Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taji a wayarta. Bata dauka ba dan yace daya zo zai kirata. Tashi tai ta fita ta bude masa gidan.

Duk ya hada zufa. Yana wani maida numfashi yake kallonta ta masa kyau. Kanta daure da dankwalin rigar.

Yana son ganin fuskartan nan fayau haka.

"Sannu"

Ta ce masa. Kai kawai ya iya daga mata yana wucewa ciki. Kan kujera ya zauna yana kokarin daidaita numfashin shi saboda gudun dayai.

Hannunshi yakai ya bayan kanshi ya taba. Runtse idanuwanshi yai yana cire hannunshi. Ciwon na mishi zafi har yanzun.

Sai lokacin ma ya tuna da wasu su ado da abinda ya faru. Murmushi kawai yayi dan yagama rama abinda sukai mishi tunda ga safiyyar nan zaune a gabanshi.

Saida bugun zuciyarshi ya koma dai dai tukunna ya mike ya tafi bedroom. Wanka yayi ya sakko kaya ya fito.

Kallonshi safiyya take. Wandon jikinshi yaga ce a jiki kusan daga gwiwarshi har kwauri.

Blue ne mai haske sai riga ja a jikinshi. Yayi kyau matuka waje ya samu ya zauna.

Tunda ya tashi cikinshi yake ji wayam ga gudun dayai ya kara kona calories. Wata yunwa ke cinshi. So yake bakwai da rabi tayi su fita gabaki daya.

Baima san makarantar daya kamata yakaita ba. Da yai tunanin yakaita FAAN inda su hussaina suke. Sai kuma ya fasa.

Tunani yazo masa. Yakai ta crescent kawai inda pha.iza ta gama. Ya yarda da makarantar tana da kyau sosai.

"Sofi dauko hijab dinki mu tafi. Sai mu ci wani abu a hanya ko?"

Tashi tayi ta nufi daki. Cikinta a wani kulle. Tunanin komawa makaranta na mata dadi ta wani fannin kuma yana bata tsoro.

Bata san ya zata tsinci kanta a makaranta ba. Gashi ko turanci bata ji. Sai dai ita bamai girman kai bace ta wannan fannin.

Tunda ta dauko hijab dinta take ma kanta alkawarin zata tsaya sosai ta maida hankali kan karatunta.

*

A hanya yai musu takeaway na dankalin turawa da kwai da fresh milk. Ya samu waje yai parking suka ci. Sannan suka wuce.

Tun daga gate din makarantar taji ta karaya. Duk kwarin gwiwar data fito dashi ya kara wargajewa da suka shiga cikin makarantar.

Ga wani irin girma tana dashi. Kayan makarantar kansu abin kallo ne. Sai dalibai ko ina suna kai kawo.

Daka gansu kasan yayan masu hannu da shuni ne. Tsaf dasu. Bata san lokacin da ta kama hannun fu.ad ta dumtse gam cikin nata ba.

Yasan a tsorace take. Hannunta ya rike sosai cikin nashi suka wuce office din principal din.

Saida suka samu wajen zama sannan ya saki hannun safiyya yana maida hankalinshi kan principal din.

Safiyya na zaune tana ta zare idanuwa. Kanta a kasa tana jin yanda fu.ad din suke magana cikin harshen turanci.

Bayanin komai yai masa. Da matakin data tsaya a karatu da kuma cewar bata jin turanci gashi bata da takardu ko daya sai dai ya siya mata na nan.

Shawara principal din ta bashi cewar safiyya ta fara dafa jss1 fur fu.ad yace baisan wannan ba. Baya so ko kadan matarshi taji kaman an rainata.

Kudi shi zai biya. Daga ss1 yake so ta fara. A samu malamar da zai biya ta dinga zuwa gida tana koya mata.

Extra lesson komai da ake bukata dan a taimaka mata. Amman ba za.a nuna an raina karatunta ba.

