Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taki kallonshi. Kan gado ya zauna. Ta ajiye man a kasa ta na tsugunnawa. Man ta dangwala tana murza shi cikin hannunta.

Kanta a kasa yake amman tanajin idanuwan fu.ad kafe a kanta da suke sata jin wani iri.

Kafarshinta kama kaman yaro ta murza mishi man tun daga kwaurinshi zuwa kasa. Sake dangwalowa tayi ta dan daga kafarshi tana hada tafin hannunta da tafin kafarshi ya wani motsa yatsun kafar.

Sake kokarin murzawa tai ya janye kafar yana dariya. Baya so komai ya taba mishi tafin kafa. Wajen is ticklish.

Kula tayi tai dayar kafar taba janyo ta. Hannun tasa da sauri jikin tafin kafarshi tana wasa da ita. Ba shiri ya mike yana dariya hadi da murza kafafun jikin kafet.

Kaman yana son goge abinda tabari. Dan har lokacin yana jin hannuwanta jiki. Gaba daya tsikar jikinshi tai wani irin tashi.

Dariya sosai safiyya take yi. Ta dauka ita kadai ke jin wannan abin. Shi a kafa ne. Ita wuyanta ne bata so a taba sam.

"Ka zauna a karasa"

Dakuna fuska yai yana daga mata kafada daya.

"Bana so....."

Kallonta yake da murmushi a fuskarshi. Dariya take mishi sosai sosai. Towel din dake kugunshi yasa hannu ya cire.

Wani ihu ta saki tana rufe idanuwanta. Dariya ya kama yi sosai harda rike ciki.

"O. M. G sofi da boxers dina fa....."

Mikewa tai da gudu tabar dakin. Har yasa kaya dariya yake. Man ya karasa shafawa a hannuwanshi kawai sannan ya fita.

Tana zaune falo tana raba idanuwa. Yana kallonta ya sake kwashewa da dariya. Tai kasa da kanta tana murmushi.

Mikewa tayi tana nufar dining. Yabi ta ya zauna cikinshi har wata kara yake.

Muryarshi babu wasa yace mata.

"Sofi wayai girki?"

Tun kamun ma ta bude warmers din. Kallon fuskarshi tayi.

"Ni na dafa maka"

Kai ya dan daga kawai. Yunwa ke cin shi tun shigowarshi. Ganin safiyya dine ma yasa ya share.

Tana budewa wani kamshi ya doki hancin shi. Plate ta dauka ta zuba mishi farar shinkafar data dafa da ruwan kwakwa.

Sannan ta samu dan wajen zuba miya ta zuba masa miyar data sha ganye da naman kaji.

Ta saka cokali a ciki ta tura gabanshina nutse. Wani dan kwanon ta dauka ta zuba dambun naman da tayi a ciki ta ajiye masa a gefe.

Sannan ta dauki cups guda biyu daya ta zuba masa ruwa daya ta zuba masa exotic. Tunda ya tafi suna nan shaqe da fridge.

Ba damunta sukayi ba. Ba sha take yi ba. Komawa tayi ta zauna ta zuba mishi idanuwan. A sanyaye tace.

"Ban san me kafi so ba. Bansan ko kana cin wannan ba"

Cokalin yasa ya dibi miyar ya zuba a gefe yadan cakuda. Ci yayi yadanyi jim.

Gabanta faduwa yake yi kar ko abincin bai mishi ba. Dagowa yai ya sakar mata wabi murmushi mai taushi hadi da fadin.

"Yamun dadi sofi. Kin iya girki haka bakya mun?"

Yar dariya tayi tace.

"Da baka nan na koya. Anty laurat da su khadija suke koyamun"

Sosai yake cin abincin. Takuma ji dadin ganin yana cin abinda ta girka da hannuwanta.

Kallonshi take. Yanayin yanda yake cin abinci na burgeta tun randa ta fara gani.

Zaka rantse yanayin dan cin abinci kawai aka halitta mishi shi. A nutse yake yi fuskarshi na nuna yanda abincin ke mishi dadi.

Dagowa yai ya kalleta.

"Ke ba zakici ba?"

