Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata.

"Ina kewar su inna sosai. Kuma kwana biyun nan ina yawan mafarkinsu.

Kawai ina son sanin halin da suke ciki ne......"

Ta karasa tana kwantar da kanta a jikinshi. Kamata yai yana jin wani iri a zuciyarshi. Kamata yai ya mikar da ita tsaye.

"Muje ki shirya mu tafi"

Da sauri tace

"Ina?....."

Ba wani alamar razana yace

"Wajen su inna. Abinda ya kamata inyi ne tuntuni. Rashin son ganinki cikin damuwa ya hana"

A tsorace take girgiza mishi kai. Riketa yai a jikinshi. Kuka take tana tuno yanda su inna suka koreta.

"Sofi please. Bana son kukan nan ko kadan. In bamuje ba ba zaki daina ba"

Kankame shi tai tana girgiza kai.

"Tsoro nake ji"

Kissing dinta yai a goshi yana kamata zuwa bedroom.

"Ina tare dake. Ni da ke zamu iya yin komai a tare. Zamuje in su inna sun karbemu fine. In basu karbemu ba zamu dawo.

Zamu sake komawa wani lokaci. Zamuyi ta komawa har sai sun karbe mu"

Da maganar shi ta samu dan kwarin gwiwa ta shiga bandaki ta wanke fuskarta. Ta fito ta dauki mayafinta tasa takalmi suka fita.

*

Wani irin dokawa zuciyarta take saboda tsoron da take ji. Tun fu.ad na kokarin janta da hira harya hakura.

Sai dai lokaci lokaci zai kai hannu yadan taba nata yana son nuna mata yana tare da ita a duk abinda zai faru.

Zuciyarta ci gaba tai da dokawa fiye dana da ganin anyo kwanar layinsu. Komai take ji yana kwance mata.

Harya karasa kofar gidansu yai parking. A tsorace ta kalle shi idanuwanta cike da hawaye. Hannu yakai ya rike nata. Cikin sanyin murya yace.

"Be strong sofi. In shaa Allah komai zai zo da sauki"

Hawayen da suka zubo mata ta goge. Tana kallo ya fita daga motar ya rufo. Zagayowa yayi ya bude mata.

Ganin taki fitowa ne yasa ya kamo hannunta ya fito da ita. Gabanta faduwa take. Ji take kaman ta ruga ta koma mota.

Idan su inna suka sake korarta fa? Suka sake mata abinda yafi na farko. Wani bangare na zuciyarta kuma yake fada mata bakomai ai. Ko dai sun sake korarta tagansu.

Taga suna nan lafiya. Hankalinta saiya dan kwanta. Tare suka taka har kofar gidansu. Kafafuwanta sun mata wani irin nauyi.

Bude baki safiyya tai zatai masa magana dai dai fitowar wata yarinya daga gidan da zata kai shekaru sha biyar.

Da mamaki safiyya ke kallonta dan zata rantse bata taba ganinta ba kaman yanda ita ma take kallon safiyyar.

Wani miyau ta hadiye sannan tace ma yarinyar.

"Sannunki...."

Ta amsa da.

"Ina wuni"

A tsorace safiyya ta kali fu.ad sannan ta maida dubanta zuwa ga yarinyar.

"Su inna suna ciki?"

Da mamaki yarinyar tace.

"Innarmu kike nufi?"

Safiyya ta girgiza mata kai.

"Aa masu gidan"

Cikin rashin fahimta yarinyar tace

"Mune masu gidan ai"

Da sauri safiyya ta tureta ta shige cikin gidan bata damu da yanda fu.ad ke kwala mata kira ba.

Wata mata ta samu tana jan ruwa. A tsorace ta saki gugar ya koma ciki ganin safiyya babu ko sallama.

"Ina inna?"

Ta tambaya tana karema gidan kallo. Cike da tsoro matar tace.

"Wacece ke? Daga ina haka babu ko sallama wacce innar?"