Shawara ce taba fu.ad yaki ji. Makaranta ce ta kudi. Kuma sune suke magana. Nan take akai masa lissafin komai daga kan kudin makaranta zuwa na uniform zuwa litattafai.

Nan ya biya komai. Da sunce saiya je bank. Ya bada dubu daya yace su aiki wani yakai.

Uniform aka duba kala biyu aka ba safiyya. Tasa wata malama ta rakata inda zata cire na jikinta ta gwada wa.annan.

Kallo daya zakai mata kasan a tsorace take. Saida ta kalli idanuwan fu.ad yadan daga mata kai da cewar babu matsala sannan tabi matar.

Kaman an aunata haka uniform din ya zauna mata. Ta sakko hijab din ta fito. Da kayan data cire a leda malamar ta sakko mata.

Kallonta yake da murmushi a fuskarshi tayi kyau sosai. Yace a kara mata kala biyu uniform din. Ca sukai yabar safiyya sai karfe hudu ya dawo ya dauketa.

Inyaso zasuyi magana kan wadda zata dinga zuwa gida tana koya mata. Gabansu ya kama hannun safiyya ya jata gefe.

Kallonta yai sosai.

"Nasan zaki iya sofi. Karki ji tsoron komai kina jina ko? Ga dubu daya kici wani abu. Ina wayarki"

Mika masa tayi. Ya karba ya kashe yasa a aljihu ya bata dubun.

"Anjima zanzo in dauke ki. Kiyi karatu sosai kinji"

Kai kawai ta daga mishi tanajin kamar karya tafi yabarta. Hannu yasa yadan cupping fuskarta yace mata.

"I love you"

Murmushi tai ta sadda kanta kasa a kunyace kamin ta wuce ta koma inda malamar ke jiranta.

Kara kallonta yai sannan ya fice daga office din.

*

Yana mota ya kira lukman yace masa yana school su hadu acan. Buk ya wuce saida ma yadan jira lukman din ya fito lecture karfe goma.

Mota ya bude ya shiga. Kallon fu.ad din yake ya masa wani haske.

"Ya naga kayi wani fresh?"

Lukman ya tambaya. Dariya fu.ad yayi.

"Bana son iskanci lukman. Sofi nakai makaranta shine na biyo ta nan"

Wani murmushi murmushi ne fuskar lukman.

"Did you?....."

Naushi fu.ad yakai masa a kafada fuskarshi nayin wani ja. Girgiza kai fu.ad yake yi.

"Inalillahi lukman. Kai bakinka bashi da tsarki. Idan nayi ne ma fada maka zan......"

Dariya sosai lukman yai ganin yanda fuskar fu.ad din ke kara yin ja.

"Ashe akwai abinda kake jima kunya?"

Dariya shima yakeyi.

"You are gross lukman"

Tashin motar yayi yana juyata. Lukman dake dariya yace.

"Kai ina da lectures fa karfe sha dayan nan"

Ai kamar ma fu.ad baiji shi ba ya ci gaba da jan motar.

"Da gaske nake maka"

"You are skipping tunda ba test bane. Yawo zamu"

Dariya kawai lukman yayi. Fu.ad rikici.

*#TeamAS*
[7/5, 11:14 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:15 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 25
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


25

Karfe uku da rabi a crescent tai mishi. Sai da ya fara shiga sukai magana da matar da zata dinga zuwa gida tana koya ma safiyya karatu.

Ba wata babba bace ba can. Yoruba ce sai dai taji hausa kaman ba gobe. Duka ba zata shige shekaru ashirin da hudu ba.

Magana sukai ta fahimta. Fu.ad yai mata kwatancen gidansu. Kusan unguwarsu daya ma. Layi uku ne tsakaninsu.

Suna gamawa ya fita waje ya tsaya jikin motarshi yana jiran safiyya ta fito. Sai ware idanuwa yake yaga ta inda zata bullo.

Hango ta yai rungume da litattafai. Wani murmushi ya kwace masa. Hango shi tai itama lokaci daya yaga murmushi ya bayyana a fuskarta.

