Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kiran hussaina number dinta a kashe. Na mijinta kuma baya zuwa. I know she is not okay. Inaji a jikina ne kawai"

Murmushi fu.ad yai. Jini daban ne. Bond din dake tsakanin hassan da hussaina yasa yana ji a jikinshi in tana cikin matsala.

"Calm down. Tana asibiti zata haihu ne"

Sauke numfashi hassan yayi.

"Wanne asibiti?"

Fu.ad ya amsa shi da.

"Ban sani ba wallahi. Yanzun anty fatima ta tafi kuma. Buh' momma tace maza basa zuwa.

Ba zasu barka ka shiga ka ganta ba"

Wayarshi yake dannawa da alama anty fatima zai kira hadi da fadin.

"I don't care zan tsaya a waje. Ina son zuwa....."

Wucewa yai yana ficewa daga dakin.

"Hassannnn"

Fu.ad ya kira. Aiko juyowa baiba ya wuce abinshi. Fu.ad yaja numfashi yana girgiza kai. Shi kanshi ya damu. Musamman daya san mata har mutuwa suke wajen haihuwa.

Akwai team mate dinshi da matarshi ta mutu wajen haihuwa. Wani tsoro yake ji har ranshi. Ya dauko wayarshi da shirin kiran anty fatima saiga momma ta fito tana fadin.

"Hussaina ta haihu. Namiji"

Sauke wani numfashi fu.ad yayi da baisan yana rike dashi ba.

"Alhamdulillah. Momma tana lafiya dai ko? Ita da babyn?"

Kai momma ta daga mishi tana murmushi. Kamun nana data fito ta rike mata hannu da fadin.

"Granny muje muga baby din. Ina son babies fa"

Dariya momma tayi.

"Ke da kaninki. Zakuje ku ganshi ni kam ba yau ba"

Shagwabe fuska Nana tayi. Ta kalli fu.ad.

"Dady please"

Murmushi yai.

"Zamuje harda mumynki anjima"

Dariya tayi hadi da fadin.

"Muka dai banda tsofi ko dady"

Ware mata idanuwa yai kamun momma takai hannu taja mata kunnuwa.

"Wayyooo"

Nana ta fadi tana rugawa wajen fu.ad. Dariya kawai yayi.

"Je ki dauko hijab dinki nasan mumynki ta dawo daga aiki. Sai muje muga babyn ko?"

Da gudu ta tashi ta nufi bangaren momma ta dauko hijab dinta. Sallama sukai mata suka wuce abinsu.

*

Indomie da dafaffen kwai suka samu safiyya na zaune tana ci. Zama sukai gefe. Nana tace

"Mumy har ice cream muka je muka sha."

Harararsu tayi saboda bakinta a cike yake da abinci. Saida ta hadiye ta nuna su da fork din dake hannunta.

"Ku biyun nan baku da kirki"

Dafe kirji sukayi a tare suna ware mata idanuwansu masu kala daya.

"Yes baku da kirki. Kunsan bazan ci abinci ba baku ragemun ba ko?"

Langabe fuska Nana tayi. Fu.ad yai saurin cewa.

"Nace Nana ta ajiye miki fa. Tace mu cinye kina cina office"

Kallonshi Nana tayi harda gasping.

"Dady......"

Ware mata idanuwa fu.ad yai dake fassara ko ba ayi hakan ba?

Kallonta ta mayar kan safiyya da ido take rokonta ta fahimta. Dariya safiyya tayi.

"Nasan princess ba zata ci bata tunani ba"

Dakuna fuska fu.ad yayi.

"Me kike nufi?"

Daga mishi kafada tayi alamar duk abinda ya dauka hakan take nufi.

"Mumy wajen baby zamuje. Babyn anty hussaina"

Sosai fara.a ta bayyana kan fuskar safiyya.

"Hussaina ta haihu ne?"

Ta tambayi fu.ad ya daga mata kai.