Girgiza kai safiyya take. Zuciyarta na barazanar barin kirjinta. Kallon matar tayi idanuwanta cike da hawaye tace.

"Dan Allah masu gidan nake nema"

Sai lokacin matar ta gane inda ta dosa.

"Allah sarki. Mu muka siyi gida. Watansu biyu kenan da tashi"

Wani abu safiyya ke ji yana mata yawo cikin kunnuwa. Da gudu ta fito ta samu fu.ad dayake kai kawo a kofar gidan.

Da sauri ya kamata ganin tana shirin shidewa. Fuskarta yake dan bubbugawa.

"Sofi menene?"

Dakyar numfashinta na wani sama sama tace.

"Sun tashi. Basa gidan...... Wallahi basa nan"

Ware idanuwa fu.ad yai. Kamun yadan saita kanshi sanin tana bukatar shi.

"Aa sofi. Ki kwantar da hankalinki. Babu inda suka je. Ki jirani anan bari in tambayo mutanen can"

Kai kawai ta daga mishi tana kallonshi ya tsallaka inda majalissar take.

Yana magana dasu. Wani irin dokawa zuciyarta takeyi. Yana tahowa ta kasa jira ya karaso ta taka suka hade.

Fuskarshi kawai ta kalla zarginta ya tabbata. Tsuggunewa tai a wajen tana sakin wani irin kuka.

Rikota yai dakyar. Ya jata ya bude motar ya rufe saboda mutane sun soma kallonsu sannan ya zagaya ya shiga shima.

Saida ya ja motar suka fita daga unguwar gabaki daya suka hau titi tukunna yai parking ya nutsa hankalinshi kan safiyya dake zaune ta hade jiki tana wani irin kuka.

Dafe kai yayi. Tuqa motar yai saboda yamma ta soma yi likis. Yanzun a kira magrib. Insun je gida ya san yanda zaiyi da ita.

*

Da zazzabi ta kwana ruf a jikinta. Dayai maganar suje asibiti ma kuka ta sake saka mishi dole ya hakura ya kyaleta.

Da safe ma shiya tayata har wanka tayi fuskar nan ta kumbura. Shima yai wanka tunda ranar zai tafi.

Saida ya gama shiryawa tsaf tukunna ya dawo inda take kwance.

"Kina so inyi menene? In tafi inbarki da wannan damuwar?"

Shiru tayi tana kallonshi. Saboda bazai taba fahimtar abinda take ji ba.

Ya ci gaba da fadin.

"Na gaya miki ba jimawa zan ba. Idan na dade sosai sati hudu. Kuma ina da kwanaki da yawa.

Na miki alkawari zan nemo su sofi. Duk inda suka je ni zan nemo su. Ko baki yarda dani bane?"

Da sauri ta dago ta kalle shi. Ta kasa magana. Kawai so take ya mantar da ita ciwon da take ji a zuciyarta ko na awa dayane.

"Please......"

Kawai ta furta tana barin idanuwanta na nuna mishi bukatarta. Lokaci ya kalla. Awa daya da rabi yake da ita kamun jirginsu ya tashi.

Hannunshi ta kamo tana mishi wanni kallo daya batar mishi da tunanin da yake yi.......!"

*

Tun yana wanka yake jinjina kuskuren dayai. Son safiyya ya rufe mishi ido.

Ko da yake babu yanda za.ai ace rabo ya gifta a dai dai lokacin nan. Beside yadai kusa maganin matsalar gabaki daya.

A gurguje ya shirya. Kissing safiyya kawai yayi yana fadin.

"Sai munyi waya. I love you......"

Sannan ya fice daga dakin da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke tana lumse idanuwanta........ !

*#TeamAS*
[7/5, 11:20 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:21 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 29
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

29

*Kuyi hakuri. Saboda chapter din tayi tsaho bazan samu saka sakonninku ba. Kuci gaba da turomun ra.ayoyinku AKAN SO. Zamu hadu a chapter na gaba in shaa Allah. Nagode*

"Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji kazo ka dauke ni please"

Dariya lukman yayi ta cikin wayar sannan ya amsa da.

