Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soma cewa.

"umm.... Wallahi..... Ado..... "

Fu.ad dake tsaye kallon safiyya yake yanda ta rikice gabaki daya kamun ya maida kallonshi kan ado.

"Waye kai kuma din?"

Ya tambaya yana masa wani kallon wulakanci. Shima adon kallon da yake mayar masa kenan.

"Me kake tsaye da matata?"

Ya tambaya. Wata dariyar takaici fu.ad yake. Me ma sofi zatai da wannan dan kauyen. Kazamin yake tambayar kanshi. A fili kuma yace.

"Ka kama hanya kawai. And kar bakinka ya sake kiranta da matarka"

Ya karasa yana nuna safiyya dake tsaye kamar an dasata. Su jummai kansu baki bude suke kallon ikon Allah.

Cikin bacin rai ado yace.

"Lallai ma. Kaji mun wani karfin hali. Kai asuwa to? Malam tunda mutuncinka kabar wajen nan wallahi.

Bansan ya akai take tsaye dakai ba. Ba kuma zai sake faruwa ba dan matata....... "

Bai karasa ba ji kake wani tas! Fu.ad ya kwada masa mari. Ai kam ado ba tsaya jira ba ya kaima fu.ad din naushi a fuska.

Ramawa yai. Hashimu yai kokarin shiga tsakaninsu amman sai fu.ad ma ya sauke masa naushin dayake kokarin kaima ado.

Ko da wasa ba zaka hada girman jiki da karfin fu.ad dana ado shi kadai bama ballantana da hashimu.

Kamun kace wani abu hashimu yai sama da fu.ad ya tiqa da kasa.

Wata kara safiyya ta saki. Shi aka doka da kasa amman ciwon har cikin zuciyarta taji shi.

Dafe fuska tai da hannuwa biyu. Kota ko ina ado da hashimu suke turmusa fu.ad kaman wanda akaima wahayi.

Ganin mutane sun fara taruwa yasa jummai da lami jan safiyya tana turjewa tana wani irin kuka.

Janta suke tana kokarin komawa kaman zata shigar ma fu.ad da yanzun ya daina ma rama dukan da suke masa.

Duk sun fasa masa baki da gefen fuska. Ga shi sun turbuda shi cikin kasa yai futu futu.

Sannan mutane suka fara kula aka taru kansu. Dakyar aka janye ado daga kan fu.ad yana fadin.

"Kai din banza zaka zo har kauyenmu kai mana fitsara.

Wallahi ka sake dawowa sai dai waninka. Safiyya matata ce kana jina!!!"

Wasu ne suka kama fu.ad suka daga shi yana maida numfash. Ciwon dayake ji daban ne dana jikin shi.

Idanuwanshi da guda daya harya soma rufewa da alamar kumbura yake duddubawa baiga safiyya ba.

A firgice yake fadin.

"Sofi......... No.....Sofi......."

Wani mutum ne ya kama shi saboda yanda yaga kaman jini na kokarin dibarshi.

Duba shi yai yaga ya fasa bayan kai. Jini kuma bai bar zuba ba har lokacin. A rikice yace.

"Subahanallah. Dan Allah ku kamashi aje ko chemist ne jini yake zubdawa....... "

Ture shi fu.ad yai muryarshi harta soma canzawa. Hannu yasa ya dafe gefen kanshi yana fadin.

"sofi...... Ta tafi...... "

Wani ya dafa yana tafiya yana hade hanya. Mutane suka kamashi. Kanshi ya saki yana ture su.

Baya son taimakon kowa. Momma yake so. Gida yake son zuwa. Wannan fadan bana shi bane shi kadai.

Dole mutane suka sake shi saboda yanda yake ture su yana fadin.

"Fuck off!"

Wajen motarshi yana nufa. Kanshi ya sake dafewa yana jin wani luu. Da babu motar daya kai hannu jiki daya fadi.

Wani datijjo mai ruwan kamala ya dubi mutanen dake tsaye yace.