"Ke mukazo mu tafi muga baby din a tare suna asibiti ma"

"Kai Alhamdulillah. Na koshi ma bara inyi wanka sai mu tafi"

Nana ta sakko kasa ta dauki plate din tana komawa kan kujera dashi.

"Dawo ki ajiyemun abuna in na dawo zan cinye. Ku da kukaci delicious"

Dariya nana tayi tana dibo wa da fork din.

"Dadi bude bakinka muci"

Ture hannunta yayi.

"Um um ke na koshi fa"

"Please.... Pretty please"

Ta fadi tana mishi wani puppy eyes da ya kasa ce ma aa. Bude baki yai ta saka mishi.

Bakinshi a cike yake fadin.

"Nana nakoshi wallahi kici"

Cokali daya tasa a bakinta ta dakuna fuska tana hadiye shi batare data tauna ba ta ajiye plate din saboda yanda taste dinshi yai mata wani iri a baki.

"Kici mana"

Cikin sanyin murya tace.

"Ba yunwa nakeji ba daman"

Kai ya daga mata ba tare da tunanin komai ba. Haka suka zauna suka jira safiyya ta fito suka kama hanya.

Suna hanya ne ya kira anty fatima tace musu suna aminu kano. Safiyya tace ma fu.ad.

"Munje hannunmu na dukan cinya"

Dariya ta bashi.

"Tunanin da nake kenan fa. Ko mu biya baby dream mu siya abu"

Kai ta daga mishi. Haka kuwa sukai baby dream suka fara biyawa suka siya kayan babies masu yawan gaske. Ba yanda baiba su hada kayan safiyya tace aa.

Kowa ya siya da nashi kudin yakai. Itama ai kanwarta ce. Har pha.iza can suka sameta.

Fu.ad ko ta kansu baibi ba idanuwanshi kan hussaina da take ta murmushi. Ya karasa ya zauna gefenta.

"Hey lil sis. Sannu"

Dariya tayi tana kasa da kanta a kunyace. Babyn na hannun anty fatima ta taso tana miko ma fu.ad shi.

Kallonshi yake a hannun anty fatima. Ya mishi kyau sosai. Sai bacci yake. Yatsan shi yasa yadan taba fuskar shi.

"He is so so cute..."

Ya fadi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi.

"Ka karbe shi mana"

Anty fatima ta fadi. Ya girgiza mata kai alamar aa. Ganin shi yake dan kararrami.

Mika mishi shi tayi. Ya ware idanuwa yana bude hannayenshi ya karbe shi. Nana ta taso daga wajen pha.iza tana kokarin hango shi.

Zama fu.ad yayi suna kallon yaron tare. Safiyya ta taso ta karaso wajensu. Mika mata shi fu.ad yayi yana tashi daga wajen ta zauna.

Rocking dinshi take a hankali. Tana murmushi. Fu.ad ya kalleta ya kalli Nana sai yaji wani abu tun daga yatsan kafarshi ya taso yazo dai dai zuciyarshi yayi tsaye.

Da sauri ya fice daga dakin yana doko kofar da dan karfi. Kallon safiyya su anty fatima sukayi sannan suka kalli kofar.

Tashi tayi ta bama anty fatima babyn ta fita tabi fu.ad. Yana tsaye bakin kofa hannayenshi cikin aljihun wandonshi.

"Me hakan yake nufi?"

Safiyya ta bukata. Ya juyo ya zuba mata idanuwanshi.

"Baki gani ba kenan? Sofi bazan iya baki wancen farin cikin ba. You loook so so........."

Kasa karasawa yayi saboda dacin dayake ji har zuciyarshi. Sauke numfashi tayi.

"Ka daina tunanin nan please. Na samu nana koda bamai tsahon kwana bace a duniya naji me akeji.

Na wuce gorin haihuwa har abada. Nasan soyayyar ya'ya wannan kawai kyauta ce mai girma"

Yanayin yanda ta karasa maganar ya mishi wani iri. Karasawa yai batare da damuwa da cewa a asibiti suke ba yai hugging dinta.