Jinshi yake wani iri. Kamar da duk takun da take ta karaso wajenshi har iskar wajen canzawa takeyi.

Kaman ya ruga ya rungumeta. Tana karasowa tai masa kyautar wani murmushi daya taba mishi zuciya.

"Ina wuni"

"Sofi yan makaranta. Sannu da kokari"

Ya amsa. Dariya tayi. Ya bude motar ta shiga. Ya zagaya shima ya shiga yaja motar.

"Ya makarantar? Badai wata matsala ko?"

Girgiza masa kai tayi.

"Dukkansu suna da kirki sosai. Wasu ma sun karbi litattafaina zasu tayani rubutun da aka wuce ni"

Yaji dadin hakan. Yanda suka karbar masa safiyya.

"Babu wanda yai miki wulakanci dai ko? Daga daliban zuwa malamai"

Kai ta girgiza masa. Dan ita kanta ta yi mamakin yanda sukai mata karamci. Da sun fara mata turanci. A kunyace tace musu bata ji.

Mamaki kawai taga sunyi maimakon raini. Da alama dukkansu yan manyan gida ne. Dan haka ta amsa fu.ad da.

"Haka ma sukace zasu taimakamun. Gaskiya suna da karamci"

Jinjina kai yayi. Dan Allah ne kadai zai rabashi da duk wanda ya nemi ya raina masa safiyya ko ya wulakantata.

Suna isa gida tai mamakin ganin an bude musu gate. Kallon fu.ad tai yagane tambayarta tun kamun ta bude baki.

"Dazun yazo. An samo mana mai aiki ma"

Tadan ji dadi. Ko ba komai taji motsin mutum banda su cikin gidan. Tayata daukar litattafan yayi yana fadin.

"Anjima sai muje a siyo jakar makaranta"

Tare suka shiga ciki. Tun daga bakin kofa ya cire takalmin da socks din daya siya mata a makarantar.

Kauda su tayi waje daya. Sannan ta shiga ciki. Fu.ad yabi bayanta. Kan kujera ya ajiye litattafan nata.

Zuciyarta taji ta wani doka da su inna suka fado mata. Tana tuna yanda baba yaso ta ci gaba da makaranta data nuna tana so sai dai bashida karfin.

Zata so ace sun ganta a yanzun. Sunga yanda take makaranta data tabbatar tana da tsada sosai.

Tasan zasu ji dadi suga ta samu ci gaba a rayuwa. Ita tana nan bata san halin da suke ciki ba.

Bata san wasu hawaye sun zubo mata ba saboda wani nauyi da zuciyarta tayi.

Yaga tunani take. Hawayen dayaga ni a fuskarta yasa shi tashi da sauri ya koma kan kujerar da take.

Hannuwanshi yasa ya tallabo kafadunta. Jinshi da duminshi ya sa taji ta karasa karaya.

Cikin kuka tace masa.

"Ka kalleni. Cikin kwana hudu rayuwata ta sauya. Bansan halin da iyayena suke ciki ba.......bansan..... Kawai......"

Riketa yai gam. Kukanta na taba mishi zuciya. Ji yake yana wani ci masa rai.

"Shhhhh"

Luf tai a jikinshi tana sauke ajiyar zuciya. Riketa yayi yasa hannunshi daya yana goge mata fuska.

"Laifi na ne sofi. Ki dora shi a kaina. Ni na shiga rayuwarki na hargitsa komai.

Kila da banganki sanda naganki ba da ban jefa ki cikin halin nan ba. Da....."

Da sauri tasa hannu tasa hannu ta rufe masa baki tana girgiza masa kai idanuwanta cike da hawaye.

Karantar maganganunshi take tana jin wani irin yanayi. Muryarta kaman ba tata ba tace.

"Da baka ganni a sanda kaganni ba daya na nufin ban sanka ba......."

Lumshe idanuwanshi yayi yana sake riketa gam. Dan duk kalaman dayai zuciyarshi karyatawa take.