Ya bukata. Kai ta girgiza mishi. Nutsuwa tayi tana kallonshi. Tsaf ya cinye plate din data zuba mishi ya na fadin.

"Sofi karamun......"

Kara mishin tayi. Baima cinye ba yasha lemon kadan ya shanye ruwan yana hamdala.

Kallonta yai.

"Thank you"

Ta rasa me yasa turancin shi ke mata daban. A kunyace tace.

"Don't mention"

Ware idanuwanshi yai a kanta. Tasa hannu tana rufe fuska hadi da yin dariya.

"Bude fuskarki sofi. Naji dadi fa. Come on bude fuskarki ki kalle ni"

A hankali ta sauke hannunta. Ta kalle shi. Yanayin dake fuskarshi na kara mata kwarin gwiwar yi masa magana da iya turancin datai kokarin ji.

"You look good"

Dariya yai cike da jin dadi. Mikewa yai ya zagaya inda take ya dan tsugunna ya sumbace ta.

"I fucking love you sofi"

Dan dakuna fuska tayi hadi da fadin.

"Meye fucking?"

Dan sosa kai yayi maimakon amsa tambayarta sai cayai.

"Taso kiga....."

Yana kama hannunta zuwa falon. Zama sukai tare ya janyo akwatin ya bude.

Wani dan box ya fiddo. Zobe ne me kyau sosai silver. Ya zaro shi daga dan gidanshi.

"Banma san ko zai zauna a yatsunki ba...."

Hannunta ya kamo cikin nashi yasa zoben a yatsanta na biyu yadanyi yawa. Na tsakiyar ya saka. Cif ya zauna.

Kallon zoben da takeyi. Da F a tsakiya. Wani box din ya dauko ya bude ya mika mata. Iri dayane saidai na shi S ne a jiki.

Kaman yanda yai mata tai mishi. Ta kama hannunshi ta saka zoben. Saidai na shi yatsa na biyu ya zauna.

"Nagode....."

Hannunta ya kamo ya sumbaci inda zoben take. Itama mayar mishi da abinda yai mata tayi.

Dariya yayi ya fito da wasu takalma pink da sukai mishi kyau ya mika mata. Itama kyau sukai mata sosai ma.

Mikewa tayi tana ture kunyar dake addabarta gefe ta manna mishi sumba a kunci sannan ta koma ta zauna.

Ya kasa daina murmushi. Cikin kanshi yake godema duk wanda ya canza sofin shi haka.

Mayar da akwatin yai ya rufe san sauran kayan dake ciki na su pha.iza ne. Kallon safiyya yai.

"Ina son zuwa gida amman ban gaji da ganinki ba wallahi"

Dariya tai mishi.

"Kaje nasan suma sunyi kewarka. Ina nan me zan dafa maka?"

Hannu yakai ya tallabi fuskarta. Sannan yace

"Akwai sauran abincin dana ci dazun?"

Ta daga mishi kai. Ya lumshe idanuwa kamun ya bude su akanta.

"Zan taho da fruits. Shi zan sake ci"

Da mamaki take kallonshi tasan da yawan mutane basa son sake maimaita kalar abinci a rana daya. Tace

"Shi kaci yanzun fa. Ka fada wallahi indai na iya zan dafa maka"

Mikewa yai yana murmushi.

"Banda matsala da cin kalar abinci daya kullum indai zai mun maganin yunwa balle kuma inya mun dadi"

Fu.ad bazai gaji da bata mamaki ba. Har kofa ta rakashi. Ya sumbace ta sannan ta tafi.

Kwanonin daya bata ta dauke daga wajen tai kitchen dasu. Bata wani jira mama indo ba tunda ba yawane dasu ba ta wanke.

****

Yana shiga gida husssaina ta fara ganinshi da gudu ta karaso ta rike shi.

"Inata kiranka baya zuwa ashe ka dawo ne.

Kaga nace anty pha.iza takai ni gidanka ta kiya"

Dakuna fuska fu.ad yayi.

"Pha.iza bata kyauta ba. Kibarni da ita. Ni zanzo dakaina in dauke ki muje"

Rike da hannun hussaina data karbi akwatin daya shigo dashi ta na tayashi ja suka shiga cikin gida.