"I am so sorry sofi. Ni ya kamata ace ina biyan zunubin kuskuren danayi bawai mu raba tare ba"

Sake matse shi tayi.

"Ni da kai. Ko ka manta ne. Ka dinga hango me mukayi *Akan so* zamu jure wannan in shaa Allah.

Allah yasan damu"

Kissing gefen fuskarta yayi.

"I love you"

"Nasani....."

Kawai ta amsa shi da. Hakan take amsawa duk idan ya fadi i love you din nan tun bayan maida auren su.

Tana jin sonshi. Sake furta mishi zai dauki lokaci. Da alama ya fuskanci hakan.

****

Shagali sosai akayi bayan sunan hussaina. Lokacin fu.ad ya fara gane kan kasuwancin su. Duk da abbah bai fara fita kasa she dashi shigo da kaya ba.

Saidai yabarshi nan shagunan su na cikin kantin kwari. Haka rayuwa tafi gaba da tafiyar musu cike da kauna da zumunci mai ban mamaki har bayan *Wata biyu*............!!!

*#TeamAS*
[7/17, 7:18 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/18, 6:07 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 46
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

46

*A rayuwa bakomai da kake so bane kake samu. Ba komai da katsara bane yake zame maka alkhairi*

*Bakomai da kake ki bane sharri akanka. Lokutta da dama zaka samu jarabta fiye da zatonka. Karka dauki hakan kaman cewar kai kadaine*

*Ka dauka cewa kusancinka da Ubangiji mai girmane shisa ya dora maka ita*

*Ummu sudais. Mjay. Amalus. Hasken annuri. Safiyya galadanchi. Billy galadanchi. Samrah. Hashal anani. Idan mace NAGODE tayi kadan sosai. Kawai #AnaTare*

*TASKAR LUBIEE MAITAFSIR. Wannan page din nakune*

Kanta a kasa tun zamanta wajen. Idan tace batajin zuciyarta kaman zata fado saboda kuna karya take.

Inda wani fraction na zuciyarta na tunanin auren jabir zai fasu yau ga tabbatarshi nan a gaban idanuwanta.

"Fatan zaku bani hadin kai wajen ganin mun zauna lafiya cikin amana da aminci da juna?"

Cewar jabir da idanuwanshi ke yawo akan su duka biyun. Nisawa jana tayi sai lokacin ta dago da kanta ta kuwa sauke idanuwanta cikin na jabir.

Tana karantar farin cikin dake cikinsu da yau ba ita bace sanadin bayyanar shi. Dan murmushi tai mishi ya mayar mata nan take kamun ta maida dubanta ga ayna da kanta yake lillibe tanata wasa da hannayenta.

Sauke numfashi jana tayi saboda yanda wani kishi na ban mamaki yake dibarta. Ganin ga kugun ayna gana jabir. Muryarta a sanyaye tace.

"Bazan maka alkawarin komai ba honey J. Fatana Allah ya bamu hakurin zama da juna ya tabbatar mana da alkhairin dake cikin aurenkun"

"Amin"

Jabir ya amsa yana tabbatar da ya nuna mata godiyarshi a kan fuskarshi. Murmushin dai ta sake mishi tana dorawa da fadin.

"Amarya ga amanar mijina. Allah ya bashi ikon yi mana adalci"

Shiru ayna tayi amman har ranta tana jinjina kokari irin na jana. Batajin zata iya wannan kartin halin. Mikewa jana tayi tana fadin.

"Ango nikam zan barku saida safe ko? Na baku sati hudu aci amarci lafiya"

Ware mata idanuwa jabir yai daya sa ta juya tana nufar hanyar fita daga bangaren ayna din. Muryarshi can kasa yace ma ayna.

"Bara in rakata in dawo"

Kai kawai ta daga mishi. Sosai ta sake ganin kokarin jana yanda taji wani kishi ya turnuke ta dajin maganar raka jana kawai.