"Malam garba ka taimaka ma yaron nan mana. Ko gidansu ya fada a tukashi. Kana ganin yanda jini ke dibarsa"

Dayake malam garba direba ne. Yana jan motoci. Daga shi har datijjon mutanen arziqi ne matuka da ake girmamawa dagani da mutunci a unguwar. Babu musu ya karasa wajen fu.ad.

"Kai kam samari kabari a taimaka maka mana"

Dakyar fu.ad yace

"Ni gida zanje. Kaina...... "

"Sannu kaji. Ka fadamun inda kake sai inje in sauke ka. Ni direba ne"

A yanda yake jinshi kaman ba a duniya yake ba. Yasan bazai iya tuqi ba. Haka ya gayama malam garba inda zai kaishi.

Shi ya karbi mukullin motar. Ya bude ya kama fu.ad ya saka shi a ciki. Sannan ya kalli dattijon dayai magana yace.

"Sai inga wani yazo mu tafi tare. Dan gudun matsala"

Kallon kallo suke an rasa wanda zai bishi dan tunda sukaga motar fu.ad din kowa ya sha jinin jikinshi. Datijjon nan ya taka zuwa inda motar take yace

"Muje..... "

*

Sun nisa sosai. Sama sama fu.ad kejin ringing din wayarshi. Hannu yasa cikin aljihunshi ya zaro wayar da screen dinta ya farfashe.

Kanshi na wani irin juya mishi. Dakyar ma wayar ta dannu ya amsa ya kara a kunne.

"Ina ka shiga haka. Inata kira not reachable"

Dakyar ya iya ce ma haneef.

"Ka so dai dai dawanau. Please ka taho....... "

Cikin alamun razana haneef yace.

"Fu.ad are you okay?"

Da bala.in dauriya ya amsa shi da.

"kazo mana. Ka taho..... "

Yanajin haneef na magana amman bazai iya amsa shi ba
Kanshima wani ciwo yake da duk karar data shiga kunnen shi.

Dattijon dake baya tare dashi ya mika ma wayar da fuska yake rokonshi daya taimaka ya karba.

Karba yai ya kara a kunne hadi da sallama. A razane haneef yace.

"Waye kai? Me ya same shi ne wai? Kuna ina?"

A nutse ya fara ma haneef bayani da cewa.

"Ka kwantar da hankalinka. Mu taimakon shi mukai. Fada sukayi ne yadan samu raunuka. Kaman yanda yace kazo zamu tsaya dai dai dawanau"

Jin anyi shiru yasa shi mikama fu.ad wayar da yake jingine jikin kujera.

*

"Lafiya wai?"

Momma ke tambayar haneef da duk ya rikice.

"Momma fu.ad.....zan miki bayani...... "

Da gudu ya fita daga falon tana kwala masa kira. A harabar gidan yaci karo da lukman.

"Muje please...... "

Kawai yace suka bude mota. A hanya yake fada mishi iya abinda ya sani.

*

Dai dai dawanau suka hango Range Rover din fu.ad tsaye. Parking yai suka fita shi da lukman.

Wani dattijo suka hango tsaye jikin motar. A kagauce yace

"Yana ina?....... "

Lukman kam baibi takansu ba. Motar ya bude. Hannunshi yakai ya dafe kai. Kwata kwata kamannin fu.ad din sun sauya.

Ga wani numfashi yana ja dakyar. Rasa ina zai kama a jikinshi yai. Dan jinin dayake gani baisan daga inda yake fitowa ba.

Haneef ya zagayo ya ture lukman.

"Ya Rabb......... "

Ya fadi yana zira jikinshi cikin motar ya kamo hannuwan fu.ad ya tallaboshi ya fito dashi.

"Fu.ad......."

Yake kira amman da alamu ma baisan abinda yake yi ba. Daga shi yai cak a kafada ya nufi mota da gudu.