Gaisawa sukai da momma take tambayar safiyya.

"Momma ina haneef?"

Da fara.a tace.

"Yana wajen aiki"

Zaro idanuwa fu.ad yayi. Sau nawa sukai waya da haneef bai fada mishi ya fara aiki ba. Muryarshi a sanyaye yace.

"Bai fadamun ba"

Kallon wanna matsalarku ce momma tai mishi. Dan bai shafeta ba.

"Nayi kewar abbah sosai"

A tausashe momma tace mishi.

"Yana dakin shi. Shima jiya ya dawo"

Bai ko bari ta rufe baki ba ya mike. Tana kiranshi ko juyowa baiba ya wuce da saurin shi.

Kwankwasa kofar dakin yayi. Muryar abba ta amsa shi da.

"Shigo......."

Sallama yayi ya tura kofar. Hade rai abbah yai da yaga fu.ad ne.

Karasawa fu.ad yayi ya tsugunna gaban abbah. Idanuwanshi ya sauke cikin na abbah.

"Wallahi na gane laifina abbah. Ya zanga albarka in kana fushi dani?

Abbah baka daga wayata. Baka son ganina. Laifin danai bazai yafu bane?"

Ganin abbah yai shiru yasa shi riko hannunshi da nashi duka biyun. Cikin ido yake kallonshi yana so yaga nadamar kuskuren daya aikata cikin idanuwanshi.

"Abbah ka yafemun dan Allah. Bazan sake ba. Kamun kowanne hukunci banda nisantata"

Gaba daya yanayinshi ya karyarma da abbah zuciya. A sanyaye yace.

"Allah yai maka albarka"

Da sauri fu.ad ya amsa da.

"Amin abbah nagode. Nagode Allah ya kara girma"

Hira suka danyi da abbah sannan ya mishi sallama ya fito. Momma ya kalla da fara.a a fuskarshi.

"Ni da abbah mun shirya"

Numfashi momma ta sauke. Taji dadi sosai. Dan har tsoron yin maganar fu.ad take a gaban abban.

Wucewa yai da fadin.

"Momma na tafi. Ina so inga lukman sannan in wuce gida"

Ta amsa da

"To shike nan. A kula da Allah"

"In shaa Allah"

Fu.ad ya fadi yana ficewa.

*

Ya jima sosai wajen lukman suna hira. Har yamma likis kamun ya mike da fadin.

"Bara in wuce kar magrib tayi"

Lukman yace.

"Ya kamata kuwa. Kabarta ita kadai"

Wayarshi ya zaro yana danne danne. Kamun ya kalli lukman yace.

"Sofi tana fadamun kana zuwa duba ta. Bana son in fada ta cikin waya......."

Kallon shi lukman yayi yana katse shi da.

"Wallahi karka fara. Karka sona fu.ad"

Wayarshi taji text ya shigo. Ya dauko ta kan gado. A kufule ya kalli fu.ad.

"Meye hakan?"

Dan ganin kudi ne ya tura mishi a account.

"Biyana zakai kome?"

Da sauri yake girgiza kai.

"Bazan taba iya biyanka karamcinka ba lukman.

An biyani kudina ne na wannan watan. Nayi laifi dan na bama dan uwana?"

Sauke numfashi lukman yayi. Fu.ad din ya dora da.

"In baka karba zanji kaman ban isa in maka kyauta ba"

"Ba haka bane fu.ad abin ne yana yawa"

Girgiza kai fu.ad yayi.

"Zami bata duk randa ka sake cemun ba maka abu yayi yawa lukman. Kaman kana zagin abokantakarmu ne.

Zakaimun fin haka in kaine a matsayina"

Jim lukman yadanyi kamun yace

"Hakane. Nagode....."

Dakuna fuska fu.ad yayi.

"Emotional freak....."

Dariya sukai su duka sannan sukai sallama fu.ad din ya fice. Haneef ya kira bugu daya ya dauka da yin sallama.

Amsa shi fu.ad yayi ya dora da.