"Ni nace kazo babu sanarwa. But seriously ban sa ranka yau ba. Duka satinka uku ko?"

Daquna fuska fu.ad yai hadi da fadin.

"Oww lukman. Surutun nan in kazo munyi. Ka taho nidai"

Dan jim lukman yayi kamun yace.

"Ba wani dan ladabi"

"Please.."

Fu.ad ya fadi yana kashe wayar da alkawarin shake lukman in ya karaso.

So yake yaga fuskar sofin shi saboda sam bata sa ranshi ba. Daya kirata jiya harda kukanta saboda yace bazai dade ba yana kuma gaya mata saiya kara kwana goma.

Murmushi yake tayi shi kadai. Yana hango soyayyar da zai nuna mata yau din nan. Ji yake kaman yai tsuntsuwa ya karasa gida.

Motar lukman ya hango. Ya mike bashida kayan komai sai jakar system dinshi. Hannunshi cikin aljihun 3-quarter dinshi ya taka zuwa inda lukman yai parking.

Ya bude motar yana fadin.

"Allah yai maka yanda kamun lukman"

Dariya yai yaja motar.

"Ya hanya?"

Lukman ya bukata. Hararshi fu.ad yai ya sake yin dariya.

"Da na taimaka nazo? Bacci nake wallahi ka wani tashe ni"

Wannan karin fu.ad din ne yai dariya.

"Haneef na kira nace yazo ya daukeni. Zagina ma yai"

"Madallah. Nima kawai saboda safiyya. Da sai dai ka shiga taxi"

Hira suke jefi jefi da lukman har suka karasa. Bai shiga da motar ba iya kacin shi kofar gidan fu.ad din.

"Zan shigo anjima in shaa Allah. Ka gaishemun da hajiya please"

Tabe baki lukman yai.

"In ka shigo kaje da kanka"

Ficewa fu.ad yai daga motar yana fadin.

"Zanzo dinne ai. Sai anjima"

"Ka gaida safiyya....."

Wucewa fu.ad din yai. Lukman ya juya da motar.

*

Zaune take kan kafet tana yanke farce. Kwankwasa kofa taji anyi. Bata kawo ma ranta komai ba tace.

"Shigo....."

Zatonta ma anty laurat ce. Tunda suna hutu yanzun. Wani lokacin indai ta fito takan biyo su gaisa da safiyyar.

Dago kai tayi dataji an turo kofar. Wani ihun murna ta saki ta tashi da gudu ta karasa ta rukunkume shi.

Dariya yake shima hugging dinta yai sosai. Sun jima a haka sannan ya sake ta yana sumbatarta.

"I miss you sosai sofi"

Ta kasa daina fara.ar da take yi. Hannu tasa tana jan kumatunshi.

"Shine kace mun sai nan da kwana goma ko"

Rike hannunta yai yana fadin.
"Wayyo sofi. Yi hakuri ina son surprising dinki ne fa"

Jakarshi tasa hannu ta cire daga bayan shi tana kama hannunshi. Kan kujera ta ajiye jakar a hankali dan tasan system dinshi ce a ciki.

Zama yai yana kwance igiyar takalminshi. Ya ajiye su gefe ya sauke mata idanuwanshi dake cike da gajiya.

"Yunwa sofi"

Hannunta rike sa kugu ta harare shi a zolayen ce. Hadi da fadin.

"Bansan da zuwanka ba ai. Banda abinci"

Ware idanuwanshi yai akanta. Ya yamutsa fuska.

"Da gaske?"

Kai ta daga mishi alamar eh. Kai ya dafe dan inyace har saiya fita ya siyo abinci yunwar nan ta gama wahalar dashi.

Coffee ne kawai a cikinshi. Shima dan baccin daya ji yana jine ya sha. Baici komai ba.

Ganin yanda yai da fuska yasata kwashe wa da dariya. Kitchen ta wuce ta samu plate ta zubo mishi taliyar datai jalof da dankalin turawa.