Lukman ne ya tsaya. Ya zaro kudi a aljihunshi ya kamo hannun dattijon nan ya damka mishi hadi da fadin.

"Mungode sosai baba"

Zagayawa yai inda malam garba yake ya karbi mukullin motar dake hannunshi ya ja motar yana bin bayan haneef.

*

Aminu kano suka nufa dashi. Suna karasawa sukai parking.

Haneef ya bude bayan motar. Lukman ya karaso suka tallabo fu.ad.

"Fu.ad....."

Haneef ya sake kira yana taba kumatunshi. Dakyar ya bude idanuwanshi kamun ya sake lumshe su ya wani langabe a jikin haneef din.

Kasa sukai a tare saboda wani nauyi dabai tsammani da fu.ad din yayi.

Lukman ya dafa a rikice yana fadin.

"Call for help........ "

Da sauri lukman ya tashi ya na karasawa cikin asibitin da gudu.

Girgiza shi haneef yake yana fadin.

"Wake up fu.ad.....su waye sukai maka haka?"

Wasu nurses ne suka fito da wheel chair. Kama fu.ad suka saka shi ciki.

Da sauri suka gungura shi. Wata nurse ke cema haneef.

"Ba zamu taba shi ba saida yan sanda gaskiya....... "

Kai kawai haneef ke jijjiga mata. Lukman ne mai karfin halin dauko waya ya kira su momma yake fada musu. Su taho da yan sanda.

Wani numfashi haneef yaja hadi da fadin.

"Am going to fucking end ko waye ya taba fu.ad............!"
[6/26, 7:32 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[6/29, 7:13 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 19
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

19

"Ya isa haka mana safiyya. Sai kinja ma kanki wani ciwon. Tunda kika ga har dare yayi haka da wahala ado yazo ya fadama su baba"

Jummai tace tana dan bubbuga bayan safiyya dake kwance jikinta tana wani irin kuka tun barin su wajen.

Lami tabe baki tayi.

"Ni inama mamakin kine wallahi. Duk abinda yai muku amman kice kin damu dashi?"

Idanuwanta ta dago cike da hawaye tace ma lami.

"Tun da ance miki zuciyata tasan wannan ko? Na gaya miki ne dan nai alkawari bawai dan ki auna mun abinda yake faruwa dani ba.

Nafiki sanin rashin dacewarshi"

"Ki rabu da lami kema safiyya. Allah dai ya kawo karshen abin. Bara mu tashi mu tafi gida. Sai kuma gobe in Allah ya kaimu"

Fadin jummai tana janye safiyya daga jikinta. Har suka sa kai suka fita daga dakin ta kasa ko magana.

Kukanta ta ci gaba dayi ko zataji sauki. Duk yanda fu.ad ya rama dukan dasu ado sukai masa bai mata ba.

Su biyu suka tarar mishi. Koya ta rufe idanuwanta sai taga hoton abin. Girman jiki da shekaru ta tabbata su ado sunfi fu.ad.

Wata tsanarshi ta kara cika mata zuciya. Wani irin abu take ji a zuciyarta. Fata take fu.ad din ya kirata taji lafiyarshi.

Abinda zai biyo baya bashi ke damunta ba. Lafiyar fu.ad a yanzun tafi mata komai.

****

"Haneef kaci wani abu mana"

Girgiza kai yai. Ranshi yana baci. Amman bai taba kai matakin na yau ba. Dan har wani duhu duhu yake gani cikin idanuwanshi.

Wani abu yake so yakaima duka koma menene yadan rage abinda ke boiling a zuciyarshi.

Daga shi sai lukman zaune a dakin da aka kwantar da fu.ad. Bayan tabbatarma da su haneef cewar zai tashi.

Yadai samu concussion saboda buguwar dayai akai. Amman komai lafiya kalau. Yana bukatar hutu ne.

"Allah lukman ko su waye sai sun gane kurensu.... "

Wani numfashi lukman ya sauke.