"Nazo baka nan"

"Yanzun na shigo gida. Ruwa kawai na watsa momma ke fadamun"

"To bari in karaso gidan yanzun nima na fito gidan su lukman"

Amsa shi haneef yai da fadin.

"Alright...."

Sannan ya kashe wayar.

*

"Ashe ka fara zuwa aiki baka fadamun ba"

Da mamaki haneef yace.

"Seriously?"

Yana kallon fu.ad cikin fuska. Langabe kai yayi.

"Eh mana. Ko addu.a ai zan maka dai"

Tabe baki haneef yayi sannan yace.

"Yaushe rabon daka fadamun zakai abu? Bari nai inka dawo kaji"

Sake langabe fuska fu.ad yayi.

"Na dauka we are good fa. Maganar ta wuce"

"Nace bata wuce bane?"

Sosai fu.ad ta kalle shi.

"Please. Bazan sake bafa. Kaga abbah ma ya daina mun fushi. Wallahi naji daban da momma ta fadamun."

Sauke numfashi haneef yai yana kallon fu.ad.

"Shikenan. Muje muyi sallah naji an kira"

Tare suka wuce masallaci suna taba hira. Ana idar da sallah fu.ad yace gida zaije dan ya bar sofi tun dazun.

****

Wata mika fu.ad yayi kan gadon hadi da yamutsa fuska yana kallon safiyya dake kwance gefenshi.

"Gajiya ko?"

Ta tambaye shi cike da kulawa. Hade sauran space din daya rage tayi tsakaninsu. Yana dora hannunshi kan nata. Kanshi ya mayar kan pillow dinta yana hade goshinsu.

Wani tabare mata fuskarshi yayi.

"Sosai fa. Jikina duka ciwo"

Hannu tasa ta dangwale mishi hanci ya rike hannun yana sumbatarshi. Lokaci daya ya shiga nuna mata yanda yai kewarta.

Mamaki da sonta ne ya shige shi jin yanda ta saki jiki dashi take tarbar duk wata soyayyar shi da yake son nuna mata.

Kaman wanda aka dokama guduma akai yai tsaye cik. Fuskarshi safiyya ta taba dan jin yai tsaye kaman wanda ya sandare.

Muryarshi can kasan makoshi yace mata.

"I love you"

Yana gyara mata kwanciya a jikinshi. Bata amsa shi ba. Shiru kawai tayi yanajin har bacci ya dauke ta.

Dafe goshin shi yai. Sam bai zaci zata sake dashi haka ba. Ba a shirye yake ba. Baya son kuskure daya ya ja masa dana sani.

Yai hakurin kusan watanni biyu da dori. Kwana daya bazai canza komai ba. Sosai yai bincike kan tsarin iyali komawarshi.

Saidai gaba daya wanda ya danganci bangaren mata akwai complications da side effects da yawa. Bazai taba iya risking din sofi ba.

Duk da akwai yiwuwar taki samun matsalar da ake samu. Amman bazai iya daukar wannan ba. In kuma aka samu matsalar bazai taba yafe ma kanshi ba.

Zai amfani da protection a yanzun kamun ya samu yanda yake so yai maganin matsalar gabaki daya. Dakyar ya samu wani wahalallen bacci yai gaba dashi.

**

Sallar asuba ya dawo ya dawo ya sake kayan jikinshi ya fita jogging. Yana dawowa ya samu safiyya a kitchen.

Ta baya ya rungumeta. Hannuwanshi ta kama tanajin yanda zuciyarshi ke dokawa da sauri da sauri da fitar numfa shin shi.

"Sofi baki shirya ba?"

Ya fadi yana wani maida numfashi. Kwan da take soyawa ta saki hannunshi yana rungume da ita ta baya ta juya.

Sannan tace.

"Shirin me?"

"Makaranta...."

Ya amsa cikin kunnenta. Murmushi tayi tana kokarin janye jikinta daga rikon dayai mata. Sake makata yai yana fadin.

"Um um fa....."

Sauke frying fan din tayi daga kan wuta ta ajiye gefe tana rike hannayenshi sannan ta juya suka fuskanci juna.