Duka ta juyo mishi dan tasan da wahala ma ta ishe shi. Tana gamawa ta zuba ma maigadi da mama indo nasu ta juye tata a warmer.

Bama taci ba ashe rabonshi ce. Da cokali ta taho mishi da cup. Ta soma ajiye abincin kan table taja shi zuwa inda yake.

Sannan ta wuce ta zubo mishi lemo a cup din ta hado da robar ruwa. Tana fadin.

"Bari ko dankali in kara soya maka...."

Da sauri yace.

"Dawo please. Wannan zaiyi rikeni na wani lokaci. Zauna kawai inganki"

Murmushi tayi. Ta samu waje ya zauna tana kallonshi yana cin abincin cike da yanayin nan da yake burgeta.

Hira suke danyi kadan kadan harya gama. Rakashi tai ya shiga wanka ta zauna ta jirashi ya fito.

Ita ta tayashi shiryawa ya gama tsaf sannan yai kissing dinta.

"Bara inje gida sofi. Inma dauko mana wata motar nagaji da wannan"

Murmushi tai mishi.

"A dawo lafiya. Ka gaishe dasu"

Tare suka fita falo ya dauki jakar system dinshi ya fice. Kitchen ta shiga ta dora indomie.

****

Su hussaina na islamiyya. Bai samu kowa gidan ba sai momma da haneef.

Take fada mishi babban yaya ma yai accident amman da sauki tunda babu karaya sai ciwuka.

Sama yahau ya samu haneef suka gaisa.

"Muje gidan babban yaya mana in duba shi"

Gyara kwanciya haneef yai.

"Sa.ankane ni da zamu jera muna zuwa unguwa tare"

Dariya fu.ad yayi.

"Dan Allah"

"Ka kyaleni fu.ad bacci zanyi"

Daga nan saman fu.ad ya wage baki yana kiran.

"Mommaaa!!! Kice haneeef ya rakani!!!"

Mikewa haneef yai yana toshe Kunnuwa fu.ad ya kama dariya.

"Wallahi ranka zai mugun baci. Kaje ku tafi da kukman mana"

Juya idanuwanshi fu.ad yayi.

"Hajiya ta aiki lukman. Ka tashi muje tare"

Yasan halin fu.ad sarai bazai barshi ya huta ba inba tashi yai ba. Dole ya mike suka fito tare.

Motar fu.ad din suka shiga. Haneef ya dauke jakar system dinshi dake ajiye a inda zai zauna.

Saida ya zauna ya dora jakar kan cinyarshi. Fu.ad yaja motar suka tafi.

*

Basu wani dade gidan babban yaya ba. Dan yama fita sai matarshi kawai suka gaisa da.

Fu.ad din yace a gaishe masa dashi zasu dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kaimu.

Sun fito suna hanya ne fu.ad a dole saiya tsaya ya siyi shawarma. Biris yai da tsegumin da haneef yake mishi.

Yai parking din motar ya fice. Siyowa yai ya dawo suka wuce gida zai ajiye haneef din.

Fu.ad ya fara fitowa daga motar. Haneef ya bude motar shima yana fitowa jakar dake hannunshi yakai zai ajiye zip din ya bude.

Da sauri ya tare system din da takardun da suke kokarin zubowa yana fadin.

"Ya Rabb......."

Komai yake kokarin gyarawa yanda yake wasu takardun asibiti suka ja hankalinshi. Zaro su yai ya rufe motar yana dubawa.

Fu.ad ya zagayo bangaren haneef din. Das yaji gabanshi ya wani fadi ganin takardun da suke hannun haneef.

Har ranshi yai niyyar gaya mishi amman ba yanzun ba. Sam ba ta haka yaso haneef yagani ba.

A hankali yace.

"Haneef....."

Hannu kawai haneef ya daga mishi fuskarshi kafe kan takardun dake hannunshi. Lumshe idanuwa fu.ad yayi.

Baya son damuwa da wani ciwon kai. Fuska haneef ya dago ya kallo fu.ad da wani irin yanayi da yasa zuciyar fu.ad dokawa.