"Fu.ad din dai ya tashi muji ya akai"

A kufule haneef yace

"I don't care ko shine bashi da gaskiya. Abu daya nasani. They are going to pay for this"

Shiru lukman yayi. Dan ko shi tun tasowarsu a yarinta bai taba ganin ran haneef ya baci haka ba.

Asali ma shine yake kokarin basu hakuri in wani abin ya taso.

*

Nan suka kwana tare da haneef. Tunda safe lukman ya tafi saboda yana da lectures.

Har wanka nan haneef yayi. Da su pha.iza zasu zo suka taho masa da kaya. Har suka gama zamansu suka tafi fu.ad bai farka ba.

Haneef na zaune yana karatu da wayarshi yaji kaman an motsa. Wayar ya ajiye ya matsa sosai kusa da fu.ad.

Motsawa ya sake yi. Ya dafe kanshi yana fadin.

"Owwhh....... "

"Fu.ad?........"

Idanuwanshi ya bude a hankali. Ya samu yan mintina yana tunani kamun komai daya faru ya dawo mishi.

Abu dayane ke masa yawo cikin kai.

Mikewa yai da saurinshi. Haneef ya kama shi dam yana fadin.

"Kabi a hankali. Baka ganin ruwa ne a jikinka"

Muryarshi a dakushe yace.

"Tun yaushe nake nan?"

Da mamaki a fuskar haneef ya amsa shi da.

"Tun jiya"

Dafe kai yayi. Bashida lokaci mai yawa. Gobe ne daurin auren safiyya.

Ganin da gaske saukowa yake sonyi daga kan gadon yasa haneef fadin.

"Ka nutsu mana. Ina zakaje ne haka?"

Yana dafe kanshi dake juyawa. Yace

"I need to go haneef. Ba zaka gane bane. I have to........."

Tunanin haneef ko buguwar da fu.ad yayi akaine take son bashi matsala. Mikewa yai yana fadin.

"Koma ina ne zakaje. Ka jirani anan. I will be right back."

Kamun ya amsa shi ya fice daga dakin da sauri yana barin fu.ad zaune.

Karin ruwan da ke jikinshi ya cire. Kalle kalle yake cikin dakin. Yako hango mukullin motar haneef.

Dauka yayi. Yanajin kanshi na wani sarawa kaman zai balle ya fadi. Takalmanshi dke ajiye a gefe ya dauka.

Dakyar ya saka su. Ya lallaba ya fice daga dakin yana nufar hanyar da zata fitar dashi daga asibitin.

*

Haneef kam fita yai danya kira doc ya fada mishi fu.ad ya farka. Yaci karo da wani abokin shi da tun da suka gama secondary school rabon dasu hadu.

Aka tsaya ana gaisawa. Yake tambayarshi kowa ya kawo.

"Brother dina ne. Nama fito ne in kira doc. Kaifa"

Abokin ya amsa shi da.

"Matar brother dina akaima aiki. Ka fadamun number din dakin da kuke. In na fito sai in shigo duba shi"

Fada mishi haneef yai. Sukai exchanging numbers sannan ya wuce yai magana da wani likita.

*

Dakin yagani wayam. Ya girgiza kai. Zaton shi fu.ad na bandaki. Dan hauka kuma ya cire ruwan.

Zama yai kan kujera yana jiran ya fito. Har likitan daya kira ya shigo amman fu.ad shiru.

Da kanshi ya tashi yaje yai knocking kofar bandakin hadi da kiran sunanshi. Nan ma shiru kakeji.

Turawa yai.

"Ya Allahu......."

Ya fadi daya ga fu.ad din baya ciki. Dawowa yai dakin ya sake dubawa ko dai idanuwanshi sun samu damuwa.

Mukullin motar daya ajiye kan drawer ya kai idanshi kai baya wajen. Aiko takan likitan dake tsaye haneef baibi ba ya bude dakin yana fita da gudu.