"Ka kyaleni in karasa aikina"

Cikin idanuwa yake kallonta.

"Bakwai saura sofi. Zaki makara"

Murmushi tai mishi.

"babu inda zani."

Ware idanuwa yai.

"Saboda me?"

"Saboda kana gida. Saboda kwana yau kadai nake da ita tare dakai. Sai kuma bayan wata nawa kace?"

Yanda ta karasa maganar ya sashi langabe mata fuska.

"Haba mana sofi kina magana kaman laifina ne"

Ajiyar zuciya ta sauke.

"Kwana biyune sunyi kadan"

Saida ya sumbace ta sannan ya hada goshin shi da nata.

"Nasani sofi. Bake kadai ba"

Sumbatar shi tai a goshi.

"Kaje kai wanka inyi aikina"

Wani shagwabe fuska yayi.

"Ni an koreni"

Dariya tayi kawai. Ta juya ta ci gaba da aikinta. Ta baya ya hada kumatunta dana shi sannan ya wuce.

Ta lumshe idanuwanta soyayyarshi na shigarta. Har ranta kwana biyu ya mata kadan.

*

Wajen goma na suna zaune a falo ta dauki wayarta. Game din BASE da khadija ta tura mata ta nutsu tanayi.

Wayar taji fu.ad ya fisge ta kalle shi fuskarta a shagwabe.

"Kaban wayata"

"Me kike yi"

Hannu takai ta karbe wayarta kamun tace.

"Wani game ne mai dadi khadija ta tura min"

Komawa yai kan kujerar da take. Mai guda daya ce dan haka ya dagata ya zauna sannan ya zaunar da ita kan cinyarshi.

Game din suka dinga yi tare. Ya kai hannu zai danna ta ture hannunshi.

"Bafa nan bane. Saika sa an kamani......"

Dangwala wa yai ta mintsine shi.

"ouuchh sofi da zafi fa....."

Wayarshi tahau ringing. Safiyya ta mika hannu ta dauko mishi. Lukman ne.

Tana game dinta ya gama wayarshi. Matse ta yai jikinshi sannan yace.

"Fita zanyi"

Hade rai tayi.

"Haba mana. Dan Allah kace ma lukman yabarmun kai yau"

Dariya tabashi. Wayar ya mika mata.

"Kira shi ki fada mishi"

Murmushi tayi a kunyace tana tashi daga jikinshi. Mikewa yai shima yai cupping fuskarta.

"I love you......"

"I love you too"

Ta amsa shi. Sannan ya fice.

Hijab dinta ta dauko ta zagaya ta kira mama indo dan ta tayata ko gyara cefane ne dan girkin yai mata sauri.

*

"Wai me zakayi a chemist?"

Lukman ya tambaya cike da rashin fahimta. Narrowing idanuwan shi fu.ad yayi yana fadin.

"Ba kyau yawan bincike"

Lukman da hankalin shi ke kan tukin da yake yadan juyo ya kalli fu.ad din kamun ya ci gaba da abinda yake.

"Allah ko?"

Shiru yai ya kyale shi. Bakin wani babban chemist lukman yai parking. Ya kalli fu.ad yace.

"Kai sauri......."

Bai dai kula shi ba ya fice daga motar. Yakai minti sha biyar sannan ya dawo.

Sosai lukman ke nazarin shi ya zauna kanshi a kasa yana wasa da zoben hannunshi.

"Fu.ad?..."

Ya kira cike da alamar tambaya. Dago fuskar shi da tai wani ja yai ya kalli lukman sannan ya maida hankalinshi kan zoben shi.

"Ba damuwar ka bane. Just drop it......"

Kallonshi lukman ya ci gaba dayi.

"Me ka siyo?"

Ya bukata. Dago idanuwa fu.ad yai ya kalle shi cikin ido.

"Banda kai please. Ni da kudina mai chemist da mutanen dake ciki sun bi ni da kallon dake screaming dan iska.

Saboda me mutane ba zasu bar abinda bai shafesu bane?"

Rike baki lukman yai yana wani jan numfashi. Cike da tashin hankali yace.

"Tell me ba abinda nake tunani bane fu.ad......"