Kallon shi haneef yake yana so yaga ina kaninshi yake. Kaninshi daya san bazai taba wannan abin bai shawar ce shi ba.

Kaninshi da bazaiyi wannan rashin hankalin ba. Wannan ba fu.ad din saya sani bane. Wani fu.ad ne a tsaye a gabanshi da baisan daga inda ya fito ba.

A tsorace fu.ad yace.

"Haneef nine...."

Saboda ya karanci kallon da haneef din ke mishi. Takardun ya sake kallo ya dago ya kalli fu.ad. Girgiza kai fu.ad yake ganin katangar da ke ginuwa tsakanin shi da haneef din lokaci daya.

Tunda yake a rayuwarshi bai taba jin yayi kuskure har cikin ranshi ba kamar yanzun. Kuskuren daya shiga tsakanin shi da dan uwanshi.

Cikin gida haneef yai da takardun a hannu. Da gudu fu.ad ya bishi yana fadin.

"Haneef. Ka saurareni dan Allah....."

"Mommaaaaaa!"

Haneef ke kiranta. Hannunshi fu.ad ya riko ya fisge yana ture fu.ad din.

"Don't. Just don't....."

Fuskar haneef daya kalla yasa shi tsayawa kawai yana dafe kai.

"Damn.....!"

Momma ce ta fito daga daki da sauri kallo daya tai ma yanayinsu tace ma haneef.

"Lafiya? Me ya faru?"

Dai dai lokacin da abbah yai sallama. Momma ta amsa mishi. Ganin su cirko cirko yasa shi cewa.

"Me ke faruwa ne?"

Kallon haneef momma tai. Shikuma ya kalli fu.ad idanuwanshi da wani irin distant look a ciki. Har yanzun ya kasa yarda da abinda yake gani.

Takardun ya sake dubawa dan ya tabbatar da gaske ne abinda yake gani fu.ad ya aikata.

"Fu.ad wai lafiyarku kuwa? Kuna ji anata magana kunyi shiru"

Cewar momma a tsawace. Idanuwa fu.ad ya sauke a kanta. Shi baima niyyar gaya musu ba. Daga lukman sai haneef.

Sake kallon haneef yai da idanuwanshi yake rokonshi da abin ya tsaya tsakaninsu. Kai ya girgiza mishi ya maida hankalinshi kan momma.

Sannan ya dubi abbah. Pha.iza ce ta fito daga kitchen itama tai tsaye tana kokarin fahimtar abinda ke faruwa.

Cikin wata irin murya da wani yanayi a fuskarshi haneef yace.

"Momma fu.ad. Fu.ad bashi da hankali ko kadan.........."

Kanshi ya nuna da duk hannayenshi ya ci gaba da fadin.

"Ni banda wata daraja a idanuwan fu.ad ban isa ya fadamun ba kamun yai wannan haukan"

Ya karasa yana mikama momma takardun data karba bakina sake. Lumshe idanuwa fu.ad yai hadi da fadin.

"Haneef......"

Hannu ya daga mishi alamar baya son ji. Sannan ya juya ya sauke idanuwanshi kan fuskar fu.ad.

"Bana son ji. Bana son jin duk wani abu dazai fito daga bakinka........"

Takardun momma ke dubawa hannunta har rawa yake. Idanuwanta sun tsaya kan kalma daya *VASECTOMY*.

Cikin kanta take duddubawa inda ta adana bokonta take son fahimtar kalmar. Kai take girgizawa. Abbah dake tsaye ya karaso ya karbi takardun daga hannunta yana fadin.

"Wai menene?"

Dubawa ya shiga yi. Jingina da bango fu.ad yayi yana jin kaman ace yana da wani sihiri da zai iya bacewa bat.

Su neme shi su rasa da su tirke shi kan abinda yake tunanin bai shafe su ba. Rayuwarshi ce ba tasu ba.

Wani irin kallo momma take ma fu.ad muryarta na rawa tace.