Tana fita daga bangaren ta dafa kujerar dake falo tanajin duk jikinta ko ina bari yake yi. Wasu siraran hawaye suka zubo mata.

Hannu tasa ta goge su a fili take furta.

"Allah kabani juriya. Allah ka bani hakuri. Allah kai ka dora mana kishin nan Allah kabani mai sauki......"

Ta baya taji jabir ya rungumeta. Ta lumshe idanuwanta tana sauke numfashi hadi sa shakar kamshin turarukan dake jikinshi.

Kamshin na mata bakunta a hancinta saboda bata saba jinshi a jikinshi ba sam. Komai na mata wani iri.

Sumba ya manna mata gefen kuncinta cikin kunnenta yace.

"Jana sati hudu. Yayi yawa. In ke ba zakiyi kewata ba ni zanyi taki. Saboda me zaki mana haka"

Hawayenta take kokarin mayarwa. Tasa hannu tana cire nashi dake kugunta. Kaman ta tunzura shi daya sake matse ta dam.

"Please you are making this hard honey j. Ka bar yarinya ita kadai kaje abinka sai da safe"

Juyo da ita yai suka fuskanci juna ya dora hannunshi daya kan kafadarta yasa dayan yana dago da habarta idanuwanshi cikin nata.

"Ina sonki. Ina sonki sosai ki rike wannan"

Kai ta daga mishi. Ta manna mishi sumba yar karama a kumatunshi hadi da hugging dinshi. Har ranta takejin wata irin kewarshi taban mamaki.

A hankali ta zame jikinta hadi da fadin.

"Saida safe."

Bata jira amsarshi ba ta juya ta tafi. Dafe kai yayi ta wani bangare daban yana jin zuciyarshi tayi nauyi kamun ya juya ya koma bangaren ayna.

*

Tana karasawa dakinta kan gado ta fada ta saki wani irin kuka zuciyarta nayi kaman zata fashe. Lumshe idanuwanta tayi abinda zuciyarta ke hango mata yasata mikewa babu shiri.

Bandaki ta shiga ta dauro alwala. Salloli ta fara jerowa na farko in za.a yankata bata san me take ba saboda wani irin duhun kishi da take ji.

Wani irin kunci marar misaltuwa. Haka ta ci gaba tanayi hawaye na zubo mata har wata nutsuwa ta soma shigarta.

Yanzun kam a nutse take sallolinta da bata san iya lokacin data dauka tanayi ba. Tana idarwa ta zauna kan daddumar tana sauke ajiyar zuciya.

A hankali taji an turo kofar. Da mamaki ta dago kai tana kallon kofar. Kai ikram ta zuro tana lekowa.

Ido biyu sukai da jana. Hakan yasata dan tsayawa ganin janar na kallonta.

"Kawai zan dubaki ne mumy"

Ikram ta fadi. Wani abu na daban jana taji a zuciyarta. Da hannu tai mata alama ta shigo. Karasowa tai cikin dakin ta zauna gaf da jana.

Hannunta ta kama. Dan dazun ta leqo ta sameta kife kan gado tana kuka.

"Are you okay?"

Kai jana ta daga mata. Muryarta a dakushe tace.

"Bakiyi bacci ba?"

Kai ikram ta girgiza mata.

"Na leko naga kina kuka. Na kasa bacci ne. Dady yana wajenta ko?"

Ganin jana tai shiru yasa ikram tabe baki

"Na tsane ta wall....."

Bata karasa ba jana ta dille mata labba dayasa ta saurin kai hannu tana kallon maman nata cike da mamaki.

"Kar in sake jin wannan maganganun a bakinki. Kina jina? Me tai miki? Bakisan Pa dinki na sonta ba? Zakiyi respecting dinta ki koyi sonta kema kinajina? Babu inda zataje she is here to stay you deal with it"

Turo baki ikram tayi dan tana taya mamanta kishi har ranta. Tana kuma mamakin ke yasa mumynta zata ce ta so matar nan datai turo musu kai cikin rayuwa.