Katse shi yai da fadin.

"I don't want kids. Fucking shut up....."

"Fu.ad?"

A kufule yace.

"Fucking stay out of this lukman"

Shima a kufule yace.

"Fine......."

Ya fisgi motar. Lumshe idanuwa fu.ad yayi. Baisan sanda yan nigeria zasu canza ba. Shiga abinda babu ruwansu...........!"

*#TeamAS*
[7/5, 11:18 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:20 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 28
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


28

*Thank you for all your support and comments. Daga yanzun akan kowacce chapter zan saka sakkoni ukku da sunayen wanda suka turo mun su. Meye naku ra.ayin AKAN SO?*

Tana yin sallar la.asar ta koma falo ta zauna tana kallo. Tun da suka ci abinci fu.ad ya sake fita.

Anan ya sameta da ledoji a hannu da safiyya tasan kayan ciye ciye ne a ciki. Tun tana mamakin kalar cin abincin fu.ad harta daina.

Kasa ya zauna yana ajiye komai. Robobin ice cream ya fiddo guda hudu ya ajiye. Ya kalli safiyya da idanuwanta ke kanshi.

"Sakko mu sha"

Batai mishi musu ba ta sakko. Ta dauko roba daya ta bude. Harya soma koya mata yan ciye ciyen nan.
Bata ko shanye rabi ba ta ajiye.

Dan yanzun tana iya fara tari. Sam basa shiri da sanyi.

"Kinyi me kenan?"

Fu.ad ya bukata yana ajiye robar daya shanye ya dauki wata ya bude.

"Na koshi. Saika yi mura ko?"

Ware idanuwanshi yai akanta. Yana ci gaba da shan ice cream dinshi. Hankalinshi ya maida kan film din da take kallo na hausa zuri.a.

"Wai duk yaran ta ne wannan ukkun?"

Ya tambayi safiyya ta amsa shi da.

"Eh mana. Abin sha.awa ko"

Yamutsa fuska yai hadi da fadin.

"OH-OH ..."

Da mamaki take kallonshi.

"Basu burgeka ba kenan"

Girgiza mata kai yayi.

"Ko kadan...."

Dariya ya bata.

"Inka haifi naka zasu burgeka"

Ware idanuwanshi yai akanta yana fadin.

"Wa? A duniyarmu babu yara sofi. Daga ni sai ke"

Dariya ya bata. Fu.ad akwai zolaya ta fadi a ranta bata ce mishi komai ba har akai magrib. Sannan ya fice masallaci.

Kwashe robobin ice cream din daya shanye guda uku tayi. Sauran nata kuma ta bude fridge ta saka in mama indo ta shigo ta bata.

Kamun ta wuce dakinta.

*

A kwance ta fito daga wanka ta same shi kan gadon yana danne danne da wayarta.

Zama tayi gefenshi. Ya dago ya kalle ta. Sosai yakai kanshi jikinta yana shakar kamshinta.

"Wanne irin turaruka ne wannan?"

Dariya tadanyi.

"Bansan sunan su ba. Anty fatima ta hadomun randa mukaje gidan tan nan"

Sake shaka yai yana wani sauke numfashi. Sun mishi dadi sosai.

"Nima a shafamun"

Hannunta ta goga a fuskarshi.

"Gashi nan"

Rike hannun yai.

"Wayau ko sofi?"

Boye kanta tai a jikinshi. Sumbatarta yai sannan ya jata sosai suka koma tsakiyar gadon.

Wata irin soyayyarshi yake nuna mata mai tsayawa a zuciya. Dakyar yakai hannu jikin switch din ya kashe musu kwan..........."

*

"I love you so so much sofi. Nagode...."

Yake fadi yana sumbatar kanta. Ya wani riketa kamar za.a kwace mishi ita.

Tun dazun ya fadi mata i love you din nan yafi a kirga. Ta kasa cewa komai saboda sanshi da kunyarshi da suka hadar mata.

"Tashi muyi wanka sofi"

Wani makalewa tai a jikinshi. Ko ina ciwo yake mata. Kai ta girgiza mishi. Yar dariya yayi ya mike daga kan gadon.