Inda yai parking mota ya karasa baiga motar ba. Tsaye yai dan ya rasa me ma ya kamata yayi.

****

Inna ce zaune kusa da safiyya da tun jiya wani irin zazzabi mai zafi ya saukar mata.

Ga ciwon kai. Abinma karuwa yai da taji fu.ad bai kirata ba ballantana sakon shi.

Dafata inna tayi.

"Safiyya ko dai muje asibiti"

Girgiza kai tayi. Idanuwanta na cika da hawaye. Yanzun ta kara tabbatarwa ba zata iya zama da ado ba.

Ji take in ta aure shi mutuwa zatai ko da kuwa ba zata sami fu.ad ba. Muryarta na rawa da sauri dan karta kasa tace.

"Inna dan Allah a fasa auren nan...... "

A razane inna ta dafe kirji.

"Subahanallahi. Safiyya? Meya shigeki haka? Kinsan me kike fada kuwa?"

Hawayen da suke idanuwanta suka gangaro. Kai ta daga ma inna alamar tana sane sannan ta ce.

"Inna dan Allah....."

Rufe mata baki inna tai. Dan jikinta har kyarma yake kar wani ma yaji me safiyya ke fadi.

"Zafin zazzabine kawai safiyya. Kiyi shiru karma wani yajiki. Bari inga ko usman ya kawo maganin"

Mikewa inna tai ta fice daga dakin. Tabar safiyya ita kadai.

Hijab din dake jikinta taja ta rufe kanta tana ci gaba da wani kuka marar sauti dayake fitowa daga zuciyarta.

Ba magani take bukata ba. A warware maganar aurenta da ado shi ne kwanciyar hankalinta.

Ga fu.ad shiru har yau din nan babu kiranshi babu sakon shi. Addu.o.in duk da suka zo mata ta shiga jerowa tana fatan Allah daya dora mata wannan abin ya kawo mata mafita.

****

Wani irin gudu yake da motar. Koda yaganshi kan titin gidan su safiyya bai tsaya ba. Inda ya saba tsayawa yaja motar ya tsaya.

Aljihunshi ya laluba. Ya sauke wata ajiyar zuciya hadi da godema Allah jin wayarshi na ciki.

Kunnata yai yaga ta sake mutuwa alamar babu chargy a jiki. Cikin motar yasa chargy yai zaune yana jingina kanshi da sitiyari.

Wani irin dokawa zuciyarshi take kamar zata fito daga kirjinshi. Hanya daya ce ta rage masa akan safiyya.

Hanyar dayake tsoron safiyya ba zata taba amincewa tabi tare dashi ba. In kuwa har bata bi ba baisan me zai iya faruwa dashi ba.

Wayar ya duba yaga ta dan hau. Hannunshi har rawa yake ya dubo lambarta yai dialing.

Bai taba jin tashin hankali irin na yau ba tunda yazo duniya. Cikin shi ya wani kulle.

*

Wayarta taji tana vibrating. Da sauri ta mike daga kwanciyar da take ta dauko ta.

Dannawa tai ta kara a kunne tanajin wanni sanyi na ratsa ta. Har zazzabin da takeji ya soma sauki.

"Kana lafiya? Ba abinda ya same ka ko?"

Safiyya ta tambaya muryarta na rawa saboda wasu sabbin hawaye dataji sun zubo mata.

Shima tashi muryar na rawa yace.

"Ina inda kika sameni jiya. Ki fito please. Ki fito tukunna insan ko zan sami lafiya ko bazan samu ba"

Kamun tace wani abu ya kashe wayar. Zuciyarta kawai tabiyewa ta mike. Fitowa tai daga dakin. Mutanene cike da gidansu anata hidima.

Buta ta dauka dake can gefe kaman zata shiga bandaki. Ta tsaya jim taga ko wani na kula da ita.

Hidimarsu suke tasha. A hankali gabanta na wani irin faduwa ta wuce da sauri ya nufi soro.