Sumbatar goshinta yai yana jin kaman ya mayar da ita cikin cikinshi dan kar wata kaddara tazo ta ko da gifta ta tsakaninsu ne balle kuma azo maganar ta rabasu.

Hannu yakai kan cikinta ya dafa.

"Me kika sakamun a cikinki?"

Dariya ta danyi tana dora hannunta kan nashi saboda wasu abubuwa da taji suna mata yawo a cikin da tasan suna da alaka da hannunshi.

Mamakin yanda take jin kaman shekara hudu sukai ba kwana hudu ba.

Wani irin sabo take jin sunyi da fu.ad da ta tabbata ba aikinta bane na zuciyarta ne.

Yanda ya samu karbuwa a yanzun take jin numfashi daidaitacce ma da wahala ta iya yinshi in baya kusa mamaki yake bata.

Bata san sanda ta dumtse hannunshi gam ba. Hakan yasa shi saurin ce mata.

"Sofi menene?"

Cikin idanuwanshi take kallo. Kalarsu take karema kallo yau. Ruwan kasar nan masu wani ratsin haske haske.

Wani abu ke fisgarta daya sa take son manta yanda ake numfashi.

Shima kallon nata idanuwan yake. Yana karantar rokon sa ke cikinsu.

"Ina nan sofi. Muna tare. Ba nace miki ni da ke ba"

Kai ta daga mishi. Tana sauke idanuwanta zuwa kan fuskarshi.

"Me kika ci?"

Fuskarta takai hannu tana gogewa hadi da fadin.

"Bansan sunan shi ba. A makaranta dai muka siya da su khadija"

Dariya yayi.

"Kice har kinyi kawaye ma"

Itama dariyar tayi. Tana saka hannu a aljihun wandonta. Dari shiddan daya rage ta dauko masa.

"Ga canjin. Na kashe sosai dai. Bansan da tsada ba"

Ware idanuwa yai yana dariyar mamaki. Dari hudu ta taba ciki. Ganin ya tsaya kallonta ya sata jin duk babu dadi.

Tasan ta kashe masa kudi sosai kuma har ranta bata san abinda suka siya da tsada ba da bata fara ba.

Muryarshi taji yana fadin.

"Sofi Allah ya shiryamun ke"

Dariya ya bata sosai sosai.

"Amin. Nima ana mikomun canji sai da gabana ya fadi"

Wannan karon shi yai dariya.

"Kinga ke din nan ko. Daga yanzun in na baki kudin makaranta. Duka ne na baki.

In kin kashe fine. In baki kashe ba ki rike canjin"

Rike baki tayi. Bata san wacce kalar godiya zatai masa ba. Sai dai addu.a.

"Allah ya baka aljanna"

Da sauri ya amsa da

"Amin. Tare dake muyi zamanmu"

Mikewa yai yana riko hannunta.

"Kin batamun fuskarki da hawaye. Tashi muje a wanke"

Wata yar kunya taji ta rufe ta. Tai masa murmushin nan da yake masa wani abu a zuciya da bashi da kalaman dora shi akai.

Binshi tai ya rakata har bedroom din ta wanke fuskarta. Tayi la.asar tun a makaranta.

Kallonshi tayi.

"Barin watsa ruwa. An bamu aikin gida ban iya ba saika dubamun"

Wani daga mata girarshi yai duk biyun yana ciza lebe. Sannan ya fice daga bandakin yana barin zuciyarta da wakar yanda kyanshi yake.

*

Falo ya koma ya zauna abinshi. Ji yai ana kwankwasa kofa. Ya tashi yaje ya bude.

Pha.iza ce an ci uban gayu. Sallama tai masa hadi da fadin.

"Ina wuni"

Wucewa tai cikin falon. Batama jira amsar shi ba. Ya maida kofar ya kulle.

Ya dawo ya zauna. Sai lokacin ya kula da ledar dake hannunta.

"Momma tace in kawo muku abinci. Sai kuma muje wajen tela da matarka"

Yanda muryarta tayi a kalmar matarka ya mishi wani iri.

