace.

"Momma babyn wacece?"

Kallon shi take yanda ya lumshe ido yana jijjigasu shida babyn. Ta kalli nana dake jikinta. Gaba daya sai tausayinshi ya cika mata zuciya.

Da sanyin murya tace.

"Arfat. Yar pha.iza ce"

Bude idanuwanshi yai yana ware su kan momma. Zuciyarshi tai wata irin dokawa. Sauko yarinyar yai daga kafadarshi data soma bacci.

Hakan yasata fara kuka. Kallonta yake sosai. Yar fara ga wasu kumatu. Jijjigata yake taki yin shiru. Ya bude baki zai magana.

Pha.iza ta fito daga hanyar daya san ta kitchen ce hannunta dauke da feeder tana daure murfin.

Tsayawa tai cak. Idanuwanta kan fu.ad. Shima kallonta yake. Wani miyau ya hadiya. Zaka rantse arfat tasan akwai wani abu dake faruwa daya fi kukan da take muhimmanci.

Shiru tayi. Kallonta yake. Kaman ba pha.izar daya sani ba. Tayi girma sosai. Bude baki yai.

"Pha.iza....."

Baima san maganar bata fito ba. Ita dake tsaye daga nesa zata iya karantar sunanta akan labban shi duk da bai fito ba.

Shekaru sha daya. Ya sa kafa ya fice yabarsu batare daya juyo ba. Wani abu ya tsaya mata a wuya. Mikewa momma tayi ta kama hannun Nana.

"Zo muje....."

Ba musu Nana ta mike tana rike da hannun momma. Dan sam bata kuka da pha.iza ba suka nufi sashin momma a tare.

A hankali pha.iza take takowa tana jin yanda idanuwanta ke cika da hawayen dataqi bari su zubo. Karasowa inda yake tayi.

Hannu ta mika zata karbi Arfat. Ga mamakinsu yarinyar kara makale fu.ad tayi. Dariya yai yana bude idanuwanshi.

Kallon arfat pha.iza tayi ta daquna fuska.

"Baki san uncle dinki bai damu damu ba kike makale shi ko?"

Wani abu yaji a kirjinshi da maganarta.

"Pha.iza......"

Ya fadi da wani irin yanayi. Cikin idanuwa ta kalle shi.

"Shekara sha daya. Ko ka dauka weeks ne?"

Ya rasa me zaice mata. Arfat ta karbe daga hannunshi data soma kuka. Ta samu waje kan kujera ta zauna tana lallashinta.

Gabanta ya tsugunna yana wani dafe kai.

"Pha.iza please......"

Sai lokacin hawayen da take rikewa suka zubo. Muryarta dauke da dacin da take ji tace.

"Da sai wani cikin mu ya rasu zaka dawo? Baka taba tunanin ka waiwaye mu ba ko sau daya. Why? Laifin da mukai maka yai girma har haka?

Da bro lukman bai kiraka ba ba zaka taba dawowa ba ko? Ka manta kana da yan uwa? Ko baka sonmu baka tunanin mu muna sonka? Bro ko......."

Hannunta ya kama da sauri yana katse mata abinda tai niyyar fadi. Idanuwanshi ya sauke cikin nata. Yana so taga nadamar dake cikinsu.

Yana so taga yanda girman kaunarsu yake a zuciyarshi kamun yace.

"Ni mai kuskure ne pha.iza banda abinda zan fada. Ki yarda dani da ina da iko dana koma shekaru sha daya na gyara komai.

Ina biyan kuskuren dana aikata da zuciyata pha.iza............ki yafemun"

Hannunta tasa tana goge fuskarta. Ta riga ta yafe masa. Duk da za.a dauki lokaci kamun ta daina jin dacin laifin shi.

Jin tayi shiru ya sashi fadin.

"Ki yafemun. Bance ki manta ba......."

Katse shi tai da fadin.

"Na yafe maka bro. Ka yafemun nima. Dana kiraka. Dukkanmu muna da laifi.

Yan uwantaka abune mai girma. Zumunci abune dabai kamata bacin rai yai sanadin yankewarshi ba.

Daya daga cikinmu ya kamata ya ajiye bacin rai ya nemi daya. Duk bamuyi ba.

Yanzun sai mu duba gaba....."

Kai yake jinjina mata alamar duk yaji abinda taje dan yaji din. Baya son ko tunanin abindq zaisa ya nisance su yanzun.

Komawa yai kan kujera gefen pha.iza ya zauna. Arfat take kallo.

"She is so cute......"

Mika mishi ita tayi. Ya karbeta. Hannuwanta tasa tana sake goge fuskarta. Da dan murmushi tace.

"Sauran will love to meet you"

Dariya fu.ad yayi.

"Su nawa?"

"Su hudu...."

Ware idanuwa yayi sukai dariya gabaki daya.

"Akwai kabir da muke kira (Amir) yana da sunan in-law dina. Sai Yassar da yasir. Ridwan sai arfat gata nan"

Da mamaki fu.ad ke kallonta.

"Kina da twins?"

Ta daga mishi kai. Lokaci daya fuskarshi ta canza. Muryarshi can kasa yace

"Nayi missing abubuwa da yawa......"

Yanda yai maganar ya taba mata zuciya ba kadan ba. Cikin taushin murya tace.

"Make sure bakai missing wani abu ba nan gaba okay?"

"Damn right....."

Dariya sukai gabaki daya. Lokacin da suka ji sallama. Su duka suka daga kansu zuwa hanyar shigowa falon.

Hassan ne. Yana ganin fu.ad yai baya zai koma. Da sauri fu.ad ya mikama pha.iza arfat yana binshi da gudu.

"Hassan......."

Bai tsaya ba. Asalima kara sauri yai batare daya juyo ba. Yana jin takun fu.ad din ya karaso inda yake. Hannu yasa kan kafadarshi yana juyo dashi.

Fuskar hassan babu annuri yace.

"Sannunka"

Yana sake juyawa. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Ya sake juyo da hassan. A kufule yace.

"Hit me! Yell at me in kana so. Buh' for goodness sake ka daina mun kaman baka taba sani na ba"

Ture shi hassan yayi da hannuwa duka biyun hadi da fadin.

"Da gaske baka so? Baka son inayin kaman ban sanka ba? Kasa kafa kabarmu? Ko ance ba zuciya a kirjinmu kaman kaine?

Saboda me zaka dawo kasan ba zama zakai ba. Ka tuna mana yanda muke kaunarka ka sake tafiya ko me?"

Har wani huci hassan yake. Komai na rayuwarshi. Tun tasowarshi duk wani burinshi bai wuce na ya zama kaman fu.ad ba.

Shi kadai yasan abinda tafiyar fu.ad tai mishi. Tai musu gabaki daya. Sosai fu.ad ya kalle shi.

"Babu inda zani hassan. Ba inda zan sake zuwa. Kaima ka yafemun mana ko zan ji sauqi a rayuwata"

Wani kallo hassan yake mishi cike da rashin yarda kamun ya juya. Hannunshi fu.ad ya riko.

"Hassan....."

Juyowa yai ya na zame hannunshi daga na fu.ad murya a gajiye yace.

"Ka kyaleni. Please kabarni kawai....."

Girgiza kai fu.ad yake. Yaga abinda kyaliya tai mishi a baya baya fatan tarihi ya sake maimaita kanshi.

"Ba zaka iya yafemun ba hassan? Zan fahimceka in ba zaka iya ba? Ka fadamun cikin idanuwa sai in sani.

Ka fadamun ba zaka iya sake bani

Please Login or Register in order to submit comment