Jin kafafuwanta take kaman na roba tsabar tashin hankali da zullumin kar wani yaganta da take ciki.

Hijabinta ta jawo ta sama tana sake rufe fuskarta dan kar wani yagane ta.

Unguwar shiru kaman babu mutane. Mamakin kafafuwanta takeyi. Har sarkewa suke su kadai kaman wanda babu kashi a ciki.

Motar data gani duk sa bata taba ganin kalarta ba yasa tasan fu.ad ne a ciki. Ta karasa tana dube dube ko wani na ganinta.

*

Yana zaune sai zufa yake kaman babu Ac a motar. Wani irin yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa.

Idanuwanshi nakan hanya yana kallon ta inda zata bullo ya hangota. Wani dan karamun relief yaji.

Bude murfin motar yayi yace mata.

"Shigo Sofi..... "

Idanuwan nan nata dake hargitsa masa tunani cike da tsoro ta sauke masa hadi da girgiza kai.

"Dan Allah ki shigo muyi magana. Ko kina so wani yaganki?"

Da alama maganarshi tai tasiri dan shiga motar tayi da saurinta. Hannu yakai ta rakube jikinta.

Gyarawa yai ya rufe motar. Yana kallon yanda ta matse jikin kujera kaman zata shige ciki dan kar hannunshi ya taba jikinta.

Gyara zama yayi.

"Ni bansan ta inda zan fara ba"

Ya fadi yana murza zoben dake yatsanshi kaman zai bashi idea ne.

Safiyya kam gabanta ke wani irin faduwa. Dan sauran hankalinta na son tai amfani dashi wajen tunani amman zuciyarta ta fi karfin shi yau.

Ita ke da mulkin a hannu. Ganin fu.ad. fuskar shi da take a kumbure. Sanin sanadinta ne hakan ya faru dashi.

Jin muryarshi. Komai saiya karasa kwacewa daga hannun ta. Yau zuciyarta ce da mulkin. Saidai tana tsoron hukuncin da zata iya yanke mata.

A tsorace da abinda zai iya biyowa fu.ad yace.

"Naso ace iyayenki sun bani aurenki lokacin da akazo nemar mun sofi......

Bamu da lokaci. Gobe war haka na rasa ki......"

Muryarshi ta wani makale saboda abinda yake ji a zuciyar shi.

Lumshe idanuwanta tayi. Tunanin maganarshi na mata yawo. Gobe warhaka ta zama mallakin ado.

Girgiza kai take. Ba zata taba iya zama da ado ba. Wautar amincewa aurensa take gani karara.

Wani kuka ya kwace mata. Ganin hakan ya sake dagama fu.ad hankali.

Jin kukan yake yana wani ci masa rai.

"Sofi..... Please. Hanya daya muke da ita. Kizo mu gudu! Kibini muje a daura mana aure a wani waje........ "

Da sauri take masa wani kallo dake fadin tabbas bashida hankali.

Hakan ya karanta yasa shi karawa da.

"Karki mun haka sofi...... Wallahi zan iya mutuwa. Zuciyata zata iya tsayawa in kika auri wani....... "

Kuka take sosai. Zuciyarta nason amincewa abinda fu.ad din yazo dashi. Bayan haka ma ai aure yace zasuyi ba wani abin ba.

Cikin kuka tace.

"Inna fa? Ga baba ma. Ince musu me? *Akan So*nka nabarsu?"

Abinda ko da wasa wani yace zaiyi a shekarunshi abin ba karamar dariya zai bashi ba wato kuka.

Hawaye ne yake jinsu cike da idanuwanshi yau. Shi fu.ad zai kuka wa wata mace.

Cikin rawar murya yace.

"Ki kalleni mana ni. *Akan so* yau ni fu.ad zan iya yin komai sofi. *Akan so*nki komai ya warwaremun.