Kallonta jana takeyi. Ga kanta na wani irin ciwo ga ikram zata kara mata wani ciwon kan kuma. Bata son yarinyar ta taso da tsanar kishiya tun tana yar mitsitsiyarta.

Beside ita ba kalar matar da take son turama yaranta akidar tayata kishi bace ba. Tarbiyarsu da kasancewarsu masu nagarta yafiye mata komai muhimmanci.

Kamo ikram din tayi daba musubta kwanta kan cinyarta tana hade jikinta. Cikin taushin murya jana tace.

"She is not our enemy ikram. Ba a tsanar mutum babu dalili. Ba abu bane me kyau. Ki bata chance kiga halinta. Zaki iya mun wannan kokarin?

Ki mata kirki?"

Kai ikram ta daga ma jana.

"Promise?"

Kai ta sake dagawa. Jana tadanyi murmushi.

"Tashi kije ki kwanta. Dare yayi sosai"

Mikewa ikram tayi ta kalli jana tana shagwabe fuska.

"Mumy zan kwana anan please"

Nisawa jana tayi. Ta kalli gadon. Ba dakinta bane ita kadai kusan gaba daya rabi da kwatar rayuwarsu da jabir anan sukayita.

"Muje in kwana a dakinki"

Ware idanuwanta ikram tayi sannan tai murmushi. Mikewa ikram tayi ta kamo hannun jana suka mike tare. Dakin ikram din suka nufa.

Ita ta gyara ma jana wajen ta kwanta sannan tahau gadon ta kwanta taja kashe musu kwan dakin ta na sake matsawa jikin janar tana sauke numfashi.

Addu.a jana tayi musu. Tana jin ikram din tana sake numfashi alamar bacci ya dauketa. Hannun ikram din ta kama cikin nata ta dumtse wata nutsuwa na saukar mata.

Addu.o.i ta shiga jerowa duk kalar da suka zo kanta. Kamun bacci ya dauketa..........!

****

"Wai menene dadin wanna shirin da kika like wa?"

Fu.ad ya tambayi safiyya da gaba daya ta mayar da hankalinta kan My Tv series suna maimaita shirin Bade ache lagte hai.

Batare data juyo ba tace mishi.

"Ba zaka gane ba"

Remote din dake kusa dashi ya dauka ya danna yana canza channel din. Juyowa tayi.

"Ohhhh please ka mayarmun"

Turo mata lips dinshi yai.

"Wanna shirin yafini muhimmanci"

Kaman zata fashe da kuka tace mishi.

"Bai fika ba. Now please ka mayarmun ana wuce wa fa"

Remote din ya mika mata yana dakuna fuska. Mikewa yai daga kwanciyar da yake hadi da fadin.

"Barin duba Nana"

Kai ta daga mishi. Tasan bacci take. Da wahala magungunan data sha su saketa da yanzun. Jikinta ya soma zafi kwana biyun nan.

Ya dafa hannayenshi kenan zai mike Nana ta fito daga dakin tana dakuna fuska. Kallonta yake ta kara ramewa fiye da sanda yazo.

Wani abu ya soki zuciyarshi. Murmushi yai mata data kasa mayar mishi saboda yanda take ta kokawa da numfashinta.

Dakyar ta iya cewa.

"Mumy....."

Da sauri safiyya ta juya ta kalleta. Wani irin jiri ke dibar Nana din ta soma ganinsu bibbiyu saboda yanda numfashinta yaki kaiwa.

Kanta yayi wani irin zafi kamun taji gabaki daya duniyar tana juya mata. Fu.ad ya soma mikewa da gudu ya karasa wajenta yasa hannu yana tallabeta saboda karta fadi.

Girgiza ta yake amman ko motsi batayi. A rikice yake cema safiyya.