"Sunanta safiyya. Thank you da kika gane matata ce. In ba zaki tayani sonta ba. Kibar abin a ranki"

Sauke ajiyar zuciya pha.iza tayi a sanyaye tace.

"Kayi hakuri. Kawai zuciyata ta kasa nutsuwa da ita ne. I have this hunch..... "

Katse ta yai da fadin.

"Spare me mana. Na dauka kin girmi wannan pha.iza"

Dan daga kafada tayi.

"Fine. Allah ya baku zama na lafiya"

Murmushi yayi. Ya amsa da.

"Amin"

Yafi so dukansu su tayashi son sofi. Kaman taji ambatonta dayai a zuciya ta fito daga daki.

Jikinta sanye da doguwar riga ta dauro dankwalin. Dan tsayawa tai ganin pha.iza.

Fuskar pha.iza ba yabo ba fallasa tace.

"Ina wuni"

A kunyace safiyya tadan karaso ta zauna gefen fu.ad hadi da fadin.

"Ina wuni. Ya su mama"

"Suna lafiya. Tana gaishe ku. Inajin bama sai munje dake ba. Inada tape kawai sai in auna ki"

Hakan ma yafi ma safiyya dadi. Tape din pha.iza ta dauko da yar takarda da biro. Ta auna safiyya ta rubuta.

Tana gamawa ta kalle su tace.

"Ni kam dai na wuce. Sai anjimanku"

A hankali safiyya tace.

"Sai anjima. Mungode"

Yanda ta yamutsa fuska sai tai mata yanayi da fu.ad sosai sosai. Irin abu daya hancinsu yake yi.

"Bro kaji ta. Wai kungode"

Dariya fu.ad yayi ya dora da.

"Pha.iza ki kawo mata sauran kayan da mukai magana fa"

Dan dukan goshinta tayi.

"Kaganni ko. Suna mota fa. Barin dauko"

Fita tai daga dakin. Batafi minti biyar ba ta dawo da ledoji har hudu ta ajiye musu tsakiyar falon tana juyawa da fadin.

"Na wuce....."

Daukar ledojin fu.ad yayi ya mika ma safiyya. Ta bude su. Daya kayan baccine sai under wears.

Da sauri ta rufe dan tunanin fu.ad yagansu kawai yasata jin kunya.

Dayan kuma takalma ne. Ta dauko guda daya ta gwada. Kaman pha.iza ta auna kafarta sun zauna cif.

"Sun miki kyau"

Fu.ad ya fadi yana kallon yar kafarta da ta burge shi. Kallon shi tayi sosai.

"Nagode. Nagode sosai....."

"Shhhhhh"

Ya fadi yana mata murmushi. Shi ya tayata suka dauki kayan zuwa bedroom din daya soma kira nata.

Ya bude wardrobe ya zuba mata kayan ciki. Sannan suka dawo falo.

Assignment din english din datai masa magana ta dauko. Yai mamaki sosai ganin rubunta. Ko da yake ba wai a karatu bane abun.

Iya rubutu baiwa ce. Ko shi baida handwriting me kyau haka. Wannan sai su haneef. Kaman ya sace lokacin da suke makaranta.

Bayani yake mata yaga dai ba iya yi zatai ba. Dole komai sai a hankali. Rubuta mata answers din ya fara yi.

Yayi layi biyu yaji tace.

"Kai kai kai"

Shi kanshi rubutunshi ya kalla ya kalli nata. Saiya kwashe da dariya. Ya manta when last yai rubutu inba a system ba.

Dakuna fuska tayi. Alamar rubutun bai mata ba. Idanuwanshi yasa cikin nata yana mata wani cute eyes.

"Allah saina rubuta."

Dariya tayi.

"Kamun a wata takarda sai in kwafa"

Dauke littafin yai yana make kafada.

"Naqi. A ciki nake sonyi"

"In yaga rubutun ba iri daya bafa? Saika jamun bulala"

Zaro idanuwa yai fuskarshi nayi wani serious lokaci daya.