"Kace mun kokarin yi kake baka aikata ba......"

Abbah ma idanuwa ya zuba mishi. Yana jiran yaji amsar dazai bayar dan ji yake zuciyarshi har wani daci daci take yi saboda takaici.

Duk wata kaddara mai muni da zata auka mishi daga fannin fu.ad take tasowa. Yau shi ya haifi yaron da baya son haihuwa.

Daya bayan daya fu.ad ke kallon fuskokinsu. Cikin sanyin murya yace.

"Na riga nayi momma. Shi ya mayar dani wannan karin. Inajin cikin ku abbah ne kawai baisan bana son yara ba.

Na sha fada ba sau daya ba. Kuma a gabanku. Ban dauka dan nayi wannan zai zama wani babban abu ba..."

Wannan karin momma ce ta karasa inda fu.ad yake ta dauke shi da mari. Rike kunci yai yana kallonta cike da mamaki.

Abinda bata taba mishi ba tun daga yarinta sai yau. A kufule tace.

"Fu.ad ka fita idona wallahi. Har yaushe kai hankalin da zaka yanke irin wannan hukuncin"

Pha.iza kuwa tana ta ware idanuwa jin fu.ad yace.

"Banga wani abu a vasectomy ba momma. Rayuwata ce wannan saboda me zaku kasa fahimta....."

Da mamaki da wani yanayi momma ke kallon fu.ad. Daga hannu tayi zata sake marin shi abbah yai sauri ya rike hannunta da fadin.

"Ki rabu dashi kawai. Ba zamu zauna shi kadai yana bata mana rai ba.

Alhamdulillah tunda bashi kadai muka haifa ba. Kai da ba a haihuwa za a haifoka ne.

Duka shekarunka nawa da har zaka yanke hukuncin baka son zuri.a?"

In ran fu.ad yai dubu ya baci. Ya rasa meye abin daga hankalin cikin wanna abin. Jikinshi ne. Rayuwarshi ce idan basu bashi goyon baya ba sai su zuba mishi ido.

Kanshi a kasa yace.

"Abbah bani da wajen su ne a rayuwata. Yanzun nake kokarin building career ta.

Dame zanji? Me......"

Hannu abbah ya daga mishi yana jin kaman ya shake shi ya huta kawai. Muryarshi a dake yace.

"Duk wani abu daka sani naka ne a gidan nan ka kwashe. Aje ai building din career lafiya.

Kar kafarka ta kara shigomun cikin gida?"

Gabaki dayansu ware idanuwa sukai akan abbah. Momma kanta kallonshi take yi tana ganin tsaurin hukuncin daya yanke.

Su hussaina ne suka shigo da sallama an rasa me bakin amsa musu. Abbah suka fara rikewa da murna kamun hussaina taga fu.ad.

Da gudunta ta karasa inda yake ta riko mishi hannu. Duk da abinda yake ji bai hana shi yi mata wani guntun murmushi ba kamun ya maida dubanshi zuwa abbah daya ce.

"Kaji abinda nace. Kabarmun gida fu.ad kabarmin gida karka sake shigomun ballanta na inganka raina ya baci"

Momma ta kalli abbah kamun tai magana yace.

"Zabi biyu kike dashi. Ko ni ko danki. Nagaji da halinshi. Ban haifi yaron da zai samun hawan jini ba.

Tunda ban saka ma nawa iyayen ba."

Yana rufe baki ya juya ya nufi sashin shi. Wasu hawaye suka zuboma momma ta kalli fu.ad tace.

"Kaga abinda rashin hankalinka ya janyo ko"

Hussaina da bata fahimci meke faruwa ba ganin momma na kuka yasa ta kama ita. Pha.iza ma kukan take.

Wani numfashi fu.ad yaja yana jin gaba ki daya duniyar ta mishi zafi. Zuciyarshi yaji ta wani bushe. Saboda me abbah zai mishi haka.

Akan ya zabi ya tsara rayuwarshi ba tare da ra.ayin kowa ba. Hussaina dake rike da hannunshi ya kalla. Yasa hannu ya cire nata ya nufi sashinsu.