Inna da baba zasu gane. Bawai mun tafi kenan ba. Zamu dawo muyi musu bayani"

Ganin yanda kalamanshi ke shirin yi mata tasiri yasata bude motar ta fita. Da sauri ya bude yana rufa mata baya.

Tsugunnawa yai kasa. Gwiwa biyu yana fadin.

"Sofi.... Karkimun haka. Dan Allah karki auri wani"

Kallonshi take. Bata damu da duk wanda ma zai wuce ba. Hawaye tagani yana zubo masa.

Yana kallonta da idanuwansa da take karantar rokon da zuciyarshi take mata ta cikinsu.

Zuciyarta a dake tace.

"Ka jirani. Ka jirani anan. Inhar da gaske kana sona zaka jirani.

Zanyi wani abu guda daya. Inhar baiyi dai dai ba zan dawo....... "

Kamun yace komai ta juya ta koma. Idanuwa ya bita dasu yana kallonta.

Mikewa yai ya koma kusa da motarshi yana jin kaman a tashi rayuwar komai ya kare.

Zamewa yai jikin motar yana zama a kasa. Cikin dattin dake wajen. Ko damuwa bai ba.

Kanshi ya hada da gwiwarshi wasu hawaye dabai san ta inda suke fitowa ba suna zubar mishi.

Tari yaji ya soma zuciyarshi na wani irin zafi. Kamar iskar dake cikinta na fita.

*

Da wani irin karfin gwiwar da batasan daga inda yazo ba. Ta shiga gida. Inna ta hango. Ta karasa wajenta. Hannunta ta kamo tajata zuwa daki.

Ita kanta innar mamaki ya hanata magana. Haka tabi safiyya baki a sake.

Sakin hannun inna tai ta tsugunna kasa ta rike kafafuwanta. Idanuwanta sun wani bushe.

"Inna dan Allah kar a auramun ado. Wallahi bana sonshi. Wallahi zan iya mutuwa idan na auri ado"

Salati inna ta saka. Tana kara wani kan wani. Ko dai asiri akaima safiyya ne haka. Wannan wanne irin abune.

"oh ni. Safiyya wai me ya shiga kanki haka? Gobe fa daurin aurenku. Sannan zakice bakya son shi?

Aikin ke bakinki yake wata bakwai da suka wuce?"

Girgiza kai safiyya take. Inna ta gane mana. Ta fahimci amsarta ita zata yanke mata decision din da take son dauka.

Da faduwar gaba da inna keta fama dashi tun jiya tace.

"Kinga kiyi shiru. Wallahi inhar babanku yaji maganar nan ranki da nawa inyai dubu saiya baci.

Kinfi kowa sanin baya magana biyu. Ko da gawarki za akai gidan ado saikin aure shi.

Kar kuma na sake jin wannan sakarcin dan karma wani yaji baki ya kamaki"

Kan safiyya a kasa tace.

"Ki gafarceni inna. Kice ma baba ma ya gafarceni"

Kamata inna tai tana janyewa daga jikin kafarta. A tausashe tace.

"Bakomai safiyya. Kita addu.a kinji ko? Kinga mutane na jirana. Nasan su lami zasu zo babu jimawa"

Batace komai ba har inna ta fito. Kar wadda take cikin trance haka take jinta. Mikewa tai.

Harta fice babu wanda ya kula da ita. Wani abu can cikin ranta da batasan ko menene ba yanata mata wasu maganganu da bata ganewa.

Bakuma ta fasa tafiya tana nufar inda motar fu.ad take ba.

*

Baisan iya lokacin daya dauka nan zaune ba. Kawai dai yasan komai ya kare masa.

Da tafiyar safiyya ta tafi da duk wani farin ciki nashi. Ya rasa meke ja masa tarin nan dake sarke shi.

Numfashin shi ne yake fita dakyar dakyar. Kaman daga sama yaji tace

"Muje....... "

Sam baiji zuwanta ba sai muryarta. Dago kanshi yai. Yana ci gaba da tarin dake tsayar masa da iska.