"Na fada musu matar aure ce ke. Zamu hau bene mu fado da duk wanda ya tabamun jikinki"

Dariya kawai tayi.

"Nikam kabani littafina"

Daga hannunshi yai sama da littafin yana girgiza mata kai.

"Nasani ai. Rubutuna bashida kyau ko? A haka zan miki. In ance na waye kice na mijinki ne"

Dariya take sosai. Hakan na mishi dadi. Mikewa tai kan gwiwoyinta tana kokarin kai hannu ta kamo nashi dake rike da littafin.

"Kaga kana dakuna mun ko?"

Dariya yake mata. Sosai ta mika hannunta ta kamo nashi ya janye. Jikinshi ta fada. Binta yaida kallo.

Itama kallonshi take sosai. A hankali ya sauke hannunshi idanuwanshi na cikin nata. Har wata iska yake ji shuuu mai wani irin nutsuwa.

A hankali yake rankwafowa yana kai fuskarshi dai dai tata. Kusan numfashi daya suke shaka ita dashi.

Kara matsawa yake sosai yana jin yanda numfashinta ke fita da sauri. Kwankwasa kofar akai.

Ya lumshe idanuwanshi. Da sauri safiyya ta tashi daga jikinshi tana wani maida numfashi.

"Fuck....."

Ya fadi da alamar kowaye ya bata musu yanayi. Mikewa yai da irritation a muryarshi yana fadin.

"Waye?"

"Ni ce"

Aka fadi. Bai gane muryar ba. Dan haka ya karasa kawai ya bude kofar. Wata mata ce mai matsakaicin shekaru.

Kare ma shigarta kallo yake.

"Lafiya?"

Ya bukata muryarshi a dakile. Cikin taushin murya tace.

"Indo ce. Malam isa ya turoni"

So yake ya tuna waye ma malam isa? Ganin kamar bai gane ba yasa sata fadin.

"Wadda zatai muku aiki ce"

Sake tamke fuska fu.ad yai yana fadin.

"Oh. Shigo"

Matsa mata yai. Ta rabashi ta wuce. Da fara.a safiyya ta tarbeta.

"Ina wuni"

Ta gaishe da ita. Wani dakuna fuska taga fu.ad yayi. A kiyasce matar zatai shekara talatin.

Kasa ta zauna. Safiyya tace mata.

"ki hau sama mana"

Dan murmushi tayi.

"Nan ma yayi"

Shiru suka danyi kamun fu.ad yace mata.

"Bawani aiki bane mai yawa. Nasan ya baki kudin aikinki na wata biyu.

Shara ce. Sai duk aikin dai da take so. Zaki iya dafa abincin da zakuci da maigadi.

Yanda kika ga zaifi miki. In kwana zaki dinga yi. Akwai BQ in kuma gida zaki dinga komawa dai"

Kallon fu.ad safiyya take. Yanda ya hade fuska kaman bai taba dariya ba. Yanayin muryarshi kaman ranar farko data fara ganinshi.

Sai bataji dadin yanda yaima matar nan magana babu wani tausasawa ba.

"Ba kusa nake ba. Cikin dawanau nake da zama. Zan dinga kwana anan din. Sai dai zan koma duk ranar juma.a in dawo ran asabar in Allah ya yarda"

Wani kallo fu.ad yai mata. Yace

"Wazai aikin gidan na ranar juma.a din kenan?"

Sake saukar da murya tayi.

"Saina gama tukunna. Ran asabar din in shaa Allah da wuri zan dawo"

Ganin yana girgiza kai yasa safiyya fadin.

"Allah ya kaimu. Babu komai ai. Koni sai inyi"

Mikewa fu.ad yayi. Ya dauki mukullan dake gefenshi ya zari wasu ciki ya ajiye kan table din tsakiyar dakin yana fadin.

"Ga mukullan inda zaki dinga kwana. Yana nan baya dakin zagaya"

Baiko tsaya dubanta ba ya karasa inda safiyya take ya kama hannunta ya mikar da ita yana janta zuwa bedroom din.