"Sofi please kiyi wani abu. Bata numfashi....... Wallahi bata numfashi"

Wani yawu safiyya ta hadiya. Ba wanna bane na farko a wajenta shisa take da yar nutsuwa fiye data fu.ad din. Daki ta shiga ta dauko hijab dinta da mukullin mota.

"Dauko ta mu tafi asibiti"

Girgiza mata kai fu.ad ya shiga yi yana sake rike nana gam a jikinshi.

"Taki tashi sofi"

Dafa kafadarshi tayi cikin taushin murya tace.

"Zata tashi. Sai munje asibiti. Please fu.ad ka taso"

Mikewa yai yana sabar nana a kafadar shi suka fice tare. Bayan motar ya bude ya shiga yana kwantar da ita a jikinshi.

Wayarshi ya dauko bayan safiyya ta tashi motar suna ficewa daga gidan. Momma ya kira ta daga da yi mishi sallama.

Ko amsawa baiba yace mata.

"Momma nana..... Muna hanyar asibiti yanzun"

Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Yana sake jijjiga nana ko zata bude idanuwanta. Zuciyarshi ciwo take kaman ya cire ya ajiye.

*

Ta window din yake tsaye yana kallon yanda wajen likitoci hudu suke kan Nana an saka mata oxygen mask ya juyo ya kalli safiyya da take zaune ta hade kanta da gwiwa.

Kusa da ita ya koma ya zauna ya dafa kafadarta. Dagowa tayi ta kalle shi. Muryarta da yanayi na damuwa tace.

"Zan kira su inna ne. Ina so su ganta before you know........ May be"

Hannunshi ya zagaya yana kwanto da ita jikinshi. Kansu ya hada yana fadin.

"No sofi......ki daina cewa haka. This is not it. Wata nawa akace? Ba shidda ba yanzun fa ake wata na hudu.

Muna da sauran time"

Ita yake fadawa amman dakaji yanayin yanda yake maganar kasan cewa yana kokarin convincing din kanshi ne fiye da safiyya din.

Batace mishi komai ba sai sake makalewa datai a jikinshi. Tanajin kukan da zuciyarta takeyi amman hawaye ko daya sunki zubo mata.

Suna nan zaune momma ta zo. Tashi fu.ad yayi ya karasa wajenta yana kallonta so yake tace mishi komai zaiyi dai dai. Ta fada mishi nana zata samu sauki

Ta fada mishi komai baizo karshe ba. Kai momma ta girgiza mishi. Hakan yasa shi dafe goshi. Raba momma yayi yana ficewa daga wajen gabaki daya.

Kusa da safiyya ta karasa ta zauna. A hankali safiyya tace mata

"Ina wuni"

Dafa ta momma tayi saboda bata san me zata ce mata ba. Nana jikarta ce idan har tana jin wanna fargabar bata san su kuma me suke ji ba.

"Fu.ad......"

Safiyya ta fadi tanajin hawayen da suka ki fitowa tun dazun suna zubowa.

"Kinsan halin shi safiyya. Yana son zama shi kadai a yanzun. Inba haneef ko lukman ba bazai saurari kowa ba"

Wayarta safiyya ta cire daga key tai ma haneef text.

"Muna asibiti da Nana."

Ko minti biyu ba aiba tsakani ya dawo mata da amsa.

"On my way"

*

Zaune yake bakin kofar asibitin saboda yanda yaji iskar ciki ta mishi kadan.

Baya son tunanin komai banda na lafiyar nana. Ko kadan bai kula da motar haneef ba. Saboda hankalinshi na wata duniya ta daban.

Tun shigowarshi asibitin ya hango fu.ad din zaune. Har yai parking ya fito. Hannayenshi ya hade waje daya hadi da murzasu lokaci daya kuma yaja iska yana fitarwa ta bakinshi.

Sannan ya taka ya karasa wajen fu.ad din ya dafa shi. Da sauri ya dago. Ganin haneef din ya bashi mamaki nadan lokaci.

"Haneef"

Ya fadi cikin alamar gaisuwa. Zama gefenshi haneef yai hadi da fadin.