Dakyar ya iya cewa.

"Sofi kece ko dai nine nake hallucinating?"

Tsaye tai bata ce masa komai ba. Ita kanta ji take kamar ba ita ba. Kamar wani abunne yai taking control din jikinta yake aiwatar da komai.

Mikewa yai. Ya bude mata mota yana kallo ta shiga. Tsaye yai na yan mintina yana kallonta.

Gani yake kamar zata bace. Kamar komai dake faruwa mafarkine kawai dazai iya farkawa ko da yaushe.

Tuqi yake yanayi yana kallon safiyya ko zata bace. Tana nan zaune. Banda fitar numfashinta dayake ji.

Zaka iya rantsewa bata motsi.

Safiyya kam har lokacin wani shiru take ji cikin kanta. Wani abu ke shirin faruwa da ita. Tana ji a jikinta.

Wani abune mai girma data kasa tsayar da aukuwarsa. Gaba daya kamar wadda ta rasa hankalinta take ji.

****

Momma ya fadama duk abinda ya faru. Da yanda ya dauko taxi zuwa gida.

Salati take.

"Anya ba asiri akaima fu.ad ba? Ko dai aljana ce ya hadu da ita? Wannan wanne iri bala.i ne?"

Haneef dake zaune ya karbi ruwan da pha.iza ta miko masa.

"Wallahi ni abinma tsoro yake bani kuma. Banma san me zan ba?"

Pha.iza ce tace

"Mubi shi ko can din ya nufa"

Kai haneef ya daga mata yana fadin.

"Bara inji ko lukman ya dawo gida. Bazai ji dadi mu tafi babu shi ba"

Momma dake tsaye ta rasa abinda zatayi tace

"Bara nima in kira abbanku in sanar dashi. Ya kamata a dauki mataki ba sai yaje ya kashe kanshi ba"

Wuce wa tai zuwa dakinta inda tabaro wayarta. Tabar haneef din da pha.iza ana dan yan biyu suna makaranta.

****

Baisan inda zaiyi dasu ba. Baisan wa zai kira ya daura musu aure ba.

Baisan me zaiba. Bayason ya kira lukman ko haneef. Yasan babu wanda zai goyi da bayanshi.

Saboda babu wanda yake gane abinda yake ciki. Ko yake ji. Hamza ya kira suna shiga cikin kano ya fada masa inda zai zo ya same su.

*

Cikin mota yabar safiyya. Ya fita sukai magana da hamza ya fada masa abinda yake so da kuma yanda yake a shirye daya biya koma nawane.

Yasan malamin da da dubu goma zai daurama fu.ad aure. Saidai shi kanshi yana ganin rashin hankalin fu.ad din.

Duka duka nawa yake dazai jajibo ma kanshi aure. Jin yai shiru yasa fu.ad fadin.

"In baka sani ba ka fadamun in nemi wani"

"Sorry. Dadina dakai gajen hakuri"

Bayanin komai hamza yai mishi. Wajen hamza ya ranci kudi dan bai fito da atm dinshi ba suka tafi.

Har lokacin safiyya kaman ba a hayyacinta take bata san meke damunta ba.

****

Momma, haneef, lukman, pha.iza, yan biyu, abbah su duka suna zaune a falo jugum.

Har bichi su haneef sunje basu ga fu.ad ba. An kira duk wasu abokai da ake tunanin ko yana tare dasu amman shiru.

Sam basu san inda yai ba. An kira wayar shi a kashe. Gaba daya hankalin su a tashe yake.

Dan hussaina ma kuka take tayi tunda wuka dawo makaranta aka fada musu.

Abbah na shirin tashi sukai report police station sukaji sallamar fu.ad.

Mikewa sukai su dukansu. Momma na hamdala da Allah ya dawo mata da danta lafiya.

"Ina kaje haka fu.ad?"

Haneef ya tambaya. Kan fu.ad din a kasa har

Please Login or Register in order to submit comment