Kowa kallo yabi shi dashi harya bacema ganinsu. Dakin shi ya shiga. Jaka ya dauka ya bude wardrobe dinshi.

Kayane kawai a ciki. Gani yai babu abinda zai dauka ciki. Karema dakin kallo yake. Wani pink din hanky ya hango kan gadon shi.

Hussaina ta bashi shi. Bazai manta ba har yana ce mata na mata ne tace ta rubuta sunanshi a jiki da hannunta har cakewa tai da allura zaice baya so.

Hannu yasa ya dauki hanky din yana jin kaman ya ciro zuciyarshi ya ajiyeta gefe daya yadan huta. Dakin yake kare ma kallo.

Yana ma kanshi da zuciyarshi alkawarin kin sake tako gidan ma ballantana dakin. Bazai saka ma abbah hawan jini ba kaman yanda yace.

Lumshe idanuwanshi yai tamkar wanda yake son dibar duk wani memory daya taba spending cikin dakin ya adana su dan karsu bace mishi.

Jakar ya ajiye kan gadon saboda babu abinda zai zuba ciki. Wardrobe dinshi ya sake budewa ya dauki wata riga da momma ta taba siyo mishi.

Bai taba sakawa ba saboda ta mishi girma sosai. Ya ajiyene saboda yasan yanda ta siyo mishi rigar cike da kaunarta a wajenshi.

Kafarshi da wani irin nauyi ya ke takawa ya fito daga dakin. A hankali ya janyo kofar karar rufeta na rufewa da wani kyaure a zuciyarshi da baisan inda ya samo shi ba.

Dakyar kafafunshi suka kai falon. Suna tsaye inda yabarsu. Pha.iza ya fara samu. Tana tsaye tana kuka. Kallonta yake.

Muryarshi a dakushe da dacin abinda yake ji yace.

"Be safe. I will always love you"

Rike mishi hannu tayi tana wani irin kuka saboda ta kasa ma magana. A hankali ya zame hannunshi daga nata ta durkushe a wajen tana wani irin kuka.

Kome fu.ad ya aikata. Bataga dalilin dazai sa a kore shi daga gidan ba. Abbah ba kanshi kadai ya kamata ya duba ba har dasu.

Wajen momma ya karasa ya zuba mata idanuwa. So yake ya kalleta sosai dan zai musu nisan da bainsan randa zai sake ganin fuskarta ba.

Cikin kuka tace.

"Karkayi fu.ad karka sake wani kuskuren. Kaje gida zan shawo kanshi......"

Kaiya girgiza mata yana jin wani abu game da abbah daya kasa fahimtar ko menene. Zuciyarshi yaji ta kara bushewa.

"Momma ki yafemun. Zamana zai iya samar miki da matsala......"

Kasa karasawa yai saboda wani abu daya tsaya mishi a wuya. Wuce ta yai ya karasa inda haneef yake.

Baya kaunar abinda yake gani cikin idanuwan haneef sam. Baya son yanda yake kallonshi.

Karantar hugging dinshi da fu.ad ke shirin yi yasa haneef dan matsawa baya. Ware idanuwa fu.ad yayi da mamaki.

Cikin wata irin murya haneef yace.

"Inhar ka tafi karka dawo. Inka tafi ka tabbatar da ka barmu kenan. Ka tabbata shine kuskure na biyu mafi girma da za ka aikata........"

Wani abu daya tsaya mishi a wuya yake kokarin hadiyewa amman yaki wucewa sam. Shima haneef din ya tsane shi kenan.

Kallon shi yai sosai baice komai ba ya nufi hanyar waje. Da gudu hussaina ta bishi ta rike masa riga tana kuka.

"Ina zaka tafi wai? Momma kuce ya tsaya"

Lumshe idanuwanshi yai. Ya juyo ya tallabi fuskarta dake jiqe da hawaye. Rankwafawa yai ya sumbaci goshin ta.