"Me kakeyi a waje?"

"Iskar cikin ce nakejin tamun kadan na fito nan"

Ya amsa shi. Dafa shi haneef yayi.

"Ba yaro bane kai fu.ad. Ya kamata ka koyi tarbar matsalolinka. Gudunsu bazai canza komai ba"

Tauna maganganun haneef din yake yanajin gaskiyarsu na zaunawa tare dashi.

"I...i.... Ni bansan me ya kamata inyi bane ba"

Wani irin helplessness yake ji da tunda yake a rayuwarshi bai taba jin kalar shi ba. Mai yakai kana sane cewar da duk mintinan dake wucewa rayuwar yarka yake tafiya dashi tashin hankali?

Jinjina mishi kai haneef yai. Ko bai fahimci kalar abinda fu.ad yake ji ba yana kamantawa. Kuma yana tausaya mishi.

"Ka tashi muje. Kana bukatar spending duk wani lokaci tare da ita. Zata so haka"

Mikewa fu.ad yayi yanajin zuciyarshi na wani irin dokawa. Hannunshi yasa cikin na haneef kaman karamin yaro.

Kyale shi haneef din yayi. Yasan yana bukatar kwarin gwiwane in rike hannunshi yana samar mishi da hakan saboda me zai hana shi?

Lokacin da suka karasa ciki basu ga su momma a waiting area din ba dan haka suka shiga cikin dakin. Suna zaune gefen Nana kaman yanda suka zuba mata idanuwa zai sa ta samu sauki.

Haneef gaisawa sukai da momma da safiyya yana musu yamai jiki kamun ya samu waje ya zauna. Zagayawa fu.ad yayi ya koma saitin kan Nana.

Hannu yasa ya shafi goshinta da alama bata ma san duniyar da take ba. Dan rankwafawa yai ya sumbaci goshinta yana sauke murya.

"Allah ya baki lafiya princess. I love
you so much. Kinsani ai ko?"

Dafe fuska safiyya tayi cikin hannayenta. Momma da haneef suka hada idanuwa suna rasa kome ya kamata suyi.

*

Zuwa yamma gabaki daya dakin ya cika. Tun daga kan anty fatima duk sunzo. Har zainab dan da lukman yace ta zauna saboda cikin satin ake sa mata ran haihuwa kuka ta kamayi.

Dole ya taho da ita. Doc ne ya shigo sake duba Nana yagansu cikin dakin. Ware idanuwa yayi hadi da fadin.

"Gaskiya ku fita. Ana so ta samu hutu wadatacce ne. Ba.a son hayaniya ko kadan"

Kallonshi lukman yayi yace.

"Kamun ka turo dakin nan kasa ran zaka ganmu fiye da mu goma a ciki?"

Girgiza mishi kai doc din yayi.

"Kaji magana ko daya na fita daga dakin?"

Ya sake girgiza mishi kai. Rai a bace lukman yace.

"Do your damn job ka barmu muji da abinda yake damun mu."

Fu.ad dake gefenshi ya rike hannunshi. Idan zai kirga wannan ne karo na biyar daya taba ganin ran lukman a bace

"Lukman please. Kabarshi yai aikinshi. In yana ganin zamu takurata sai mu fita"

Cikin idanuwa lukman ya kalle shi yace.

"Ku fita ban hanaku ba. Ina nan nikam"

Kallon doc din fu.ad yayi. Shi yanzun kam bayajin wani karfi ko na sisi balle har energy din rikici. Hakan doc din ya kula dashi. Yanajin idanuwansu gabaki daya akanshi.

Dan haka yabarsu tunda da gaskiyar lukman ba surutu suke ba. Wanda suke tsaye suna tsaye. Wanda suke zaune suna zaune abinsu.

Baiga matsala tare da kasancewarsu a dakin ba. Kalar kaunarsu ga nana har mamaki ta bashi. Dubata yayi yaga komai na tafiya yanda suke tsammani sannan yace.