Wanka ya shiga yayi. Yana fitowa ya goge jikinshi ya hau kan gadon. Dago ta yayi.

Sam taki hada idanuwa dashi. Cik ya dauketa yana nufar toilet da ita.

"Zan iya zuwa da kaina........"

Cikin fuska ya kalleta.

"Kin tabbata?"

Kai ta daga mishi. Bai sauketa ba sai daya kaita cikin bandakin sannan ya janyo mata kofar a hankaki.

Wardrobe ya bude ya dauko mata wata rigar baccin. A hankali ya tura bandakin ya mika mata.

Sanda ta fito bakin kofar bandakin ta same shi a tsaye. Hannunta ya kama suka hau gadon tare.

Riketa yai jikinshi. Wata sumba mai taushi ya manna mata. Hannu tasa tana ture shi.

"Yi hakuri....."

Ya fadi yana sauke numfashi.
"Bacci nake ji......"

Ta karasa muryarta can kasa. Gyara musu blanket yai yai musu addu.a. Cikin sanyin murya yaji ta sake rike shi tace.

"Tun daga ranar daka shigo rayuwata komai ya dai daita..."

Da murmushi a fuskarshi ya ce.

"Bansan akwai abinda na rasa ba a tawa rayuwar saida na mallake ki..."

Sumbatarta yai a goshi yana jin numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa kamun shima wani ni.imtaccen bacci yai gaba da shi.

*

Sama sama yake jin kiran asuba. Dakyar ya iya tashi ya shiga bandaki yai alwala. Bai tashi sofi ba dan yasan shiya hana mata baccin kirki jiya.

Ya fita masallaci. Yai mamaki daya dawo ya sameta zaune kan kafet. Karasawa yai ya zauna gefe.

A kunyace tace mishi.

"Ina kwana...."

Dan rankwafa kanshi yai yana kallon fuskarta da taki dagowa.

"Sofi ki kalle ni mana"

Hannu ma tasa ta rufe fuskarta tana dariya. Janta yai jikinshi.

"Nagaji da kunyar nan fa. Taso kiga in kara rage ta......."

Ture shi tai tana dariya.

"Kin tashi lafiya? Ba inda ke miki ciwo ko?"

Kai ta daga mishi alamar babu. Tana mikewa.

"Ina zaki?"

"Zan shiga kitchen in hada maka abinda zaka karya kamun ka tafi"

Riko mata hannu yayi.

"Sai sha goma zan fita. Barshi sofi mudan kwanta. Anjima in na shirya zan siyo mana wani abu"

Hamma tayi kamun tace.

"Allah ya kaimu"

Kallonta yake sosai. Yana sake gode ma Allah daya bashi ita.

"Bacci ko?"

Ya bukata. Daga mishi kai tayi alamar eh. Mikewa yai ya kama hijab dinta ya cire ya ajiye gefe daya yana fadin.

"Kuma hakuri zaimun saboda na fishi bukatarki"

Murmushi tayi tana sadda kanta kasa. Hannunshi ya dora saman kafadunta yana mata wani irin kallo.

"Say mi' name sofi. Ina son ji akan lips dinki"

Murmushin dai ta sake yi. Hade space din dake tsakaninsu yayi. Cikin kunne yake gaya mata kalaman da sirri ne tsakaninsu.

Kanta ta boye cikin kirjinshi tana dariya kamun ya soma aika mata sakon da yasa daga shi har ita tsayuwar ta gagare su. Dan haka ya jata kan gadon.....!

*

Takalminshi yake daurawa sofi da comb dinshi a hannu yanajin yanda take yamutsa mishi sumar kanshi da comb din.

A dole taje mishi take tana kokarin kwantar da ita baya. Karasa daura takalmin yai ya riko hannayenta duk yana sauke idanuwanshi cikin nata.

"Kwana biyu sun mun kadan....."

Ta fadi can kasan makoshi. Ya lumshe idanuwa. Tun kamun su hada gado ma kewarta na azabtar dashi ballantana yanzun.

Yasan sai ya fita shiga damuwa. Mikewa yai ya zaro wayarshi daga aljihu.