"Duk nisan dazan kina zuciyata hussaina....."

Hassan ya kalla. Ya girgiza mishi kai hadi da fadin.

"Karka tafi. Kome kayi muna bukatar ka. Wazai je yaga ko zan iya zama dan ball nima?

Wa zai rabani fada da hussaina?"

Miyau fu.ad ya kara hadiya. Dakyar ya iya cewa.

"Ga haneef nan. Ga pha.iza gasu babban yaya"

Girgiza mishi kai hussaina take.

"Babu wanda zai somu kaman ka. Dan Allah karka tafi"

Banbare hussaina yake kokarin yi daga jikinshi. Pha.iza ta karaso inda suke idanuwanta a bushe.

Hussaina ta kama ta janye tace.

"Tunda ya zabi yabarmu ki kyale shi mana. Sai mu fasa rayuwa dan baya nan?"

A hankali yace.

"Pha.iza...."

Ware idanuwanta tai akanshi. Irin kallon da haneef yake masa yake gani cikin idanuwanta. Wani numfashi yaja kamun tace.

"Ka tafi abinka. Kaunarka ba zata kashe mu ba"

Jan hussaina tayi da take wani irin kuka tana kokarin kwacewa. Momma ya kalla ta kauda kai gefe.

Itama ya karanci zabin dasu haneef suka bashi take bashi batare data furta ba. Wucewa yai da duk takun da yake zuwa fita daga gidan yana jin yanda yake barin wani bangare na zuciyarshi.

Dakyar yakai mota. Ya bude ya shiga
Wani dishi dishi yake gani.......!

*

Ta rasa me yasa gabanta yake ta faduwa tun dazun. Wayarta ta dauko ta kira fu.ad har sau uku bai dauka ba.

Mikewa tai taje wajen window ta tsaya saboda haka kawai taji hankalinta ya kasa kwanciya. Tana nan tsaye taga motarshi ta karaso.

Wata ajiyar zuciya ta sauke saboda yanda taji hankalinta ya kwanta. Tana ganin ya fito daga mota ta karasa ta bude kofar.

Dai dai shigowarshi. Bai ko sallama ba yajata jikinshi yai hugging dinta. Wani sauki sauki yake ji a zuciyarshi.

Hugging dinshi tai itama tana karantar akwai abinda ke faruwa. A hankali ta zame jikinta ta daga kai tana kallon fuskarshi.

Wani irin haske taga idanuwanshi sunyi. Gabaki daya ya canza kaman ba fu.ad din data saba gani ba. A tsorace takai hannu ta taba kuncin shi.

"Menene?"

Ta tambaya da wani yanayi a muryarta. Hannunta ya rike ya sauke numfashi kamun yace.

"Abbah ya koreni sofi. Baya son in sake shigar mishi gida"

Ware idanuwa tai ta rike baki hadi da fadin.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un. Me kayi mishi? Ko akan aurenmu ne? Baka ce ya hakura ba...."

Ganin yanda ta rikice yasa shi rikota jikinshi. Kuka take wanda baya so saboda tana kara rikita mishi lissafi.

Tana kirjinshi kwance luf tace.

"Me kayi?"

A hankali yace mata.

"Vasectomy....."

Da rashin fahimta tace.

"Menene shi din?"

Dan bata san ma.anar abin ba bakuma taga alakarshi da korarshi da abbah yai ba. Muryarshi can kasa taji yace.

"Kwayayen haihuwata na kashe gabaki daya."

Kamar wadda akaima allurar rashin kuzari take dagowa daga jikinshi. Yana jin yanda take zamewa daga jikinshi.

Wani irin ihu zuciyarshi keyi. Kallon safiyya yake harta bar jikinshi ta sauke idanuwanta cikin nashi da wani yanayi.

Kunnuwanta ke amsa maganar da yayi. Takai mintina biyu tana tauna nauyinta. A hankali maganar ke yawata zuciyarta.

Tana gayama duk wani waje daya yarda da fu.ad

Please Login or Register in order to submit comment