Suna shiga ya tura kofar ya saki hannunta yana mayar da nashi kan kugunshi.

"Idan ina magana da masu aikin nan ki daina saka baki. Kudi na biyata bawai kyauta nace tazo ba.

Saboda me zakiyi mata aikinta?"

Yanayin shi ma tsoro yabata. Ya wani tamke fuska. A darare tace.

"Kayi hakuri"

Lumshe idanuwanshi yai yasa hannu yana murza goshi. Kamota yayi ya rungume a jikinshi.

Bayason tsoronshi daya gani cikin idanuwanta. Kaman yanda bayason kowa ya raina mishi ita.

****

*Bayan sati biyu*

Komai na tafiyar musu da ci gaba. Da wata irin shakuwa mai karfi da take kara shiga tsakaninsu.

Dan safiyya ji take bata da sauran kowa a wannan sabuwar duniyar da bata san gabas dinta ba sai fu.ad.

Cikin satin farko kwana uku ta jera kullum ta dawo daga makaranta sai tayi kuka.

Amman yanzun ta hakura. A duk rana da kewar su inna take tashi da ita kuma take kwana.

Saidai a hankali take sabawa da ita. Ranar makaranta karfe biyar anty laurat ke zuwa gida ta koyama safiyya karatu.

A sati biyun nan sun fara sabawa da ita sosai. Safiyya ta fara sakewa da ita. Haka ma mama indo kamar yanda take kiranta.

Tare suke share sharensu in fu.ad baya nan. Mama indo ta dafa musu abinci. Ita ta ke koyama safiyya amfani da kayan kitchen din.

Dan tayi aiki gidajen masu kudi bayan rasuwar mijinta yabarta da yara har shidda da suke hannunta.

Fu.ad bayaci. Wai kazanta saidai ya siyo musu abincina waje. Itama safiyyar in yana gida bata isa taci ba. Tana gudun fadan shi.

Bata kuma son ace gata yana fita waje siye abinci. Ta masa magana yakaita inda zata koyi kalaluwan girkin da yake so yace aikin zai mata yaea ba yanzun ba tukunna.

A makaranta kuwa suna gaisawa da duk yan ajin. Haka mazan suna ganin girmanta da aka ce musu tana da aure.

Zasu gaisa a mutunce. A natan kuwa khadija da aisha ne suka zama kaman kawayenta. Suna kokarin koya mata karatun turanci da kuma gane yaren.

****

Zaune yake dakin lukman. Kallo daya zakai ma fuskarshi kasan yana cikin bacin rai.

"Ka share kawai. Zai sakko with time"

Cewar lukman. Sake bata rai fu.ad yai hadi da fadin.

"Haba lukman? Nan da yaushe. Kullum fa saina kira abbah a waya baya dagawa.

Na dauka inya ganni ido da ido yau zai hakura. Amman ina gaishe dashi ko kallo na baiyi ba"

Jinjina kai lukman yai.

"To ita kuma safiyya tace me? Kai kullum saika ga momma da su pha.iza."

Tauna maganar lukman yai. Ya nisa yace.

"hakane with time. Itama in shaa Allah zan shirya ta da nata family din tunda ni ne silar bata su"

"Ko kaifa. Ashe ka fara hankali"

Dariya fu.ad yayi kamun yace.

"Jibi fa zan tafi. Ni banma san ta inda zan gaya ma sofi ba"

Fito da idanuwa lukman yayi.

"Wai bata sani jibi zaka tafi ba?"

Sauke numfashi fu.ad yayi.

"bama tasan zan tafi dinba at all. Maganar bata taba hadamu ba"

Kallon shi lukman yake.

"Aikam baka kyauta ba. Yanzun tafiyar zatai mata wani iri"

Langabe kai fu.ad yayi.

"Aiba ita kadai ba"

Harararshi lukman yayi.

"Dilla kauce daga nan. Abin ma haushi"

Dariya fu.ad yayi ya tabare fuska hadi da fadin.