Kumatunshi ya hada da nata ya daga camera din yana daukarsu hoto. Wani kuma ya rungumota ta baya.

Sannan ya mayar da ita aljihu. Yai cupping fuskarta.

"Tafiyar lokaci ne kawai abinda ke rike ni inhar nabar nan. Saboda nasan da duk mintin dazai wuce da kusantar kwanakin da suka ragemun in sake ganinki"

Hannunta ta dora kan nashi tana kokarin tarbe hawayen fuskarta.

"Banda kallon turawa wanda suka fini kyau....."

Dariya ta bashi ba kadan ba. Yana dariya yace.

"Sofi idanuwana kadai zasu kalle su. Na miki alkawari zuciyata na tare dake komin nisa"

Har ranta ta yarda da maganarshi. Tanajin tsakanin jiya da dare da yau da safe soyayyar daya nuna mata babu shakku a cikinta.

Hannunta ya kama ya dora kan kirjinshi dai dai inda zuciyarshi take.

"Karfin dokawarta zamanki ne a ciki"

Batasan lokacin data cire hannunta ba ta sumbaci inda yabari. Cikin idanuwa ta kalle shi.

"Ina sonka. Ina sonka sosai"

Hugging dinta yai yana jin wani irin emotion da baisan ta yanda zai fara fassara shi ba.

Kofa ta raka shi.

"Allah ya tsaremun kai a duk inda kake. Allah ya bada sa.a ya dawomun dakai lafiya......"

Ta karasa maganar muryarta na rawa. Girgiza mata kai yake. Baya son hawayen dayake gani cikin idanuwanta.

Sumbatarta ya sake yi sosai yana kokarin shanye duk wata damuwa da take ciki.

"Sai munyi waya"

Kai ta daga mishi tana kallo harya fice yai wajen mota inda driver ke jiranshi.

Ajiyar zuciya ta sauke tasa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Sannan ta koma cikin daki ta kwanta.

Kiran fu.ad kawai ta tsaya jira su sake yin sallama kamun wani bacci mai nauyi ya dauke ta cike da mafarkin fu.ad.

****

In tai duba yanda kwanaki suke wucewa suna zama satika. Yanda satika ke wucewa zuwa watanni abin har mamaki yake bata.

Wai yanzun har sunyi watanni bakwai suna cikin na takwas da fu.ad.

Kusancin su na bata mamaki sosai. Dan ji take yi kamar sunyi shekaru ne ba watanni ba. Banda kewar su inna da take manne zuciyarta tana tunasar da ita abinda suka rasa na cikar farin cikinsu.

Zata iya rantsewa babu matar data kaita sa.ar miji. Danma lokaci na musu kadan. Duk da hakan baya hana fu.ad nuna mata doyayarshi.

A watannin nan duk bayan sati takwas yake zuwa yai kwana biyu. A dawowarshi ta biyune ya bude mata account.

Da kanshi suka je ya koya mata yanda zata cire kudi ta ATM wanda bai mata wuya ba saboda ci gaba sosai data samu a bangaren karatu.

Su khadija ke bata shawarar ta tafi account class dan abu biyu zaka dauka daman a aji hudu.

Safiyya art ne da account nata combination din kuma sunga tafi gane calculations.

**

Wannan dawowar ya karanci akwai damuwa tattare da safiyya. Kyaleta yai saida ya nutsu ya huta sannan.

A hankali yace mata.

"Sofi meke damunki?"

Kallonshi tayi a sanyaye ta girgiza kai alamar babu komai.

Tashi yai daga kujerar da yake a koma ya tsugunna gabanta ya kalle ta sosai.

"Wa kike dashi dazai ji damuwarki fiye dani?"

Wasu hawaye masu dumi suka zubo mata. Ware idanuwa fu.ad yai.

"Subahanallah sofi dan Allah menene? Ko na miki wani abu ne?"

Kai ta girgiza mishi alamar a.a. ya koma gefenta ya zauna ya riko hannunta.

"To menene?"

Kallonshi tai wasu hawayen na sake zubo

Please Login or Register in order to submit comment