"Ko motsi tayi kumin magana"

Kai kawai fu.ad ya daga mishi. Safiyya ce mai karfin halin yi mishi godiya kamun ya fice daga dakin.

*

A asibitin sukai sallar magrib da isha.i ganin babu wani canzi yasa momma ta tusa kowa tace ya tafi gida.

Tunda sunga Nana din. Addu.a tafi bukata daga wajensu ba wannan zaman ba. Kan dole suka tattafi. Daga safiyya sai fu.ad aka bari a asibitin.

Kallon shi safiyya tai yana zaune ya tusa Nana gaba yana jira yaga ko motsi tayi. Tace mishi.

"Kaci wani abu"

Girgiza mata kai yayi saboda bayajin zai iya saka ma cikin shi wani abu. Da sauri ya dago kai yace ma safiyya.

"Bamu fadama Ansar ba"

Dafe kai tayi itama tanajin rashin kyautawar hakan. Text tayi mishi ta fada mishi tana bashi hakuri.

Shi kanshi fu.ad din yasan Ansar nada hakkin sani koba komai yai dawainiya mai girma da Nana kuma bazai manta ba.

Bayan haka yasan ita kanta Nana ba zata yafe musu ba in taji basu fada mishi ba. Aikam kasa hakura yayi.

A daren saida yazo yaga nana duk da bai jima ba ya koma. Ansar na tafiya safiyya ta sauka kasa dan kafafuwanta sun gaji.

"Ka sauko kaci abinci"

Kai ya girgiza mata. Ko magana baya sonyi. Gajiya tayi ta hakura ta kyale shi. Saida ta kira su inna kaman yanda ta saba tai musu saida safe take fada musu suna asibiti ma sannan ta kwanta.

Damuwar dake zuciyarta bai hana barawon bacci sace ta ba cike da mafarkai barkatai.

Hannunshi fu.ad yasa cikin Na nana ya dumtse yanda koya dayan kuma yana kan cikinta ya dora kanshi jikin gadon yanda data motsa zaiji.

Anan bacci ya dauke shi......!

****

A dakin ikram tai sallar asuba sannan ta tashi ikram din itama ta shiga toilet tayo alwala. Tun jiya sun san duk da monday ce ba zasu je school ba saboda gajiyar hidimar biki.

Fita jana tayi daga dakin ta tashi sauran yaran suyi sallah suma in yaso sai su koma baccin su. Ta tashi atika ma. Sannan tai dakinta.

Tana shiga dakinta wanka tayi ta fito ta zira ma jikinta wata doguwar riga ta atamfa dinkin simple ta daura dankwalinta sannan ta nufi kitchen.

Dankali ta fara ferewa tana so ta taya atika dan kar aikin yai mata yawa. Ta dora kenan ta dafa shi atika ta shigo kitchen din.

Tare suka kama aikin. Zuwa bakwai da kusan rabi sun gama komai. Sauri sauri jana ta kara watsa ruwa ta fito tana shirin tafiya aiki.

Dan ta makara sosai yau. Tana karasawa ta lalubo wayarta taima jabir text ta fada mishi ta wuce office.

Ga mamakinta text dinshi har hudu tagani. Biyu jiya da darene yake mata godiya daya kuma saida safe. Biyun da safen na ne yake tambaya yata kwana ya yara.

Dayan yanzunne ba jimawa ya turo mata shi.

"Please reply"

Murmushi tayi. Har ranta taji dadin kalar kulawar daya nuna mata.

"Afuwan honey J. Yanzun na dauki wayar. Duka mun kwana lafiya. Fatan kaima. Zan wuce office ne yanzun saina dawo.

Love you"

Ta tura. Har zata saka wayar cikin jaka wata zuciya daban da mai kishin data hanata tambayarshi ya kwana ayna take ce mata bata kyauta ba.

Ko badan ayna din ba jabir zaiji dadi.

Please Login or Register in order to submit comment