"Em gonna miss her"

Rike hanci lukman yayi.

"You are disgusting fu.ad"

Dariya sukai gaba dayansu kamin fu.ad ya mike.

"Barin koma wajen matata. Zama dakin gwauro yana mun somehow"

Pillow lukman ya dauka ya jefa mishi. Ya kauce ya fice daga dakin yana dariya.

**

Tunda ya koma gida ya samu safiyya da anty laurat zaune a falo sun baje litattafai. Sannu da zuwan anty laurat ma datai mishi dakai ya amsa ya shige cikin bedroom.

Kallon safiyya tayi.

"Ki je ko yana bukatar wani abu"

A iya sanin halin fu.ad da tayi yasa ta girgiza kai.

"Idan yana son wani abun zai kirani"

Ta amsa tana karasa rubuta abinda takeyi. Kallonta anty laurat tayi.

"Look at you. Oya tashi kije. Ko baya bukatar wani abin ki masa sannu da zuwa properly"

A kunyace ta mike ta nufi bedroom din. Yana zaune gefen gado yana danna waya safiyya ta shiga da sallama.

Wani numfashi ya sauke. Atamfar dakw jikinta ta karbeta. Ga dinki ya zauna mata cif. Wani sonta yake ji yana yawata masa.

Hannunshi ya mika mata data karasa. Karasawa tai tasa hannunta cikin nashi tana zama. A tabare yace

"Ki sallame ta sofi. Ina bukatar ki a kusa dani"

Murmushin nan ya samu mai cike da kunya. Bata ce komai ba ta mike ta fita falo. Murmushi tai tayi batasan ta yanda zata ce ma anty laurat ta tafi ba tunda yau weekend ne.

In tazo karfe hudun nan sai magrib. Suna da sauran mintina talatin kamun lokacin tafiyarta yayi. Kallonta anty laurat tayi hadi da yin dan murmushi.

"Sai Allah ya kaimu gobe. Ki duba abinda mukai yau"

A kunyace tace.

"Allah ya kaimu. Nagode sosai"

Har bakin kofa ta rakata ta kulle gidan sannan ta koma. Yana zaune inda tabarshi. Agogon wayarshi ya duba.

Ya mike tsaye ya taka zuwa inda take. Hannuwan shi yasa kan kafadunta ya jata zuwa jikinshi.

Rungumeta yai yana dan rocking dinsu. Sunkai mintina biyar a haka. Baisan yanda zai fara gaya mata zai koma Europe ba.

Sai yai sati shidda inya koma kamun ya samu yazo yai kwana biyu. Da ace waje daya zai zauna inya je ba abinda zai hana yaki tafiya da ita.

Dakyar ya iya janye jikinshi daga nata hadi da fadin.

"Bara inyi alwala...."

Kai kawai ta iya daga mishi. Ta karasa gefen gadon ta zauna. Alwala yayi ya fito. Ya tafi masallaci.

Tasan ba dawowa zaiyi ba sai yayi isha.i. Dan haka ta shiga bandaki tayo alwalar itama ta fito tai sallah.

*

Sanda ya dawo masallaci. Mama indo ta shigo tai musu saida safe. Ya kulle nasu side din. Suka ci abincin daya siyo.

Dakinshi ya wuce can yai wanka. Itama tayi. Rigar bacci ta saka ta daura dankwali. Taji dadin yanda pha.iza ta samo mata wadatacciya. Duk da haka har yanzun kunya take ji fu.ad na kallonta ciki.

*

Suna kwance taji ya karasa hade sauran wajen dake tsakaninsu. Sannan yaja blanket din ya gyara musu rufa. Hannu daya ya dora kan fuskarta yana kare mata kallo cikin wutar dakin da bata da hasken kirki.

"Sofi bansan ta ina zan fara ba"

Murmushi tai mishi. A sanyaye saboda yanda kallon dake mata da kusancinsu ke kashe mata

Please Login or Register in order to submit comment